Showing 1 words to 3000 words out of 84387 words

Chapter 1 - Daren Aurena Book Complete

07 Sep 2026

280

����������
*�DAREN AURENA�*
����������

*Daga alk'alamin 'yar mutanan zazzau Naanah M Sha'aban�*

_Labari mai tab'a zuciya😭_

_Wannan littafin sadaukarwa ne ga k'ungiyata da kuma jaruman cikinta�_


*Wannan labarin k'irk'irarran labari ne ban yarda a juya min littafi na ta kowacce hanya ba�*

Shafi na 1

.............📖Kuka take tamkar ranta zai fita kwance take a kan d'an k'aramin gadon d'akin ta
duk'unkune a cikin bargo ta rintse idonta zuciyarta nayi mata wani irin zafi da k'una cikin da
sasshiyar muryarta ta fara magana "tabbas nayi dana sanin, sanin Jabir a rayuwata, ka cuceni,
ka yaudareni bazan tab'a yafe maka ba har duniya ta nad'e, Insha...insha Allahu, Allah sai ya
saka min abin da kayi min Kuma....." Sai Kuma ta kasa k'arasawa saboda irin kukan da ya
shak'eta.

Aunty Murja ce ta shigo d'akin da sallama d'auke a bakinta zuciyarta cike take da tausayin
k'anwarta ta saboda Jabir yabar mata mugun tab'o Wanda bazan tab'a gogewa a cikin zuciyarta
da ma rayuwarta gaba d'aya, yayi mata abinda ba za ta tab'a mantawa ba a daren aurensu.

Zuwa tayi kusa da ita ta zauna tare da jawota jikinta suka k'ank'ame juna suna kuka, sun d'auki
kusan mintuna biyar suna kukan Aunty Murja ta had'iye nata kukan domin ta samu ta rarrashi
k'anwarta ta, Cikin muryar rarrashi ta fara magana "Khadijatullah nasan akwai zafi sosai a cikin
zuciyarki, abin da Jabir yayi miki sai dai muce Allah ya saka miki domin kinsan mu ba wani
arzik'i ne damu ba, barantana muce zamu kai shii k'ara kotu abi miki hakk'inki, Kuma ko min kai
Jabir k'ara a zamanin nan na yanzu babu abinda za'ayi Masa saboda Yana da kud'i, Dan Allah
Khadijatullah kiyi hakuri kinsan yawan kukan nan zai iya haifar miki da wata matsalar Ina tsoron
kar in rasa ki kamar yadda muka rasa iyayanmu ke kad'ai nake kallo nake jin dad'i a cikin
zuciyata" ta k'arasa maganar hawaye na zuba daga cikin idanuwanta.

Khadijatullah ta d'auki kusan mintuna goma tana kok'arin tayi magana Amman kukan da take ya
hanata tayi dakyar ta samu ta sassaita kanta ta fara magana cikin sark'ewar muryar "Aunty
Murja nasan bakya son kina ganina a cikin irin wannan yanayin, Amman Aunty Murja Ina ga ba
zan tab'a daina kuka ba, zuciyata ba zata tab'a daina min zafi ba, saboda yanzu mun d'aura
k'awance da tashin hankali, Aunty Murja wallahi ina ga bak'in cikin Jabir ne zai kasheni" wani
sabon kukan ne ya kwace Mata Aunty Murja ta k'ara rumgumeta sosai a jikinta, Khadijatullah ta
d'auki kusan mintuna biyar tana kukan kafin ta cigaba da magana "Aunty Murja wallahi na tsani

Aure kuma na tsani maza, wallahi da za'a bani dama da sai na kashe duk wani namijin da yake
duniyar nan tabbas na yarda da maganar hausawa da suke cewa namiji ba d'an goyo bane duk
yadda ka Kai ga goya shi wata rana sai yayi maka abin da ba kayi tunanin zai yi maka ba,
Kuma idan kaga namiji a rana karka sake kace zaka jawosa inuwa idan kuwa ka jawosa wata
rana kai zai tura cikin ranar, Aunty Murja namiji yayi min abinda har abada ba zan manta dashi
ba a DAREN AURENA". Duk tana kuka take maganar zuciyarta na cigaba da yi mata zafi.

