Showing 3001 words to 6000 words out of 12514 words
karfi ya
shiga jikinsa wanda bai tabajin kamarsa ba
tamkar zai iya nada gammo ya dauki duniya
gaba dayanta.
koda aljani markazulu yaji sauyin yanayi
ajikinsa sai yayanke hukuncin ya debe
ragowar kayan tsafin gaba dayansu.bayan ya
kwashe kayan tsafin ne sai kuma sai ya juya
ya nufi kofar fita daga kogon
koda aljani markazulu ya iso bakin kofar
kogon sai yasa hannu ya bude kofar kogon
tamkar yadda shaho yake daukar dan tsako
sannan ya fita daga kogon.
koda markazulu ya fito daga kogon sai ya
cika da tsananin farin ciki don ganin ya tsira
d rayuwarsa bai halaka ba aciki.
sannan kuma yaji wani irin girman kai ya
shiga jikinsa.
nan take kuwa ya daga kansa sama ya fara
yiwa kansa kirari yana cewa
saini hadari malafar duniya
ayaune nacika sunana markazulu kuma
ayaune zan addabi duk wani abu mai rai
dake doron kasa.
kuma daga yau nafi karfin nayi bauta ga
kowanne bil'adama dake doron
kasa,ballantana ulumanu kaskantaccen boka.
sai ni rugugin bala'i
saini rijiya gaba dubu
saini gobara daga kogi
koda yazo daidai nan a kirarinsa sai ya bude
fuka fukansa ya tashi sama ya luluka acikin
gajimare.
++ ++ ++ ++ ++
wanna shine abindaya faru a kogon dodo
sarmanu da aljani markazulu
++ ++ +n+ ++ ++
a can fadar boka ulumanu kuwa yaga duk
abindaya faru ga aljani markazulu da dodo
sarmanu
da irn bakaken magan ganun daya fada
masa.saboda haka sai yaji ya tsani
markazulu saboda bakaken magan ganun
daya fada masa
da kuma asarar babban hadiminsa da yayi
wanda ya yarda dashi.
tabbas yasan cewa yanzu baida karfin sihirin
da zai yaki markaulu yanzu
saboda sihirin da yake cikin battar karfen
dodo sarmanu sihirine mai karfin gaske.
don haka sai boka ulumanu ya yanke
hukuncin sai bayan ya gama mamaye
nahiyar da karfin sihirinsa dana sarauta
sannan zai kama aljani markazulu yayita
gana masa azaba har sai ya mutu
nan take ulumanu ya tashi wani hadimin
aljaninsa ya bashi wata wasikar yaki ya
aikashi ya kaiwa sarki abu saiman.
nan take aljanin ya cika umarni bayan kwana
daya aljanin ya fawo da wasikar raddi ya
mikawa boka ulumanu.
cikin kankanin lokaci baka ulumanu ya fara
hada rundunar yakai ta gaban kwatance kai
kace duniya zasu yaka.
bayan kowanne badakare ya hallara sai boka
ulumanu ya daga hannunsa sama yana mai
nuni da kowa yayi shiru
nan take kuwa gurin yayi tsit kamar mutuwa
ce ta gifta bayan shudewar wasu yan lokuta
sai ya soma jawabi kamar hak.
yaku daukacin hadimaina kuyi sani ayanzu
zanfara shirin yakin daban tabayin kamarsa
ba atarihin rayuwata.
saboda haka ubangiji na ya umarceni na fada
muku cewa ni zan barku anan kuyita baiwa
kanku horon yaki na tsawon wata guda
nikuma zanje kudancin birnin kisra domin na
samo wani wanda zai iya kashe macijiyar da
birnin zaharul maswur suke bautawa
amatsayin ubangijinsu..amma idan d mai
tambaya sai yayi.
nan take kuwa wani hadimi yada ga
hannunsa sama alamar yana da tambaya.
sai boka ulumanu ya bashi umarnin yayi
tamabayar.
