Showing 1 words to 3000 words out of 17403 words
Chapter 1 - UNCLE NE BOOK COMPLETE BY NIMCY SARAUTA
_✨UNCLE NE...!!✨_
_✍NIMCYLUV_
*1*
Allahamdulillah Allahamdulillah Thanks to almighty Allah (swt) for giving me opportunity to start
this book, Ma sha Allah nasan You have been waiting for me so long,to NIMCYLUV is back sai
a KAKKAƁE zani a gyara zama, special greeting to Maimuna Abdullah(heroine) love you wix all
my hrt, secondly Hafsat Rano alkairin Allah ya kai maki,Queen Nasmer my sturbbon friend love
you,How can I forget my lovely fans...? kuna raina kamar yadda kuke saka ran ganin littafaina
thanks for the love and care hrt You all here is my new book UNCLE NE am sorry to say na
ajjiye maganar TUGGU BIYU i have a big issues da nayi hakan so guys follow my pen...love
my story, dedicated to my papa ALAHAJI SULAIMAN DAGACIN JA'OJI.
wanda bai karanta book ɗin nan ba,bazan ce an barshi a baya ba domin a koda yaushe yana
iya karantawa,amma idan ba'a fara dakai ba..it is going to be a hit that i promise You,nayi
wannan littafin ne from The very depth of my heart,wani time ɗin nai dry wani lokacin nai
hawaye,wani tym ɗin ina jin waƙa.
officially welcome You to the very frist chapter of UNCLE NE..
_Bisimillah_
IBADAN
is the the capital and most populous city of Oyo state in Nigeria.
SANGO AREA
Unguwar Masu kuɗi ce,Unguwa ce da babu wanda ya damu da rayuwar wani,Unguwa ce
mai cike da Attajirai,Malamai,haɗi da ƴan boko,Haka kuma Unguwa ce mai cike da ƴan duniya
wanda idanunsu suke a buɗe,basa jin wa'azi balle faɗa,haka nan babu wanda ya isa ya
tunkaresu da niyyar gaya masu kuskurensu.
Dugun layine wanda yake shimfiɗe da lafiyayyan titi wanda ya ƙara fito da ƙyan unguwar.
Wasu jajaye fitilone sukaiwa titin unguwar ƙawanya,wanda a kullum suke haska unguwar
musamman cikin dare,gefe da gefen titin wasu green flowers ne masu ƙyau wanda suke fidda
wani daddaɗan ƙamshi.
Can kusan ƙarshen layin wani haɗaɗɗan gidane ginin zamani,tun daga jikin tafkeken get ɗin
zaka san tabbas wannan gidan bana ƙana nan mutane bane,ajikin get ɗin anyi rubutu inda aka
rubuta hause no 133.
Sosai harabar gidan taƙawatu da kurayan furanni na zamani masu ƙyau da tsari,Compound
ɗin gidan cike yake da manyan motoci na zamani irinsu,boggatti,ferari,da sauransu.
Yanayin ginin gidan irin mai sama da ƙasa ɗinanne ma'ana dai ginin bene mai hawa biyu.
Side ɗin parko na gidan wanda ya kasance hawan farko na gidan,babban parlour zaka fara
tararwa gefen parlour'n kuma ɗakuna ne masu ɗan yawa kusan bedroom ɗin shida,left hand
ɗina nayi domin shine yafi jan hankalina fiye da sauran part ɗin, Tun daga ƙaramin parlour'n
dake cikin part ɗin na fara jiyo fitar numfashi mai kama dana zaucewa a hankali na tura kaina
cikin bedroom ɗin kasancewar a buɗe yake,saurin tsayawa nayi sabida ganin wata ƙyaƙƙyawar
matashiyar mata wacce aƙalla ba zata huce shekara ashirin da biyar ba zuwa shida.
