[02/06 16:26] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *ROMON HAƘURI* 🤍 MRS SADAUKI ✍️ FCWA ☀️ *Wannan labari ba ƙirƙira ba ce,labari ne da ya faru a gaske ina fatan za ku bibiye shi sau da ƙafa* *__________________________________________________* 01 Wuri guda na ƙara curewa ina kallon yadda magen ke wasar juya launin idanunta,tamkar fitilar hannu haka haskensu ke dalle nawa idon.Gumi ya jiƙa ni sharkaf kamar wacce ta yi wankan kwance,yayin da kuma fitar numfashina ya zama kamar na wacce aka maƙallawa oxygen.Bugun zuciyata ya tsaya cak da bugawa ne a daidai lokacin da na ga magen daf da ni kamar ƙyaftawar ido. “Sannu Suwaiba ya jikin?” murya Mamu ta sauka a dodon kunnena a daidai lokacin da na buɗe idanuna na tsinci gangar jikina kwance a gadon asibiti. “Zan yi fitsari” shi ne abin da na faɗa tare da yunƙurin tashi,ta zo da sauri ta taimaka mini na miƙe tsaye.Ina dafa bango a haka na shiga toilet ɗin wacce ke da ƙarancin haske,kan fo na hau tare da lumshe ido na soma yin fitsari .A daidai nan kuma na soma jin wata murya na yin suwa cikin kunnena,“mun san abin da ya ke damunki ki yarda mu taimaka miki ” da sauri na ware idanuwana zuciyata na matsanancin bugawa,sai dai na kasa gaskata ma abin da na ji ɗin.Ruwa na kama kafin na fito na samu Mamu na gyara shimfiɗar da na tashi a kai,tana ganina ta sake jefo mini tambayar ɗazu. “Ya jikin naki?” “Da sauƙi Mamu.Ƙarfe nawa yanzu?” Sai da ta duba ƴar ƙaramar Nokia ɗinta kafin ta ce “ƙarfe uku ba kwata” Ban ƙara cewa komai ba na je na sake kwanciya,duk yadda na so yin bacci kuma kasawa na yi.Sai Mamu ce dai ta rumtsa,a yadda take baccin kawai na fahimci na gajiya ne da dukkan alamu tun bayan da da suka fargar halin da nake ciki ba ta rumtsa ba.Wani tsoron ne ya sake rufe ni tuna abin da ya faru,addu'a na soma yi sai na dinga jin sassauci.Ina a haka har aka kira sallar asubah,a hankali na sauka na shiga toilet na sake yin ɗahara sannan na ɗaura alwala.Ina shirin fitowa ƙofar ta wani rufo kanta da ƙarfi,jiki na rawa na kama handle na soma kiciniyar buɗewa ta amma tamkar ma ina sake rufe ta haka take ƙara mannewa.Bakina na rawa na soma kiran sunan Mamu ina kuka kafin na waiwaiya bayana da nake jin kamar ana son damƙe ni,nan na yi tozali da fuskata a cikin madubi da kuma inuwar kaina wacce ta rabu biyu ina kallo a gaban idanuna kuma duka inuwoyin biyu suka haɗe wuri ɗaya.A daidai nan kuma na ji numfashina na barazanar sake ɗaukewa a karo na biyu,sai kuma ƙarar buɗe ƙofar ta ziyarci kunnena hakan shi ya ɗan farfaɗo da numfashin nawa.Wani tsalle na yi na fito waje ina haƙi,sai na ga Mamu na ta ci gaba da yin baccinta.Kusa da ita na je tare da ɗan jijigata,ta wani firgita tare da tashi tana zarar ido. “Lokacin sallah yayi” na faɗa a sanyaye.Sai ta jawo wata leda daga ƙarƙashin gado ta miƙo mini hijabi tare kuma da wani zane,shi na shimfiɗa na gabatar da sallar.A sujudar ƙarshe sai da na yi dogayen addu'o'i sannan na ɗago,bayan na gama Mamu ita ma ta yi tata sallar.Babu wani jimawa kuwa likita ya shigo ya duba ni,sannan ya ce muna iya tafiya gida zuwa ƙarfe takwas na safe. Lokaci na cika kuwa muka fito ni da Mamu muka tari adaidaita muka dawo gida.A bakin ƙofa muka haɗu da Abba yana kiciniyar fitar da babur ɗinsa,shi ne ya soma yin magana kafin mu. “Har an sallamo ku?” “Eh!” ta basa amsa a ɗan dake tare da jan hannuna muka shige ciki.A tsakar gida Lantana ce zaune da ƴaƴanta suna gyaran gyaɗa,Mamu ta yi sallama duk suka amsa cike da fara'a Lantana ta taso ta wani zo ta kama hannuna tana cewa “Uwata ya jikin naki? Sai yanzu kawai Abbanku ke sanar da ni wai jiya cikin dare suma kika yi Allah ya yi sa'a ma Mamunku ta zo tashe ki don ki bata ko kuɗin adashe sai ta ga ba ki numfashi” Ɗan murmushi na saki kawai,sai Mamu ce ke bata ba'asi. “Dare bai ma yi wani sosai ba,Sulaimanu ne ya dawo a jiyan shi ne fa nake tashe ta don bani makullin frigine na basa lemu mai ɗan sanyi” Mamu ke yin bayanin,ban sani ba ko ta lura da yanayin Lantana ya canza wacce muke kira da Mama.Ta haɗiye wasu yawu tana mai cewa “Sulaimanu ya dawo?” Da ɗan mamaki ita ma Mamu ɗin ta dube ta tana mai cewa “kina nufin Surajo bai sanar da ke ba? Ai tare suka shigo shi ya ma kawo shi fa” Idanun Mama Lantana suka yi wani irin ja tana mai cewa “amma shi ne ko ki kira ni Zainaba ? Fatan dai yana lafiya ko?” Ɗan shiru Mamu ta yi kafin ta amsa a takaice “Alhamdullah” Wani irin abu ne nake ji yana shigar hannuna da Mama Lantana ta riƙe,babu shiri na ƙwace abina ina mai yin gaba na wuce can ɓangarenmu.Da akwatin Yaya Sulaimanu kuwa na fara cin karo a nan falo,kan kujera na kwanta ina jan numfashi babu jimawa Mamu ta shigo. Ledar hannunta ta ajiye tana masifa ƙasa-ƙasa,“ƴarka ba ta da lafiya amma ka kasa fitowa mu je asibiti don kawai kana ɗakin wata ,hum! Ai ciwo ne ya san ɗakin kowa” “Mamu me yasa a kullum kike ganin laifin Abba amma kika yarda da Mama Lantana? Ai ko ma mene ne ita ce ta hana shi fitowa” “Kwanta ki huta dai,kin fi sanin halin Abban naku ne ” daga haka sai ta fice,ni kuwa wayata na ɗauko na rubutawa ƙawata Ubaidah saƙo babu jimawa kuma ta kira ni.Hira muka soma sama-sama kafin na bata labarin abin da ya faru da ni ,ta ce “hum! Yanzu fa in na ce miki na yi mafarkin hakan sai ki ƙaryata ni ko? Wallahi Suby ba tun yau ba ake nuna mini a mafarki wata baƙar mata na binki da sharri,kuma kin san ni dai wacce nake zargi?” Na ce “a'a”,ta bani amsa da “Mama Lantana,shi yasa ma ni sam na tsane ta saboda ita na rage zuwa gidanku don muddin na je can in dai har muka haɗu to ranar zan wuni da azababen ciwon kai ne” Ina shirin magana Mamu ta shigo hannunta riƙe da leda,ni ta miƙowa tana cewa “ga shi ki ci in kin gama sai ki sha magani” karɓa na yi ina cewa “toh” sai kuma ta sake ficewa. Na ja numfashi ina cewa “ƙawata don Allah in kin samu dama ki zo gidanmu ko da dadare ne gudun kar ki haɗu da ita wallahi akwai maganar da nake son sanar da ke mai muhimmanci ” Ta ce “a'a ke ya kamata ki zo dai,ko ki bari SUL zai zo sai ki biyo shi ku taho” Na yi ɗan murmushi mai sauti na ce “wai ya sanar da ke ya zo ne? Ni fa har yanzu ba mu haɗu ba” Ta ce “ni ma sai yau da safe ya sanar da ni,ya ce mini ba zai jima ba zai koma” “Kuma a hakan kike so na biyo shi? Ban takura muku?” “Ke dalla ki zo, SUL ɗin ne ba ki sani ba da magana ma wuya take yi masa?” “Ok to babu damuwa” daga haka sai muka ɗauko hirar makaranta kuma inda kusan nan dai katin wayarta ya ida kafin mu yi sallama. Ledar da Mamu ta kawo mini na buɗe,waina ce da miya haka na juye a kwano na ci na ƙoshi sannan na sha magani sai kuma na ɗan kwanta don na huta.Sai dai hakan ba ta samu ba sakamakon shigowar Yaya Sulaimanu,da sauri na miƙe tare da zuwa na ƙanƙame shi cikin murna ina hawaye. Yayi ɗan murmushi wanda ya bayyana tsantsar kamar mu da shi sai dai na fi shi kyawu,“Autar Mamu ?” ya furta yana goge mini hawayen fuskata da suka kasance na farin cikin ganinsa,shi kaɗai ne ƙwaya ɗaya tilo ɗan uwana da muka fito ciki guda shi ya raine ni,ya sangartar da ni. Na amsa da “na'am” kafin kuma na yi shiru.Ya ja hannuna muka zauna kan kujera kafin ya riƙe dukkan tafukan hannuwana yana kallona,kallo ne wanda ta shi kaɗai ne yake iya karantar damuwata saboda girma da ya zo mini yasa na bar faɗa masa damuwata don na lura shi ma tasa damuwar wacce yake dako shi ɗaya. “Me ya sumar da ke jiya?” ya jefo mini tambayar kamar daga sama. Ni kuma don kawar da zancen na ce “me yasa ba ka je dubo ni ba asibiti?” “Ni na kai ku fa,sai dai na baro can ne saboda kiran ujila da na samu” ya bani amsa. “Mun yi waya da Ubaidah ta ce in za ka tafi mu je tare” na faɗa ina kallonsa ni ma,ya ce “ta faɗa mini amma sai dai gobe don yau akwai inda zan je” Na ɗan ɓata rai kafin na ce “to ka kai ni sai ka yi tafiyarka in ka dawo sai ka biyo ka ɗauke ni ” “Ya biyo ina?” Mamu wacce ta shigo yanzu ta tambaya. “Gidansu Ubaidah kin san kamar wasu tagwaye haka suke” Mamu ta washe baki tana mai cewa “jiya ma mun haɗe da Mamarsu ɗin tana yi mini zancen saka rana,na ce ai magana tana wurinsu tun da su suke da mace” Sulaimanu ya ɗan sunne kai yana mai cewa “abin da ya kawo ni kenan Mamu sai dai kuma jiya ban samu mun yi maganar ba” Mamu na jin haka ita ma ta samu wuri ta zauna,shi kuma Sulaimanu sai ya saki hannuwana da tun ɗazu suke cikin nasa ya fuskanci Mamu da kyau yana cewa “Mamu dama na zo ne a yi bikin in an gama komai ina so in tafi da Ubaidah can inda nake aiki” “To ai hakan ba wani abu ba ne,zan kira Kawunku na sanar da shi sai ya je ya samu iyayen nata ya sanar” “Yawwa hakan ma yayi” Sulaimanu ya faɗa yana jan numfashi,daga nan kuma sai Mamu ta soma tambayarsa wurin aikinsa tun ina saurarensu har ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba . ★A can ɓangaren Mama Lantana kuwa ɗaki ta shige ta bar Hassana da Hussaina da kuma Ramatu ga aikin gyaran gyaɗar da take yin digadigi.Kamar ta yi hauka haka take ji,waya ta ɗauko ta shiga duba lambobi har ta kai ga wacce take so ta danna okay kiran ya tafi yayin da sunan malam Yawale ke yawo kan ɗan ƙaramin screen ɗin wayar .Bugu biyu ya ɗauka,ko gaishe shi ba ta yi ba cikin ƙasa da murya take cewa “malam da fa matsala ka ga Sulaimanu wai ya dawo jiya ” “Ya fa dawo? Kin tabbata kuma kullum kina yin wuridin da na baki?” “Ko yau na yi shi malam,ni dai yanzu abin da nake so a sake sabunta aikin nan shi ne kawai” “Zan sabunta amma da buƙatar yanka wannan karon,jajayen zakaru guda uku sai kuma ki sayo jan muski guda ɗaya da fari guda biyu” “Zan turo maka kuɗin sai ka sayi duk abin da kake buƙata” tana faɗar haka ta kashe kiran tare da dafe saitin zuciyarta da ke barazanar faɗowa ƙasa tun bayan lokacin da ta samu labarin zuwan Sulaimanu. “Hassana?” ta ƙwala kiran sunanta,daga can waje Hassana ta tashi figai-figai ta zo domin amsa kiran mahaifiyarta. “Ga ni Mama” ta faɗa ,Mama Lantana ta ɗauko wata robar mai wacce take ajiyar kuɗi a ciki ta ɗauko kuɗi ta ƙirga kafin ta ce “ungo je ki turawa malam Yawale kuɗin nan,ki yi sauri kuma ki dawo don za mu je markaɗe” Ta karɓa tana mai cewa “har yanzu bai ƙara aiko mana da rubutun ba dai” “Zai aiko ni na dakatar da shi” Mama Lantana ta faɗa. Hassana ta ɗan ɓata rai kafin ta ce “amma Mama ...” kafin ma ta ida ta tari numfashinta tana mai cewa “don ubanki a wannan gidan a ina za ki yi wankan magani a tsakar gida? Na bari ne sai Kaka ta dawo sai ku je can gidanta hankali kwance ku yi komai ku dawo“ Hassana na jin haka sai ta washe baki,hijabi ta ɗauka da ɗan saurinta kuwa ta fita zuwa tura kuɗi. Mama Lantana na ganin kiran malam Yawale ta san da tuni ya ga alert.Ta ɗaga tare da yin shiru,ya ce “in sha Allah ina mai tabbatar miki yau da zarar jinin zakarun nan ya zuba ga ƙasa Sulaimanu zai koma can ƙauye” Mama Lantana ta washe baki tana cewa “na gode sosai Malam,goben ni ma zan zo saboda batun aikin ƴan biyun ” “Babu damuwa hajiya” ya faɗa tare da kashewa. Mama Lantana ta fito tsakar gida wanda yayi daidai da fitowar Sulaimanu shi ma daga can shamakinsu.Kamar kullum wani irin tsoronta ne ya ji ya ziyarce shi mai haɗe da faɗuwar gaba.Da wani irin sauri ya je gare ta yana gaishe ta,ya sunne kai sam ya kasa ɗago kai ya dube ta. Mama Lantana ta saki wani makirin murmushi ganin har yanzu dai da sauran aikin da ta yi a jikinsa,“Lafiya lau Manu wannan bazata ,zuwa babu shawara?” Zuciyarsa ce ta ƙara tsananta tsoron nata,yana jin in ta yi masa faɗa tamkar zai iya rasa ransa ne.Murya na ɗan rawa ya ce “yi haƙuri Mama na zo ban sanar da ke ba tukuna” “Bai komai yarona Allah yi maka albarka ,sosai na yi farin cikin ganinka” Mama Lantana ta faɗa cikin ɗaga murya tana mai shafa kansa ganin Mamu ta fito. Ita kuwa Mamu baiwar Allah murmushi ta saki duk da kuwa wannan ba baƙon abu ba ne duk mai shigowa gidan nan ya san yadda Mama Lantana ke nuna tsantsar soyayyarta ga Sulaimanu,da kuma shi kansa yadda ya ɗauke ta kamar uwa yake yi mata biyayya don in mutum baƙo ne zai iya dubin Mama Lantana ce ta haife shi ba Mamu ba. Ba tare da tunanin komai ba Mamu ta ce “ashe ɗanki matarsa ya zo tafiya da ita ” ta yi furucin ne cikin raha. Ita kuwa Mama Lantana zuciyarta ce ta ƙara rinewa da baƙin hassada amma kuma sam ba ta nuna hakan a fuskarta ba,wata uwar guɗa ta yi tana wani juyi . Hassana da ta shigo ta ce “Mama lafiya kike rawa?” “Auren Yayanku ya tashi” ta bata amsa,ƴan magana sun ce barewa ba ta yi gudu ɗanta yayi rairafe ba to haka ƴaƴan Mama Lantana suke duk ta koya musu makirci haka su ma suka hau murna wanda hakan ya sanyaya ran Sulaimanu yana kallon ƙannen nasa waɗanda suke uba ɗaya,har zai fita ya ji suna zancen fitar da anko. Mamu kuwa haka ta zauna cikinsu suna ta zanen kalolin ankon biki da za a fitar kafin kuma ta ɗauki waya a gabansu ta kira Kawunsu wanda ya kasance ƙanen mahaifinsu ne ta sanar da shi.Tana ajiye wayar ita ma Mama Lantana ta tashi ta shiga ɗaki ta yi nata kiran,ta sanar da malam Yawale wanda duk unguwar da yake babu wanda bai tsoro da shakkarsa. ★Suwaiba Ban san adadin lokacin da na ɗauka ba ina bacci.Ko da na farka fitowa na yi na ɗauki buta na shiga banɗaki,sai bayan na fito ne na samu Mamu a madafa ina tambayarta abin da aka dafa. “Wake da shinkafa” ta bani amsa,gabana ne ya yanke ya faɗi har ban san lokacin da na furta “innalillahi wa'inna ileyhi raji'un!” wanda yayi daidai da shigowar Abbanmu a rikice yana kiran sunan Mama Lantana. Mamu ce ta fito tana cewa “malam lafiya?” “Ina fa lafiya wai Isiyaku ne mota ta kaɗe yanzun nan ko shurawa bai yi ba” ya bata amsa. Mamu da ke riƙe da tasar da za ta soya mai sakinta ta yi tana cewa “kawun yaran ne ya rasu? Yanzun nan fa muka gama waya da shi” Abba ya ce “ya kira ni,kuma ma sai da ya shaida mini kun yi waya da shi kan ya je ya tuntuɓi iyayen Ubaidah game da sa ranar biki shi ne ya ce bari ya kira ni kafin ya je ashe babu rabon zuwan” Tamkar wacce ta hau tauri haka ƙafafuwana suka soma yin rawa,kafin kuma na soma yin kuka kamar raina zai fita.Duk a tunaninsu saboda mutuwar kawun ce nake yin kuka,ni kuwa a'a ba ita ba ce sai dai abin da zai faru a gaban ne nake yi wa kuka muddin dai mafarkin nawa ya ci gaba da zama gaskiya.Rarrashina suka haɗu suna yi tare da yin nasiha. Mama Lantana ta fito wani kallo ne ta yi mini wanda yake mugun jefa ni cikin tsananin tashin hankali. “Me yake faruwa?” ta tambaya,Abba ya bata amsa. “Allah ya jiƙansa,Zainaba shirya mu tafi ki kwashe waken a kula mu tafi da shi” shi ne abin da Mama Lantana ta furta tare da juyawa tana yin wani murmushi wanda sarai da idona na ga haka. Babu ɓata lokaci duk muka shirya, lokacin bai wuce ƙarfe ɗaya na rana da wasu mintina.Adaidai sahu muka shiga,Mamu da Mama Lantana da kuma ƴan biyu a can baya yayin da ni kuma da Ramatu muka shiga gaba.Ko da muka isa tuni an haƙa rumfa,dangi na kusa ma tuni sun zo. Duk saukowa muka yi Mamu na miƙa kuɗin ɗan sahun Mama Lantana ta jefo tambayar “ni kam an sanar wa da Manu batun mutuwar?” Mamu ta girgiza kai,kallonta na yi ni dai yadda ta ɗauki mutuwar kamar wani biki sai murna take. “Hassana ungo kira Yayanku ki sanar da shi” ta faɗa tare da miƙa mata wayar,sai bayan mun shiga ciki har mun zauna sannan ta kira wayar ina jin yadda muryar Yaya Sulaimanu ta bayyanar da tsantsar tashin hankali. Jingina na yi ga bango ina mai lumshe idanuna,wani irin ƙunci nake ji da ban taɓa ji ba a rayuwata.Tamkar ba gidan makoki ba haka mutane ke ta yin surutu,ga Mama Lantana sai maimaita kalmar ko yau an yi waya da shi game da auren ɗan wurin Mamu .Tun mutane ba su ɗauki abin wani kala ba har wata ta ce “ah wannan aure kuwa anya akwai alkhairi a ciki? Kila ma yana kan hanyar zuwa gidan ne aka kaɗe shi” Da sauri na ware idanu sai na ga idanun Mamu sun nuna ƙin jin daɗin furucin,yayin da ita kuma Mama Lantana ke cewa “to wa ya sani abu kamar annoba sama da wata shidda kenan da kai dukiyar auren ” Tsam na miƙe saboda ba zan juri ire-iren waɗannan maganganun ba.Idanuna har wani lumshewa suke tsabar yadda baƙin ciki ke naƙarƙasata,ban san inda nake jefa ƙafa ba kawai tafiya nake bayan na fito daga gidan mutuwar.Na yi tafiya mai nisa kafin na samu wata bishiya na zauna kan wata ƙatuwar tayar mota,ajiyar zuciya na yi ta saukewa kafin na kira Ubaidah.Tana ɗauka na fashe mata da kuka,duk sai ta rikice ta soma tambayata lafiya amma ban ce mata komai ba har sai da na ji ta ce “gani nan zuwa” “Ba ni gida” “Kina ina to?” ta tambaye ni,sai a lokacin na duduba wurin da nake sannan bata amsa da “wajen makarantar makafi ” kashe kiran ta yi,ba fi minti ashirin ba sai ga ta cikin mota.Ta buɗe murfin da ta fito tare da zuwa da sauri ta miƙar da ni tsaye,jikinta na shige na ci gaba da yin kukan ban yi shiru ba sai da na ji Ubaidah ta kama mini ita ma tana kukan. Na yi ɗan baya tare da jingina jikin motarta murya na ɗan rawa na ce “wai kuka kike yi?” “Me kike so na yi Suby? ”sai kuma ta kama hannuna tare da buɗe mini gaban mota ta zaunar da ni,sannan ta zagaya ta zauna ita ma tare da yi wa motar key.Gudu take yi sosai har sai da na ji tsoro,“ina za mu je?” na tambaye ta. “Nigeria” ta bani amsa. Wa waro ido na ce “Nigeria kuma? Wurin me?” “Sayar da ke zan yi na huta da tashin hankalin da kike saka ni a kullum” Ban san lokacin da murmushi ya kubce mini ba,sai na jinginar da kaina a kafaɗarta ina mai cewa “ke ce farin cikina my Udah ” Gefen titi ta samu ta parker motar tana mai cewa “tun kafin dai yayanki ya more ni duk kin bi kin ɗale mini jiki” Na janye daga gare ta ina mai yi mata hararar wasa na ce “jikin naki ma da bai da komai sai shegen tauri ” Ta yi wata mahaukaciyar dariya kamar ba gobe kafin ta daki bayana sai kuma ta yi shiru tana wani murmushi.Inda ta ƙurawa ido na duba sai na hango wani mutum yana tahowa da dukkan alamu kuma wurinmu zai zo. “Wane ne kuma wannan mutumin Ubaidah?” na tambaye ta saboda tsikar jikina da ta soma tashi sakamakon iya ganin zubin halittarsa da nake iya gani a yanzu da yake daf mu.Fari ne sosai,sai dai wani abu duk ya ɓata masa fuska kamar ƙuraje kamar kuma cutar kuturta.A kallon farko kawai da mutum zai yi masa zai iya ajiye shi cikin ƙabilar Fulani duba da ƙaramin jikinsa. Gilashin motar ya ƙwanƙwasa ta yi ƙasa da shi,ya miƙo mata wata gora mai cike da madarar shanu yana mai sauke idanunsa a kaina. “Wane ne wannan mai cike da ƙuncin rayuwa?” ya tambaya cikin hausarsu ta Fulani. “Ƙanwar Sulaiman ce“ ta basa amsa tana mai jan wani dogon numfashi. Bai ce komai ba sai idanunsa da ya tsura mini masu matuƙar kaifi,ni ma kamar wacce aka yi wa dole haka na ƙi sauke nawa..... [03/06 09:10] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *ROMON HAƘURI* 🤍 MRS SADAUKI ✍️ FCWA ☀️ *Wannan labari ba ƙirƙira ba ce,labari ne da ya faru a gaske ina fatan za ku bibiye shi sau da ƙafa* *__________________________________________________* 02 Tamkar yana lalubo ruhina haka nake jin idanunsa masu matuƙar kaifi na kashe duk illahirin jikina.Ajiyar zuciya na soma saukewa akai-akai kafin kuma na lumshe idanuna na shige can jikin kujerar da nake zaune sosai. “Zai iya ƙara masa ruwa ko kuwa haka zai sha shi zalla?” na ji muryar Ubaidah na tambayawa. Cikin muryar nan tasa ta Fulanin da ba su jin Hausa sosai ya ce “zai ƙara ruwan zam-zam ko kuma ruwan hadari,sannan ki kula sosai da kanki kamar yadda na faɗa miki da sauran lokaci har yanzu kar ki wani tashi hankalinki da sannu duk katangu sharrin za su rushe dama duk abin alkhairi kafin a same shi sai an sha daga” Cikin wata irin murya mai cike da takaici na ji Ubaidah na cewa “uncle Suhail ka fi kowa sanin yadda nake kula da kaina wannan dalilin ne yasa mugaye ma ba su fiya son zuwa inda nake ba ,babbar damuwata shi ne yadda ake cutar da na kusa da ni saboda an san zan ji zafi” “Jira ina zuwa bari na kawowa ƙawarki wani magani” jin furcin da ya furta ya saka ni saurin buɗe idanuna,sai na ga tuni ma ya juya baya yana tafiya.Tamkar wanda ake tunkuɗawa gaba haka tafiyar tasa take kai ka ce cikin iska yake.Bai wani jima ba ya dawo hannunsa riƙe da wani ɗan ƙullin magani cikin tsumma. Jikina ne ya soma rawa jin yana cewa “ta shaƙa wannan cikin hanci zai sassauta mata yawan firgicin da take shiga” Tsabar mugunta irin ta Ubaidah sai cewa ta yi “Uncle Suhail ka shaƙa mata da kanka mana” ta yi furucin ne tana mai sauke gilashin ɓangaren da nake zaune . Bakina ya soma rawa,cikin rarrabe wa murya na ce “ban..ban. so” sai dai tuni ma ya zagayo inda nake.Babu shawara ballantana neman izini kawai kama kaina tare da yin sama da shi,ido na rumtse jin hannunsa da wani bala'in sanyi kamar wanda ya fito daga mutuware can inda ake ajiyar gawa.A daidai lokacin da ya shaƙa mini maganin kuwa ji na yi kamar an ɗora ƙwaƙwalwata ne kan kan tanda ana yi mata juyin waina.Da wani bala'in sauri na ware idanuna ina jin su ma suna yi mini yaji,atishawa na soma yi ba ƙaƙautawa.Yayi ɗan baya yana kallona kafin ya ce “akwai damuwa sosai a rayuwarta sai dai ƙofofin taurarinta sun ƙi buɗewa ballantana a san ta ina za a soma” A wannan karon muryar tasa sai na ji ta tamkar ba ma ta mutane ba,da wani irin sauri na damƙo hannun Ubaidah ina mai kallonta da jajayen idanuna so nake na ce mata mu tafi amma na kasa furta ko da harafin A. Sauran maganin ya ɗaure tare da cillo mini shi kan ƙafafuwana ya ce “a duk lokacin da kike cikin tsoro ki shaƙa wannan ” ko kallon inda yake ban yi ba,cikin wata murya kamar ta mai yi mini faɗa ya ce “ko ba ki ji ba? Ki riƙe maganin a hannunki” jiki na rawa kuwa na ɗauke shi na jimƙe. “Allah ya tsare” ya furta , Ubaidah ta amsa da “amin!” kafin ta mayar da maduban motar ta kuma yi mata key.Duk sanyin Ac da ke tashi bai hana zufa tsatsafo wa a goshina ba,atishawar ta tsaya sai dai ajiyar zuciya da nake saukewa akai-akai ina jin kuma zuciyata na rage nauyin abin da nake jin ya danne ta. Har muka isa gidansu babu wanda ya cewa kowa komai.Ta yi horne mai gadin gidansu ya tura ƙofar da sauri ta wuce,cikin jerin manyan motocin da kusan kullum sai ka ga sabbi ta ajiye tata.Sai a lokacin ta dube ni “ya jikin naki?” ban ce mata komai ba sai muguwar harara da na yi mata.Ta sakar mini murmushi kafin ta buɗe murfi ta fita ta zagayo ta buɗe mini ni ma,a hankali na ziro ƙafata ta dama na fito sai dai fa tamkar wacce aka yi wa duka haka na ji duk jikina na yi mini ciwo ga kuma ƙafata ta hagu da ta ƙage.Hannuna ta kama muka nufi hanyar da za ta sada mu da lafiyayyen falonsu mai cike da kayan more rayuwa,kujeru na zama kusan kala uku ne ma a ciki sai babban teburin cin abinci wanda shi kansa abin kallo ne. Tsit falon yake babu kowa sai ƙatuwar tv wacce ta kusa cinye bangon ɗakin tsabar girmanta,iya hotuna kawai take nunowa babu magana.Can ɗakinta muka haura ba tare da ta damu da kashe tvn ba,muna shiga ta je ta ɗauki remote ta saita sanyin Ac kafin ta ce “bari na haɗa miki ruwan wanka” sai ta wuce can bedroom ni kuma kan kujera na zube ina maida numfashi tare da tunanin mutumen nan da ta kira uncle Suhail. Ina nan ta fito,ta zo ta kama hannuna tana cewa “taso ki je ki yi wankan,ko na yi miki?” Duk da ban jin jikina sai da na yi dariya tare da kai mata duka na ce “ki jira in kin auri Ya Sulaimanu can ki yi masa amma ni jikina ya fi ƙarfinki” Wani kallo ta yi mini na tara saura kwabo kafin ta ce “farar fatar ce ta fi ƙarfina ko me? Daɗin abin dai launina ya fi tsada” “Matsalata da ke hauka,ana gabas kina yamma yanzu ke sai ki yi mini wanka?” “Me yake yi to? Ai bisa larura ne” “Mu je to ki yi mini” na faɗa ,banza ta yi da ni tare da haye kujera ta soma latsa waya.Na yi murmushi tare da tafiya na shiga bedroom na wuce can toilet ɗinta wacce ta ko ina ta haɗu.Komai na cikinsa pink ne kamar yadda falonta yake,cikin bahon wankan na shiga na kwanta bayan na cire kayana.In ba a gidansu Ubaidah ba ban taɓa yin wanka ko da pampon sama ba ne ballantana shiga bahon wanka,saboda ni ko toilet ɗin ɗaki ba mu da shi iya ta waje ce kawai ita ma babu pampo a ciki. Ido na lumshe ɗumin ruwan na ratsa ni,ina jin kamar yanzu ne muryar Uncle Suhail ke cewa akwai damuwa a cikin rayuwata.Hawaye masu ɗumi suka silalo mini tuna abin da ya fito da ni daga gidan makoki.Ture tunanin na yi na yi wanka soso da sabulu har zan fito sai kuma na warware dunƙulin gashina na wanke shi fes yayi taushi da sheƙi.Gaban shower na je na ƙara wanke jikina sannan na ɗaura towel da kuma ɗaukar ɗaya ina tsane jikina.Inda take ajiye abin busar da gashi na duba sai dai ban gansa ba,cikin ɗaga murya na ce “in kin gama soyayyar zo ki bani abin busar da gashi” amma shiru ba ta ce komai ba,na nufin falon ina mai cewa “wallahi Udah zan yi miki rashin mutum...” sauran maganar ce ta maƙale mini a maƙoshi sakamakon ganin Ya Ubaidullah da ke tsaye ƙiƙam yayi tsayuwarsu ta sojawa kunnensa maƙale da bluetooth ɗaya yayin da kuma ɗayan ke a hannunsa.Yadda ya zubo mini ido yana kallo ni ma haka nake kallonsa da nawa cike da tsoro,muryata na ɗan rawa na soma i'ina. “Ban san..ban san ka shigo ba ,Udah ce...” hawayen da suka zubo mini shaaa su suka katse mini maganar.Daidai nan kuma Ubaidah ta shigo a shagwaɓe tana cewa “ni dai don Allah ka yi haƙuri har zuwa gobe wallahi ban gansa ba” Sai a lokacin kawai Ya Ubaidullah ya maida dubansa ga Ubaidah wacce ni ma ita nake kallo idanuna na ci gaba da zubar da hawaye.Muna yin ido huɗu da ita ta ce “Ya Ubaidullah me yasa za ka hukunta Suby madadina? “ sai ta zo da sauri ta rungume ni yayin da shi kuma ya fita. Wata ajiyar zuciya na sauke ,a duk lokacin da Ubaidah ke tare da ni a yanayin damuwa ina jin wani sassauci sai nake jin ita ɗin tamkar garkuwa ce a gare ni. “Yi haƙuri kin san halinsa in allurar sojojin ta motsa masa bai da mutumci,rabon a yi ne yasa na ɗauki motarsa jiya na tafi shopping to ban san ina na jefa key ɗin ba shi ne fa kawai.Faɗa mini me yayi miki Allah sa dai ba marinki yayi ba?” sai ta ɗago tana duban fuskata. Na ce “bai yi mini komai ba fa,kin san ni dama tsoronsa nake yi tun bayan dukanmu da ya taɓa yi” Ubaidah ta ja wani uban tsuki tana mai cewa “aikin banza! Shi ne kike hawaye? Wai ke sai yaushe za ki girma ke komai kuka,shan magani ma kuka kike yi masa” “Ke dalla bani abin busar da gashi” na faɗa tare da yin gaba,sai da na je gaban madubi ne na tuna cewa ashe towel ne ɗaure a ƙuguna,firgicin ganin Ya Ubaidullah duk ya mantar da ni.Wata irin kunyar kaina ce ta kama ni, Ubaidah ta zo tana busar mini da gashi bayan ta gama sai ta shafa mini mayuka ta kuma ɗaure shi. Kayanta ta ɗauko ta bani na saka sai dai sun kama ni saboda na fi ta ƙiba da kaɗan.Hotuna ta shiga yi mini kamar kullum saboda ita ciwon hoto ce,har sai da na gaji na je na kwanta bakin bed.Na lumshe ido ina mai cewa “ba ki tambaye ni dalilin kukana da ɗazu ba” “Malama taso mu ci abinci,ƙarfe biyu ta kusa” Ni sai yanzu ma da ta ambaci abinci na tuna da yunwa ce ta tashe ni daga bacci a ɗazu.Saukowa na yi ba tare da na ce komai ba muka fito,har yanzu babu kowa falon.Dianing muka je,ta soma buɗe kwanukan da ke kan teburin tana mai cewa "me za a zuba miki? ” Na dubi ɗaya kular da ba ta buɗe ba na ce “ita wannan mene ne a ciki?” Buɗewa ta yi,ƙamshi ya bugi hancina wanda ya zaburar da yunwar da nake ji.A duniya ina mugun son farfesun kifi,tana murmushi ta ɗauko plate ta saka mini ƙaton kifi guda ɗaya tare da sakwarar doya. Hannu na saka na soma ci hankali kwance ita ma ta zuba nata kalar abincin muka shiga yin hirar makaranta. Ƙamshinsa ne ya fara yi mana sallama kafin shi ya ƙaraso,kamar an yi ruwa an ɗauke haka na yi shiru.Jikina ya yi sanyi liƙis ganin ya ja kujera ya zauna wato shi ma abincin zai ci,Ubaidah ta ajiye cokalin hannunta ta miƙe ta zuba masa farfesun kifin tana mai kawo wata tasar ruwa wacce kusan kullum tana kan dianing ɗin ban taɓa sanin amfaninta ba sai yanzu da na ga ya wanke hannunsa ya soma cin abinci. Ɗan satar kallonsa na yi ,sai na ga ya kalli plate ɗin gabana.Wani irin dammm ƙirjina ya bada wato abin da na fahimta iya shi ɗaya aka girkawa abincin amma rashin mutumcin Ubaidah yasa ta zuba mini ni ma. Ji na yi duk na tsargu kawai sai na miƙe da sauri,ya ɗago ya dube ni.Idanunsa har sun fi na Uncle Suhail kaifi da shiga jiki,wannan yasa saura ƙiris na faɗa kansa amma duk yadda na yi ƙoƙarin haka sai da hannuna mai kumfan abinci ya kai jikinsa.Zuwa wannan lokacin tuni fitilun idanuna sun disashe don tsoro,murya na rawa na ce “yi..yi haƙuri” sai kuma na nufi hanyar kitchen duk da ina jin idanunsa a kaina ban tsaya ba. Saura ƙiris na kai wa bango karo Allah yayi sa'a ƴar aikinsu ta fito ita ce ta riƙe mini hannu kafin ita Ubaidar ta iso.Har kitchen ɗin ta yi mini rakiya na wanke hannuna,ta buɗe frigine ta ɗauko mini gorar ruwa mai sanyi ta bani na sha.Babu laifi na ji ƴar nutsuwata ta dawo,sai a lokacin na harari Ubaidah ta ƙyalƙyace da dariya tana mai cewa “to me kuma na yi yanzu?” Cikin jin haushi na ce “a'a ki dai kashe ni sai ki huta kawai,kin san iya shi aka yi wa girkin amma kika zuba mini” “To me yake yi? Shi fa bai da matsala kawai raini ne bai so da rashin jin magana” ta faɗa . “Yanzun ma ai raini ne tun da kin san ba zai ji daɗi ba” na faɗa tare da zuwa na leƙa sai na ga tuni ma ya bar falon. Ta matso kusa da ni tana mai cewa “mu je ki ƙarasa cin abincinki” “Na ƙi ɗin” na faɗa tare da fitowa,ina ƙoƙarin hawa step ta biyu shi kuma yana saukowa daga benen ɗakinsa ya canza kaya sai ƙamshi yake bazawa yana kallon wayarsa yana yamutsa fuska.Ina ganin zai ɗago na yi saurin tafiya a guje ina haɗawa da gudu-gudu hakan ya fitar da sautin takalmin ƙafata. “In dai kika faɗi babu wanda zai hana ni yin dariya” Ubaidah ta faɗa tana take mini baya.Ina shiga direct toilet na shiga na yi alwala na zo na gabatar da Sallah,ita ma haka.Bayan mun gama ne nake bata labarin mafarkin da na yi ina cewa “ina tashi kuma daga baccin na ga Mamu wake da shinkafa ta dafa,kuma kamar a mafarkin dai haka aka kwashe shi aka kai gidan makoki.Babban tashin hankalina shi ne yadda wannan karon ma aka sake...” sai kuma na yi shiru jin kuka zai zo mini , Ubaidah ce ta ƙarashe zancen tana cewa “aka ɗaga bikinmu ko? Hum! Na sani dama ai kin ji yanzu ma uncle Suhail ya ce da saura” Da ɗan mamaki na dube ta na ce “ya aka yi kika san abin da nake son sanar da ke?” “Saboda ni ma na yi mafarkin” ta bani amsa. “Wai wane ne Uncle Suhail ɗin nan?” “Oho! Ni ma ban sani ba“ Baki da hanci na saki ina kallonta kafin na ce “kuma kika je wurinsa?” “Eh magani yake bani” “Ya kuke da shi?” “Ni ma fa ban sani ba,kin ga zo na nuna miki kayan da na sayo mana jiya ” Sai ta miƙe ta buɗe drower ta ciro manyan ledoji ta zube abin da ke ciki kan capet,saukowa na yi muka shiga duba kayan a ciki muka ga key ɗin motar da ta yi ta nema.Ta ɗauke shi ta ɗora kan ɗan ƙaramin teburin madubi tana mai cewa “na huta da uƙubar Ya Ubaidullah,ko da yake ma ai kin sa ya canza kayan” “Wai har yanzu yana nan da aƙidarsa ta in ya sa kaya sai ya dubi motar da za ta hau da su?” na tambaye ta ina dariya.Ta ce “to Ya Ubaidullah fa aka ce miki,wai nan duk cikin gayu ne don a burge anty Hamida ” “Budurwarsa?” “Eh cousin ɗinmu wacce nake faɗa miki ta maƙale masa ta rantse in ba shi ba to ba za ta yi aure ba” “Tana tare da wahala kuwa,ni ko don ban taɓa soyayya ba amma gaskiya ina jin ba zan maƙalewa namiji guda ba na ce dole sai shi” “Ke wa yake biye ta taki? Macen da ko kwalli ba ta sakawa ido to wane banzan namiji ne ma zai kula ki da ido kamar na macen ɓera” “Eh na ji dai,kawai sai na saka abin da zai hana ni sukuni ” “Kawai dai don kin sakawa ranki ne amma daga shafa kwalli sai ido ya hau ƙaiƙayi?” “Ba za ki gane ba ne” na faɗa cike da damuwa. ★A can gidan makoki kuwa haka Mama Lantana ta saka shakku a zukanta duk wani na kusa da ita ana sukar auren Sulaimanu ana alaƙanta shi da hatsarin da Kawunsu yayi.Tun Mamu na jurewa har ta kasa musamman da ta ji matar shi kawun tana cewa “ai tun da aka fara zancen ƙaddararren auren nan malam bai zauna lafiya ba,kullum cikin jajensa yake yi ga shi kuma ya zama ajalinsa” “Haba! Haba matar malam ya za ki ce haka? Ta ina auren Sulaimanu ya zama ajalinsa sai ka ce dai shi ne mutum na farko da ya taɓa mutuwa a hatsarin mota? Ku fa musulmai ne ,ƙaddara mai kyau ko akasinta yana ɗaya daga cikin ginshiƙan imani.Kar ku bari sheɗan yayi tasiri a zukatanku mana ” Mama Lantana ta karɓe da cewa “laaa to ai ni sai yanzu na fahimci me suke nufi,ta ina dama mutuwar kawun yara ke da alaƙa da auren Manu ? Wannan sam ba adalci ba ne matar malam ko kowa ya faɗa ke ai bai kamata ki ce ba mene Manu ɗin bai yi muku? Hatta da abincinku na wata in ya kai gidanmu haka yake kawo wa nan gidan” Mamu wacce ita sam ba ma ta da labarin haka ta ce “abincin wata ?” Mama Lantana ta ce “i,ai duk wata sai ya kawo musu abinci ga kuma matar malam ɗin nan ki tambaye ta in ƙarya nake yi” Mutane dai da ba su san halin Mama Lantana ba sai kallonta suke,don ta zama tamkar sawun keke ba a san gaba ba ballantana baya. Ƴan biyu ma suka shiga nasu tsiyar gumin suna kare Yayansu,hakan da suka yi sai ya sanyaya zuciyar Mamu take ganin iya Lantana da ƴaƴanta ma kaɗai sun isa su tare mata ba sai ta saka baki ba. ★UBAIDULLAH Shi ne babba a kaf gidansu Ubaidah,shekarsa talatin da shida.Captain ne na sojoji,bai da yawan fara'a yana da tsanani sosai a wurin da ya kamata ya nuna tsananin.Yana son ƴan uwansa musamman ma Ubaidah kasancewar ita kaɗai ce mace kaf gidansu kuma autarsu.Amma ƙauna da gatan da yake yi mata ba su hana yi mata hukunci ba in ta yi laifi,sau ɗaya tak ya taɓa yi mata mugun duka ita da ƙawarta a ranar da ya kama su suna rawa a wani shagalin biki da aka shirya tsakanin ɗalibai.Yadda ake cuɗanya maza da mata shi ya hassala shi tun a can wurin taron ya naɗa musu na jaki sannan ya sako su a mota ya kawo gida. Tun bayan wannan lokacin bai ƙara saka Suwaiba da idonsa ba sai yau da ya ganta a cikin yanayin da ya kasa barin tunaninsa.Har ji yake a ransa da ya san zai same ta a haka da ya haƙura da key ɗin motar tun farko,saboda ko bayan ya fita ya koma sashensa kasa sukuni yayi haka yayi ta ganinta tsaye da towel tana hawaye. Yanzu ma abin da ta yi sosai yayi mamakin yadda ya ga tsoronsa ya rufe mata idanu,hakan yasa ya bi bayanta da kallo yana jin wani sanyi a duniya yana son mace mai matuƙar jin tsoronsa da ganin girmansa.Bai ma damu da kayansa da ta ɓata ba haka ya je ya sauyo ya fito,yana karanta saƙon Hamida wacce ke tambayarsa in girkin da ta aiko masa yayi daɗi sosai .Yamutsa fuska yayi yana shirin maida mata ya soma jin sautin takun Suwaiba ,a dole ya ɗago ya dube ta yana kallon yadda kayan da shi ne ya sayawa Ubaidah suka ɗame mata jiki. Fasa mayar mata da saƙon ya yi kawai ya fice,ɗaya daga cikin motocinsa ya ɗauka yayi mata key. Direct gidansu Hamidar ya wuce,tarba mai kyau ya samu daga ahalin gidan wanda suka kasance ƴan uwansa ne.Duk kowa ya bar falon sai kuma a lokacin Hamida ta fito cikin shigarta ta kullum wato sari,kasancewarta marar ƙiba yasa ta zaɓi sari matsayin sutura. Tun da ta fito ya kafe ta da ido,yadda take tafiya tamkar iska zai ɗauke ta sama tsabar sirranta.Ita kuwa tana ganin haka ta ci gaba da lanƙwasa ƙafafu tana tafiya cikin salon jan hankali.Tana zuwa ta zauna tana mai cewa “ya dai? Kallon fa? Ko na canza? Na yi kyau sosai?” Kamar zanar bunu bakinsa ya furta “eh amma ba ki kai ta ba!” Hamida ta gimtse fuska ta ce “wace ce?” Ubaidullah ya ɗan lumshe ido yana sauraren bugun zuciyarsa da ya canza gudun tun bayan da ya ga Suwaiba.Murya a ɗan dake ya ce “Jeedah mana” A nan take wani murmushi ya suɓuce mata tana mai cewa “in kuma ta ɗauko kamannina madadin naka?” Ya ware idonsa ya kalle ta kafin ya ce “jinina ya fi naki ƙarfi,ina ji Jeedana da ni za ta yi kama” “To na ji! Yanzu dai faɗa mini ya ka ji girkin yayi daɗi kuwa?” “Sosai ma sai dai ban wani ci sosai ba” Ta ɗan ɓata rai ta ce “saboda me?” Ya yamutsa fuska kafin ya ce “kin san Ubaidah da shirme yau ƙawarta ta zo gidan” Hamida ta ja tsuki tana cewa “ƴar talakawa za ka ce wacce ta sauya mata ra'ayi ta ƙaƙaba mata Yayanta ” Ubaidullah ya ce “Hamida me yasa kike da riƙo a rayuwarki? Allah ne bai nufa Abdul Hamid ya aure ta ba shi ne kawai,sannan ki bar zaginta ban so” “To“ shi kaɗai ta furta tare da yin shiru,a duniya in akwai wacce ta tsana to bayan Suwaiba take ba don komai ba sai don ta yi yaƙinin cewa tsabar tsagwaron ƙaunar da Ubaidah ke yi mata ce har ta kamu da son Yayanta Sulaimanu. “Zan wuce!” ya furta tare da miƙewa tsaye,Hamida ba ta ce komai ba har sai da ta ga ya juya sannan ta miƙe da sauri ta rungume shi ta baya.Ya ɗan rumtse ido,a lokutan baya yana matuƙar jin farin ciki in Hamida ta yi masa haka amma yau a karon farko da ya ji tsanar haka. “I love you !” ta furta tana wani murmushi mai sauti,tana jiran ya juyo da ita su fuskanci juna kamar yadda ya saba yi mata sai yayi mata kiss a goshi amma shiru kake ji sai ita ce ta zagayo da kanta ta yi tsaye tana kallonsa. “Wai fushi kake yi don na zagi wacce ta yi silar raba ɗan uwana da farin cikinsa?” ta furta idanunta na ƙanƙancewa. “Zan tafi sai in mun yi waya” ya sake furtawa. Ta ɗan ja da baya saboda ta fi kowa sanin halin Ubaidullah in yayi haka to fa babu wanda ya isa ya sauya masa ra'ayi.