Showing 15001 words to 18000 words out of 31290 words
jinta. Sai ta kwace wayar ta soma karantawa. Farin cikinta ya kasa boyuwa a
fuskarta.
Ta ce, “Ki ji yaro da lauya magana, wallahi sai ta tafi in ba haka ba ba’a rabu da Bukar ba an
haifi Habu muddin tana cikin gidan yana ganinta. Ta ruwan sanyi za ta tafi babu duka babu zagi
balle bakar magana”.
A nan ne Mamin ta yi magana, “Ina ganin mu kyale yarinyar nan Halima tunda dai an samu ya
yi kokarin da ba’a zata haka cikin sauri ba. Baki san Khalipha ba a kan abin da yake so, kamar
kuma yadda ya ce din ne AURENA zai yi tangal-tangal idan ya dawo ba ta gidan, babu kuma
wata kwakkwarar magana kan inda ta shiga”. Dr. Halima a fusace ta ce, “To shi kenan, na rantse kuwa za ta zama kishiyarki idan Khalipha bai
aura ba. Kuma ai ba korarta za ayi ba, kiranye za ayi mata ta koma mahaifarta ko za a kasheta
ba za ta yarda ta dawo ba. Ai muma Musulmai ne, ba cutarta zamu yi ba”.
Ta yadda da maganar Dr. Halima dari bisa dari har cikin ranta.
** **
“Daddy yaushe za ka dawo?”
Khalipha ya tambayi Baba Dacta a raunane, bayan sun gaisa ta waya. Maimakon ya ba shi
amsar tambayarshi sai ya ce, “Ya ya na ji maganarka so cool, wani abu ya faru ne?’
Ya girgiza kai cikin karin hawaye ya ce, “Eh to, magana nake so muyi ta fahimta.....”
Sai kuma ya yi shiru.
“Ba za a iya barin maganar har sai na dawo ayi ta face-to-face ba? Tunda na lura mai nauyi
ce?”
“To shi kenan Daddy, yaushe za a dawo?’
“Yanzu haka na taho on transit nake a Germany. Zuwa asubahin gobe ina Kano insha Allahu”.
** **
Dawowar Daddy gida lafiya, da kuma ganin yanayin fuskarsa bai canza ba ko kankani, yasa Dr.
Asma’u cikin kokonton anya Khalipha ya yi abin da ya ce zai yi bisa umarninta? Irin kayan da
ake shigowa dasu ana jibgewa a (store) ya kara tabbatar mata da lallai Khalipha ya rainata.
Kayan furnitures ne ‘yan ubansu-ubansu da manyan jakunkunan zamani shake da duk wani
nau’in suttura ta kwalliyar mata da suka fi kama da kayan lefe.
Dr. cikin walwala yake matuka, a lokacin da yake nuna mata kayan, yana yi mata bayanin lefen
Khalipha ne. Ya kaikaice ya zaro warawarai guda shida na farin zinare daga aljihunsa, ya ce ga
shi ta adana, shine sadaki.
A wannan lokacin ya kwantar da harshe ya ce,
“Asma’u na san bani da kalaman wanke kaina daga daudar mai laifi a gareki, amma ina baki
hakuri, bani kuma da hannu a ciki. Kamar yadda na ce ba zan hada ba ban hada ba, su suka
hada kansu, ni kuma na ture komi, na zabi in cika umrnin Ubangiji in ya so in yi kaffara a kan
alkawarin da na yi miki. Tsakanin ‘ya’yanki da ‘yar amanar da Allah ya bamu. Zan iya cewa ban karya alkawari ba, tunda kuwa ban hada soyayya tsakanin Khalipha da
Rayhanatu ba. Ki sa fahimta a cikin lamarin nan, ki sa albarka, ki dauki duniya da sauki.
Khalipha ke son auren Rayhanah, ni kuma na ba shi da na tabbatar da amincewarta. Ga
wannan.....” Ya tura mata bandir din bugaggen (invitation card) na daurin aure da yasa aka buga masa a
Dublin..
Ya kare da cewa, “Jibi Lahadi insha Allahu za a daura auren a gida Takai, Hakimi shine
waliyyinta. Don haka ga wannan”. (Ya tura mata ATM Card dinsa na bakin (Gruaranteed Trust).