Tana durƙoshe gaban bed ɗin dake ɗakin yayinda hannunta ke riƙe da gadon gaba ɗaya jikinta
rawa yake,banda nishi da gurnanin wahala babu abinda ke fita a bakinta,yayinda turtsetsen
cikinta ya sauka zuwa mararta banda juyawa da motsi babu abinda “ƊAN” cikin nata yake,da
alamu shima ya ƙago yazo duniya,karkarwar jikin tane ya tsananta gaba ɗaya ta jigata ta fita
haiyacinta banda kiran sunan Allah babu abinda bakinta yake ke faɗi,Can ƙasan zuciyarta kowa
maganar data keson furtawa a saman bakinta tane ta kasa,burinta bai huce bakinta ya buɗe ta
samu damar faɗin abinda ke damunta cikin rai da kuma zuciyarta,Runtsa idanunta tayi da
ƙarfin sabida wani juyi da abin cikinta yay tare da naushin mararta nan take jini ya ɓalle mata ya
soma zuba,cikin yanayin na fitar hayyaci tare da zaucewa haɗi da fidda rai ta ɓude baki da ƙyar
tace.
"Ya hayyuu ya ƙayyumuu
ya kaliƙu ya zul arshidd majidd,ya fa'alulluma yurid biraha matika astagisuuu"
Takai ƙarshen addu'ar tana sakin wani fitinanan nishi wanda ya kusa ta fiya da numfashinta ya
rabbi nan take wani..
Kamar amafarki Mameey dake ƙwance bisa tangamemen royal bed ɗinta ta jiyo sautin
numfashin Zulfa cikin kunnuwanta lumshe idanu tayi tana jin kamar a magagin barci take, da
sauri ta miƙe zaune daga ƙwancen da take wani irin hantsilawa Mameey tayi daga gadon zuwa
ƙasan gadon,a gigice ta fara gyara ɗaurin zaninta dake kuncewa sabida fargaba,tabbas idan
bata manta ba yaune E.D.D Zulfa ya cika gaba ɗaya ta manta,cikin tsoro fargaba kiɗima tashin
hankali ta fara sakkowa daga stairs ɗin benen.
Tun a babban parlour ta fahimci aƙwai matsala kuma ta ƙara tabbatarwa kanta Zulfa naƙoda
take da sassarfa ta ƙarasa shiga cikin part ɗin Zulfa,cikin sauri Mameey ta ƙarasa shiga cikin
bedroom ɗin,tana shiga ta samu Zulfa durƙoshe cikin jinin wanda ya ɓata jikinta gaba ɗaya,da
sauri ta ƙarasa wajanta tana salati tare da faɗin.
"Zulfa mene zan gani haka?kika zauna cikin ciwo kin san illar duguwar naƙuda kowa?ohhh ni
Salamatu yau naga abinda yafi ƙarfina wannan wanne irin jinine haka?mun shiga uku",
Ta faɗi hakan tana sakin kukan tausayi halin da Zulfan ke ciki,sabida ganin jinin dake zuba ta
jikinta ga kuma yadda numfashinta ke sarƙewa jikinta banda rawa babu abinda yake,da hanzari
ta ƙarasa matsawa inda take sabida kan babyn da taga yana fitowa,wata jijjiga Zulfa ta fara
idanunta na kafewa.
Ganin hakan yasa Mameey sakinta tare da ficewa da gudu tana tafe tana ƙwala kiran sunan
Alhaji!! Alhaji!! Alhaji!!!
Alhaji Kabeer na kishin giɗe saman wata lafiyayyiyar sofa,hannunsa dafe da saitin
zuciyarsa,yana jin yadda take buga masa da ƙarfi,ga wani raɗaɗi da ɗaci daya keji a cikin
maƙoshinsa,gefe guda kuma yana jin tsoro da fargaba haɗi da zullumi wanda bai san kona
menene ba. Ya rasa dalilin daya sanya yake mafalki mara ƙyau akan Zulfansa mace mafi soyuwa a cikin
ransa,tabbas bazai jure ganinsa cikin wannan halin mafalkinba,kamar yadda bazai jure ganin
Zulfa cikin wani hali ba.