“To babu damuwa ka kula da kanka sosai” Wani murmushin ne ya suɓuce masa bai shirya ba wanda kusan kullum in ta furta masa ya kula da kansa sai ya ga kamar ma ta raina shi ne ko tana yi masa ɗaukar yaro.Ya ce “kina bani mamaki Hamida sai ki ce wai na kula da kaina,sai ka ce wanda bai da cikakken hankali dai” Ta yi ɗan murmushi tana mai cewa “Ubaidullah a kullum in kana faɗar irin haka sai na ga kamar ba ka fara sona ba har yanzu,saboda zuciyar da ta kamu da so ne kawai ke fahimtar kalaman so da bege da kuma tattali.In na ce ka kula da kanka ai don na damu da kaina ban so wani abu ya same ka” “To na ji na gode” ya furta tare da ficewa ita kuwa ta bi shi da ido har ya ɓace mata.Da wani irin sauri ta nufi sashen mahaifiyarta tana ƙwala kiranta “Ummah? Ummah?” “Lafiya ?” Ummah da ke zaune kan gado tana jera sarƙoƙin da take yi wa Hamida tariya a cikin akwati. “Ba lau ba Ummah, Ubaidullah ya sauya mini fuska ya kamata ki kira malam Yawale ” jikin Ummah ya ɗauki wata rawa ta ce “me kuma ya faru? Cewa ya yi bai son ki? Halan maganar auren kika yi masa? Kin san da sarai malam Yawale ya ce kar ki furta masa kalmar aure ki bari da kansa zai faɗa ko?” Hamida kallon Ummah ta dinga yi,in Ummah na yin wani abin sai ta ga kamar ma ta fi ta damuwa akan ta auri Ubaidullah ɗin.Ba ta ce komai ba dai ,sai Ummah ta kira shi a waya suka yi magana ta kashe kafin ta dube ta tana mai cewa “ki ɗauko ƙwan da ya baki ki juya shi cikin ruwa har sau bakwai kina ambaton sunan Ubaidullah sannan ki je ki yi wanka” Hamida ta ce “to” kafin ta fita zuwa ɗakinta,ruwa ta zuba a bokiti ta ɗauko wani ƙwan kaza da aka yi wa rubutu a jiki ta shiga juya shi tana kiran sunan Ubaidullah sannan ta yi wanka da ruwan.Kamar kullum yau ma wani mugun sonsa ne ta ji ya ƙara luluɓe ta,daman hakan ce ke faruwa da ita muddin ta yi wankan.... [03/06 17:48] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *ROMON HAƘURI* 🤍 MRS SADAUKI ✍️ FCWA ☀️ *Wannan labari ba ƙirƙira ba ce,labari ne da ya faru a gaske ina fatan za ku bibiye shi sau da ƙafa* *__________________________________________________* 03 Sai wuraren sallar magrib Ubaidah ta maido ni gida,sai dai a rufe muka tarar da gidan alamun har yanzu su Mamu ba su dawo daga gidan makoki ba. “Gidan naku a rufe kin ga dole yanzu mu koma dama ban gaji da ganinki ba ki ka wani matsa ala dole sai kin dawo sai kace wacce ta bar yaron da take shayarwa ” Ubaidah ta faɗa tana buga sitiyarin motarta. Na ce “a'a zan fita na jira su” “Yau ga Ubaidar mahauka ba,sai na bar ki a nan ke ɗaya” “Gidansu Fiddo zan shiga sai na jira har su dawo” Ta haɗe rai tana cewa “wai meke haɗinki da Fiddon nan ? Magana ɗaya biyu sai kin kawo mini zancenta” Na yi ƴar dariya na ce “Yaya Surajo ke sonta fa” Ta ja dogon tsuki ta ce “wace marar aji ce za ta so Surajo? Ga muni ga ƙanzanta ga kuma shaye-shaye taɓ” Duk da abin da ta faɗa gaskiya ne amma sai ban ji daɗi ba kasancewar shi ɗin ɗan uwana ne,ubanmu guda shi ne babban yaron Mama Lantana.Wata harara ta banko mini ƙila na ganin na canza fuska ne kafin ta ci gaba da cewa “ke ai dama duk waɗanda ba su ƙaunarki kin fi manne musu to je ki ga Surajo ɗin,ina ce dai uwarsa ce ta saka ki kwana asibiti” “Uwarsa kuma?” na tambaya cike da mamaki,ta yi ɗan shiru kafin ta ce “to eh mana,kika ce saboda ita Abba ya ƙi fitowa” Na ja doguwar ajiyar zuciya ina mai cewa “haka ne” Key ta yi wa motar muka koma gidansu,sam ban yi mata gardama ba don wani sanin sa'in Udata akwai rigima da mayar da ƙaramin abu babba. Tana yin parking duk muka fito amma ban ɗauko ledar kayana da ta raba ta bani ba.Ciki muka shiga sai muka tarar da Ammy ta dawo daga aiki, Kasancewa ita ɗin babbar likitar mata ce tana yin aiki a asibitinta da ma sauran asibitoci na gwamnati da na kuɗi. “Oyoyo da Suby,yau an tuno da mu” shi ne abin da ta faɗa tana murmushi,ba tare da wata kunya ba na gaishe ta tare da zuwa na rungume ta ina cewa “ai tun ɗazu na zo mun fita ne” “Ubaidah me yasa ba ki kira ni ba? Tun ɗazu na sauka kawai na tsaya cikin office ne ina duba saƙonnin wayata.Ina Mamarki fatan duk kuna lafiya?” “Lafiya lau tana can gidan rasuwa,kawunmu ya rasu” na bata amsa. Ta ce “innalillahi yaushe? Amma kuma ba ta kira ni ba Allah ya jiƙansa” “Amin !” Ubaidah ta yi saurin amsawa tare da zuwa ta janye ni daga jikin Ammy tana cewa “ya isa haka to malama,Ammy ni yaushe rabon da ki saka ni jikinki saboda Allah?” Sallamarsa ita ta katse mana ɗan nishaɗin da muke yi,ni dai sunne kai na yi ban sake ɗagowa ba ina jin su dai suna magana Ubaidah na shaida masa ta ga key ɗin motarsa. Ammy ta ce “ku wuce can sama in kun yi sallah ku sauko akwai aikin da zan saka ku” kamar ta luntsuma ni aljanna haka na ji,wannan yasa har tuntuɓe nake yi wurin nufar sashenta sai dai ban ma kai ga fara hawa step ba Ubaidah ta yarfa ni. “Ita fa can tsoron Ya Ubaidullah take yi shi yasa ki ga tana wancan saurin” shi ne abin da ta faɗa tana dariya,na juyo zan yi mata masifa karaf idanuna suka sauka cikin nasa a dole na fasa kawai sai na sa kai. Cikin fushi na shiga toilet ɗin, wannan karon ma kamar jiya a asibiti haka na ji ana yi mini magana cikin ƙwaƙwalwa sai dai wannan karon ban iya tantance me ake faɗa ɗin don ji nake kamar muryoyi dayawa ne ke magana lokaci guda.A nan take kaina yayi wani mugun sarawa,a dadafe na ɗauro alwala na fito. Jiri na soma gani kafin na ji wani abu mai ɗumi ya biyo hancina,na kai hannu na laƙato na duba sai na ga baƙin jini baƙi ƙirin mai duhu.A nan take casbin hankalina ya tarwatse,daidai nan kuma Ubaidah ta shigo.Da idanuna da nake jin tamkar an sauya mini su na dubo ta a raunace,ta zo da wani irin sauri ba tare da wani tunani ba ta saka hijabinta ta fara goge mini jinin wanda kamar ma sake tunkuɗo shi ake yi. “Me ya faru? Don Allah yi haƙuri ban san ranki zai ɓace” tana furucin ne idanunta na cikowa da hawaye. “Udah kaina! Ciwo yake yi mini” na furta dakyar ina mai kama kan,yayin da ita kuma ke ci gaba da goge mini jinin da zarar ya ƙara zubowa. “Kin ga zo mu sauka ƙasa” ta faɗa tana wani jana da ƙarfi,haka na take mata sawu.Step ma bibiyu muke taka shi . Ko da muka sauka tuni jini ya gama wanke mini gaban rigata don tun zan shiga alwala na cire hijabina. “Ammy? Ammy ?” haka take ƙwala kiran Ammy sai dai ba ta fito ba sai Yaya Ubaidullah ne ya fito sanye cikin farar jallabiya,ɗan madaidaicin gemunsa na ɗigar da ruwa da alamu alwala yayi. “Subahanallah ! Me ya same ta?” ya tambaya. “Ni ma ban sani ba kawai na same ta jini na ɓulɓulo mata ta hanci” Ubaidah ta basa amsa. Ya ce “shi ne kuma kika bar ta a tsaye madadin ki zaunar da ita“ yayi furucin a ɗan ruɗe kafin ya kama hannuna ya zaunar da ni kan kujera sai ya ɗaga kaina sama tare da soma bubuga goshina yana yin addu'a “As'alullahul Azima Rabbal Arshil Azimi an yashfiki” ya karanta wannan addu'ar har sau bakwai kafin kuma ya ja “lahaula wala ƙuwata illa billah!” ita kuwa ban ma san adadi ba,sannu a hankali duk na ji abin da ya taso mini ya ɗauke ɗif sai ajiyar zuciya da na shiga saukewa. Ya ja da baya yana kallona,na ɗan sunne kai murya na rawa na ce “na gode” bai ce komai ba ya fice .Ubaidah kuwa kusan ƙafafuna ta zauna ta saka ni a gaba tare da zuba uban tagumi,na fi kowa sanin ta yanzun nan sai ta shiga damuwa saboda hakan.Ta ƙasan ido duk nake ƙare mata kallo kafin na ɗago na ce “ tashi mu je mu yi sallah Udah” tana jin na ambaci wannan sunan sai ta ja numfashi saboda muddin ina fushi da ita ban kiranta da shi,sau tari kuma ina ambatonsa don nuna mata ƙaunarta a raina dashe ne daga Rabbi. A tare muka koma can sama, wannan karon da zan shiga banɗaki sai da na yi addu'a.Rigar na cire na yi wanka haɗi da alwala na fito na gabatar da sallah,ita ma kusa da ni ta zo ta yi.Muna zaune dukkanmu muna lazimi Ammy ta shigo ita da ɗaya daga cikin ƴan aikin gidansu ita kuma hannunta riƙe da kayan gugar tiles.Duk inda jinin ya ɓata ta goge,Ammy ta zo tana tambayata jikin kafin kuma ta ce “doctor na kan hanya zai zo ya duba ki” “Ammy ai na warke kin ga jinin ya tsaya” na faɗa . Ta ce “ba ni ce na kira shi ba Yayanku ne“ Ban ƙara cewa komai ba sai Ubaidah ce ke cewa Ammy “don Allah ki kira a gidansu ki ce a bar ta nan ta kwana har zuwa da safe sai ta koma” Ammy ta ce “kin ga na ma manta ina cewa in kira ta na yi mata ta'aziyya kafin mu je” Sai kuma ta fita,sai a lokacin kuma na harari Ubaidah ina mai cewa “yarinya ni gidanmu zan je” Ta ce “daɗin abin dai ni ma gidanmu ne kuma na fi ki iko da shi saboda wata rana dole ki fita cikinsa zuwa gidanki” “Tun da ni na ce miki zan yi aure...” sai kuma na yi shiru jin sallamar Ya Ubaidullah daga can falo. Da sauri ta fita kafin ta dawo tana yamutsa fuska,na ce “ya dai?” “Ki fita ga likitan nan” ta bani amsa . “Kamar ya na fita? Ke kuma fa?” Kafin ta bani amsa daga can falo Ya Ubaidullah ya kira ni “Su...by” yanayin yadda ya kira sunan yasa muka saki murmushi tare ni da ita. Na amsa da “na'am” kafin na miƙe na kamo hannun Ubaidah don mu fita tare amma ganin ta tirje yasa dole na fita zuwa falon.Suna a tsaye shi da wani farin matashi siriri,gaishe su na yi a ladabce shi kaɗai ya amsa yana mai cewa “ita ce patient ɗin?” “Eh ka duba ta” ya basa amsa. “Zauna” doctor ɗin ya faɗa tare da nuna mini kujera,na zauna yayin da shi kuma ya buɗe ɗan akwatinsa na likitoci ya saka safar hannu tare da ɗauko fitila da kuma wani abu dogo siriri.Nan take tsoro ya kama ni,murya na ɗan rawa na ce “ban so” Da mamaki ya ce “me?” Na nuna masa abin ina cewa “ban so ka sa mini shi a hanci” “Babu wani zafi” ya furta tare sunkuyo wa zai kama kaina da wani irin sauri na kauce. “Ya Ubaidullah ina ga sai ka riƙe mini ita” doctor ɗin ya faɗa .Ina jin haka na soma yin hawaye muryata na ɗan rawa na ce “Udah?” ita ce kawai za ta zo na samu sukuni sai kuma ta ƙi fitowa. Ban ga tahowarsa ba sai ganinsa na yi a gabana,kan nawa ya ɗaga tare da sa ɗaya hannun ya rufe mini idanu.Kokowa kawai na soma yi da numfashina ina jin doctor ɗin na taɓa hancina,ba a wani ɗauki lokaci ba Ya Ubaidullah ya matsa sai na buɗe ido ina kallon doctor ɗin da yake yi mini dariya. Wani ɗan ƙaramin book ya fiddo yana mai cewa “me sunanki?” “Suwaiba Abdullahi ” na basa amsa sai ya rubuta tare da ƙara yin wata tambayar “shekarunki fa?” Shiru na yi ina tunani kafin na ce “na manta amma Udah ta bani shekara uku da ko wata nawa ma ne.... Na manta amma bari na tambayo ta” Ido ya tsura mini yana yi mini kallon burgewa,ni kuwa ban damu ba na shiga can uwar ɗaka.Na samu Ubaidah zaune a bakin bed tana kallon ƙofa.Na yi mata hararar wasa ina mai cewa “dalla Malama ni faɗa mini shekaruna nawa ?” Sai da ta yi wani murmushi kafin ta ce “goma sha bakwai da wata uku” “To ban gode ba” na faɗa tare da fitowa,na ce masa “yawwa 17years da wata uku” Murmushi yayi ya rubuta,ni kuma na koma wurina na zauna.Wayar Ya Ubaidullah ta hau ringing sai ya fita,doctor ɗin ya bi shi da kallo kafin ya juyo gare ni ya ce “lambar wayarki ” sam ban kawo komai a raina ba haka na basa ya rubuta,sai ya ce “zuwa gobe in na gama bincike zan sanar da ke result kin ji preety” Na ɗan murmusa tare da sunne kai na lura yana son barkwanci. Ya Ubaidullah ya shigo yana cewa “Abdul Hamid in ka gama ka same ni a mota ka ɗan yi sauri amma” “Na ma gama mu je” ya furta tare da bin bayansa suka fice ni kuma na koma wajen Ubaidah na ce “na dawo ba su cinye ni ba sai ki taso ki mayar da ni gida” ★A can ɓangaren Ammy kuwa ko da ta koma ɗaki Mamu ta kira ta yi mata ta'aziyya tare da neman alfarma tana son Suwaiba ta kwana a nan saboda akwai aikin da za su yi mata. Mamu ta ce “babu damuwa ni ina ma nan gidan makoki a nan zan kwana,ashe can ta tafi sam ba ta sanar da ni ba ma” “Eh tana nan in sha zuwa goben za mu zo tun da ita ta san gidan ai shikenan ” ba su wani tsaya tsawaita hirar ba suka kashe.Ammy ta miƙe cike da damuwa tana tunanin maganar da yau wata bararoji ta faɗa mata.Allah ya gani ita mace ce mai riƙo da addini sam ba ta ma wani yarda da canfi ba,amma sai ga shi maganar wata ƙasƙantaciya ta yi tasiri a ranta.Ta ja ajiyar zuciya tana mai cewa “ni kam banda maƙiyi a duniyar nan ai ballantana na ce shi ne ke son ganin na tozarta ” Sai kuma ta ƙara lulawa duniyar tunani nan ɗin ma ba ta samo maƙiyi ko ɗaya ba.Waya ta yi a can asibiti,wata nurse ta ɗauka Ammy ta ce “ki duba gado mai lamba uku har yanzu bararojin nan bacci take yi?” “To madam” ta furta can kuma ta ce “eh ga ta nan har yanzu ba ta farka ba” Ammy ta ce “yawwa kina jina kar a saki a bari ta fita,ki cewa doctor wanda ya hau gobe na ce kar a bata takardar sallama” “To Madam ” ta sake faɗa,Ammy ta kashe kiran tana ɗan jin sanyi a ranta. ★A can gidan makoki kuwa tun da Sulaimanu ya shiga cikin gidan Mama Lantana ta soma cewa “to ga ma angon nan,ku dube shi ɗan albarka mai farar zuciya amma za a canfa aurensa ” yana jin haka ya fito ya bar su Mama Lantana na ƙara gishiri da magi a maganar.A haka har yamma ta yi,tsabar mugunta yasa ta fito waje cikin maza ta yi wa Abba magana ya taso ya zo inda take. “Ka ga dai bai kamata a ce duk mun tafi an bar matar malam ita ɗaya ba,shi yasa na yanke shawara ni zan koma gida domin kula da yara.Ita kuma Zainaba ka ce ta zauna a nan ɗin don ɗebe kewa” Abba wanda tun tuni ya zama mijin ta ce yayi na'am da zancenta.Har cikin gida ya samu Mamu ya bata umarnin kwana a nan yayin da ita kuma Mama Lantana ana gama kiran sallar isha'i ta tattara ita da ƴaƴanta suka koma gida zuciyarta fesss don ta yi alƙawarin yau sai ta tsorata Suwaiba fiye da jiya. Suna isa ta tarar da gida a buɗe,duk a tunaninta Suwaibar ce ta buɗe shi kasancewar ita da Mamu kowa nada makulli.Direct ɗaki suka shige,dama sun ci abinci a gidan makoki.Waya Mama Lantana ta soma yi ita da Kaka kamar yadda suke kiran mahaifiyarsu ta tabbatar mata zuwa jibi take dawowa daga ƙauye. Sun raba dare suna hira kafin Abba ya shigo,duk sai suka nufi ɗakinsu.Mama Lantana ta soma juya idanunta wanda hakan yasa Abba yayi saurin zama ƙasa kamar wani ɗanta ya ce “me kuma na yi yanzu?” “Ba ka yi komai,dama so nake na ja ma kunne in ka kwanta kar ka fito sai sallar asubah da kaina ma zan tashe ka” Cike da ladabi ya ce “to hajiyata” Mama Lantana ta washe baki don tana mugun jin daɗi in ya kira ta da wannan sunan.Har uwar ɗaka ta yi masa rakiya sannan ta dawo falo ta kwanta bayan ta rufo ɗaki.Lamo ta yi kamar mai shirin yin bacci kafin ta rikiɗe ta zama mage,ta window ta fita tare da nufar ɗakin Mamu ta kuwa ci sa'a yana a buɗe sai dai tana shiga wayam babu Suwaiba. Cike da takaici ta fito ta haye katangar maƙwabta ta soma koke-koke “minyau! Minyauuu!” amma babu wanda ya kula ta don in da sabo su makwabtakan ma tuni sun saba da wannan kukan saboda kusan ko wane dare suna jinsa.Mugunta kawai take son yi,wannan yasa ta bi gidaje sai dai yau ba a fito a sa'a ba.Har tana shirin komawa gida kuwa ta tuna cewa muddin Suwaiba ba ta gida to ba ta da wurin zuwa in ba gidansu Ubaidah ba.Kamar abin tsiya haka ta dinga ƙetara katangu tana wucewa har ta je gidan. ★ Duk yadda na so zuwa gida hakan ba ta faru ba saboda Ammy da kanta ta zo ta shaida mini yadda suka yi da Mamu.A dole na haƙura,na so kiran Mamun jin wai a can za ta kwana sai dai sam ban son jin wannan yanayin nata na damuwa. Bayan sallar isha'i Ubaidah ta kawo mana abinci muka ci,sai kuma muka fiddo takardun makaranta muka shiga dubawa bayan nan muka yi shirin bacci. Ni na soma kwanta ina mai lumshe ido,ta ce “gobe in Allah ya tashe mu tun da safe zan yi miki kitso irin mai taliyar nan” Na saki murmushi na ce “a'a ni mai tuwo nake so” ita ma dariyar ta yi ta soma yi mini surutunta,tun ina saurarenta har ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba.Sai dai bai yi nisa ba na soma jin kukan mage a can kusan window da ke rufe da madubi amma duk da hakan bai hana kukan nata ratsa dodon kunnena ba.A hankali na ɗan ware idona,ɗakin tarau yake da haske ba a kashe ƙwan lantarki ba hakan ya bani damar hango Mama Lantana cikin madubi tana a tsaye ta kafe ni da,juyawa na yi da sauri saitin window nan kuma mage na gani madadinta ina sake maido kallona cikin madubi sai kuma na ga Mama Lantana da kanta na mutane jikinta kuma na mage tuni ta ratso madubin window ɗin ta yi tsalle tana niyyar dirowa kan gado,ɗif numfashina ya tsaya cak ..... [05/06 09:03] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *ROMON HAƘURI* 🤍 MRS SADAUKI ✍️ FCWA ☀️ *Wannan labari ba ƙirƙira ba ce,labari ne da ya faru a gaske ina fatan za ku bibiye shi sau da ƙafa* *__________________________________________________* 🚫Don Allah ko ba ki karanta ki yi sharing a wasu group domin mutane su amfana da darasin ciki. 04 Ubaidah wacce fitowarta kenan daga toilet ta hango mage kan gado tana son hayewa kan Suwaiba da ke kwance.Da wani mugun sauri ta ɗauki pilow tare da yin tsalle ta danne Mama Lantana da ke cikin siffar mage. Zillo ta soma yi tana son fitowa amma ita kuma Ubaidar sai ƙara danne ta take yi,duk da idanunta ba su iya ganin cikakkiyar siffarta amma ta yi imani cewa ba normal mage ba ce muguwa ce.Wani irin kuka Mama Lantana ta soma yi irin na jarirai wai don ta tsorata Ubaidah ba ta san ta yi ga banza ba sam Ubaidah ba ta da tsoro.Cikin wata irin murya mai cike da ɓacin rai ta soma yin magana "wato kin zo ki cutar da masoyiyata duk damuwar da take ciki so kike ki ƙara mata wata akai to zan kashe ki ” Mama Lantana na jin haka sai ta ɗauke numfashi ta yi kamar ta mutu, Ubaidah jin tsit sai ta ɗaga pilown wuf Mama Lantana ta yi tana mai yin tsalle ta haye window.Da wani irin gudun bala'i ita ma Ubaidah ta je ta ja madubin window sai ya dantse ƙafar magen ta baya,ta saki wata razananiya ƙara sai dai wannan karon ta muryarta ce dak.Da ƙarfi ta ja ƙafarta ta fito ta soma ƙetara katangu ta gudu ta bar gidan. Ubaidah ta ja numfashi tana mai duban Suwaiba,sai a lokacin ta lura sam ba ta yin numfashi.Ruwan sanyi ta ɗauko ta zuba mata amma shiru ko yatsa ba ta motsa ba,da wani irin sauri ta fita tana kuka tana kiran Ammy. Ubaidullah da ke nan babban falo yana kwance yana waya da Hamida yayi saurin ɗagowa ya dubi Ubaidar yana cewa “ke lafiyarki?” Nuni ta yi masa da can saman ɗakinta,ya cewa Hamida “ ina zuwa” bai jira cewar ta ba kuma ya kashe kiran ya ƙara fuskantar ƙanwar tasa,kafin ya sake tambayarta ta ce “mayya ta shigo ta tsotse jinin Suby ga ta can a kwance babu rai” Ƙirjin Ubaidullah ne yayi wata mummunar faɗuwa,jin ta ambaci mayya da kuma mutuwa.Idonsa na rufewa ya soma haurawa can saman,sam bai wani damu ba na ganinta sanye da kayan bacci.Taimako ya soma bata ta hanyar zuba mata ruwan sanyi jin ta ambaci har da mayya sai ya ƙara da tofi.Hannunta ya riƙe yana murza tafukanta da sauri yana mai ambaton sunan Allah da jero duk addu'ar da ta zo bakinsa,dandanan suka fara ɗaukar zafi sannu a hankali kuma bugun zuciyarta ya soma tafiya. “Suwaah?” na ji amon muryar da ko cikin duhu ko magagin bacci ba za ta ɓace mini ba.Ina jinsa sarai yana mai ci gaba da tuntsire sunana na Suwaiba yana mayar da shi Suwaah ban sani ba ko tsayi yayi masa oho,abin da na sani shi ne kawai ba zan iya amsa ba saboda wani abu mai nauyi da ya danne mini kai.Duk yadda na yi yunƙurin buɗe idanuna kuma na kasa,kukan Ubaidah na soma ji a gefe yayin da muryar Ya Ubaidullah ke cewa “je ki tada mota Ubaidah ina ga sai mun wuce da ita asibiti” Sautin kukanta ta ƙara ina ji,har lokacin da ta soma kiciniyar neman key ina jin motsi sai dai banda damar yi musu magana. “Ki je key ɗin motata na kan kujera a falo” ya furta tare da sunguma ta.Ina jin duk lokacin da yake taka step yana sauka da ni ƙasa,har sa'ilin da iskan Ubangijin ya bugi gangar jikina. “Zauna baya ki tallabe ta ni zan yi tuƙin” ya furta,ina jin lokacin da ya saka ni a motar sai kuma Ubaidah ta rungume kaina tsammm a ƙirjinta daidai nan na ja wata ajiyar zuciya tare da fashewa da kuka ina mai buɗe idanuna. Ya Ubaidullah da ke ƙoƙarin yi wa mota key ya juyo da sauri cike da mamaki yana kuma yi wa Ubangiji hamdala.Har wata sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke wacce yake jin tamkar an dawo da ransa ne. “Subyna?” Ubaidah ta faɗa tana bubuga bayana alamun rarrashi,ban amsa mata ba sai sautin kukan da na rage tare da tashi zaune. Ya Ubaidullah ya fita tare da buɗe ƙofar ɓangarena,a hankali na ziro ƙafata wacce take sintir babu takalmi.Kamar wata baturiya haka na yi tsaye da kayan baccin waɗanda suka kasance wando ne iya gwiwa sai rigar marar hannu,gashin kaina wanda ya sha gyara sai tashi yake yi cikin iska. Kamar yadda yake kallona haka ni ma na ɗan tsura masa nawa idanun da har yanzu ba su bar zubar da hawaye ba. Hannuna ya kamo yana mai cewa “me kike ji? ” Hannun nawa da ya riƙe na kai duba akai kafin na girgiza masa kai,ci gaba ya yi da kallona kafin kuma ya dubi inda Ubaidah take a tsaye jikin mota .Ni ma sai na kai dubana,sai na ga ta harɗe hannuwa ta tsura mana na mujiya. A hankali na janye hannuna daga cikin nasa kafin na kama hanyar komawa cikin falo,ina tafe ina son tuna abin da ya faru da ni amma sam na kasa tunawa.Ko da na isa can ɗakin Ubaidah sai na yi zaune tare da zuba uban tagumi,Mamu ta faɗo mini a rai na ɗauko wayata zan kira ta sai kuma na fasa gudun kar na tayar mata da hankali. A can kuwa ɓangarensu Ubaidullah,wani irin sanyi ne gwiwansa suka yi sam ba zai iya cewa ga dalilin da yasa ya damu da ita har haka ba.Ga shi kuma ƙanwarsa na yi musu wani kallo,ko don ta ga ya riƙe hannun ƙawarta ne oho.Ya cije leɓensa na ƙasa kafin ya cewa Ubaidah “ki shiga ciki sannan ki kula da ita,ƙila duk don ɗazu ta samu matsalar nan ne ta haɓo” “To” ta furta tana mai goge fuska kafin ta wuce,ya bi bayanta da kallo har ta shige.Zagayen gidan ya soma yana tuna wasu hirarraki da suka yi da Hamida kaɗan daga ciki su ne “Ya Ubaidullah duk ranar da ka fara mugun sona to za ka ji iskan shaƙa na yi maka kaɗan,za ka fi son iskan waje kan na ac.Kuma za ka ce na faɗa ma duk ranar da ka tsunduma a kogin so to za ka kasa controling kanka ƙila ma ka yi abin da bai dace ba” ido ya rumtse kafin ya nufi can inda ke da flower dayawa ya soma shafa ta yana mai ɗaga kai yana kallon benen ɗakin Ubaidah. Ya jima sosai yana kallon wurin kafin ya koma ɗaki,wayarsa ya ɗauka kafin ya ɗauki hanyar da za ta kai shi ga tabkeken benen part ɗinsa wanda shi ne ma ya kusan cinye rabin falon tsabar girmansa. Yana shiga a falonsa ya zube kan kujera ,kiran Hamida ya shigo.Ya ja uban tsuki yana jin takaicinta,haka yayi ta kallon screen ɗin har call ɗin ya yanke.Sai a lokacin ya ga ta yi masa kira sama da ashirin,ya ja uban tsuki yana mai cewa “sai ka ce ita kaɗai ta fara sona a duniya kira kamar mayya, wannan da mayyar ce ƙila da tuni ta yi farfesuna ta cinye” sai ya saka wayar a silence kawai ya lumshe ido kamar mai shirin yin bacci. Hirarsu da Dr Abdul Hamid ta faɗo masa wacce suka yi ɗazu bayan ya gama duba Suwaiba.Babu kunya Dr Abdul Hamid ɗin ya ce yana son Suwaiba ta yi masa ,har da yi mata wani suna wai shi pretty.A take ya ji ya tsani sunan da shi kansa wanda ya ƙirƙiro shi .Ganin baccin ba zai samu ba ya sa miƙewa ya wuce bedroom,wanka yayi ya zo yayi nafila tare da niyyar yin istikhara na dangane da abin da yake ji yana tunkaro shi in alkhairi ne Allah ya ƙara tsoma shi a ciki.Akan dadduma yayi bacci,bai farka ba sai da aka soma yin kiran sallah.Wanka ya sake yi sannan ya wuce masjid,bayan an idar da sallah ya dawo .Kamar ya je can ya dubo ta haka yake ji amma ganin gari ma bai gama yin haske ba ya haƙura ya koma ɗakinsa. ★Da ɗingishi Mama Lantana ta koma gida,tsinuwar da ta yi wa Ubaidah kafin ta isa gida ta fi shuren masaki.Ta yadda aka yi ta canza siffa daga mutum zuwa mage ta wannan hanyar ta sake bi.Tana gama ɗaukar siffarta ta bil'adama sai ta kai dubanta ga ƙafarta ta hagu yadda ta kumbura ta yi suntum tuni ma akaifar ƙaramin yatsa ta fice tana zubar da jini. Miƙewa ta yi dakyar za ta fita daidai Hassana ta fito tana hamma,wani irin turus ta yi tare da maƙalewa jikin katanga tana kyarma tana mai ci gaba da kallon yadda idanun Mamarsu ke wani ƙyalli suna canza kala. Mama Lantana a jikinta ta ji ana kallonta wanda kuma haka ne duk wani mugu ko ya aka ga ɓarrakar siffarsa yana ji cikin ruhinsa ne.Da wani irin sauri ta lumshe idanunta kafin ta waiga daidai inda Hassana ke tsaye ƙyam,“ke don ubanki tsayuwar me kike yi mini a falo?” Hassana ta yi saurin jan ajiyar zuciya ganin idanun nata sun dawo daidai,ta ce “wallahi Mamarmu mugun mafarki na yi wai Hussaina ta mutu mayya ta damƙe mata kurwa,ina tashi kuma na ji mugun ƙishi shi ne fa na fito amma ba yawo nake yi ba” Suman tsaye Mama Lantana ta yi jin an ambaci wai mayya ta kashe mata ƴa,a cikin zuciyarta ta ce ‘ Allah yasa ba gaskiya ne ba,don in dai mayya ta kame Hussaina ai asirina ya gama tonuwa a idon duniya’ A fili kuma sai cewa “kin kwanta babu addu'a ba dole ki yi mugun mafarki ba,je ki sha ruwan ki zubo mini a babbar roba ni ma zan saka ƙafata” Hassana ta je ta buɗe ɗaki tana mai cewa “me ya samu ƙafar?” ƙin tanka ta Mama Lantana ta yi har ta fita,babu jimawa kuma ta dawo da ruwan kamar yadda ta ce ta ajiye mata a gabanta. Mama Lantana aka samu wuri aka zauna sannan ta ƙara jawo robar,tana saka ƙafarta sai ta soma sauke ajiyar zuciya sanyin ruwan na ratsa ta. ★Sulaimanu Tun da ya ji kawu ya rasu ya ji a ransa dole a bar maganar auren nasa zuwa wani lokaci.Garin ya ji duk ya fice masa wannan yasa ma ya dawo gida,tun dawowarsa daga gidan makoki bai tafi ko ina ba yana ɗaki.Iya Ubaidah kawai suka yi waya yana jin kamar ya janyo ta ya kawo ta kusa da shi.A cikin dare kasa yin bacci yayi saboda tunanin duniya,ga zuciyarsa na wani irin nauyi sam garin ya fita ransa . Washegari ko da ya dawo daga sallar asubah sai yayi wanka ya jawo akwatinsa ya ƙara gyara shi.Lokacin da ya fito gari yayi haske,tuni su Mama Lantana ana waje a tsakar gida.Tana ganin Sulaimanu jaye da akwati ta saki wani makirin murmushi tana jin a ranta ba ƙaramar sa'a ta yi ba da ta samu Yawale matsayin malami ba. “Ina kwana Mama” Sulaimanu ya faɗa cike da ladabi ,a gadarance ta amsa tana tsure shi da idanun da kullum su ne ke ƙara raunata ruhinsa yake jin tsoronta kamar rai da ajali. “Sai tafiya?” ta jefo masa tambayar, Sulaimanu wanda ya sunne kai tun bayan da yayi ido huɗu da ita ya ce “eh Mama sai kuma in na sake dawowa” “To ai ko ka tashin ba za ka sanar da ni ba sai dai na gan ka tun da yanzu ba a bakin komai nake ba” Mama Lantana ta faɗa cikin ɓacin rai wanda malam Yawale ne ya tabbatar muddin tana nuna masa haka to tabbas Sulaimanun zai ƙara tsoronta. Jikinsa na wata kyarma kuwa ya zube gwiwansa a ƙasa yana bata haƙuri,amma saboda mugunta ta Mama Lantana sai ta juye kai tana wani yin ƙyaci a zuci tana cewa ‘ yadda saboda ƴar uwarka na ji ciwo kai ma sai na azabtar da kai’ “Mama don Allah ki yi haƙuri wallahi in kina fushi sai na dinga jin zuciyata na ƙunci kamar ana gasa ta a wuta” ya faɗa cike da rauni irin na wanda aka asirce. Surajo wanda shigowarsa kenan ya ji kuma abin da Sulaimanun ke cewa,da mamaki ya dubi Mama Lantana yana mai cewa “wai ke mene ne haka ? Kullum cikin sabuwar masifa kike tsirowa ” Jikin Mama Lantana ita ma yana ƴar rawa ta ce “Manu tashi ka tafi” bawan Allah sai ya miƙe,Surajo ya zo ya ɗauki akwatinsa yana mai hararen Mama wacce duk taƙadirancinta tsoron babban ɗan nata take ji Surajo don ba ƙaramin aikinsa ba ya ɗirka mata na jaki saboda ƙwaƙwalwarsa ba daidai take ba shaye-shaye ya rikita ta. Suna fita Sulaimanu ya ja wata ajiyar zuciya,jininsa ya haɗu da Surajo sosai.“Ya kamata ka nutsu Surajo babu kyau yi wa iyaye irin haka,Mama uwa ce duk abin da ta yi daidai ne” “Kai dai za ta yi wa,ni ta isa ma ta wani sa na zube ƙasa a gabanta? Dubi dalla yadda ta sa kayanka suka ɗau ƙura” ya faɗa yana wani juye baki irin ƴan daban nan.Shi dai Sulaimanu bai ce komai ba,a haka suka isa tashar mota dama ba su da wani nisa sosai.Sai da motarsu za ta tashi sannan Surajo yayi masa sallama da fatan sauka lafiya,Sulaimanu ya ciro kuɗi aljihunsa ya basa yana mai cewa “ga wannan amma don Allah iya abin amfani za ka saya da su” Ya karɓa yana godiya kafin ya ɗaga masa hannu.Sulaimanu dai jingina yayi a jikin kujera yana jin ƙunzi,ko kaɗan kuma zuciyarsa ba ta wani tuna masa da Mamu ba kuma wannan yana ɗaya daga cikin makircin Mama Lantana ita ce ta asirce shi ta hana ƙwaƙwalwarsa tunanin daidai,duk wata daraja da ƙimar uwa ta maido ta a kanta madadin ya yi wa uwarsa Mamu. Sun yi gudun awa uku kafin su isa,wani huci mai zafi ya furzar sa'ilin da ya fito ya shaƙin iskan garin wanda da ace yana da ikon canza ƙaddararsa da ko sunan garin ba zai ƙaunaci a furta ba ballantana yayi aiki cikinsa.Akwatinsa aka sauko masa,ya tari ɗan acaɓa ya kwatanta masa inda zai je kafin ya hau. An yi gudun kamar min goma sannan suka isa wani gida ginin ƙasa. Sauka yayi ya basa kuɗinsa ya ja akwatinsa,yana tura ƙofar ta buɗe .Kamar kullum yau ma gidan,matan banza sun cika shi sai ba'a suke da raha a tsakaninsu da kuma waɗanda suka kawo su.Kai ya kawar saboda kaf cikin matan babu wata mai suturar kirki,mai dama-dama a cikinsu ce ta yi ɗaurin ƙirji. “Ah Sulaimanu har ka dawo?” Abbas ya tambaya yana mai ɗan ture wata mace da ke kwance a jikinsa.Ya ɗan murmusa ba tare da ya dube shi ba ya ce “eh wallahi yanzu na shigo” sai kawai ya nufi babban falon nasu wanda ke ɗauke da ɗakuna a jere sun fi biyar.Makulli yasa ya buɗe nasa ɗakin ya shiga,yana ƙoƙarin kwanciya Abbas ɗin ya shigo yana cewa “fatan dai lafiya na ga jiya-jiyan nan ka tafi?” “Lafiya lau” ya basa amsa a takaice,sarai Abbas ya san suna cutar da abokin nasu wanda kaf cikin ƴan sandan da suka zo wannan yanki shi kawai ne bai harakar mata. Zama yayi kan kujera tare da yin shiru yana kallon Sulaimanun wanda damuwa ta gama aurensa tasss. “Ina su Mamu da kuma Auta?” ya faɗa don ya san a faɗin duniyar nan su ne kawai ke haska rayuwar Sulaimanun. “Suna can na baro su gidan makoki kawu ya rasu maganar auren ma da na je yi shiru babu wani labari” ya faɗa kamar zai fasa kuka. Abbas ya ji babu daɗi sosai a ransa nan ya shiga basa haƙuri,suna cikin haka ne ɗaya daga cikin baby's ɗin da suke kawowa ta shigo babu ko sallama,hannunta riƙe da plate sai wani yauƙi take ita ala dole ga macen da ta waye. “Ga abinci ” ta faɗa tana miƙowa Sulaimanu plate ɗin,wani kallon tsanake yayi mata.Sanye take da ɗan ƙaramin sket iya gwiwa sai wata shegiyar riga wacce ba ta da marabi da bra,cibiyarta a waje ta saka mata wata wani ɗan kunne.Gabansa banda babu faɗuwa babu abin da yake yi,ba tun yau ba take gwada sa'arta wurin jan hankalinsa ya taɓa kama su suna hira ita da abokansa da kuma nata tana cewa “ni dai ina mugun ra'ayin Sulaiman,ku taimaka ku ce ya kula ni ko sau ɗaya tak” Kansa ya kawar yana mai cewa “Abbas zan kwanta na huta saboda jiya ba wani baccin kirki na yi ba” yana faɗar haka ne tare da yin kwanciyarsa ya juya musu baya. Abbas ya dube ta ya ce "mene ne haka? Don Allah fita.Sulaimanu ka yi haƙuri zan yi musu magana dukansue” sai kuma ya ja ta da ƙarfi suka fice suka bar Sulaimanu cikin wani yanayi da ya gwammaci ya mutu kan ya saɓa wa Ubangijinsa,hawaye ne masu zafi suka dinga ƴar rige-rigen fita daga idanunsa.Ya jawo wayarsa yana dubawa,sai a wannan lokacin ma ya tuna ko sallama bai yi wa Ubaidah ba. ★Washegari bayan mun yi sallar asuba ba mu koma bacci ba haka muka zauna ni da Ubaidah muna yi wa junanmu tambayoyi akan addini,hakan ba shi ne farko ba don ko a makaranta haka muke haɗuwa mu da sauran ɗalibai muna zancen addininmu. “Faɗa mini surori nawa ne suka fara da Alif lamra? Sannan ki kawo mini su” Ubaidah ta tambaye ni. Na ce “shidda ne,suratul Yunus, Hud,Yusuf,Ar-Ra'ad, Ibrahim da kuma Al-hijir” “A wace sura ce aka taɓa faɗin sunan ɗaya daga cikin Sahabban Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama?” “Suratul Ahzab” “Wane sahabi ne?” “Zaydu” “Aya ta nawa ce?” ta ƙara jefo mini tambayar cikin salon ala dole sai ta ƙure ni,na ɗauki pilow na jefa mata na ce “wannan dai ya koma mugunta ” Tana dariya ta ce “to ki faɗa mana aya ta nawa ce?” “Ta talatin da bakwai ” Ya Ubaidullah ya faɗa daga can falo,sai muka kalli juna ni da Ubaidah kafin ita kuma ta fita da sauri tana ce “Ya Ubaidullah me yasa ka bata satar amsa?” Daga nan inda nake ina jin yadda yake murmushi mai kamar dariya kafin ya ce “to ai duk ɗaya ne?” “Kai da ita?” na ji ta jefa masa tambayar. Shiru na yi ina jiran na ji amsar me zai bata sai kuma na ji tsit.Ƙamshinsa da na ji ya mamaye ɗakin yasa na yi saurin ɗagowa,ba tare da na shirya ba na ce “ina kwana Ya Ubaid?” Yayi wani ɗan guntun murmushi iya leɓe,bai amsa gaisuwar ba sai ce mini yayi “ya jikin naki?” “Da sauƙi sosai alhamdullah!” na basa amsa tare da sunne kai saboda yadda yake juya ƙwayar idonsa cikin nawa ba salon yadda ya saba ba ne. Ganin yayi tsaye ƙiƙam bai tafi ba na ɗan ɗago zan saci kallonsa sai na ga ashe har yanzu idonsa na kaina.Gabana ne ya shiga faɗuwa,sai na soma tunanin ko wani laifin na yi masa. Ubaidah ta shigo tana cewa “Suby sauko ƙasa mu ci abinci kafin mu shirya mu tafi ” “Ina za ku je?” “Wurin gaisuwa kawu ya rasu” “Allah ya jiƙansa” A tare muka amsa da Amin ,na miƙe muka fito ni da Ubaidah muka bar shi a can ɗaki.Har muka zauna muka soma yin kari bai fito ba,ni kuwa sai faman ɗaga kai nake yi ina kallon bene da na kasa haƙuri na ce "Udah ina jin tsoro kar dai a ce wani laifin na yi wa Ya Ubaid” Tana shirin magana ya soma saukowa idanunsa a kanmu,kamar yadda mu ma muke kallonsa.“Ya Ubaidullah zo ka ji Subyna ta samo maka sunan ƴan gayu” “Ƴan gayu kuma?” ya tambaya yana mai ƙarasowa,ta ce “ eh! Wai Ubaid” Na ɗan harare ta na ce “yanzu don na ce Ya Ubaid shi ne wani abu?” Ta ce “Eh ɗin me yasa ba ki ce Ubaidu ba” Ban san lokacin da dariya ta kubce mini ba na ce “haba dai sai ka ce wani ɗan ga ruwa” shi kansa sai da ya dara kafin ya ja kujera yayi zaune,daidai nan aka ranga uwar sallama.Duk muka juya muna kallonta kafin Ubaidah ta yi ihu ta ce “laaa anty Hamida ” sai kuma ta je da sauri ta rungume ta har sari ɗin da ta naɗe jikinta yana warware wa . Basket ɗin hannunta ta miƙawa Ubaidah,suna tafe tana ƙoƙarin gyara sarin har suka iso wurinmu.Ban sani ba ko ba ta lura da ni ne ba ko me,sai ta ja gemun Ubaidullah da ke yi mata wani kallo ƙila na mamakin ganinta. “Ka ga ta warware mini sari,gyara mini?” ta faɗa a shagwaɓe tana wani karya dogon wuyanta,a tare Ya Ubaid da Ubaidah suka kalle ni sai dai kowannensu da manufar nasa kallon..... [06/06 10:21] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *ROMON HAƘURI* 🤍 MRS SADAUKI ✍️ FCWA ☀️ *Wannan labari ba ƙirƙira ba ce,labari ne da ya faru a gaske ina fatan za ku bibiye shi sau da ƙafa* *__________________________________________________* 05 “Kin ga taso mu koma ɗaki muddin kina a gaban anty Hamida sai kin sha kunya,yanzu daga naɗin sari kin ji ta ce ya bata abinci a baki” cikin dariya da salon raha Ubaidah ta furta hakan. Na ce “to” tare da miƙewa ba tare da na gama cin abincin ba,Ya Ubaid ya ce “zauna” tare da tsure ni da idanunsa masu matuƙar kaifi.Babu shiri na zauna ɗin sai na ga ita anty Hamidar na yamutsa fuska kafin ta gyara sarin da kanta sai kuma ta ja kujera ta kusa da shi ta zauna tana mai cewa “Ubaidah zuba masa girkin da na yi masa,yau dai na sha alwashi a gabana za ka ci abincin ka bani maki ” ta ƙarashe tana murmushi. Ubaidah ta ciro kulolin daga cikin basket tare da ajiye su kan teburi sannan kuma ta buɗe su.