sai wannan badakare yce ya shugabana
tambaya itace menene abin dogaron shi
wanna aljani da zai iya yaki da abar bautar
sarki abu saiman?
da jin wannan tambaya sai boka ulumanu ya
bushe da dariya sannan yace
yakai marwan kayi sani cewa
shidai wannan aljanj ana kiransa da suna
harisula mar'uf
kuma baya dogaro da wani karfin sihiri sai
wata takobi da yake da ita itace kadai abr
dogaronsa.
sannana kuma yanada matukar karfin
damtse.
don a yanzu babu alanin daya kaishi karfin
damtse da iya yaki a duk fadin duniyar nan
yazu haka harisul maruf yayi rantsuwa akan
bazai sake aiki a karkashi kowanne mutumba
face wanda ya dawowa da mahaifiyarsa
ainihin siffarta daga siffar gunki zuwa ainihin
kamarta
kuma aduk duniy ni kadaine nakeda sihirin d
zan iya wannan aiki. Koda boka ulumanu yazo nan a zancensa
sai wani aljani mai suna arman yace
ya shugaba na muna so muji tarihin harisu
maruf dakuma gwagwarmayar dayasha a
rayuwarsa
dajin haka sai boka ulumanu yabushe da
dariaya sannan yace hakika kunyi mini
tambaya mai matukar mahimmanci don haka
zanyi kokarin takaice muku tarihin shi
wannan sadaukin aljani.
nan take ya soma labari kamar haka
a wasu shekaru da suka gabata a can
kudancin birnin kisra anyi waji sadaukin
aljani mai tsananin karfin damtse wanda
duniyar sadaukai ta yadda dashi
shi dai wannan aljani ana kiransa da suna
harisul mar'uf
wata rana harisul ya tafi tarauta don samo
abinda zasuci shida mahaifiyarsa.
koda ya dawo gida sai yayi bakin gamo da
abinda ya tsana aduniya.
bakomai ya gani ba face mahaifiyarsa mai
suna zumaira a kwance akasa kafafunta a
nan nade da alama ta zama gurguwa.
nan take harisul mar'uf ya ruga da gudu
gareta ya dauketa ya dorata akan gadonta na
itatuwa.
sannan ya dubeta yace yake ummina ki
gaggauta fadamini abindaya sameki bayan
tafiyata faruta.
koda aljana zumaira taji wannan tambaya
daga bakin danta aljani harisul mar'uf sai
aljana zumaira tace
yakai dana bayan tafiyarka sai na wanzu ina
mai zaman jiran dawowar ka a wannan waje.
ina cikin wannan haline kwatsam sai naga
wannan gida da nake ciki ya soma girgiza da
kuma wani irin jan hayaki.
wanda bansan ta inda yake shigowaba
ina cikin wannan haline kawai sai naje
kafafuna sun soma nan nadewa.harsaida
suka zuke suka koma kanana.yadda bazan
iya taka suba.
koda tazonan a zancenta sai ta dada
fashewa da kuka.
lokacin da harisul mar'uf yaji bayanin
mahaifiarasa sai sai nan take ya rungumeta
akirjinsa tare da fashewa da wani sabon
kukan.
daga can kuma sai ya janye jikinsa daga
nata sannan yace
yake ummi na nayi rantsuwa da wannan
hawye naki duk wuya duk rintsi sai na samo
miki maganin wannan lalura duk wuya duk
rintsi.
kuma sai na hallaka duk wanda nagano dasa
hannunsa acikin wannan aiki.
nan take harisul Mar'uf ya bde fuka fukansa
ya nausa cikin daji don samowa
mahaifiyarsa duk wani kayan amfani da zata
bukata na tsawon shekaru dari uku.
sannan yayi sallama da mahaifiyarsa ya tafi
wajen wani amintaccen bokansa.
sai da yayi tafiya sa'a bakwai sannan ya isa
bakin kogon garmanu nan take ya saki fuka
fukansa ya sauka bisa turba.