Saurin buɗe idanunsa yay jin muryar uwar gidansa na kiran sunansa,da sauri ya dira daga kan
sofar yana fita sukaci karo da Salmerh a birgice ya kalli Salmerh tare da faɗin..
"Salmerh mene ya sami Zulfa?..kada ki sake bakinki ya faɗi babban kalamai dazai sanya
zuciyata bugawa.."
Bakinta na rawa tace
"Zulfa haihuwa inajin.."bai bari ta ƙarasa maganar ba ya ƙwasa da gudu zuwa part ɗin Zulfa.
da gudu Mameey ta mara masa baya,suna zuwa tana haihuwa ganin zata danne jaririn ya
sanya Alhaji Kabeer saurin isa gareta,yana zuwa ya saka hannu ya gyara mata zama,tare da
amsar rezar hannun Mameey ya yanke cibiya,cikin ikon Allah a lkcn mahaifa ta faɗo,yana ganin
haka ya saka hannu ya miƙar da ita tsaye cikin murna da farin ciki ya rungometa a jikinsa yana
shafa sumar kanta idanunsa fal hawayen farin ciki,bai taɓa tunanin zai samu haihuwa nan kusa
ba,sai gashi ubangiji ya azurtashi da ita a lkcn dabai taɓa tunanin samunta ba,tabbas ya yarda
da wannan kalmar da ake cewa inda rai da rabo,haka kuma mutum baya fidda rai da samun
rahamar ubangiji,domin shine mai bayarwa a lkcn da yaso haka kuma shine mai hanawa a lkcn
dayaso,wasu hawayene suka fito daga cikin idanunsa cikin muryar farin ciki yace.
"Thank you soo much my Anuuu,Allah yay maki albarka nagode sosai da ƙyautarki nagode
Allah ina sonki Allah ya baki lafiya"
Mameey janye jaririn tayi jin yana tsala kuka a wani zani mai ƙyauta ta ɗaukesa,kana ta zaune
bakin bed,catton da zaitun ta fara goge masa jiki da ita,murmushi tayi ganin yadda yake ƙoƙarin
sanya hannu a baki da alama da yunwa yazo,sai tsala kuka yake,a cikin ranta take jinjina ƙyan
yaron da kuma baiwar da ubangiji yay masa,domin ƙwayar idanunsa ta kasance blue
ce,kamarta turawa,ga wani ɗan cindo a gefe yatsanshi.
A sanyaye Zulfa ta rungome mijinta Alhaji Kabeer idanunta na zubar da ƙwalla tace "Yaa
rahamanu"murmushi yay tare da sumbatar goshinta,kamar an tsikareta ta sanya hannu ta ture
Alhaji Kabeer daga jikinta,a hankali ta fara yin baya ganin hakan ya ƙara matsuwa kusa da ita
yana shirin kamata yaji ta fasa wata uwar ƙara,a gigice ya ƙarasa wajanta kafin ya riƙeta tasa
hannu ta hankaɗesa tare dayin waje da gudu jinin haihuwa nabin jikinta....
