Showing 1 words to 1431 words out of 1431 words
AHMED B. SARDAUNA
.
FACEBOOK ACCOUNTí ½í±‡í ½í±‡
(Ahmed bello sardauna)
WHATSAPP NUMBERí ½í±‡í ½í±‡
(08169047840)
.
NOTE: bana tura littafai a private, amma inada group na whatsapp da facebbok..
.
.
Gyaran fata da kankana
Kankana na daya daga cikin ‘ya’yan itatuwan dake dauke da sinadaren gyaran jiki da gautsin
fata da kuma rage tsufar jiki domin tana dauke da sinadaren dake wanke maikon dake taruwa a
magudanar gumi a fata wanda yawanshi ke haifar da fesowar kuraje da dama. Don haka,
amfani da kankana a jiki na da matukar mahimmanci sosai ga rayuwarmu ta yau da kullum. A
yau na kawo muku hanyoyi da dama da za’a bi domin yin amfani da kankana domin samin fata
mai laushi da kuma sheki a kodayaushe
Kodewar fuska; markada kankana tare da gurji sannan a rika shafawa kamar sau biyu a rana na
matukar magance wannan matsalar. Sannan za’a iya markada kankanar zalla sai a dauko
auduga ana tsomawa ana shafwa a fuska sannan a barshi ya bushe na tsawon mintuna goma
sha biyar. Za’a iya markada kankana da ganyen na’ana’a sannan a rika shafawa a wannan
wajen da fatar ta kode. Amma abu daya nake so a yi amfani dashi a cikin ababen da na lissafo.
Domin yankwanewar fata;a markada kankana sannan a zuba mata zuma kadan sai a rika
shafawa a inda fatar ke yankwanewa sau biyu a rana. A samu kankana da ruwan lemun tsami
da sukari sai a hadasu guri daya. Kafin sukarin ta narke sai a rika dirzawa a inda fatar ta
yankwane domin mikar da fatar. Rage shekaru; a samu kankana da man zaitun da kindirmo da kuma kwanduwar kwai sannan a
kwaba a rika shafawa a fata a kullum domin samun sakamako mai kyau mai inganci. Za’a iya
markada kankana sannan a samu ayaba a kwaba sannan a hadasu guri daya sai a rika
shafawa a fata. A samu markadaddiyar kankana da madara da kuma fiya sannan a kwaba a
rika shafawa a fata domin samun sakamako mai kyau.
kurajen fuska; a sami kwallon kankana a busar a rana sannan a daka yayi laushi sannan a
tafasa ruwa a zuba sai a tace sannan a rika wanke fuska dashi .
Gautsin fata; a markada kankana sannan a zuba mata man ridi da na kwakwa sai a shafa a fata
a barshi ya kai tsawon mintuna ashirin sannan a wanke.
Yadda za a magance kodewar fata
Kodewar fata na aukuwa ne a lokacin da mutum ya kasance yana yawan shiga cikin rana domin
neman halaliyarsa ko kuma don yini a rana. Idan hakan ta kasance, sai fatar ta zama baka.
Wannan abu ya fi aukuwa ne a fuska. Sai a ga fuskar gefe daya ta yi baki daya gefen kuma da
dan haske. Wannan abu ba a sanin lokacin da suke faruwa. Shi ya sa a yau na kawo muku
hanyoyin da za a bi don neman kariya daga wadannan kunar ranar ko kuma kodewar fata.
• Ruwan dankalin turawa; a fere dankalin turawa sannan a wanke sai a kankare a matse ruwan
sannan a rika shafawa a fuska musamman inda fatar ta kode. Yin haka na magance matsalar
fatar sannan kuma yana kare sake aukuwar hakan.
• Madara ; a samu madara a sanya a gidan sanyi har sai ta yi sanyi sosai sannan a samu tawul
karami a rika tsomawa ana goge fuskar da shi. Madara na sanya hasken fata sannan kuma
tana warkar da wannan kodewar fatar.
• Ruwa; a yawaita shan ruwa sosai idan ana dauke da wannan matsalar sannan za a iya sanya
ruwan ya yi kankara sannan a rika shafa wannan kankarar a inda fatar ta kode.
•Gurji; a samu gurji sannan a yanka sannan a sanya a gidan sanyi har sai ya yi kankara sannan
a rika shafawa a wannan wajen da fatar ta kode ko kuma a rika daurawa wurin har sai ya narke.
• Koren ganyen shayi; za a iya tafasa koren ganyen shayi hade da na’ana. Bayan sun tafasa
sannan a bari hadin ya jiku kamar na tsawon sa’a daya sannan a sanya a gidan sanyi, sannan
a wanke fuskar da hadin ko kuma a samu auduga ana shafawa a inda fatar fuskar ta kode.