Aunty Murja kuwa bata iya cewa komai ba, ta cigaba da rarrashin k'anwarta ta har ta samu baci
b'arawo ya saceta hamdala Aunty Murja ta shiga yi a cikin zuciyarta domin ta samu yau
Khadijatullah tayi bacci Wanda rabon da tayi bacci tun ranar DAREN AURENTA wanda yau
kwana uku kenan.
*'BANGAREN GIDANSU JABIR*

Zaune yake a kan kujera wacce ake iya kwantar da ita a kwanta, a farfajiyar gidan ya saka
shisha a gaba yana zuk'arta a hankali daga shi sai wani gajeran wando dan ko riga babu a
jikinshi, fari ne tas wanda kana ganinshi za kasan balarabe ne, gashin kansa ya kwanta luf sai
shek'i yake yi yana da manya_manyan idanuwa wad'anda farare ne tas, dogon hancinsa yayi
matuk'ar dacewa da d'an k'aramin bakinsa, wayarsa wacce take gefensa ce ta shiga ruri
hannunsa yasa ya d'auketa tare da duba screen d'in wayar ganin wanda yake kiran nashi
*Teemarh namo* ya gani, wani gajeran murmushi yayi sannan cikin sanyayayyar muryarsa ya
ce "yau akwai harka kenan" d'aga kiran yayi ba tare da ya ce komai ba, daga b'angaren
Teemarh namo kuwa cikin shagwab'a ta fara yi magana "baby shine jiya ba ka zo club ba ina ta
jiranka, kuma bayan kasan kwana biyu nayi missing d'inka sosai" ta k'arasa magana cikin
nark'ar da murya, Jabir ya d'auki kusan mintuna biyar kafin ya ce "Am so sorry dear wallahi na
d'an je wani guri ne kuma ban dawo da wuri ba". Cikin nuna tsantsar kishinta a fili ta ce "ina
kaje? kodai kaje gurin wannan tsohuwar matar taka" wata iriyar dariya Jabir yayi wacce kana jii
kasan ta tsantsar mugunta ce yana dariyar ya ce "haba dai ai wannan ta riga da tayi expired,
please ki kwantar da hankalinki, ai yayinta ya riga da ya huce tuntuni" Murmushi teemarh namo
tayi ta ce "to shikenan baby yanzu yau dai zaka zo ko? Kasan wallahi nayi missing d'inka sosai i
miss your hug i miss you so so much" murmushi Jabir yayi ya ce "zan shigo da daddare yanzu
ina d'an hutawa ne" yayi maganar kamar wanda ake yi masa dole "Ok to shikenan sai da
daddaren ina nan ina jiranka"
"Ok" yayi maganar a takaice.
"i love you"
"thanks you dear"
Daga nan kowannan su ya ajiye wayarsa Jabir ya cigaba da zuk'ar shishar.

*'BANGAREN KHADIJATULLAHI*

Ta d'auki kusan awa d'aya tana bacci a jikin Aunty Murja dan ita ma har baccin ya d'auketa
kamar an tsikareta ta farka a gigice, irin yadda ta farka ne yasa Aunty Murja ita ma ta tashi ta
rikota "Khadijatullahi meya faru"

Kallon Aunty Murja take hawaye na kok'arin zubowa daga idanuwanta "bakomai" tayi maganar
cikin muryar kuka rumgumeta Aunty Murja tayi tana bubbuga mata bayanta tana cigaba da yi
mata nasiha mai ratsa zuciya daga waje suka jii anyi sallama ana kok'arin shigowa d'akin
"Assalamu alaikum" Mai shigowar ta fad'a tare da tura kofar d'akin ta shiga, Murmushi Aunty
Murja ta sakar mata tare da amsa Mata sallamar "Wa'alaikissalam Amatullahi"
"Ina wuni Aunty Murja" Amatullahi ta tsugunna har k'asa cikin ladabi tana gaisar da Aunty
Murjan
"Lafiya kalau ya kike"
"Lafiya alhamdulillah"

