Showing 1 words to 3000 words out of 4267 words

Chapter 1 - Rana Daya Book 3 Hausa Novels By Halima Abdullahi Mashi

Rana Daya
BOOK 3
By k Mashi
Page 1


ALhaji Isa ya shiga cikin Falon yana kiran,

"Hajiya!"

' Badi"atu ta fito daga dakinta tana yi
wa Alhajin sannu da zuwa,sannan ta ce,

"Yaya Mustapha ya kai ta Kaduna".

Ya kalli agogon bangon falon tare da fadin,

*Nan da Kaduna shine har yanzu sai ka ce wadanda suka tafi Abuja?

Badi'atu ta ce,

"Sai da suka yi sallar azahar sannan suka tafi"

Ya ce,

"Kai Hajiya tana da shiririta sosai. Ni da
muka yi da ita za su tafi tun safe?"

" Ya ja tsaki tare da fadin,

"Yanzu dubi fa shida saura, kuma ta san ina azumi"

Badi'atu ta ce,

*Ga shayinka can yanzu na gama dafawa, na sa a flask"

Ya ce

"*Shayin ne kadai matsala ta kenan?

Tana sani na tsani in dawo ba ta gida. To wai su nawa suka yi tafiyar ne?"

Badi'atu ta ce,

"Su da Mama Ya nufi dakinshi yana fadin,

*Bari in kira ta"
Daidai wannan lokacin Shatima yana tsakiyar

falon cikin tsansnin damuwa, da tashin hankali. Minti daya tak din da Hajiya ta ba shi ne ya yi
mugun tsorata shi.

Sam ba ta ba shi isasshen lokacin da zai yi tunani ba. Ya nufi kujera da nufin zama ko zai samu
basirar shawo kan matsalar. Don rudewa sai ya kai zaman kafin ya isa kujerar. Hakan ya sa shi
zubewa a kasa
Salatin da ya ji dakin ya dauka gaba daya ne yasa shi lunshe ido, tare da fatan Allah ya sa
mafita ce wannan Ya saki jikinshi tamkar wanda hankalinsa ba ya tare da shi Nan duk suka yi
kansa suna kiran sunansa. Hajiya tana fadin, "Na shiga ukuna! Shatima don allah ka tashi! Ku
debo min ruwa
Mama ta ce, "Tsaya mu gani ko dai juwa ce ba suma ba ne?"

Aliya da su Amna sai nanata sannu suke yi.

Hajiya ta dibi ruwa ta wanke mishi fuksa tare da fadin,

"Sannu Shatima, ka tashi don Allah

Duk yana jinsu, ko babu komai sanyin ruwan ya rage masa zufar da take tsiyaya a jikinsa.
Sannan ya sauke wata irin ajiyar zuciya.

Mustapha cikin bacin rai ya ce, "Ban ga dalilin yin wannan zantukan ba tunda ba su ne suka
kawo mu ba"

Shatima kuwa addu'a yake a cikin zuciyarsa,yana kiran sunayen Allah tsarkaka. Fatanshi Allah
ya
fidda shi cikin wanna fitina. Miyan bakinshi ya tsaya

cak! Lokacin da ya ji muryar Hajiya tana maimaita ya wartsake a yi ta ta kare, don ba zan bar
wannan damarba.

Mama tace, "Haba Hajiya! Don Allah ki bar wannan maganar, a bi komai sannu

Alhaji ya yi ta duba wayarshi a daki, sai ya tuna tana mota inda ya jona ta a caji. Ya cire
kayanshi ya
maida jallabiya mai gajeran hannu, sannan ya fita.

Missed calls ashirin na Mustapha ya gani, Tsoro ya kama

shi, tare da fargaba suka darsu a zuciyarshi. Tuni ya
Raya cewa sun yi hatsari ne. Cikin rawar hannu ya bi
kiran.

Da sauri ya daya,

Alhaji don Allah ka kira Hajiya yanzun tazo tana ta fada da abubuwa a gidan ga shi nan har Ya
Shatima ya fadi!*

"Faduwa?" Alhaji ya tambaya da karfi.

