Showing 33001 words to 36000 words out of 63648 words

Chapter 12 - Mutallab Book Compelet Novels Nimcyluv

ta fice daga cikin gidan secretly amma no way "wai ina magana kina ji ba zan shariyar nan naki damuna yake, na zo Webe miki damuwa da kewa na rashin Ashraf kamar yadda Ummi ta bu?ata duk da ciwon da bakina yake mini ina da zuba ke kina ignoring nawa for God sake"

"Idan ba ?i auro ba sai ki auri Wan daban kawai" Kinal ta yi tsaki ta ce "Kuma zan iya, mene a ciki"

"Shi auren Wan daban?" Fiyya ta bu?aci amsa tana kallon Kinal. Kinal ta ce "Deal, nama yi miki al?awarin in dai ina da numfashi wallahi wallahi sai na auri Waya daga cikin ?an daban nan, kamar ni mawa?iya za su yi wa haka? Uhm" Fiyya ta lumshe idanu ta buWe deep down ?irjinta na bugawa sai ta ce

"You most like them ma, ?an daban ai sun iya soyayya"

"Ke ta ya kika san sun iya?" Shoulders kawai Fiyya ta Waga ba tare da ta ce komai can ta sauke numfashi tana kallon Kinal ta ce

"Kinal Ashraf ya rasu, mijin da zan aura ya bar ni Kinal ina cikin damuwa ina jin da old Safiyyerh ce ba zan ce ina cikin damuwa ba, gwara ta kashe ni haka nake ji" Kinal ta jinjina kai "Fiyya something is over doesn't mean your life is over, ki yi ha?uri mu Wauki ?addara ki yi wa Ashraf addu'a Please kar ki saka damuwa wani abun ya zo yana damun ki daman ke idan kika birki ce kamar mai ?ar mero a ka, ?addararmu zata zama mai kyau muna tare da addu'ar iyaye ai" sun jima tare da Kinal har yamma kana ta tafi gida tana jin dole ta sake komawa wajan ?an kodin Win nan.

Da ?yar da daddare Fiyya ta sakko ?asa bayan tayi sallar issha tana sanye da hijabi har ?asa, fuskarsa looking ok ba yabo ba fallasa sai dai ta faWa idanunta ya fito akwai damuwa a tattare da ita. Inda ta yangi su J ta nufa ta shiga tsakiyar ?an mazan ta zauna a nutse ta ce "Sannun ku" Awais ya Wago ya kalleta ya ce "Yawwa Manager ya ?arin ha?uri?" Idanunta ya juya ta cije baki ta ce

"Allahamdulilah,thank you" daddy dake kallon ta cike da tausayi ya ce "tashi a nan wajan Safiyyerh"

"Daddy me ya sa?"

"Ki dai tashi na ce ko?"

A sanyaye ta mi?e sai kawai ta yi sama ya bita da idanu a hankali ta ce "Sai yaushe zaka faWa mata batun auren?" Daddy ya ce "Da sai an kammala Visa Win ta, na san wacce take da ita a baya ta yi expired, to Safiyyerh stubborn girl ce da na yi maganar visa zata kalli cikin idanuna ta fara mini turanci wayonta tsoro yake bani, kuma yanzu i feel very comfortable da Aliyu matsayin mijinta duk da basa shiri amma ba zai Waga mata ?afa bana son dai ta yi rayuwa a wajan shi kamar Prisoner, za ta yi shakkar yi masa abu"

"Kana ganin zata amince da auren?" Ya mi?e tsaye yana haurawa sama ya ce "In sha Allah" daman daga sallah ya dawo shine ya zauna. J dai baya uhm baya uhm'uhm abubuwa da yawa ke yawo a ?asa wanda baya rasa nasaba da tunanin wace Safiyyerh waye Aliyu?

Ummi ta kalli yadda ya shigo ba wanda ya kula kamar bai ga kowa ba ta ce "Aliyu tun safe ina ka je ne?" Ya buWe ido ya yi shiru ta ce "Kuma ka ci abinci ne? Kodayake ba'a tambayar soja ko ya ci abu da za'a buWe cikin ka duk ganye ne" kallon Ummi kawai yake kuma ya yi shiru

"Yaushe zaka tafi goben?"