Sai kuma ta komar da dubanta kan Khadijatullah wacce tayi luf a jikin Aunty Murja.
"K'awata ba dai har yanzu kuka kike yi ba, haba Khadijatullah dubi yadda fuskarki ta koma
idanuwanki duk sunyi ciki_ciki saboda kuka ya kamata kisan cewa wannan k'addara ce Allah
ubangiji ya d'ora Mana, Kuma dukkan musulmi ya kamata ya rumgumi duk iriyar k'addarar da
tazo Masa Mai kyau ce ko akasin haka".
Shuru kawai Khadijatullah tayi tana sauraronta tana sauke ajiyar zuciya idanuwanta na cigaba
da zubar da hawaye, tabbas tasan su Aunty Murja ba zasu tab'a fahimtar irin tashin hankali,
bala'i da masifar da take ciki ba, taya za'ayi a daketa Kuma a hanata kuka, bayan sun san irin
cutar da Jabir yayi mata tana jin labarai a gidan t.v, kuma tana jin labarai iri_iri wad'anda maza
suka yiwa matayensu na cin mutunci, Amman ita Bata tab'a jin labarin irin abin da Jabir yayi
Mata a DAREN AURENSU ba, ta yaya za'ayi ta manta da wannan daren, wanda take kiransa
da bak'in dare domin ita DAREN AURENTA ya kasance Daren bak'in cikinta, Wanda har yanzu
take cikin bak'in ciki.

Amatullahi ta saka hannunta a kan fuskar Khadijatullah tana goge Mata hawayenta,nan ita da
Aunty Murja suka sakata a gaba suna yi Mata hira domin su samu ta hak'ura, ita dai kawai jinsu
take Amman a wannan karon tayi kok'arin had'iye kukanta domin ta fahimci kukanta Yana jefa
masoyannata guda biyu cikin tashin hankali, Aunty Murja ce ta tashi ta d'auko musu abincin da
ta girka a wani d'an k'aramin kwanon silba, ta dawo gurin da take ta zauna tare da bud'e
kwanon shimkafa da Mai da yaji ce, "Kash! na manta ban d'auko cokula ba" Amatullahi tayi
murmushi "To Aunty Murja bari in d'auko miki" mik'ewa tayi ta nufi inda kwandon kwanukansu
yake wanda babu wani kayan kirki a cikinsa, ta d'auko cokula guda biyu wad'anda kana ganinsu
zaka san sunyi mugun dad'ewa domin har sun fara lank'washewa, zama tayi tare da mik'awa
Aunty Murjan cokulan "Gashi Aunty Murja" cokali guda d'aya ta k'arb'a sannan ta ce "to matso
sosai muci abincin" Da sauri Amatullahi ta girgiza kai domin abincin dake kwanon bama zai
ishesu ita da Khadijatullah ba, saboda bashi da wani yawa "Kaii Aunty Murja Alhamdulillah
wallahi sai da naci abinci sosai kafin in zo" sai kuma ta mik'awa Khadijatullah cokalin tana fad'ar
"gashi nan kici abincin" girgiza kai ta shiga yi alamar bata cin abincin, cikin d'aurewar fuska
Aunty Murja take magana "wato abin da kike son ki tsira kenan rashin cin abinci, ai shikenan
tunda haka kika zab'ar wa kanki" sai kuma ta fashe da kuka, cikin tashin hankali Khadijatullah ta
karb'i cokalin hannun Amatullahi "Aunty Murja Dan Allah ki dena kuka zan ci" ta fad'a tare da
saka cokalin a cikin abincin, shuru Aunty Murja tayi ita ma ta shiga cin abincin loma biyar

Khadijatullah tayi ta ajiye cokalin, ta zame ta kwanta a kan yaloluwar katifar da take kan gadon
ta rufe Ido domin Bata so Aunty Murja ta k'ara takura Mata taci abinci, Aunty Murja ma Bata ce
Mata komai ba, Amatullahi kuwa mik'ewa tayi tare da cewa "to Aunty Murja zan tafi".
"Amatullahi yau tafiya da wuri haka" murmushi tayi ta ce "wallahi Aunty Murja zamu je Unguwa
ne da Mama shine nace Bari inzo na ganku kafin mu tafi" Aunty Murja ta ce "Allah sarki
Amatullahi to mun gode sosai" "Haba Aunty Murja bakomai ai" zagayawa tayi dai_dai saitin kan
Khadijatullah ta shafa fuskar ta ta tana cewa "To k'awata sai na sake dawowa gobe idan yau
min dawo da wuri zan k'ara dawowa na ganku" Kai kawai ta d'aga mata, Amatullahi ta k'ara
yiwa Aunty Murja sai anjima sannan ta fita daga gidan da saurinta, Aunty Murja ta tashi ta shiga
gyara d'akin daga nan ta dawo kan gadon ta kishim gid'a tana sauraron radio da ta kunna a
wata matatciyar radio duk rayi raga_raga.

