Showing 78001 words to 81000 words out of 84387 words

Chapter 27 - Daren Aurena Book Complete

07 Sep 2026

302

bar nan dan Allah zai kasheni" Mai adaidaitan ya ja da gudu sunyi nisa
sosai, ya juyo yake tambayarta "Hajiya ina muka nufa?" Anan tayi masa kwatancen inda zai kai
ta, suna k'arasowa, ta fita tare da ce masa "Ina zuwa yanzu zan shiga gidan, mai gadi zai kawo
maka kud'inka" Mai adaidaitan ya ce "To shikenan babu damuwa" Juyawar da za ta yi suka
had'a ido da Alhaji Mansur yana tsaye a bakin motarsa, da sauri ta k'arasa gurinshi tana kuka
"Dan Allah Abban Jabir"........ "Ya isa Asiya ki yi min shuru, ba na buk'atar sake ganinki a
rayuwata, tunda ke butulu ce baki san darajar d'an adam ba" Durk'ushewa tayi akan guiyoyinta
tana kuka "Duk abin da ka fad'a min na san na chanchanci fiye da haka ma, zaka iya kirana da
abin da ya fi butulu ma, Amman dan girman Allah Abban Jabir koda ace zaka yanke alak'ar da
take tsakaninmu, ina rok'onka ka yafe min, na san nayi maka butulci ban kyauta maka ba, ka
yafe min dan Manzon Allah" Alhaji Mansur jikinsa ne ya yi sanyi sosai, dan shi a rayuwarsa
baya so ya ga matarsa tana kuk saboda shi "To na ji, ta shi tsaye" Mik'ewa tayi tana jin jiriri yana
kok'arin kayar da ita, muryar Alhaji Mansur ta ji yana tambayarta "Wanchan fa, meya tsaya yi"
Ya yi maganar yana nuna man adaidaita "Shi ya kawoni, kud'insa zan biya sa" Ta basa amsa
kanta a sunkuye.

Zuwa ya yi gurin da mai adaidaitan yake tsaye ya d'auko naira dubu biyar ya mik'a masa, nan fa
ya shiga godiya ya ja adaidaitarsa ya yi gaba, shi kuma Alhaji Mansur ya dawo gurin da Hajiya
Asiya take tsaya ya ce "Yanzu ai kin ga abin da son zuciyarki ya janyo miki, ni dai yanzu na yafe
miki Allah ubangiji ya yafe mana gaba d'ayanmu" Godiya Hajiya Asiya ta shiga yi masa tana
kuka, ya dakatar da ita da cewa "Ya isa haka, ni yanzu ina da gurin zuwa zaki iya yin tafiyarki"
Hajiya Asiya ta ce "To zan tafi amman dan Allah ina neman wata alfarma a gurinka, ina so ka zo
muje tare na nemi yafiyar su Innata dan na san indai na je ni kad'ai ba za su saurareni ba" Alhaji
Mansur bai mu sa mata ba ya ce ta shiga mota su je, ta shiga gurin mai zaman banza ta rufe,
shi kuma Alhaji Mansur ya ja motar ya nufi gidan su Asiya.

To fa k'ak'ak'ara k'ak'a shin iyayen Hajiya Asiya zasu ya fe mata kuwa, ku biyoni dan jin yadda
labarin zai kasance💃🏽.

Suna isa gidan Hajiya Asiya ta ga gaba d'aya ya chanza mata ya koma irin na manyan masu
kud'i ta san ko ba'a fad'a ba, Alhaji Mansur ne ya gyara gidan ya zama abin ban sha'awa, ta
bud'e murfin motar ta fita amman me sai ta kasa motsawa daga gurin da take, wasu zafafan
hawaye suna zubowa daga cikin idanuwanta yanzu da wane idon zata kalli iyayenata wanda
rabon da ta saka su a idonta tun ranar aurenta da ta fita ta koma gidan k'awarta Aisha, Alhaji
Mansur wanda har ya yi nisa ya juyo yana kallon Asiya, tabbas yasan tafi nadama amman ya

