Showing 18001 words to 21000 words out of 153326 words

Chapter 7 - Ba Kowanne So Bane Book Compelet By Ouummey

Ummey   

22 Jul 2026

758

jin magana, ina fatan ki koya daga gare ta ko kya samu damar gyara
kura kuran ki na baya, ban na san rashin kunya gare ta dan ko ba aure Ita din gaba take da ke,
na san halin ta babba da karami dan haka in naji sabanin kwanciyar hankalin da na saba gani a
gidana to daga gare ki ne, ke kuma dear".

Ya fada tare da juyawa ga Sa'adah yana sake matse hannun ta cikin nasa, kana ya sassauta
Muryar sa zuwa sigar rarrashi da neman alfarma

"Ki.dauke ta kamar kanwar ki Please, abinda ta kuskure ki gyara mata kin san tana da lapses
da se an taimaka mata ta gyara, in da ta gaza ki kama mata, ki kuma cigaba da yi min biyayyar
da na sanki da ita, ki kara kaimi wurin kyautata min, ina tabbatar miki in kika yi hakan babu wata
ya mace da zata iya kai ko da kwatankwacin matsayin ki a raina talkless of ta kamo ki har ta fili".
"I'll insha Allah Hubby".

Ta fada tana rungume shi, shima ya sa hannu ya kulle ta a jikin sa. Duk abin nan da suke yi ina
zaune ina assimilating kalaman sa a kaina, ta wani bangaren a boye yana nufin ina da mugayen
halaye sabanin salihan na matar sa, dan haka duk a ka sami matsala to fa ni ce..................��.

Vote
Comment
Share fisabilillah

Ouummey 📚��.



Ouummey 007 [ 21/06/2024 9:10 pm ]

BA KOWANE SO BANE...
(yake zama samu)

�� Oummey
Free book!!!







Ouummey 007

Page 7�⃣

_____________________Karo na biyu kenan ko nace na uku, Mama na ta fadi hakan lokacin
da take dukana, haka Hajiya Yayah ta fada min haka da tana min nasiha, yanzu gashi shima ya
bayyana.

Lallai dolen dole ma haka ne, na sani a da ina da taurin kai da kafiya, tsiwa, da rashin kunya in
an tabo ni, haka kuma ban fiya hakuri ba, se dai ban da su ban san wasu halaye nawa marasa
kyau ba dan bana neman tsokana kawai dai in an taba ni bana bari ne, haka ina da saurin sabo,
kawaye na kuma na fadin ba ni da rowa dan abu na be rufe min ido ba, ta daya bangaren ina da
tausayi, dan kusan almajira layin mu duka se da na sa aka sa musu kwano a gidan mu, daga
baya da nake sana'a take kai min kuwa rabin samu na a gidan marayu da kan almajirai yake
karewa, amma ban sani ba ko ina da wani hali mara kyau ne da ni ban fahimta ba, sedai koma
yayane yanzu na yadda, halaye na basu da kyau sam tun da har baki uku suka fada.

"Kwana bibbiyun yayi Hubby".

Kalaman ta suka maido ni hayyaci na, na kuma fahimci ana batun rabon kwana ne, lamarin da
ya sake sa gaba na ya yanke ya fadi, ban sani ba ko tsoro ne ya sa hakan ko kuwa fargaba, ba
na ce ba.

"To shikenan, Allah ya bamu zaman lafiya baki daya, me girki zata dafa da kowa a lokacin
kwanan ta, kina iya tafiya".

Zumbur na mike sanin da ni yake, ban tsaya komai ba kuma nayi falon da nake, hankali na
baya tare da su balle wata soyayyar da suka fara a falon ta dame ni.

Kan kujera na fada jagwab, se na sami kaina da addu'a da fatan Allah ya sa ba da ni za'a fara
zagayen kwanan ba yau, se kuma naji dariya ta kwace min lokacin da zuciya ta ta fada min
babu abinda ze kawo shi daki na, ko da ace da gaske ya raba kwanan sedai ya tafi dakin sa ya
kwanta, to mutumin da na lura ma san baya san kallan fuska ta me ze kawo shi kusa da ni.
Da wannan tunanin hankali na ya kwanta tas na tashi na canja kaya na zuwa na bacci na
kwanta bayan na kara feshe dakin da room fresheners.

Addu'o'i na nayi na bacci na rufe idanu na cikin neman bacci, sedan cikin ikon Allah shiru yaki
zuwa, har kusan awa uku ina kwance se juyi nake,daga karshe dai na shiga karatun suratul
Kahf a raina idanuna a rufe kamar me bacci.