Ƙamshin girkin ya garwaye ko ina,yau kuma waina ce da miyar kayan ciki.Anty Hamidar ce ta ɗauki plate ta zubawa Ya Ubaid kafin ta dubi Ubaidah ta ce “ku zuba naku ku ci ke ma ki faɗa mini in yayi daɗi sai ki bani maki” Ubaidah ta yi dariya tana mai cewa “waina na ɗaya daga cikin abincin da muke so ni da Suby ” sai kuma ta ɗauko plate ta zuba wainar,tana soma zuba miyar hankalina ya tashi yadda na gani miyar ta rikiɗe zuwa jini ,su kuma kayan cikin ɗanyu ne ba a dafe ba. Plate ɗin Ya Ubaid na duba wanda har yanzu bai ma kalli wainar gaban nasa ba ballantana ya ci.Motsi na ga kayan cikin na yi tamkar wasu masu rai,jikina ne ya ɗauki wata irin rawa kaina ya soma sara mini ita kuwa Ubaidah a gabana ta turo plate ɗin tana shirin zama ni na miƙe ina cewa "Udah ki kama ni kaina na yi mini ciwo” nan take kuma hancina ya soma zubar da jini,duk sai suka shiga ruɗu ita da Ya Ubaid ɗin.Wannan karon duk yadda ya so ya tsayar da haɓo ɗin abu ya cuttura dole muka fito zuwa asibiti. Muna isa aka yi katari kuma Dr Abdul Hamid yana nan ,shi ne ya yi mini aiki wanda kusan ba a hayyacina yayi shi ba saboda yadda nake jin ana yi mini magana a ƙwaƙwalwa. Ba a ɗauki wani lokaci ba jinin ya ɗauke,Udah ta zo ta zauna kan gadon na nake tare da kamo hannuna ba tare da ta ce komai ba. “Tun yaushe kike shiga wannan yanayin?” Ya Ubaid ya tambaye ni.Kai na girgiza masa ba tare da na ce komai ba,wayar Ubaidah ta yi ringing sai ta fita ta bar ni da shi.A hankali ya soma takowa,wanda duk tako ɗaya har cikin zuciyata nake jinsa.Daidai kusan kaina ya tsaya tare da kama yi ɗan matse,na lumshe ido ina jin wani irin motsi na kai komo. “Kina da jinnu?” tambayar da ta saka na ware idanuna cikin nasa kenan,na buɗe baki dakyar na ce “a'a banda” “Ba ki da ko kuwa ba ki sani ba dai?” ya sake jefo mini wata tambayar. Na yi ɗan shiru kafin na ce “ban sani ba” Ya janye hannunsa tare da sauke ajiyar zuciya,Dr Abdul Hamid ya sake shigowa wannan karon tare da Ammy wacce tun da muka tashi ban saka ta a ido ba. Kusan a tare muka gaishe ta ni da shi kafin ta tambayi jikina ya amsa da “sauƙi” kafin kuma ya ɗora da cewa “na je ɗakinki gaishe ki ban gan ki ba,wayarki kuma ba ta shiga ashe kina nan asibiti” “Eh wallahi akwai abin da ya hana ni sukuni ne shi yasa na zo” Hannunta ya kama suka fita waje,sai a lokacin Dr ɗin ya matso yana cewa “pretty ya jikin naki? Kin ga ki bar yawan damuwa shi ke jawo miki haɓo” Kai na jinjina masa ina ɗan murmushi kafin na ce “na gode sosai” hira ya zauna yana yi mini wacce rabinta duk akan aikinsa ne,ya gabatar mini da kansa tun daga sunansa har manufar karɓar lambata a jiya da yayi. Na dube shi na ce “wato wayo ka yi mini?” “Ni na isa na yi miki wayo pretty? Kyawunki ne ya hana ni yin magana” “Ni ai banda kyau” na furta ,ya ce “a'a bari faɗa don hakan babban zunubi ne,zo mu yi selfie” ya faɗa tare da ciro wayarsa ya ɗauke mu hoto,kafin kuma ya soma yin video yana cewa “yi murmushi mana prettyyy” ina shirin yin murmushin Ya Ubaid ya shigo sai na sunne kai ,murya a ɗan dake ya ce “ki sauko mu tafi” “A'a da ka bar ta har zuwa an jima” Dr Abdul Hamid ɗin ya faɗa . Ya ce “a'a yanzu za mu tafi” kallonsa na yi a raunace ,ni ma zan fi so na zauna a nan ɗin saboda na fara jin daɗin hirar Dr Abdul Hamid ko don ban taɓa yin saurayi ba ne oho. “Sauko” Ya Ubaid ya furta tare da zuwa ya kamo hannuna,a dole na sauko na miƙe tsaye.Har muka fito farfajiyar asibitin bai saki hannuna ba,can na tsinkayo Ubaidah a tsaye tana waya.Hannuna na fizge tare da nufar a guje saura ƙiris na zame na faɗi,“ki bi a hankali” na ji muryarsa ya faɗa da ɗan ƙarfi amma ban juyowa ba na ƙarasa na rungume ta. “ Hubby zan kira ka daga baya” ta furta tare da yanke kiran ta dube ni tana murmushi “ya jikin naki? Gida za mu wuce?” Na ce “ni ma ban sani ba Ya Ubaid dai ya ce na fito ” “Ok mu je” ta faɗa tana mai kamo hannuna,cikin tsokana na ce “wato sai ka ce wata ƙaramar yarinya har hannuna ake riƙewa” “To mene ne banbancin? Ke ma baby ce dole a kula da ke” ta faɗa tana ƴar dariya,ban dai ce komai ba har muka isa kusa da motar Ya Ubaid ,Ammy muka tarar a zaune a gaba wannan yasa mu muka koma baya . Sai da muka hau kan titi sosai sannan Ammy ta ce “da mun isa gida sai ki canza hijabinki Suby kawai mu wuce gidan makokin nan” “Haba Ammy mene ne kuma na sai mun koma gida? A saya mata sabo kawai a hanya” Ya Ubaid ya faɗa. Ammy ta ce “yanzu da safen ai ba kowa ya fito ba” bai ce komai ba sai gudu da ya ƙara,wani kantin kuwa ya tsaya da mu .Shi kaɗai ya shiga bai wani jima ba ya dawo mota tare da miƙo mini leda,na karɓa ina mai yi masa godiya sai na fiddo hijabin mai kyau kuwa launin green.A nan cikin motar na sauya shi,Udah ta ce “yayi matuƙar yi miki kyau kuwa” sai ta yi mini hoto Ni kuwa iya murmushi kawai nake zubawa ban ma san ta yi mini video ba saboda hankalina da ya ɗauku da idanun Ya Ubaid da ke kallona ta cikin madubi.Sunne kai na yi sai a lokacin kuma ya tambaye ni hanyar da za mu bi,dakyar na soma yi masa kwatance har muka iso gidan.Duk muka fito,a nan ƙofar gida suka yi wa Abba gaisuwa kafin mu shiga daga ciki.Mamu na a tsaye bakin murhu tana kaɗa kunu,duk cikin mutumci suka gaishe ta haɗi da yi mata gaisuwar,Ya Ubaid ya fita jin ana cewa a wuce can ƙurya matar malam na can. Ni na kai su suka yi mata gaisuwa, sannan muka zauna.Muna nan irin kamar minti ashirin aka soma shigowa da kayan abinci .Mama Lantana wacce shigowarta kenan da dukkan alamu kuma ba ta lura da mu ba ta ce “wane ne wannan mai motar ? Manu dai bai da ita ballantana na ce shi ne ” Hassana ta ce “bari na tafi wallahi sai na ga ko wane ne,maduban motar duk baƙaƙe ne zan bari sai ya fito” Ni dai kallonsu kawai nake yi,ita Hassana ta fita yayin da ita kuma ta ida ƙarasowa tana ɗingishi.Kan tabarma ta sube tana cewa “matar malam ana zaman makokin shi ne kika runtuma wannan uban turare mai ƙanshi haka?” “A'a Hajiya ce ta zo surukarmu” matar malam ta bata amsa,sai a lokacin kawai ta juyo inda muke.Da farko yanayin fuskarta duk a cije amma da yake ta iya munafurci sai ta washe baki tana cewa “ina kwananku Hajiya ashe kun ji labari,Manu ya sanar da ku ko? To ya za a yi kawun yara lokaci yayi babu rabon ganin bikin auren Manu” Ammy ta amsa da “dama haka ne kowa bai wuce lokacinsa Allah bai nufa za a yi da shi ba” “To Allah yasa dai a yi bikin wannan ɗage-ɗage ai ba na lafiya ne sai kace babu alkhairi tun ana ɗagawa yanzu an soma yin mutuwa.Wai amaryar ce nan? Ja'ira wato ba za ki gaishe ni ba ko kin yi tunanin kakar Manu ce kishi ya rufe miki ido?” Ubaidah ta yi ɗan murmushi tana cewa “ina kwana Mama ya kuma haƙuri?” Mama Lantana ji ta yi kamar ta je ta shaƙe mata wuya saboda ta sanadin bugun da ta yi mata ne yanzu take ɗingishi. “An godewa Allah a ci gaba da haƙuri kin ji ƴar nan ” babu wanda ya amsa mata duk shiru aka yi kafin Ammy ta miƙe duk sai muka mara mata baya,“Uwata ina kuma za ki je? ” Mama Lantana ta faɗa duk da na san da ni take amma ban juyowa ba,ta sake cewa “izala kika koma kuma wannan uban hijabi yana sharar ƙasa?” na ɗan juyo na dube ta kawai kafin na fice dama ni ce a baya. A tsakar gida muka haɗe da Mamu tana ta shimfiɗa tabarma,ni da Ubaidah muka ƙarasa shimfiɗarwa yayin da ita kuma da Ammy suka koma gefe suna tattaunawa. Ubaidah ni ma ta dube ni da kyau tana mai cewa “wai kin ga yadda Mama Lantana ke ɗingishi kuwa?” Na ce “na gani ƙila faɗuwa ta yi ” ta girgiza kai ta ce “ina zargin wani abu,amma dai bari in an jima mu koma wurin Uncle Suhail mu ji me zai cewa” Zuciyata na ji ta wani buga da sauri jin ta ambaci sunansa ,ta yi ƴar dariya ta ce “yi haƙuri my Suby zan tafi ni ɗaya” Ina shirin yin magana Mama Lantana ta fito don masifa wurinmu ta nufo tana cewa “ba ki ji ina tambayarki ba? Ina ne za ki je?” “Ko ina me aka yi?” na faɗa ,tsakiyar ido ta yi mini wani kallo kafin ta koma ɗaki tana ɗingishi.Unaidah ta furta “munafuka!” “Don Allah ki rabu da ita ta yi tunanin har da ni za ku koma can gida” “Kina nufin a nan za ki zauna?” “Eh mana in na je gida me zan yi? Ƙila Mamu nan za ta zauna sai an yi sadakar uku” “Ai gobe ne,sai mu je can gidanmu goben sai koma” “Gobe fa Monday ne ko kin manta akwai makaranta?” “Daga gidanmu ba a iya zuwa ko?” “Ban ce ba” na faɗa kafin mu kamo wata hirar,da Ammy da Mamu suka matso inda muke kafin Ammyn ta ce “ku je mu tafi” Na ce “zan tsaya nan kar a ce na ƙi zama gidan makokin” “Ubaidah mu tafi to,Zainaba za mu wuce in sha Allah in komai ya daidaita zan kira ki ta waya na shaida miki yadda muka yi” “To babu damuwa” daga haka suka fice Ubaidah na cika tana batsewa har Mamu sai da ta lura da hakan ta ce “Ke ba ki iya kawaici ba? Ko da ba za ki bi su ba ai bai kamata ki faɗa ba kai tsaye, maimakon ki yi musu rakiya kin yi tsaye da wani hijabi naki kamar matar liman.Dubi yadda Ubaidah ke fushi saboda furucinki” Na ɗan turo baki gaba na ce “Mamu in don ta Udah ce to ba ta ƙi na koma gidansu da zama ba” “Je ki cire hijabin dai ki zo ki taya ni zuba kunu a kofuka ” Na amsa da “to” tare da komawa can ciki,uwar ɗaka na shiga na cire hijabin na ninke na ɗauko wani da ke kan gado na saka.Ina shirin fitowa na ji muryar Hassana tana cewa “Mama ashe yayan Ubaidah ne,inda kin gansa kyakkyawa kuwa da shi kuɗi sun kwanta ” “Yi shiru bari za mu yi maganar daga baya” ita Mamar ta faɗa. Fasa fitowa na yi daga ɗakin sai da aka ɗauki lokaci,a bakin ƙofar fita daga ƙurya ɗakin ne ashe suke a zaune.Ina fitowa Hassana ta ce “Suwaiba amma yau ba a gida kika kwana ba ko ?” “Wa ya faɗa miki? Ina Hussaina? ” na faɗa. “Tana gida sai ta gama aikace-aikace sannan za ta taho” ta bani amsa,na ce “bari na kira ta na ce ta taho wa da Mamu da wasu kayan ta sauya” “Saboda kin fi ni sanin daidai ko? Su waɗanda na kawo mata fa?” Mama Lantana ta faɗa cikin masifa tana mai jefo mini wata leda a fuska ta bugi leɓena,tsabar yadda na ji zafi har sai da na rumtse ido.Ledar na ɗauka na fita ina hawaye,Mamu na miƙawa na ce “ki yi wanka ki canza kayan” “Lafiya kukan me kike yi? Ai na yi wanka sai dai in wani zan sake” ta faɗa tare da karɓar ledar. Na ce “ki je zan yi aikin” haka ta tafi ta bar ni da rabawa al'umma kunun. Tsabar mugunta irin ta Mama Lantana da na kai mata kunun haka ta saki kofin ya wanke mini ƙafa tasss.Na fasa uban ihu don yana da zafi sosai ,kuma duk sai ta tada hankali tana yi mini masifa tana kamanta ni marar nutsuwa,mutane na ta jero mini sannu.Haka wata daga cikin matan da ke ɗakin ta jawo ni waje aka wanke ƙafar da ƙasari wai don kar wutar ta fito. Ko da Mamu ta fito daga wanka tuni ma an gama wanke ƙafar,matar ce ta yi mata bayani kunu ne ya zube mini.Babu yadda na iya dole na je na zauna wuri guda,wuraren ƙarfe goma sha biyu na rana Mama Lantana ta ja Hassana a gaban idona suka fice. ★Sam Mama Lantana ba ta taɓa kawo wa a kanta tafiya da Hassana gidan malam hakan bai dace ba.Idonta sun rufe da yadda sam ba ta ganin tsoronta a idanun Suwaiba saɓanin Sulaimanu da shi ita kanta Mamu ɗin.Adaidaita suka shiga ya kai su,da suka je sun tarar da uban jira kowacce ta kama layi kan wasu kujeru da ya zuba a babban filin gidan. Ita dai Hassana ta san shi amma iya ta waya ce sai kuma sunansa da take ji a bakin mahaifiyarta. “Mama ni dai Yayan Ubaidah yayi mini ki sa a yi aiki a kansa ya aure ni ” Hassana ta faɗa ,Mama Lantana ta yi mata wani kallo kafin ta ce “ki ma cire wannan tunanin a ranki saboda ba zai taɓa yiyuwa ba,irin wannan aikin yana da matuƙar tsada ” Hassana ta ɓata rai tana mai cewa “Mama ai sai a sayar da wani abu a haɗa kuɗin” “Wa ya faɗa miki maganar kuɗi ce? Kin ga kar ki maido mini aiki baya ,yau Kaka ke dawowa zan karɓa muku ruwan wanka sai ki wuce can in Hussaina ta zo ita ma sai ta je can ɗin ku fara tare” Ba don Hassana ta so ba haka ta ja baki ta yi shiru.Mutane na ta shiga layi na ragewa ,Mama Lantana ta miƙe don ta shiga bayi,wata da ke kusa da su ashe duk ta ji abin da suke tattaunawa ta ce “aikinsa na ci sosai muddin dai za ka bi sharaɗi,kin ga ni ma shi yayi mini aiki na auri baban yaron nan.Yanzu ma na zo ne a yi mini wani aikin mallaka mai ƙarfi” Hassana na jin haka ta gyara zama,“bani lambarki ma ina so mu zama ƙawaye” ta faɗa ,Hassana kuwa ta bata nan ta yi ta tsara ta ita kuma tana ɗaukar darasi. Ko da Mama Lantana ta dawo tuni Hassana ta iya allonta,a haka dai layi ya iso gare su. Bayan sun shiga godiya ta soma yi masa na aikin da ya yi mata , sannan ta ɗora da cewa “a haɗa maganin ƴan biyu sai kuma wancan aikin na jikin Suwaiba ina ga duk ya lalace ta bar tsorona,sannan ina son ka ƙara loda wani a kai so nake ta lalace ta soma bin maza ta haka ne kawai zan ji sanyi a raina” Malam Yawale da ya kasance matashin tuzuru ɗan shekara arba'in da biyu,baƙin buzu ne .Rawanin kansa ya gyara sannan ya soma yin rubuce-rubuce a jikin wani farin ƙyalle kafin ya ce “aikin ƴan biyu fa tuni na kammala,shi kuma wannan da kika ce ina buƙatar ɗan kamfai na Suwaibar da kuma hotonta” “Ɗan kamfai? ” “Eh wanda ta saka kuma ba a wanke shi ba,ma'ana ana cire shi daga jikinta ” malam Yawale ya faɗa cike da yaƙini. “Babu damuwa yau ɗin nan zan nemo shi zan kwana a gidan makoki sai na cire na jikinta ” “Yawwa hakan yayi” sai ya miƙo mata abubuwan da ya tanada na ƴan biyu tare da yi musu bayani.Kuɗi ta basa kafin su fito, Hassana ta ce “Mama yanzu ya za a yi ki samu wandon Suwaibar ?” “Maganin bacci zan saka bata ta sha,yanzu zan sayensa shi da na ƙunar wuta sai in ba uwarta ta bata“ ta yi furucin tana wani murmushi.Tun a hanya suka rabu Mama ta bata makullin ɗakin Kaka da na gidan ta ce ta wuce can,ita kuma sai da ta sayi magunguna sannan ta koma can gidan makokin. ★A ɓangaren Ubaidullah kuwa sosai ya ji takaicin yadda bai ga Suwaiba tare da su Ammy ba.Iya fuskar Ubaidah da ya kalla ya fahimci abin da ke faruwa,don ya san yadda ƙanwar tasa ke mugun ƙaunar Subyn.Bai ce komai ba haka suka shiga suka ɗau hanyar gida,suna isa suka tarar da Hamida a zaune ta ci uban kuka har ta gaji. Ammy ce ta tashi hankalinta ta soma tambayarta lafiya,ai kamar ma ƙara zugata ta yi haka ta tsiro da wani sabon kukan.Ubaidullah kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai tare da nufar step ɗin ɗakinsa,Ammy ta ce “ya za ka tafi kuma? Ko ba ka gane ta ba ne?” Ubaidah ta ce “ai dama mun bar ta a nan ɗin” Hamida ta tashi da sauri ta take masa baya,yana shiga ɗakinsa ita ma ta shiga ta ƙanƙame shi ta baya tana wani matsanancin kuka mai cin rai.Ido ya lumshe yana sauraren abin da take furtawa. “Don me ? Don me ita? Ni ba ka taɓa nuna damuwarka a kaina ba,har suma na taɓa yi kowa ya bi ni asibiti amma kai ka ƙi tafiya.Shi ne..shi ne ita ɗan haɓo kawai jiki na rawa ka kai ta asibiti? ” A ɗan dake ya ce “ita ɗin zaman ƙanwata take yi Hamida ” “Ni ma ai wani ɓangare ƙanwarka ce” Jawo ta yayi ya maido ta gabansa yana kallon yadda idanunta suka kumbura,“ ya isa haka ban so” ya furta a hankali.Jikinsa ta shige ta yi lamo tana jan numfashi,tsawon lokaci kafin ya ce “ki sauka ƙasa ina zuwa” a hankali ta zame tana kallonsa ta fita,shi kuwa bedroom ya wuce ya rage kayansa kafin ya shiga toilet ya sakarwa kansa shower.Kalaman Hamida sai gwaro da juna suke yi cikin ƙwaƙwalwarsa yana kuma tambayar kansa to don me yake jin ya damu da Suby? Normal group 300,Vip 600 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [08/06 08:15] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *ROMON HAƘURI* 🤍 MRS SADAUKI ✍️ FCWA ☀️ *Wannan labari ba ƙirƙira ba ce,labari ne da ya faru a gaske ina fatan za ku bibiye shi sau da ƙafa* *__________________________________________________* Masu jiran book ɗin TIF DA TAYA ya kammala 1k ne kuɗinsa amma na yi discount duk mai so ya biya 800 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 In kuma akwai wani book ɗina da mutum ke so yayi mini magana zan yi masa discount 06 Ko kaɗan bai danganta hakan wai da sunan so ba,abu guda ya sani Suby nada wani matsayi a zuciyarsa wanda ya alaƙanta hakan kuma da ƙaunar ƙanwarsa da take yi. Towel ya jawo ya ɗaura a ƙugu kafin ya fito yana tsane kansa da ƙarami kuma.Bai wani ɗauki lokaci ba ya shirya cikin kakinsa na soja,ya feshe jikinsa da turare sannan ya fito a hankali yana jin kansa wani iri tamkar bai ida cika ba. Idanun Hamida ƙurrr a kansa ko ƙyaftawa ba ta yi,wani irin azababen so ne take yi wa Ubaid ɗin wanda ita da kanta take ƙarawa kanta shi ta hanyar wanka da maganin shirkar da malam Yawale ya bata. Wata sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ƙamshin jikinsa da na turarensa suka turniƙe mata hanci,ta ɗan lumshe ido kafin kuma ta buɗe su a hankali ta ɗora su kan fuskarsa da sam babu walwala. “Na zuba ma abincin?” ita ce tambayar da ta yi saboda takaicinta babba bai wuce yadda ciwon Suby ya tashi ba tare da Ubaid ɗin ya ci abincin da ta zuba masa magani ba. Ɗan yamutsa fuska yayi kafin ya girgiza kai,ya dubi agogon hannunsa ya ce “zan wuce wurin aiki ne” “Zan bi ka” "A'a” ya furta tare da nufar ɗakin Ammy,da sallama ya shiga ta amsa cike da kulawa.Wuri ya samu ya zauna yana mai cewa “Ammy lafiya kika fita tun da safe?” Sai da ta sauke numfashi kafin ta ce “wata patient ɗina ce na je dubawa,na yi tunanin ma ta farka sai ga shi har na baro asibitin tana bacci” “Allah ya bata lafiya,ni zan wuce.Ina Ubaidah?” “Tana ɗakinta“ ta basa amsa kafin kuma ɗora da addu'ar tsari a gare shi. Ko da ya fito bai samu Hamida ba a falo,yana fita can harabar gida ya tsinkaye ta tana lalata tayar motarta, wato so take ala dole sai ya ɗauke ta a motarsa.Ya girgiza kai don shi a kullum mamakin Hamidar yake yi ,tana ganinsa ta yi saurin ɓoye ƙatuwar wuƙar hannunta.Kuɗi ya ciro a aljihunsa ya ce “in kin gama ɓata tayar motar sai ki kai a gyara miki ” kasa motsi ta yi sai shi ne ya jawo ɗaya hannun nata ya saka mata kuɗin kafin ya je ya shige motarsa.Tun kafin ya isa ga get yake horne tuni kuwa an buɗe masa shi ya fita a tsiyace yana jin ina mai yarda ya karɓi soyayyar Hamida ba,sam ba ta jin magana.Ya ja dogon tsuki a fili ya furta ita kuma “waccan ta je ta zauna gidan makoki sai ka ce wata uwar mata” Wani sashen zuciyarsa ya tambaye shi ‘ to ina ruwanka? ’ Sai kuma ya furzar da huci yana jin cewa to ina ruwan nasa ɗin kuwa,bai wani ɗauki lokaci ba ya isa can wurin aikinsu.Tun a bakin ƙofa sojawa ke ƙamewa suna sara masa har ya isa inda yake ajiye mota,wani soja ya zo da gudu ya buɗe masa ya fito yana cewa “Abraham yau kai ne haka da safe?” “Eh muna training ne,sabbin sojawan da za a ɗauka aiki yau aka kawo su” Abraham ɗin ya basa amsa. Ya ce “yau bakwai ga wata ko? Shaf na manta” Abraham ya dube shi da mamaki wai yau Captain Ubaidullah ne ke cewa yayi mantuwa game da abin da ya shafi aiki. “Aboki ko dai- ko dai?” Abraham ɗin ya faɗa . Ubaid na jin ya kira shi da Aboki ya fahimci yanzu kuma rigar abota Abraham ɗin ya ɗauko ya yaɓa ba ta aiki ba.Hararar wasa yayi masa kafin ya ce “ko dai me?” Abraham ya biyo bayansa yana mai cewa “ka fara soyayya mana” Ubaid ya ce “da dama ban soyayya ne?” “A'a Hamida dai na sonka,faɗa mini wace mai sa'a ce ta sace zuciyar santalelen tuzurun abokina?” Ubaid ya saki murmushi yana mai sa key ya buɗe ofishinsa,a tare suka shiga ciki ko ina a gyare fesss sai ƙamshi yake.Har sai da suka zauna bai basa amsa ba, Abraham ya ce “in fa aka kalle ka da kyau za a gane ka faɗa so” Ubaid ya jingina ga kujera yana ɗan juyawa haɗi da lumshe ido ,a nan take fuskar Suby ta faɗo masa.Cikin cool voice ya ce “in dai wannan alamomin su ne so to kenan na kamu da son Suwaah kenan?” Abraham ya saki baki da hanci yana kallonsa kafin ya ce “ kuma Kirista ka samu? Ko irinmu ce sababin tuba?” Ya buɗe idanunsa yana cewa “ko ɗaya musulma ce,a gidanmu ta zo” sai kuma ya kwashe duk wani abu da ya faru a gidan tun zuwan Suby. Abraham ya ce “aboki ko dai sha'awarta ce kawai kake yi?” Ya girgiza kai ya ce “inda sha'awa ce da ganin da na yi mata da towel ɗin ya jefa ni cikin yanayin nan,amma ni ban damu da zuwa wancan matakin na mu'amulantar juna ba.Kawai ni abin da nake so na dinga ganinta kullum a gidanmu” “Ta ya za ta zauna gidanku kuwa sai in aurenta za ka yi” “Hamidar fa?” “Dama ai ba sonta kake yi ba,ni tun farko ban so ka amince mata ba.Ƙila duk shiri ne babu wata guba da ta sha saboda sonka,ta yi hakan ne don ka yarda” “Don guba ta sha,kuma na amince mata ne duba da cewa ita ɗin ƙanwata ce in na tsane ta sam Daddy ba zai ji daɗi ba” “To yanzu da ka samu Suwaah duk aurensu za ka yi ko ya?” “Kenan son Suwaah ne nake yi? A'a kawai ƙauna ce” Ubaid ya faɗa don ƙaryata abokinsa dama ita kanta zuciyar tasa. Sun yi hira sosai kafin kuma su soma aiki,sallah kawai ke tsayar da su sai abinci da suka tsaya suka ci wuraren ƙarfe biyu da rabi. ★Hassana tana cikin adaidaita tana tunanin maganar da suka yi da wannan matar,gefe guda kuma tunani taf zuciyarta na dalilin da yasa Mama Lantana ke son sai Suwaiba ta yi yawon banza.A haka ta isa gidan Kakarsu,ta buɗe ƙofa ta shiga .Ɗakin yayi ƙura wannan yasa ta share shi tasss sai kuma a lokacin ne ta kira Hussaina ita ma babu wani jimawa ta zo.Bayani ta yi mata dangane da magungunan kafin su shiga yin aiki da su kamar yadda ya ce ɗin.Hira suka soma yi suna jin daɗi nan da ɗan ƙanƙanen lokaci duk za su yi aure saboda wankin ƙwaƙwalwar da uwarsu ta yi musu na cewa malam Yawale na iya yin komai sai in bai yi maka aiki ba . Lokacin da Kaka ta shigo kuwa ita ma da nata kalar maganin shirkar da ta karɓo.Cike da murna suke nuna jin daɗin gatan da ake yi musu,Kaka ta ce “yanzun nan za mu aiwatar da ɗaya aikin,kowacce za ta rufe zakara ɗaya da ransa kuna mai ambaton sunan samarinku,nan da wani sati duk za a kawo muku sadaki” Da sauri Hassana ta ce “to Kaka in wanda kake so fa kuma ba ka san sunansa ba?” “Ka ji wani sakarci ta ya za a yi mutum ya ƙi sanin sunan saurayinsa? ” Kaka ta faɗa cikin masifa tana wani juya bakinta da goro ya ɓata . Cike da damuwa Hassana ta ce “to ni dai Kaka yanzu wani ne na gani ina so kuma ban san sunansa ba” “In ke ba ki sani ba ai su aljanun da za su je aiwatar da aikin sun sansa ” cewar Kaka. Hussaina ta ce "aljanu kuma?” “I ko kin zata ni ce zan je na shiga tunanin samarin naku a hana su sukuni har sai sun kawo kuɗin?” Hassana ta tuntsire da dariya tana mai cewa “Kaka rabu da ita don Allah ” “Ku tashi mu fita kun san an ce ba a bori da sanyin hali” Kaka ta faɗa tare da jawo wata ƙatuwar ɓota,a nan tsakar gida kowacce ta gina ramenta kafin Kaka ta kwance baƙaƙen zakarun da duk aka yi musu rubutu da tozo da kuma ƙafafunsu,bakunansu kuwa an saka almakashi an datse su ko kuka ba su iyawa. Dukkaninsu idanunsu sun rufe haka suka saka zakarun da ransu,Hassana ta furta wannan wanda ta gani a yau shi take so Yayan Ubaidah tana mai zuba ƙasa ta rufe zakaran.Da yake ba kunya ta ishe su ba sai suka alwala kuma suka yi sallah tare da roƙon Allah yasa aikin ya ci. ★Sulaimanu Wayar da ya samu yayi da Ubaidah ita ta kawar masa da duk wata damuwa,ya ji sanyi a ransa tare kuma da dawo masa yaƙinin cewa sannu a hankali wata rana komai zai wuce kamar ba a yi ba.Tunani ya soma yi yana murmushi shi ɗaya a haka bacci ya ɗauke shi, lokacin da ya farka kuwa tuni gidan kowa ya watse.Wanka yayi sannan ya ɗora indomie ya ci sannan yayi alwala ya wuce masjid,bayan ya dawo ne kuma ya kimtsa cikin kakinsa na ƴan sanda.Mashin ɗinsa ya fiddo roba-rina,wurin aikinsu ya tafi duk da kuwa cewa ya ɗauki hutun kwana biyar amma babu amfanin zaman nasa shi ɗaya . Waɗanda suka san da zancen tafiyar tasa sai tambaya suke yi lafiya amma bai faɗa musu ba,saboda ba a yi ciki don cin abinci kawai ba .Aiki yayi tuƙuru har dare,nan ya ci abinci kafin ya wuce gida.Yanzu kuma moɗi ya tarar suna yi suna shan shayi sai dai iya su kaɗai ne banda mata, wannan yasa baya sun gaisa shi ma ya ja kujera ya zauna aka soma shan shayin da shi suna moɗi shi kuma yana chating da Ubaidah sai murmushi yake yi shi ɗaya kafin kuma ya miƙe ya je ya cika bokiti yayi wanka,bayan ya fito ya shige ɗaki ya kunna fanka sannan ya kira ta. Tana ɗauka ya ji ransa ya daɗa yin haske kafin su soma hirar masoya ,ƙarara yake faɗawa Ubaidah rashin haƙurinsa akan rashinta da kuma yadda yake muradin samunta a kusa da shi.Ita kuma kwantar masa da hankali take yi, musamman abin da ya faru na dangane da mutuwar kawu. Cikin wani irin yanayi yake cewa “Ubaidah ko dai ba alkhairi ba ne auren nan? Kin san a baya kusan kullum Mama sai ta faɗa mini haka tare da bani sharawa...” sai kuma yayi shiru,zuciyar Ubaidah kamar za ta kama da wuta haka take ji .Ta sani sarai wa yake nufi da Mama, wannan yasa ta ce “shawarar me take baka?” Kamar ba zai sanar da ita ba sai kuma ya ce “wai na janye maganar auren” “Dalili?” “Gani take yi kamar kin wuce ajina duba da cewa ke ƴar masu hali ce,ni kuma talaka” Ta ce “arziki ai na Allah ne,da a ce don kuɗi ake aure ai da na auri Ya Hamid amma na zaɓe ka Sannan ba tun yau ba na sha faɗa maka ba duk abin da Mama ta ce ne gaskiya ba,kawai in ta faɗa maka abu ka saurare ta sannan ka yi watsi da shi” Ya ja numfashi ya ce “to Udar Suby ” ya ƙarashe yana wani murmushi mai sauti,Ubaidah ta turo baki ta ce “ai na yi fushi ma da ita,wallahi Sul ban san me yasa Allah ya jarabce ni da ƙaunarku ba kai da Suby kuma kullum ku ne ke wahalar da ni kuna ɓata mini rai .Dubi fa tun da ka zo ba mu ga juna ba,ka kwashi jiki ka koma.Ita kuma yau ta zaɓi zama gidan makoki kan ta zo tare da ni ” “Yi haƙuri mana Matar Sul kar ki yi kuka” ya faɗa cikin sigar rarrashi, Ubaidah ta soma yi masa kukan shagwaɓa wanda hakan ya dagula masa lissafi da sauri ta nutsu jin yadda ya canza yanayin magana,wani irin tausayinsa take ji.Shi ma gudun kar abin ya tsananta daga ƙarshe ya cutu sai kawai yayi mata sallama,magani ya sha saboda kansa da ya soma sara masa kafin ya kwanta.Babu jimawa bacci ya ɗauke shi,sai dai bai yi wani nisa ba bala'in da kunuwansa suka soma jiyo masa ya tashi da wani ƙarfi yana dafe saitin zuciyarsa.Jikinsa har rawa yake yi wurin jawo jallabiya ya saka,duka gidan ba ka jin komai sai sautin abokansa da matan banza suna masha'a wa'iyazubillah. Idonsa na wata irin rufewa saboda takaici da baƙin cikin shiga haƙinsa da suka yi, babban abin haushin ma wasu a falo ma suke ba a ɗakinsu ba . Gidan ya buɗe ya soma tafiya cikin duhun daren kamar wani mahaukaci,yayi tafiya mai ɗan nisa kafin ya zauna yana kallon sama.A zuci ya soma yin magana ‘ Ya Allah in kana yin haka ne don jarraba imanina Allah na tuba ka yafe mini,iya abin da kunnena ke jiye mini kusan kowanne dare yayi mini yawa ga shi yau kuma na soma gani da idona har ana yi mini tayin zina.Allah ka tsare ni kamar yadda ka tsare Annabinka Yusuf da ƙangin zina’ sai wasu hawaye masu zafi suka zubo masa,ya maido kansa ƙasa yana danna waya domin kiran Ubaidah. ★Suwaiba Sannu a hankali ƙafata ta soma borarrai alamun wutar ta fito har ta yi ruwa .Banda hawaye babu abin da nake yi,sai kuma a wannan lokacin ne na tuna wayata na can ɗakin Ubaidah.Mamu kuwa sai sannu take jero mini,inda na samu sassauci shi ne ɗan bacci da na samu shi ma bai yi wani nisa ba na ji wani azababen zafi a ƙafata ina buɗe ido na yi tozali da Mama Lantana ce ashe ta latsa wutar da ƙarfi duk suka fashe.Hawayen azaba ne suka soma zubo mini ina shirin janye ƙafar kuma ta soma barbaɗa mini magani tana cewa “shegen rawar kanki uwata duk shi ya kai ki ga haka,Zainaba ga wannan shi kuma ta sha in za ta kwanta yanzu na sayo shi bayan na karɓo mata maganin ƙunar” Mamu ta shiga yin godiya kafin ta karɓi maganin,yayin da ita kuma Mama Lantana ta ci gaba da yin iya yinta na kalar dangi mutane kuwa sai yaba mata suke yi. Sallolin ranar nan duk a zaune na yi su,ga shi kuma na kasa cin komai har dare.Bayan sallar isha'i Mamu ta ɓallo maganin ta bani ƙwaya biyu,na karɓa na saka bakina tare da kora shi da ruwa.Bai wani ɗauki lokaci ba na amayar da shi,cike da masifa Mama Lantana ta karɓa tare da ɓallo mini wasu biyun haka na karɓa na sha ina soma yin kakarin amai ta kama bakina ta dantse da hannu,tun ina yunƙurin har maganin ya zauna don dole.Wata irin zufa ce ta soma karyo mini,ba a kuma jima ba na soma jin jikina na yin wani irin mutuwa.Na miƙe dakyar,Mama Lantana ta ce “ina za ki je?” “Banɗaki na yi wanka”na bata amsa kafin na je na cika bokiti ina ɗingishi,wanka na yi tare da yin ɗaurin ƙirji na fito.Can uwar ɗaka na shiga na cire zanena tare da shanya pant ɗina da na wanke sannan na mayar da kayana na kwanta,sai dai mugun sanyin da ya soma rufe ni yasa na je na ɗauko ƙaton hijabin da Ubaid ya saya mini na saka . Ina shirin kwanciya sai kuma na soma jin wani ƙunci na luluɓe ni ,babu abin da nake da buƙata sai kaɗaice wannan yasa na fito ina ɗingi ban zame ko ina ba sai ƙofar gida .Kan dakali na zauna ina yin hawaye , ƙwaƙwalwata kuwa kamar ana meeting ɗin majalisar ɗinkin Duniya haka nake jin ana yin magana barkatai a cikinta.Wani haske ne ya soma sauka a gare ni,na kai hannu na rufe fuskata sai na ga mai motar na gangarawo inda nake kafin ya kashe fitilun ya kuma fito,duk da ƙofar gidan babu ƙwan fitila hakan bai hana ni gane shi ba.Da wani irin sauri na tashi tsaye ina mai cewa “Ya Ubaid?” “Me kike yi a ƙofar gida?” ya tambaye ni,kamar mai jira haka na fashe da matsanancin kuka ina mai faɗar wani sirri da ya fito daga can cikin ruhina. “Ƙunci nake ji,na tsani komai ban son mutane ji nake yi kamar na ta yin ihu” na furta ina shafar ido,ina jin idanunsa masu kaifi suna kallona a cikin duhun daren. “Shiga mota” ya faɗa cikin salon bayar da umarni sai kuma ya buɗe mini gidan gaba,saura ƙiris na faɗi wurin shiga saboda yadda idanuna suka soma kumshe wa,shi ne ya taro ni tare da rufe ƙofar sannan ya zagayo ya zauna tare da yi wa motar key. Muna tafe ina ɗan gwale idona ina son hana baccin ɗaukata,cikin magagin bacci na ce “ina za mu je?” “Wurin Ubaidah zan kai ki” ya bani amsa,ban ƙara cewa komai ba na jingina kaina ga madubin mota daga nan ban sake sanin abin da ke faruwa ba. Ubaidullah A natse yake kallon Suby wacce yanzu yake jin tamkar rayuwarta ta fi tasa muhimmanci.Tun da ya tafi wurin aiki ya kasa sukuni,daidai da sakan ɗaya ƙwaƙwalwarsa ba ta gushe ba akan tunaninta.Haka kawai yake jin kamar tana cikin damuwa ne wannan dalilin yasa ya je can gidan makokin,sai kuma zatonsa ya zama gaskiya yana shigo layin ya hango ta kamar aljana ita ɗaya a zaune cikin hijabin da shi ne ya saya mata shi.Gefen hanya ya parker ganin yadda kanta ke ɗan buguwa ga madubin in ya hau tudu,a hankali ya jawo ta ya gyara mata zama ya maƙala mata belt sannan yayi ɗan baya da kujerar .Goshinta da ke tsatsafo da gumi ya kai hannu a kai sai ya ji shi gau kamar gatau,iya gumin kawai ya goge mata kafin ya ci gaba da tuƙi.Tun akan hanya ya kira Ubaidah sai dai tana busy wannan yasa ko da isarsa bai ɓata lokaci ba ya kewaya can ɓangaren ya ɗauki Suwaibar ya nufi ciki da ita. A falo ya so ajiye ta sai kuma ya fasa ya nufi benen Ubaidah,yana shiga ya soma ƙwala kiranta yana mai shimfiɗe Suwaibar kan doguwar kujerar falon.Ubaidah wacce take a rikice jin Sulaimanu ya sake kiranta yana yi mata kuka kamar ƙaramin yaro,yanzun ma a ɗan firgice ta fito jin muryar Ya Ubaid ɗin don sarai ta ga kiransa na shigo mata ne sai dai babu halin ɗauka ne. Tana fitowa ta yi tozali da Suby,ƙafarta na fitar da jini.Da sauri ta ce “innalillahi wa'inna ileyhi raji'un na shiga uku ni Ubaidah ” sai kuma ta zo da sauri ta kama ƙafar,shi Ubaid sai yanzu ma ne ya lura da ko takalmi babu a ƙafarta ga kuma ciwo.Har wani hayaƙi ya ji zuciyarsa na yi kamar an ɗiga masa dalma,tambayarsa Ubaidah ke yi amma ya kasa cewa komai.Sai sauka da yayi ya kira Ammy kasancewar ita likita ce tana gani ta fahimci ƙunar wuta ce sannan ta sha maganin bacci ne,akwatinta na asibiti ta ɗauko ta wanƙe ƙafar sannan ta saka mata magani ta naɗe ta da bandeji. “Cire mata hijabin ta sha iska” Ammy ta faɗa tana kallon Ubaidah da ke yin kuka,dakyar ta motsa ta cire hijabin.Suby ta ja wani numfashi,Ya Ubaid ya dubi kwantancen gashin gaban goshinta yadda ya wani lafe yana tsatsafo da gumi.Sanyin ac ya ƙara kafin ya fice ya nufi sashensa. ★A can gidan makoki kuwa Mama Lantana tuni bacci ya ɗauke saboda nutsuwar ruhi da ta samu za ta yi aiki a tsakar dare na tuɓe ɗan kamfan Suwaiba.Wannan yasa ba ta ma san lokacin da Hassana ta dawo ba,ita kuma ta zo nan ne da tunanin gobe ƙila Ubaid zai dawo.Lokacin da ta zo kusan kowa yayi bacci,bokiti ta cika da ruwa ta je ta yi wanka sannan ta shiga ɗaki.Matar malam ta gani a rakuɓe tana kukan kewan mijinta,ba ta ce mata komai ba ta shanya pant ɗinta sai kuma ta ga wani mai bala'in kyawu.Sam ba ta kawo na Suwaiba ba ne sai ta ɗauka ta saka sai dai yayi mata yawa Kasancewarta siririya a dole ta fidda shi ta ajiye.Nata ɗin ta mayar tana tunanin kar yadda ta so sace na wata ita ma a ɗauke nata,can waje ta fita ta kwanta.Cikin tsakiyar dare Mama Lantana ta farka,kamar munafuka haka take tafiya har ta shiga can uwar ɗaka inda take da tabbacin Suwaiba na nan amma wayam. “Wa kike nema?” matar malam ta tambaya wacce ta dawo daga banɗaki. “Ina Suwaiba?” “Ta yi wanka ta fita ai har yanzu ba ta dawo ba” ta bata amsa tana mai zuwa ta yi kwanciyarta.Cikin sa'a idanun Mama Lantana ya kai ga ɗan kamfan,a yadda ta gansa tsadede ta fahimci iya mai kuɗi zai sayensa wato Ubaidah ta bai wa Suwaiba shi.Ɗan kamfan ta ɗauka sannan ta fita,can banɗaki ta shiga ta kira malam Yawale wanda kamar Aljani take da wuya ka kira ba ka same shi ba,yana ɗagawa ta ce “na samu ɗan kamfan amma ƴar baƙin cikin ta wanke shi” Ya ce “babu matsala ki yage daidai tsakiya ki kawo mini” cike da farin ciki ta kashe kiran,tsabar mugunta da baki ta yi amfani ta ciri tsakiyar pant ɗin kafin ta fito ta mayar da shi inda yake,sauran kuma ta ƙulle ga haɓar zane....... Normal group 300: posting biyar a sati Vip 600: posting goma a sati Via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 Kowacce ta zaɓi groupe ɗin da take da ra'ayi, wannan ba kalar sauran labaran da na saba yi ba ne sha ƙundum ne,ga soyayya ruwa-ruwa,ga kuma daru da tsantsar darasi [08/06 12:46] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *ROMON HAƘURI* 🤍 MRS SADAUKI ✍️ FCWA ☀️ *Wannan labari ba ƙirƙira ba ce,labari ne da ya faru a gaske ina fatan za ku bibiye shi sau da ƙafa* *__________________________________________________* 07 Washegari tun asubar farin aka soma hada-hadar sadakar uku.Duk wani dangi na nesa da na kusa da abokan arziki sun zo.Hidimar nan ta mantar da Mamu wata Suwaiba ballantana ma har ta neme ta, wannan kuma ba yau ne farko ba sau tari tana jin wani duhu ya gilma mata ta mance ma tana da wasu ƴaƴa musamman ma Sulaimanu.Wannan yasa hankali kwance duk ta tsaya kai da fata komai ya tafi kan tsari,a ɓangaren Hassana kuwa ta kasa ta tsare tana tsaye a bakin ƙofa tana baza ido cikin taron dandazon mazan da ke wurin.Ita kuwa Mama Lantana kamar fitar tusa haka ta fice ta bar gidan zuwa na malam Yawale ,yau kam ta yi sa'a babu kowa sai wata mata da suka yi ban hannun makafi ita tana fita ita kuma tana shiga. Kan tabarma ta zauna tare da kwanto wani sashe na pant ɗin Suwaiba ta miƙawa malam Yawale shi kuma ya karɓa tare da saka shi cikin wata baƙar rariya sannan ya ɗora kan wata ƙwayar da ke cike da kiyashi.Magani ya barbaɗa kan ɗan kamfan yana mai furta wasu surkulle na shirka,sannan ya ɗauko wani jan ƙyalle ya saka guntun pant ɗin a ciki ya ɗaure ya miƙawa Mama Lantana ya ce “ki jefa shi a cikin masai/salanga ” Ta karɓa tana mai washe baki tana cewa “ka tabbata zai yi?” Malam Yawale ya nuna mata rariyar da ke kan ƙwarya ya ce "yadda kiyashin nan duk suka baro ƙwarya suka yaɓe rariya haka mazan banza za su dinga tururuwar bin layin lalata da ita” Zuciyar Mama Lantana fesss ta ce “ita ma na uwar nasu da buƙatar a sabunta aikin,na ga take-takenta ta soma yunƙurin nuna mini cewa ƴaƴanta ne tana da iko da su.Kamar yadda ka saba yi,ka saka mata ganin laifi da baƙin Abdullahi mijinmu sannan ka nuna mata ni ce babbar masoyiyyarta sannan duk wani sirri nata kar ta ɓoye mini in ta yi yunƙurin yin haka kuwa ka saka Aljanu su yi ta birkita mata lissafi suna yi mata magana cikin kwanya har sai ta kasa jurewa ta zo ta sanar da ni ” Malam Yawale ya ɗauko wani baƙin kundi nasa ya rubuta jawaban Mama Lantana kafin ya ɗago ya ce “wannan aiki dole yana da buƙatar yanka,za ki nemo baƙar akuya mai gemu ki sa a yankata nan tsakiyar gida ,akwai wani magani da zan baki sai ki cilla shi cikin ramen da jinin akuyar ya zuba kafin ki rufe.Zuciyar akuyar kuma ni za ki kawowa ita akwai aikin da zan yi da ita ,sai dai wani sharaɗin lokacin yankan ba mu buƙatar ambaton sunan Allah domin wa aljanin da zai yi miki gadin Zainabar za a yi yankan” Ba tare da wani shakku ba ta ce “wannan duk babu damuwa,kenan sai ka aiko da ɗaya daga cikin almajiranka ya zo yayi mini yankan ,ka ga ba zan kirawo wani bare ba in faɗa masa sirrina” Malam Yawale ya ce “babu damuwa,kuɗin aiki kuma sai komai ya tafi yadda ake so zan sanar da ke” nan ta yi masa godiya kafin ta fito.Tana tafe tana magana ita ɗaya “wato har wani tunƙaho kike yi ɗanki zai auri ƴar masu kuɗi zai zama ɗan gata shi ma a mallaka masa dukiya,ita kuma munafukar ƴarki ta ɗauki girman kai ta ɗorawa kanta ita ma jiran mai kuɗin take yi.Hasken fatar da ta ɗan fito da shi shikenan ta mayar da shi jari,to in kin zama karuwar gida sai na ga ta jiran mai kuɗi” Sai da ta zo bakin hanya ta samu abin hawa,sam ba ta koma gidan makoki ba gidanta ta wuce ta je ta aiwatar da baƙin nufinta ta cilla abin a masai sannan kawai hankalinta ya kwanta. Lambar Iroro ta kira wanda shi ne ke kula mata da sayen duk wata dabba da malam Yawale ya buƙata.Bayan ya ɗauka ta faɗa masa irin akuyar da take so har da masa alƙawarin tukuici mai tsoka.Shi ma da jin haka ya bazama nema,hankalinsa bai kwanta ba har sai da ya samo mata ita.Ta biya kuɗin akuyar da kuma na alƙawarin da ta yi masa, sannan ta ɗaure ta ga turmi. ★A can gidan Ammy kuwa cikin wani irin yanayi Ubaidah ta ƙara kai wayarta a kunne ganin har yanzu bai kashe kiran ba.Ta ja wani dogon numfashi ta ce “ka yi haƙuri” "Me ya samu Suwaibar?” “Ƙafarta ce ta samu ƙuna,amma da sauƙi Ammy ta yi mata aiki ga shi tana ta bacci ma.Ya naka jikin?” “Babu sauƙi Udah ji nake kamar na yi hauka,ke kawai nake da buƙata a kusa da ni don Allah ki nemo mafitar da za a bikinmu nan kusa domin ki tare” Jikinta duk yayi sanyi ta ce “in sha Allah zan yi ƙoƙari Sul kar ka damu” nan ta ci gaba da kwantar masa da hankali har suka yi sallama. Pilow ta ɗauko da blanket ta yi shimfiɗa kan capet ta kwanta tare da tsurawa fuskar Suby ido,duk da tana bacci amma farin sanin da ta yi mata yasa tana iya hango zallar damuwar da ke ƙunshe a ruhinta.Ta lumshe ido tana jin ya zama dole gobe su tafi wurin Uncle Suhail,domin kuwa tsugunne ba ta ƙare musu ba.Cike da tunani iri-iri ta samu bacci ya ɗauke ta mai cike da mafarkai iri-iri kamar yadda ta saba. Suwaiba A hankali na soma ware idanuna da nake jin sun yi mini nauyi .Sanyin ac haɗi da ƙamshin da ya ziyarci hancina su suka tabbatar mini a inda nake kafin kuma ƙwaƙwalwata ta tariyo mini abin da ya faru.Da sauti na yunƙura na tashi zaune,sai na ga ƙafata naɗe da bandeji ga kuma Ubaidah a kwance tana bacci wato gadina ta tsaya yi.Na saki ɗan murmushi tare da furta kalmar da ko kaɗan ban taɓa tunanin za ta sauya ƙaddarar ƙawar tawa ba. “Allah ya kula da lamurranki fiye da yadda kike kula da ni,ya so ki ya ƙaunace ki,ya wanke miki duk wata damuwa da ƙunci,kamar yadda kike ƙoƙarin yi mini” sai kuma na miƙe a hankali ina ɗingishi na buɗe frigine sai dai babu komai a ciki sai mangoro da madara,ni kuma ƙishi nake ji.Wannan yasa na fita na sauka ƙasa tare da nufar kitchen,falon yayi tsit babu motsin komai an kashe fitilu sai hasken da ya keto maduban ƙofa ya shigo. Na san komai na gidan wannan yasa ina shiga kitchen ɗin na kai hannu ga maɓallin wuta zan kunnawa amma sai na ji wani hannun a kai.Wani uban ihu na buɗe baki da niyyar ƙwalawa na ji an toshe mini baki,tsoro da firgicina sai suka ƙaru dandanan numfashina ya fara bazaranar ficewa. “Ni ne” na ji muryar Ya Ubaid ya furta a slow yana mai janye hannunsa da ya toshe bakina da shi.A take na yi ajiyar zuciya ba tare da na ce komai ba na sake yunƙurin ƙara kai hannu na kunna wutar nan ma ya tare ni yana cewa “kar ki kunna” kallonsa na soma yi ta cikin duhun wanda yake sharara ba mai ƙuna ba.A hakan na iya gane babu riga a jikinsa,ƙila kuma shi ne dalilin da yasa bai so na kunna haske. Kamar wata yarinya mai koyon magana bakina ya soma rawar furta “ruwa..so..in sha” shi ya buɗe frigine ɗin ya ɗauko ya bani gora ɗaya,na buɗe ina ƙoƙarin kai bakina suka zubar mini a jiki wani sanyi ya ratsa ni na ja wata irin doguwar ajiyar zuciya kafin na soma shan ruwan.Kamar zan mutu idan na sauke gorar haka nake ji, wannan yasa ban cire ta daga bakina ba sai da na shanye su tasss shi kuma yana tsaye yana kallona.Gorar na miƙa masa ya karɓa,na ce “na gode” sai kuma na juya na barsa nan. Na hau step ina takawa a hankali,jikina ya bani ana kallona na dubi ɓangaren kitchen inda yake sai dai ban iya ganinsa a yanzu.A haka har na ƙarasa ɗaki na zo na kwanta kusa da Ubaidah don ban saba kwanciya kan kujera ba.Ko kaɗan bacci ya kasa ɗaukata,sai tunanin Ya Ubaid nake yi da dalilin da yasa ya fito a wannan yanayin .Sai kuma na tuna shi ne ya kawo ni nan gidan,ga shi kuma na yi bacci cikin motarsa.Na waro ido wani tunani na shigo mini,na miƙe da sauri tare da tayar da Ubaidah ta ware ido tana kallona. Da sauri cikin rawar murya na ce “ wa ya kawo ni nan ɗakin?” “Ya Ubaid” ta bani amsa tana mai mayar da ido ta rufe,na ƙara jijigata ta tashi ta ce “me?” “Gaske shi ya ɗauko ni ya kawo nan?” “Eh! Me aka yi?” cike da takaici na ce “oh ba a ma yi komai ba kenan?” “Suby bacci nake ji don Allah ki bar ni” ta furta tana mai juya mini baya.Tashi na yi na wuce bedroom ɗinta,wayata na ɗauka da na duba sai na ga baƙuwar lamba a ciki kuma ya gabatar mini da kansa.Mayar masa na yi da saƙon babu jimawa shi ma ya maido nan muka shiga yin chating, kasancewar shi ɗin mai barkwanci ne babu wuya na ji na saki jiki da shi .Ya tabbatar mini yana asibiti a can zai kwana,wasa-wasa sai ga shi har an soma kiran sallar asubah muka yi sallama na je na yi wanka haɗi da alwala na fito. Na buɗe drower Ubaidah ina mitar yadda duk kayanta sun matse ni ta shigo,cikin nata haukan ta ce “wa ya ce ki zama ƴar lukuta ai ga irinta nan” Na ce “ai dai irinmu ake yayi” Ta ce “oho dai je ki ga yayin,in kika yi aure babu wata soyayyar turawa yo wane ɗan banza ne zai iya ɗaukar ki lukuta da ke” Cike da jin haushi na buga mata doguwar rigar hannuna da na ɗauko ina cewa “shi ne kuma Ya Ubaid ya iya ɗauka ta?” Tana dariya haɗi da nufar toilet a guje ta ce “shi ai soja ne,ko kuma sai in shi za ki aura” Cak na tsaya da ƙoƙarin binta na dake ta ina juya kalmar sai in shi zan aura.Ta shige toilet ta bar ni da abin duniya,dakyar na iya watsar da tunanin na saka rigar na zo na yi sallah.Bayan na gama kan bed na haye tare da yin shiru ina mai ci gaba da tunanin maganar Ubaidar,ta zo ta hau gefen gadon tana cewa “kar ki koma bacci Malama don wallahi na samu labarin yau za a yi mana jarabawar bazata kin ga tashi mu ƙara duba takardunmu ” “Wane malami?” na tambaye ta a sanyaye. Ta ce “malamin lissafi mana ai kin san halinsa” ban ƙara cewa komai ba na miƙe muka shiga dubawa ɗin.