"A'a, night Ummi" ya ce yana shigewa cikin Wakin shi dake part Win mazan.

Fiyya ta ci kuka a Waki kamar rai da sauri ta buWe system Winta taga sa?o a e-mail nata tun sanda sukai last called da Ashraf bayan hakan ta minti ashirin da wajan biyar. Maganar daya tura mata ya saka ta buWe idanu sosai.

_Safiyyerh daddy ya zo ya fita yanzu, ko ma dai menene ki tabbatar ba ki bawa wani damar mallakar FS WORLD INVESTMENT COMPANY ba Fiyya mutane biyar sune mamallakan wannan kamfanin mutane masu haWari ko ni ban san su ba, da ina da yadda zan yi a yanzu zan faWa miki komai domin sau?a?a miki, ki fara nemo ma'anar FS shine key Win binciken, don't cry when you miss me i love you"_

Safiyyerh was shocked, thinking me ya saka Ashraf ya yi mentioned sunan daddy a lokacin, meke shirin faruwa ne gabaWaya kan ta ya Wauki zafi da gaske ta yi rashin Ashraf sai yanzu ne take jin gudun zuciyarta na ruSanya aikinta a kan Ashraf Win. Ta kwanta tana rufe idanunta ?arar notification na wayarta ta saka ta buWe idanu tana janyo wayar a hankali, rubutu a ta?aice mai Wauke da azanci da Soye manufar abin da ake so a bayyana.

_ laifi akan laifi again? Kodayake shi laifi tudu ne Safiyyerh ke inuwar wani ce ki yi ?o?ari kar a saka ki shiga wuta _

A gigice ta ce "Na shiga uku ni Safiyyerh"

****
Cikin dare ne wajan biyu da arba'in motarsa na gefen titi cikin duhun daren ya saka facemask ya rufe fuskarsa tsoro da fargaba ya gaba gitta masa zuciya a hankali ya zuge glasses Win motar babu mai cewa shine a ciki, yana buWewa ya faWo cikin motar ya ce "Kira cikin dare? Ban fiya son ina tsaka da wani aikin kuma ana kira na wani ba, ya akai?"

Photo ya fito masa da shi na wani kyakkyawan yaro fari tas da shi idanunsa buWe ya shagwaSe fuska tare da mi?a hannu alamar a bashi wani abu, yana sanye cikin wasu ?ananun kaya ba?a?e. "Na gani photon waye? Wannan yaron fa?"

"?an gidan Safiyyerh ne" ya furta yana lumshe idanu tare da yin baya ya jingina da kujerar zuciyarsa na buWewa sosai tsoro da fargaba na cika shi "What! Safiyyerh yaronta kuma?"

"E, idan kaga Safiyyerh ka gan shi kamar an yi kaki ban san ko ta san da yaron ba a tabbatar an gano mini inda sa Safiyyerh take"

Kwanakin wajan biyar da rasuwar Ashraf daddy bai faWawa Fiyya batun auren ba, haka ma Aliyu Fiyya kullum sai ta fita wajan aiki ba kuma ta dawowa da wuri. Yamma wajan magariba take driving a gajiye take sosai fahimtar ana bin bayanta ya saka ta ?arawa motar giyar da sauri ta Wakko waya number J ta fara kira amma bai Wauka ba, ta shiga kiran ta daddy amma a kashe duk wanda take tunanin kiran number shi a gidan ta kira bata samu ba,



ta kalli madubin taga har yanzu motar na biye da ita, tare da wasu babura biyu bata iya hango fuskar mutanen amma kallo guda ta yi musu ta san ?an daba ne, ko dai masu satar mota ne ko satar waya ta shiga uku. Baburan guda biyu suka cimma ta Waya ya saka hannu ya daki glasses motar nata, ta yi gefe tare da ?arawa motar gudu suma suka take mata baya a lokacin tsoron da ya yi mata yawa ya saka ta fara gani dishi dishi kan motar na neman kwace mata, cikin sauri tana ?an?ame steering ta shiga lalubar numbersa bata da tabbacin ko tana da ita cikin sa'a ta gani ta danna kiran sai da ta yi kiran biyar bai Wauka ba, gashi hanya babu mutane a kira na shida ya Waga cikin Waga murya da fitar hayyaci ta ce

"Yaya na shiga uku Captain wasu ne"

Ya yi mata shiru can ya ce "Who are you?"