Wajejen karfe sha daya na dare naji an Turi kofar daki na, na dan firgita amma se na sake
lafewa zuciya ta na bugu a kai a kai, ban ji an shigo bedroom din ba tsayin lokaci se na sadada
a hankali zuwa window na daga curtains din hannu na na rawa, se kuwa na sauke idanu na a
kan shi, yana tsaye yana karewa dakin kallo kafin kuma ya karasa kan doguwar sofar dake nan
ya zauna, a hankali na ga ya cusa yatsun sa cikin sumar kan sa yana hargitsawa.

Tsayin lokaci yana a haka kafin yayi addu'a ya gicciye ya kwanta, kujerar tayi masa kadan sosai
dan kuwa dogo ne Masha Allah, ni kaina da na fi Sa'adah tsayi kaina be karasa kafadar sa ba
da kadan, ita kuwa a damtsen hannun sa kan ta yake.

A sanyaye na saki curtains din na koma kan bed na zauna, daga ganin yadda ya kwanta ba se
an fada min ba yazo kwana ne, wato dai rabon kwanan da ni aka fara, wanda na sani dama
haka ya kamata se dai yanayin yadda auren yake ya sa naji bana san hakan.

A zaunen ina tunani se bugawar karfe É—aya na dare naji, dole na koma na kwanta, wani abin
mamaki kuma ko minti biyar ban yi ba bacci yayi gaba da ni.

Kiran sallar farko ya farkar da ni kamar yadda na saba tashi kullum, na zauna har baccin ya dan
saki idanuna kafin na tashi zuwa toilet nayi alwala na fito, dankwali na shimfida tare da sa daya
daga hijabs dina biyu da aka sakomin a kaya na wanda da shi nake sallah na tayar da nafila

kamar yadda nake yi kullum.

Addu'o'i kuwa cikin sallah ta har ba zan iya kayyade adadin da nake roko ba, mafi maimaituwar
addu'a ta itace Allah ya kawo sassauci a zuciyar iyaye na, ya sake reuniting tsakanin mu ya
kuma yafe min saba musu da nayi tun farko, se kuma Allah ya tashi kafadun Mama ya bata
lafiya.
Ina addu'a ina kuka cikin sujjada haka ma da na idar, a haka naji shigowar sa bedroom din, ban
yi mamaki ba dan nasan tashin wannan lokacin sabon sa ne tun farko ba kamar ni da se
shekarun baya na fara ba.

Alwala yayi ya fito daga dakin, lokacin har na mike dan tayar da wata sallar, a kan idanuna ya
buÉ—e wardrobe ya shiga daga kayana, na sani pray mat yake nema dan haka cikin sanyin
murya nace

"Babu pray mat se dai ka dauki dankwali na, nima akan shi nake yi".

Tsaki ya ja ya juya ya bar dakin gaba daya, ni kuma na tada sallah ta.

*****Masdooq****

Ba'a san ran sa ya raba kwanan ba se dai ba yarda ze yi da fadar Ubangiji, a da yaso ya share
sedai nasihar da yaji yau a masallaci yasa tsoron Allah sake ratsa shi.

Base iya shiga dakin da take ba dan baze iya haÉ—a makwanci da ita ba, haka kuma ba ze iya
haÉ—a numfashi da ita ba, kai gaba daya rayuwa da ita a under one roof ne be shirya wa ba,
amma tun da Allah ya tsaro hakan ze daure yake kwana a falo har zuwa lokacin da Allah ze yi
ikon sa a kan su.
A nan yayi addu'a ya kwanta kan doguwar sofa, sedai kamar abin shiri kamshin ta me sanyi da
dadi ne ya kai wa hancin sa ziyara wanda ke nuni da itama wajen zaman ta kenan a falon.

Da sauri ya tashi ya juya zuwa É—aya hannun kujerar, sedai shima hakan take, kawai dai be kai
can karfi ba.

Haka dole ba dan yaso ba ya kwanta, ya dade bacci be dauke shi ba har wajen daya da mintina
sannan, saboda yadda be yi bacci da wuri ba yasa be ji kiran farko da wuri ba, se da wasu
msallatan suka sake yi tukuna.

A hankali ya mike zuwa bedroom din ta dan a matse yake sosai, baya jin ze iya jira ya kai dakin
sa, ko da ya shiga banÉ—akin kamshi ne ya sake kai masa ziyara da ya sa ya lumshe ido batare
da ya shirya ba.