Mustapha ya ce,

"Faduwa kuwa, yanzun haka ba ya cikin hankalinshi

Alhaji ya ce, "Ai babu batun kira, bari kawai inkira Babanku Musa muzo gidan

Mota ya fada a hakanshi, sannan ya kira layin dan uwansa Alhaji Musa. Lokacin da Alhaji Musa
ya daga wayar Alhaji ya kusa fitowa daga layinsu. Alhaji Musa ya ce, ga shi a Jaji sun z0 duba
jikin Alhaji Yakuba abokinsu, wanda ya hadu da ciwon mutuwar Barin jiki.

Alhaji ya ce, "Gani a hanya, jira ni a titi zan dauke ka mu wuce"

Alhaji Musa ya ce, "Ina zamu Wuce!?"

Alhaji ya ce,

"Kaduna gidan Shatima, Hajiya Amina da suka je dubiyar jikin Nafisa ta tada musu wata fitinar.
Ga shi can an ce jikin Shatima ya tashi har ya fadi yana da rai ko ya mutu ma? Ni ban sani ba"

Gudu sosai Alhaji ke yi, cikin mintuna ya iso

Jaji, ya dauki Alhaji Musa ya kuma daukar hanya

Cikin lokaci kalilan Shatima yana jingine da kujera

kanshi yana cinyar Aliya wadda wadda idanu suka yima jajir don kuka.

Page 2


Yace Hajiya, Ki saurare ni zan yi mikI bayani yanda za ki fahimta'

Ta mike tana fadin,

"Kana bata min lokaci, ga shi can ana kiran magariba. Ni kawai cewa na yi ka saki waccan
abin", Ta nuna Salma wadda ke durkushe a kan Kafafunta, tun gurin da aka titsiye ta Kafatunta
sun yi sanyi sun sage, har ba ta san ta yi motsi mai karti don azabar da suke yi mata.

Shatima ya ce, "Hajiya.Ta sake katse shi,

"Bana son jin komai daga gare ka, sakinta kawai na ce ka yi. Ba zan fahimci komai ba"

Alhaji ya fado Takin babu sallama, ya amshi zancen Hajiya da cewa,

"Wa za a saki?"

Shatima ya mike da sauri tare da fadin, Alhamdu lillahil.

Alhaji Musa ya ce,Zauna Babana, zauna kar ka sake faduwa

Alhaji ya isa gaban danshi da sauri ya kama shi, ya zaunar tareda fadin, "Zauna abinka

Shatima ya zauna cikin farin ciki, tare da ci gaba da yi wa Allah godiya.

Hajiya ta yi matukar girgiza, mamaki ya cika ta da ganin Alhaji. A zuciyarta ta ce,

"To wa ya fada ma Alhaji?"

Alhaji ya dube ta rai bace, fuska daure, "Yanzu Hajiya Amina kin yi daidai kenan? Ki taso tun
daga

Zaria da sunan gaida mara lafiya don ki samu lada, amma ki buge da tada husuma cikin gidan
danki?

Ina hankali da tunaninki suka shige? To wa kike fadin a saki ma?"Ya kalli Alhaji Musa,

"Dubi wani abin kunya don Allah

Alhaji Musa ya ce

"Ga wadda za a ce ta yi abin kunya nan. Kin z0 gidan"yarki gaban kishiyoyi, gidan suruki kin
tada hankali? Wannan abin fadin da me yayi kama? To da kin yi sanadin rayuwarshi, me za ki
Ce?"

Hajiya cikin borin kunya ta ce, "Ni ban tada wata husuma ba.

Wane munafuki ne ma ya kira Alhajin?"

Ta kai Karshen maganar tare da kure Mustapha da ido.

Shatima ya ce, "Alhaji, don Allah ku zauna, nidai na gode wa Allah da ya turo mini ku a daidai
wannan lokacin. Don Allah ku taimaka min ku zauna

don a warware wanna matsalar. Domin duk wata

matsala a duniya ana warware ta ne ta hanyar zama a tattauna ba ta 鈥瀉nyar tashin hankali
ba. Ba kuma ta hayaniya ba

Alhaji yace "'Mu yi sallar magariba tukunna ko?"