"Yaya Safiyyerh ce wasu ?an daba suka biyo ni gashi titi babu kowa, Captain suna da yawa wasu a babur wasu a mota na kira number kowa a gida basu Wauka ba gashi ciwon kaina kamar zai tashi bana ganin hanya sosai kan motar ?wace mini yake" ta cikin wayar Captain ya yin siririn tsaki can ya ce

"Ina ruwana?"

"Captain kashe ni fa za su yi innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!"

"Allah Ya ji ?an ki"


littafin MUTALLAB
Na kuWi ne we're still on free pages. Ka biya a yi adding naka a paid book before mu yi cutting free pages Win. MUTALLAB.
Book 1, 2 &3
500 Naira
0116886423 Union Bank Na'ima Sulaiman S. A tura shaidar biya ta nan 08164069385[10/17, 8:12 PM] Nanameera: *d'
=?%? MUTALLAB d'
=?%?*

Page 10
*Bright pens..2nd batch*


"Kamarya Allah Ya ji ?ai na, Captain ina faWa maka biyo ni ake yi za'a kashe ni, kana cewa Allah Ya ji ?ai na, i called you saboda na rasa wanda zan kira Please help me" ta cikin wayar Captain ya yi tsaki ya ce

"Kee, ina ruwana idan sun kashe ki who cares about your life, zan kira daddy a Wauki gawarki ok" kashe wayar ya yi. Safiyyerh wani irin zafi ta ji a zuciyarta da raWaWi bata san ma wanne gurbi zata saka Aliyu ciki ba idanunta ya kawo hawaye ba?in cikin kiran da ta yi masa tana zargin kanta da laifinta ne. Ta cikin madubin motar take sake kallon motar dake bib bayanta da kuma sauran baburan ta runtse idanunta a fili ta ce "Ya Allahu Ya Rahmanu ka dubi Safiyyerh ka kawo mata Wauki..Daddy!"
Ta kira sunan daddy a gigice tana sakin steering motar bata sake sanin abin da ya faru bayan nan ba.

Yana tsaye fitowar shi daga motar kenan ya dubi yadda ta yi flat kwance a ?asa gefen kanta da jini ya kalli sauran jami'an tsaron da suke wajan "Is she ok? Tana numfashi?"

"She is, buguwa ne kuma Allah Ya rufa asiri motar ta tsaya da kanta, ba'a yi nasarar kama ko mutum Waya ba, yarinyar ce dai bamu san wace ita ba za mu duba id card nata sai a kira iyayenta a shaida musu ko asibiti ne a tafi da ita" ya yi maganar cikin girmama kan shi a ?asa, wanda ke tambayar ko Fiyya na raye ya yi baya rungume da hannunsa can ya duba a gogo sai bai ce komai ba "Sir meeting Win naka? Ina tunanin ka je kawai za mu kula da komai tunda shugaban jam'iyya da secretary na jam'iyya na jiran zuwan naka" kafin ya yi magana cikin sauri wata mota ta ?arasu wajan kamar zata tashi sama ko gama daidaita tsaiwar motar bai yi ba ya fito idanunsa a kan Safiyyerh, mutumin ya dubi fuskarta shima a hankali kuma ya ce.

"Easy Captain, ka kira ni sanda muke kan titin da take ta kuSuta Allahamdulilah" jinjina kai Aliyu ya yi cikin girmamawa ya ce "thank you"