Ƙarfe bakwai saura muka ƙara yin wanka ta bani uniform ɗinta ɗaya na saka,sannan muka sauko ƙasa. Ammy muka ga ta shigo da dukkan alamu fita ta yi,a tare muka gaishe ta kafin ta ce “bari na je na kira Ubaidullah ya fara kai mu wurin addu'ar uku kafin ku wuce makaranta. A ta ɓangaren Ubaidullah kuwa ,sam bai samu baccin kirki ba ga shi kuma bawan Allahn ya ƙi yarda kan cewa ya kamu da son Suby.Wannan rikici na tsakanin zuciyarsa da tunaninsa su suka haifar masa da ciwon kai,duk da ya yi wanka abin ba sauƙi.Wuraren ƙarfe huɗu na dare ya fito kitchen don ɗauko ƙanƙara saboda frigine ɗin ɗakinsa iya sanyi kawai take saka ruwa.Bai daɗe da shiga ba ya ji bugun zuciyarsa ya sauya,a hankali ya ɗan leƙo kuma sai ya hango Suby na ɗingishi .Ba zai iya fita ba don hasken falo ya fi na nan ɗin yawa wannan yasa ya tsaya har ta zo,kamar ya san kuwa za ta kunna ƙwan lantarki in ta shigo shi yasa duk ya ɗauki wani mataki.Ba ƙaramin jin daɗi yayi ba da Allah yasa ba ta gansa a wannan yanayin ba,ƙanƙarar ya ɗauka ya tafi bayan ya tabbatar ta gama shigewa.Cikin wani towel mai taushi ya saka ƙanƙarara ya dinga ɗorawa a kansa,a sannu a hankali ya soma jin dama har bacci ya ɗauke shi.Kiran sallar asuba ya tashe shi,bayan ya dawo daga masjid ya shiga ɗakin motsa jiki sama da awa ɗaya kafin ya fito ya je yayi wanka ya shirya cikin manyan kaya amma bai saka hulla ba.Yana fesa turare Ammy ta soma danna ƙarar rawar neman izinin shiga.Wayoyinsa ya ɗauka da kuma agogonsa ya zo ya buɗe,cike da girmamawa ya gaishe ta kafin su juyo su yo ƙasa. Ubaidah ta ce “ma sha Allah tubarkallah yau ka fito sak ango ” Kaina na ɗaga ina dubansa cikin wata fitinaniyar farar gizner da ƙyallinta da zubin ɗinkin da aka bazama mata suka haɗu suka fitar da kukan kuɗi.Agogon hannunsa yake gyarawa kafin a hankali ya ɗago idanunsa ya sauke su cikin nawa,zuciyata ta soma rawa nan take babu shiri na sauke idanun ƙasa. “Ya Ubaid ko ɗaurin aure za ka je?” Ubaidah ta sake faɗa. “Ba ki iya gaisuwa ba sai shegen surutu” ya furta yana dungure mata kai kafin ya ja kujera ya zauna.Ina jin idonsa a kaina amma na ƙi ɗagowa,ga shi ina son gaishe shi amma ina tsoron ya ce don na ji ya yi wa Ubaidah ƙorafi ne. “Ya jikin?” ya furta cike da nutsuwa,sai a lokacin na ɗago a hankali na dube shi tare da buɗe baki dakyar cikin sauti can ƙasan maƙoshi wanda na tabbatar bai ji ba sai dai in yanayin motsin laɓana ya duba. “Da sauƙi” “Ubaidah ya na ga kin bar ta za ta je makaranta?” ya furta yana mai soma cin abincin da Ammy ta zuba masa,ita na kalla ina jiran amsar da za ta basa. “Muna da jarabawa ne ” ta basa amsa kafin ta zuba mana abincin mu ma,sai dai wani abin mamaki kasa ci na yi a gaban Ya Ubaid wai kunyarsa nake ji. Juyin duniya ko ruwa na kasa sha,sai wata ƙaramar kula da Ubaidah ta saka ƴar aiki zuba mini nawa a ciki. Duk fitowa muka yi, Ammy ta shiga motar Ubaidullah ni kuma ta Ubaidah.Kamar yadda ta ce za mu je can gidan makokin haka muka yi,muna fitowa da Hassana idanuna suka fara yin tozali tana tsaye sai raba ido take yi kamar mayya.Yadda ta yi wani murmushi tana mai fitowa waje gaba ɗaya shi yasa na juya domin ganin abin da take kallo har ya saka ta farin ciki haka,Ya Ubaid na gani wanda ke gaisawa da Abbanmu. “Mu je mana ko ba ki iyawa na ɗauke ki?” Ubaidah ta faɗa ,na ɗan harare ta kafin mu wuce ciki Ammy na take mana baya.Yau ma cikin ɗaki muka shiga,har ina shirin zama na tuna na shanya pant ɗina a can uwar ɗaka sai na je na ɗauko shi .Ganinsa na yi a yage,cike da takaici har zan jefar sai kuma na riƙe shi a hannu. Mamu ta zo muka gaisa kafin ni da Ubaidah mu fito don lokacin shiga aji ya kusa.Muna isa bakin mota sai ganin mutum na yi a gabanmu,ya dube ni ya kai kallonsa ga ƙafata wacce na saka silifas kafin ya dubi Ubaidah ya ce “ki kula dai da ita in kin ga wata matsala ki kira ni” “To in sha Allah ” sai kuma ya buɗe mini ɗaya ɓangaren,cike da mamakin abin da yayi ɗin na dube shi ,laɓansa na gani sun motsa amma ban ji sautin ba. “Ki kula da kanki sosai” shi ne abin da suka bayyana mini. Ya rufo mini ƙofar kafin ita kuma ta soma tuƙin ,tana mai cewa “Subyna wani abu nake gani a idanun Ya Ubaid da zai tabbata haka tabbas da na fi kowa farin ciki” Yi na yi kamar ban ji ta ba duk da kuwa na fahimci me take nufin,pant ɗin na buɗe ina cewa “kin ga pant ɗin da kika sayo mini an samu wani ɗan baƙin ciki ya yage shi” Wani irin ƙuuuu! Ta soma yi tana ƙoƙarin jan birki har sai da na ji tsoro,pant ɗin ta wani fizge tana cewa “innalillahi!” sai kuma ta figi mota ta canza hanya,na dube ta na ce “lafiya? Ina kuma za mu?” “Wurin Uncle Suhail,Suby ke ban san meke damun ƙwaƙwalwarki ba da ba ta kawo wuta.An ciri pant ɗinki amma hankalinki kwance,wato duk abin da za a yi ke ko oho” "Don Allah kar ki kai ni wurinsa ban so! ” na furta cike da tashin hankali ba tare da ni kaina na san dalili ba,sam ba ta saurare ni ba sai ma gudu da ta ƙara.Yau ba mu tsaya ko ina ba sai wani wurin da yake kama da wurin kiyon dabbobi,ta ko ina shanu ne da sauran dabbobi. Daga inda nake zaune nake hango shi yana a duƙe yana tatsar madarar shanu,miƙewa yayi ya je ya tara wani ƙaton bokiti a ƙarƙashin wani raƙumi da ke takaka fitsari sannan ya nufo motarmu.Jikina ne ya ɗauki wata kyarma ganin ya zo ta ɓangarena ya buɗe tare da furta “fito” kamar wacce ya tsafe haka kuwa na fito ɗin sai a lokacin ita ma Ubaidah ta fito .Shi yayi mana jagora zuwa cikin wata ƙatuwar buka wacce muna shiga ƙafata ta sandare na kasa motsi ballantana tako ɗaya. Normal group 300: posting biyar a sati Vip 600: posting goma a sati Via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 Kowacce ta zaɓi groupe ɗin da take da ra'ayi, wannan ba kalar sauran labaran da na saba yi ba ne sha ƙundum ne,ga soyayya ruwa-ruwa,ga kuma daru da tsantsar darasi [09/06 17:28] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *ROMON HAƘURI* 🤍 MRS SADAUKI ✍️ FCWA ☀️ *Wannan labari ba ƙirƙira ba ce,labari ne da ya faru a gaske ina fatan za ku bibiye shi sau da ƙafa* *__________________________________________________* 08 Tamkar na shiga wuta haka nake jin wannan bukar,ga shi kuma na kasa yin motsi kamar bishiyar da aka dasa. Ubaidah ta yi tsaye tana kallona yayin da shi kuma Uncle Suhail ɗin ya ɗauko wani turare mai wani irin ƙamshin wanda kana ji ka san ba dai wa al'ummar bil'adama ba sai dai jinnu.A hankali na ji jiyoyina sun fara ci gaba da aiki kafin na soma tafiya,wata tabarmar kaba ya nuna mini a can na zauna Ubaidah ma ta zo kusa da ni ta yi zaune. Ruwa ya ɗebo cikin wata randa ɗaya da wata ƴar ƙaramar moɗa ya miƙo mini, Ubaidah ta kai hannu za ta karɓa ya ce “a'a barta da kanta ta karɓa” Kamar mai ciwon hannu haka na kasa miƙa sa ballantana na karɓa,sai ya zo da kansa ya matse kaina tare da soma yi mini karatu nan take na ji wata halitta a cikin jikina tana kuka ta bakina amma sarai na san da ba ni ce ke yinsa ba. Ruwan ya soma ɗura mini waɗanda nake jin tamkar saukar dalma a cikin hanjina,yana gama yi mini ɗuren ya koma gefe nan na soma kakarin amai ina wani gurnani. Ya dubi Ubaidah yana mai cewa “akwai daɗaɗen sihiri jikinta,irin wanda ake yi wa mutum tun yana ƙarami ga kuma motsin jinnu nan a kanta” Ubaidah ta ce “yanzu ya za a yi kenan?“ Ya ce “ke da ita akwai banbanci,kamar yadda na faɗa miki ke jinnunku na ahalinmu ne wanda kusan kowa yana da su,sannan kuma ba su cutar da ke sai ma dai don baki kariya.Saɓanin ita da nata suke na ture ga kuma sihiri,dole da buƙatar a yi mata ruƙiya don gaskiya magani ba zai isa ba” Ubaidah ta miƙa masa pant ɗin tana cewa “ka ga kuma yau ɗin nan ta samu an ciri wani sashe na ɗan kamfanta ” Uncle Suhail ya karɓa tare da dubawa yana kallona,zuwa wannan lokacin na dawo hayyacina.Kallon tausayi yake yi mini kafin ya ce “ke kam laifin me kika yi wa mutane da har suke bibiyarki da sharri haka? ” Wasu hawaye suka zubo mini masu ɗumi,ya maida hankalinsa ga Ubaidah kafin ya ce “da dukkan alamu wanda ke bibiyarta da sharrin nan babban maƙiyinta ne, wannan aikin na ɗan kamfai ana yinsa ne domin saka mace yawon banza.Amma tun da har Allah yasa an yi saurin fahimta zan bata magani wanda za ta dinga amfani da shi da auduga sannan abu mafi muhimmanci shi ne addu'a da yaƙini.Ya kamata ki dage da addu'a,ki tsare zikirorin safe da yamma,ki kuma kiyaye haƙoƙin Allah,ki guji sauraren kiɗa” Ubaidah ta kamo hannuna ta jimƙe cikin nata don ƙarfafa mini gwiwa,sai dai tamkar saƙaƙo haka na zama jin wai an yi mini sihiri ne don na dinga yin yawon banza. Jan muski,da muski A'isha ya haɗe wuri guda ya soma yin karatu a ciki muna zaune sama da minti talatin kafin ya rufe kwalbar ya miƙawa Ubaidah ta karɓa sai kuma ta sunne kai. “Mene ne kuma?” Uncle Suhail ya tambaye ta. Ta ɗago fuskarta shaɓe-shaɓe da hawaye kafin ta ce “ Uncle Suhail ina cikin damuwa,jiya Sul ya kira ni ya ce sam babu sauƙi game da rayuwarsa ta can.Kwanaki in ba ka manta ba na yi maka magana kan matar da ke bibiyarsa,to har yanzu ba ta bari jiya ma ta so jan ra'ayinsa” Uncle Suhail yayi murmushi ya ce “duk sun yi su gama,ki ce masa ya ƙara yin haƙuri da izinin Allah komai zai wuce” Ta goge hawayenta ta ce “yau na yi mafarkin an yi auren amma wai kafin ma a kai ni ya mutu” “Sharrin sheɗanu ne,bari na baki jibda duk dare in za ki kwanta ki tabbatar kin shafe jikinki da ita musamman bayan kunnenki” Sai ya ɗauko wata ƴar ƙaramar kwalba ya bata,ta miƙe tsaye ni ma da sauri na tashi muka fito ba tare da na ga ta basa ko ƙwandala ba .Muna shiga mota na ja numfashi ina mai cewa “wai wane ne wannan mutumin?” “Uncle Suhail ne,ƙanen Ammy ne ya mutu a wani hatsarin mota da suka yi a hanyar Maiduguri,bayan wasu shekaru kuma sai ya dawo amma ahalinsa suka ƙi karɓarsa suka ce fatalwa ne” Baki da hanci na saki ina kallonta,na haɗiye wasu yawun tsoro na ce “kina nufin wurin fatalwar ne kika kai ni har ya bani magani?” Ta yi wani ɗan murmushi mai sauti kafin ta ce “ba fatalwa ba ne,mutum ne wallahi sai da abubuwan da ya fuskanta a rayuwar da yayi bayan mutuwar bogin yasa duk ya canza za ki ga yana abu kamar aljani ” Wani irin tsoro ne na ji ya mamaye ni jin ta ambaci aljani,don ni duk duniya na tsani abin da ya shafe su.Har muka isa makaranta a takure nake ga Ubaidah sai sake zaƙulo wasu ababen tsoron take yi.Ko da muka isa bakin aji tuni malami ya shiga,amma bai hana mu ba muna shiga muka ɗauki takarda muka soma zana jarabawar.Duk da mun zo a latti amma sai da muka rige wasu idawa,fitowa muka yi sai kuma a lokacin ne ta bani abincina na yi zaune kan step ɗin ƙofar ajinmu na soma ci hankali kwance ita kuma tana daga tsaye tana yi mini hira.Na ɗauki kamar minti biyar haka sai na ji jikina na ɗaukar rawa,da sauri na rufe kular tare da cewa “Ya Ubaid ya shigo makarantar nan Udah” sai na soma waige-waige. “Wane Ubai...” shirun da na ji ta yi shi ya tabbatar mini da ita ta gansa,na juya saitin inda take kallo sai na hango shi a tsaye kunnensa maƙale da waya amma idanunsa suna kaina sai na ji duk jikina ya ƙara yin sanyi,wato yana ta kallona ina buga loma ban sani ba.Da wani irin sauri Ubaidah ta nufe shi ,babu shiri ni ma na miƙe na soma tafiya a hankali saboda ciwon ƙafata.Har na isa idanunsa na kaina,kusa da Ubaidah na yi tsaye ina ɗan jingina da bayanta na kuma riƙe ta gam na ɗora kaina kan kafaɗarta,a hankali na ce mata “na gaji” “Aikin me kika yi ko cin abincin ya gajiyar da ke?” ta faɗa .Na turo baki tare da kai hannu na mitsike ta,tana dariya ta saki ƴar ƙara daidai nan Ya Ubaid ya gama wayar yana mai kallonmu.Ita ce ta soma yi masa magana,“Ya Ubaid me ka zo yi sukul ɗinmu?” “Ya jikin nata? ” yayi tambayar yana kallona kuma madadin ya dubi wacce yake tambayar,na ɗan lumshe ido ina sauraren bugun zuciyata. “Ga ta nan dai babu abin da ke yi mata ciwo sai dai yunwa kawai da take ji,dubi yadda ta rame“ Ubaidah ta faɗa tana ƙoƙarin janye ni daga jikinta,na takure wuri ɗaya na ƙi yarda. “Mu je na kai ku restaurant ” ya furta tare da juyawa, Ubaidah ta ce “mu tafi ko?” “Na fa ƙoshi iya ruwa nake son sha” na faɗa a sanyaye ba wai don kuma na ƙoshin ba,a'a ban so ina yin kusa da Ya Ubaid ɗin ne wata irin kunyarsa nake ji. “To mu je ai can ma ana sayar da ruwan” ta faɗa tare da soma tafiya. Na ce “ga kularki can fa na baro bakin ƙofar aji” “Bai komai in Bahijja ta fito ta ɗauke mana” ta faɗa ,Bahijja a banci guda muke zaune ita ma ƙawarmu ce sai dai ba mu shaƙu sosai ba kamar yadda muke ni da Ubaidah. Haka muka wuce,tuni ya shiga motarsa wannan farin gilashi ne da ita hakan yasa ina iya hango shi yanzu ma wata wayar ce yake yi.Muna isa Ubaidah ta buɗe gidan gaba ta ce “Suby shiga” Na ce “zan zauna a baya ki shiga kawai” “In muka dawo ke za ki shiga gaba yarinya” ta faɗa tare da shigewa,gabana ya faɗi jin wani zance haka na shiga baya ɗin ya figi motar . Mun hau kan titi sosai ya ajiye wayar,madubin gabansa ya gyara da kyau hakan ya bamu dama kallon juna ni da shi.Wani irin amintaccen kallo ne yake yi mini,na sunne kai ina murmushi wanda sam ban yi tunanin shi ne mabuɗin alaƙar zuciyoyinmu ba. Wani haɗaɗen gidan cin abinci ya kai mu,VIP PALACE can aka nufa da mu.Komai na ciki na ƴan gayu ne,Ubaidah ce ta zaɓa mana abin da za mu ci yayin da shi kuma ya ɗauki iya abin sha. Da aka kawo mana abincin sai da na kasa ci na yi ta juya cokali,a hankali Ya Ubaid ya miƙe ya je can kusan window tare da yaye labulen wurin ya tsaya yana kallon abin da ke wakana a ƙasa. Sai a lokacin kawai na soma ci,shi ma ban wani saki jiki ba.Ubaidah banda aukin murmushi babu abin da take yi sai kuma kallonmu,bai dawo mazauninsa ba har sai da na kammala ci ina shan lemu. Zuwa aka yi aka kwashe komai da ke kan table ɗin,sai kuma ya soma yin magana. “Ya jarabawar?” “Ta yi daɗi sosai,su Suby tun da aka duƙe kai ba a ɗago ba an ga banza” ta faɗa tana mai kallona,harararta na yi na ce “ke ma ai banzar kika gani” “Ya kamata dai tun yanzu ku ƙara ɗaura ɗamarar yaƙi,don da zarar kun ci exam za ku wuce jami'a a can karatun ya fi tsanani” “Ni ai ɓangaren da zan karanta babu wani tsanani ,ka faɗawa dai likitoci” Ubaidah ta faɗa,ya zubo mini ido sai kuma bai ce komai ba ya miƙe.Bayan ya biya kuɗin muka fito yana mai tambayar in makaranta zai mayar da mu,“gidansu Suby za mu je” ta basa amsa.Bakin motarsa muka isa sai ta yi saurin shiga baya ina shirin shiga ni ma idanunmu suka sarƙe cikin na juna,ba don na so ba na zagaya ta can ɓangaren sai kuma na yi tsaye na kasa buɗewa sai shi ne da ya shiga ya buɗe mini ta ciki.Tsabar yadda jikina ke yi mini rawa na buge ƙafata mai ciwo,na rumtse ido ina mai daurewa na shiga na zauna.Sosai na yi ƙoƙarin mayar da hawayen da suka taru a idona,ita ce ta soma yi masa kwatance.Har muka isa ban ɗago ba, Ubaidah ta yi saurin fita yayin da shi kuma ya duƙo yana cewa “mu ga ƙafar” a hankali na ciro ta hawaye na zubo mini shaaa har suka ɗiga gefen kunnensa.Ya ɗago yana kallona,“ko in kai ki asibiti?” Kai na girgiza,“zan sayo miki magani to” ya furta. Ban ce komai ba,ya kai hannu ya buɗe mini murfi,tare da zaro hankici ya miƙo mini na karɓa na goge fuskata sai na fita.Ina shiga cikin gida na ga Ubaidah a tsaye kamar an dasa shuka. “Lafiya?” na tambaye ta,da hannu ta yi mini nuni da wata baƙar akuya mai gemu ta kuwa ƙuro mana idanunta jajaye. “Wane ne?” daga can ɗaki muryar Mama Lantana ta faɗa kafin kuma ta fito.Tana ganinmu ta haɗe rai tana cewa “lafiya kuka wani tsaya nan? Ke don ubanki jiya ina kika kwana?” Jikina na rawa na ce “gidansu Udah” “Can ɗin gidan ubanki ne? Daga za ta auri ɗan uwanki shi ne kika kwashi jiki kika tafi can kika kwana saboda kalar dangi ,ki ci kaza ki sha lemun kwalba kin dai ji kunya.Ko da yake laifin gantalaliyar uwarki ce wacce ba ta san mutumcin kanta ba ballantana na ƴaƴanta...” sai da ta kawo nan kawai Ubaidah ta yi magana. “A'a Mama in za ki yi mata faɗa ki tsaya iya ita amma kar ki taɓa Mamu don wallahi ba zan yi shiru ba.Ko ita Suby ɗin don kar a ce na yi rashin kunya ne da wallahi ba ki isa ki faɗa mata biyar ba ban faɗa miki goma masu muni ba” duk yadda nake son dakatar da Ubaidah amma ta ƙi yin shiru har sai da ta faɗi son ranta. Mama Lantana sai ta kasa cewa komai,na yi matuƙar mamaki ashe Surajo ta gani ya shigo.Ba a ɗauki lokaci ba kuwa ya soma yi mata saukar kwandon rashin mutumci yana kamo sunanta yana ɗura mata zagi,sai tangaɗi yake alamun ya sha abar. Ɗakinmu a rufe yake,ga shi kuma banda makulli dole muka fito muka samu adaidaita ya mayar da mu makaranta.A hanya Ubaidah sai masifa take yi har muka isa,motarta kawai ta ɗauko muka shiga na yi tunanin gidansu za mu wuce amma na ga ta kama hanyar gidan Uncle Suhail. Roƙonta na fara yi amma ganin ɓata lokacina ne nake yi kawai sai na haƙura ,da zarar mun haɗa ido da ta wani kallo ne take yi mini mai kama da harara irin kana jin takaicin mutum.Yanzu da muka isa wata yarinya muka tarar yana yi wa ruƙiya cikin ƙira'arsa mai bala'in daɗi kamar sarewa,bayan an kammala mata ya ba mahaifiyar yarinya magunguna kafin su tafi .Sai kuma ya zubo mana na mujiya,Ubaidah ta yi gyaran murya tana cewa “yanzu muka je gidansu,sai muka tarar da baƙar akuya mai gemu a ɗaure da dukkan alamu kuma ta kishiyar Mamu ce kuma na faɗa maka ai ina zarginta ban yarda da ita ba” “Akuya mai gemu dai alama ce ta sadaukarwar ruhin wani ga aljani,an fi amfani da ita wurin yin tsafin rarabuwar kai a tsakanin mutane” yana kawowa nan yayi shiru. Ubaidah ta ce “Uncle Suhail don Allah ka yi wani abin” Ya saki murmushi yana mai cewa “Ubaidah babu abin da zan iya yi akai dole sai wacce kike nema wa maganin ta yarda da kanta ba ta da lafiya” Yana furta haka sai ta juyo ta dube ni,ta kamo hannuna tana mai cewa “Suby ki yarda don Allah ” Bakina na ƴar rawa na ce “toh” faɗar haka ke da wuya sai Uncle Suhail ya miƙe ya ɗauko wani abu tare da zuwa ya riƙe kaina da kyau ya ɗiga mini shi cikin idanuna,bai da zafi sai wani irin sanyi mai kamar zai makantar da mutum don sai da na yi kamar kusan minti biyu ban ganin komai kafin kuma fitilun idanun nawa su dawo normal. "Bayan fitarki a nan shekaran jiya faɗa mini abubuwan da kika gani wanda a can farko kafin na shaƙa miki magani ba ki iya ganinsu” ya furta cike da kulawa,nan take na soma jin ana yi mini motsi cikin kai kafin kuma tunanina ya fizgo mini wani baƙin sirri da ake mantar da ni. Muryata na rawa na ce “Mama Lantana ta zo gidansu Ubaidah cikin siffar mage ,tabbas na ganta a madubi.Sai kuma ...sai kuma Hamida ” shiru na ɗan yi ,Ubaidah ta ƙara jimƙe hannuna ta ce “kar ki ji tsoro ki faɗa masa me Hamidar ta yi?” Hawaye suka zubo mini sha kafin na ce “girkin da ta kawowa Ya Ubaid ta zuba magani a ciki wannan yasa na ga kayan cikin na motsi kuma tamkar ba a dafa su ba” a fuskar Ubaidah na karanci tsantsar mamaki haɗi da baƙin ciki,sai dai ta kasa cewa komai sai shi Uncle Suhail ɗin ne ya fara bayani. “Ya tabbata Mama Lantana mayya ce,sannan tana daga cikin masu aikata shirka .Ita kuma Hamida tana yin wannan ne domin mallakar Ubaidullah.Zan baki wani hayaƙi ki turara shi a tsakar gida a duk lokacin da kika ga wani abu wanda bai dace ba,sai kuma nonon raƙumi da na yi wa karatu ki tabbatar kin bai wa duk wanda ya ci naman akuyar nan, ya sha kofi ɗaya da izinin Allah zai amayo shi” Sai ya ƙara miƙewa ya je ya ɗauko mini duk abubuwan da ya kamata , wannan karon da ƙarfin gwiwata na karɓa har da yi masa godiya. Bayan mun fito ne na jingina ga mota ina fashewa da matsanancin kuka,Ubaidah ta ce “me aka yi kuma?” Cikin muryar da ba ta fita soyayya na ce “me na kashewa Mama Lantana Udah? Shin akwai inda na gaza ne wurin bata girmanta?” Ubaidah ta taɓe baki ta ce “ai godiya za ki yi wa Allah tun da har ya toni asirinta” Ban ce komai ba,haka muka shiga mota muka koma can gidanmu.A daidai wannan lokaci ne muka tarar ana yanka akuyar a tsakiyar gida,ita kuwa Mama Lantana ta riƙe ƙugu tana kallo. Cikin ɗaga murya Ubaidah ta ce “tawakaltu alallahi laa haula wala ƙuwata illa billah! Hasbunallahu wani'imal wakil!” wanda ke yin yankan ne ya ɗago ya dube mu,idanunsa ya ranbaɗa musu kwalli ga wata ƙatuwar casbi a wuyansa.Hannunsa na kalla mai riƙe da wuƙa,sai na ga sam ba iya nasa ne ba kaɗai tamkar har da na wani ɓoyayyen ruhi wanda ba a iya ganin siffarsa sai dai inuwarsa. Cikin ɗaki muka shiga ni da Ubaidah,duk yadda ta so Mama Lantana ta kula ta kuwa banza ta yi da ita.Muna kallo ƙiri-ƙiri Mama Lantana ke yin tsafi kafin a feɗe akuyar,na dai ga an saka masa naman a leda amma ban san wane ɓangare ne aka cira ba. Jikina yayi wani irin sanyi,zubewa na yi kawai na kwanta ina jin zazzaɓi na rufe ni.Ubaidah kuwa sai addu'o'i take tofe ni da su. ★Hassana Ta yi nasarar ganin Ubaidullah,sosai yayi mata kyau cikin shigar gizner ɗin.Sai da ta yi duk iya yinta kafin ta samu magana ta haɗa su da shi,gaishe shi ta yi ya amsa ba tare da ko ya kalle ta ba.Sam kasa sukuni ta yi tun bayan jin muryarsa,ciki ta koma tare da keɓe kanta ta dinga saƙa da warwara.Can kuma ta ji wani abu na luluɓe ta mai kamar inuwa ,wani irin canji take ji a jikinta tsikar jikinta na tashi ko ina yana yi mata yammm! Yammm! Wata irin ganga ce mai zaƙi take jin tana dokawa a kunnuwanta,a take kuma tunaninta ya canza zuwa na yadda halittar da ta gama shigar a yanzu ke burin ganin ta zama.Fitowa ta yi ta soma tafiyar ƙasa,duk nisan gidan malam Yawale haka ta je a ƙafa cikin rana.Layi ta kama tana zaune tana mai ci gaba da jin yanayin na ƙara mamaye ta,a haka har layi ya zo kanta. Da ta shiga kallo ɗaya malam Yawale ya yi mata ya gane ta, Hassana ta zauna tare da gaishe shi sai kuma ta yi shiru. Ya ce “ina jinki” “Ina son ka yi mini aikin da zan mallaki wani saurayi da na gani ina so,aurensa nake son yi” ta faɗa tana jin tamkar ana matse zuciyarta. Rubutu ya soma yi kan wani guntun madubi kafin ya ce “aikinki yana da farashi mai kauri,muna yin wannan aikin ne ta ɗayan biyu.Za ki duba a cikin almajiraina ki zaɓi mutum ɗaya wanda yayi miki,zan yi rubutu a jikin al'aurarsa sai ya yi mu'amala da ke domin cikar buƙatarki a rana ɗaya tak, sannan daga ƙarshe za ki biya miliyan ɗaya” Normal group 300: posting biyar a sati Vip 600: posting goma a sati Via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 Kowacce ta zaɓi groupe ɗin da take da ra'ayi, wannan ba kalar sauran labaran da na saba yi ba ne sha ƙundum ne,ga soyayya ruwa-ruwa,ga kuma daru da tsantsar darasi [10/06 16:19] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *ROMON HAƘURI* 🤍 MRS SADAUKI ✍️ FCWA ☀️ *Wannan labari ba ƙirƙira ba ce,labari ne da ya faru a gaske ina fatan za ku bibiye shi sau da ƙafa* *__________________________________________________* 09 Hassana ta dube shi a ɗan firgice,ba wai yin mu'amalar ce damuwarta ba a'a hasalima da ya furta kalmar ji ta yi kamar ma a ce ta samu wani namijin ta yi masa fyaɗe.Damuwarta ɗaya, miliyan ɗaya da ya ambata. “Miliyan ɗaya?” ta tambaya cikin wani yanayi,wanda yasa malam Yawale faɗa mata ɗayar hanyar.Ya ce “za ki iya yarda ni na mu'amulance ki amma ba za ki biya ko sisi ba” Ko ida rufe bakinsa bai yi ba ta ce “na amince” Malam Yawale na jin haka ya danna waya ƴar ƙarar rawa wacce ke nuni da ya tashi daga aiki sai kuma gobe,haka duk mutanen da ke zaune kan layi suka fara fita. Can ya fito ya duba ya ga babu kowa sannan ya koma can ciki,a gabanta ya zumbule suturar jikinsa ya kuma yi rubutun shirka kamar yadda ya faɗa tun farko yadda tsarin yake.Bayan haka ya umarce ta da ta kwaɓe kayanta, babu kunya ballantana tsoron Allah malam Yawale ya mayar da Hassana cikakkiyar mace.Ta ci azaba fiye da ma kalmar,saboda ba iya ƙarfinsa na ɗan Adam ba ne a'a har da na maƙarabansa.Bayan komai kammala ya fita ya samo mata ruwan ɗumi ta yi wanka sannan suka ƙara dawowa ya soma rubuce-rubucensa tare da haɗa mata magani iri-iri wanda za ta saka masa a abinci da kuma wanda za ta yi hayaƙi da shi in zai zo.Karɓa ta yi ta fito tana tambayar kanta ita na za ta ga Ubaidullah da har za ta zuba masa magani? Amma a haka ta nufi gida. ★Hamida Cike da takaicin abin da Ubaidullah yayi mata ta jawo motarta ta kai ta can gareji aka gyara mata tayarta da ta soma lalata wa da kanta.Daga nan gida ta wuce ,babu kowa sai ƴan aiki da suke ta faman bauta.Ɗakinta ta wuce,direct ta shiga toilet ko kaya ba ta cire ba ta sakarwa kanta shower hawayen takaici da baƙinci suna masu tsiyayo mata suna haɗe wa da ruwan pampo.Yadda ta ga Ubaid na rawar jikin kai Suby asibiti ya fi komai baƙanta mata rai fiye ma da ƙin cin abincin da yayi,don tana da sauran maganin za ta iya saka masa shi a gaba. Kamar wata mage da ta sha kashin ruwa haka ta fito daga toilet ɗin ruwa na yi mata tsiyaya.Sai da ta je gaban madubi sannan ta warware sarin ya faɗi ƙasa,sai ta tsaya iya riga da wandon da ta sa a ƙasan sarin. “Ko lukuta yake so ne? ” ta yi tambayar a fili kafin kuma ta girgiza kai ta ce “kai bai yi yiwa Ubaidullah ya so Suby wannan ƙaramar yarinyar da ko kama ruwa ba ta iya ba, sannan ba ta da wani ilimi” da wannan ta watsar da zancen Suby ta ida cire jiƙaƙun kayan ta sauya wasu na shan iska. Cike da izzar da ta saba ta kira ƴar aikinsu ta gyara mata ɗaki,kan gado ta haye tana mai buɗe system ɗinta ta fara bincike akan asibitocin da ke buƙatar ma'aikatan kiyon lafiya cikin sa'a kuwa ta ga babbar asibitin da duk ƙasar Nijar babu kamar ta na neman ma'aikata.Wani ɗan ihun murna ta yi saboda ta yarda da kanta a fagen ilimi za ta iya cin jarabawa.Sam ba wai kuɗin da za a dinga biya na albashi ba ne damuwarta,a'a a kira ta matsayin ma'aikaciyar asibitin ma babbar nasara ce. Haka ta yi wuninta cikin bincike babu sallah ko ɗaya da ta yi sai ta magrib kawai.Bayan sallar isha'i ta fito saboda ta ji motsi,Ummah ce ta dawo daga yawon bin malamai ta gaji duk ƙafafu sun yi mata fututu kamar mahaukaciya. A yunwace take shan frut ɗin masu sanyi saboda uwar wuyar da ta sha. Hamida ta ce “Ummah ina kika je yau? ” sai kuma ta nuna ƙafafunta ta ce “dubi yadda ƙafarki ta yi” “Haba ke ta ƙafa kike,ni babban baƙin cikina shi ne ta yadda ban samo gidan Bokan da aka kwatanta mini ba.Tun safe muke shiƙa ni da ƙawata amma a banza ba mu ga gidan ba” Hamida ta yi saurin zama gefenta tana mai cewa “Ummah mu da muke da malam Yawale har akwai wani malami da ya fi shi ne?” “ Wannan fa boka aka ce miki ya fi ƙarfin malam Yawale,saboda a lamarinsa shi sam babu wani abu da ya danganci Allah ” Hamida ta ce “yanzu ya za ki yi kenan?” “Gobe za mu sake komawa,in kuma kina zuwa ki shirya mu tafi don kin san an ce zuwa da kai ya fi saƙo gara ki bi mu ki yi wa boka bayanin damuwarki tun da Ubaidullah ya cika taurin kai gara a kai shi ga bokan ” “Ummah ai na yi tunanin saboda ni kike son ganin Bokan,amma to in haka ne ke wane aiki zai yi miki?” Ƙwarewa Ummah ta yi ,da sauri Hamida ta miƙo mata ruwa ta karɓa ta sha.Sai kuma ta miƙe ta bar mata falon,Hamida ta bi bayanta da kallo tana mamakin Ummar sam ita ba ta yi tunanin akwai wata damuwar da ta shige mata ba da har take son ganin boka. Tv ta kunna tana kallo,kafin ta sa ita ma a kawo mata fruit ɗin ta soma sha. Abdul Hamid yayi sallama,ta amsa ba tare da ta dube shi ba idanunta na kan tv.Kusa da ita ya zauna yana mai ɗaukar ayaba ya kai bakinsa ya ce “ƙanwar na fa samu mata aure” Da wani irin sauri Hamida ta juyo ta dube shi tana washe baki,cike da tsantsar farin ciki ta ce “a ina? Wane aiki take yi? Ƴar wane family ce?” Ido ya zuba mata kafin ya ce “ke ban son shirme ni ina ruwana da family ɗinta,kawai ni dai ina son ta” Hamida ta taɓe baki tana cewa “tun da ka faɗi haka ya tabbata kuwa ƴar talakawa ce,to Allah yasa dai tana da kyau don in ka ɗauko mummuna abin zai yi yawa wai shege da hauka ” Kallon mamakin da yake yi mata yasa ta ci gaba da cewa “eh mana yadda kake babban Dr ai ka san dole ka tsaya ka ɗauko matar shiga tsara wacce ba za ka ji kunyar nunawa ba akan kowanne irin taro” Kai ya girgiza yana mai cewa “na ma fasa nuna miki hotonta” Ta ce “ai gara dai ka nuna mini in ba ta yi ba na sanar da kai,saboda ina son matar da za ka aure a ce ta fi Ubaidah kyawu ta hakan ne za ka nuna mata ka yi mata zarra” Abdul Hamid ya ce "wallahi ta fi Ubaidah kyawu kawai dai don iyayenta ba masu kuɗi ba ne amma ina mai tabbatar miki in ta ji gata sosai za ta fito da irin ƴaƴan Daddy” Hamida ta yi shewa tare da cewa “to kai ka sa ta zama ƴar gidan Daddyn,bari ma na tashi na ɗauko takarda na yi maka liste na abubuwan da za ka saya mata,cikin wata ɗaya kacal za ta dawo ƴar gayu” ba tare da ta jira cewarsa ba ta miƙe ta je ta ɗauko takarda kuwa ta zauna ta soma rubuta masa shi dai yana daga gefe yana kallo sai bayan ta gama ya karɓa ya soma karantawa. ★Sulaimanu. Bayan sun gama waya shi da Ubaidah sai ya ƙara ɗaukar tazarar lokaci kafin ya koma gida.Ya ci sa'a kuwa duk sun kammala masha'arsu yana jin wasu suna hirar batsa yayin da wasu kuma ke baccin gajiya.Ɗakinsa ya shiga,ya kunna fanka sannan ya kwanta yana tunanin ko mene ne ya samu Suwaibar amma bai ji hankalinsa ya wani tashi sosai ba saboda ya san Ubaidah sai ta fi kowa kulawa da ita.Cikin hukuncin Ubangiji ya samu bacci mai daɗi ya ɗauke shi har da tsarabar mafarkin Ubaidah,da ya farka sallar asubah sosai ya ji daɗin mafarkin don ya samu ya rage dattin da ke damunsa.Tsabtace jikinsa yayi ya fito ya wuce masjid,yadda Abbas ya wani shige sawun gaba sai ya bai wa Sulaimanu takaici.A zuci ya ce ‘ ko kunya bai ji,jiyan nan ya gama yin laifi mafi muni amma ga shi a sawun gaba,ko da wane irin ƙarfin zuciya ne ya zo ganawa da Ubangijinsa?’ sai kuma ya basar,ko da aka gama sallah bai koma gida ba nan ya zauna yayi ta zikirori da jinjina haɗi da godiya ga Ubangijinsa da yake tsare shi daga dukkan tarkon matan banza.Sai da rana ta hudo sannan ya fito daga masjid ɗin,yana shiga gida ya tarar matan suna ƴar rige-rigen shiga banɗaki yin wanka.Kai kawai ya kawar yana istigfari kafin ya shige can ciki,wayarsa ya ɗauko ya turawa Ubaidah saƙo sai kuma ya hau facebook hana chating hakan ya ɗauke masa da hankali sam bai ba kwanyarsa damar ma tsayawa jin abin da suke cewa ba.Kafin wani lokaci gidan ya ɗauki wani shiru,sai a wannan lokacin ya fito sai ya ga Abbas na wankin toilet.Suna haɗa ido ya ɗan sunne kai,shi kuwa Sulaimanu baki ya taɓe yana mai cewa “kunyar Ubangijinka ya kamata ka ji ba tawa ba,ni mene ne nawa a ciki? Lada gare ni ko zunubi? Iya abin da zan ce ma shi ne ka ji tsoron ka guji saɓon da ke rushe aikin lada a nan take” Abbas wanda can farko mutumin kirki ne,zama da mutanen banza ne ya ja ra'ayinsa.Ɗan numfasawa kawai yayi yana sauraren abokin nasa kafin ya ce “ka shiga ka yi wankan,na gama wanke toilet ɗin” Sulaimanu ya saki baki cike da mamaki yana kallon Abbas ɗin kafin kuma ya shige banɗakin ya yo wanka ya fito.A gaggauce ya shirya cikin uniform ɗin ƴan sanda kafin ya fiddo babur ɗinsa ya wuce. ★Ubaidullah Bayan ya ajiye su Suby direct gidan gonarsa ya wuce,yau jinsa yake wani iri na daban tamkar sabon jariri sabuwar haihuwa wanda ya shigo zangon wata sabuwar rayuwa da bai san da ita ba.Murmushin da Suby ta yi masa har ƙahon zuciyarsa haka ya ji shauƙi ya cake shi,yana driving yana tunaninta har ya isa aka buɗe masa babban get ɗin. Ya jima sosai zaune cikin mota kafin ya fito,ma'aikata masu kula da wurin duk suka zo suka gaishe shi.Zagaye ya soma yi kafin ya nufi wani keɓaɓen wuri da aka tana domin hutawarsa shi ɗaya.Wayarsa ya fiddo yana jin ina ma yana da lambarta da ya kira ta ko ya tura mata saƙo don jin ya take,saboda haka kawai yake jin kamar ba ta cikin walwala.Tun yana jurewa har ya kasa ya kira Ubaidah,bayan sun gaisa sai kuma ya yi shiru ya rasa ta ina zai fara. “ Hello!” Ubaidah ta faɗa . Ya ja numfashi kafin ya ce “tana ina? Ya jikin nata?” “Ta nan a kwance zazzaɓi ya rufe ta kuma ta ƙi shan magani,sai addu'o'i dai da nake yi mata a ruwa tana sha” ta basa amsa ,shi kuwa ido ya rumtse yana cewa “zan turo likita ya duba ta” “A'a Ya Ubaid ban so don Allah...” ya ji amon murya Suby daga can cikin shashekar kuka.Hankalinsa sai ya ida tashi,kiran ya katse ya kira Abraham cikin ɗan taƙaitaccen lokaci yayi masa bayani kasancewar shi Abraham likita ne a cikin sojan. “In kuma an ce ka faɗa soyayya ka ƙaryata mutane ” Abraham ya faɗa yana ƴar dariya. Ubaid ya ce “don Allah duk mu yi wannan daga baya amma ka je ka duba ta,ni na yi nisa da gari kafin na iso za ta galabaita” Abraham ya ce “ ok turo mini location ɗin gidan” “Zan turo maka lambar Ubaidah sai ka kira ta ” a haka suka tsayar da zancen,yana kashewa ya tura masa lambar shi ma sai ya tashi ya fito ya shiga motarsa domin komawa cikin gari. ★ Ban taɓa sanin tashin hankali na haifar da zazzaɓi ba sai yanzu,zuciyata wani irin ƙuna take yi mini ga shi kuma babu wata mafita don na san ko na sanar da Mamu ba za ta yarda ba,uwa uba daɗa Abbanmu wanda ba wai mu da muke gida ɗaya ba hatta maƙwabta sun san da an shanye shi. Kaina na kan cinyar Ubaidah sai addu'o'i take yi mini a ruwa ina sha tana kuma shafa mini ruwan a fuskata da take daɗa yin zafi fiye da ko ina na jikina.Ina jin lokacin da take waya da Ya Ubaid saboda hand free/main libre ta sa saka.Cikin ƙwatowar numfashi na roƙe kar ya turo likita,jin ya datse kiran na yi tunanin ya bar zancen har sai da na ji Ubaidah na yin wata wayar tana yi masa kwatancen gidanmu.Ba a ɗauki lokaci ba kuwa ya zo,ita ce ta fita ta shigo da shi.Ina jin maganar Mama Lantana na cewa “abin kuma har ya kai da shigo mana da ƙattai cikin gida?” “Mama ni likita ne na zo duba marar lafiya ne” na ji muryar wani namiji na yi mata bayani. Ta ce “a'a ba sai ka yi ƙarya ba ɗan nan wuce ai kowa da sana'ar da ta karɓe shi” cikin tsantsar farin ciki take faɗar haka. Sosai kuma na yi mamakin ta yadda aka yi Ubaidah ba ta tanka ta ba har suka shigo ita da likitan.Wani ƙarfi ne ya zo mini na tashi zaune ina ce masa “don Allah kar ka yi mini allura ka bani magani” “Ina ga wannan sai kin riƙe mini ita” ya faɗa,Ubaidah ta matso za ta riƙe ni na ce “wallahi in kika taɓa ni cizon ki zan yi” Ta yi wata dariya tare da zuwa ta yi mini kyakkyawan riƙo,wasu hawaye ne suka soma zubo mini kafin kuma na soma yin ihun azaba.Bayan ya yi mini allurar ya warware bandejin ya zuba magani sannan ya sake mini wani. “ A yi shiru Madam an gama” ya faɗa cikin raha,sai kuma ya kira Ubaidullah a gabanmu yana mai cewa “aboki kana fa da jan aiki a wurin nan,dakyar na samu na yi mata allura abu sai ka ce ana yaƙin duniya” ban ji abin da Ubaid ɗin ya ce ba, Dr dai yayi ƴar dariya kafin Ubaidah ta yi masa rakiya ta dawo.Babu jimawa kuwa Mamu ta dawo, Ubaidah ce ta yi mata bayanin banda lafiya ne wani abin mamaki ko kaɗan Mamu ba ta nuna damuwarta ba a kai ballantana na yi tsammanin samun kulawa. Kiran Ubaid ya sake shigowa wayar Udah,amma sai ba ta ɗaga ba saboda yadda damuwa ta sauko mata sai wani satar kallon Mamu take yi.Horne muka ji a ƙofa,ta miƙe tana cewa “ina ga Ya Ubaid ne”sai ta fita babu jimawa ta dawo ta ce mini “shi ne.Ki ƙoƙarta ki taso mu tafi” “Tsoron fita nake yi Udah,ban son ganin jini” na furta. “An rufe ramen fa,ki taso mu je” ta faɗa .Sai da na wanke fuskata kafin na miƙe na canza hijabi,hannunsa cikin na Ubaidah muka fita.Yana zube cikin motarsa ,yana ganinmu ya fito.