Showing 1 words to 2012 words out of 2012 words
“CLASS MATE”
( ungulu da kan zabo )
ZAINUDDEEN JIBRIL
Tel: 08034840276
Email: deenysalaf08@gmail.com
GODIYA
Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai, wanda iyawarsa ta zarce tunaanin kowa da komai,
shi ne masanin sirri da ma abin da ke sarari, ikonsa ya wuce hasashen mutum bare dabbobi,
shi ne kadai ke tafiyaar da lamura ba tareda karkata ba.
Salati ba adadi na yo gun Annabi Muhammadu (SAW) dan gata kuma sha lelen ubangiji, wanda
binsa ya zamo wajibi kuma tilas akan duk mai kaunar ya sami dacewa da gidan tsira a gobe
kiyama.
Na hada da iyalan gidansa da sahabbansa, tareda duk wadanda suka bi tafarkinsu ya zuwa
ranar tonon asiri.
Ina mika godiyata zuwa ga mahaifiyata, da Allah ya sadata da gidan aljanna ya kuma kara
daukakata ya yafe mata zunubanta ya lullubeta da rahama da jinkansa. Inason mamata sosai.
Masoyana, ina jinjina gare ku, da kokarin karatun kwamacala da nake gwaba muku, a hakan dai
kuke daurewa kuke karantawa, Allah ya bar mu tare, ina yin ku irin sosai dinnan.
TSOKACI
Wannan labarin gajere ne kuma kirkirarre ne, na rubuta shi ne lura da wata barna da ke faruwa
a cikin jama’a; in da za ka ga tsakanin mace da namiji kamar wasu mata da miji ko muharramai
a yadda mu’amula ke gudana tsakaninsu, duk da sunan “class mate” wato abokin karatu a aji.
Labari ne na Sumayya tareda mai gidanta Ahidu, wadanda suke zaune lafiya da junaansu, suke
gudanar da komai a gidan aurensu yadda ya dace, kafin tsautsayin “class mate” ya hau kan
Sumayya, wanda ya yi sanadiyyar rusa duk wani farin ciki da suke ciki har ta yi danasanin
kasancewa daya daga cikin wadanda suka yi boko.
Kamaar yadda na fada a sama, cewa labarin kirkirarre ne, sunaye da wurare da na yi amfani da
su suma kirkira na yi, duk wanda ya ga sunansa ko halayyarsa ta dace da labrin ko jigon
labarin, dace ne kawai.
Na yi wa dan gajeren labarin suna da “class mate”. Ina rokon ubangiji da ya datar da mu da
alkhairi ya kuma sa abinda za mu rubuta ya fadakar ya kuma sa ya zama sanadiyyar tsirarmu a
gobe kiyama.
*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_
Kamar kullum yau ma tun safe na ci kwalliya bayan da muka kammala break fast ni daHuubyna,
tun ina cikin shower nake tuannin yadda yake kallona cikin shauki da nuna soyayya, hakan ta
sa sai rero wakoki nake na Hausa hip-hop na Zainuddeen Zain ina cike da murna da bege hade
da shaukin kauna, har nake ji, ba macen da ta kai ni dacen miji. Mijina ba ta yadda safiya za ta
waye ba tareda ya gayamin zantuka masu ratsa zuciya ba, haka ko a cikin mutane ba ya
gazawa wurin nunamani kauna, hakan ta sa nake bugun gaba da shi.
A jikina English wears ne, dan guntun skirt wanda ba zai wuce rabin cinyata ba, baki ne, wanda
ya baiwa farar cinyata damar bayyana sosai, sai pink riga da ta matse ni sosai kamar dai yadda
skirt din ya matse ni, sai rolling na gashin kaina da na yi kasancewar ba kitso a kaina, sosai ni
kainaa ina jiyo kamshin gashin kaina wanda ya yi tsawo kuma ya ciko, duk ba wannan nake
alfahari da shi ba, sai yadda Ahidu ke hadiyar yawu a duk lokacin da ya dora idanuwansa a
surar jikina, ni kuwa sai tashi nake da gangan da sunan dauko wani abu a fridge ko daki, kawai
domin na yi rangwada ta gabansa yadda zai ji dadi.
Sai fira muke yi kasancewar duk ranar weekend haka muke yi, ba ya zuwa ko’ina sai da
maraice mu fita yawon zagayawa a kafa. Soyayya dai tsakanina da mijina har ta wuce
kwatance.