kamata ya koya mata hankali sosai "Me ki ka tsaya yi anan? Kin kawo ni ne dan ki tsaya kina
kuka" Tafiya ta fara yi inda Alhaji Mansur yayi gaba tana bin sa a baya, wani babban falo suka
shiga inda nan take tayi ido biyu da iyayen nata, kuka ta saka tare da k'arasawa gabansu ta
zube, magana take son yi amman ta kasa saboda irin kukan da ya ci k'arfinta, su kuwa Malam
Kalla ido kawai suka zuba mata, "Dan Allah Inna da baffa ku yafe min abin da nayi muku, na
san ban kyauta muku ba idan har baku yafe min ba, to tabbas haka rayuwata zata cigaba da
tafiya cikin bak'in ciki da k'unci, ba zan tab'a ganin dai-dai ba, dan Allah ku yafe min na tuba"
Alhaji Mansur ya ce "Baffa ku yi hak'uri ku yafewa Asiya tabbas tayi nadamar abin da tayi a
baya, dan Allah ku yafe mata" Inna ta sauke ajiyar zuciya tare da cewa "Bakomai Mansur na
yafe mata" Malam Kalla ya ce "Tabbas Asiya kin ci darajar Mansur yau da ke kad'ai ki ka zo
gidan nan sai na b'alb'allaki, amman bakomai na yafe miki Allah ubangiji ya shiryeki" Nan Alhaji
Mansur yayi musu godiya sannan ya mik'e tare da yi musu sallama, ya fita daga falon.

Inna ta cewa Hajiya Asiya "Tashi na nuna miki d'akinki","To" Tayi maganar tare da mik'ewa ta bi
bayan Innar, suna shiga d'akin Hajiya Asiya ta ce "Innata ina 'yan uwana","Gaba d'ayansu sun
yi aure, amman Hajara tun tafiyarki da 'yan kwanaki aka nemeta aka rasa har yau ba'a ganta
ba" Zaro ido Hajiya Asiya tayi ta ce "Inna na shiga uku ina Hajara ta je?" Inna ta ce "Wallahi
bamu sani ba, ni na rasa ma ya zan yi"Ta k'arasa maganar tare da fashewa da kuka "Kiyi hak'uri
Innata ai na dawo zan je zan nemo duk inda 'yar uwata ta je, zan dawo da ita gida" Hajiya Asiya
tayi maganar tare da rumgume Innar tana rarrashinta, har tayi shuru haka dai Innar tayi ta ba
wa Asiya labarin irin neman da su ka yi wajen neman Hajara amman ba su sameta ba, kuma
basu ji labarin komai a kanta ba "Ina tunanin wani ne ya bata labarinta, shiyasa ta gudu" Hajiya
Asiya ta juyo cike da rashin fahimtar inda maganar Innar ta nufa "Inna ban gane ba, labarinta
kuma, wane irin labari ne?" Inna ta gyara zama tare da cewa "Hajara ba 'yarmu ba ce tsintota
Baffanku ya yi, mun b'oye muku ne saboda ba ma son ku nuna mata wani abu da zai sa ta
fahimci ba iyayenku d'aya ba, musamman ke dan nasan indai kika san hakan za ki yi mata gori
ne" Hawaye ne ya shiga zubowa Asiya "Innata insha Allah zan nemota, duk inda taje ai bai
kamata tayi mana haka ba, ko da ace wani ne ya fad'a mata asalinta ya kamata,ta fad'a muku
domin mu ta ya ta nemo iyayenta, bai kamata ta gudu ba" Haka dai Hajiya Asiya tayi ta
kwantarwa da mahaifiyar hankali abin gwanin ban sha'awa, ni kam 'yar mutan zazzau nace
Hajiya Asiya ko ke fa🤣.

*BAYAN WATA 'DAYA DA SATI BIYU🌼*

Jabir hankalinsa ya gama tashi ko bacci ba ya iya yi saboda tunanin Khadijatullahi, zuwansa
gidan Hajiya Mama yafi sau ashirin dan ya samu ya ga Khadijatullahi ya nemi yafiyarta amman
kullum yaje baya samun damar ganinta, zaune yake a cikin office d'insa kasancewa Abba ya
bashi jagorancin ma'aikatarsa wacce ake yin shainkafa, ya zabga tagumi wayarsa ce ta shiga
ruri ya kalli wayar wacce take ajiye a kan taburin office d'in *Bro Aliyu* shine ya bayyana a kan
screen d'in wayar, Jabir cike da jin haushin Aliyu gami da wani a zababban kishi da ya taso
masa, ya katse kiran Aliyun tare da sakashi a blacklist dan Shahida ta bashi labarin Aliyu ne
yake son Khadijatullahi dan har an kusa saka ranar aurensu, tarin takaddu ne a gabansa
wad'anda ake jira ya saka hannu, amman ya kasa duba koda guda d'aya baren tana ya saka

hannun.