Ya ce, “Ki dauki abin da zai isheki, daga naira dari har zuwa miliyan biyu na lamince miki ki fara
shirye-shiryenki. Na taho da komai na kawata gida, kayan kithcen ne sai ku mata. Da sauran
abubuwan da babu sai ki karasa. Duk wasu activities da kike ganin za a yi ayi, amma ban da
wanda za a hada mata da maza. Kin yi hakurin Mamina kin fahimceni?” Sakatoto! Ta yi tana mishi kallon takaici, kamar ta amayo zuciyarta ta huta. Ta so yin kissa ta
karya, amma ba halinta bane, don ba ta iya ba. Wadanda take yi a baya ma duk Dr. Halima ke
koya mata, ga shi kuma ba ta zaci haka ba, ba ta koyo yadda za ta karbi zancen ba.
Sai kawai ta aje warawaran da ya dora mata a cinya da katinan daurin auren a nan gabanshi ta
mike ta yi dakinta ba tare da ta ce da shi komi ba.
Ta zauna a gefen gadonta jikinta yana bari ta kira Khalipha. Bugu biyu ya amsa cikin nutsuwa,
domin yana bisa sallaya ne yana mikawa Ubangiji bukatunsa, bayan sallame nafila raka’a hudu,
wadda a kowacce raka’a ya karanto suratul Ikhlas kafa bakwai.
Sallah ce ta neman zabin Allah ita ma, amma ba Istikhara ba. Tuni Khalipha ya dade da samun
nutsuwar zuciyarsa albarkacin ruwan zam-zam mai sanyi da ya mayar ruwan shan sa.
Ko ya ya rayuwar ta zo, ya shirya karbarta, in dai zai wanye lafiya da mahaifiyarsa, kuma
mahaifinshi kada ya ga laifinta.
Ya manta shima uba yana da nashi hakkin amma Khalipha ji yake ya gwammace bacin ran
Daddy a kan na Mami. Daddy mai saukin hali ne ba ya daukar al’amuran rayuwa da zafi.
Duk da haka ya san idan sunan Mami bai fito ba, duka laifin kanshi zai kare, domin Daddy baya
son karanta kuma baya shiri da mai magana biyu, balle a kan ‘yar da ta fi nashi ‘ya’yan a
zuciyarsa.
Zai karbi duka laifin in dai hakan shine farin cikin Mami, wadda yake wa wani irin so na UWA
wanda ya zarta wanda yake yiwa ubansa Dr. Mansur.
Tana huci kamar mesa ta ce, “Abdallah!”
Ya amsa “Na’am Mami”.
“Ni ka yaudara ka wulakanta ko?”
Ta fada tana nishi kamar wadda ta yi tsaren ceton rai.
Ya ce, “Subhanallah! Kada Allah ya nuna min ranar da zan yi miki dayan biyun hakan, ya dauki
raina kafin in yi hakan....”
“Rufe min baki”.
Ta fada cikin tsawar da bai taba ji ta yi ba.
“Ka ce za ka kira Dacta ka fada mishi cewa ka fasa auren matsiyaciyar yarinyar nan Radhiyya
kake so, shine baka kirashin ba kuke shirye-shiryen biki ta waya har I.v an bugo jibi daurin aure.
Wane irin tozarci kake so ka yi mini? Na ce ban yarda ba, ba ta isa ba, ba ta isa ba wallahi in yi
suruka da ita. Zan la’ance ka Khalipha…….. muddin ka yarda aka daura ma aure da yarinyar
nan jibi.....”
Ta kashe wayarta, ba ta saurari uzurinshi ba, ta barshi a wani hali da ya kasa tantance wane iri
ne.
Wayyo! Allah sarki Daddy...... ashe shi yana can yana yi min gata ban sani ba...... ashe shi yana
can yana so ya yi surprizing dina a kan alherin da ban taba son wani abu kamarsa ba.
Amma sakamakon sa shine in karya masa zuciya in zubar da mutuncina a idanunsa. Kullum
cikin hirarsa sai ya ce, “Karamin mutum shine mai saka hairan da wulakanci, yau zan zama
mayaudari, a RAYUWAR RAYHANAH! Zan ceci auren uwata, ni in tsira da hakan, Allah ya baki
hakuri Rayhana, ya baki wanda ya fini......” Ya kifa kai jikin gadonsa yana kuka da sauti.
