Showing 3001 words to 3444 words out of 3444 words
Chapter 2 - Auren Nesa Book Complete By Khadijah Abdullahi Bature
minta da ita,
"Bari nad'akko mota ta a gurin fakin ,na amsa mata da to.
Barin gurinta keda wuya sai ga wani dattijo bahaushe ya karaso gurina a cikin ujila ,"duk a
binda kuke yi da waccan matar ina ganinku na ganki yar arewa a dalilin suturar da kika Sanya
Kuma na ga alamun ke musulmace saboda haka ki gaggauta barin gurinnan kafin ta dawo, ni a
nan nake yin sana,a ta ina ganin yadda suke zuwa su na yaudarar baki da zummar taimako
musamman idan sun lura mutum ya na cikin damuwa don ai saurin amincewa da su.
Indai tak'aice miki yan k'ungigar Shan jini ce ,ki yi gaggawa kibar gurin nan , ni kaina ina cikin
hatsari in ta ritsani a nan tare da ke , har ya juya zai tafi ya juyo meyene matsalarki ? na ce cikin
rawar murya ku ku din mota ta ne ya fadi , ya ciro dubu uku ya mik'omin "ungo wannan ki
zagaya can wajan fasinjoji ki naimi taimako ya yi saurin barin gurin na neme shi na rasa ya
b'ace tamkar walkiya.
Nima na yi sauri na ta shi tunda na samu d'an sassauci a dalilin abincin da ta siyamin, da
sassarfa na bar gurin na za gaya ta baya inda fasinjojin suke na shige cikin mutane inda na
San da wuya ta ganoni a nan na fara magiya kamar yadda mutum ya bani shawara ina naiman
taimako a karo na farko a cikin rayuwata.
A bun mamaki saiko naga a nata mik'omin saboda duk wanda ya ganni sai ya tausaya min ,
musamman da sukaji ina kuka ina cewa kudin motata ne ya fadi daga cikin fasinjojin wani
mataship wanda daga ganinsa naira ta zauna ya matso ya yi min magana a cikin tausayi" wane
garin Zaki ? na ce Kano ya ce a she tafiyar mu d'aya to ina zuwa, in takaicewa maikaratu nan
ya biyamun ba a jima ba muka mika mukad'au hanya .
Tunda muka zo Zariya na farajin kamshin garin Kano, na ji nutsuwa ta fara saukar min.
Masha Allahu la kuwwata illabillah
Shi ne a bunda na fad'a lokacin da na ji matashinnan da ya biyamin kud'in mota na ji ya na
cewa mun iso garin Kano ina zaki?, na sa kaina ta taga ina shakar kamshin garina wata
daddad'ar iska ta doki fuskata na lumshe idona , bansan lokacin da fatar bakina ta fara furta
kirarin garin kanoba da k'arfi , Kano ta dabo tunbin giwa tunjumin gari mai dala da goron dutse
mai Mata mai Mota.
Alhamdulillah.