Yana daya daga cikin qualities din ta da a baya suke sake tsuma shi cikin so da kaunar ta, wato
tsaftar ta da tsananin soyayyar ta ga turare, zaman sa da ita da kuma neman ribato so daga
gare ta yasa shima ya koyi kauna ga turare ta yadda baya jin zafin yiwa turare zuwa hudu ko
biyar ya dire empty container.
Hali me kyau É—aya daya samu daga gare ta wanda har yau be iya ya bari ba, hasalima yana jin
dadin hakan, sedai Sa'adah kuma bata fiya tu'ammali da turare ba, ba wai bata sawa ba, a'a
tana sawa amma ba irin sawar da ya saba ya ke kuma kauna ba.

Hankali kwance ya gama abinda ze yi ya watsa ruwa tare da maida kayan sa kana ya daura
alwala ya fita.

Wardrobe din ta ya shiga bincikawa dan neman pray mat, duk da yayi mamakin ganin tsirarun
kaya a kwabar ba kamar yadda ya san ta da san suttura ba, se be baiwa hakan mahimmanci
ba, a lokacin ne yaji sassanyar Muryar ta da ada babu sautin da ya Kaita dadi a kunnuwan sa,
sautin dake ratsa jinin jikin sa ya kara masa so da kaunar ta ya kuma yi increasing heart beat
din sa.

Tsaki ya ja mata bayan jin abinda tace, haushi da tsanar ta suka sake tuko shi, shi be shiga
harkar ta ba haka kuma baya san ta shiga tasa, to a kan me zata masa magana.

Wannan yasa ya fusata ya fice daga dakin tare da mata banging kofar.

Sallah ya tada a dakin sa na nafila da shafa'i da wuturi, ana kiran sallar biyu kuma yayi
raka'atanul fajr kana ya wuce masallaci.

**Ina idar da Sallah na tashi na shiga gyaran daki na batare da na koma bacci ba, dan ban
manta ba jiya yace me kwana ce zata yi girkin duka gida.

Karfe shida da rabi na fita zuwa falon, na dan kare masa kallo sannan na wuce kitchen, ja nayi
na tsaya turus cikin karewa kitchen din kallo, nawa ne dai na shekarun baya ba'a can ja komai
ba hatta woodds din, kawai dai an canja paint ne, se gaba daya na ga yayi min wani daban
haka kayan cikin sun min yan tsurut, dan kuwa lokacin yana nawa a cike yake damkan da
kayan amfani kama daga kan electrics zuwa ragowar kaya, dan hatta freezer biyu ne haka ma
fridge dogo da karami, yanzu kuwa duk daidai ne.

Shiga nayi kan shawara da zuciya ta kan in taba mata kaya ko kar in tava, amma ai in ban taba
ba bani da kayan yin amfani, dan haka tabawar ta zama dole gare ni, se nayi sighing na bude
freezer na fiddo naman kaza, wani bowl me dan fadi na dauka na zuba ruwa a ciki se na saka
kazar na bar ta ta narke, gefe daya kuma na debo chips na shiga peeling.
Cikin abinda be kai awa ba na hada hadadden farfesun kaza, chips da kwai na kuma dafa
shayin da yaji kayan kamshi.

Komai na zuba shi a inda ya dace kana na ake kan kitchen island na fita falo, har lokacin me
aikin bata fito ba wanda so da yawa tun shida na ke jin fara aikin ta amma yau shiru, se kawai
ban jira ta ba na shiga gyaran falon da kaina, within minutes se gashi na kammala, na koma
daki na na dauko turaren daki na na fesa na fesawa na wuta kuma na zuba a burner na jona.
Take kamshi me sanyin dadi ya cika falon se kuma lokacin na koma kitchen na shiga fiddo
warmers din zuwa dining, na jera su in style na ake duk abin bukata sannan na wuce bedroom.

Wanka nayi na canja kaya zuwa abaya peach color na gyara gashi na na sa masa ribbon, daga
gaba kuma na tsaga shi in style kana na feshe shi da turaren gashi, karamin mayafin abayar na
ware na nada shi se ga shi cif a kaina, ta gaba gashi na dake kwance ya fito haka ta tsakiya a
bude take, ta baya kuwa parking É—in chignon dina ya sauka kan wuya na, se ya zama kamar
gammo ne me kyau na nada.

Dan kunne na karami da nazo da shi gidan tun aure na wanda gold ne na makala batare da
sarkar ba, hannu na kuwa na wadata shi da zobunan aure na.