• Ganyen ‘aloe bera’; a samu wannan ganyen sannan a matse ruwan da ke ciki a rika shafawa
a fuskar a kullum har sai kodewar ta yi sauki. Wannan ganye na da matukar mahimmanci a
fatar mu don haka yana da kyau a kowane gida a shuka.
• Ruwan tuffa; za a iya samun wannan ruwan ne bayan an kankare sannan a matse. Sai a rika
shafawa a fuska har sai ya bushe. Haka za a rika yi a kullum.
• Masu karatu kada su hada duka wannan hadin su ce za su yi shi a lokaci guda. Sai dai su zabi
daya daga cikinsu. Hada wadannan ababen da na lissafo na iya haifar da wata cutar fatar
fuska. Da fatan za a kiyaye.
AMFANI DA AYABA WAJEN MAGANCE MATSALOLIN FATAR FUSKA
Ayaba: Wata ‘yar itaciya ce wacce ta ke kunshe da sinadarai masu muhimmanaci ga lafiyar
jikin dan Adam. Ayaba na kunshe da sinadarai da suka hada da bitamin A, B, da E.
Bayan amfani da ake yi da ita wajen girke-girke, hada lemuka, ko kuma aci haka a matsayin
kayan marmari, muhimmanci ta bai tsaya anan ba, domin tana bada babbar gudumawa wajen
gyara fatar jikinmu, musamman fatar fuska, domin tana kunshe da sinadaran da ke hana fata
bushewa, cire matacciyar fata/saba, kare fata daga saurin tsufa musamman in za ki juri amfani
da ita a kullum. Amfaninta ga fatar mu bai tsaya anan ba, don tana bawa fata kariya daga
kunar hasken/zafin rana idan aka yi amfani da ita wajen samar da wani hadi na abin shafawa a
fuska wanda a turance ake kira da BANANA FACE MASK.
ABUBUWAN DA ZA KI BUKATA WAJEN KWABIN AYABA. (BANANA FACE MASK).
*Ayaba guda daya 1
*Rabin cokali na zuma.
* Rabin cokali na ruwa lemun tsami.
Kafin mu kai ga yadda zamu kwaba wannan hadin, yana da kyau mu san amfani kowane abu
da na lissafo a sama.
Ayaba- Hana fatar fuska saurin tsufa, rage girman kofofin fatar fuska ta yanda dati bazai samu
damar shiga ba har yayi silar haifar da kurajen fuska.
Zuma- Na bawa fata kariya daga bushewa, haskaka ta, da rage fitowar kurajan fuska fitowa.
Lemun tsami- Na kunshe da sinadarai masu kare fata daga fesowar kuraje, da haskaka ta.
YADDA ZA KI HADA KWABIN AYABA (FACE MASK)
Ayabar ki mai kyau guda daya, sai ki bare ta a kwano mai tsafta, ki matse lemun tsamin ki, sai ki
ajiye shi a gefe, wannan ayabar da ki ka bare za ki dauko sai ki markada ta a bulanda(
blender)ko kuma ki yi amfani da ludayin karfe ki daddaka ta har sai ta narke.
Bayan kin gama wannan sai ki dauko matsatsan ruwan lemun tsaminki, ki zuba rabin cokali
akan wannan ayabar, sannan ki dauko zuma itama ki zuba rabi cokali, sai ki juya har sai ya
zama kala daya, sai ki ajiye agefe.
A binda za ki yi yanzu shi ne ki wanke fuskar, bayan kin tasne fuska da tawul sai ki shafe
wannan kwabin a fuskar bayan minti 15-20 sai ki wanke fuskar.
Uwar gida abinda zan ja hankalinki akai shi ne, ba wai zubar da ragowar kwabin za ki yi ba, sai
ki shafe a jikin ki kamar sauran minti 15 za ki shiga wanka, za ki iya yin haka sau biyu ko sati.
Sannan za ki iya amfani da bawon ayaba, bayan kinyi burushi, sai ki dauko bawon ki gurgurza
a kan hakoran ki, ke kanki sai kin yaba ha hasken su.
*Ayaba guda daya 1
*Rabin cokali na zuma.
* Rabin cokali na ruwa lemun tsami.
Kafin mu kai ga yadda zamu kwaba wannan hadin, yana da kyau mu san amfani kowane abu
da na lissafo a sama.
Ayaba- Hana fatar fuska saurin tsufa, rage girman kofofin fatar fuska ta yanda dati bazai samu
damar shiga ba har yayi silar haifar da kurajen fuska.
Zuma- Na bawa fata kariya daga bushewa, haskaka ta, da rage fitowar kurajan fuska fitowa.
Lemun tsami- Na kunshe da sinadarai masu kare fata daga fesowar kuraje, da haskaka ta.
...
Domin neman karin bayani ko tambaya, shawara ko gaisuwa mu hadu a WHATSAPP ko
FACEBOOK.
.
í ½í±‡í ½í±‡
FACEBOOK- ahmed bello sardauna
WHATSAPP- 08169047840