Idan kun bazashi ya amsu wajan mutane za kujine
08119237616
_✨ UNCLE NE ✨_
_✍ NIMCYLUV_
*2*
Duk inda ta taka sai jini ya zuba hakan ya tabbatar masa da cewa ba ƙaramin jini ke zuba a
jikinta ba,gudu take sosai tamkar ba mara lafiya wacce ta haihu ba, Yadda take indai ba ficewa
tayi daga hankalinta ba babu shakka zai iya cewa aljanunta ne suka ƙara mata gudu ganin
yadda take gudun ko joyowa ba tayi, Duk yadda yaso yacim mata kasawa yay sai nisa take
masa,kasan cewar harabar gidan nada girma sosai yasa tun daga nesa yake ƙwalawa mai gadi
kira,amma ya makara sabida Malam Habu yana ɗakinsa yana sharara bacci kamar
matacce,ganin harta isa bakin ƙofar wajan gate tana shirin buɗewa yasa Alhaji Kabeer buɗe
murya iya ƙarfinsa jikinsa duk rawa yake cikin kiɗima da firgici yace,
"No!! Zulfa stop kada ki fita bakki ganin halin da kike ciki ne?zoga babbynmu na kuka ke kaɗai
yake buƙata,ke ya keso yaji ɗumin jikinki come back please my dear innalillahi wa'inna ilaihir
raji'un meke shirin faruwa da Zulfana menene hakan?wanne irin gudu ne haka?ya rabbi ka
kawomin ɗauki" ya faɗa idanunsa na kawo hawaye,ina Zulfa kam sam bata cikin hayyacinta balle taji abinda
yake faɗa,domin da zarar tayi niyyar juyawa sai taji ihu da gurnani sun cika mara kunne,can
gabanta kuma wata inuwa da kuma tarin bishiyo haɗi da furanni masu ƙyau take ganuwa,abin
mamakin idan ta kusa da bishiyoyin sai taga sun ƙara yi mata nisan gaske,hakan tasa take ƙara
gudu domin ta isa garesu cikin sauri tasa hannu ta buɗe ƙofar dake jikin gate ɗin,tana buɗe
ƙofar ta fice da gudu.
Layine irinna masu kuɗi babu kowa duk suna cikin gida jensu hakan ya bawa Zulfa damar
damar gudu a tsakiyar layin a haka harta isa babban titi inda manyan motoci suke shigewa.
Ɓan garan Alhaji Kabeer duk yadda yaso ya buɗe ƙofar gate ɗin kasawa yayi sabida cijewa da
ƙofar tayi sakamaƙon rufewar da Zulfa tayi mata da ƙarfi wajan fita,cikin zafin nama yasa ƙafa
ya daki ƙofar nan take ƙofar ya buɗe hakan yay dai-dai da lokacin Malam Habu mai gadi ya fito
daga cikin ɗakinsa hannunsa ɗauke da gora yana shirin kaiwa Alhaji Kabeer duka a tunaninsa
wanine ya shigo gidan kasan cewar bacci yake shiyasa bai gane waye a bakin gate ɗin ba,cikin
sauri haɗi da jarumta Alhaji Kabeer ya fice daga cikin gidan tare da soma ke waye layin yana
faman ƙwalla kiran sunanta Zulfa!! Zulfa!! Zulfa!! amma babu ita babu labarinta,Innalillahi
wa'inna ilaihir raji'un ya fara ambata a fili,ina zashi?ina zai ganta?wazai tambaya?shin mene ma
ya fiti da ita a halin da take ciki?menene ya sameta?wannne irin firgicine haka wanda har zai
saka ta manta da “ƊAN” data haifa,ya rabbi ka kawomin ɗauke wannan wanne irin abune
haka?meke shirin faruwa ne damu baki ɗaya,zubewa yay a tsakiyar layin tare da kifa kansa a
tsakanin cinyoyinsa duk yadda yaso ya daure kasawa yay,cikin raunin zuciya ya fashe da
kuka,ya ɗauki a ƙalla kusan 30minutes yana durƙoshe kafin ya miƙe da sauri tare da ɗaukan
wayarsa dake cikin aljihu ya fara dailing wata number,ringing ɗin farko akai picking call daga
can ɓangaren Acp Anwar ya gyara tsaiwarsa tare da saurin ɗaga hannu ya buga ƙafa yace.
"Evening sir fatan lafiya? domin na daɗe banga miss call naka ba"
Numfashi Alhaji Kabeer ya sauke mai ƙarfi tare dasa hannu ya share zufar dake bin saman
ƙoshinsa,gaba ɗaya jikinsa rawa yake kallo guda zakai masa kasan cewa baya cikin hayya
cinsa,ga kuma tsantsar tashin hankalin dake yawo cikin ƙwayar idanunsa,lokaci guda duk ya
sosoce tamkar ba Alhaji Kabeer Mai atile ba,ga yadda narkakkun idanunsa suka sauya kala
daga fari zuwa jaa jijiyoyin kansa sun fito sunyi raɗa-raɗa,jin yay shuru babu alamun zai
magana yasa Acp Anwar ƙara kamewa waje guda haɗi girgiza kai cikin kiɗima shima ya ƙara
faɗin.