"Anything for you Aliyu, amma ku kula tana da harshe zuciyar nan tata irin take ce, Allah Ya bata lafiya" Aliyu dai na tsaye idanunsa akan fuskarta ya kasa magana har mutumin ya shiga motarsa driver ya ja, jami'an tsaron suma suka shiga motar suka marasa masa baya cikin tafiyar sirri. Ya jima yana kallon ta hannunsa ri?e da wayarsa tunanin yadda zai yi da ita, ?ar mitsitsiyar yarinya ta fito da shi, banda darajar daddy da babu abin da ya yi masa zafi sanin cewa idan Fiyya ta mutu hakan na nufin tsayawar numfashi daddy ya saka ya lallashi zuciyarsa. Cak ya Wauke ta ya saka ta a gaban mota yana yin baya da kujerar a ransa ya ji ba zai zama drivernta ba, ya Wauki wayarta ya rufe motar yana shiga ya tare da zama ya sake juyawa ya kalle ta da kyau sosai jinin ke fita a goshin nata ya taSe bakinsa kawai a hankali kuma yana Wora mata tissue ya furta

 Fitinanniyya... Safiii

Farar safiya ce gari ya yi shiru amma shi idanunsa biyu, yadda ya ga dare haka ya ga rana idanunsa tarwai a sararin subuhana yana kallon sama da abubuwan da Ubangiji ya wanzar a cikinta, a hankali ya juya ya kalli Darma da Goje sai kuma Mangal dake can gefe guda ya sha ta gaya masa babu daWi sai lilo yake da ?afarsa a sama. Mangal ne ya buWe idanunsa da sauri ya mi?e zaune yana murza idanunsa alamar bai gama wastsakewa ba.

"Jeji naka dawa taka ka huta mai dawa, ba dai gaba da gaba ko ta baya ?aryar mutum dan uwatar ya aka yi ba ka yi kasa bane ka raya daren da gadin mu?" Moh ya yi shiru ?irjinsa sai Wagawa yake. "Ina tsoron shirun nan naka don ba zai haifar da Wa mai ido ba, ka tara dafi a cikinka jira kake ka samu inda zaka sauke ?arin dake damun jikinka ka sarara a kaiwa mai duka lillahi kukan kawai" sai a lokacin ya juyo da gajiyayyun idanunsa da suka shige ciki duk girman da suke da shi, sun yi wani bala'in ja ya zubawa Mangal ido

"Talk da turanci kenan da hausa na goga maka yi magana sarkin jeji"

"Mangal"

"Yes inji masu jajayen kunnuwa bi ma'ana na'am" muryar Moh bata fita sosai a lokacin duk wanda ya nutsu zai hango wani irin sanyin murya da yake da shi da sauti maraya hayaniya. "Wacce cuta aka taSa yi maka a rayuwa wacce ba zaka iya yafewa ba?"

"Kan uban nan, ni ai ka sani a kusurwa kaina ya kulle wanda sukai mini kuma tuni sun girbe abin da suka shuka bana yafiya bana cuta bana bari a cutan" cije baki kawai Moh ya yi yana lumshe idanunsa da sauri ya buWe su tar saboda yadda yake jin kakari da numfashin fitar ranta yana yi masa amo a kunne, ya mirgina kaWan ya Wauki ?afarsa Waya ya Wora akan Waya yana girgiza wa ya zubawa zara-zaran yatsun ?afarsa idanu tare da rungume hannayensa a ?irji.

"Wai what happened Mai dawa?"

"Ka dai na yi mini turanci don uwarka"

"?an tsinanniya ba, ba uban da ya iya kuma ya san ai duk bama ji shima a Legas ya koya" cewar Goje yana farkawa tare da zama dukkan su babu wanda yake da niyyar mi?ewa domin yin sallah. Goje ya kalli Mutallab ya ce "Yaushe za a kwalo berewar nan ne? Ka yi shiru karfa ka ji?a masa aiki"

Da sauri Mutallab ya kalli Goje jin sunan daya kira na barewa ya lumshe idanu ya buWe zuciyarsa na bugawa sosai sai bai ce komai ba can dai ya mi?e zaune a hankali kuma ya tashi tsaye ya zaga bayan katanga ya daWe kafin ya dawo wajan Darma ya kalli hannun Mai dawa ya buWe idanu ya ce "Bura... Wannan ?wayar ka shanye to kwarankwasa ka shirya zama mahaukaci, ?wayar doki ce fa? Wai kashe kanka za ka yi akan wasu ?an?an jakuna ka fito musu gaba da gaba mana, a yi komai duk abin da zai faru ya jima bai faru ba, ?arshe dai gidan Wan kande ne kuma mu ba wai ba?in ta bane"