Ƙatuwar leda ya miƙawa Ubaidah sai kawai ta tafi ta bar ni a nan tsaye,nan take jikina ya fara yin rawa dole na jingina jikin motarsa. “Ya jikin naki ? Ya kukan kin gama?” ya tambaye ni. Na ɗan sunne kai murmushi jin wai har da kuka ya tambaya. Ya ce “ko a sake kiran Dr Abraham?” kai na girgiza masa cike da tsoro,sai na ji yana murmushi mai sauti na ɗauke a hankali na dube shi idonmu ya sarƙe cikin na juna ,na ɗan kawar da kai na dubi ƙofa na ce “har yanzu ba ta dawo ba” “Kin matsu ta dawo ta tafi da ke don kar na tsere da ke ko?” Kunya furicinsa ya bani sai na rufe fuskata,yanzu ma dai murmushi mai sauti yayi yana cewa “wuce ki koma gida” “To” na furta tare da saurin tafiya,tako biyu kawai na yi na ji amon muryarsa na cewa “ki kula da kanki” ban juyo ba sai dai sosai kalmar ta dake ni har na kasa motsi na wani ƴan sakanni kafin na wuce ciki. A tsakar gida na tarar da Mamu ita da Mama Lantana suna yankan naman akuyar tsafi,ban ce musu kanzil ba na wuce ɗaki.Ubaidah na ganina ta soma yin dariya,"su Suby an shiga kogin soyayya ” “Wace soyayya kuma?” na tambaye ta,sai ta yi mini kallon kar ki raina mini hankali kafin ta nuna mini abin da Ya Ubaid ɗin kawo.Fruit ne da jus sai kuma magunguna,iya lemun kawai muka sha kafin Ubaidah ta yi mini sallama ta tafi ta bar ni nan ni ɗaya. Sai da aka kira sallar la'asar kawai na fita na ɗauro alwala,ina ƙoƙarin komawa na ga Mama Lantana ta ciro zuciyar dabba wacce nake kyautata zaton ta akuyar nan ce,an rubutu a jikin zuciyar sannan an tsire ta da wani tsinke.Kan garwashi na ga tana juya ta tana gasa ta,fuskarta ɗauke da murmushi.Daidai nan Mamu ta fito daga banɗaki ,kan wani dutse ta zauna tana dafe ƙirji haɗi da watsa ruwa jikinta. Ƙafafuwana suka ɗauki wata irin rawa,dakyar na isa ɗaki na zube kamar wasu kayan wanki.So nake na sanar da Ubaidah sai dai kuma ina ganin lokaci yayi da zan ɗauki dakon damuwata ni ɗaya na bar Udah ta huta haka nan,dakyar na gabatar da Sallah.Ina nan zaune kan dadduma Mamu ta shigo,ita ma a zaune ta yi sallar tana idawa ta kwanta tana mai cewa “bani ƙanƙara a frigine ” Na tashi dakyar na buɗe na ɗauko na miƙa mata,cikin riga ta saka shi daidai zuciyarta sai ta soma jan numfashi kamar mai shirin mutuwa.Gefe na koma na zabga uban tagumi,kafin kuma tunanin kiran Sulaimanu ya faɗo raina.Cikin kuka na shaida masa Mamu ba ta da lafiya,sai dai amsar da ya bani ita ta ƙara saka ni wani tashin hankalin. “Mama Lantana ta sani? Ni yanzu ba zan iya barin nan ba kin san halinta sarai in na je faɗa za ta yi mini,kuma na san ko na tambayi izininta ba barina za ta yi na zo ba” ya faɗa cikin wata murya. “Wa kenan zai baka izini?” na tambaya don dai tabbatar wa. “Mama” ya bani amsa,sai kawai na kashe kiran.Haka na ci gaba da kallon Mamu na murƙususu,tun ina hawaye har ta kai da na yi ƙarfin halin tashi na fito.Mama Lantanar dai na gani a inda take tana gasa zuciya sai wani baƙin abu take ɗiga wa mai wari.Idona sun rufe , wannan yasa kawai ba tare da wani tunani ba na tunkare ta tare da zuwa na ƙwace tsinken hannunta na zaro zuciyar.Ta wani miƙe da sauri za ta karɓa kawai na tsira mata tsinken a hunnunta har sai da ya hudo ta bayansa,ta saki ihu yayin da ni kuma na je na ɗauko ruwa mai sanyi na zubawa zuciyar tare da ina mai nufar ɗaki a guje sai na samu Mamu tana wani jan numfashin sassauci.... Normal group 300 Vip group 600 Via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [11/06 17:41] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *ROMON HAƘURI* 🤍 MRS SADAUKI ✍️ FCWA ☀️ *Wannan labari ba ƙirƙira ba ce,labari ne da ya faru a gaske ina fatan za ku bibiye shi sau da ƙafa* *__________________________________________________* 10 Nan take na ga bacci ya ɗauke Mamu ,tausayinta na ji kawai sai na shiga yin kuka ga ni kuma da gasassar zuciya a hannuna wacce dukkan alamu suka nuna an yi aikin ne domin cutar mini da mahaifiya.A can tsakar gida na soma jin maganar Abbanmu,yadda muryarsa ke rawar tsoro na fahimci tuni ya samu labarin aika-aikar da na yi wa Mama Lantana amma dai ban fita ba sai ma zaune na yi ina tunanin yadda zan yi da zuciyar.Uncle Suhail ya faɗo mini da rai sai dai banda lambarsa dole dangin naƙi na kira Ubaidah,tana ɗagawa na fashe mata da kuka. “Mene ne kuma? ” ta tambaya. “Ki zo gida ina cikin tashin hankali Udah ,Mamu na shirin mutuwa saboda aikin da Mama ta yi da zuciyar akuyar nan” na faɗa ita kuma ba ta ce komai ba ta kashe,ina nan cikin halin da ya aure ni ta zo.Miƙa mata zuciyar na yi,kafin ta ce “tashi mu tafi” dama da hijabi a jikina haka na miƙe muka fito. Tsakar gidan babu kowa ,muna fita waje muka shiga motarta sai gidan Uncle Suhail ɗin.Yanzun ma Ubaidah ce ta yi masa bayani,ya karɓi zuciyar,yana karatu yana bubuɗe ta nan ne fa asalin tashin hankalin yake yadda can cikin zuciyar yayi ta ciro jariran allurai ƙananu sosai duk in ya cire ɗaya sai wani baƙin ruwa mai wari ya ɗiga a haka har ya kammala ya ɗebo ruwan randar nan ya wanke zuciyar ya ce zai fita ya rufe dukkan abin nan.Bayan ya dawo ya ce “ya kamata ku fallasa matar nan in ba haka ba ta'asar da sheɗancin da za ta yi a gaba sai ya fi wannan” Ubaidah ta dube ni na ce “ko na faɗa babu wanda zai yarda,Abbanmu ya zama mijin ta ce sai abin da ta shimfiɗa masa ta hau akai ne kawai yake yi.Yayana ma da Mamun ta haifa shi ma ya zama ɗan Mama Lantanar na kira shi a yau ina sanar da shi mahaifiyarmu ba ta da lafiya amma ya ce sai ya tambayi izinin Mamar kawai zai iya zuwa.Faɗa mini to,wane ne zan sanar da shi don tona mata asirin ? Babu ” Uncle Suhail ya furzar da huci kafin ya ce “to ki dage da addu'a domin ita kaɗai ke canza ƙaddara” da wannan muka fito daga gidansa. A ɓangaren Mama Lantana kuwa,cikin raɗaɗin azabar nan ta je ta shiga ɗakinta ta kira Abban yara ta sanar da shi.Babu jimawa ya zo kuwa,yadda ya ga tsinke a hannun Mama Lantana sai hankalinsa ya tashi ya soma tambayarta amma babu amsa sai asibiti da take cewa ya kai ta.Cikin adaidaita suka je, asibitin kuɗi ce wannan yasa dandanan aka yi mata aiki aka cire tsinken tare da yi mata allura aka kuma naɗe hannun da bandeji.A bisa hanyar dawowa gida Mama Lantana ke cewa “daga na ce don me za ta jawo mana ƙato har cikin gida inda ka ga mugun kallon da ta yi ta ma kama hannun saurayin suka shige ɗaki,abubuwan da kunnuwana suka jiye mini marasa daɗi yasa na je na leƙa saboda kar a ce don tana ƴar kishiyata ce,wallahi malam turmi da taɓarya na tarar da su .Haka na dawo jikina na yi mini rawa inda nake gasa nama,da yaƙe ƴar nan tantira ce shi ne a gaban idona ta zo ta cika bokiti za ta yi wanka,saurayin ne da ya fito na tare masa hanya na ce ba zai fita ba nan muka hau kokowa shi ne fa ta tsira mini tsinken nan a hannu amma da niyyarta idona da ya gansu ta so makantarwa” tun da ta fara magana zuciyar Abba ke tafasa yana jin kamar zai ƙone,wani abu da ya tokare masa zuciya shi ya hana shi yin magana sai mai ɗan sahun da ya ɗauko ne ya ce “ai Hajiya yaran yanzu sai addu'a haka ƴar maƙaucina ke yin wannan iskanci,yadda kika san ana layin waina haka za ki ga samari masu mota na zuwa wurinta,kuma a cikin motar fa take shiga ana yin hirar” “Ana dai yin iskanci,ita wannan ganin uwarta ba ta gidan ne shi ne dalili kawai ni kuma ba a bakin komai nake ba” Yadda Mama Lantana ke cacabkewa ita da mai adaidaita ita tana muzanta Suwaiba shi kuma ƴar maƙaucinsa saura ƙiris jinin Abba ya hau amma Allah ya tsare . ★ Sai wuraren magrib sannan muka iso gida,Ubaidah ta sauke ni tare da wucewa.Ina shirin shiga gida adaidaita ta tsaya a ƙofar gidanmu,Mama Lantana ta fito tana cewa “Abbansu ina ce ka gani da idanunka ? Dubi an sauke ta daga mota” “Daga gidan uban wa kike?” Abba ya fito yana mai tambayata,kasa cewa komai na yi saboda ƙarya ba tabi'ata ba ce kuma ba zan iya ce masa gidan Uncle Suhail ba. "Wane ne wancan da ya ajiye ki a mota?” ya sake tambayata,hankali tashe na ce “Abba Ubaid...” marin da ya kifa mini shi ya hana ni ƙarasawa,ina jin lokacin da mai adaidaitar ke cewa “innalillahi Ubaidu? Wane ne shi?” Mama Lantana ta basa amsa da “kwartonta ne” Ganin mutane sun fara tsayawa kallo sai na nufi gida a guje ,Abba ya biyo ni ya ci gaba da dukana yana cewa “uban wane ne shi Ubaidun ? Aure aka ɗaura muku da shi? Karuwar gida kika zama ban sani ba?” yana yi mini tambayoyin ne yana dukana,Mama Lantana da mutumin da ban san ya suke da shi ba suna ƙara hura wutar rikicin. Tun ina iya tsayuwa har na faɗi,irin dukan da Abba yayi mini ko kama ni yayi da namijin da idonsa to sai haka. “Haba malam kana tsaye kana kallo ba za ka riƙe shi ba?” wani ladani ne na unguwarmu ya furta hakan yana mai riƙe Abba da yake ta yin huci.Ga gidanmu tuni mutane sun fara shigowa. Mama Lantana na ganin haka don muzanta Suwaiba sai buɗe baki ta yi za ta maimaita abin da ta shirya na sharri na cewa ta kama ta da namiji. “Malam Idi don ba ka san me ta yi ba wallahi....” “In kika furta ko da kalmar A ce ban yafe miki ba,kuma wallahi akan aurenki” Abba ya furta yana jin ƙunci na luluɓe shi,tsit kake ji Mama Lantana an yi shiru sanin igiya ɗaya ta rage mata a cikin auren. Malam idi ne duk ya fitar da kowa sannan ya turo ƙofa,sai kuma a lokacin Mamu ta fito tana tambayar abin da ke faruwa. Cikin zafin rai Abba ya ce “ki tambayi ƴarki ga ta nan” Mamu ta dube ni ta ce “Suwaiba lafiya?” ban bata amsa ba sai yunƙurawa da na yi dakyar na tashi zaune.Da rairafe na isa ɗakinmu,ina jin yadda Mama Lantana ke ta ƙoƙarin dole sai ta sanar da Mamu ɗin amma ta kasa ƙila tsoron furucin Abba ɗin. Wuri guda na samu na cure,a haka Mamu ta shigo ta yi sallar magrib bayan ta gama ta tsura mini idanu.Wasu hawaye masu ɗumi suka sake keto idanuna suka zuba kan kumatuna,murya na ɗan rawa na ce “Mamu ban yi komai ba,Ubaidah ce ta zo ta sauke ni a mota amma dole Mama Lantana tana son juya maganar wai namiji ne” “Shi kuma wanda kika kawo ɗazu har cikin ɗakin nan?” Abba ya jefo mini tambayar yana mai zuwa bakin ƙofa yayi tsaye.Cikin sauri na ce masa “wallahi Abba likita ne ya zo ne ya duba ƙafata da na ƙone” “Likitan mata ko? Wanda bai duba mace sai kowa ya watse” wannan karon Mama Lantana ce ta faɗa daga nan kusan window. Mamu ta dubi Abba ta ce “ni har yanzu ban fahimci meke faruwa ba” “Za ki fahimta in na ɗaura mata aure aka kai ta can ƙauye” Abban ya faɗa cikin zafin rai yana ida shigowa. “Aure kuma? Karatun nata fa?” “Ai ta san da karatun ta soma kula Mazan banza,tun da auren take so ai gara na yi mata shi kafin ta jajiɓo mini abin kunya” “A'a wallahi ba zan bari ka yi wa ƴata aure ba,sai ta gama karatunta tun da tana da ilimi” Mamu ta faɗa tana mai tashi tsaye,Mama Lantana ta yi wuf ta shigo tana cewa “kin ga ta'asar da ta yi mini ita da tantirin saurayinta tsinke suka tsira mini a hannu har sai da ya kusa katse mini jijiya ” Mamu ta ce “duk ina a ina hakan ta faru?” Wani kallo Mama Lantana ta yi mata kafin ta ce “wato Zainaba ƙaryata ni kike ƙoƙarin yin alhalin da idona na kama su suna masha'a? Yanzu ai kai gabanka shi Ubaidun da ta ce ya sauke ta a mota bayan sun dawo daga yawon ta zubar” Wani irin kallo Mamu ta yi mini wanda ya saka zuciyata bugawa.Kai na shiga girgizawa,yayin da ita kuma Mama Lantana ke ta ƙarawa abin gishiri har da cewa ta ga lokacin da ya ɗora bakinsa kan nawa.Ido kawai Mamu ta rumtse yana saurare kafin can ta ce “ya isa haka Lantana,ya isa ban son jin komai” Mama Lantana ta kalle ni tsakiyar ido kafin ta fice,Abba ya ce “yanzu ai kin ji abin da ta yi ko? To don haka ki fara shirin miƙa ta gidan miji“ yana gama faɗar haka ya fice.Mamu ma nan ta bar ni ta wuce can uwar ɗaka,duniyar ce na ji ta tsaya mini cak na rasa meke yi mini daɗi. Har aka kira sallar isha'i ina nan zaune,har sai da dare yayi sosai sannan na je na cika bokiti da ruwa na yi wanka na zo na yi sallolina.Wayata kuwa kashe ta na yi,sai na haye kan kujera ina sauraren yadda cikina ke ƙugin yunwa amma ba shi ne damuwata ba .Mamu nake son gani a wane hali take? Wane hukunci ta yanke? Amma na kasa tafiya na gani,cikin wannan yanayi ne bacci ɓarawo ya ɗauke ni.Nan ne fa na soma yin mafarki marar daɗi,ga ni nan ina gudu shanu na bin bayana suna son cutar da ni.Duk gidan da na zo zan fake sai kuma na gansa a rufe,a ƙarshe dai kan bishiya na haye sai dai nan ma ban tsira ba baƙin kare ne ya zo yana haushi shi ma yana son ya cije ni sai girgizar bishiyar yake wacce a ƙarshe ta karye ina shirin faɗowa na tashi daga baccin ina buɗe idanu kuma Mamu na gani a tsaye ta saka ni a gaba tana kallo. Na tashi na zauna ina mai kallonta,muna haɗa ido ta tafi ta shige ɗaki.Wani irin ciwo gaɓaina suke yi,ga kuma zazzaɓi wannan yasa na jawo ledar ɗazu na ɗauko jus da magani na sha.Ban ƙara komawa bacci ba sai bayan na yi sallar asuba ,muryar da na ji sama-sama ce yasa na yi saurin tashi. Ammy ce ita da Ubaidah,gaishe ta na yi ta amsa cikin sakin fuska sai na dubi Udah ta ɗan sakar mini murmushi kafin ta ce “ya jikin?” “Da sauƙi” na amsa,Mamu ta ce “tashi ki je ki yi wanka ga ruwa can na tafasa” cike da mamakin canzawar da ta yi na dube ta sai na ga kuwa fuskarta babu alamun damuwa.Haka na miƙe dakyar,Ubaidah ta take mini baya ita ce ta juye ruwan a bokiti ta ƙara mini da na pampo ta kai mini banɗaki.Soso da sabulu kawai na ɗauka na je na shiga,yayin da ita kuma ta tsaya bakin ƙofa har sai da na kammala na fito muka shiga tare nan muka tarar da Ammy na cewa “wallahi kamar yadda na faɗa miki wata mata ce bararoji da na yi wa aiki ta shaida mini haka,yanzu kuma kin ga maganin da ta bani ta ce a turara shi nan gidan da kuma can gidanmu” “Suwaiba samo mana garwashi” cewar Mamu,haka na fita na ciko kasko da wuta.Ammy ta zuba maganin tana cewa mu fita da shi waje,haka kuwa aka yi Ubaidah na yin murmushi ta ce “in sha Allah komai ya zo ƙarshe,za su ji kuma za su gani ” Daga can ɗaki muka soma jiyo tarin Mama Lantana,can kuma sai ga shi ta fito tana masifa. “Tsafi kuma aka soma yi a cikin gidanmu?” ta faɗa tana taɓa hannuwa,ba mu kula ta ba haka muka ci gaba da yin hira hankali kwance.Sai muka ga ta koma ɗaki kafin kuma ta fito mayafi a kafaɗa ta fice. “Ya Ubaid ya ce na gaishe ki da jiki” ta furta tana yi mini wani kallo sai na kasa cewa komai,ta ce “amma kin san kuna son junanku ko?” “Me yasa yau ba ki je makaranta ba?” na tambaye ta don kawar da waccan maganar.Ta ɗan yamutsa fuska kafin ta ce “na san ba za ki je,to ni in na tafi me zan yi a can?” Fitowar Ammy yasa duk muka yi shiru,sallama suka yi mana suka tafi .Duk a tunanina shikenan mun shirya ni da Mamu amma ko motarsu ba ta gusa daga ƙofar gidanmu ba Mamu ta canza fuska,duk sai na ji wani iri.Haka ta shige ɗaki ta bar ni nan tsaye,a sanyaye na je ni ma na shiga na zauna kan kujera ina kallon tarin magungunan da ke gabanta. “Ki kira mini Sulaimanu” ta faɗa ba tare da ta dube ni ba,haka na ɗauko waya na kira shi.Amma har ta tsinke bai ɗaga ba, sai a kira na biyu ne ya ɗauka da sauri na miƙawa Mamu. Ina gefe ina sauraren yadda take amsa gaisuwar da yake yi masa kafin ta ce “an tsayar da ranar ɗaurin aurenku nan da kwana uku,wato juma'ar nan.Zan aiko maka da maganin da za ka dinga yin wanka da kuma wanda za ka sha.Babu buƙatar sai ka zo don dai iya ɗaurin auren za a yi,bikin kuma sai nan da wata uku lokacin Daddynsu Ubaidar ya dawo daga Ingila ” Wani irin sanyi ne ya ratsa mini zuciya,ga dai bikin zuwa amma babu zanen ɗaurawa.Ina son fitar da tsantsar murnata amma babu hali,ban ji shi me Sulaimanun ya ce ba amma sai na ji Mamu na cewa “kar ka faɗawa kowa wannan maganar ta zama sirri,saboda ka ga yadda lamarin auren ya kasance ” Daga haka suka yi sallama ta kashe tana jan ajiyar zuciya,ta dube ni tana mai cewa “da zarar an gama zancen auren nan in sha Allah sai ki haɗa kayanki ki koma can ƙauye wurin Yadikko,in komai ya lafa sai ki dawo.Saboda muddin Abbanku na ganinki ba zai fasa aura miki duk wanda ya rakito ba,rayuwa dai taki ce kin kuma zaɓi wacce kike so” “Mamu yanzu ke kin yarda zan iya yin abin da ba daidai ba?” na faɗa ina hawaye. “Eh to ta ya ba zan yarda ba alhalin Lantana ta ce ta gani da idonta,inda ma a ce Abbanku ne da sai na ƙaryata na ce ko ƙiyayyar da yake yi mini ce ta shafe ki” A abin da na fahimta duk duniyar nan babu wacce Mamu ta bai wa dukkan yardarta irin Mama Lantana, wannan yasa ban ma ba kaina wahala ba wurin son wanke kaina daga zargin da aka yi mini. Daga can tsakar gida aka rangaɗa sallama,gabana ya faɗi don kuwa na gane wacce ke yin sallamar.Muryar Kaka ce mahaifiyar Mama Lantana,matar da tsabar mugunta inuwarta ma ba kowane lokaci take binta ba. Jikin Mamu har wani rawa yake wurin amsa sallamar kafin ta miƙe ta fita,ta window na leƙa nan na hango Mamu ta zube gwiwa har ƙasa tana gaishe da Kaka,ga Hassana da Hussaina a tsaye gefenta su ko gaishe ta ba su yi ba. Bayan sun gama gaisawar ne su suka wuce ɗakin Mama Lantana ita kuma ta dawo namu.Wayata na jawo na kunna tare da turawa Ubaidah saƙon congratulations,sai ta turo mini emoji na alamun jin kunya hakan ya wanzar mini da murmushi. Mamu ta karɓe wayar daga hannuna tana mai cewa “mene ne ya faɗa miki kike murmushi? To ba zan sake baki wayar nan ba sai ranar da za ki je gun Yadikko” ƙuuu ta shige uwar ɗaka.Ni kam abin mamaki ma ya bani,fita na yi can ƙofar gida na yi zaune. Babu jimawa kuwa sai ga Mama Lantana,mugun kallo ta yi mini tare da shigewa cikin gida.Ni kuwa sanyi itaciyar da ke kaɗawa shi yayi mini mugun daɗi,haka na yi zamana fiye da awa uku kafin na tashi na shiga gida.A zaune na tarar da su dukkansu har da Mamu suna cin abinci,ga uban nama cike da faranti.A gaban idona Mamu ta yi loma da ƙatuwar tsoka,buta na ɗauka na shiga banɗaki ina jin Mama Lantana na ce “ni kam Zainaba me surukarmu ta zo yi yau tun da safe? Allah yasa dai ba zancen Suwaiba na bin maza kika yi mata ba shi ne ta kasa haƙuri ta zo?” Ido na rumtse,amma takaici bai ida rufe ni ba sai da na ji Mamu ta saki baki tana cewa “dama zancen auren Sulaimanu ne ta ce tun da ta ga abin ya ƙi ci ya ƙi cinye wa ...” da wani irin sauri na fito na ce “Mamuuu?” duk sai suka juyo suna kallona. “Me ne?” Mamun ta tambaye ni,na ce “zo ki gani” “Me zan gani gani a banɗakin kuma?” Mamu tambaya rai ɓace,inda na yi farin ciki shi ne zuwan Goggo Saude wato ƴar uwar Mamu ce nan garin take aure ita ma.Murnar ganinta ya saka Mamu farin ciki tana mai cire hannunta cikin abincin ta miƙe tana cewa "wuce mana” Wata sanyayyar ajiyar zuciya na sauke,Mama Lantana ita da Kaka kamar za su cinye ni da ido,wani abin mamaki ma har da ƴaƴan. Banza na yi da su na wuce can cikin shamaki na yi zaune tare da cin alwashin duk wuya ba zan bari Mamu ta fallasa zancen auren Yaya Sulaimanu ba ne gun maƙiyanta na ɓoye.Wannan yasa bayan fitowar Goggo Saude ma ban bari sun keɓe da ita ba,tamkar inuwa haka nake bin Mamu sam ban damu da mugun kallon da take yi mini ba.A haka har dare yayi,nan fa na ga jarabawa yadda ciwon ciki ya tisa Mamu a gaba.Allah ya ceto ni na yi saurin ɗauko haska, wannan yasa na ɗauko nonon raƙumin da Uncle Suhail ya bani na miƙa mata ina cewa “ga magani ki sha Mamu ” karɓa ta yi saboda uwar wuyar da take sha yasa ta mayar da gushinta gefe.Duk da ba ta wani sha dayawa ba amma ta samu sassauci kafin kuma wani lokaci ta fita a guje can tsakar gida ta soma kelaya amai . Fita na yi da sauri na tsaya kusa da ita, Abba da shigowarsa kenan ya hasko fitilar hannunsa yana mai cewa “kin ɗauko mana abin kunya ko?” wato abin da na fahimta yayi dubin ni ce ke yin aman,ita kuwa kwalba uwar sharri har ta fito . “Abbansu ƙara hasko mini nan na gani mene ne nake gani?” Mamu ta faɗa,Abba ya haska ƙasa sai ga shi gudan tulun tsutsotsi na ta yawo a ƙasa,wani irin tsoro na ji ya kama ni yayin da Abba ke cewa “innalillahi wa'inna ileyhi raji'un! Zainaba aman tsutsotsi ne kike yi? Me kika ci haka?” Mama Lantana na kalla wacce jikinta yayi sanyi,ni kuwa hamdala na yi kafin na ɗebo ruwa a buta na miƙa wa Mamu ta wanke bakinta da jikinta.Ƙasa na ɗebo na sa abin kwasar shara na kwashe aman na kai can waje na zubar.Ko da na dawo tuni kowa ya kama gabansa,da na shiga ɗaki ma tuni Mamu ta samu bacci. Washegari ya kama ranar Laraba ,saura kwana biyu ɗaurin aurensu yaya Sulaimanu.Tun safe Mama Lantana ta zo duba Mamu tare da bugun cikinta sai so take yi ta tambaye ta amma na ƙi barin ta ji ba'asi don kuwa hatta banɗaki in Mamu za ta je haka nake bin bayanta.Hakan ya ci gaba da faruwa har daren juma'a wanda sam Mamu ta kasa yin bacci,cikin tsakiyar dare na ji ta buɗe ɗaki ta fita.Ta window na leƙa,sai na hango Mama Lantana zaune a kan turmi kamar mai jiran wani abu.Babu shiri na fito sai na laɓe ban ƙarasa wurinsu ba. “Dama gobe ne ake son ɗaura auren Sulaimanu ina ta son faɗa miki ban samu hali ba” na ji Mamu ta faɗa tana daga tsaye a bayan Mama Lantana,tana faɗa kuma ta juyo ta koma ɗaki yayin da kuma na ga Mama Lantana ta kafe bayan Mamu da idanunta irin na mage can kuma ta tashi ta nufi ɓangarenta.Sam ban koma ɗaki ba sai da na ɗauro alwala na shiga na soma jera sallah ,yau a tsaye ma nake yi don addu'ar ta yi saurin shiga duk da kuwa ina jin zafi a ƙafata. A can ɓangaren Mama Lantana kuwa kamar za ta ƙone haka take ji,dakyar ta iya barin gari ya waye sannan ta je wurin Malam Yawale. Tana shaida masa zancen auren shi ma yayi matuƙar mamaki sai ya soma yin bincike,nan take zufa ta karyo masa ya dubi Mama Lantana ya ce “sai dai fa ki yi haƙuri,akwai wata addu'a da ta yi wa aljanun da ke kula da wannan lamarin auren ƙunar baƙin wake.Sam ban ma lura ba,don kusan kwana uku kenan da komai ya caɓe” “Addu'a kuma malam? Dama akwai wata addu'a da ta fi ta ƙarfin ta malamai?” Mama Lantana ta faɗa cikin damuwa. Malam Yawale ya ce “addu'ar da za a yi wa mutum ba tare da saninsa ba tana da matuƙar tasiri, musamman ma in ta fito daga zuciyar mai tsarki” “Wato har yanzu Mamu na yi wa Sulaimanu addu'a ita ga uwa?” “Wannan lamari ba daga ɓangaren Sulaimanu yake ba,addu'a ce daga Suwaiba in ba ki manta ba tun farkon zuwanki a nan na shaida miki tana da taurari masu kyau sannan imaninta a tsaye yake daram babu wata tangarɗa wannan dalilin ne ma yasa aiki a kanta yake da matuƙar wahala kina dai ganin hatta jinnun da aka tura mata na tsawon shekaru shidda har yanzu babu wani tasiri da suke yi a kanta.Yanzu ma a binciken da na yi kamar tana tsaye tsayin daka tana faɗa da duk mai son hana auren nan ta hanyar yin addu'a ” Wani ɗan ƙaramin ihu Mama Lantana ta yi kafin ta ce “ina ga kashe Suwaiba kawai zan yi don na huta da baƙin cikinta,kana ji yanzu ka ƙara loda mata wani sharrin ina so a yawon bin mazan ta yi ciki ta yadda babu wanda zai ganinsa ballantana a zubar da shi sai dai kawai mu ji kukan jariri” Malam Yawale ya dubi Mama Lantana da kyau kafin ya ce “wai ni kam wane laifi ne Suwaibar nan ta yi miki? Na ga yadda kika tsane ta ko ita Zainabar da kike kishi da ita albarka” “Ina ruwanka ? Kai dai aiki na saka ka yi na biya ka,wallahi ko zan yi yawo tsirara sai na tozarta Suwaiba a idon duniya” Bai ƙara ce mata komai ba,sai nonon akuya da ya ɗauko yayi tsare-tsarensa ya ɗauko rariyar nan da yayi aiki da ita ranar nan ya tace nonon a wata kwalba kafin ya ce “wannan ki zubar da shi a watsar da shi a ƙofar gida,yadda ya zube haka duk wani mutumcinta zai zube,wannan kuma ki jefa a masai ” jikinta har rawa yake yi ta karɓa,da za ta fita ya ce “wannan aikin shi ne top wurin son lalatar da rayuwar ƴa mace,domin a gaban kowa ma za ta iya yin tarayya da namiji haka kuma za ta iya buɗa baki ma ta yi zantukan banza don fallasa wa duniya ita karuwa ce” Wani sanyi ya ratsa zuciyar Mama Lantana,tana zuwa gida kuwa tun a waje ta watsar da nonon duk ya faltsa ko ina,da ta shiga gida kuma ta cilla ɗaya abin a masai suka haɗe da tun wancan na farko. ★Bayan sallar juma'a,duban jama'a suka shaida auren Sulaimanu Abdullahi tare da amaryarsa Ubaidah Yusuf.Ɗaurin aure ne da hatta Abba bai sani ba,ya dai ga wani ɗan uwansa da ke can Katsina ya ziyarce shi sannan kuma shi ya bada shawarar su je masjid ɗin.Duk da wani ɓangare yayi murna amma hakan bai hana shi yin masifa ba. ★Suwaiba Tun da aka tafi jama'a hankalina ya ƙi kwanciya,wanka na shiga domin yau na ɗauki alwashi sai na tafi gidansu Ubaidah tun da banda waya a hannuna.Ina fitowa da Ya Ubaid na soma cin karo yana tsaye a tsakar gidan,Allah yayi sa'a ina sanye da hijabi. Gaishe shi na yi ya amsa yana mai ɗan kawar da kai,da sauri na wuce ciki a gaggauce nake shirin sai a lokacin kuma Mamu ta gama sallah tare da fita tana amsa sallamar da ni dai lokacin da ina wanka ban ma ji ba.Har ɗaki ta yi masa iso,a lokacin kuma tuni na shimfiɗa dadduma sai na soma yin sallah amma a hakan ina jin yadda yake yi mata barka da kuma fatan alkhairi a ƙarshe kuma ya ce ya zo ya tafi da ni ne Ubaidah ke son haka.Ina gama sallah ya fita bayan yayi mini wani kallo,turare na fesa sai kuma na yi zaune. “Ki je yana jiranki” cewar Mamu, har zan tafi sai kuma ta miƙo mini wayarta ta ce na kira mata Sulaimanu.Yadda na ga tana farin ciki sai na ji wani sanyi a raina,ina jin ya ɗauki kiran na fita.Zaune ciki mota na same shi,ya buɗe mini gidan gaba na shiga na zauna tare da gaishe shi,bai amsa ba sai ce mini da yayi “na yi kewarki ” wani irin dummm na ji kunnuwana sun yi sai na ji kamar dai ni ce ban ji daidai ba,amma abin da ya ci gaba da cewa yasa na yarda eh hakan ne ya furta. “Har lambarki na karɓa gun Ubaidah sai dai ba ta shiga” Ina shirin yin magana sai ganin Abba na yi ya shigo layin,idonsa kuwa na kan motar. “Suwaah?” ya kira sunan da shi ne ya ƙirƙiro shi,na amsa da “umhum?” ba tare da na juyo ba,key ya yi wa motar muka bar wurin daidai lokacin kuma shi Abba ya isa a ƙofar gidan.Na ja wani dogon numfashi saboda ko ba komai bai zubar mini da mutumci ba a gaban Ya Ubaid. Sai da na ga mun hau titi da kyau amma Abba bai biyo mu ba sannan kawai na saki jikina.Na ɗan waigo na dube shi sai na ga ni ɗin yake kallo,na saki ɗan murmushi tare da sunne kai.Bai ce komai ba har muka isa can gidan nasu wanda ya cika da jama'a saɓanin namu da babu wanda Mamu ta sanarwa.Cikin zumuɗin son ganin Udah na ɓalle murfi na fita,ina shiga kuma direct a can ɗakinta na yi tsinke.Ba ta yi shiri ba,tana dai zaune danginta duk sun kewaye ta. Guɗa na yi tare da zuwa na faɗa jikinta,a tare muka saki kuka muna rungume juna gam.Tsawon lokaci muna a haka kafin na janye daga jikinta,na ja hancinta ina mai ce “my Udah ta zama amarya” Ta turo baki gaba,na ce “ki je ki yi wanka ki yi shiri ” “Na ƙi! Sai yanzu za ki zo?” ta faɗa tare da kama hannuna zuwa can bedroom,“ki zaɓar mini kayan da zan saka zan shiga wanka na fito” ta faɗa tana nuna mini tulin kayan amare da ke kan gadon,haka na shiga duba su ko da take fitowa tuni na fitar da waɗanda za ta saka ɗin.Ni na taimaka mata ta shirya,sannan ta miƙo mini wanda zan saka su ɗin size ɗina.Na ga jikina na cire na saka sabbin,hatta sarƙa da ɗan kunne duk nata na saka. Muna fitowa aka soma yi mata hotuna kafin mu sauka ƙasa,inda mai hoton da aka kira ya yi mana iri-iri.Har da Ya Ubaid ya shigo a hoton ,inda na gode wa Allah da har aka gama shagalin bikin anty Hamida ba ta zo ba.Sai ana dab magarib na baro gidan,cikin adaidaita na koma. Ina shiga gidanmu Abba ya ce “daga gidan uban wa kike? Wato ni za ki nunawa ke kin isa kin tunbatsa a gabana ƙato ya zo ya ɗauke ki?” tsaye na yi jikina na rawa . Mamu ta fito tana kallona,yayin da Mama Lantana ke cewa “ƙarshen raini ya kai a ɗaura auren ɗanka amma ba ka da labari? Amma ai gara dai auren kan yawon ta zubar da take yi ,ni kamar ma ciki ne da ita ya kamata dai ka kai ta asibiti a duba mana ita kar ta kwaso mana abin kunya” Tamkar ta zuga Abba kuwa haka ya soma yin masifa yana zagina ni da Mamu,a ƙarshe ya ce wa Mama Lantana ta duba ni tun da dama ta saba yin ungozumanci. “Ban gane ta duba ta ba?” Mamu ta tambaya cikin wani irin yanayi. “In kika ƙara yin magana Zainaba akan aurenki,ke Lantana ja ta ki duba mini ita” Abba ya faɗa,Mama Lantana ta karɓi fitilar hannun Abba tana mai kallona.Daidai nan free page ya ida,mai son ci gaba group biyu ne. Normal group 300:Posting biyar a sati Vip group 600: posting goma a sati. Via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 NB: Daga lokacin da ya zama complete 1k ne farashinsa. [12/06 12:37] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐 """"""""""""""""""""""" LoVe aNd HoRrOr StOry☠️ ```MRS SADAUKI```💫✍️ FCRW☀️ ____________________________________________ 01 Cikin duhun dusar ƙanƙara wata mata mai ƙusumbi ke ta ɗangala sanda cikin sauri har ta isa wani ƙaton kogo mai cike da hayaƙi kamar an yi gobara.Tana shiga kogon ya fara rawa yana fitar da wani sauti,baƙin bargon da ta luluɓe kanta da shi ta sauke kan kafaɗunta hakan ya bayyanar da shafafar fuskarta wacce babu ido,babu tsinin hanci sai iya baki kawai.Bakinta ta buɗe tana yin wani gurnani mai fitar da magana cikin wani yare na ƙarnin baya “ uleja naho kajulu ramhakaya fyayal!” cak kogon ya tsaya da rawar da yake tare da ɗaukar wani irin shiru kamar mutuwa ta ratsa,babu jimawa kuwa wasu fararen halittu suka fara shawagi ko ta ina. Da sauri ta zube kan gwiwanta tana mai buga gundulalun tafukan hannunta a ƙasa tana mai daɗa furzo wasu kalaman. “Za ki iya gabatar da abin da ke tafe da ke” wata murya ta ratso iska ta bata umarni. “Naomi!” ta furta cikin rawar murya. “Alƙaluman doka sun riga da sun ƙafe babu wani canji da za mu iya yi miki” aka bata amsa. “Ita ɗin yarinya ce ƙarama ƙwaƙwalwarta ba za ta iya ɗaukar wannan hatsabibin tashin hankali ba” tana gama rufe bakinta wata tukunyar ƙasa ta faɗo a gabanta ,“ki bata waɗannan ruwan ta sha daga nan komai zai tafi kan tsari” Tukunyar ta ɗauka kafin ta gyara luluɓinta sai kuma ta fito,bai wuce tako uku da ta yi ba sai ta furta wani furuci wanda ya haifar da wata hatsabibiyar guguwa tashi ta zo ta zagaye ta tana fitar da wani iska,sannu a hankali guguwar ke daɗa yin sama da ita a haka ta ɓace ɓat kamar walƙiya ba ta bayyana ko ina ba sai a ƙofar gidanta. Ina zaune ina ƙulla garin magunguna na ji motsi,da sauri na ɗago kai sai na hangi Maa na daidaita rufin ƙyauren gidanmu.Murmushi ne ya wanzu a fuskata ba tare da na ce mata komai ba na ci gaba da kallonta har ta ƙaraso ta zauna kusa da ni tana mai miƙo mini tukunyar hannunta.Na karɓa,sanyin haɗi da wani shock suka ratsa ni yayin da na ji kwaɗayin shan ruwan ciki.Baki na kafa na soma shan abin da ya kasance a ciki don sai bakina ne kawai ya iya tantance mini kallon kitse na yi wa rogo don kuwa ba zallar ruwa ne ba. Ina ajiye tukunyar sai na ji tamkar wacce aka yi wa wankin ƙwaƙwalwa,wasu abubuwa da suka keɓancin mahaifiyata nake son sani. “Maa me yasa ake kiranki da mayya?” “Saboda ababen bauta sun mallaka mini baiwar da ta keɓanta da ta sauran mutane” “Kina nufin makantar ido?” “Eh! ” “Amma ai kina gani duk da babu gurbin ido a fuskarki ” “Naomi??” muryar ƙawata ta katse zaren tambayoyin da nake yi wa mahaifiyata wacce ta kasance jigona,bango abin jiginata. Miƙewa na yi da sauri ina ƙara gyara zaman fatar dabba wacce ta suturta tsaraicina ina mai duben Debora wacce ke sanye da wani tsohon bargo duk ta yane jikinta da shi.Murmushi ta sakar mini kafin ta yi mini alama da hannu,Maa na duba ina mai cewa “zan yi wa Debora rakiya ne” “To kar ki jima saboda lokacin zuwa farauta ya kusa” Maa ta bani amsa,ba tare da na ce komai ba na kama hannun Debora muka fito ƙofar gidanmu wanda ya kasance na kara. “Ya meke labari?” na tambaye ta . Kamar munafuka ta yi ƙasa da murya ta ce “zo mu je na nuna miki wani abu” sai kuma ta fara ɗan gudu-gudu tana nufar bayan gari yayin da ni kuma nake take mata baya har muka isa bakin Teku .Da wani irin kallo na bi ta da shi ina mai cewa "me kuma za mu yi a nan?” Da hannu ta yi mini nuni da can tsakiyar ruwa,sai dai sam ban ga abin da take son nuna mini ɗin ba.Lura da hakan yasa ta ce “yi kamar za ki rufe idonki” hakan na yi na lumshe manyan idona kafin na ɗan buɗe su a hankali sai a lokacin na ga wani abin mamaki wanda tunani da hankali ba za su ɗauka ba.Dogon tsani ne a cikin ruwan tare da shata wata doguwar hanya da alamu za ta ɓulle a wani wurin.Umarnin zuciyata ƙafafuwana suka bi ba tare da na shirya hakan ba na ji sanyin ruwa ya ratsa ni.A hankali nake tafiya har na isa kan tsanin na fara taka matakalansa sai dai ban fi tako uku ba na ji kamar an tunkuɗo ni sai ganina na yi a wani wajen na daban ko kuma na ce wata duniyar wacce ta sha banban da wacce na taso na tsinci kaina a cikinta. Wasu halittu ne masu irin siffata sai dai yanayin launin fatarsu da kuma shigarsu ya sha banban da irin ta duniyarmu.A karon farko da na ji tsoro,don ban taɓa ganin irinsu ba .