saukarsa keda wuya sai ya cika da mamaki
bakomai yaganiba face boka garmanu
fuskarsa cike da fara'a.
nan take ya fara yiwa harisul mar'uf kirari
yana cewa
lale marhaban da sadaukin duniya tarwatsa
maza.
ajali kake bakasan hakuriba
dodo kake mai razana manyan sadaukai
duhu kake mai firgita manyan maza afilin
daga
kabari kake makomar duk wani mahaluki
ya sarkin sadaukan duniya.
lokacinda boka garmanu yazo nan a
kirarinsa
sai yace da harisul mar'uf
yakai sadaukin zamani kasani cewa
bakowane yayi mahaifiyarka wannan sihiriba
face sarkin bokayen duniya.
wato boka salban sakamakon binciken da
yayi a cikin tsafinsa ya nunamai cewa kai
kadaine saka iya zame masa matsala acikin
al'amuran da yake guda narwa a doron
kasa.har kayi yunkurin hanashi
saboda hakane yakara tsananta bicike a
madubin tsafinsa daga karshe yagano cewa
dolene ka shiga sha'anin zaluncinsa
muddinsa muddin bai zaunarda mahaifiayrka
awaje dayaba.
ma'ana ya aika mata da sihirin da zata daina
tafiya baki daya.
koda boka garmana yanzo nan a zancensa.
sai harisul mar'uf yace.
to yanzu a ina zansami boka salban na
hallakashi don nadauki fansar abinda ya yi
mini?
dajin wannan tanbaya sai boka garmana ya
bushe da dariya kamar bazai daina ba.
dagachan kuma saiya tsuke bakinsa kamar
an aiko masa da sakon mutuwa.
sannan yace
yakai gwarzon shekara mahaifiyarka bazata
taba samun lafiya ba hsar sai kaje kowanne
bakgare na duniya ka samo mata wasu
tsumummuka ka hada su waje daya ka bata
tasha sannan zata sami lafiya kamar babu
abindaya sameta.
sai kaje ka samo wadannan abubuwa sannan
zakayi shirin tunkarar boka salban
kodajin haka sai harisul mar'uf ya ta karkare
ya kwarara uban ihu
yace narantse da darajar hawayen
mahaifiyata saina samo mata wadannan
tsumummuka koda zan rasa rayuwata
sannan na yanko kan boka salban na tsireshi
atsakiyar birnin da yafi kowanne birni yawan
matsafa don hakan ya zamo gargadi
agaresu.
dajin haka sai boka garman yace
ina da wani taikako da nakeson baka na
wani sihiri mai karfin gaske wanda zai
kareka dga dukkan wani hatsari da tsautsayi.
sai harisul mar'uf yayi murmushi ga boka
garmana
sannan yace
ina da takobin da indai ina tare da ita zata
dinga bani kariya.don haka daga yau abzamu
sake haduwa ba ni dakai sai ranar da naje
na samo wannan magani.
kuka daga yau mun kulla bakar gaba da
boka salban.
koda gama fadin haka saiya bude fuka
fukansa ya tashisama ya luka acikin
gajimare cikin azababben gudu na gaban
kwatamce.
duk inda ya gifta ya tarar da wani ayari na
aljanu da sun ganshi saidai kaga sun chanja
hanya saboda tsananin kwarjiinsa.
idan kuwa tarom yan fashine cikin kankanin
lokaci yake tarwatsasu.
sai daya shafe kwanaki bakwai yana tafiya
sannan ya iso bakin wani birni na aljanu don
haka ya yanke shawarar ya shiga wannan
gari ya kwana idan gari ya waye sai ya kama
hanya ya cigaba da tafiyarsa.
nan take kuwa ya sauka abakin kofar wannan
kasa sannan ya matsa gaban kofar ya
kwankwasa.