****
[12/24/2019, 21:47] Takori: Daddy na kan hanyar Takai bayan motarsa shake da goro da alawa
lokacin da wayar Khalipha ta shigo masa. Don haka bai daga ba domin baya amsa call yana
tuki, shi kuma Khaliphan bai fasa kira ba.
Kira a kai a kai wanda ya tabbatarwa Dr. Mansur cewa wannan kira ba na lafiya bane, domin
Khalipha baya takurawa mutum da kira, kusan kullum ma shi wayarsa a (voicemail) take. Sai ya
ratse kan hanya ya parker motar ya amsa kiran Khalipha.
A nutse suka gaisa shi da Daddyn, sai dai yadda Daddy ya ji muryar Khalipha babu amo (a
dushe) kuma sanyinta ya yi yawa ya tabbatar Khalipha ba shi da lafiyar zuciya da kuzari cikin
gangar jikinsa. He is always very energetic a murya da zuciya, kuma a muryarsa yake karantar
halin da zuciyarsa ke ciki. Bayan sun gaisa ya ce,
“Ina kan hanyar Takai ne zan kai wa Hakimi goro da alawar daurin auren ka, gobe insha Allahu
za a daura karfe goma sha daya na rana.
So ka bar kome kake yi ka taho Takai a yau, abin ne ya zo a kurace, don haka a kuracen za ayi,
duk wata gayyata na gamata a jiya sai ko ‘yan office din ku su ma ka yi text kawai ka turawa
kowa.
Na jika ba a yadda na saba jinka ba, wani abu?”
Hawaye suka ziraro daga idanun Khalipha, sharrrrr..........suke zuba kamar an sunce famfo. Ya
ce cikin rishin kuka, “Daddy na gode da kaunarka da kulawarka gareni, da kyakkyawar
zuciyarka mai son faranta min a kullum.
Abin da zan fada yanzu don Allah Daddy kada ka yi masa wata fassara daban, ko ka yi tunanin
na yi ne don in mai da kai abokin wasana, ko kuma na yi don in tozarta in wulakanta ka, ko don
ban gode maka ba, ko don in karya maka zuciya.
Na yi hakan ne domin neman masalaha tsakanina da Ubangijina. Na fasa auren RAYHANAH a
daura da Radhiyyah ‘yar Dr. Halima. Ita kuma Rayhanah Allah ya huci zuciyarta ya ba ta wanda
ya fini”. Kawai sai yasa masa kuka.
Dr. Mansur ya dade bai yi magana ba, zuciyarsa ke wani irin tukuki na fushi da Mami mai
tsanani, fushi irin wanda bai taba yi ba a rayuwarshi ta duniya.
Tabbas Asma’u ce ta yiwa Khalipha barazana da matsayinta na (uwa) domin dankafar da
Rayhanah da martaba nata Dan.
“To ai shi kenan”.
Bai san sanda ya gayawa Khalipha hakan ba.
“Ta nuna power dinta a kanka, nima zan nuna tawa da wanda na haifa nake da iko da shi.
Dadin haihuwa kenan. Yau da ban haihu ba da Asma’u ta nuna min iyakata ta nunawa duniya
BA NI NA HAIFE KA BA!
Babu komai, daina kuka Khalipha, zan mata yadda take so, nima zan yi yadda nake so. All the
best Khalipha, yi biyayya ga mahaifiyarka domin samun tsira a gidan duniya da lahira baki daya.
Kada ka damu da bacin raina, wallahi ko kadan baka bata min ba, ban kalleka da matsayoyin
da ka lissafa a baya ba, face na yi maka kallon DA MAI NEMAN ALJANNAH a diga-digan
mahaifiyarsa.........”