Hajiya ta ce, "Ni fa kawai a yita ta kare, ya saki *yar can mu kama gabanmu". Ta fada tare da
nuna Salma.

Duk suka dubi gurin da Salman ta ke a tsugunne, sai lokacin Alhaji ya ga Salma din.

Hajiya ta ci gaba da fadin, "Ni fa duk wannan abin lafiyarsa ni ke yi ma wa, ku ba za ku fahimta
bane an fada min cewa uwar yarinyar nan ta je ta kai sunan Shatima an tsaface shi don ya
dinga kashe musu

kudi. An hada asirin da yawun bakinta, an yi surkulle an ba shi ya ci. Kuma asirin ya ci shi
domin ga shi yanzu duka yaushe aka yi auren ma ya sa ta a makaranta mai tsadar gaske,
kullum sai ya ba ta dubu da dari biyar. Ita na haifar ma shi kenan?" Salma ta fashe da sabon
kuka tana fadin. "Na rantse da Allah Hajiya, Innarmu ba ta zuwa gurin masu asiri.
Ko Babanmu da yake da ciwon Barin jiki cewa tayi yi kar a kai shi grin masu maganin gargajiya
ciwonshi na asibiti ne kar su bata masa jinya su ce wani ne ya yi masa asiri. Allah na rantse ba
mu taba yi wa Yaya asiri ba. Allah ma ba zai barmu ba, domin shi taimakonmu ya yi. Na sani
ban kai Yaya Shatima ya aure ni ba, mu tsoro ma muka ji da ya ce shi zai aure ni. Ga ma Yaya
din a tambaye shi, ko ruwan gidanmu bai taba sha ba bare har ma mu ba shi nama ya ci"

Ta saki ajiyar zuciya, sannan ta karasa maganar a hankali,

"'Ko yanzun da nike matarshi bai ci abincina ya kai sau goma ba. Cewa yake ni ban iya girki ba"

Ta jero shesshekar kuka a tare, sannan ta ci gaba da gunjin kuka.Alhaji ya kalli Hajiya,

"To ke da ki ka ce an fada miki, wane ne ya fada miki din?"

"Hajiya Azumi ta yo min tambaya a gurin malamai, kuma ta ce guri biyu ta je duk bakinsu daya

Alhaji ya kalli Alhaji Musa ya ce, "Ka ji ko?

Imaninta ta saida a gurin makaryatan bokaye. To da izinin wa ki ka je?" Ta zaro ido cikin firgici,
ta ce,

"A'a Alhaji, Niba zuwa nayi ba. Ina fada maka Hajiya Azumi na aika

Shatima ya amshe zancen da cewa,

*Alhaji,kamar yanda Salma ta fada ne, ko ruwan gidansu ban taba sha ba. Hajiya ma da ta
yarda da wanna karyar ta

so ta yarda ne. domin ta fi kowa sanin yanayina domin ba kowane abu ni ke iya ci ba,

Kuma kudi da Hajiya take magana ina ba

Salma, ita ce ma ba ta samu gatansu ba, komai na

sauran matana ya fi na Salma. Gida da Hajiya ke magana haya ce na kama musu, ba siya na yi
ba don ko alakar aure ba ta hada ni da 'yarsu

ba ina yi musu. Taimako irin wannan ban san adadin da na yi ba, Munnir ya san haka ba sai na
zo na ce

Hajiya, ko Alhaji na taimaki wasu ba. Haka ko a hanya na sha kashe rigimar kudi da aljihuna in
wucce Ba ina fada ba ne don alfahari ko gori ba, ina son a fahimce ni.

Maganar kud矛 wane magulmaci ne ya fada?"