bisa mamaki sai wani aljani ya leko yan
cewa wannan wanne me karar kwanane yake
bugu mana kofa alokacin da muke morewa
da kyawawan matanmu?kowanene ya
gaggauta juyawa da baya tun kafin fishina ya
sauka akansa.
koda wanna me tsaron kofa yazo nan a
zancensa sai ran aljani harisul mar'uf ya
baci.amma saiya basar yace nine harisul
maruf wanda yake neman mutuwa da
kudinsa kuma akoda yaushe.
dajin haka sai ran mai tsaron kofa ya baci.
nan takekuwa ya bude kofar wannan kasa.
sai dakaru sukayita fitowa da makamai iri iri
tamkar duniyar zasu yaka.
bayan wadannan dakaru sun gama zagaye
harisul maruf sai sukayi kukan kur suka afka
masa da sara da suka.cikin tsananin zafin
nama d ajuriya da bajinta nan take aljani
harisul mar'uf ya shiga kai sara da suka
cikin salo irin an manyanyan jarumai.
cikin kankanin lokaci ya karar dasu ya
zamana saura shugabansu.
nan take kuwa shugaban masu tsaron kofar
ya ruga aguje domin ya fadawa sarki
abindaya faru.
tafiyar keda wuya sai sai harisul maruf ya
matsa gaban kofar wannan birni wacce
takeda girma sosai.idan ta fadi sai an sami
manyan giwaye guda dari biyar sannan zasu
iya dagata.yasa kafarsa ya doki kofar.
nan take kuwa wannan kofar ta rufta ciki.
kuma adai dai wannan lokacin ne sarkin
wanna garin ya iso.
koda yaga abindaya faru sai ya kwarara uban
ihu. Koda yaga irin muguwr barnar da yayi masa
sai ransa yayi matukar baci tare d kwalla
ihu.
domin bincike ya tabbatar da cewa aduk
lokacin d wani sadauki ya balla wannan
kofar to daga ranar to daga bashi ba mulki
acikin kasar harsai ya nemi hadin kan
wannan sadauki sun tari masifar d zata afko
musu.
nan take kuwa ragazalu yasa hannu ya
finciko sarkin kofa sannan ya dubeshi yace
ka jawo mana bala'in da bamu taba
shigaba,tundaga sanda aka kafa wannan
kasa,tunda ka janyo mana sadaukin aljanun
duniya harisul mar'uf,don haka hukuncinka
shine kisa.
nan take yasa takobi ya datse masa
kai,sannan yayi wurgi da gawar,tare da bawa
dakarubsa umarnin suyi mubaya'a ga harisul
maruf
nan take dakarun suka cika umarni
sannan sarkin ragazalu ya tao da kafafunsa
yazo gaban harisul maruf yayi mubaya'a tare
da fadin
kagafarceni ya sadukin duniya bisa irin
tozartar da akayi maka acikin kasata.
bakomai ya jawo hakaba face tsaurin ido rin
na sarkin kofa,
yakai wannan babban jarumi dagani har
jama'ata mun mika wuya agareka,kuma
muna neman taimakonka sakamakon karya
alakadarin kasarmu dakayi na balla mana
kofa,
kuma bincike ya nuna cewa daga lokacin da
aka balla wannan kofa zaman lafiya zai kare
a wannan nahiya,sakamakon kawo mana
farmaki da kasashen ahokan gaba zasu
dingayi badon komaiba sai don su mallaki
dukiyarmu ta dangin zinare da lu'u lu'u
yanzu haka.maganar da nake maka wasu
kasashen sun fara shirin kawo mana
mamayar bazato yau ko gobe.
lokacin da sarki ragazalu yazo nan azancnsa
sai ya fashe da kuka,
al'amarin da yasa zuciyar harisul mar'uf tayi
sanyi kenan don haka sai yadubi sarki
ragazalu yace
yakai wannan adalin sarki zan
taimakeku,saboda banason ganin anzubarda
jinin wanda baijiba bai ganiba.