Ihu Khalipha ya saka masa. “Daddy ba kai ka haifeni ba? To wane ne? Shege ne ni?” Kara yake
saki da ihu mai gigitarwa saida shi kansa Dr. Mansur ya razana. Da tsoron kada Khalipha
yayiwa kansa wani lahani. Bai san sanda ya soma kuka ba shima ya soma kira cikin lallashi da
nadamar bacin ran da ya kai shi ga furta abinda yayiwa kansa alqawarin har abada bazai furta
ba,
“Cool down Khalipha!!! Ba shege kake ba, da ubanka, ita ta haifi abinta da mijinta na fari, tun
auren saurayi da budurwa, bayan haihuwarka suka rabu, kana da shekara biyu ya rasu.
Ni da ita mun hadu ne a jami’ar Trinity din Ireland (Dublin) ta zo karatu nima na zo, tana zaune
da Uncle din ta da matarshi tare da kai, Nanny na kula da kai ita kuma tana karatu. Da muka yi
aure ne na karbeka muka karasa karatu muka dawo, da shekaru hudu da auren mu ta haifa min
Ibraheem. To ka ji, kwantar da hankalinka har gobe kai Dana ne Khalipha, ba wanda ya isa, ba abin da ya
isa ya kankare wannan sunan Abdullahi Mansur Takai, sai wanda ya halicce ni ya halicceka.
Mahaifinka Balaraben Hurghada ne (Egyptian) ya zo Jos kasuwanci ne ya zauna a cikinta
tsayin lokaci har ake kiransa (Ba Hurgade Mukhlis), ya kuma bar maka tarin arziki mai yawa
wanda iyayensa suka zo suka kwashe, suka kuma ki karbarka, a cewarsu basu san da zancen
auren ba tunda bai gaya musu ba, duk da fata ta nuna amma kamanninka da ita ne sak. Tun daga lokacin na mai da kai Da na Khalipha, kuma har gobe matsayinka kenan. Share
hawayen nan Khalipha bana son su and I’ll stand by you..... ina a bayan ka yiwa mahaifiyarka
biyayya domin ta sha wahala da kai yadda baka zato a Dublin. Ga karatun medicine ga rashin
lafiyar ka ta ciwon hanta har Allah ya baka lafiya.
Tunda ba ta so to ba ta so din ne, ko anyi abin ba zai yi albarka ba, ba kuma za ta bari a zauna
lafiya ba. Kyale Asma’u da kafiya a kan abin da bata so, in fa ba ta son abu ba za ta taba son
sa ba.
Tana da hakki mai girma a kanka wanda ni bani da shi. Zan kuma nuna mata nima na haifa,
kowa ya yi iko da nasa”.
Ya ci gaba da lallashin Khalipha wanda ke kuka mai keta zuciyar duk mai imani, har suka aje
wayar Khalipha bai daina kuka ba. Shima Dr. Mansur hawayen yake ta sharewa da hankicinsa.
Ya tada motar ya hau kan titi ya karasa Takai.
A kofar gidan Hakimi ake ta sauke huhun goro da alawa da Dr. Mansur ya zo dasu shake a boot
din motarsa. Wajen matan gidan ya fara shiga aka gaggaisa da su Haj. Karima, sannan suka
kule a falon Hakimi shi da dan’uwansa suna tattauna mai yiwuwa. A take aka soma gayyatar
daurin auren da za ayi a gobe Lahadi. Bayan Khalipha ya yi kukansa har ya gaji, idanunshi sun soma yi mai zafi da wannan sabon
al’amari da ya tunkaro shi. Ya girgiza zuciya da ilahirin gangar jikinsa.
Wai Baba Dacta ba shi ya haife shi ba. To shi din wane irin mutum ne mai karamci da
kyautatawa ga al’umma? Mutane irinsa tsiraru ne a cikin al’umma.
Mami ya kira, muryarsa sak kamar babu komi a cikinta.
“Alright Mami. It’s done, sai ki sanar da Dr. Haliman Daddy ya ce in gaya miki gobe in sun dawo
daga daurin auren da za suyi a Takai za su zarto nan Kano a daura na Radhiyyah. Mami kisa
min albarka! Albarkarki kawai nake nema Mami, bayan wannan babu wani abu. Zan samu
Mami???” Hawaye ne suka sake zubo masa, wanda bai damu da ya sharesu ba, suna ta zuba a kan
cinyarsa.