Mik'ewa ya yi da sauri ya d'auki wayarsa tare da mukullin motarsa, ya fita daga office d'in bayan
ya kulleshi motarsa ya shiga yana tuk'i amman gaba d'aya hankalinsa baya kan titin ya lula
tunanin Khadijatullahi da kuma yaronsa Affan, Jabir bai yi aune ba sai ji yayi ya daki wata
k'atuwar mota, wanda haka ya yi sanadiyar motarsa ta fad'a cikin wani babban rami ta kama da
wuta gaba d'aya motar ta cinye, Innalillahi wa inna'ilaihiraju'un mutanan gurin suke ta faman
fad'a koda suka lek'a ramin basu ga alamar akwai mutum ba, dan kuwa komai a cikin motar ya
k'one kurmus, da yake wasu a gurin sun san motar Jabir nan aka samu wanda yake da number
wayar Alhaji Mansur nan suke fad'a masa Jabir ya yi hatsari kuma gaba d'aya motar ta k'one
kuma yana cikin motar, Alhaji Mansur ana fad'a masa haka ya zube a k'asa tare da rushewa da
kuka, Aunty Murja ta k'araso tana tambayarsa menene, ya kwashe duk abin aka fad'a masa ya
fad'a mata yana kuka "Shikenan yanzu yarona ya mutu, ina tsananin son Jabir kamar raina
amman yanzu ya mutu ya bar ni" Aunty Murja gaba d'aya hankalinta ya tashi, haka dai tai-ta
rarrashin Alhaji Mansur har ya yi shuru, nan ya d'auki wayarsa ya kira Aliyu, Aliyu wanda yake
zaune a falon Hajiya Mama suna hira ya ji wayarsa ta d'auki ruri ya yi tunanin Jabir ne, amman
da ya kalli screen d'in wayar ya ga number Abba, ya d'aga jin muryar Abba a chan k'asa k'asa
yasa Aliyu ya saka wayar a speaker don ya ji abin da Abban zai ce masa "Aliyu kazo yanzu,
Allah ya yi wa d'an uwanka rasuwa a hanyarsa ta dawowa gida ya yi hatsari motar gaba d'aya
ta k'one kuma yana cikin motar" Mik'ewa Aliyu ya yi jikinsa na rawa hawaye suka shiga zubo
masa, nan da nan gumi ya dinga keto masa ya jik'ashi shark'af "A'a Abba d'an uwana bai mutu
ba, yana raye ba zan yarda ba wallahi ba zan yarda ba" Aliyu ya yi maganar tare da yin jifa da
wayar, Shahida kuwa hannu ta d'ora akai tare da kurma wani uban ihu "Mun shiga uku yayanmu
ya mutu, innalillahi wa'inna ilaihi raju'un" Aliyu kuwa fita ya yi da sauri ya shiga motarsa ya nufi
gurin da Jabir d'in ya yi hatsari.

Ya na zuwa gurin nan ya nufi gurin rumin gadan-gadan, da yake akwai hanyar da ake bi a shiga
cikin ramin Aliyu yana shiga ramin ya nufi gurin motar Jabir da ta k'one, yana kuka jikinsa ya yi
sanyi domin ganin irin yadda motar ta k'one tabbas ya san ya rasa d'an uwansa dan gaba d'aya
motar ta zama toka, nishin da ya ji a bayansa ne yasa ya juya da sauri, Aliyu ya mik'e ganin
Jabir a kwance cikin jini rumgumeshi ya yi yana jin wani irin farin ciki yana shiga zuciyarsa,
d'aukarsa ya yi cak suka fita daga cikin ramin a mota ya sakashi ya nufi asibitin Abbansu, suna
isa asibitin Aliyu ya fito daga cikin motar, wasu nurses guda goma suka nufo shi suna tura
gadon da ake d'aukar mara lafiya idan an kawoshi, Aliyu ya fito da Jabir ya d'ora shi a kan
gadon, nurses d'in suka tura gadon Aliyu yana bin bayansu har aka shiga da Jabir emergency
room, Sai a lokacin Aliyu ya dawo cikin hayyacinsa ya zaro 'yar k'aramar wayarsa ya kira Abba
ya fad'a masa Jabir bai mutu ba yanzu ma suna asibiti dashi, sannan ya kira Shahida ita ma ya
fad'a mata, ko minti goma ba'ayi ba sai ga su Hajiya Mama da Abba sun shigo cikin asibitin
suka yo kan Aliyu suna tambayarsa "Ina Jabir d'in" Nan yake nuna musu d'akin da aka shiga da
Jabir "Alhamdulillahi Allah mun gode maka, ya ubangiji ka tashi kafad'un wannan bawan na ka"
Hajiya Mama ta yi maganar tana kuka, dukansu suka amsa da "Amin" Khadijatullahi ta ce "Yaya
Aliyu ka tabbatar Jabir bai mutu ba" Ta yi maganar cikin yanayin damuwa "Eh Dija Mijinki bai
mutu ba" Khadijatullahi ta kalli Aliyu cike da mamaki amman ba ta iya cewa komai ba, Teemarh