Aliya ta ce, "Ai na sani kudin nama ne ka ke bata, mu kuma kana saka mana nama a fridge. Na
fadama Hajiya"

Shatima ya kalli Alhaji,

"Ga su nan rago na dubu talatin-talatin nike siya musu su uku, kowacce a gyara a saka mata a
fridge ga kaji guda goma-goma na wata daidai kenan, amma cikinsu na Amna ne kawai

ya kai watan. Su kafin haka nasu ya fare, ita ko Salma

dubu daya a wata, dubu talatin, sannan bana sai mata kaza. In na siyo gasasshiya har da su
nike saye. Haka kuma akwai kudin kati da nike saka musu duk sati, ita ko ko wayar ma ba ta
mallaka ba bare kudin kati ya je mata

Shatima ya dubi Hajiya,

"Zancen makaranta kuwa,alkawari na dauka tsakanina da mahaliccina cewa, zan taimake ta tu
帽 kafin in yanke shawarar zan aure ta

Ya numfasa sannan ya kalli Mama,

"Akwai abin da ba ku sani ba. Babu son Salma ko digo a cikin zuciyata, so na soyayya dai sam
babu wannan. Na auri

Salma ne don in taimaki rayuwarta ta yi karatu. Ta so in aura mata wani ne, in mata kayan daki
don ta cika

burin Babanta. Ni kuma na aure ta don ta cika duk
burikan guda biyu ne. Zan iya zama da Salma har karshen
rayuwarmu, in kuma da zuri'a a tsakaninmu har mu
samu rabo, ba zanyi Ki ba. Amma ba don so ba. In kuma tana bukatar rabuwa da ni yayin da
burinta ya cika, zan iya sahale mata ta je ta auri wanda ta ke so, yake sonta.

Ban fadi haka don cin fuska ga Salma ba, sai don hakan shine gaskiya, kuma Hajiya ta gane
cewa,Salma ba su yi min asiri ba

Salma kanta a sunkuye wasu zafafan hawaye ke

zuba a idanunta masu radadi. Tun da aka soma rigimar

bata tsinci kanta cikin bakin cikin da ya kai na yanzun
nan ba. Kalaman Shatima sun yi tsauri, kuma sun yi
ma zuciyarta daci, sannan sun yi ma kwakwalwarta nauyi. Har ma ta ji da ma ya bi umarnin
mahaifiyarsa

ya sake ta din zai fiye mata jin wadannan munanan
kalaman da suka fito daga bakinsa. Ta soma rainon
zuciyarta, har ta soma koyon sonshi, da tantance son

Page 3


Don ta samar da sotsan tsamara gauraye. Ashe ita tana aikin banza ne, gara ma da ta sani tun
da wuri.

Ta dago jajayen idanunta ta kalle shi, yana da Kimar da ba za ta iya maida mishi magana ba,
don haka ta sake sunkuyar da kanta.

Alhaji yace

"Duk abin bai kai a yi wannan tone-tone ba, kada in Kara jin an yi zancen saki, ko
asiri

Ya dubi Hajiya Amina, yace

"In kin ci gaba da dagewa a kan wannan maganar zan ta sa ki har gaban Hajiya Azumin,
sannan mu je gurin malam su bani hujja'

Ya nuna ta da yatsa,

"Kin san zan iya Alhaji Musa ya ce,

"Wannan shine gaskiyar magana

Mama ta ce, 芦Ni wallahi duk wannan abu ba a son raina suka faru ba. Ban so aka tono
wadannan zantukan ba, tunda ban san komai a kai ba. Mun dai z0 duba mara lafiya

Alhaji yaja tsaki, "Ga shi mun rasa jam'in
magariba a kan zantukan nan marasa tushe, bare makama

Ya kalli Hajiya,

'"Ke ce babbar mai laifi a cikin wannan al'amarin"

Ya kalli Salma 芦Tashi yarinya kin ji daga wanna durkuson

Salma ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta yunkura da niyyar tashi. Kafafunta sun yi tsami, ba za
su iya daukarta ba, don haka ta koma ragwat! Ta zauna.

Alhaji Musa ya ce,

'"Sannu, Kafafun naki duk sun yi tsami ko?"