*'BANGAREN GIDANSU JABIR*

Shirye yake cikin wasu k'ananun kaya, kyau iya kyau ya gama yi, turarurrukan dake kan
madubin d'akinsa wanda kamar shagon kanti saboda yawansu, ya shiga fasawa a duk jikinsa
saboda duk yawan turaren nan sai da ya bisu d'aya bayan d'aya yana fesasu a jikinsa, wani
d'an k'aramin kum ya d'auka k'irar dubai shi kanshi kum d'in abin tsayawa ka kalla ne, ya shiga
taje kannasa da kum d'in a hankali tamkar wanda a kace dole sai ya taje kannasa, sai da ya
d'auki kusan awa d'aya yana shiryawa, sannan ya nufi hanyar fita daga d'akin, ko kulle d'akin
bai yi ba haka ya nufi b'angaren Mami Yana taku d'aya_d'aya kamar wanda yake tsoron tafiyar,
a haka har ya isa part d'in Mami to sallama bai yi ba haka ya tura kai cikin falon nata a zaune ya
tarar da ita tana kallon wani film a zee word, da sauri ya k'arasa kusa da ita ya rumgumeta tare
da yi Mata kiss a kumatunta, Murmushi Mami tayi tare da shafa kansa "Wow my son you look
so Masha Allah" Murmushi yayi tare da cewa "Thanks you Mum I really love you so much"
Mami ta ce "Me too My son I love you so much" Mik'ewa tsaye yayi tare da cewa "Mami zan tafi
club sai na dawo a chan zan kwana naga magriba tayi ana ta nema na akwai Abu Mai
muhimmanci da zanyi me" yayi maganar cikin Yana yin shagwab'a "To sai ka dawo, Allah ya
kaika lafiya, Amman goben ka dawo da wuri saboda Aliyu zai dawo daga dubai Kuma da wuri
sai sauka" cikin yanayin farin ciki Jabir ya ce "Kaii d'an uwana Aliyu Ashe dai zan k'ara ganinsa
kaii kamar ma kar inje club d'in saboda naga d'an uwana nayi ten year fa ban saka shi a idona
ba".
Murmushi Mami tayi "Ai sai gobe zai dawo kaga bai kamata kak'i zuwa club d'in ba saboda kace
akwai abinda zakai Mai muhimmanci ai sai gobe zai dawo ai har ka dawo ma" cikin yanayin jin
dad'i ya ce "please Mami karku je d'aukoshi har sai na dawo" wani k'ayatatcen murmushi tayi ta
ce "karka damu zamu jiraka" wani irin tsalle yayi sannan ya nufi kofar fita daga falon Yana fad'ar
"Yawwah Mami nagode sosai" da murmushi ta bishi sannan ta cigaba da kallonta hankalinta
kwance, shi kuwa Jabir Yana fita kai tsaye wajen da aka tanada d'an ajiye motoci ya nufa, ya
shiga sabuwar motar da Abbansu ya Aiko Masa da ita, Mai gadi ya bud'e Masa gate ya fita da
gudu daga gidan bai zame ko ina ba sai club, ai kuwa Yana isa club d'in tun kafin ya fito daga
mota aka saka Masa ihu, Yana fitowa daga cikin motar zee namo tazo da gudunta ta
rumgumeshi tana yi Masa kiss ta ko ina a jikinsa, d'aukarta yayi cak dan Daman Shima a matse
yake yazo club d'in ya huta da zee domin Yana jin dad'in yarinyar sosai hotel d'in club d'in ya

nufa da ita, ana fa guri ya k'ara hau tsinewa da ihu, shi kuwa Jabir bai bii ta kansu ba domin
burinsa kawai ya samu ya biya buk'atarsa da Zee d'in, d'akin da aka basa ya shiga, ya ajiye zee
d'in a kan gado, ya cire mata kayan jikinta daman ba wani kayan k'irki bane a jikin nata rigar
bacci ce wacce ko gwiwarta Bata Kai ba, Bata da hannu d'an haka ya zama duka rabin k'irjinta
duk a waje suke, Anan ya shiga tsotsarta ta ko ina tamkar ya samu wata alewa, Zee abin nema
ya samu dan haka ta sakar Masa dukkanin jikinta Yana tsotsarsa, Anan dai sukai ta shek'e
ayarsu (ni kuwa 'yar mutanan zazzagawa nace Allah ya shiryeku Amin) sai wajen isha'i sannan
ya sauka daga kan Zee d'in Amman ita Zee d'in sam Bata so haka ba, saboda bata gama
dawowa dai_dai ba, toilet ya shiga da niyyar yin wanka, Zee ya mik'e ta shiga cikin toilet d'in, ta
tarar da Jabir har ya fara yin wankan bayansa ta hau ta fara shafashi a hankali "Baby kasan fa
baka gama dani ba, dan ni ban koshi ba".
Jabir dai shuru yayi domin ya rasa masifa irin ta Zee kullum idan yayi sex da ita duk irin
dad'ewar da zai yi a kanta sai tayi Masa korafin Bata koshi ba, janyota yayi ta dawo gabansa
Yana kallonta tana kallonsa tana wurga Masa wani shu'umin murmushi.