don haka nayi alkawarin taimakon
mayakanku,don haka yanzu sai kuyi shirin
Suleiman Zidane kd
Whatsapp. 08161272634
gyara kofar wannan gari tun kafin abokan
gaba su cimmaku.
koda sarki ragazalu yaji haka saiya kamu da
tsananin farinciki sannan ya umarci wani
badakare da yaje yayi shelar ana neman duk
wani magini da yake cikin kasar da ya
hallara abakin kofar wannan birni
nan take kuwa wannan badakare angama ya
shugabana sannan ya bace.
kafin cikar.sa'a biyu duk wani magini ya
hallara
sannan sarki ya basu umarnin fara gini
kafin cikarsa'a bakwai sungama gini wannan
kofa
sannan aka aka dada kara dakarun tsaro ako
ina acikin garin aka cigaba da jiran ta inda
dakarun zasu bullo
a.haka.suka.kasance cikin shigar yaki taban
tsoro.
saida suka shafe yini guda sannan abokan
gaba suka iso.
awannan rana anyi gagarumin yakin da
ba'ataba kamrsaba awannan nahiya.sannan
anyi asarar dukiya mai tarin yawa.
bisa dole kowanne bangare yajanye
dakarunsa gaba daya.
tundaga wannan rana kasashen dake duniya
suke matukar tsoron wannan birni saboda
arin sa'ar da suka samu awannan yaki.
a zatonsu har yanzu harisul mar'uf yana
cikin kasar.
wash gari kuwa da sassafe harisul mar'uf
yatashi yabar kasar bayan sunyi sallama da
sarkin garin da yan majalisarsa.
sannan yanausa cikin gabashin duniya don
nemowa mahaifiyarsa magani,
sai da yayi tafiyar shekara guda sannan ya
iso dajin da yake dagashi sai bangon
duniya.na gabas
saboda haka sai harisul mar'uf ya zaro
sihirtacciyar takobinsa dake daure a
kugunsa.
sannan ya zaro wata yar taswira wacce ya
samu agurin sarki ragazalu
yabudeta ya duba.
nantake yayi arba da wani kogo acikin
taswirar,wanda yake nuni da shine hanyar da
zata kaika bangon duniya nagabas.
nantake kuwayasake bude fukafukansa yana
mai kusantar kogon kai tsaye.
yana shiga cikin kogon sai yayi arba da wata
yar siririyar hanya wacce take da tsananin
nisa.
nantake kuwa ya nufi wannan hanyar kai
tsaye yana mai gyara rukon takobinsa.
kwatsam sai yayi arba d wata bakar kunama
wacce ta tokare hanyar kogon gaba
daya.sannan wannan kunamar tasa kafa ta
daki wani dutse da kafarta guda daya
nantake kuwa wannan dutse ya gangara yaje
ya toshe hanyar da harisul maruf ya shigo.
mai makon ma harisul mar'uf ya firgita
sai abin ya bashi mamaki don ganin irin
wannan azababben karfi irin na wannan
kumama.
bakomai yabashi mamakiba face gani yadda
ta iya ture wannan dutse da kafarta daya.
alhalin inza'a tara manyan aljnu guda ashirin
bazasu iya mirgina wannan dutseba.
yana cikin wannan tunanine yaji kunamar
takawo masa harin bazato.
cikin tsananin zafin nama ya daka tsalle ya
koma gefe daya don ya soma tunanin ta
hanyar dazai bullu mata.
nanfa aka soma kallon kallo tsakanin sa da
wannan kunamar na tsawon yan dakiku.daga
chan sai harisul mar'uf ya nufi kunamar cikin
mugun nufi,
suna haduwa aka ruguntsume da masifaffen
yaki nagaban kwatance suka wanzu suna
masu kaiwa junansu sara da suka.
shidai yana amfanine da takobin sihirinsa ita
kuma tana amfanine karinta da kuma
hannayenta wajen kai masa hari.