ce ta rumgume Khadijatullahi tana kuka "Dan Allah Khadija ki taimakawa mijina ki yafe masa,
ina da tabbacin sanadiyar tunaninki ne yasa ya yi hatsarin nan" Khadijatullahi gaba d'aya ta
rud'e ta ma kasa magana, sai bin mutune da ta ke yi da ido, haka dai suka nemi guri kowa ya
zauna, kowannansu ka kalli fuskarsa zaka ga tarin damuwa da tashin hankali mara misaltuwa.
*'BANGAREN LADO DA INNA LARAI💃🏽💞*

Durk'ushe yake a gaba mahaifiyar ta sa yana kuka yana neman gafararta "Dan Allah Innata ki yi
hak'uri da duk abubuwan da nayi miki ki yafe min na san tabbas ban kyauta miki ba, na zalince
ki ni ba d'a na gari ba ne" Inna Larai tayi murmushi ta ce "Bakomai Lado na yafe maka, abin da
na shuka ne nake girbarsa" Lado ya ce "Nagode Innata Allah ya saka miki da alkhairi, ki tashi
muje d'akina ni zan koma d'akinsu Lawal" Inna Larai ta mik'e Lado tana gaba Lado yana bin ta a
baya, ta shiga d'akin Lado, kayansa ya shiga tattarawa yana kaiwa d'akinsu Lawal har ya gama
ya zauna suka d'an yi hira da Innar ta sa, daga k'arshe ya yi mata sallama ya fita.

Yana fita su ka yi kicibus da Zaituna, kallonsa tayi cike da girmamawa tana sakar masa
murmushi "Yaya dan Allah kayi hak'uri ka yafe min, ban yi maka rashin kunya dan"............. "Yi
shuru Zaituna meyasa ki ke ba ni hak'uri, ai gaskiya kika fad'a min kuma nagode da kika dawo
da ni hanya madaidaiciya, kuma insha Allahu zan gyara kuskuren da nayi a baya" Murmushi
Zaituna tayi ta ce "Indai kayi hakan ni kuma na amince zan aureka, domin kuwa kasan Ina
tsananin son Inna" Zaituna tayi maganar tana rufe fuskarta, Lado ya ji matuk'ar dad'in kalaman
Zaituna wani farin ciki ya shiga tsarga masa, ita kuma Zaituna ganin kallon da Ladon ya ke yi
mata yasa ta shige d'akin da Inna Larai take da gudu tana dariya, shima ya nufi d'akin su Lawal
yana jin dad'i a cikin zuciyarsa.

*BAYAN KWANA BIYU✌🏽*

Aka saka ranar auren Zaituna da Lado wata d'aya farin ciki gurin wad'annan masoyan ba'a
magana, nan suka shiga nunawa junansu wata iriyar sabuwar k'auna kamar su cinye junansu,
kullum suna tare Lado yana zuba mara ruwan kalaman soyayya, ni kuwa er mutan zazzau nace
Lado ya za ka yi mana haka Amatullahi fa�Karka manta ita ce tsohuwar zuma🤣.
*BAYAN AWANNI GOMA SHA BIYAR🤧*

Da taimakon Allah Likitoci su ka yi nasarar, ceto rayuwar Jabir bayan gwagwarmayar da suka
sha, kafin su yi nasarar ceto rayuwarsa dan gaba d'aya likitocin jikinsu ya yi sanyi ganin irin
yadda jini yake zuba kamar famfo daga jikin Jabir, dakyar suka samu suka yi masa aiki har jinin
ya tsaya, Doctor Isham ne ya fito daga d'akin yana gyara rigar jikinsa da sauri Alhaji Mansur ya
taresa yana tambayarsa "Ya jikin Jabir" Murmushi Doctor Isham yayi ya ce "Alhamdullahi da
taimakon ubangiji mun yi nasarar ceto rayuwar Jabir, yanzu dai mun yi masa allurai nan da awa
d'aya zai iya farfad'owa" Kowannansu ya shiga furta "Alhamdulillahi" Doctor Isham ya nufi office
d'insa, Nihal ce ta shigo asibitin da gudu tana kuka dan Shahida ta kirata ta fad'a mata Jabir ya
yi hatsari "Abbanmu ina Yaya Jabir d'in yake" Abba ya ce "Ki kwantar da hankalinki yana nan