"Sir are you okey?komai dai-dai ne ko?"
Ya ƙara faɗa cikin hausar shi wanda baya fita sosai,ajjjiyar zuciya Alhaji Kabeer ya sauke tare
da fesar da iska daga cikin bakinsa murya na rawa yace.
"Acp munyi missed Zulfa yanzu,ka yaɗa photonta da ba yananta a kafafen sada labarai
redio,t.v,social media,gaba ɗaya a baza rahotanni kota ina,wannan ya zama breaking news
kada kayimin wasa Anwar rayuwata na rasa,ina tabbatar maka idan har Zulfa tayimin nisa
tabbas zan iya shiga wani hali,zuciyata ba zata jura ba,ina gaya maka hakanne domin ina maka
kallon ɗa a wajena bana da kowa wanda zai shigemin gaba,ka tabbatar duk inda tashoshin
mota,jirgi,suke kasa an rufesu duk da mana da tabbacin zatai nan wajan"
zubewa Acp Anwar yay akan sofarsa dake makeken office ɗinsa,Aunty Zulfa missed?wannan
shine tambayar daya kewa kansa amma babu amsa,shi kansa rayuwarsa tana cikin wani hali
indai ba aga Zulfa ba,domin itace shedar kawai data rage masa akan damuwarsa itace
garkuwarsa wacce zata tseratar dashi tayaya wannan abun zai faro,anya ba sanya hannun
wasu akan wannan labarin,numfashi ya sauke tare da faɗin.
"Amma baka ganin aƙwai sa hannun wasu cikin wannan abun?tayaya mace zata gudu a lokacin
data haihu lokacin daya dace ta zauna ta huta a kuma kula da ita,tayaya uwa zata gudu tabar
ɗanta gaskiya nidai ina shakku akan wannan matsalar"
Cikin ɓacin rai da kuma takaicin abinda Acp Anwar ya faɗa,Alhaji Kabeer yay sauri daga masa
tsawa ta hanyar faɗin.
"Kai!! banson zancan banza,shikenan Ubangiji bazai taɓa jarabtar bawansa ba sai ace wanine
dalili ko kuma wani yay asiri,babu ruwana da wannan shirman kabarni da abinda na keji kada
ka ɗuramin hakkin wasu akaina haka kurum,Allah shi kaɗai yasan abinda yake ɓoye,kafin nan
da awa guda ina son na sami labari akan Zulfata" Yana faɗin hakan ya kashe kiran kana ya juya ya nufi gidansa,yana zuwa ya shige cikin part ɗin
Zulfa inda Mameey ke zauna tana faman jijjiga babbyn daya keta faman tsala kuka duk ya cika
gidan.
Ganinsa cikin tashin hankali wanda bata taɓa ganin irinsa ba,a duk tsayin shekarun da suka
ƙwashe tare da juna,jiki a sanyaye ta sanya hannu ta ɗauki babyn tare da ƙara sawa inda yake
tsaye ya sunkuyar da kansa ƙasa,babyn ta rungome a ƙirjinta tare dasa hannu guda ta taɓa
kafaɗar Alhaji Kabeer,still bai ɗago ba hakan tasa tayi sauri ƙarasawa gabansa,abinda ta gani
yay mugun bata mamaki,zata iya cewa wannan shine karo na biyu da taga hawaye na bin
fuskar mijin nata,da lokacin da aka ɗaura masa aure da Zulfa sai kuma wannan ranar,cikin
tashin hankalin daya sameta itama tace.