Wata rana da ba zan taba mantawa da ita ba, mun tafi shopping mall domin mu yi sayayya,
daga isarmu, na hango Sufy. Sufy class mate dina ne da muka yi kratu a jami’a ta JASU (Jarwo
State University). Daga nesa muka fara jefawa juna zagi, “ke shegiya, ashe kina nan?” “shege
mugun kwaro ina kuma aka shige?” daga isowarsa ya miko min hannu, ni kuwa abinka da sabo
na mika masa muka tafa, ya rike hannuna cikin nashi, sai fira muke ta tuna baya, hannuna a
cikin nashi yana wasa da shi, cen ya kalleni ya ce, “wallahi Sumy kinanan da kyawunki kalli fa
yadda sai wani fresh kike karawa ga jiki duk ya ciko..” sai a lokacin na tuna fa tare muke da
mijina Ahidu, kuma a kusa yake da ni, waigowa da zan yi, na ganshi sai mamakinmu yake,
fuskarsa cike da alamar tambaya, gaba daya idanuwansa suka rikide suka koma ja, Ahidu da
yake da haske sosai Fulani ne ga gemu mai tsawo da kasumba, amma haka fuskarsa ta dawo
jawur, ya hadiye fuska kamar wanda aka turowa da sakon mutuwa. Na kalle shi, cikin rashin
nadama na sake mayar da kallona zuwa ga Sufy, sai na ce “ga mijina” shi kuwa cikin rashin
nadamar abinda ya aikata, kuma ya ki ya saki hannun nawu ya kalle shi ya ce “Ah! Yallabai kai
ne ka kwashe muna most beautiful yarinya on campus?” ba tareda ya kalle fuskarsa ba, kawai
ya dubi hannunsa da ke rike da nawu hannun, ya fara tafiya zuwa mota. Ganin haka nasan
akwai matsala, cikin sauri na fizge hannuna cikin nasa, yana cewa “lafiya” na kasa ko na amsa
masa, na fara sauri domin na tarar da mijina da ke kokarin bude kofar mota.
Sufy kuwa sai ya rike baki yana mamakin wannan abin, cen ya gyada kai ya wuce.
Ina masa magana, amma sam ya ki ya kulani nayi magiya na yi shagwaba na roke shi amma
sam ya ki ya ko kalleni, tuki kuwa sai takar mota yake yi kamar wanda zai tashi sama, saura
kiris mu buge wata mai tuyar awara kan titi.
Da misalin shida da sha bakwai na maraice muka karaso gida, ya fita ya bude gate din gida ya
shiga ya yi parking, har yanzu dai ya ki ya ko kalle ni, ‘yan kayayyaki da muka siyo daga
Shopping Mall dole ni na dauko su na saka cikin gida.
Shigowata ta yi daidai da shima zai fita, har yanzu fuskarsa a murtuke, har ma murtukewar
yanzu ta dara ta farko. Na rike hannunsa, na ce “Hubby me ke faruwa ne?” ya janye hannunsa
ba tareda ya kalleni ba ya fice abinsa cikin sauri.
Bayan na ajiye kaya, na shiga zullumi da tunanin me na yi wa wannan bawan Allah, iya sanina
muna zaman lafiya, yau shekararmu daya da wata uku da aure, duk da ban haihu ba, ko kadan
bai taba nunamin wani abu da rayuwata za ta iya baci a kansa ba, yana nunamin kulawa da
soyayya, har ta kai ga ya shwagwaba ni, yau kuma ga shi yana kokarin jefa ni cikin yanayi da
ban taba tsintar kaina a ciki ba. Nan wasu zafafan hawaye suka fara rigangayar sauka a
lallausan kumatuna, tuni sautin kukan ya ci karfina har da shessheka, naci kuka har aka tada
sallar magariba, na je na yi sallah, na dawo na dauko abincin da na girka muna kafin mu fita, na
jera kan dining table, na shiga kamar yadda na saba na tsala wankana, da daukar kwalliya mai
jan hankali, na dire kan TV ina kallon tashar Equity TV, ina jiran shigowar Hubbyna, amma shiru
har aka fara sallahr isha, abinda ya bani mamaki sosai kenan, domin tsawon zamana da shi,
duk inda yake, to bayan magariba yana gida, domin a lokacin muke cin abinci, idan muka
kammala isha kuma, sai mu shiga fira har ila ma sha Allahu.