Mutallab ya tsaya cak a tsakiyar wajan naman jikinsa na motsawa musamman kakkauran ?irjinsa mai faWi sai kawai ya shagiWe bakinsa gefe kamar zai yi murmushi da sauri ya tsuke fuska zuciyarsa na tuna masa shekarun da suka shige a fusge ya furta "Sai godiya" gabaWaya suka mi?e tsaye suna maimaita

"Sai godiya"

Basu fargaba sai ganin tarin wasu ?an daba suka gani suna fitowa daga wasu lunguna a ?alla sun fi su ashirin Wauke da gorori wasu wu?a?e. "Dara ta ci gida lallai an raina mu, mu wasu da?i?ai zasu kawowa farmaki har lukanmu?" Cewar Darma Mangal ya kalle su ya ce "Kuma suwaye ku yara?"

Wani daga cikin su ya fito ya tsaya a gaba ya ce "Sanin sunana ko waye ni bashi da wata fa'ida a gare ka, da zaka tambayi wanne kalar kisa zan maka zai fi maka, amma saboda gudun tilawa ko tafiya ?iyama da tunanin wanda ya kashe ka lallai zan goga maka sunan nawa". Ya zaro wu?a daga cikin ?ugunsa idanunsa akan Moh da bai ma kalle su ba sama kawai yake kallo yana jin yanayin na yi masa daWi ya Wora da "Uban ?an daba nake maganin ?ananun yara masu Soyewa a sa?o, to cut you short sunana Lauje, ban du?o dan na saka muku makami ba, na zo na tafi da uban gidan naku salin alin akasin hakan wajan bijire mini zai saka an samu kwacewar lissafi dar kenan" wanda ke kusa da Lauje mai suna Modara ya ce

"Ka saSo shi a wuya mana sai ka tsaya Sata yawun da Ubangiji ya halitta a bakinka Oga?"

"Ban zo don rigima ba, bisa umarnin Hon na zo wannan shine"

Darma ya matsa gefe yana nuna musu Mai dawa Moh kenan ya ce "Bisimillah gashi nan kuje da shi kuna da hannu na san" Moh ya sake juya musu baya maganganunsu da gaske ciwon kai da zafin zuciya suke ?ara masa hannunsa kawai yake dun?ulewa yana hura iska sama ko yaushe ya zama sa'annin yara irin su Lauje?

"Ji mana"

Mutallab ya juyo yana gyara tsaiwa idanunsa a birkice Lauje ya dinga kallon Mai dawa, shi bai ya yi tunanin haka yake ba yaji ana Mai dawa da Mutallab sai ya ji sunan Mutallab kamar na ?ananun yaran ganin Mutallab cikakken namiji a tsaye mai kakkauran hannu da buWaWWan ?irji gabaWaya jikinsa a murWe yake musamman damtsen hannun ya basar ya ce "Shige muje"

Da hannu Mutallab ya yi masa alama da ya zo ya tafi dashi, Lauje ya nufi wajan Mutallab ba tare da sanin cewa akwai shafin hannu a jikinsa ba ganin ba wani makamani hannunsa ya saka ya nufe shi. Yana mi?a hannu da sunan kama shi Mutallab ya yi masa wani naushi a gefen ?irji, nan take Lauje ya fara fari da idanu ?ashin gefen ?irjinsa ya yi ?ara ya sulale a wajan ba numfashi. Ganin hakan ya saka su Modara ja baya a tsora ce ya ce
"Kut ya bazar dashi ba, wannan mahaukaci ne"

"Bai mutu ba tafiyar zango ?alilan ya yi kawai ya samu karaya a ?irji, kar dai ku manta da Mai dawa kuke magana masu jeji da namomin jejin da kansu matsalar gajanci kenan kun tari mutumin dake da shafi a hannunsa duka Waya ka sume gwara ya saka maka kaifi daya saka hannu, ya zame muku hadda. Yi batu waye ya aiko ku?"

"Hon MaWatai"

"Wani abu ne haka? Me za a yi masa?"

Modara ya ce "Bamu sani ba, ya ce yana bu?atar ganinsa shi kaWai kuma a sirrince"

"To ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login