Maimakon Mamin tasa mishi albarka kamar yadda ya roka, sai ma ta hau tambayarshi wai
daurin auren wa su Daddyn za su yi a Takai?
Khalipha don bakin ciki sai ya sanya kansa cikin gwiwoyinsa kamar karamin yaro ya ci gaba da
kokawa kansa-da-kansa. Ita kuma Mamin a can ta gaza sukuni.
Ga dai Khalipha ya haifu ya yi mata yadda take so, ya hakura da farin cikin rayuwarsa domin ya
faranta mata, ya samu albarkarta amma zuciyarta ta gaza nutsuwa da son sanin auren wa za a
daura a Takai?
Kada zancen Dr. Halima fa ya tabbata, Rayhanah ta zama kishiyarta Dr Mansur ya yi auren
huce haushi da ita. Tasan zuciya irin tasa idan ransa yayi mummunan baci bahagon hukunci
yake yankewa. Ai sai ta mike ta zari makullin mota ta nufi gidan Dr. Halima a gigice domin
maganar ta fi karfin ayita a waya. Dr. Mansur macijin sari ka noke ne, shirunsa a kan al’amari na
nufin daukar mataki wanda ba zai yiwa victim dadi ba.
Tana tafe da gudu tayar motarta ta gaba ta fice, motar ta gangara ta bugawa wata katuwar mota
duk fitilunta suka kwankwatse, Allah ya sota ba abin da ya sameta, sai buguwa da kanta ya yi a
jikin sitiyari, sai dan gilashin da ya yanki goshinta.
A take jami’an tsaro suka cika wajen suka jawo mata bacin lokaci da biyan cin hanci. Ba ta isa
gidan Dr. Halima ba sai da magariba.
Dr. Haliman ta ganta afujajan ga jini na zuba duk ya bata tsadadden swiss lace yellow dake
jikinta. Ita ta yi mata dressing din wajen ta rufe da plasta, sannan Mamin ta koro mata bayani.
Maimakon Dr. Halima ta tayata jimamin abin da take wa gigita da tsoro a kai, sai guda ta je ta
sakarwa Radhiyya a ka, ta kira Babanta a take ta sanar da shi.
To dama shi Alh. Kabir shanyayye ne, take babu bin ba’asin wannan kagararren aure ya soma
gayyatar jama’arsa ta waya. Radhiyya ta kunna (Nancy Agram) tana taka rawa a gaban Mamin
har ta ji wani bangare na zuciyarta ya yi mata ba dadi, amma ta kasa nunawa ko a fusaka sai
dariyar yake take taya Radhiyyah. Ta kuma ce, “To Radhiyyah kinga dai kokari da fadi-tashin da muka sha ni da mahaifiyarki don
samun farin cikinki, kin kuma san Khalipha ba shi ya ce yana ra’ayinki ba.
Don haka (handle him with care Radhiyyah), ki kular min da shi don Allah shima ki yi hakuri da
shi sai a hankali, insha Allahu komi zai daidaita”. Radhiyya ta rungume Mami har da hawayen
farin ciki a idanunta.
Haka Mami ta dawo gida a salube gwiwa babu nauyi. Don ko cikakkiyar sallama basu yi da Dr.
Halima ba, ba ta tofa wani abu a kan damuwarta ba, she is busy calling her people su zo daurin
auren Radhiyya da Khalipha gobe.
Idan Mami ta ce ta yi barci a daren yau ita kanta ta san karya ne. Ga azabar ciwon kai, ga
radadin ciwo, ga tunani, fargaba da damuwa.
Har sha biyun dare Dr. Mansur bai shigo gidan ba, tana falo tana dakon shigowarsa amma har
karfe biyun dare babu ko inuwarsa, wannan ya tabbatar mata a Takai zai kwana.
Ta soma kiran wayarsa ana cewa a rufe. Sai ta koma kiran Khalipha shima a rufe. Tamkar
wadda aka yiwa allura ta zabura ta yo dakin ‘ya’yanta mata, kwayar idanunta sun zurma ciki
sosai tashin hankali da zullumi.
Abida da Jawahir kowacce na barci a gadonta, sai Azizah a kan sofa take nata barcin. Daga
can kusurwar karshe ta dakin ta hango Rahane tana kan sallaya da hijabin da ya