Ƙafata ta hagu na ɗan mayar a baya ina kallon yadda wani mutum ke musayar wuta shi da maƙarabansa,ina daf da na koma cikin ruwa muka yi ido huɗu da shi hakan ya haifar mini da matsanancin faɗuwar gaba tare kuma da rikicewar tunani.Mun shagala da kallon juna ,ƙarar wani abu da ban san me ake kiransa ba ya dawo da ni hayyacina.Sai da na yi dogon nazari sannan na fahimci cewa ta cikin ƙirjinsa ne aka halba masa abar kashe mutane.Faɗuwa yayi ƙasa,wanda hakan ya jawo hankalin tawagarsa kusan su duka na ji sun ce “yalaɓaiii?” kafin su yo kansa,ɗaya daga cikinsu ne ya zube ƙasa tare da ɗora kansa kan cinyarsa yana mai cewa “Naslam?” cikin tashin hankali yake kamar yadda fuskokin sauran suka bayyana. Abokan adawarsu ne suka fara yi musu sarƙa suna gargaɗarsu da su miƙa musu wannan mutumin kawai suke buƙata in kuma sun ƙi za su kashe su duka su tafi da shi. “Rayukanmu fansa ne akan shugabanmu babu gudu babu ja da baya don haka dakaru ku juya ku fuskance su” shi ne abin da ya faɗa yana mai shimfiɗe Naslam ɗin. A wannan gaɓar ce na ga wani al'amari mai shige da irin rayuwarmu ta can duniyar,yadda su mutanen da ke neman ran Naslam duk suka wani zazzalo harshe waje suna sarrafa shi,kafin ƙyaftawar ido sai gawarwaki nake gani suna faɗuwa. Idona na ji suna yi mini ƙaiƙayi ,babu jimawa suka furzo da wani hatsabibin haske wanda ya tarwatsa taron Mayun duk suka faɗi babu rai sai ɗaiɗaiku ne suka gudu. “Naomiiii?” na ji muryar Debora tana kirana daga ta can ɓangare,kamar kifi haka na faɗa ruwa na koma duniyarmu.Ko da na fito daga cikin ruwa jama'ar gari na tarar duk sun cika wurin suna jiran fitowata.Ko kaɗan babu wani damshi ruwa a jikina a bushe nake ƙamas,sai dai a akwai banbanci tsakanin lokacin da na shiga da kuma yanzu da na fito.Kaf illahirin jikina ya rine yayi baƙi yayin da kuma wani abu da nake tunanin ƙusumbi ne ya bayyana a bayana.Fuskokin wasu cike da mamaki yayin da wasu kuma na hango tsoro da hassada a tattare a ciki. “Naomi me kike yi ƙasan ruwa kusan kwana biyu ba ki fito ba?” ƙawata Debora ce ta zo gare ni tare da tambayata. “Kwana biyu ?” na maimaita yayin da kuma cike da mamaki,ɗaya daga cikin tsofin garin ta matso tana mai nuna ni da yatsa tana mai cewa “dama tun ranar da aka haife ki na hango ajalin mahaifiyarki a tattare da ke saboda kin tabbata butulu ki rasa wacce za ki kashe sai wacce ta kawo ki duniya” sai kuma ta juya ta fuskanci mutanen gari tana mai cewa “kuna ta tambayar wa ya kashe Maa to ƴarta ce” Normal mutane ne kawai suka tsorata da furucinta yayin da su kuma dangina masu ido uku suka rufo kaina suna mai cewa “ita ma a kashe ta” sai dai ko kusa da ni ban bari sun ƙaraso ba na yi wani furuci duk suka ƙame ƙyam a wuri guda kamar wasu bishiyoyi. Magana na soma yi sai dai abin mamaki ba muryata ba ce ke fita,ta mahaifiyata ce.Gargaɗi ne mai ban tsoro haɗi da bushara ga waɗanda suka yarda suka miƙa wuya a bisa sabuwar dokar da na shimfiɗa musu.Kamar yadda ake rusunawa sarki haka duk suka zube suna jinjina mini haɗi da gaishe ni,ƙawata Debora ce kawai a tsaye tana wani mayen murmushi mai fitar da tsantsar farin ciki. Hannunta na kama na ratsa ɗimbin jama'ar muka wuce,har muka isa gidanmu ni da ita babu wanda ya cewa wani kanzil.A ɗaki na tarar da gawar Maa a kwance tuni ta fara ruɓewa tsutsotsi na shige da fice ta bakinta.A lokacin ne na ji wata murya daga can cikin ruhina tana bani mafita da shawari,yayin da ni kuma na yi tako ɗaya na aiwatar da abin da na ji.Hannuna na ɗora a goshin Maa na soma yin wani furuci wanda ban koya ba,kawai zuwar mini yayi.Babu jimawa ta soma bajewa tana komawa hayaƙi a haka har ta baje gaba ɗaya sai sautin muryarta da ya soma yi mini bushara “ ina tare da ke a duk inda za ki kasance ƴata Naomi kar ki yi baƙin cikin rabuwarmu wannan shi ne matakin nasararki,hidimar da za ki yi kuma na san mahaifinki zai yi alfahari da ke.Zan tafi na koma asalina,a duk lokacin da kika yi kewata ki je magudanar ruwa ki cilla dutsen karlis zan jiyo sautin kiranki” tana gama faɗar haka aka kece da ruwa mai bala'in ƙarfi wanda rufin ɗakinmu bai iya tare shi ba.Na yi saurin lumshe idona ina jin sabuwar halittata na yi mini wani irin motsi haɗi da ƙara girma wanda silar haka na ji kafaɗata ta ƙara nauyi hakan ya haifar mini da ɗan rusunawa kamar dai yadda mai ƙusumbi ke yi. An ɗauki lokaci kafin ruwan ya tsaya cak ,sai a lokacin kuma na tsinci muryar Debora na cewa “haƙiƙa kin kasance mai babban rabo ƙawata,ina mai sanar da ke cewa nan ba da jimawa ba amon mulkinki zai ƙetare duniyarmu ta ruwa ya tsallaka duniyar turɓaya ” Sai da na haɗiye wasu yawu masu ɗaci kafin na ce “a yau na ga wata duniya ,wasu mutane na gani a siffar tawaga biyu,ɗayar tawagar ta kasance ta Mayu ce yayin da ɗayar kuma ban san ta mece ce ba abin da kawai na iya gani shi ne fuskokinsu na fitar da wani irin haske mai natsuwa haka ma hannuwansu.A goshin shugabansu na ga abin da ya kusan dakatar da numfashina,wani baƙin tabo ne wanda ya ƙawata goshin nasa ya kuma fitar da tsantsar hasken fuskar tasa” “A yadda kika siffanta su sak sun fito a al'ummar nan da ke bautar wani Ubangijin Ka'aba,sam ba su nuna tausayinsu ga matsafa da kuma waɗanda suka saɓa dokar Ubangijinsu” Zuciyata ce na ji tana wata irin tafasa hakan yasa na juyo a fusace ina kallon Debora wacce ita ɗin ta kasance ƴa ga babban malamin ilimin tarihin duniya.Tun da na ji ta ambaci haka tabbas kuma na san gaskiya ta faɗa ,“dama har akwai masu tsanar Magic a duniya? Shin ba su san tasirin tsafi ba ne ko kuwa sun jahilci lamarin ne?” “Ko ɗaya! Su ɗin sun yi imani a kaf duniya babu wanda ke tafarkin gaskiya sai wanda ya kasance ɗaya daga cikinsu.Wannan dalilin ne ma yasa suke shirya yaƙi duk shekara suna shiga ƙasashen matsafa.Kin ga mu bar maganar nan ma saboda ba ta shafe mu ba” “Ta ya za ki ce ba ta shafe mu ba alhalin kin san duniyarmu ba mu yarda da wani addini ba? In fa suka farmake mu?” ban san me yasa na ji tsoro da shakku dangane da mabiya addinin ba, musamman in na tuna fuskar mutumin nan Naslam. Debora ta riƙo hannuna tana mai cewa “masana tarihi sun tabbatar mana cewa yankinmu zagaye yake da ƙoramai ta yadda babu wata halitta da ta isa ta ƙetaro izuwa nan sai da izinin esprit ɗin ruwa,kina tunanin uwayen gijinmu za su lamunta a kawo mana hari ?” wani irin numfashi na sauke ko ba komai kalaman ƙawata sun ɗan rage mini fargaba amma duk da haka ban yi ƙasa da gwiwa ba na yi shela ina son ganin dukkanin matsafan garin domin zuwa kowacce kusurwar ruwa su kai saƙo zuwa ga aljanai da ruhikan ruwa....... [12/06 12:37] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐 """"""""""""""""""""""" LoVe aNd HoRrOr StOry☠️ ```MRS SADAUKI```💫✍️ FCWA☀️ ____________________________________________ 02 Ƙananun shekaruna ba su hana ni jagorantar tsoffi da kuma dattizai zuwa bakin kowacce kusurwar ruwa ba.A tsaye nake ƙiƙam ina kallon yadda ake masayar kalamai tsakanin aljanun ruwa da kuma matsafa,kamar yadda na faɗa musu tun farko ina son a bai wa garinmu kariya haka su ma suka faɗa sai dai aljanun sun ƙi lamincewa da ƙudirinmu kai tsaye sai da suka kawo nasu sharuɗan.Daga ciki akwai bayar da jinin baƙaƙen dabbobi duk ranar laraba, sannan a kowacce ƙarshen shekara ɗaya daga cikin mutanen yankin zai zama hadiya ta aljanai. Shiru wurin ya ɗauka suna kallona,suna jiran amsata a matsayina na shugaba.Ni ma shirun na yi ina nazari,wanda ban san ashe cewa tazarar lokacin da na ɗauka kafin na miƙa yardata ya fusata aljanun ruwan sun komawarsu. “Sun fusata ba za su sake yin magana ba sakamakon shirun da kika yi yayi yawa.A matsayinki na shugaba ya kamata a ce kina bada amsa ne a kai ba tare da nazari ba” ƙawata Debora ce ta yi wannan furucin idonta na kallon tsakiyar ruwa.Dukkan matsafan sun yi amanna da furucinta,ban ce komai ba sai taku da na fara yi ina ɗaga kafaɗata gefen da ke da ƙusumbi na shiga can tsakiyar ruwan.Tafin hannuna na hagu na kalla ina yin wani furuci nan take ya tsage jinina ya soma ɗiga a cikin ruwan.Duk ɗigo ɗaya ina iya jiyo wani nishi daga can ƙasan ruwa,na ɗauki kamar minti biyu a haka kafin na dakatar da zubar jinin sai kuma na soma yin magana cikin sauti ƙasa-ƙasa “joliho kuntahee namaruju kalmari hanaighar kashmuh balbilancaaaa!” babu shiri na lumshe ido jin yadda wata irin guguwar ruwa ta tashi tana tunkuɗo duk wani masarafin tsafi izuwa gare ni. “Ya ke ƴa ga Bazuka ki sani cewa kowanne tasiri da farashinsa,sannan mu halittun ruwa ba mu taɓa mance duk wata alaƙa da aka ƙulla da mu .Za mu bai wa garinki kariya kamar yadda kika buƙata sai dai ki sani a duk lokacin da kika take dokarmu za mu bayyana miki asalin me ake kira da masifa da annoba ” wata murya da ke kama da ta macijin ruwan ta yi mini jawabi. “Hakan ba zai taɓa faruwa ba,zan kiyaye dukkan sharuɗanku” wannan karon na bada amsa kai tsaye. “Mu ne za mu zaɓar hadiya da kanmu,a duk sa'ilin da lokaci ya yi za mu nuna miki mutumin da muke buƙatar jininsa ta mafarkinki ” “Na amince!” “Sannan kuma haramun ne shiga ruwa ranar Laraba ” “Na amince!” ina furta haka kawai sai yanayin garin ya canza ya ɗauki wani irin launin duhu amma ba sosai ba,sararin samaniya ya cika da baƙaƙen giza-gizai yayin da kuma kukan tsuntsaye da kaɗawar bishiyoyi ya tsaya cak. “Aroroke! Aroroke! Aroroke!” shi ne abin da sauran mutanen da muka zo suka fara faɗa cikin murna saboda dukkan alamomin nan da suka bayyana na nasara ne. A hankali na fito daga cikin ruwan ina mai fuskantar su sai duk suka yi shiru tare da sauke idonsu ƙasa don nuna girma a gare ni. “Daga yau na sama wa garinmu suna za a dinga kiransa YANKIN MUTUWA,duk wanda ya shigo sunansa gawa ba wai mutum ba ko dabbar da ba ta wannan garin ba ta shigo na bada izini kafin a zo a faɗa mini a kashe ta” nan ɗin ma jin daɗinsu suka bayyana a fili kafin na wuce gaba su mara mini baya muka koma can tsakiyar gari inda na sa aka ƙara ƙawata gidanmu. Kan shimfiɗar da gawar Maa ta rushe na hau tare da yin kwanciya.Ina lumshe idona fuskar Naslam ta dawo mini da wani mugun sauri na buɗe su tare da tashi zaune ina jin zuciyata na harbawa da sauri.A fili na ja wani tsuki ina jin tsanarsa da su kansu mabiya addininsa.Yatsun hannuna na murza tare da furta kalmar tsafi nan take ragayar da ke maƙale a tsakiyar iccen rufin ɗakinmu ta yo ƙasa ta zo daidai inda nake wata ƴar ƙaramar takarda na gani mai ɗauke da haruffan tsohon asiri.Ban yi wani dogon bincike ba na fahimci cewa wannan takarda daga mahaifina take,mutumin da daidai da sakan ɗaya ban yi rayuwa da shi ba.Rubutun bai da yawa a ido,amma ma'anoninsa sun isa a rubuta dogon labari.Tsam na miƙe bayan na maƙale takardar a ƙuguna,daidai ƙofar da za ta ba mutum damar shiga uwar ɗaga na zube tare da shafar wurin nan take ya ɗau wani haske yana mai bayyanar mini da jan rubutu wanda aka rubuta da jinin mahaifina. “Finstako Bazaku enfinstako naheee” ina furta haka ƙasar wurin ta tsaye sai ga wata ƴar madaidaiciya wuƙa ta bayyana mai ɗauke da sunan mahaifina,nawa da kuma na Maa.Sai da na tsaga jinina ya ɗiga a kai sannan na samu damar ciro ta.Wani mummunan iska ne ya taso daga sama ya cilla ni gefe kafin guguwa ta fara haɗuwa daidai wurin da na ciro wuƙar.Wata siffa ce ta bayyana a gare ni,tun a kallon farko na ga ne shi ɗin mahaifina ne duba da fuskarsa sak irin tawa ce.Hannu ya miƙa mini,daga wurin da nake zuwa inda yake da ƴar tazara amma hakan bai hana ni ɗora hannuna kan tafinsa ba sai ya janye ni muka ɓata cikin iskan guguwa.Wata tsohuwar maƙabarta ce mai zubin ta kiristoci,kowanne kabari da nasa sunan. “Wannan ce hanyar da matsafa ke bi don kawar da maƙiyinsu ba tare da sun sha wahala ba.Da zarar kin ginawa mutum kabari to lissafin mutuwarsa zai dawo hannunki ,ke ce za ki zaɓar lokaci da kuma yanayin da zai bar duniyar bil'adama zuwa ta matattu” shi ne bayanin da Abbana ya yi mini ba tare da na tambaye shi ba. Kallonsa na yi ina mai cewa “ni banda maƙiyi ko ɗaya” “Shi kuma Prince ɗin da kuka haɗu fa? Kin yi tunanin cewa haka kawai ne kika fita daga duniyarmu ta tsakiyar ruwa zuwa duniyar turɓaya? Ya ke ƴata ki sani daga ranar da muƙamin iko na prophecy ya fara aiki a kanki to abu na farko da uwayen gijinmu suke nuna maka shi ne babban maƙiyinka” Shiru na yi ina nazarin furicinsa ,so nake na san ta ya aka yi Naslam ya zama maƙiyina,don na fahimci sarai a kansa ne yake magana. “Dalilin da yasa kika zama maƙiyiyarsa saboda ta silarki ce aka yi galaba a kansa,ba don a ce ya shagala da kallonki ba to da tabbas magauta ba za su harbe shi ba” ya ƙara faɗa kai ka ce shi ke sarrafa tunanina da har yake sanin abin da ban furta ba. “In dai duk abin da ka furta gaskiya ne,to zan so a ce a duk lokacin da yake tsakiyar fafatawa da maƙiya ya zamana ni kuma na bayyana a wurin ta yadda zan zamo rauninsa,ya gane ya kuma fahimci cewa wutsiyar raƙumi ta yi nisa da ƙasa.Ta hakan ne kawai ba zai taɓa sha'awar farmakar yankina ba” Bai ce mini komai ba sai wuƙar nan da ya cire daga gidanta ya miƙo mini tare da nuna mini wani buɗaɗen kabari wanda a jikinsa aka rubuta sunan Prince Naslam. Hannuna na tsaga jini ya zuba a cikin ramen kabarin,babu jimawa wuta ta soma ci balbal.Daga nan kuma kawai sai tsintar kaina na yi a ɗaki,ba tare da na san alƙawarin jini ne na ƙulla Ni da aljanai ba. ★DAULAR ABU NASLAM Tutar daular ce aka juye alamun babu lafiya a yankin.Dakaru haɗi da hadimai sai faman kai komo suke yi suna jiran tsammani na farfaɗowar jagoransu,madubi kuma gun babbar masarautar musulinci. Sarki Haroon mahaifi gun Prince Naslam a tsaye yake a wata kusurwa wacce ta yi daidai da alƙibla.Idonsa a rufe suke,yayin da kuma ya haɗe hannuwansa wuri guda domin nuna ladabi ga Ubangijinsa.A hankali yake motsa bakinsa,duk da ba a jin furucin amma za a iya fahimtar abin da yake cewa shi ne “Ya Hayyu! Ya Ƙayyum! Wato ma'ana Ya Rayayye! Ya dawamamme!” iya shi kaɗai yake furtawa bai dakata ba kuma sai da ya ji murya jakariya Ali yana cewa “shugaba cikin amincin Ubangiji ka'aba Prince Naslam ya dawo hayyacinsa ” “Shukuran Ya Rabb!” shi ne kawai abin da ya furta kafin yake juyowa yana kallon Ali wanda duk ya fita hayyacinsa tun ranar da suka dawo daga yaƙin tsibirin Mayu. Murmushi sarki ya sakar masa wanda ya haifar masa da samun wata ajiyar zuciya nan take kafin cike da girmamawa ya ce “yarima na buƙatar ganinka” “Mu je!” ya furta kafin sarki ya shiga gaba shi kuma Ali na take masa baya har suka shiga ɗakin yarima Naslam inda yake kwance yayin da kuma tsoho Barham ke kula da lafiyarsa. Suna haɗa ido da mahaifinsa ya yi saurin yunƙurowa da niyyar tashi,sai dai raunin ƙirjinsa ya dakatar da shi da wani mugun sauri ya koma ya kwanta yana mai yin wani irin nishi. Barham ya ce “na yi nasarar cire dattin garin mahalbiya,nan da kwana uku in sha Allah zai iya tsayuwa kan ƙafafunsa” Sarki ya ce “Ubangin ka'aba ya albarka ce ka ya ƙara maka ɗimbin ilimin sanin magani” Barham ya amsa da “ Amin ” kafin kuma ya yi wa Ali alama suka fice suka bar sarki shi da yarima. “Ya jikin naka?” sarki ya tambaye shi yana mai dafa goshin Naslam ɗin.Maimakon ya basa amsar tambayarsa sai cewa ya yi “Abih aljanar da nake baka labari ita ce silar raunin da aka ji mini,na gan ta a zahiri tana tsaye gaɓar teku sanyen da kayan arna,ƙusumbin tsutsotsi maƙale a bayanta,idon sharrinta na fitar da gubar tsafi ” “Naslam na sha faɗa maka ita ɗin ba aljana ba ce,wakiliyar duk wasu sheɗanun Mayu da matsafa ce.Ita ce aka damƙawa kundin prophecy domin cika wani baƙin ƙuduri nasu.Amma da ka gan ta wane yunƙuri ka yi?” “Abih ta ya zan iya yin wani abu? Yanzu dai ina so a shirya dawakan yaƙi su ƙara komawa can domin binciko mini ita” Shiru sarki yayi kafin kuma ya fita,cike da bayar da umarni ya sa aka shirya dawakai majiya ƙarfi da kuma dakarun yaƙi . Jakariya Ali shi ne ya shugabanci tawagar,sai dai sama da awa biyar suka kwashe ko kusa da ruwan sun kasa zuwa saboda tsantsan tsaron da aka shimfiɗa musu a dole ya jawo su suka dawo gida a lokacin tuni yarima Naslam ya kasa sukuni ya sa an kawo masa farin ƙyalle haɗi da abin zane haka ya zauna ya zana Naomi kai ka ce ta gasken ce . Ido ya tsura mata cike da tsana yana tambayar kansa a zuci ‘ wace ce ke? Me yasa tun da na shiga zangon balaga kika addabi rayuwata?’ Jin an banko ƙofa yasa shi barin zancen zucin tare da maida idonsa kan ƙofar shigowa.Jakariya Ali ne sanye da kayan yaƙi,zanen ya fara kallo kafin ya cewa yarima “babu wata nasara dangane da tekun can,amma wai don Allah me yasa ka damu? ” Cikin zafin rai ya ce “aljanar mafarkina ce” “Amma fa ita ce ta cece mu lokacin da Mayu suka fara sarrafa tsafi ” jakariya Ali ya faɗa . “Bayan ta yi silar cutar da ni,Ali na tsani aljanar nan tun ba yau ba na fahimci cewa ita ɗin rauni ce a rayuwata” “Yarima a duk lokacin da na ji kana irin wannan zantukan sai na dinga jin cewa kai ma fa tamkar kana ɗauke da ikon prophecy ” Kafin yarima Naslam ya kai ga yin magana wani irin iska mai sanyi ya fara ratso ɗakin yana shigowa,babu abin da ya motsa sai zanen hoton Naomi shi ma ɗin cike da abin al'ajabi yadda bakinta ke ɗan buɗewa tana murmushi..... [12/06 12:37] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐 """"""""""""""""""""""" LoVe aNd HoRrOr StOry☠️ ```MRS SADAUKI```💫✍️ FCWA☀️ ____________________________________________ 03 Zanen fuskar Naomi bai gushe yana murmushi ba suka jiyo sautin wata waƙa wacce yarima Naslam ne da kansa ya haramta ta saboda kalaman da ta ƙunsa na tsafi da kuma kirari zuwa ga tawagar dabar Mayu da matsafa. Jakariya Ali ne yayi saurin tsayuwa kusa da window ta inda ya fi jin sautin na fitowa.Wata makauniyar tsohuwa ya gani a durƙushe riƙe da sanda tana rera waƙar tana wani jinjina kai haɗi da murmushi. “Ina ga mun yi baƙuwa ne ,ba don haka ba ai ka haramta raira waƙar nan” jakariya Ali ya faɗa . Yarima da ya cika yayi fam kamar zai fashe ya ce “a kama ta” Da wani irin gudu kuwa jakariya Ali ya fita ,babu jimawa yasa wasu dakaru biyu suka damƙe matar tare da kai ta can ɗakin ajiyar masu laifi ya kuma bada umarnin a ƙara tsaro sosai. Shi kuwa yarima Naslam zanen ya naɗe tare da adana shi ƙarƙashin pilow .Sai a lokacin kawai ya tuna akwai sallolin da suka hau kansa waɗanda bai yi ba,tsuki ya ja a fili yana cewa “duk sharrin aljanar nan ne” Cikin ikon Allah sai ga jakariya Ali ya dawo ,shi ne ya taimaka masa zuwa banɗaki ya yi ɗahara haɗi da alwala sannan ya fito ya soma gabatar da sallolinsa. Bayan ya gama ne,mai magani Barham ya ƙara shigowa ya duba shi tare da basa maganin sha da kuma na shafawa wanda cikin hukuncin Ubangiji sai ya ƙara jin ƙarfin jikinsa. “Zuwa bayan sallar asar zan haɗa maka ruwan magani a bahon wanka sai ka shiga ka yi,amma ina so don Allah ka cire duk wani tunani akan yarinyar da ka zana ” Barham ya faɗa . Yarima Naslam ya ɗago manyan idonsa masu firgita maza ya ɗora kan Barham kafin ya ce “me ka sani game da ita?” Barham ya gyara tsayuwarsa kafin ya ce “ita ɗin ba kamar sauran mutane take ba,an haife ta bayan ɗaukar ran mahaifinta,an raine ta cikin gata da soyayya sannan kuma an damƙa mata muƙamin prophecy a ranar da mahaifiyarta ta yi gushewa wannan dalilin kaɗai ya isa ya tabbatar maka iya tunaninta ma kaɗai ba alkhairi ne ba ga Sarkin goben masarautar nan” “ Ban fahimce ka ba,kana nufin ita ɗin annoba ce ga duniya baki ɗaya?” “A'a! Ita ɗin fa shugaba ce,kamar yadda kake kare Yankinka to ita ma haka jininta ke tafarfasa in aka ce an taɓa ahalin mugaye.Tana da ƙarfin ikon maitar ido,ga kuma baƙar maita ta baki wadda da za a ce ta tofa yawunta a tekun wani yanki da ba nata ba to tabbas da ruwan sun haramta saboda tasirin ƙwayoyin cutar da ke ciki.Na yi magana da jakariya Ali ya shaida mini duk yadda komai ya faru,kuma na gaskata sarauniya Naomi ce saboda abin da na tsinta a yayin yi maka magani” “Me fa?” yarima Naslam ya tambaya. Shiru Barham ya yi kafin ya tako ya iso gun yarima,cikin muryar raɗa kamar mai jin tsoro ya ce “ta jefa maka cutar ayni wato maitar ido, wannan ne ya hana ka motsi ya juye maka tunani ka manta cewa filin daga kake har sai da magauta suka yi nasarar harbin ka” Zuciyar Naslam ce ta fara tafasa kamar za ta faɗo,yana jin ina ma zai ga Naomi a yanzu da babu shakka tabbas da hannunsa zai kashe ta.Haka ya danni zuciyarsa,ya yi ƙoƙari sosai wurin manta wa da ita sai dai kamar abin isimi lokacin yin wankansa na yi na magani idanunsa suka fara yi masa gizon yadda ta kafe shi da idonta masu matuƙar girma da kyawu don tamkar gwal haka suke sheƙi. Jakariya Ali ne ke taimaka masa har ya samu ya shiga ya kwanta cikin bahon wankan,kamar jira ake yi kuwa wani al'amari ya riske shi.Ji yayi kamar an rufe shi bai numfashi kafin ya soma jin wani yanayi wanda sam ba zai iya misalta irin abin da yake ji ba.Jikinsa ne ya ɗauki wata irin kyarma sakamakon wasu halittu da yake gani dishi-dishi waɗanda ya yi imani cewa ba Mala'iku ba ne.Can kuma ya soma wani abu kamar mafarki yana tare da Naomi yana tarayya da ita kamar sauran mafarkansa na baya. Jakariya Ali da ke gefensa tuni ya fahimci abin da ke faruwa,muryarsa na ɗan rawa ya kira sunan yarima Naslam kafin ya ce “innalillahi wa'inna ileyhi raji'un!” nan take komai ya tsaya cak.Yarima Naslam yayi wata irin zabura haɗi da nishi bakinsa na fitar da baƙin jini.Jakariya Ali ne ya yi hanzarin goge masa jinin kafin ya taimaka masa ya yi wankan,da ya fito ma shi ne ya taimaka masa wurin saka kaya marar nauyi kafin kuma a gabatar masa da tafasasshen shayi wanda suke yi ko wane dare.Har ya yi sallolinsa bai dubi kofin shayin ba saboda abin da ke damun ransa,bayan sallar isha'i ne sarki ya shigo da kansa ya duba shi. “Gobe ka tura dakaru zuwa bakin Teku su ƙara binciko mini aljanar nan” yarima ya faɗa yana wani kawar da kai gefe. Sarki ya ce “zan so ka manta da batun yarinyar nan ka fuskanci sabon al'amarin da ke shirin tunkaro masarautarmu Naslam.Sanin kanka ne duk abin da ya cika naci to babu alkhairi a tattare da shi,ba tun yau ba kake faɗa mini kana yin mafarki da aljana to ka sani shigowa da ita masarautar nan daidai yake da ruguza duk wani ginshiƙi da ka gina tsawon shekaru” sai kuma ya yi shiru tare da zuwa ya ƙara ɗaukar wani kofi ya zuba masa shayi sannan ya saka cokali yana juya shi tare da miƙa masa ,ba don ya so ba ya karɓa ya soma sha.Sai kuma a wannan lokacin ne sarki ya ci gaba da cewa “gimbiya A'ishah na waje tana jiran fitowar ka ,zan so a ce ku daidaita kanku tun a yau don a samu a wuce wurin,na san daga lokacin da aka ɗaura maka aure shi kenan matsalarka za ta kau”. Ambaton sunan gimbiya A'ishah shi ya wanzar masa da nutsuwar zuciya,don yana mugun ƙaunarta har cikin ransa saboda ba ƙaramar gudunmawa ta bayar ba wurin haɓaka musulunci a masarautar nan ba. A hankali ya sauko daga gadon da yake,sai dai sam ya kasa jurar tsayuwar a dole ya koma ya zauna.Cikin ɗan ɗaga murya sarki ya ce “Ali?” shi kuwa kamar mai jira haka ya buɗe ƙofar ya shigo tare da ƙamewa. “Ka fito da yarima zuwa waje” ya faɗa tare da ficewa.Jakariya Ali ya ɗauko kujera ya taimaka wa yarima ya hau ya zauna sannan ya soma tura shi zuwa can falo wanda ya cika da ahali da kuma aminnan arziki.Tun daga nesa suka haɗa ido da ita,da wani mugun sauri ta yi ƙasa da kanta cikin kunya tana yin wani sihirtacen murmushi.Har aka ƙaraso da yarima ba ta ɗago kanta ba,haka aka shiga jera masa sannu yana amsa wa amma idonsa na kanta. “A'ishah zo ki gaishe da yarima mana kin wani tsaya wuri guda kina sunne kai kamar ba ke ce a yanzu ki ƙi cin abinci ba saboda shi” mahaifinta ya faɗa yana wani murmushi haka ma duk sauran mutanen wurin fuskarsu cike take annuri in aka cire mahaifiyar A'ishah ɗin da take jin kamar ta je ta kama wuyar yarima ta shaƙe shi har sai ya mutu. Gimbiya A'ishah ba ta ko motsa daga inda take ba,sai da mutanen suka dinga fita zuwa babban falo suka bar su iya su uku don duk inda yarima yake jakariyarsa Ali na tare da shi.Ɗan gefe kawai ya koma yana kallonsu,shi dai ko kaɗan bai ga dacewar yarima da ita gimbiyar ba duk da kuwa cewa ita ɗin kyakkyawa ce ta ajin ƙarshe. “Amincin Allah ya tabbata ga shugaban gobe” ta furta tana mai takowa inda yake tana ɗagowa haɗi da yi masa wani kallo mai tsayawa a rai wanda a can da babu abin da ke matuƙar girgiza yarima irin kallon nan amma yanzu sai ya ji sam bai burge shi ba,hasali ma na Naomi ya tsinta a fuskarta. Da sauri ya lumshe ido yana mai amsawa tare da cewa “shi ne ba ki zo kika duba ni ba tsawon kwana biyu ina a kwance” Murya na ɗan rawa ta ce “subahanallahi! Meke damunka yarima? Ai ban san ba ka jin daɗin jikinka ba,saboda tun ranar da ka haɗa ni da matan nan nake koya musu karatu daidai da ɗaya rana ban taɓa leƙowa waje ba” Wani numfashi ya furzar yana mai buɗe idonsa ya dube ta,iliminta yana ɗaya daga cikin abin da yake so a tattare da ita,“kar ki damu ai na samu lafiya” Shiru ta yi tana mai ɗagowa ta dube shi,ita sai yanzu ne ma ta lura cewa kan kujera ne yake.Sai kuma ƙwaƙwalwarta ta tariyo mata lokacin shigowar su shi da jakariya Ali, kasancewar kwanyarta dama can ba kullum take tafiya daidai ba shi yasa ne ba ta fahimci hakan ba. Rikicewa ta yi ta zube a gabansa tare da soma jero masa tambayoyi,wanda kuma in akwai abin da yarima ya tsana a tare da ita shi ne yawan tambayoyi da kuma wannan haukan da take yi a duk lokacin da wani abu na ƙi ya same shi. Da wani irin sauri jakariya Ali ya matso yana mai dakatar da ita,yana cewa “don Allah ki yi shiru mana” sai ta ɗago kai tana yi masa kallon tsana saboda tun tuni ta san cewa Ali bai ƙaunarta. Yana yi mata wani mugun kallo ya je ya kama kujerar da yarima ke zaune ya soma tura shi tare da mayar da shi ɗakinsa.Har Ali zai tafi sai kuma ya dakatar da shi yana mai cewa “kai ni wurin matar da aka kama ɗazu” Jakariya Ali ya ce “tana da matuƙar hatsari yarima ,da bari ka yi zuwa gobe in sha Allah ka ga lokacin ka ƙara samun ƙarfin jikinka” “Mu je dai ka kai ni ” ya sake faɗa ,ba don ya so ba ya tura shi zuwa kurkukun har suka isa ragar da aka killace ta. Tana kwance a duƙunƙune cikin wani tsohon bargo,hatta kanta a rufe yake amma hakan bai hana ta ganin yariman ba.Cikin wata irin murya ta ce “barka da zuwa yariman musulmai,ka sani killace ni a nan ba shi ne maganin matsalarka ba.Hakan ma babban kuskure ne ka tabka,ko da yake ba ka san ko ni wace ce ba” ta ƙarashe faɗa tana yin wani nishi sai ga bargon da ta rufa a shi ya yi wani irin sama tare da buɗe ta. Yarima da jakariya Ali suka kalli yadda bargon ya maƙale can sama cikin iska.Su duka biyun sun yi imani cewa tsafi ne ta yi,sai dai a yanayin da yarima yake a yanzu ba zai iya ɗaukar wani mataki ba a hannunsa sai kawai yasa jakariya Ali ya juya da shi. ★ A cikin abin da bai wuce kwana uku ba mulkina ya tsaga kowacce kusurwar yankinmu.Tuni na yi ƙaurin suna yayin da kuma gogaggin matsafa daga garuruwan ƙetare ke kawo mini tayin aure duba da yanayin shekaruna ina buƙatar abokin rayuwa musamman don gudanar da mulki yadda ya kamata sai dai ko kaɗan babu wanda ya kwanta mini a rai. Muna zaune kan kututuren icce ni da Debora ,sai kuwa ga wata baƙar mujiya ta soma shawagi haɗi da yin wani kuka. Debora ta furta kalaman tsafi tana mai buɗe tafin hannunta,sai mujiyar ta sauko tana mai sakar mata wata takarda ita kuwa jikinta har rawa yake yi wurin buɗewa.Rubutu ne reras da manyan baƙi,sai dai harufan na tsafi ne kuma ba su yi mini wuyar karantawa ba.A tare muka kalli juna,kafin na miƙe tsaye ina cewa “to a wane yanki ne aka kama ta?” “Ba ta faɗa ba a cikin wasiƙar,amma ina zaton ɗaya daga cikin garuruwan da suka kawo miki tayin aure ne ba ki amince ba” Shiru na yi ina tunani kafin kuma na karɓi takardar,ina furta tsafi rubutun ya goge sai na soma juya ido ina yin magana cikin raɗa rubutun ya soma rubuta kansa ina gamawa sai na umarci tsuntsuwar ta kai wa mahaifiyar Deborah .Ido na birkice suka koma farare tas ta haka ne nake iya hango gudun tsuntsuwar tana keta sararin samaniya tana wuce ƙauyuka tana shiga wasu garuruwa sai dai tana daf da ƙetara wata tutar wani yanki na ga wata kibiyar haske ta jefe ta ita kuma ta faɗi ƙasa ,duk kuma yadda na ƙware a tsafi ban ƙarashe ganin sauran abin da ke faruwa ba...... [12/06 12:37] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐 """"""""""""""""""""""" LoVe aNd HoRrOr StOry☠️ ```MRS SADAUKI```💫✍️ FCWA☀️ ____________________________________________ 04 Hankalin Debora sosai ya tashi saboda ta lura da abin da ya faru.Ko kaɗan ban ga laifinta ba saboda na san yadda mutum ke ji in mahaifiyarsa ba ta tare da shi, wannan yasa na damƙo hannunta tare da yin wani irin kalar tsafi na gushe mata da damuwar tare da saka mata nutsuwa na danne ƙuncin zuciyarta. Idonta da suka kaɗa suka yi ja na duba karin na ce “ki sani cewa babu wani sarki da zai gagare ni,ki sa a ranki ummarka tuni ta kuɓuta” Muryarta na fitar da wani irin amo take cewa “ya ke shugabata in ba ki manta ba irin haka ne mahaifina ya tarar da wa'adinsa,silar zaƙulo bincike domin rubuta tarihi ya haɗu da wasu mabiya addini mabanbanta suka kashe shi a ƙarshe sai mahaifiyata ce ta maye gurbinsa domin ci gaba da rubuta littafin kudin binciken duniyar ruhaniya” tana kawowa nan da zancenta sai ta ɗan yi shiru kafin ta ci gaba da cewa “ina jin tsoron kar a ce ita ma Umma nata ajalin ne ya zo” Kai na girgiza mata ina mai cewa “muddin ina raye hakan ba zai faru ba” Rungume ni ta yi tana sauke wata irin ajiyar zuciya,yayin da ni kuma na shiga tunanin hanyar da zan bi na ƙwato Umma ɗin saboda a duniyar nan a halin yanzu banda wani masoyi da na fi so da ƙauna sama da Debora.Cikin hikima na mayar da ita cikin gida gabanin ni kuma na fita zuwa can cikin baƙin jejin garinmu mai cike da aljanai da fatalwa. Cikin tafiyar rauni ta masu larurar ƙusumbi nake tafiya ana take mini baya,ko kaɗan ban san su wane ne ke take sawuna ba kuma ban jin tsoro ko fargaba wani abu.A haka na isa bakin wata iraciyar kuka mai zubin halittar mutum don da baki da hanci gare ta.Ina gama daidaita tsayuwata sai kuwa bisashin ganye suka fara zubowa a kaina kamar ana ruwa kafin ɗanye ƙwaya ɗaya ya faɗo a gabana.Ɗaukarsa na yi tare da tofa yawuna a kai,sai na soma juya ido babu jimawa yawun suka rikiɗa zuwa rubutu.Sai a lokacin na miƙawa itaciyar ganyen mai ɗauke da bayanin abin da ya kawo ni nan ɗin.Tafin hannuna na ji ya cika da wasu duwatsu,ina dubawa sai na ga suna sheƙi akan kowanne dutse an rubuta karlis .Ban yi jinkiri ba na nufi ɗaya daga cikin magudanar ruwa na je na yi tsaye ina kallon yadda ruwan ke a kwance sun nutsu ko motsi ba su yi.Dutse ɗaya na cilla ina sauraren yadda ƙararsa ya ratsa ruwan tare da soma yin gudu har zuwa inda nake son ya isa. Ba a ɗauki wani lokaci ba wata iska mai sanyi ta soma kaɗawa tana fitar da wani ƙanshi irin na gawa.Can sai ga Maa ta ratso ruwa ta fito,fuskarta ta yi wani fari fat kana ganinta ka ga matatta ga kuma fararen kaya a jikinta. Cike da soyayya na je da gudu na rungume ta,sai dai kamar na jimƙi iskan gas haka na ji babu wata alamar gangar jiki.Da sauri na ja da baya ina kallonta tana wani fitar da murmushi,wani irin tausayin kaina na ji wanda ko ranar mutuwarta ban ji shi ba. “Me kike buƙata Nao?” don haka take kirana a duk lokacin da take shauƙi ko kuma take son isar mini ƙaunar da zuciyarta ke ƙumshe da ita. “Maa shi kenan ba zan ƙara jin taushin gangar jikinki ba?” ita ce tambayar da na yi mata madadin na sanar da ita matsalar da ta kawo ni. Ta ce “Naomi a zangon da nake na fita daga sawun duniyar bil'adama na koma cikin duniyar matattu,ki kira ni da ruhi kai tsaye” Kallonta na yi,tabbas ita ɗin ruhi ce kamar yadda ta faɗa ɗin.Na kai hannu na shafi kumatuna da nake jin wani damshi,wanda na yi imanin cewa ruwan hawaye ne .Murya na ɗan rawa na ce “mahaifiyar Deborah ta faɗa hannun mugaye shi ne nake son sanin ta ya zan ceto ta?” “Babu buƙatar yin haka,saboda ita ɗin ba kanwar lasa ba ce.Za ta iya fitar da kanta kar ki wani damu kanki” Maa ta faɗa . Na ce “amma kuma ita ce da kanta ta aiko da takarda domin sanar da mu” “Ta yi haka ne domin ku ci gaba da rubuta littafin bayanai ba wai don kawo mata agaji ba.Ki sanar da Deborah cewa lokaci ya yi da ita ma za ta ɗauki muƙaminta na rubuta tarihi kamar yadda mahaifinta ya karɓa gun mahaifinsa,ita kuma mahaifiyarta ta karɓa daga mahaifinta,yanzu kuma ƙaddarar littafin tarihi ta dawo hannunta” Maa na gama furta haka sai ta soma nitsewa cikin ruwa haskenta na tarwatse wa haɗi da disashewa.A gaban idona ta ɓata,na lumshe idona ina mai furta kalaman tsafi tare da buɗe su kuma a nan na tsinci kaina a ɗakina. Deborah na kwance amma ba bacci take yi na.Kallonta na yi kafin a takaice na sanar da ita abin da Maa ta shaida mini,da wani irin sauri ta miƙe ta zauna tana kallona can kuma ta soma furzo da wani irin furuci sai na ji tsafin da take yi ba irin nawa ba ne yana da banbanci kamar yadda Hausar wani gari ba ɗaya take da ta wani garin ba. Babu jimawa sai muka soma jiyo kukan jemage yana wani tsala shi kamar zai fasa gidan,a tare muka fita nan muka yi gamdakatar da wani baƙin jemage baƙi ƙirin da shi ga kuma wani irin girma na ban mamaki. Kan ƙafafunsa ya sauka bayan ya cillo wani tsohon littafi ya dira a tafukan hannun Deborah. Kallo ɗaya na yi masa na fahimci cewa shi ne wanda aka wakilta domin tsare littafin ya basa kariya.A hankali ya soma yin tsalle har ya isa gun Deborah,babban farcenta na ƙafar hagu ya kama ya fasa shi tare da soma shan jininta irin sosai ɗin nan don har sai da ta soma yin wani irin haske irin na rashin jini amma ko kaɗan ban yi yunƙurin tsayar da shi ba har sai da ya gama sha sannan ya tashi sama,sai dai bai yi wani nisa ba ya ɓace ɓat. Sai a lokacin na je na kama ta na ja ta zuwa ciki na zaunar da ita,magani na ɗauko na soma rufe mata yatsan da shi wanda har yanzu yake ɗigar da jini. “Ki kwanta ki huta na san kin gaji” na furta. “Ki soma karanta littafin kafin ni na karanta miki ” ta furta tare da miƙo mini,kamar ba zan karɓa ba sai kuma na kai hannu na karɓi littafin na ajiye a gefe.Ido ta lumshe ta soma yin bacci mai kama da mutuwa,wanda na yi imani cewa a cikinsa ne za a miƙa mata wasu asirai da kuma power kariyar kai da kuma ta abin da aka damƙa mata amanarsa. A cikin wannan daren ne na soma karanta littafin tarihi wanda ya ƙunshi rayuwar jarumai da kuma irin gwagwarmayar da suka yi fama a kai.Na samu sirrika dayawa,na yaƙi da kuma yadda ake sarrafa maita ta sigogi daban-daban. Wannan littafin ya ƙara saka mawa zuciyata cewa duk inda babu magic to lalle babu rayuwa mai inganci, Magic shi ne komai na duniya a cikinsa ne za ka samu ƴanci da kuma gata.Rufe shi na yi tare da raɓawa gefen Debora na kwanta,ina lumshe idona na soma jin wani irin motsi a cikin kunnena tamkar ƙwaro na tafiya.Ƙara nutsuwa na yi sai na soma jin tamkar ana yi mini magana ne,amma ta ina? Ban sani ba.Ji na yi ana danne ni ana saukar mini nauyi,na furzar da huci mai zafi jin wasu kalmomi daga wata murya da ban san mamallakinta ba. “ A duk inda kike a faɗin duniyar nan sai na nemo ki,ni ne nan zan kashe ki da hannuna ƙaramar matsafiya muguwa mai idanun maciji” muryar namiji ce amma ban san wane ne ba, sannan ban fahimci abin da yake nufi ba har ya ƙara yin wani furucin “ina ma ace annabi sulaiman bai yi wafati ba,da na roƙi alfarmarsa ya tura rundunar aljanu su gana miki azabar da ta fi ƙarfin tsafinki ” Saurin buɗe idona na yi,ina mai tambayar kaina “wane ne kuma Annabi Sulaiman?” sai dai banda amsar wannan tambayar,in akwai wanda zai faɗa mini ita to bai wuce Deborah ba wannan yasa na kasa haƙuri na kai hannu na shafi fuskarta.Ta buɗe idonta tarau a kaina,sai dai babu ɗigon baƙi a cikinsu da alamu har yanzu ba ta dawo daga balaguron ruhi ba. “Wane ne Annabi Sulaiman?” na tambaye ta,idanunta ne suka dawo normal nan take ta tashi zaune sannan ta bani amsa da cewa “ ya kasance ɗa ga Annabi Dawuda shi ma kuma annabin Ubangijin Ka'aba ne.Yana da matuƙar power don a tarihin annabawa shi ne kaɗai ya mulki mutane da kuma aljanai,sannan kuma yana iya yin magana da dabbobi da kuma jarirai waɗanda bakinsu bai buɗe ba.Ya yi mulki cikin hikima da adalci ga al'ummarsa” Zuciyata ce na ji tana wani irin bugawa na jin bayanin da Deborah ta yi mini.Kamar mai tsoron sake jin wata buwayar na ce “amma me Annabin ke nufi?” “Mutum mai isar da wahayi daga Ubangijin Ka'aba zuwa ga al'umma ” ta bani amsa kai tsaye.Ban ce mata komai ba sai tashi da na yi na fito waje ina kallon taurari ina kuma juya kalamanta. Ƙofar gidan na ji ana bugawa,na je na buɗe sai na ga gungun matsafan garin ne da alamu sun fito maitar dare ne suka biyo. “Ranki shi daɗe mun samu baƙuwar fuska a yankin nan,wani mutum ne maharbi mun tsince shi a wata gona yana bacci.Mun ɗaure shi da duk wata igiyar tsafi amma ta ƙi yin tasiri a kansa saboda girman tsafinsa wannan dalilin ne yasa muka zo zuwa gare ki” ɗaya daga cikinsu ya faɗa . Raina a mugun ɓace na ce “me yasa ba ku kashe shi ba?” Kallon juna suka yi kafin wani kuma daga cikinsu ya ce “ kamar dai yadda ya faɗa miki ɗin ne,tsafinsa nada matuƙar ƙarfi da dukkan alamu mutum ne na daban ko a duniyar ruhaniya” Ban ce komai ba na yi gaba a fusace yayin da su kuma suka take mini baya.Tun kafin na isa gonar nake jiyo numfashin baƙin tsafinsa,ina isa ya yi saurin tashi tsaye muna fuskantar juna.