Bayan kyau na, abu na farko da ke jan hankalin me kallo zuwa gare ni shine iya tsara gayu na,
duk munin kaya babu ta yadda za'a yi ya hau jikina kunna ya nuna muni, kai hatta towel da
bathrobe a jikina kyau suke yi kamar wani kayan kawa, hakan kuma akwai baiwa a jiki bayan
iya gayu, wannan naa cikin abinda kullum nake godewa Allah akai.
Karfe takwas saura kwata na tashi zuwa falo, basu fito ba har lokacin se na zauna kan sofa na
kunna TV ina kallon labaran safe, ina zaune Ya Masdooq ya fara fitowa daga dakin sa jikin sa
sanye da suits masu kyau maroon color, wanda suka amshi chocolate skin din shi ne kyau suka
fitar da tsarin kira da zubin sa na jarumi kuma kyakkyawan namiji.
Yana gyara necktie din sa yana nufar dining, wayar sa makale a kafadar sa yana amsa kira,
tashi nayi zuwa wajen sa tare da ja masa kujerar, sedai be zauna ba se ya canja wata kujerar
bayan ya bada ratar kujera uku da wadda na ja masa ya zauna.

Ban ji haushi ba se ma dan murmushi da nayi na zauna a wadda na ja, daidai lokacin kuma
Sa'adah ta fito ta sha wanka da dan uban sun lace milk and brown color, tayi kyau sosai sedai
da alama nawa wankan ne ya dake ta dan kuwa se kawai tayi cak a tsaye tana kallo ka, irin
kallon nan na mamaki, ko bata yi tunanin gani na a wajen ba ne, ko kuwa ado na ne ya
mamaye ta oho.

Gaba daya se yanayin fuskar ta ya canja ta kasa daga kafa ta karaso har se da mijin ta ya kira
ta, se kuma ta saki dan murmushin yake ta nufe shi cikin karairaya, ta ja kujera gefen sa ta
zauna bayan ta rankwafa ta yi kissing  goshin sa, hancin sa zuwa lips din sa.

Shi kuma se sakin murmushi yake yi, na sani suna yin komai ne dan su bata min rai, kowanne

kuma da nashi kalar niyyar, shi yana yi ne dan ramuwa ga abinda bai masa shekarun baya
wanda ban ga laifin sa ba, ai a addini ma an yarda in an maka baka hakura ba ka rama, ita
kuma tana yi ne dan ta bata min rai, ba dan komai ba se dan aurar mata miji da nayi, da kuma
wulakancin da tace nayi mata a baya.
Ni dai na zuba masa komai nan aje gaban sa na koma na zauna na shiga zuba nawa, se da
suka gama love din su sannan ta zauna, ya kalle ta tare da cewa

"Serve me".

"Gashi nan fa an sa maka".

"Na bar miki, ki dauki wannan ni se ki zuba min sabo, na fi son na ci wanda kika zuba da
hannun ki".

Wani malalacin murmushi Sa'adah ta saki, ta jawo warmers ta shiga zuba masa tana masa hira,
shi kuma yana amsa ta, Allah ya sani a wannan gabar raina ya ɓaci, amma se na fadawa kaina
ai ba komai ba ne cikin irin ni abubuwan da nayi masa, dan haka se na share kawai na shiga
cin abinci na.
Na riga su gamawa na masa Allah ya kiyaye daga nan wajen, dan na lura in na zake to kam ina
dab da shan kunya so se na kama kai na, na wuce daki abina.

Daga cikin daki ina jin kyakyatun su, ga shi ni ba tv ba bare na kunna ta dauke min hankali daga
kan su, waya ba caji balle na danna, haka na cigaba da zama har ya fita, ina tunanin kunnuwa
na sun huta se kuma ga Muryar ta tana wake wake, daga baya ma se ta sa a home theatre abin
ta tana bi, haka na yi lamo kamar marainiyar da ta rasa iyaye.....................��.


Jama'a ba'a commenting fa, wattpadians bakwa comments balle vote, bayan na fada muku
littafin nan free ne, comments da vote ne ze sa na samu karfin gwiwar cigaba, akasin haka
kuma I'll stop Dan ai saboda ku readera muke duk wannan hakilon, in bakwa appreciating baby
anfani kenan, dan typing din kan sa is not easy.
Vote
Comment
Share fisabilillah.

Ouummey 📚��.

Ouummey 008 [ 22/06/2024 8:50pm ]

BA KOWANE SO BANE...

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0