lafiya" Shiga d'akin su ka yi gaba d'ayansu, zama su ka yi a kan kujerun dake d'akin suna kallon
yadda Jabir d'in ya ji raunika a jikinsa, masu kuka nayi masu tagumi da jimami nayi.

Bayan awa d'aya Jabir ya fara motsi da 'yan yatsun hannunsa tare da kiran sunan
Khadijatullahi, ras gaban Khadijatullahi ya yi mummunan bugu, duk da irin yadda ta tsani Jabir
yanzu kam wani irin tausayinsa take ji saboda ganin irin yadda gaba d'aya kamanninsa suka
chanza "Na'am" Ta amsa tana zubar da wasu zafafan hawaye, hannun Teemarh ta kama suka
k'arasa gurin gadon zama su ka yi a kan gadon, Jabir a hankali ya bud'e idanuwansa ya dorasu
a kan Teemarh "Zahra" Ya kira sunanta a hankali, duk da irin yadda Teemarh take cikin tashin
hankali sai da tayi mamakin a ina Jabir yasan sunan da danginta ne kawai suke fad'a mata
"Na'am" Cikin wata iriyar wahalalliyar murya ya ce "Ina Khadijatullahi?" Khadijatullahi ta ce
"Gani nan" Ya juya a hankali dan Khadijatullahi ta zauna ta wajen kansa ita kuma Teemarh ta
wajen k'afafuwansa, hannuwanta ya kama yana kok'arin fashewa da kuka "Dan Allah ki yafe
min, nasan ban kyauta miki ba kuma"......... "Na yafe maka tuntuni Allah ya yafe mana ga baki
d'aya" Khadijatullahi ta k'atseshi daga k'arasa maganar da zai yi "Nagode sosai, ina yarona?"
Khadijatullahi ta karb'i Affan daga hannun Amatullahi ta ajiyeshi kusa da Jabir tana cewa "Gashi
nan" Hannun Affan ya rik'e yana murmushi, gaba d'aya su Abba sun ji matuk'ar dad'in yadda
Khadijatullahi tayi wa Jabir kuma sun san nan da 'yan lokaci kad'an burinsu zai cika, wasu
kawar da k'iyayyar da Khadijatullahi ta ke yi wa Jabir.


Bayan sati uku aka sallami Jabir suka daga gidan Hajiya Mama dan ya ji sauk'i sosai, yana iya
tashi da kansa kuma raunikan da ya ji sun fara warkewa, kullum yana tare da Teemarh da
Khadijatullahi a gefensa dan bai yarda d'aya daga cikinsu tayi nesa dashi ba, Affan kuwa kullum
yana mak'ale dashi, a yau aka saka ranar auren Khadijatullahi da Jabir da kuma Amatullahi da
Aliyu wanda babu wanda ya san da haka gaba d'ayansu, Shahida ce ta fad'o falon da gudu
tana tsalle, kallonta su ka yi gaba d'ayansu Aliyu wanda yake zaune yana chatting da abokinsa
ya ce "Lafiya kuwa kodai duk a cikin gwaurancin ne" Dariya Jabir ya yi ya ce "Wallahi kuwa bro
wannan yarinyar ai sai ana yi mata uzuri" Amatullahi da Khadijatullahi suka fashe da dariya
"Kaiii sister ce fa, ita ma ta kusan shiga daga ciki Ammar zai yi wuff da ita" Khadijatullahi tayi
maganar tana kallon Shahida wacce ta had'e ranta jin ance Ammar "Allah Aunty kina yi min
wulak'anci sosai ni fa ba na son wannan mutumin" Teemarh ta ce "Kin ga kyalesu me ki ka zo
fad'a mana na san wannan bakin na ki akwai news da yawa" Shahida ta ce "Yawwah Aunty
Fatima shiyasa nake sonki da yawa, A yau ne ranar laraba da misalin k'arfe hud'u da rabi na
rana aka saka ranar auren Amatullahi da Yaya Aliyu sannan kuma aka saka ranar auren
Khadijatullahi da Yaya Jabir inda za'ayi bikin nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0