Daga ida sallah na dauko wayata coolpad, na danna lambarsa, amma har ta katse ba a dauka
ba, a raina nace inaga aiki yake yi, na sake dawowa na dirshe a bakin TV naa ci gaba da kallo.
Ban Ankara ba agogo ya buga kusan sha dayan dare, a lokacin har barci ya daukeni na farka,
na sake janyo waya, na kira, kawai sai naji karar wayar a parlour, fitowa da zan yi, sai na ga
Ahidu kwance kan three seater, waya cen kan teburi, sai kallon sealing yake yana karatun
wasikar jaki. Nazo cikin rangwada na hau kujerar na dafa jikinsa da niyyar na sumbace shi, sai
ya tashi zaune, fuska a murtuke.
Ganin haka na gurfana na saki kuka na ce “ka dubi girman Allah ka sanar da ni, laifin da na
maka.” Ganin na shiga damuwa ya ce da ni “yanzu abinda kika aikata ya kyautu, kinsan dimbin
zunubin da za ki kwasa kuwa, ace da aurenki, za ki bari wani kato ya rike hannunki a tsakiyar
titi, wacce irin rayuwa ce wannan?” “haba Hubby, sai ka ce wanda bai waye ba? Dama kan
wannan ne kake fushi? Wallahi har ka bani kunya, me ye a ciki? Class mate dina ne fa” ya sake
kallona, a wanna karon cike da tsana, kamar ya sharamin mari, kawai ya rafka tsaki ya kwanta.
Na yi rarrashinsa, amma kamar mai yi da gawa, dole na hakura, nima bansan lokacin da barci
ya dauke ni ba, dole a parlour din na yi barci.
Tun ranar abubuwa suka fara rikicewa tsakanina da mijina, ga shi na kasa na nuna cewa
kuskure ne na yi, bare na bada hakuri.
Wata rana ya kaini gun walima, dawowa da zai yi daukata, ya tarar da ni ina fira da Sufy, sai yi
muke yi tareda kyakkyewa, har ina kaimasa duka shima yana kawomin, ganin haka ya kasa
karasowa a kusa da mu, sai daga baya na hango motarsa, kafin na yi wa Sufy sallama, kawai
ya buga motar ya wuce. Rikici ya dawo sabo tsakaninmu, a ranar bai shigo gida ba sai da
misalin dayan dare. ya daina yimin magana gaba daya, ya daina cin abincina, kwwalliya idan na
yi ko kallo ba ya yi bare ya yaba. Ni kuwa ganin haka na fara yi masa masifa, ina cewa, ai idan
aure zai kara, bai dace ya dinga wulakanta ni ba, shi kuwa duk masifar da nake, ko kallo ban
ishe shi ba.
A karo na uku ya sake ganinmu da Sufy, wannan karon har da rngumar juna kafin mu rabu. Ita
ce ranar da ba zan taba mantawa da ita ba a rayuwata. Ina shigowa gida na hari daki domin
nayi wanka, bayan na fito daga wanka, kan kayan kwalliyata naga takarda, a bayan takardar an
rubuta, “zuwa gareki Sumayya” cike da mamaki na dauki takardar duk da nasan rubutun wa ye,
na buda na fara karantawa. Ai na kasa karanta takardar gaba daya, numfashina ya fara kokarin
kwacewa daga huhuna, hawaye kuwa kamar wanda aka baiwa gashi aka kwace, hankalina ya
tashi na rude gaba daya gani daga ni sai towel a jiki. Sai maimaitawa nake yi, tun ina yi a zuciya
har na fara yi a fili, “ya sake ni! Ya sake ni! Ya sake ni!” ina yi ina zabgar kuka.
Na yi bashi hakuri amma ina ya ki ya saurare ni, dole na hakura na kwashe kyana na koma
gida, shiru ina jiran ya maidani, har na kammala idda.
Tun a lokacin na dauki alkawarin ba zan sake wannan fitsara ta class mate ba, nayi nadama
sosai, ina kuma kira ga masu wannan halayyar da su duba irin hali da na shiga ta wannan
sanadiyyar su yi wa kawunansu karatun ta nutsu.
*DR. ZAIN*