Jabir ya ce
"Baby ki barni nayi wanka, zuwa anjima zamu had'u,karki manta fa muna tare yau gaba d'aya"
yayi maganar cikin salonsa wanda yake rikita yammata, narke masa tayi a jikinsa ta lumshe ido
bata k'ara magana ba, Jabir yayi² ta rabu dashi yayi wanka amman sam teemarh tak'i barinsa
sai ma k'ara nanik'e masa da tayi, haka ya kyaleta ya shiga yin wankansa teemarh na jikinsa
tamkar cingum ta mak'ale masa tana cigaba da shafa jikinsa.

D'aga ta yayi suka fita daga cikin toilet d'in, a kan gado ya samu ya kwantar da ita, sannan ya
shiga saka kayansa, ita dai teemarh da kallo take binsa idanuwanta sunyi jawur tana wani
lumshesu tana lasar bakinta tamkar mayya tana k'ara zubawa surar jikin Jabir d'in ido, shi kuwa
Jabir yana gama shiryawa ya dawo kan gadon yana shafa dukkanin jikin teemarh kuma ya
tsotsarsa, haka dai sukai ta aikata Alfasha har kowannansu bacci yayi awan gaba dashi, basu
suka tashi ba sai wajen k'arfe shida na safe, ko sallar asuba basuyi ba, haka suka tashi suka
shiga wanka a tare, suka fito Jabir ya fara shiryawa da sauri saboda yana tsananin son ya ga
d'an uwansa tunda Mami ta fad'a masa cewa yau d'in Aliyu zai dawo da kyar ya iya bacci
saboda gani yake kamar idan yayi bacci bazai tashi da wuri ba, ita ma Teemarh shiryawa tayi
cikin doguwar rigar baccinta, a tare suka fita daga d'akin Jabir ya rufe d'akin, suka nufi motar, A
hanya ya sauke Teemarh domin kuwa baya son ya k'arasa wannan matatciyar unguwar tasu, ya
ja motar da gudu bai tsaya a ko ina ba sai a gida, mai gadi ya wangale masa k'aton gate d'in
gidan ya shiga da gudu har yana kok'arin yin ciki da mai gadin, Allah ya taimakeshi ya buga
wani mugun tsalle sai da ya fad'i a k'asa har ya fasa goshi.

Da saurinsa ya fito daga motar ya nufi hanyar da zata sadashi da tafkeken falon, yana shiga ya
tarar su Mami da k'annansa guda biyu dukansu mata ne Shahida da Nihal, wad'anda baza su
huce shakara sha bakwai ba, da gudu Nihal ta k'arasa gurinshi tana fad'ar "Yawwa bro daman
kai muke ta jira yanzun nan Mami take kok'arin kiranka" murmushi yayi tare da rumgume
k'anwar tasa "to darling sister ai gani nazo kawai mu juya muje mu d'aukoshi k'ar jirgin nasu ya
sauka, bamu k'arasa ba" Mami tayi murmushi tare da cewa "Ai yau dai kam naga ana kok'arin

mantawa dani, dukkanku kuna d'aukin ganin d'an uwanku" da sauri Jabir ya saki Nihal yaje ya
rumgume Mamin "haba Maminmu taya zamu manta dake you are so speacial to us" haka su
Nihal da Shahida ma duk suka rumgumeta, Murmushi take ta faman sakarwa 'ya'yannata,
"Thanks you so much my darlings ina 'kaunarku sosai, yanzu dai muyi sauri mu k'arasa Airport
kar Aliyu su sauka bamu k'arasa ba, tunda ya ce 7:00am zasu sauka, yanzu kuma 6:30am daga
nan suka dunguma zuwa Airport mota d'aya kawai suka d'auka, k'arfe 7:00am suka isa filin jirgi
dai-dai lokacin jirgin su Aliyu yana sauka,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0