duk sa adda harisul maruf ya sari jikin
kunamar sai sai yaji kamr dutse ya sara.
ita kuma kunamar duk sanda ta kawo masa
hari ya kauce duk abindata samu nan take
yake ruburbushewa ko kuma ta haddasa
wawakeken rami.
sai da suka shafe sa'a guda suna
fafatawa,sannan kunamar ta sami nasarar
yankan harisul mar'uf agadon bayansa.
nantake harisul mar'uf ya kwalla ihu.saboda
zafi da zugin da yaji.cikin tsananin dauriya
ya daka tsalle tsalle kamar daga cikim baka
aka wullashi ya fada kan gadon bayan
kunamar sannan ya caka mata takobi a ido.
nan take kuwa idon kunamar ya fashe jini
yayi tsar tuwa.nantake kunamar ta haukace
ta dinga kawo masa mugayen hare hare
LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEME (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI)
LITTAFIN BAKAR GABA PART 3
LBR
HABIBULLAH KBR
TYPING HABIBULLAH KBR
Suleiman Zidane kd
Whatsapp. 08161272634
nan fa wannan fada ya dawo sabo kogon ya
soma girgiza tamkar zai ruguje.
cikin dan kankanin lokaci aljani harisul a fita
daga hayyacinsa saboda tsananin wahalar da
yakesha awajen kunamar.
saidaya zamana yakasa maidawa kunamar
da martani saidai yunuri kare kansa kawai
yakeyi.
koda aka shafe wata sa gudar sannan harisul
mar'uf yasami nasarar cakawa kunamar
takobi atsakiyar wuyanta.
nantake kunamar tafadi kasa ko shurawa
batayi ba.
sannan shima ya fadi kasa sumamme.
sai bayan sa'a uku sannan ya farfado daga
suman da yayi.
yana farfadowa ya tuna da ciwon dake gadon
bayansa
nantake yadauko magani daga cikin jakar
guzurinsa.yazuba aciwon dayake
bayansa.sannan ya tashi yagyara damararsa
ya nufi hanyar da zata fitar dashi daga
wannan kogo,sai bayan yan dakiku sannan
yafita daga cikin kogon.
yana fita yayi arba da wani tafkeken daji mai
matukar kwarjini daban tsoro,
shidai wannan daji yakasance babban daji
mai dauke da ababan tsoro,
don hatta bishiyoyin dajin siffofin dodanni ne
dasu,
kuma awannan lokaci rana ta bude.hakanne
ya haddasa wata iriyar zazzafar iska acikin
wannan daji.
duk haka baisa harisul mar'uf tsoroba ya
dada kutsa kansa cikin dajin cikin azabbaben
gudu acikin sararin samaniya da nufin ya
wuce ta saman dajin.
kwatsam sai yaji tamkar an ruke fuka
fukansa yadda bazai iya motsa suba.
bisa dole yaci burki asama don yaga abin da
zai faru.
yanacikin wannan haline yaji wata kakkarfar
iska ta zukoshi kasan wannan dajin.
alokacinda wannan iska ta sauke harisul
mar'uf akasan wannan dajin.
kwatsam sai yayi arba da wasu manya
manyan macizai masu matukar ban tsoro.
sudai wadannan macizai adadinsu yakai
dubu daya.haka girman kowannensu yakai
giman bishiyar dabino haka kaurinsu yakai
bishiyar kuka.
idanunsu kuwa tamkar angasa dan buda a
wuta.
alokacin da wadannan macizai sukaga
harisul mar'uf asararin samaniya sai suka
bace tamkar basu taba wanzuwa ba,sannan
itama wannan iskar ta dauke tamkar bata
taba samuwaba.
kuma alokacin ne harisul mar'uf ya daina
ganin macizan.
al'amarin daya matukar bashi mamaki kenan
sannan ya fara tunanin irin masifar da take
cikin wannan