Ɗan saurayi ne da ba zai haura shekara ashirin da takwas ba,sanye yake cikin kayan maharba ya rine gefen fuskarsa da baƙin abu yayin da kuma ƙirjinsa aka zana wata baƙar kunama. Ban tsaya tambayar wane ne shi ba na kai masa farmaki,ya tare kafin kuma mu shiga masayar kalaman tsafi muna haɗawa kuma da yaƙin gangar jiki.Kamar yadda suka faɗa ɗin tabbas shi ɗin na daban ne,ban ida fahimtar haka ba sai da ya kai ni ƙasa ya saita kibiyar tsafinsa daidai idona. Yana jan wani numfashi ya furta “kafin a farmaki baƙo a fara tambayarsa da wace aniya ya zo,duk waɗannan matakan tsaron na ruhikan ruwa da kika saka ba su iya tare ni na shigo yankin nan ba sai ke ce kike tunanin za ki hana ni yin abin da na zo yi?” shi abin da ya furta,amma duk da haka ban saurare shi ba na fito da wuƙar mahaifina na daɓa masa ita a ƙirji daidai kunamarsa yayi wata irin kururuwa da ta saka dajin amsa wa kafin ƙyafta ido sai ganin kunamu muka yi suna zubowa kamar ana ruwa..... [12/06 12:37] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐 """"""""""""""""""""""" LoVe aNd HoRrOr StOry☠️ ```MRS SADAUKI```💫✍️ FCWA☀️ ____________________________________________ 05 Yadda baƙaƙen kunamun suka dabaibaye jikina shi ya fi komai ɗaga mini hankali,ga shi kuma masarafin tsafina ya ƙi aiki.Idona ƙurrr kan mutumin da na cakawa wuƙa yana tsaye ƙyam kan ƙafafunsa,yayin da kuma kunamun suka buɗe hannuwansu da alamu umarninsa suke jira su shiga harbata. Tafin hannunsa ya buɗe ya soma yin furuci cikin Yaren tsafi wanda ya sha banban da nawa,a hankali duk kunamun suka yi ɓata dabo sai a lokacin na yunƙura na tashi zaune ina kallonsa cike da mamakin me yasa bai kashe ni ba kamar yadda na yi yunƙuri. “Wane ne kai?” na tambaye shi.Bai bani amsa ba sai nuni da yayi mini da wuƙata wacce har zuwa yanzu tana nitse a cikin ƙirjinsa.A hankali na miƙe tare da zuwa na ciro wuƙar,abin mamaki sam babu ko da ɗigon jini da ya zuba illa kawai alamun an huda ƙirjin. “Banah!” ya bani amsa,na maimaita sunan a bayyane kafin na ce “me ya kawo ka YANKIN MUTUWA?” “Ke!” ya bani amsa kai tsaye,kallon ban gane ba na yi masa kafin na ce “ni kuma?” Kai ya jinjina mini kafin ya ciro wata sarƙa da ke a wuyansa mai tambarin gumki ya miƙo mini,na karɓa tare da juya ta sannan na ɗago na dube shi. “Ba ki ga komai ba?” ya tambaye ni. “Me kake son nuna mini?” “Duba da kyau dai” ya sake faɗa ,sai na nutsu da kyau nan ne na ga gumkin jikin sarƙar zanen mace ne da ƙusumbi a bayanta. Na shafi ƙusumbin da ɗan yatsana,nan take ya kawo wani haske kamar an kunna ƙwan lantarki.Banah ya matso kusa da ni shi ma ya ɗora nasa yatsan kan nawa sai hasken ya ƙaru a hankali kuma muka fara yin sama ƙafafuwanmu suka bar ƙasa muka lula can cikin iska. Mutanen gari ne suka fara fitowa,sai kuma suka shiga yin kiɗa da bushe-bushe yayin da wasu kuma suke rawa.Ban taɓa tunanin cewa wai hakan aure ne muka ƙulla ni da Banah ba sai da wasu ruhika suka bayyana a gare mu suka yi mana bushara da hakan tare kuma da ƙara mana power. Sarƙar nan mai hoton gumkin mace da ƙusumbi ita ce kabancin sadakina,ita Banah ya saka mini a wuya kafin mu sauko ƙasa. Gefe na koma ina kallonsa,ba mummuna ne ba amma kuma ba za a kira shi da mai kyau ba.A kallon farko za ka tabbatar da cewa shi jarumi ne a fagen tsafi,kumatuna da ya shafa shi ya katse mini ɗan guntun nazarin da nake yi a kansa. “Tunanin me kike yi?” ya tambaye ni,da sauri na juya masa baya ina mai basa amsa da cewa “ ban san wane ne kai ba,daga ina kake kuma amma kai tsaye ka zo ka aure ni ba tare da neman shawarata ba” “Naomi ba fa ni ne na tsara haka ba,allolin prophecy suka ga dacewar mu haɗu ni da ke domin mu cika alƙawarin da magabatanmu suka ɗauko” Da sauri na juyo ina kallonsa na ce “to ka riƙe ni matsayin abokiyar aiki kawai” ina gama faɗar haka na soma tafiya cikin rangaji saboda yanayin larurata.Ina jin yana take mini sawu har muka isa gida,Deborah na tarar a tsaye kamar mai jiran zuwana. Da ido ta tambaye ni shi kuma wancan na bayana? Na juya na dube shi da sauri ya ƙaraso ya gabatar da kansa ga Deborah sai na ga yanayin fuskarta sam babu annuri. “Zo ina son yin magana da ke” ta faɗa tare da kama hannuna muka shiga cikin ɗaki. “Ta ya aka yi ya zama mijinki alhalin tarihi bai nuna za ki yi aure ba a doron duniya?” Deborah ta tambaye ni tana wani tsure ni da ido. Ni ma ɗin kallonta na tsaya yi saboda gaskiyar da ta fito daga bakinta wacce na san ita kanta ba san ta faɗe ta ba. “ Ba zan yi aure ba?” na tambaye ta,sai a lokacin kuma na ga ta sha jinin jikinta tare da soma yin kame-kame . “ Tun yaushe kika gano haka?” na sake jefo mata wata tambayar. Ta yi ɗan ƙasa da murya tare da sauke idonta daga cikin nawa ta ce “tun ranar da Umma za ta bar garin nan zuwa neman tarihi a wasu guraren , ta shaida mini cewa ba za ki taɓa yin aure ba muddin alamomin prophecy sun bayyana a gare ki.Ita ce da kanta ta nuna mini tsanin nan da ke cikin ruwa,ni kuma na ja ki muka je” Sosai na ji ɗaci har ƙasan raina jin wai ba zan yi aure ba alhalin a duniyar nan babu abin da na fi so kamar na yi aure na haifi yara.A daidai wannan lokaci ne kuma na ji wani abu game da Banah,ko da a ce auren bogi ne to zan karɓe shi ko ba komai dai za a kira ni sawun ma'aurata kuma zan haifi ƴaƴa. “Ƙusumbin da ke gare ki ba zai taɓa barin maza su yi sha'awarki ba,in akwai waɗanda da za su so ki to ki sani mata ne ƴan uwanki ” Deborah ta faɗa tare da kamo hannuna alamun rarrashi. “Wannan furucin naki duk ƙarya ne,kin faɗi haka ne saboda kin jima kina sha'awarta wannan dalili ne ma yasa kika tunzura ta har kika kai ta karɓa muƙamin iko alhalin wa'adin karɓarsa bai yi ba.Kin san cewa muddin Maa nada rai ba za ki taɓa samun Naomi ba” Banah ya faɗa yana mai shigowa ɗakin. Kallon tsana Deborah ta soma binsa da shi kafin ta ce “muddin ina raye ba zan taɓa bari ka cutar da Nao ba” Ya yi wani murmushi kafin ya ce “na gode da tunatarwa ” sai kuma ya maido dubansa gare ni yana jefo mini kallon so da ƙauna ya ce “ ki sa a ranki Banah yana sonki kuma zai zauna da ke ko da kuwa dukkan jikinki ciwo ne” Wata ajiyar zuciya na sauke jin furicinsa ,kafin na dubi Deborah na ce “ba zan so ki tsani Banah ba saboda shi ɗin murfin rufin asirina ne.Deborah ki sani zuciyata ba za ta taɓa lamunta rashin miji ba” Kai ta girgiza mini tana mai cewa “Banah ba mijinki ba ne,in ma dai akwai shi to ba na ce a jinsinmu ba ne don kuwa tarihi bai nuna hakan ba” Da sauri Banah ya zo ya shiga tsakiyar mu yana mai ɗan ture Deborah ya ce “dama ba tun yau matsafan tarihi ke ƙirƙirar ƙarya ba domin cimma manufarsu” kallona ta yi,sai na kawar da kai ita kuwa da sauri ta fita. ★ “Ba zan taɓa lamunta ki auri ɗan maƙiyiyata ba,ki sani cewa ko bayan raina kika auri Naslam ban yafe miki ba“ Dadda ta faɗa tana yi wa A'ishah wani mugun kallo. “Ki haƙuri Dadda amma ina son yarima fiye da raina,ki sani cewa in kika hana ni aurensa to tamkar kin yi mini shamaki da duk farin cikin duniya” A'isha ta faɗa tana hawaye. Dadda ta yi mata mugun kallo kafin ta ce “da dukkan alamu har yanzu ba ki warke daga cutar haukan naki ba,ɗan matsafiya kike sha'awar aure ki haɗa zuri'a da shi?” Ta dubi mahaifiyar tata da jajayen idonta kafin ta ce “ Dadda babu wanda ya tabbatar cewa Ummi Naslam na yin tsafi,kawai ƙage aka yi mata wannan dalilin ne ma yasa ta bi dare ta bar masarautar nan” “Wato ƙage na yi mata? Don ubanki da idona na gani tana tsafi.Tashi ki ɓace mini ko na sabauta ki ” ta ƙarashe cikin tsawa,da wani irin sauri kuwa A'ishah ta fita daga ɗakin direct can baya ta nufa inda tantabarun yarima suke.Tana zuwa ta yi tsaye tana kallonsu yadda suke ciyar da junansu da kuma yadda suke yin wanka, murmushi ta soma yi tana jin sonsu ba don komai ba saboda yadda ta san muhimmancinsu a gun yarima.Daga bayanta ta ji muryar Barham yana mai cewa “har sai yaushe ne za ki bayyana asalin fuskarki? ” Ba tare da ta juyo ba ta ce “ ranar da ka bar ɓoyen taka!” “Amma ai kin san ni da ke ba ɗaya ne ba,magani nake bayarwa domin sanin wasu tsirrai dole sai na haɗa da Magic ” A'ishah ta juyo tana wani murmushi kafin ta ce “me yasa kake saka mini ido a lamurrana? Bayan ni ai ka san waɗansu masu ɗauke da kambun baka me yasa ba za ka takura musu ba ?” “Ki iya bakinki ko kuma...” ta yi saurin katse shi da cewa “ko kuma me? Ka je ka sanar da sarki? Hahaha! To bari ka ji abin da har zuwa yanzu tsafinka bai nuna maka ba,hatta yarima Naslam maye ne,yana ɗauke da kambun baka ” Cikin zafin rai Barham ya ce “ ki sani cutar kambun bakan yarima daga Ubangijin Ka'aba take ba wai ta tsafi ba ce,ke kuwa uwarki ce ta saka miki ita.A kullum cikin yin ƙoƙarina nake na ganin na magancewa Yarima cutar nan saboda na san hankalinsa zai tashi muddin ya farga” Shiru A'ishah ta yi tana nazarin kalamansa,wai ita Dadda ce ta saka mata maitar baka hakan na nufin kenan hatta Dadda matsafiya ce? Ba tare da ta ce masa komai ba ta yi saurin barin wurin ta koma can sashensu.Sai dai tana shiga ta tarar da Dadda cikin wani irin yanayi wanda da ace normal mutum ce ita da tabbas har taɓin hankali za ta iya samu. Dadda ce cikin siffar maciya tana a tsaye gaban madubi idonta a rufe tana furzo kalaman tsafi tana haɗawa da sunan mahaifiyar yarima Naslam. A'isha ta yi tsaye tana kallon cikin madubin wanda yake ta fitar da tiriri tamkar an ɗora shi kan wuta har wani hazo-hazo ke tashi. Ummi ce ta gani wato mahaifiyar yarima Naslam tana zaune kusa da ruwa da alamu so take yi ta wuce amma ta kasa shiga ruwan.A kallon farko da za ka yi mata za ka fahimci cewa kaf illahin jikinta dabaibaye yake da mugun baƙin tsafi. Dadda ta yi wata mahaukaciyar dariya tana mai fito da harshe waje tana yin wani tsafin A'isha sai gani ta yi Ummi ta faɗa ruwan,ba ta san lokacin da ta fasa ƙara ba ta ce “Ummiii?” hakan ya jawo hankalin Dadda matsafiya ta kuwa juyo da kanta ta kalli A'ishah tare da juya idonta suka fitar da wani haske ya je ya shiga A'ishah nan take ta faɗi ƙasa a sume. Dadda ta yi saurin komawa normal kafin ta je ta dubi ƴarta,hannuwanta ta kama ta soma janta ƙiii har ta kai ta kan shimfiɗa. Wata kwalba ta ɗauko ta gubar tsafi ta buɗe tare da dangwalo maganin ta shafawa A'ishah babu jima ta buɗe idonta tarau sai dai babu ɗigon baƙi. Dadda ta soma sarrafa tsafi babu jimawa kuwa duk maganar da A'ishah ta yi ita da Barham ta shiga tariyo kanta.Dadda ta naushi iska tana mai cewa “ wato dai mugun tsohon nan ba zai taɓa fita hanyata ba” sai kuma ta luluɓa bargo ta fice ta bar masarautar. A ɓangaren yarima Naslam kuwa a daren ranar haka ya kasa sukuni,yana kwance yana tunanin Naomi haɗi da yin surutunsa ba tare da ya san cewa ba zanen hotonta da ke ƙarƙashin pilow yana naɗar duk wata magana da zai yi ta yadda ita kuma za ta ji komai cikin ƙwaƙwalwarta. Sai wuraren ƙarfe biyun dare ya samu bacci mai nauyi ya ɗauke shi,mafarkin Naomi yayi.Wannan karon ba mu'amala suke yi ba,a'a takobi yasa zai sauke mata kai bayan an ce ta miƙa wuya ta karɓi shahada ta ƙiya.Yana datsa mata takobin ta yi kururuwa wacce kai ka ce a gaske ne sai ya ji abin har kunnensa.Daidai nan ya farka yana jan numfashi tare da soma yin magana shi ɗaya. ★NAOMI Duk da ban ji daɗin abin da ya faru ba tsakanin Banah da Deborah hakan bai sa na wani damu sosai ba saboda a ganina kowanne yana da hujjar da zai kalubalanci ɗan uwansa.Ita matsafiya ce mai rubutun tarihi,yayin da shi kuma matsafi ne mai ilimin jeji don maharbi ne. Washegari haka muka zaga gari ni da Banah a matsayinsa na mijina,kafin kuma yasa shela mutane suka taru a ƙofar gidanmu.Sabbin dokoki ya ƙara kafawa kafin kowa ya kama gabansa,haka muka zauna ni da shi ina basa labarina yayin da shi kuma ya yi mini alƙawari sai da dare sannan ya bani nasa labarin.Wannan yasa ko da daren yayi a ƙage na ce masa “ina saurarenka bani labarinka ” Maimakon yayi abin da na ce,a'a sai ma fatar dabbar da na suturce jikina da ita da ya yane ya soma yana shirin kai hannu kan jikina na zabura sakamakon kalaman nan irin na jiya da na soma ji suna ziyartar kwanyata ba tare da na san daga ina suke ba. “Ya Rabb! Ka taimaka ka kuɓutar da ni daga dukkan wani tarkon sheɗanu da mabiyansu.Ya Ubangijin al'arshi ka bani kariya a duk lokacin da na fuskanci uƙubar mushrikai kamar yadda ka bai wa Annabinka Ibrahim.Ya Hayyu ! Ya Ƙayyum ! Ya zul...” da wani mugun sauri na toshe kunnuwana ina mai yin wata ƙara don tamkar ana ɗiga mini dalma haka nake ji, wannan dalili ne ma yasa ban bari na ji ƙarashe ba.Jikina na yin ɓari na ɗauki suturata na mayar kafin na buɗe ƙyauren ɗakin,sauri-sauri haka nake tafiya har na isa ƙofar gidansu Deborah . A zaune na tarar da ita kan wani kututturen icce tana kallon sama,da alamu aikin nata ne take yi wato lissafin taurari.Gefenta na zauna ina mai cewa “ki yi haƙuri” “Ki yi tambayarki kai tsaye” ta faɗa ba tare da ta dube ni ba. “Wane ne Annabi Ibrahim ?” na tambaye ta a raunace don hatta faɗar sunan ma yana yi mini wani irin raɗaɗi. “Yana ɗaya daga cikin masu isar da wahayin da Ubangijin Ka'aba ya umarce su da shi.Kamar yadda tarihi ya zo Annabi Ibrahim ya fito daga cikin al'ummar da ke bautar gumaka amma duk da haka shi tun tashinsa bai taɓa bautar wani Ubangijin ba sai na Ka'aba.Al'ummarsa sun so hallakar da shi ta hanyar jefa shi a cikin wuta amma sai Ubangijinsa ya cece shi ya mayar da zafin wutar sanyi mai daɗi ba mai cutarwa ba” Shiru na yi ina nazarin bayanin da ta yi mini,ina shirin tambayarta wane ne shi Ubangijin Ka'abar sai ga Banah ya bayyana a gabanmu kamar walƙiya.Hannuna ya kama yana yi wa Deborah mugun kallo kafin ya ce “ina mai yi miki kashedi na ƙarshe ki fita idona na rufe” Debora ta miƙe tsaye tana cewa “abin da nake da niyyar faɗa maka kenan ka guji wasa da wuta” Tamkar wata sokuwa haka na tsaya ina kallonsu,sam hankalina ya ƙi tsayuwa wuri guda abin da nake son sani shi ne wane ne Ubangijin Ka'aba?????????? [12/06 12:37] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐 """"""""""""""""""""""" LoVe aNd HoRrOr StOry☠️ ```MRS SADAUKI```💫✍️ FCWA☀️ ____________________________________________ 06 Maimakon Banah ya kai mu gida a'a daga nan sai ya wuce da mu gaɓar ruwa. “Shawoli narat kohi jayi!” ya furta kalaman tsafi cikin wata irin murya,babu jimawa wata irin ƙara ta karaɗe wurin kafin ruwan ya soma darewa yana fitar mana da hanya.Haka Banah ya ja ni muka shiga muka fara tafiya,ko tsakiya ba mu kai ba aka soma yin ƙasa da mu har muka dangane da ƙasan ruwa.A nan ne na yi arba da tsoffin garinmu waɗanda suka mutu,wasu tun banda wayo a labari ne na ji mutuwarsu yayin da wasu kuma da hankalina suka yi mutuwar. Kamar yadda ake yi wa baƙo in ya zo a wuri haka suka karrama ni,a wannan lokaci ne na ida ganin ainihin ɓoyayyar fuskar Banah shi ɗin ba iya mutum ba ne a'a jinsi biyu ne. Wani abu aka shayar da ni wanda ya dagula mini lissafi ya juye mini hankali na ji tausayi,so,ƙauna da duk wani abu da ya shafi mutumci sun fita daga zuciyata.Sai dab da za mu fitowa ne sannan aka kawo Maa zuwa gare ni,tana tsaye cikin siffar nan ta matattu sai dai yanayin fuskarta ya nuna tana cikin damuwa kamar ba ta jin daɗin rayuwar wannan duniyar. “Maa” na kira ta ina mai shigewa jikinta,yadda na ratsa ruhin nata na fita shi ya sa ni saurin janye wa na koma kan ƙafafuna. “Naomi me yasa har zuwa yanzu ba ki yi wani aikin bajinta ba wanda zai sa ruhina ya mori aikinki? Dube ni yadda na rame har yanzu ruhikan ruwa ba su yi amanna da ni ba” ta faɗa cikin wani irin yanayi. “Maa sam ban gane abin da kike nufi ba” na faɗa . Ta ce “Ta hanyar kashe mutane ne kawai zan samu abinci Naomi ” ta bani amsa ,wato so take yi na fara sarrafa maita ina damƙe kurwar mutane ina kawo mata jininsu. Tana gama bani amsa aka zo aka tafi da ita,Banah ya kamo hannuna muka fito daga ƙasan ruwan.A lokacin da muka isa gida tuni gari ya soma yin haske,cikin son sake kasancewa da ni Banah ya soma yi mini wasu abubuwan amma na dakatar da shi ta hanyar yi masa wani kallo da idona da nake jin tamkar an yi mini musayarsu.Cikin wata shakkata ya janye daga gare ni kafin ya koma gefe yana kallona,murya a dake na soma magana “ka nemo baƙar akuyar da za a yi hadaya da ita,yau laraba ruhika na buƙatar jini” sai kuma na yi shiru kafin can kuma na ci gaba da cewa “ina son jinin mutum domin shayar da mahaifiyata” Sai da na kai karshe sannan Banah ya ce “domin samun jinin mutum ya zama dole ki fita farautar dare,don yin maita da rana tsaka ba halayyar shuwagabanni ce” sai kuma ya taso ya matso kusa da ni ya tallabo haɓata yana mai ci gaba da cewa “matata zafafa ce,na san ta kowanne fanni jaruma ce kuma ƙwararriya.Zan baki shawara mai kyau amma sai in kina so” “Ina jinka ” na faɗa a dake. Ya ce “ki shirya gagarumin yaƙi domin samo tataccen jini mai tsabta wanda ba a gurɓata shi da maita ba” “Su wa zan yaƙa kenan?” “Garuruwan da ke maƙwabtaka da mu mafi akasarinsu ba su sarrafa tsafi ballantana maita,in muka yaƙe su sosai za mu samu alkhairi ” A cikin bayaninsa sosai na tsinci kishin garinmu da kuma son ci gabansa, wannan dalili yasa na ce “bayan an gama ƙaddamar da hadaya,zan so ka haɗa hankulan dukkan mutanen garin nan sannan ka shaida musu a yau ba sai gobe ba za mu je farauta ruhika” Banah ya yi wani murmushi yana mai cewa “an gama” sai kuma ya fice. Ido na lumshe ina tunanin yadda na ga shugaban nan NASLAM da tawagarsa suna yaƙar Mayu.Da wani irin sauri na buɗe idona ina mai yin magana a fili “ yaƙi cikin tsakiyar dare ya fi ɗaga hankali kan da safe,don haka farmakin dare za mu kai musu” sai kuma na yi wani murmushin mugunta wanda hakan ba ƙaramin sanyaya mini zuciya ya yi ba. Kamar yadda na umarci Banah haka ya kawo mini baƙar akuya har da ma zakaru su ma duk baƙaƙe ne.A gaban al'ummar gari muka je muka shayar da kogi jinin dabbobin kafin kuma mu juyo,Banah ya laƙanci tsafi sosai wannan yasa bai sha wuya ba wurin aiwatar da shirinmu na kai farmaki a garuruwan da babu maita. Dab da shigowar duhun dare Deborah ta zo inda nake,haka kawai na ji ban buƙatar ganinta duk da kuwa wani sashe na zuciyata yana tune da ƙawancenmu. “Abin da kike shirin yin sam bai dace ba! Babu wani sarki da ya zo mana a tarihi cewa ya nuna ƙarfin tsafi ya janyo wani yanki izuwa nasa” Deborah ta faɗa ,ba tare da na kalle ta ba na ce “wannan garina ne,ni ce ke da ikon yin duk abin da ya dace ga al'ummar ciki ba ke ba.Ruwanki ne ki rubuta tarihina a cikin littafinki,in kuma ba ki ra'ayi za ki iya barinsa” “Naom...” ban bari ta kai ƙarshe ba na juyo a harzuƙe cikin hargowa,sai kawai ganin Deborah na yi ta yi sama tare da faɗowa ƙasa cikin rauni.Na nuna ta da yatsa ba tare da na ce mata komai ba,amma sosai ta gane kashedi nake yi mata. Wani irin kallo ta soma jefo mini kafin ta ce “ta yaya kika yarda har wani baƙon haure ya raba mu? ” “Shi ɗin mijina ne,don haka na san ba zai yi abin da zai cutar da ni ba kamar yadda ke kike ƙoƙarin danganta ni da masifar rashin yin aure” Hawaye suka zubo kan kumatunta ba tare da ta goge su ba ta ce “na san kin karanta littafin tarihi,kin gani da kanki muddin shugaban tawagar Mayu ta fito a mace babu ƙaddarar aure a rayuwarta,in kuma ta yi shi to ki sani akwai ranar da mulkin sai suɓuce mata.Sannan yadda tarihi ya nuna ke dai babu aure a tarihinki da ya zo da wanda ma zai zo gaba, sannan na faɗa miki sharaɗi in ma kin yi auren to ki sani ba a wannan duniyar ta ruwa ba” Cike da tsana da takaici nake sauraren jawabinta.Da a ce za a tambaye ni babban maƙiyina a duniyar nan a yanzu to babu makawa zan ce Deborah ce,saboda duk wanda ke da ja da lamarin aurena to ban ɗauke shi masoyi ba. Baya na juya mata a karo na biyu kafin na ce “ina shawartar ki da ki bar gidan nan kafin na yanke miki ɗanyen hukunci” Ba tare da ta ce komai ba ta tafi,babu jimawa kuma shi Banah ya shigo hannunsa riƙe da ƙwallon kwakwa ƙwaya ɗaya.Tsakiyar ido ya dube ni kafin ya ce “muddin kina gama baki da matsafin tarihi to mulkinki ba zai taɓa ci gaba ba saboda a kullum so suke su canza maka ra'ayi akan abin da kake buri” “Me za ka yi da kwakwa?” na tambaye shi ba tare da na bai wa abin da ya gama faɗa muhimmanci ba. “Jirgin dare ne na Mayu ,a cikinsa za mu tafi” ya bani amsa.Kallon mahaukaci na yi masa don sam ban san komai ba game da maita saboda ban taɓa gwada yi ba.Sai da dare ya zo tsakiya ne na ga abin al'ajabi yadda Banah ya mayar da kwallon kwakwa jirgi,kuma ma ni ce farkon shiga bayan shi sai kuma ya soma zagayawa da mu yana ɗibar jama'ar gari waɗanda ke ɗauke da kambu maita ko tsafi. A wani gari jirgin namu ya yi dirar angulu,tsit garin yake kowa na yin bacci .Haka muka zagaye shi kafin mu soma sarrafa mugunta muna fito da su daga gidajensu muna cillawa cikin jirgi,duk wanda ya yi gardama a nan take muke aika ransa ga ruhikan ruwa.Cikin ƙanƙanen lokaci garin ya hargitse da ihuce-ihuce da kukan mata da ƙananun yara,gefe ɗaya kuma wuta ce ke tashi. Har mun shiga jirgi za mu koma sai idona ya sauka kan wani gida,shi kaɗai ne ba mu rogaza ba.Kukan jinjiri na soma ji,cikin azama na dire tare da zuwa na ratsa bango na wuce saboda yadda duk ƙwayoyin tsafi suka game jinina. Wata mata ce na tarar a ciki,gefenta jinjiri ne sabon zuwa duniya don ko cibi ba a yanke masa ba.A hankali na duƙa na ɗauki yaron,sai a lokacin kuma na ji muryar matar na cewa “kar ku kashe mini yaro ” yadda na ga soyayyar uwa da ɗa a cikin ƙwayar idonta shi ya tuna mini tawa mahaifiyar. Ban kai ga cewa komai ba Banah ya shigo,kafin ƙyaftawar ido ya soma jan ragamar ruhinta.Cikin gargardar murya na ji tana cewa “ Ash-hadu an la'ilaha illallah! Wa'ash-hadu anna Muhammadu Rasulullah!” wata irin walƙiya ce haɗi da zubar ruwa suka zo a nan take,yayin da kuma ni da Banah muka zabura muka yi baya saboda ɗacin amon sautin abin da ta furta yayin da shi kuma yaron da ke rungume a hannuna ya ci gaba da canyara kuka. “Mu bar wurin nan yi sauri kafin alƙawari ya karye” Banah ya furta cikin wani irin tsoro wanda ban san dalilinsa na yin haka ba.Ina ɗaga kafaɗa haɗi da sake rungume jaririn a ƙirjina na fito,ina shiga cikin jirgin Banah ya jefo mini wani mugun kallo yana kallon jaririn.Na ƙankance ido ina mai ce masa “kar ma ka fara,ka tuƙa jirgi mu tafi” Ba don ransa ya so ba ya ja ragamar jirgin namu na matsafa har muka isa yankinmu,a ƙofar gidanmu aka zube dukkan mutanen da muka kwaso kafin ni na shiga can ciki na bai wa sauran umarnin su tsaya su tsare mutanen. Kan gado na shimfiɗe jaririn,ina shirin kwanciya na ji wata murya a cikin ƙwaƙwalwata tana shaida mini an samu baƙon haure a yankina. Ba tare da na fita ba na yi surkulle na aika Banah can gaɓar ruwan,bai dawo ba sai da gari ya yi haske sai ga shi saɓe da wata mata. Kan tabarma ya shimfiɗe ta,kallo ɗaya na yi mata tal na ji ƙaunarta ba don komai ba sai don na hango tabon ruhaniya a jininta. Fuskarta na shafa nan take ta buɗe idonta,sai kuma ta tashi zaune tana mai kallona da kuma inda take. “Su wane ne ku? ” ta yi tambayar tana ajiye idonta kan gado inda na shimfiɗe jariri.Da sauri kuma na ga ta miƙe tana cewa “me yasa har yanzu ba a yanke cibi ba?” “Ban san ya ake yi ba” na bata amsa. “Bani wani abu mai kaifi” ta furta,na zaro wuƙata na miƙa mata,da ita ta yi amfani ta yanke cibin kafin kuma ta ciri suturar jikinta ta kulle daidai wurin da ta yanke ɗin. “Gefen cikin jaririn duk yayi baƙi saboda mahaifa ta taɓa shi,a kawo ruwa na yi masa wanka” ta sake faɗa . Banah ya ɓata rai yana shirin magana amma na dakatar da shi,na je na kawo mata ruwan.Sai dai tana saka hannunta ciki ta ce “waɗannan ai masu sanyi ne,masu ɗumi nake so” idona kawai na juya ruwan suka soma tafasa suna fitar da tiriri.Sai ta yi ƙuri tana kallona kafin ta ce “wannan tsafi ne kika yi kuma sarki ya haramta haka” Sai muka kalli juna ni da Banah tare da haɗin baki wurin tambayar “wane sarki?” Kai ta girgiza sai kuma ta soma yi wa jaririn wanka,ta saki murmushi ta ce “mace ce ashe” sai ta fito da ita daga cikin ruwan,ta cire uban kallabin da ta yane kanta da shi ta saka jaririyar a ciki. “Wace ce ke?” na tambaye ta. “Ni kaina ban sani ba,amma sai nake jin tamkar an aiko ni nan ne saboda isar da wani saƙo” ta bani amsa tana mai ɗago kai ta dube ni.Idona ya sauka kan goshinta nan na ga irin tabon nan da ke a goshin NASLAM ita ma yana fitar da haske sai dai bai cutar da ni ba,hakan kuma sai ya yi mini daɗi na ji a raina cewa ko da a ce ita ma wannan Ubangijin Ka'aba take bauta ma zan iya zama da ita. ★ Wuraren ƙarfe tara na safe daular abu NASLAM ta samu wani rikitacen labari.Cikin ƙarfin hali da dakiyar zuciya yarima ya miƙe kan ƙafafunsa bayan ya yi wanka da magani ya kuma sha a cikin shayi. Cikin tafiyar jarumta ya soma ratsa dakarun har ya isa inda Sarki ke tsaye yana jawabin yadda komai zai kasance,kamar kuma yadda Sarkin ya tsara jakariya Ali ne zai jagoranci tafiyar. “Zan tafi ni ma don haka a shirya dokina” ya faɗa yana mai kallon mahaifinsa cikin ido.Sarki ya kawar da kai,don ya san ko da a ce ya yi yunƙurin hana shi ba zai ji ba. Haka duk suka fito kowanne ya hau doki,da yarima zai hawa kan nasa sai da jakariya Ali ya taimaka masa amma a haka suka tafi. Tun a bakin ƙofar shigar garin suka fara cin karo da kayan tashin hankali,babu shiri yarima ya diro yayin da kuma jakariya Ali ya soma take masa sawu. Gawarwakin mutanen da aka kashe,Ali ya kalla sai ya ga duk kusan kalar mutuwar iri ɗaya ce.Ya kai hannu ya damtsi ƙasa sannan ya kai kusan hancinsa ya sunsuna,yarima ya dube shi tare da cewa “me ka fahimta?” “Farmakin Mayu ne” ya basa amsa,ran yarima ya ƙara ɓacewa amma a haka suka ci gaba da duba ko ina har suka shiga gidan da matar nan ta haihu. Cak jakariya Ali ya tsaya yana kallon ustaza Jamila,wacce ta bayar da dukkan lokacinta domin yin hidima ga addininta.Yarima ya ƙarasa yana mai cire rigarsa ta sarauta ya luluɓe ta,tare kuma da baiwa dakaru umarnin a ɗauke ta a kai ta can masarauta tun yanzu ba sai an jima ba...... [12/06 12:37] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐 """"""""""""""""""""""" LoVe aNd HoRrOr StOry☠️ ```MRS SADAUKI```💫✍️ FCWA☀️ ____________________________________________ 07 Ustaza Jamila ƙanwa ce ta jini ga jakariya Ali,mijinta ma ya mutu ne a wajen yaƙin haɓaka musulunci sai ga shi ita ma ta mutu wurin da'awar jawo hankulan waɗanda ba musulmi ba.Kamar yadda tsarin masarautar yake,suna aika maza da mata garuruwa don koyar da mutane karatu. Yarima NASLAM ya dafa kafaɗar jakariya Ali yana mai cewa “ dukkan rai zai ɗanɗani mutuwa,ka sa a ranka lokacinta ne ya yi.Mu ma muddin namu yayi babu makawa a duk inda muke mutuwa za ta riske mu” Idon Ali sun kaɗa sun yi ja sosai,muryarsa ma cikin wata irin sarƙaƙiya take fita.“Na yi imani ga Ubangijin Ka'aba,dukkan wata ƙaddara mai kyau da akasinta daga gare shi take.Sai dai babbar damuwata ɗaya ce ,cikin jikinta sam babu shi a yanzu hakan yana nufin kenan ta haihu in kuma ya tabbata haka ina jinjirin yake?” Shiru yarima Naslam yayi na wani ɗan lokaci kafin ya ce “a duk inda yake Ubangijin Ka'aba ne zai tsare shi,ka dai kawai ka sa kyakkyawan yaƙini ga ubangijinka ” kalamansa suka yi tasiri a zuciuar jakariya Ali, wannan ya basu damar ci gaba da binciken ko ina. Bayan sun gama haka suka haƙa rame aka rufe sauran kafin su juyo su dawo masarauta inda Sarki Haroon da sauran al'umma ke dakon jiransu. Suna shigowa sarki ya je ya tarbi yarima tare da soma tambayarsa abin da ke faruwa. “Farmakin Mayu ne,duk sun kashe mutanen gari da alamu kuma sun tafi da wasu.Babban baƙin cikin shi ne ba su bar wani sawu ba da zai sa mu gane ta ina suka fito ” Barham da duk ya ji abin da yarima ya faɗa sai ƙara matsawo yayi yana mai cewa “a yadda ka yi bayanin ya tabbata cewa wannan rundunar Mayun ta samu jagoranci Banah maharbi” Sarki da yarima Naslam sai duk suka maido dubansu ga Barham ɗin,shi kuwa kai ya jinjina kafin ya ci gaba da cewa “tarihin da ya fara zuwa na wannan ƙarnin ya bada labarinsa,Banah maharbi ne kuma babban matsafi wanda ya fito daga tsatson aljanar ruwa.Mahaifinsa ya kasance masinci ne,ya iya ruwa sosai a irin alƙawarin da mutane ke ƙullawa da ruhikan ruwa mahaifin Banah ya yi gamo da wata aljanar ruwa har yayi tarayya da ita suka same shi.Tun da aka haife shi a cikin jeji ya tashi tare da fatale da aljanu,kafin mahaifinsa ya mutu ya koya masa farauta da kuma baƙin tsafi na ƙarnin baya sannan kuma ya ɗora shi kan turbar yi wa aljana ZAƘUMA bauta” Barham na kawo nan da zancensa masarautar ta ɗauki wani salo,guɗa ce kamar an kawo amarya ta karaɗe ko ina kafin kuma iska ya soma tashi babu jimawa kuma aka soma yin wasu yayyafin jini. Hankali a matuƙar tashe Barham ya ce “Attakbirrrr!” Dukkan mutanen da ke wurin suka amsa da “Allahu Akbar!” nan take yayyafin jinin ya tsaya cak wanda duk ya ɓata fuskokin mutane.Sai kuma sararin samaniya ya soma ɗaukar launin ja yana nuno inuwar wata halitta marar kyawun gani can ita ma ta ɓace komai ya dawo normal. Ran sarki da na yarima ya ɓace,saboda ba tun yau suka saba ganin ire-iren waɗannan surkullen ba. Barham ya ce “ Aljana ZAƘUMA ce,wato uwar gijiyar Banah da ita yake tsafi.A kullum yana shayar da ita jinin mutane,ita kuma tana basa ƙarfin iko ” “Ina zan samu shi Banah ɗin?” yarima ya tambaya. Barham ya ce “Ubangijin Ka'aba ne kawai ya san daidai ina yake a yanzu,saboda tamkar guguwa haka Banah yake bai zama wuri ɗaya yawo yake yi gari-gari yana shanye jinin al'ummar yankin” Yarima zai buɗa baki ya sake yin magana amma sarki Haroon ya dakatar da shi ta hanyar cewa “yanzu abin da ya fi muhimmanci shi ne yi wa ustaza Jamila sutura,don haka a kira gimbiya A'ishah ta yi mata wanka” Sai a lokacin ne kawai Ayyub ƙanen sarki Haroon kawai ya saka bakinsa,“ gimbiya A'ishah tana kwance babu lafiya tun jiya,na so na sanar da kai sai kuma wannan al'amari ya danne niyyata ” Hankali a tashe yarima ya ce “meke damunta?” “Ciwon ido ne mai tsanani ,idanunta sun zama kamar gauta ” Ayyub mahaifi ga gimbiya A'ishah ya faɗa . Yarima bai ƙara cewa komai ba ya shiga can ciki,direct kuma sashensu gimbiyar ya wuce. A kwance ya tarar da ita don tun lokacin da Dadda ta fice ta bar ta take nishin azaba idonta sai ƙara ciwo suke yi saboda ta ga abin da bai kamata a ce ta gani ba. Tana jin muryar yarima ta yi ƙarfin halin buɗe idon nata sai dai tamkar mai ɗauke da sabuwar makanta haka take ji dole ta ja su ta rufe. “A'ishahhh?” ya kira sunanta cike da tausayinta.Murya na ƴar rawa ta amsa da “na'am yarima” “Mene ne ya shiga idonki?” ya sake jefo mata tambaya,sai dai ba ta kai ga amsawa ba jakariya Ali da Barham suka shigo. Barham ya matsa kusa da kanta yana ajiye jakar kayan aikinsa,bai ɓata lokaci ba ya soma zuba magani yana wanke mata idanunta duk da yana haɗawa da Magic babu wanda ya sani in ba ita gimbiya A'ishar ɗin ba. Cike da aminci ta buɗe idonta da suka dawo normal tana kallon Barham da yake yi mata ta idanu. “In yau na wanke miki ido kin samu lafiya ki sani gobe ba zan yi ba,zan bar ki da mugun halinki ” “Ban taɓa ganin inda maye yake gorantawa ɗan uwansa ba sai kai Barham” ita ma ta basa amsa ta ido. Ya ce “ni ba maye ba ne,ban taɓa yin maita ba hasali ma ina adawa akan duk masu yinta.Ke ma kin san cewa iya Magic kawai nake yi shi ma ba don komai ba sai don ci gaban masarauta” “Me yasa dole sai ni kake son na bayyana kaina? Don me shi yarima ba ka damu da tasa maitar ba?” ta tambaye shi,sai dai shi Barham ɗin bai bata amsa ba ya juye kansa ya mayar da dubansa ga yarima Naslam yana mai cewa “ba wani babban abu ba ne ya same ta,kawai wani ɗan tsautsayi ne” Yarima NASLAM ya dube ta yana mai cewa “ki kwanta ki huta” sai kuma ya fice jakariya Ali na take masa baya. Wasu mata aka samu suka yi wa ustaza Jamila wanka.Sai da aka ma fito da gawar ne sannan gimbiya A'ishah ta san abin da ke faruwa,sosai ta ji zafin mutuwar har da zubar da hawaye.Ana yi mata sallah aka kai ta gidan gaskiya,sai kuma a wannan lokacin ne jakariya Ali ya nuna rauninsa ya soma yin hawaye waɗanda zubar da su ba ƙaramin sanyaya masa zuciya suke yi ba. Sai da aka yi kwana uku ana jimamin mutuwar ustaza Jamila kafin kuma lamurra su ci gaba da tafiya. A yau ne yarima yasa aka fito da matsafiyar nan da ta raira waƙa tsafi.Gaban sarki aka gurfanar da ita,tare da umartar ta da ta faɗi laifinta. Amma ta yi shiru ta ƙi cewa komai sai yariman ne ya shaidawa sarki yana mai ƙara wa da “a yanke mata hukunci nan take ban son ajiyar mayya a cikin masarautata ” Sarki Haroon ya kafe ta da ido yana kallo kafin ya ce “ki amsa laifinki sannan ki tuba ki rungumi addinin Musulunci domin tsira da ranki” “Babu wani addini da zan shiga,na fi son zama babu alƙibla.Sannan kuma ni ba mayya ba ce duk da ina da ilimin sarrafa maitar,maganar ƙarshe kuma ita ce zan koma gida” Rai ɓace yarima Naslam ya zaro takobinsa da niyyar sauke mata kai amma jakariya Ali yayi saurin riƙe shi yana cewa “ka nutsu yarima kar ka yi saurin yanke mata hukunci jira na kira Barham” Zuciyarsa na ƙuna ya ce “ba ka ji yadda take magana ba sam babu ɗa'a?” bai ma kai ga cewa wani abu ba Barham ɗin ya shigo. Kallo ɗaya ya yi wa matar ya gane wace ce ita,hakan yasa ya ƙarasa gun sarki yana mai yin ƙasa da murya ya ce “kar ku kashe ta,za ta yi mana amfani a nan gaba” sosai sarki yake ɗaukar shawarar Barham saboda shi ɗin aminin mahaifinsa ne sannan kuma dattijon arziki na masarautar. “Ku mayar da ita” sarki ya faɗa wanda hakan sam bai yi wa yarima daɗi ba sai kawai yayi zuciya ya fita daga wurin. Jakariya Ali ya bi bayansa yana mai cewa “ gaggawa aikin sheɗan ne,matar can tana ɗauke da wani ɓoyayyen sirri wanda nake jin cewa ita ce makullin da za mu yi amfani da shi wurin buɗe duk wata ƙofa da ta yi mana wuyar shiga” Ba tare da yarima ya ce masa wani abu ba ya soma cire kayansa na sarauta yana ajiye wa.Toilet ya shiga ya soma yin wanka ko zai ji sassauci,har ya fito jakariya Ali na nan.Shi ne ma ya taimaka masa wurin tsane jikinsa ya saka kayan zaman gida,daga nan sai suka wuce can inda tantabarunsa suke. Yana son tsuntsaye, wannan yasa ko ƙunci yake sai ya ziyarce su yake jin daɗi.Jakariya Ali ya buɗe su,da gudu kuwa duk suka shiga fitowa suna nufo shi,ɗaya ta sauka kan kafaɗarsa ya kai hannu ya damƙo ta yana shafar jikinta yana murmushi. Sai ya ji kamar ana kallonsa,ido ya baza cikin tantabarun nan idonsa ya sauka kan baƙuwar tantabara idonta ƙurrr kansa.Kasancewar bai yarda da canfi ba sam bai kawo komai a ransa ba,haka ya ratsa ya je ya ɗauko ta wani irin shock ya ratsa shi nan ɗin ma bai sa a ransa wai lamari ne da ya shafi sprituality ba. Jakariya Ali ne kawai ya farga da abin da ke faruwa,amma kuma sai ya ja bakinsa yayi shiru.Duk yadda yarima ya so tantabarar ta saki jikinta amma abu ya cuttura kawai sai ya wuce da ita can ɗakinsa yana mai cewa “ban san daga ina ita wannan ta zo ba,da alamu ta ƙi sabawa da sauran ne” Jakariya Ali ya ce “ dama ai kullum cikin samun baƙi tantabaru ake yi,ita ma za ta saba” Cikin ɗakinsa ya sake ta,ai kuwa sai ta shiga yin walwalar. A can ɓangaren gimbiya A'ishah kuwa abubuwa ne duk suka dagule mata,ga rashin ƙawarta Jamila ,ga ɓatan Dadda kusan kwana uku har yanzu ba ta dawo ba,ga kuma yanayin jikinta da take jin ya sauya.Zaune ta yi cikin halin ƙaƙanikayi tana wasiƙar jaki,sai ta ji ana magana ƙus-ƙus ba ta jin abin da ake cewa, da ta nutsu sosai sai ta gane a cikin drower kayanta.A hankali ta je ta buɗe,ɓerayen da suke gurgurar kayanta suka saki ihu a tare wannan karon sarai ta ji abin da suka ce. “Wayyo an kama mu yanzu an yi ƙoƙarin kashe mu” shi ne abin da ɓerayen suka faɗa kafin su fara gudun tsira,har kan ƙafarta ɗaya ya faɗo amma ta kasa yin motsi saboda shock.Ita maitarta iya ta juya baƙi ya dawo fari ce,sai ga shi yau ta ƙara samun matsayi.Jikinta ne ya hau rawa,babu shiri ta nufi ƙofa don zuwa wurin Barham ta sanar da shi sai kuma ta yi kiciɓis da Dadda wacce ta dawo daga jejin Mayu.Da sauri ta ja baya,ita kuwa murmushin mugunta ta sakar mata tana mai cewa “Allah yasa dai ba ƙoƙarin tonawa kanki asiri kike yi ba? To ki sani muddin yarima ya ji labarin ke mayya ce to zai fasa aurenki, ba kuma zai yi jinkiri sauke miki kai ba kin fi kowa sanin halinsa fiye da ni yadda bai da tausayi akan mayu” Idon gimbiya A'ishah ya kawo ruwa,yanzu ne kawai ta yarda da maganar Barham .Tabbas a matakin da take a yanzu ta riga da ta makaro babu ta yadda za a yi ya cece ta. Dadda ta ci gaba da yi mata gargaɗi mai ban tsoro,“ in kuma kin shirya yin mutuwar kare sai ki je ki faɗa ,sanin kanki ne hatta sarauniya Sarat ta bar masarautar nan saboda laifin maita ballantana ke karan kaɗa miya ” “Amma Dadda ni ban ce miki ina son zama mayya ba,don me za ki bani kambunta?” gimbiya A'ishah ta faɗa . Dadda ta bata amsa da “saboda duniyar nan muddin babu maita da Magic to tamkar miya ce babu magi,ki zo na nuna miki mece ce ainihin rayuwar Mayu na tabba in kika ga irin shagalin da ake yi ke kanki za ki ji daɗi ki kuma gane gata ne na yi miki ” shiru gimbiya A'ishah ta yi kafin ta je da gudu ta rungume Dadda. ★YANKIN MUTUWA Zuwan baƙuwar haure daga duniyar turɓaya shi ya canza mana yanayin shigarmu.Na ajiye fatar dabba na koma saka kaya,waɗanda Banah ne da kansa ya shiga duniya shi da sauran matsafa suka kwaso su a can duniyar tuɓaya.Kai tsaye za a iya cewa suka sato,saboda dare ne suka bi suka dinga shiga kanti suna ɗebo kaya bayan an kawo haka aka zube su aka rabawa kowa ciki kuwa har da ƴar jaririya da na samo wacce har zuwa yanzu ba a saka mata suna ba. Ummilo shi ne sunan da nake yi wa matar wacce duk ƙoƙarin Banah na son saka mini tsanarta bai yi nasara ba. Zaune na yi ina kallon yadda take bai wa baby madarar da aka tatso daga dabbobi.Hannu na kai na shafi fuskar Babyn ina mai cewa “Ummilo wane suna kika zaɓa mata?” Ta yi wani murmushi mai ƙayatarwa kafin ta ce “ina son sunan Jamila saboda na riƙi ƴa mai irin sunan nan” sai kuma ta yi wani irin shiru kamar mai yin nazari,a nan ne na fahimci cewa kamar ƙwaƙwalwarta na son tuna wani abu da ya danganci rayuwarta. Ina shirin yin magana sai gani na yi gari ya ɗau wani irin duhu,yayin da kuma mutanen da na zube suna yi mini hidima suka soma yin ihu.Duk yadda na so yin tsafi abu ya cuttura,kamar minti biyar sai komai ya dawo normal.Idona na sauke ƙasa sai na ga duk ɗigon jini ne ta ko ina kamar an yi ruwansa,ina ɗago kai kuma muka haɗa ido da Banah fuskarsa kicin-kicin kafin ma na kai ga tambayarsa sai cewa yayi “ tun da kika shigo da jaririyar nan a yankin nan bala'i ya soma sauka,don haka mun yanke shawara ni da sauran matsafa za mu bayar da jininta matsayin hadaya ga ruhikan ruwa........ [12/06 12:37] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐 """"""""""""""""""""""" LoVe aNd HoRrOr StOry☠️ ```MRS SADAUKI```💫✍️ FCWA☀️ ____________________________________________ 08 “Ta ya za ka ce a ɗauki jaririya a kai wa Teku matsayin hadaya? Wannan sam ba mai yiyuwa ba ne.Wannan al'amarin da ya faru kuma ko kaɗan bai da haɗi da da jaririya Mila wani baƙin ƙulli ne daga maƙiya kuma zan binciko na gani duk masu hannu a ciki” na faɗa . Banah ya ƙanƙance ido yana kallona,na je da sauri na ɗauki Mila daga kan cinyar Ummilo na goge mata fuskarta da yayyafin jini ya ɓata.Can ɗaki na yi tsinke,ina daidaita mata kwanciya ya shigo yana mai cewa “ita kuma Ummilo sai yaushe za ta tafi tun da kin karya doka kin ce ba za a kashe ta ba” Ba tare da na juyo ba na basa amsa da “ nan ɗin masarautata ce,Ni ke da ikon barin wanda zai zauna da kuma wanda zan kashe,ka tsaya iya matsayinka na mijina in ina son shawarinka ni ce da kaina zan neme ka” Cike da takaici Banah ya fito daga ɗakin ya jefi Ummilo da wani mugun kallo wacce yake jin tsanarta sai dai fa alƙaluman tsafinsa sun kasa rubuta sunanta .Direct can bayan gari ya nufa,bai yi nisa ba ya soma furzo kalaman tsafi nan take busashen ganyen da ke zube a ƙasa ya soma tashi sama kafin kuma ya haɗa wata baƙar guguwa wacce ta yi ambaliya da gangar jikinsa ya ɓata .Cikin wani kogo ya bayyana mai ɗauke da kunamu baƙaƙe ƙirin kuma ga su manya-manya.Suna ganinsa duk suka soma basa hanya,shi kuwa haka ya dinga ratsa tsakiyarsu har ya isa can ƙarshen kogon inda wata halitta ke kwance tana ƙyafta ido kamar mai jin tsoron buɗe su ɗin. Zubewa yayi yana mai yi mata sujuda ba tare da kuma ya ɗago ba yake cewa “kin ce in na dinga shayar da ke jini za ki ɗaga martaba ta fiye da duk wani mai iko a duniyar nan,amma me yasa Naomi ke yi mini gardama akan hukuncin da na zarta alhalin hatta maganin laƙani na sa an shayar da ita shi” Ba ta basa amsa ba,sai fara saukowa da ta yi daga kan dutsen da take kwance ta zo ta fara hawan bayansa tare kuma da laulaye shi da bindinta.A hankali ta zagayo kanta kan ƙirjinsa,babu ɓata lokaci kuma ta buɗe bakinta tare da kafa masa haƙoranta masu mugun tsini ta soma tsotsar jininsa na wani lokaci kafin ta tashi sama tana wani irin kuka kamar jiniya.Dukkan kogon ne ya tsaya cak kamar babu wata halitta mai numfashi,muryarta ta soma fitowa “ka karya dokata,na faɗa maka duk wacce za ka aura to ya zama dole ka yi tarayya da ita a wannan daren sannan ka bani jinin budurcinta.Tun da har ka bijire to ya zama dole a gare ka da ka yi haƙuri da wasu ƙananun al'amurra.Sannan ita wannan mata da kake tsana ta kasance shugaba ce a wata mazaɓar duniyar ruhaniya muddin ka yi kuskuren cusa kanka a lamarinta to za ka tsinci litininka a laraba ” Sai da ta dire kalamanta sannan Banah ya ɗago,idonsa sun kaɗa sun yi ja kamar na baƙin maye.Aljana ZAƘUMA ta soma saukowa daga can saman ta zo dab da shi ta na hura ƙirjinsa wanda ya fitar da sawun haƙoranta,sai kuma ta ci gaba da cewa “a jefa jiragai cikin ruwa domin fara saye da sayarwa tsakaninku da wasu garuruwa,ta wannan hanya ce zan samu yadda nake so” tana gama faɗar haka ta cillo shi tsakiyar gari.Bai ma koma can gida ba ya wuce gaɓar ruwa,sai ya tarar da manyan jiragai guda biyu.Tsaye yayi ya lumshe ido tare da soma yin magana da ruhikan ruwa,bayan sun amsa masa ne ya tsaga yatsansa jini ya zuba a cikin ruwan da kuma jiragen. ★Naomi Bayan fitar Banah kalar nawa tsafin na yi don binciko su wane ne suka fara yi mini zamba cikin aminci,sai dai babu wanda aka nuna mini fuskarsa illa aljana ZAƘUMA.Banda ilimin tarihi wannan yasa ban san wace ce ita ba,haka na fito na samu Ummilo na tambaye ta. “Babu matsafin tarihi a wannan yanki naku?” ita ce tambayar da ta yi mini. Na ce “akwai sai dai mun yi kare jini,biri jini da ita kwanan baya” Ta ce “ke ce shugabar duk wani da ke garin nan,don haka ki aika kawai ta zo” na yi shiru na wani ɗan lokaci kafin na ga kuma eh ta yi gaskiya. Takarda na nemo da tawada na soma yin rubutu,bayan na gama sai na dinga murza ta ina yin furucin tsafi a hankali babu jimawa kuwa takardar ta fita daga hannuna ta yi sama.Ido na birkice ta yadda komai zai wakana ina gani,cikin aminci Deborah ta samu wasiƙar na yi tunanin ba za ta zo ba sai ta bani mamaki kuwa yadda ta ɗauko hanyar zuwa nan tana tafe iska na ƙara yin gaba da ita. Tana isowa ciki sai na ga ta yi tsaye tana kallon Ummilo kafin da sauri ta buɗe kuɗin da ke rungume a ƙirjinta.Sai ta rufe shi tare da sake kallon Ummilo cikin wani irin yanayi ,kamar wacce ba ta son taka ƙasa haka ta ƙaraso tare da yin tsaye. “Ranki shi daɗe ga ni na samu saƙonki ne a yanzu” ta faɗa cike da ladabi,sai kuma na ji babu daɗi yadda ta zubar da duk wata dangantaka da ke tsakaninmu ta bani matsayin shugabarta. Da ido na yi mata nuni da ta zauna,ta cire takalminta na fata ta zauna tare da maida hankalinta a gare ni. “A cikin tarihi wace ce aljana zaƙuma?” “Aljana ce mai matuƙar santsi da farin fata,tana ɗauke da kambun Maitar shan jini.Lokutan da ta fitowa shi ne dare musamman wuraren jeji ko kusa da rijiya.Tana jan hankalin mazaje musamman maharba don su ne suka fi shiga jeji,tana fitowa cikin siffar barewa haka za ta yi ta wasa da hankalin maharbi har sai ya faɗa tarkonta sai ta ja shi izuwa duniyarta” Deborah ta faɗa tana mai buɗe littafinta sai ta nuno mini hotonta,kallo ɗaya na yi masa na kawar da kai.Sosai ta fito a siffar mayyar shan jinin kuwa don bakinta kaca-kaca yake da jini. “Kika ce maharba sun fi shiga tarkonta ?” na tambaya. “Eh haka tarihi ya zo da shi” “Meke faruwa bayan ta kama mutum?” “Tana kai shi wani kogo ne,sai ta basa zaɓi biyu.Na farko zai bauta mata,in kuma ya ƙi zaɓi na biyu shi ne za ta kashe shi” Ummilo na duba ina mai cewa “dukkan alamu sun nuna ita ce ta zo yau don har yayyafin jini aka yi” “Hakan na nufin tana son jan ra'ayin wasu mazajen ne ,don haka mu zama cikin shiri” Ummilo ta faɗa . Deborah ta girgiza kai tana mai cewa “ Aljana ZAƘUMA ba ta taɓa bayyana a wurin da ba a ambace ba ko kuma sunan ɗaya daga cikin waɗanda ke baƙin tsafi da ita.Tun da kuka ga ta zo to tabbas a garin nan akwai mai yin aiki da ita” Da wani mugun sauri na dube ta,a cikin ƙwayar idonta na hango tana zargin mijina Banah da wannan ɗanyen aikin.Ban san me ta gani ba ita a nawa idon sai ci gaba ta yi da cewa “ta yiyu kuma wucewa ne kawai ta zo yi,don haka za ki iya yin watsi da lamarin mu gani in za ta sake dawowa” Numfashi na furzar tare da jinjina kai,Ummilo ta karɓi littafin tarihin tana mai cewa “ina mugun son labarun tarihin ƙarnin da ya wuce musamman a kan maita,shin a page lamba ta nawa ce zan samu tarihin Mayu da kuma yadda suke rikiɗa daga bil'adama zuwa dabbobi?” Deborah na shirin yin magana Banah ya shigo hannunsa riƙe da manyan kifaye,da dukkan alamu kuma ya ji tambayar da Ummilo ta yi duba da yanayin yadda fuskarsa ta cika da tsantsar mamaki. “Jira na zo na fayyace miki komai Ummilo ” ya faɗa yana mai miƙawa wata hadima kifin ya zo kusa da ni ya zauna sannan ya karɓi littafin tarihin ya mayar wa Deborah da kayanta sannan ya kamo dukkan hannuwan Ummilo ya ce “a duk lokacin da mutum yake son rikiɗa zuwa dabba da farko zai ɗan rage tsayi sannan ya furta kalaman tsafi yana mai tsayar da ƙwayar idonsa wuri guda ba tare da ya ƙyafta ba.Bari na nuna miki ta yadda za ki gane sosai” sai ya saki hannuwanta tare da yin tsugunne ya soma magana a hankali amma duk muna iya jiyo sautin.Cak kuwa ya tsayar da idonsa suka bar motsi,babu jimawa ya koma narkeken kare baƙi ƙirin yana wani fito da harshe waje. Duk da ni ma yau ne karon farko da na ga canjin siffa sam ban ji wani tsoro ba sai ma burge ni da lamarin ya yi na soma yin murmushi. Cikin firhici Ummilo ta furta “ Ya Ubangijin Ka'aba ka tseratar da ni daga sharrin wannan halittar” sai kuma ta soma yin ihu tare da tashi za ta zuba a guje,ni da Deborah muka yi saurin taro ta yayin da Banah ya yi baya yana haushi cikin hassala. Hakan da yake ba ƙaramin ƙara firgita ta ya yi ba,ni kuma lura da hakan yasa na juya na yi masa tsawa sai a lokacin kawai ya dawo cikin siffar bil'adama. Ummilo ta soma furzo wani zance “kar ki cutar da ni Ummu A'ishah ki sani ban taɓa aikata maita ba,wacce ke maƙale a ruhina ba sayenta na yi ba kyauta ce daga wasu ruhikan da ke zuwa mini cikin MAFARKI (MRS SADAUKI akwai littafin nan na MAFARKI complet mai so zan barsa shi a 700 maimakon 1k) .Ban so ki bari in ba haka ba zan tona miki asiri na faɗa kowa ya sani ke ce mai yin Maitar dare” tana kawowa nan sai numfashinta ya tsaya cak sai da muka tallabe ta tare da shimfiɗe ta. Deborah ta ce “ da dukkan alamu ita ma ta fito a yanki da ke maita duk da dai a yadda take furuci Maitar ba ta yi ƙarfi ba.Sannan ita wannan Ummu A'ishar tana ɗaukar siffar kare ne a duk lokacin da za ta yi maita ” Banah ya matso yana cewa “ai da na san haka ne da na ɗauki wata siffar,amma sam ban yi haka da wata manufa ba” Na ce “kar ka damu na fahimta,daga yau sai ka kiyaye” ya jinjina kai. Deborah ta ce “ni zan koma,in ta farka ki ce ina yi mata sannu da jiki” haka muka rabu. ★ Yarima NASLAM ne kwance yana yin bacci yayinda tantabarsa ke tsaye ƙiƙam tana kallonsa sai da ta gaji don kanta kafin ta ɗaga fukafukinta ta je ta sa ƙafafunta ta ciro shi sama tare bi ta window da shi ta fita.Haka ta dinga zaga duniyar ɓoye da shi yana cikin wani yanayi wanda shi ba bacci yake yi ba kuma idonsa ba a farke ba. Cikin wani jeji mai cike da dragon ta sake shi ,shuuu yayi kamar zai faɗi amma sam jegaran ba su bari hakan ta faru ba haka suka buɗe fukafukinsu wuri ɗaya ya faɗo a sama. Kafin kuma su kai shi kan wata lafiyayar shimfiɗa da aka yi da ganyen furen floris. Yarima NASLAM ya ja wani dogon numfashi tare da ɗan ware idonsa,nan ne ya yi arba da sarauniya Naomi cikin shigar ganye,ta rufe ƙirjinta da fatar lemun zaƙi kugunta kuma ta suturta shi da bayan albasa.Gashin kanta kuwa ya ci ado da ganyen lemu,tafiya take yi cikin yanga da jan hankali har ta zo gare shi.Kan shikinsa ta kwanta tare da yi masa rumfa kafin wasu lamurra su biyo baya waɗanda suka kusan sheƙa shi lahira.Yana gama samun nutsuwa ya farka daga baccin,a kan shimfiɗarsa ta asali ya samu kansa ƴar tantabarsa na can gefe tana bacci. Ya dafe kansa yana jin wani irin takaici na rufe shi,saboda shi babu wacce ya tsana irin aljanar mafarkinsa.A gajiye kamar wanda yayi mu'amalar a gaske ya ƙoƙarta ya tashi tare da shiga toilet,sai dai fa babu ruwa ba ciki babban bokitin ruwan ba.Ya ja tsuki ya fito kafin ya soma ƙwala kiran sunan jakariya Ali,dama ɗakinsa yana kusa da nasa babu jimawa kuwa ya shigo hannunsa riƙe da sharɓeɓiyar takobi duk a tunaninsa farmaki ne aka kawo musu. Turus yayi ganin iya yariman ne kawai a ɗakin,ya yi saurin ajiye takobin yana mai cewa “ranka shi daɗe me kake buƙata?” “Babu ruwa a banɗaki” yarima ya faɗa yana jin ƙyanƙyamin kansa,da sauri jakariya Ali ya fita babu jimawa ya dawo jaye da baro an lodo ruwa a ciki.Banɗakin ya shiga ya juye ruwan kafin ya fito,sai a lokacin yarima ya shiga sai ya ga hatta bahon wankan Ali ya cika masa shi da ruwan. Kwanon da ake zuba ruwa a ciki domin yin alwala ya ɗauka ya soma wanke hannunsa sau uku bayan ya ɗauki niyyar wankan.Daga nan yayi ɗahara sai ya wanke kansa tasss kafin ya game jikinsa duka,daga ƙarshe ya kurkure bakinsa ya kuma yi shaƙar hanci.Sai a lokacin kawai ya ji nutsuwa ta ratsa shi sai ya shiga bahon wankan ya kwanta a ciki,tunanin gimbiya A'ishah yake son yi amma da zarar ya fara cankar surarta sai fuskar Naomi ta zo ta yi fakan-fakan a dole ya haƙura ya fito ya ɗaura alwala ya zo ya fara yin sallar nafila. A ɓangaren gimbiya A'ishah kuwa tsakiyar dare Dadda ta tashe ta,tana shirin yin magana amma Dadda ta toshe mata baki tare da janta suka je bakin window suka yi tsaye suna fuskantar farin wata da ke wasar ɓuya cikin giza-gizai. Dadda ta soma yin magana a hankali tana cewa “a wurin Mayu dare shi ne lokaci mafi tsaro domin farauta,duk da cewa ana iya sarrafa maita safe ko rana amma irin wannan lokutan an fi yinta a cikin siffar bil'adama yayin da ita kuma ta dare ake ɗaukar ɓoyayyar siffa.Yau zan nuna miki romon da muke sha duk dare ni da sauran Mayu na wannan Daular ” Cike da mamaki gimbiya A'ishah ta ce “dama bayan ke akwai wasu Mayu a cikin daular nan?” Dadda ta yi wani irin murmushi kafin ta ce “idonki za su yi matuƙar mamaki in ki ka ga wasu mutanen” tana gama faɗar haka sai ta jimƙe hannun gimbiya A'ishah tana furta wasu surkulle nan take suka sama wasu ƴan ƙananu kamar sauro tare da tashi sama suka bi ta window..... Za ku iya fara yin payment domin shiga paid group . 500 ta wannan account: 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank Shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 [12/06 12:37] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐 """"""""""""""""""""""" LoVe aNd HoRrOr StOry☠️ ```MRS SADAUKI```💫✍️ FCWA☀️ ____________________________________________ 09 Yana ɗaya daga cikin tabi'un Mayu yin yawon dare a lokacin da mutane ke yin bacci,saboda babu dare yana ƙunshe da sirrika dayawa.Gimbiya A'ishah baki da hanci ta buɗe tana kallon duniyar ƙasa,cike kuma da burge wa da ban sha'awa take ware idonta tana kallon gidajen da aka rufe babu bismillah.Kamar misalin tukunya ce babu murfi,haka idon Mayu ke gane gidajen da ba a ambaci sunan Allah ba a lokacin da ƙafa ta tsana za a kwanta. Suna cikin shawagin suka yi ta haɗuwa da jiragen dare na Mayu, waɗanda suka kasance na tsafi ba wai zahiri ba. “Duk ina za su je Dadda? Ya na ga mutane cikin gwangwanin kifi?” gimbiya A'ishah ta tambayi mahaifiyarta sai dai kafin ma ta bata amsa wani jirgin na tsintsiyar tsaye ya bi ta gabansu shuuu yana ɗauke da wata tsohuwa da kuma ƙaramin yaro. Dadda ta yi murmushi tana mai cewa “A'ishah a duniyar ɓoye abubuwan da ba za su taɓa faruwa ba ne a duniyar zahiri suke gudana a nan ɗin.Muna amfani da duk wani abu da kika sani matsayin jirgin farauta,kamar irinsu turmi,jan zanen isimi,tsintsiyar tsaye da sauransu.Ke ma in kina sha'awa ai za ki iya hawa madadin ki yi yawo kamar leda” “To mene ne banbancinsu Dadda?” “Sauri! In kin hau jirgi kin fi saurin zuwa inda kike so,ko ba ki lura yadda mutane ke ta wuce mu ba?” “Na gani,amma me yasa mu ba mu shiga ba?” “Dama ina son fayyace miki komai ne,amma yanzu da zarar wata tawagar mayun za ta wuce zan tsayar da su don rage mana hanya” Ai kuwa babu jimawa sai ga wata tsohuwa zaune kan baƙar akuya mai ƙahonni dogaye.Dadda ta tsayar da ita tare da neman alfarma,tsohuwar ta ƙara matsawa gaba gimbiya A'ishah ta fara hawa sannan Dadda daga ƙarshe.Kamar wani babur haka akuyar tsafin ke keta hazo da su. Gimbiya A'ishah wacce duniyar ɓoye take sabuwa a wurinta sai cewa ta yi “ita ma akuya tana cikin jerin jiragen yawo?” Wannan karon tsohuwar ce ta bata amsa bayan ta yi ƴar dariya mai fitar da zallar tsufanta,ta ce “ jikata ita akuyar nan protector ɗina ce,suna da banbanci da jirgin dare saboda ita tana numfashi sannan kuma tana kare ni daga dukkan sharri” gimbiya A'ishah ba ta kai ga cewa wani abu ba tsohuwar ta yi ƙasa da ƙahonnin akuyar sai ta yi shuuu ta fara yin ƙasa har ta sauka a wani babban gawo wanda ya cika tanƙam da Mayu da kuma matsafa. Girki ake yi kan wata tunkunya wacce ke da zanen ƙwarangwal ta buɗe baki.Gimbiya A'ishah ta sauko daga kan akuyar tana wani riƙe Dadda ,ita kuwa sai cewa ta yi “ wannan ita ce TUKUNYAR MAYU ( ga mai son complete na Tukunyar Mayu yayi mini magana zan yi masa discount) duk dare muna haɗuwa a nan mu ci abin da wasu daga cikinmu suka yo farauta” Sai kuma Dadda ta ja ta suka ƙarasa,hannu ta saka cikin tukunyar da ke ta faman tiriri ta tsamo wani abu mai kamar zare amma su a wurinsu nama ne,bakin gimbiya A'ishah ta kai ita kuwa ta buɗe ta saka mata sai ta soma ci tana jin wani irin yanayi na ratsa ta. Dadda ta saki murmushi tana jin wani sanyi na luluɓe ta,a yanzu shirye take tsaf wurin tursasa ƴarta ta auri yarima Naslam ba don komai ba don ta san a cikin tabi'ar Mayu babu kara babu jin kunya,hatta uwar da ta kawo su duniya suna iya damƙewa ita kuma babban burinta shi ne ta bayar da yarima NASLAM a dafa shi kowa ci kamar yadda yasa aka yanke wa Ummarta hukunci kisa daga kawai asirinta ya tonu ta damƙe kurwar iyayen jakariya Ali. Bayan sun gama cin naman sai idanun gimbiya A'ishah suka ƙara buɗewa ta soma gani tarau ,babu abin da ba ta iya gani da ke jikin mutum ko dabba.Rawa suka soma yi suna zagayen wuta,duk da mutane sosai hakan bai hana ta gane wasu fuskokin ba sosai kuma ta yi mamaki kamar yadda Dadda ta ce mata tun kafin zuwansu. Alfijir na dab da ketowa suka koma gida,ta inda suka fita ta nan suka shigo.A gajiye duk suka zube suka ta yin rankon baccin da ba su yi ba. A ɓangaren yarima Naslam kuwa tun bayan sallar asubah ya je ya samu sarki da maganar aurensa da gimbiya A'ishah.Ya yi haka ne duk don ya bar mafarkin Naomi,ba tare da ya san alƙaluman ƙaddara sam ba su rubuta masa auren wata mace ba bayan maƙiyiyarsa. Gari na yin haske sosai sarki ya bada shelar baikon yarima zai kasance a yau bayan sallar asar in sha Allah. Jakariya Ali ne ya dinga taimaka masa wurin shiryawa,yana daidaita masa hullar sarauta a kai ya ce “kana ganin kun dace kai da gimbiya A'ishah?” “Me ya ja ra'ayinka wurin yin wannan tambayar?” cewar Yarima yana kallon mai tsaron lafiyarsa Ali . Shi kuwa kai tsaye ya ce “na ga ba sonta kake yi ba” “Haka kuma ban ƙinta“ “Duk da haka dai ya kamata a ce ka yi dogon nazari,na fi yi maka sha'awar auren soyayya gaskiya” “Ita ma ina sonta tun da har na damu da ita” yarima ya faɗa yana mai zuwa bakin gado ya yi zaune,jakariya Ali ya duƙa ya soma saka masa takalmi yana mai cewa “in kana son mutum bai kai sai ka faɗa ba,ayyukanka ne za su bayyana hakan” “Ko ma dai mene ne na yanke shawarar zan aure ta,kuma ta dace da ni tun da tana da addini sosai iya wannan ya wadatar” yarima ya faɗa yana tsayar da idonsa kan tantabarsa wacce ta yi wani saƙo kamar mai sauraren hirar da suke yi. Jakariya Ali ya juya ya dubi inda yake kallo,sai ya saki ɗan murmushi kafin ya je ya ɗauko ta ya miƙawa yarima.Ya karɓa tare da soma shafar kanta,“zan je na duba na gani in sun gama shirya wurin taron” Ali ya faɗa tare da ficewa. Yarima ya miƙe tsaye tare da zuwa bakin window yana kallon yadda ake ta kai komo cikin masarautar.Ko ina yayi kyau,hatta dawakai an yi musu ado na sarauta .Dokinsa wanda yake hawa a duk lokacin da zai fita yayi wani irin kuka,tantabarar hannunsa ta fizge tare da fita a guje tana kaɗawa yarima iskan fukafukinta da sauri ya lumshe ido kafin kuma ya ware su yana kallon yadda ta je ta hau kan dokin,duk wannan ɗin ma bai sa ya zargi wani abu ba kawai murmushi ya yi tare da fita. Masjid ya fara zuwa,bayan an gama sallah ne duk aka dugunzuma zuwa wurin da aka ware domin gudanar da shagalin bikin baikon. Zinare sarki ya ware masu yawa ya bayar matsayin kyautar mun gani muna so.Ayyub wanda ya kasance mahaifin gimbiya A'ishah da matuƙar farin ciki ya shaida wa dukkan taron jama'ar ya bai wa yarima damar auren ƴarsa,duk sai aka yi kabbara tare kuma da yin addu'o'i kafin a fita zuwa can inda za a yi wasar dawakai. Ta madubin tsafi Dadda ke kallon komai,tun lokacin da aka yi shelar yin baikon ta shirya baƙin tsafi mai ƙarfi ta tura domin hallaka yarima.Ita dai gimbiya A'ishah cike take da farin ciki duk gajiyar nan ta jiya sai ta neme ta duk ta rasa,duk da cewa kuwa ta sha bacci sosai sai wuraren goma na safe ta farka.A bakin mahaifiyarta kuma ta ji abin da ke faruwa,sosai ta so a ce ta fita ta ga yadda komai ya wakana sai dai hakan haramun ne a masarautarsu zuwan mata a irin wannan taron. Cikin rangaji ta ƙaraso ta zo ta yi tsaye ita ma tana kallon yadda ake wasar tseren .Wani irin murmushi ya suɓuce mata lokacin da ta ga yarima Naslam ya je kusa da dokinsa za su yi wasar tseren shi da wanda ya yi nasara akan dukkan dakarun da aka tsara wasar da su.Ita ma Dadda nata murmushin ta saki tana jin cewa saura ƙiris burinta ya fara cika don ta jefa kibiyar tsafi akan dokin yarima saboda in ya hau shi sai ya masakance. Yarima ya hau kan doki yana mai ambaton sunan Allah tare da yin kabbara,Dadda ta ɓata fuska tana mai ɗan satar kallon gimbiya A'ishah wacce har yanzu murmushi ya ƙi barin fuskarta. “Dadda dube shi ki ga yadda yake da ƙwarjini da cikar zati, wannan shi ne mijin A'ishah ” “Haka ne ki yi fatan Allah yasa ya ci gasar kar ya kwabsa abin ya zama abin goranta miki” Dadda ta faɗa tana mai shafar madubin haɗi da yin wani surkulle daidai nan su yarima suka fara gudun.Ƙafar dokin ta ƙure da ido ta na shirin aika masa wata gubar tsafin kawai sai ganin bakin tsuntsuwa ta yi ya caki madubin ya tarwatse. A tare suka ja ba,kafin su kalli juna.Da wani irin gudu kuma gimbiya A'ishah ta fita don jikinta ya bata babu lafiya,mayafinta ta ja ta rufe fuskarta lokacin da ta isa filin sukuwar. Yarima NASLAM wanda ya lashe wasar tseren dokin ya juyo yana kallon inda take a tsaye,suka haɗa ido da sauri ta sunne kai tana wani murmushi kafin ta juya da sauri ta koma.Ya ja numfashi yana jin a ransa ya yi dacen mata. ★ An ɗauki tsawon lokaci kafin Ummilo ta farfaɗo wannan karon ma tana yin wasu kalamai a cikin Yaren da ban fahimci me take nufi. “Alhamdulillahi lazhi ahayana ba'ada ma'amattana wa'ileyhi nushur” ta furta tare da ware idonta a kaina,na sakar mata murmushi na ce “sannu Ummilo” ba ta amsa ba sai martanin murmushin da ta maido mini tana mai shafar gefen fuskata kafin kuma ta miƙe ta fita.Haka na take mata baya sai na ga ta shiga banɗaki,can kuma ta fito ta soma wanke hannuwa da baki da fuska da hannuwanta hatta kai da kunne sai da ta shafa haɗi kuma da wanke ƙafafu. Mayafinta ta gyara kafin ta zo ta fara yin wata irin bauta da ban san ta mece ce ba,ni dai ido kawai na tsura mata da na ga ba ta da niyyar idawa kawai na je gun baby Mila na ɗauke ta dama tun ɗazu ta tashi.Madara na soma bata tana sha tana kallona cikin ido, murmushi na saki ina jin sonta na ratsa ni. Banah wanda tun bayan abin da ya faru ya koma can ƙofar gida yayi tsaye,sai yanzu ya shigo yana mai tambayata “mene ne can Ummilo ke yi?” “Ina kifin har yanzu ba a gama dafawa ba?” na tambaye shi ,don sau tari in yayi mini tambayar da raina bai so ba nuna masa nake yi kamar ban ji ba sai na ɗauko masa wani zancen. Fita ya yi ba tare da ya ce mini komai ba,can kuma sai ya dawo riƙe da kwano yana tiriri.Kamshin kifin ya daki hancina,nan take yawuna ya tsinke sai na shimfiɗe Mila na karɓa na soma ci shi kuma Banah yana aukin kallona.Ina gama ci na ji wata kasala ta rufe ni,sai na kwanta ni ma sai a lokacin kuma Ummilo ta shigo. Banah ya ce “ga kifi nan da Naomi ta rage ki ci” Da fara'a kuwa ta karɓa tare da gyara zama ta sa hannunta,sai dai fa ta gagara ci sai yamutsa fuska take haɗi da yunƙurin kai shi bakinta.Can dai ta haƙura tare da ajiye kwanon tana mai girgiza kai ta ce “in na ci wannan ai tamkar na cinye kaina ne,a'a sam maita ai ba hauka ba ce da zan ci jinsina ” Banah ya ƙanƙance ido yana kallonta kafin kuma ya fice ya bar mu.Maƙoshina ne na ji yana wani irin zafi kamar ana hura wuta,murya kamar ta mai koyon magana na ce “Ummilo sanyi nake ji ki rufe ni” sai kuwa ta miƙe ta ɗauko bargo ta luluɓa mini.Daga wannan kwanciyar ban ƙara farkawa ba sai washegari da zakara ya fara cara,na buɗe idona da suka yi mini nauyi kafin na yunƙura zan tashi sai dai na kasa sakamakon bayana da na ji ya riƙe kafaɗata ta ƙara nauyi. “Banah?” na kira sunansa kasancewar ni da shi ke kwana a ɗaki ɗaya,Ummilo kuwa cikin jerin ɗakunan da aka yi daga baya take kwana ita da Mila. Shiru ban ji motsinsa ba,sai na ƙara yunƙurin tashi a wannan karon gangar jikina ta baro shimfiɗar sai dai na gagara tsayuwa kan ƙafafuna na faɗi kwacaaa.Jeren kwanukan da ke ɗakin duk ya baje,ƙarar ta jawo hankalin Ummilo ta shigo tana tambayar lafiya sai dai muna haɗa ido da ita ta ɗau haske.Da sauri ta zo ta taimaka mini na miƙe tsaye tare da riƙe ta gam,murya na ɗan rawa na ce “ki kai ni banɗaki na yi wanka” ita ce ta kai ni,sannan kuma ba ta fito ba sai da ta yi mini wanka.Bayan ta saka mini kaya sai ta miƙo mini wani icce ta ce na riƙe,na karɓa ina jin ƙusumbina da ya ƙara girma ya rinjaye ni na yi mini wani motsi..... My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [12/06 12:37] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐 """"""""""""""""""""""" LoVe aNd HoRrOr StOry☠️ ```MRS SADAUKI```💫✍️ FCWA☀️ ____________________________________________ Daga yau discount ya ida. Last free page 10 Wata rusunawar dole ce ta zo mini saboda girman ƙusumbina ya wuce a yi kwatance sam tsayuwa ko tafiya babu sanda ba zai yiyu a gare ni ba.A haka na fito daga banɗakin ina jin wasu canje-canje na daɗa ƙaruwa a jikina,ban zame ko ina ba sai a ƙofar gida inda mutane birjit ke a wurin dukkansu kuma a ƙarƙashin ikona suke.Tamkar sun ga ubangijinsu haka duk suka tsaya da abin da suke yi suka zube ƙasa tare da yin kwanciya suna yi mini wani irin kirari da ba a taɓa yi mini shi ba.Idona na ƙanƙance ina kallon Banah da ke can ɗan nesa da ni yana wani irin murmushi da ban san mene ne ma'anarsa ba,don ko kaɗan ban zargi cewa a cikin kifin da ya bani na ci ba ne wannan girman ƙusumbin ya ƙaru. “Sabbin dokoki sun sauka,don haka al'ummar gari ku kasance cikin shiri ga dukkan abin da shugaba za ta zartar” Banah ya faɗa yana mai takowa yana doso inda nake hannunsa riƙe da kwari da baka. Sai da ya zo dab da ni sannan ya saita kibiyarsa a sama yana mai furta ɗalasiman tsafi,ji kake shuuu kafin wata wuta ta baje a sama.Babu kuma jimawa sauran jama'ar gari suka fara ɓullowa ta kowace kusurwa,tuni wurin ya ɗauki harama ya cika tanƙam.Sai kuma a lokacin ne na soma yin magana,“daga yau an zartar da yin hadaya duk ƙarshen mako,ruhikan ruwa su ne ke da alhakin zaɓar wanda suke so ko dai mu ɗauke shi mu bayar ko kuma su da kansu su kira mutum zuwa can domin ɗaukar ransa.Abu na gaba shi ne duk wani jinjiri da za a haifa sai an kai shi bakin kogo uwa gijiya ta saka masa albarka tare da ƙa'ide masa adadin shekaru ko watannin da zai yi a duniya” Yanayin fuskokinsu duk sun nuna ba su ji daɗin wannan sabon tsarin ba,sai dai babu wani mai zarrar yi mini magana duba da irin ƙarfin ikon da ya ƙara hawa kaina ba tare da ni kaina na shirya masa ba. A haka aka watse na koma ciki na tarar da Ummilo a zaune ta yi uban tagumi.Tana ganina ta miƙe tsaye tare da nufo ni,“na tuna wace ce ni ” shi ne abin da ta furta mini.Cike da jin daɗi na ce “kin tuna? Kai wannan babban abin farin ciki ne amma ya na ga ba ki murna?” Idonta ya kawo ruwa tana mai cewa “na fito a yankin da aka haramta maita da kuma tsafi,ba tare da shuwagabannin sun yi la'akari cewa ba babu wani babban tarihi da magabatanmu suka shuɗe suka bari kamar Magic,ita Maitar ma ba ta fiya ƙarfi ba. Surukina kafin mutuwarsa ya yi matuƙar ƙoƙarin wurin ganin ya daƙile duk wata baƙar shirka,sai dai abin takaici Mayun ne suka haɗin gwiwa wurin kai shi barzahu.Wannan ya fusata mijina har ta kai shi da yin wani tsari shi ne kafa masarauta,yasa an gina babban wuri tare da yin shelar duk wanda ya shirya karɓar addinin gaskiya to ya shigo a cikin sabon ginin da aka yi.Ta wannan hanyar ce aka yi walƙiya aka gano mayu da matsafan cikinmu,sai ya soma yaƙarsu har ya yi nasara a kansu.Sai dai abin da bai sani ba ita maita bibiyar jini take yi,ga shi dai ya kashe tushenta amma bai cire inda ta yabanya ba.Sannu a hankali lokaci na tafiya mace-mace ya fara yawaita a daular,a bisa binciken wani mai bayar da magani ya gano cewa cutar maita ce sai kuma aka ƙara ƙarfafa tsaro.Tun ana yi wa mutum afuwa in an kama shi da cutar maita har aka zo zamanin yarona inda ya yanke ɗanyen hukuncin cewa duk wanda aka kama da laifin maita ko tsafi kisa ne kawai” tana kawowa nan ta yi shiru tare da kamo ni tana cewa “zo ki zauna hakan za ki gaji sosai,ya kamata ma Banah ya nemo miki sanda mai kyau” Kan kujerar da aka sassaka da icce ta zaunar da ni kafin ta ci gaba da bani labarin. “Mahaifin matar ƙanen mijina shi ne mutum na farko da ɗana ya fara cirewa da hannunsa saboda laifi mafi muni da ya aikata ya kashe mahaifan hadiminsa wanda ya ɗauka tamkar amininsa.Ƙarfin wannan raɗaɗin ya saka ita kuma matar ƙanen mijin nawa ta ɗauki tsanar duniya ni da ɗana ta ɗora mamu” nan ɗin ma shiru ta yi tana kallona tsakiyar ido da dukkan alamu akwai wani sirri mai nauyi da take son sanar da ni wanda baki ba zai iya furtawa ba. Ta idonta kuwa ta shaida mini cewa “ni mayya ce! Ina ɗauke da kambun Maitar prophecy” sai kuma ta yi saurin janye idonta daga cikin nawa kafin ta je da sauri ta shige ɗakinta.Na lumshe idona tare da buɗe su kafin na yunƙura dakyar ina dogara sanda na take mata baya. A zaune na tarar da kan shimfiɗarta,na ajiye sandar hannuna ni ma na zaune tare da kamo hannunta.Sai ta ɗago ta dube ni tana wani irin murmushi da ya fi kuka ciwo kafin ta ce “ban taɓa yin maita ba,ban taɓa cin ɗan wani ba kawai dai abin da na sani wani lokacin ina rikiɗa na zama kifi a irin haka ne har ita Dadda ta ganni cikin wannan siffa shi kenan ta je ta sanarwa sarki ai ni ma mayya ce.Ba tare da maganar ta fita waje ba aka titse ni sai na faɗi gaskiyar magana,in kuma na yi shiru na ƙi faɗa gobe gaban al'ummar gari za a yanke mini hukuncin kisa bayan an tabbatar shi ne kawai na yanke shawarar bin dare na gudu.Amma duk da haka bai ishi Dadda ba sai da ta jefe ni da baƙin tsafi ta haukata ni” Na ce “don me yasa kika gudo kika bar ahalinki? Me yasa ba ki zauna ba ki sanar da su babu wata baiwa a duniyar nan da ta wuce maita? In ma ba ki son a sani ai sai ki ɓoye kayarki ” Kai ta girgiza mini tana mai cewa “akwai wani garin magani da ake shaƙawa mutum a hanci muddin yana da ɗigon maita a jininsa to zai bayyana cikin ɓoyayyar siffarsa ne ya dinga tonawa kansa asiri” Na ja dogon numfashi kafin na ce “shi kuma yaronki fa,kin yi tunanin halin da zai shiga bayan tafiyarki? Me yasa ba ki taho da shi ba?” Wani murmushi ne wannan karon ya suɓuce mata bai bayyanar da tsantsar farin ciki da dukkan alamu tana mugun son ɗan nata.Ta ce “Ba fa yaro ne ƙarami ba,ko a lokacin da na bar masarauta ya haura talatin da ɗaya kawai dai a idona ne nake ganinsa ƙanƙane” “Me sunansa?” Kai ta girgiza cike da kunya tana mai cewa “a al'adarmu ba mu faɗar sunan ɗan fari, wannan yasa na yi masa laƙabi da Noor” Samun kaina na yi ni ma da yin murmushin kafin na ce “me Noor ɗin ke nufi?” “Haske!” ta bani amsa. Na ce “zan so na gansa kuwa,da na ji daɗi sosai ni ma zan yi babban yaya” ina faɗar haka sai ta ɗan ƙara matsawa ta jawo kaina ta ɗora kan cinyarta,sai ta cire luluɓin kaina ta soma warware manyan kitson kaina tana mai cewa “wata rana za ki gansa ai ” “Yaushe kenan?” “Ranar da lokacin komawa ta can ya yi,ai zan tafi da ke ne ki ga yayanki in ya so sai Banah ya tsare miki daularki ” Shiru duk muka yi,bayan ta gama warware kitson sai kuma ta ɗebo ruwa ta zuba yaɗo ta wanke mini dogon gashina sannan ta ƙara yi mini wani kitson mai kyau duk da ƙwaya biyu ne kacal amma ya yi kyau.Wunin ranar ne muka ƙara yin wata shaƙuwa ta musamman ni da Ummilo ta dinga bani labarin Yaya Noor lokacin da yana ƙarami da kuma abubuwan da yake so da waɗanda ke saurin saka shi fushi. “Wane abinci ya fi so?” na samu bakina da tambaya. “Gurasa da zuma,yana matuƙar son cin gurasa yana dangwala ta a cikin zuma” ta bani amsa tana murmushi. Na ce “ni ma ina son zuma,kullum in na je farauta sai na je na nemo ta na sha” “Wato yayanki kika ɗauko wajen son zaƙi.Bani labarinki,ina iyayenki suke?” Ummilo ta faɗa . Wani iri na ji duk babu daɗi kafin na ce “dukkansu sun mutu,shi Abbana ban san shi ba ita kuwa Maa a ranar da na karɓi prophecy ɗina ta yi gushewa.Ina sonta sosai,ina jin kewarta a kodayaushe samunki ne ya maye mini gurbinta nake jinki tamkar ke ce ita” na ƙarashe faɗa hawaye na silalo mini masu zafi.Na ƙanƙame ƙafar Ummilo ita kuwa ta shiga shafar kaina haɗi da rarrashina kafin ta ce “ina matsafiyar tarihi sai yaushe za ta zo?” “Ta ce na yi miki sannu da jiki ma tun jiya ” “Ina amsawa,ina ne gidansu?” “Ita ma ba ta da iyaye mahaifinta ya rasu,mahaifiyarta kuma an damƙe ta” “Ayya ki ce ta dawo nan wurina sai mu zauna tare” Ummilo ta faɗa ,sam ban ji zan iya yi mata muso ba hakan yasa ba tare da na shawarci Banah ba na ƙara aika saƙon wasiƙar tsafi zuwa ga Deborah ba ta kuma ɓata lokaci ba ta zo har da ƙullin kayanta.A ɗakin Ummilo na yi mata masauki ,a ɗan wunin da muka yi a tare sai kuma muka ƙara ɗinkewa ni da ita muka manta mun taɓa samun saɓani. Da dare muna zaune bayan mun gama cin abincin,Ummilo na ririga Mila da ke yin rigima ta ƙi yin bacci sai ta soma rera waƙa wacce ta saka mu duk nutsuwa.Ba da Yaren da muke magana ba ne,haka kuma ba Yaren tsafi ba ne wani yare ne can daban da ita kaɗai ta san ma'anarsa amma sosai na ji daɗin baitin.Babu jimawa Mila ta yi bacci sai ta shimfiɗe ta tana murmushi tare da cewa “a duk lokacin da Noor ya fitine ni da kuka wannan waƙar nake rera masa ko kuma in ina son saka shi bacci” "Amma Ummilo da wane yare ne wannan?” na tambaya,Deborah da ke rubutu cikin littafin tarihi ta yi karaf ta bani amsa da “Yaran serena ne,yare ne da halittun ruwa ke yi ita kuma waƙar suna yinta ne domin janyo wani ruhi zuwa gare su domin aiwatar da abin da suke buri” Ido na tsura mata ina kallonta ta hasken farin wata,kafin na ce “ ta ya aka yi kika sani?” “Ta ya ba za ta sani ba,matsafiyar tarihi ce fa” Ummilo ta faɗa . Deborah ta yi murmushi tana mai cewa “tun jiya da na yi tozali da Ummilo na cika da mamakin me ya kawo Siren a nan” Na ce “ai na lura da yanayin yadda kike kallonta,to sai da safenku zan je na kwanta” na faɗa tare da lalubo sandata na miƙe na shiga ciki. Kan gadona na kwanta tare da yin shiru ina nazari,can sai ga Banah ya ratso rufin ɗaki ya shigo.Sam hakan bai kuma bani mamaki ba,illa kawai na mujiya da na zuba masa ina kallon yadda jikinsa ya ƙara rinewa kamar wanda ya fito daga cikin rijiyar kunama. Gefen gadon ya zauna tare da miƙo mini wata ƴar kwalba ya ce “shafa mini” ba tare da na miƙe daga kwancen da nake yi ba na karɓa na soma shafa masa sannu a hankali tiririn dafin jikinsa ya soma disashe ganina. ★ Da dare bayan gama bikin baiko sai aka zauna kan teburin cin abinci.Yarima NASLAM ne da dakarunsa masu taya shi yaƙi,suna cin abinci suna raha yayin da shi kuma yayi shiru yana ta juya gurasar da aka ajiye a gabansa ya kasa ci.Jakariya Ali da ke gefensa ya ce “bari na nemo maka zuma in ba za ka iya ci da markaɗaɗen yaji ba” Ya ɗago ya dube shi tare da yin murmushi kawai, Jakariya Ali ya fita zuwa madafa bai wani sha wahala ba don ya tarar da masu aikin kula da abinci ita ta miƙo masa zumar ya karɓa kafin ya zo ya kawowa yarima. Cikin ƙarfin hali yarima Naslam ya karɓi zumar ya soma dangwala gurasar a ciki ya kai bakinsa,sai dai ko kaɗan bai ji wani ɗanɗano ba.Gudun kar ya ɓata wa kansa lokaci sai ya ture abincin, Jakariya Ali ya dube shi cike da mamaki yana shirin yin magana yariman ya miƙe ya nufi ƙofa sai a lokacin ne kuma Ali ya hango baƙin tambarin maita ya fito yau a bayan wuyan yarima Naslam.Cikin bugawar zuciya shi ma ya miƙe ya fita,bai zame ko ina ba sai gidan Barham.Kamar zai ɓalla ƙofa haka yake bugunta,Barham ya buɗe yana mai kallonsa da mamaki yake cewa “lafiya dai ko?” Sai da ya shige ciki tare da rufe ƙofar sannan ya basa amsa da “ina fa lafiya yau baƙin tabon maita ya fito a wuyan yarima sam ya kasa cin abinci” Barham ya saki kofin hannunsa yana mai kallon jakariya Ali cike da tashin hankali,kafin ya ce “tabo? Wane iri? Baƙi ko ja?” “Na faɗa maka baƙi ne” “Hakan na nufin bayan kambun baka yarima na ɗauke da ɗigon baƙar maita ?” Barham ya faɗa tare da zuwa ya ɗauko wani littafi sai dai duk bincikensa ya kasa samo gamsashiyar amsa ,tsabar firgici goshinsa har ɗigar da gumi yake.Ya ɗago ya dubi Jakariya Ali cike da rauni yana cewa “babu abin da na samu a binciken da na yi” Ali ya ce “ya zama dole mu nemo mafita tun yau kafin gari ya waye ,saboda muddin aka kwana to Maitar za ta rinjaye shi ya fara sarrafa ta ” Idon Barham suka kaɗa suka yi ja,ya rasa meke yi masa daɗi kafin can ya ce “yawwa ina matsafiyar tarihi da aka damƙe?” “Tana can a kulle” ya basa amsa. “Mu je ka kai ni can ita ce kawai za ta bamu mafita” Barham ya faɗa tare da ɗaukar wata takarda.Haka suka dugunzuma zuwa can inda ake ɓoye masu laifi,ko kaɗan babu wanda yayi gigin hana su shiga saboda duk wani dakare a ƙarƙashin ikon jakariya Ali yake shi ne shugaban dakaru gaba ɗaya. Suna zuwa suka tarar da ita a zaune tana yin rubutu a ƙasa,ba tare da ta ɗago ba ta ce “me kuka zo yi? Kun zo tafiya da ni ne a kashe ni ?” Sai suka kalli juna kafin Barham ya yi shahadar cewa “wane laƙani ne ake yin amfani da shi domin daƙile bujurowar baƙar maita tsafi wacce ke bibiyar jini?” Ta ɗago da sauri ta dube su kafin ta ce,“ba zan taɓa faɗa ba ,kamar yadda yake son tozarta al'ummar Mayu da matsafa shi ma sai na bari ya tozarta a idon duniya kowa ya san wane ne shi” Barham ya furta surkullen tsafi sai ga shi tsundum cikin ragar da take ciki,har ƙasa ya zube alamun roƙo kafin ya ce “kar ki dubi wannan ɓangaren,ki dubi matsayinki na babbar matsafiyar tarihi ki sanar da ni laƙanin” Ta kawar da kai tana mai cewa “babu wani laƙani da zai daƙile maitar yariman masarauta ,sai dai a basa magani domin ɓoye ta.Daƙile ta duka kuma dole sai sarauniyar matsafa ce da kanta za ta iya yin haka” “Bani na ɓoyewar” Barham ya faɗa ,ta juya masa baya tana mai cewa “yana can a kusa da duniyar ruwa,fure ne na floris mai matuƙar muhimmanci da zarar ka kai gare shi za ka ji ƙamshinsa na sanar da kai shi ne abin da ka zo nema“ Barham ya miƙe yana yi mata godiya,yana shirin tafiya ta ce “ban ƙare jawabi ba,masu tsaron furen nan fararen fatale ne da ba su aminta da irin tsafinka ba” Barham ya juyo cike da tsoro kafin kuma ya dubi Jakariya Ali ya ce “na gode” Yana fitowa sai kuma suka fara shawarar ta yadda za a yi su fita daga cikin masarauta ba tare da kowa ya gani ba.Jakariya Ali ne ya je inda ake ajiye dokin yarima,kamar yana magana da mutum haka yayi masa bayanin komai kafin ya jawo shi ya fito. Barham ne ya fara hawa don shi ne ya san hanya sannan shi Ali ɗin daga ƙarshe.Cikin amincin Allah suka fita daga masarautar zuwa inda aka shaida musu za su samu maganin,ana kawowa wurin kuwa ƙamshi ya buge musu hanci kafin su yi wani yunƙuri kuma fatale duk sun zagaye su shi kuwa Barham ganin mutuwa a maƙoshi tsautsayi yasa ya furta baƙin tsafi,sai kuwa aka damƙe su aka jefa ɓoyayyar duniya. A can masarauta kuwa yarima Naslam ne kwance a ɗakinsa,har aka yi sallar asuba bai farka ba sai da hasken rana ya hudo ya daki tabon maita na wuyansa,wani irin kuka yayi da ya girgiza masarautar.Daidai nan free page ya ida,duk mai son shiga paid group zai biya kuɗin karatunsa 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 *Daga yau discount yake idawa 13.April* *NB:* Da zarar book ya kammala kuɗinsa 1k ne. MRS SADAUKI