"Dan farin ciki yaywa mutum bai dace yay kuka ba,zaifi ƙyau ace al'wala kayi tare dayin sallah
domin miƙawa Allah godiyarka bisa wannan ni'ima da yay maka ta baka ƙyautar mutum mai
tarin baiwa,amma kuka sam bai dace da fuskar ƙwarzon namiji kamar ABBOU ba,idan kayi
kuka ita Zulfan tayi me?" Sunan Zulfa data faɗa ya sashi saurin ɗago kansa tare da saka hannu ya amshi babyn ya
manna a ƙirjinsa,wata sassayiyar ajjiyar zuciya ya sauke lokaci guda kuma wasu zafafan
hawaye suka ƙara fituwa ta cikin idanunsa,so yake yay kuka irin kukan nan mai yawa wanda
yake tafiya da ƙunci da kuma zafin zuciya amma sam ya kasa,sai ajjiyar zuciya da yake
saukewa a jajjere,ganin yanayinsa gaba ɗaya ya sauya kamar ba mijinta wanda ta sani da
dauriya da kuma jarumta ba,mai tsayawa akan ra'ayinsa,mutum ne shi kaifi guda babu wani
wanda ya isa ya sauya masa abinda yay niya,cikin muryar tashin hankali Mameey ta ƙara
taɓashi tare da faɗin.
"Wai lafiya naga gaba ɗaya ka sauya make faruwa ina Zulfa take?tana ina ya kamata ace tayi
wanka yanzu sabida jikinta ɗanye ne babu ƙwari"
Sai a lokacin ya ɗaga kai ya kalleta da jajayen idanunsa cikin wata iriyar murya mara sauti
wacce kuka yaci ƙarfinta yace..
"Rayuwata data babynmu tana ciki matsala,zamu shiga cikin ƙunci da baƙin ciki haɗi kuma da
kaɗaici,mun rasa farin cikinmu,walwalarmu,jin daɗinmu,uwa uba garkuwanmu,Zulfa tayi mana
nisa Mameey nisa mai yawan gaske,ban san ina take ba ban san inda zan sameta ba,aljanu
sun hauƙatamin uwar yarona Zulfa ta haukace..." Cikin wani sabon tashin hankali Mameey ta tari numfashinci ta hanyar faɗin.
"What! hauka fa?tayaya hankan zai kasance tayaya Zulfa zata haukace,nasan cewa naƙuda
nasa mutum yay jijjiga amma man taɓa ganin inda ta haukata mutum ba,nasan cewa Zulfa nada
mutanan ɓoye amma ban taɓa jin inda aljanu suka haukata mutum ba,mun shiga uku innalillahi
wa'inna illaihir raji'un,Allahumma ajirni fil musibati wa'aklifni kairan minha,Ubangiji ka bai yana
mana Zulfa cikin ganggawa"
Ta ƙare maganar tana saka wani kuka mai tsuma zuciya,kukan data daɗe batai
kamarsa,soyayya dan Allah ta kewa Zulfa,bata taɓa ɗaukanta matsayin kishiya ba,akoda
yaushe kallo ƙanwa take mata,hatta lokacin data samu ciki ji take tamkar ita ta samu cikin,haka
kuma yanzu kallon babyn take tamkar wanda ta tsuguna ta haifa. Alhaji Kabeer ƙyawawan idanunsa ya zubawa jaririn ganin yadda yay shuru a ƙirjinsa sannu a
hankali kuma bacci yay gaba dashi,halittar jaririn ya kalla,musamman yadda yaga suna
muguwar kama da Zulfansa,farine tas irin farinnan na shuwa arab,ga wani dugun siririn hancin
daya kawo har wajan bakinsa,uwa uba tulin sumar kan jaririn wacce tai ƙwance abinta baƙa
siɗik sai shegeƙi take,ga wani ƙaramin bakinsa wanda yake ɗauke da jajayen laɓɓansa sai
sharning suke,kallonsa ya sakko zuwa ga yatsun hannunsa a hankali yasa hannu ya taɓa ɗan
cindon dake gefen ƙaramin yatsanshi.
wata zafaffiyar