Ya sa hannu a cikin aljihunsa ya ciro kudi ya kirga naira dubu goma sha biyar ya mika wa
Shatima, ya ce,

"Ga shi ka sai mata waya ko karama ce, don ita ma ake saka mata katin ko da iyayenta sa
gaisa

Ta dubi Alhaji Musa ta ce,

"Baba na gode".Muryarta tana rawa.

Yace

"Babu komai "yata"

Yaci gaba,'da Kowacce ta koma gurinta ta zauna lafiya da mijinta da

"yar uwarta, zuciya daya

Amna ta kalli Hajiya,

"Babu maganar asiri-asiri ko?"

鈥� Alhaji ya amshe,

"Babu wata magana da ta

shafi asiri, duk sharri ne'

Ta ce,To, ku gaida gida".

Ta nufi sashenta cikin jinjina abin da ya faru.

Aliya ta mike tana fadin, "Ga shi ko abincin ma ba ku ci ba. To ku gaida gida"

Salma ta bi Aliya da kallo, ba ta shakka ita ce ta hada komai. Ta soma tuno wasu abubuwa da
ta yi mata masu kama da ingiza mai kantu ruwa.

Salma ta yunkura ta mike da kyar ta dubi su

AlhajiBaba ku gaida gida"

Ta kalli su Hajiya,

- "Sai anjimanku, Allah ya tsare hanya Su Alhaji suka ce,

"To sai anjima, ki yi hakuri kin ji ko?"Hajiya ta tabe baki tare da raka Salmar da harara.

Nan Alhaji ya yi ma su Hajiya fada sosai,sannan suka ce,

"Ku shirya bari mu yo sallah mu zomu wuce"

Salma ranar da zazza6i ta kwana, haka kuma ba

ta jin cewa za ta je a yau. Lokacin da Shatima ya shiga
gurinta da safe tana nade a zanin gado a can tsakiyar gadonta. Ya kira sunanta,

"Salma".

Da kyar ta daga idanunta jajir ta ce, "Na'am."

Ya ce, "Ya ya dai, ba ki da lafiya ne?"

Ta maida idanu ta rufe, zuwa yanzu ba ta son taji ko ta ga Shatima. Ta ce,

*"Dan zazzabi ne'

Ya hau gadon ya saka bayan hannunshi a sassan wuyanta. "Kai! Haka jikin naki ya yi zafi?
Tashi in kai ki asibiti

Ta yunkura tare da fadin, "Ka barshi kawai, zai bari anjima kadan

Ya ce, "To in turo Aliya ta duba ki?"

Ta ce,

"Ka barta anjima kadan zan warware"

Ya ce,

"Yaushe ki ka soma gardama da ni?"Salma ta yi shiru,

Ya kama hannunta,

"'Sakko in kai ki asibiti"

Jallabiya ta saka suka tafi.A bakin

makarantarsu suka tsaya, ya rubuta *yar takarda ya bawa mai gadi ya ce ya kai ofishin
shugaban makaranta.

An ba ta allura da magunguna, ya dawo da ita

gida. Ya shiga gurin Aliya. Da ma ta ga fitarsu, ya ce,

don Allah ta lura da ita ba ta da lafiya.

Aliya tace, "To"Yana fita ta zauna cikin fargaba, kar dai ita ma

wannan cikin gare ta? Na ba ni ni Aliya, nice kenan zan zama karshe?"

Ta mike da sauri tare da fadin, "Bari na je dakin Salmar na gani"

Ta same ta kwance kan kujera. Salma tana gaminta a ranta ta ce, "Allah ka yi min tsari da duk
sharrin da matar nan ta zo min da shi

Aliya ta je gabanta ta tsaya tare da rike kugu,

"Ashe ba kya jin dadi?"

Salma ta ce,

"Uhum".

Aliya ta ce,

"*Ko ke ma cikin ne?"

Salma ta ce, "Oho! Ni ma ban sani ba"
Ta sake matsawa kusa da ita,

"Wane irin gwaje-
gwaje aka yi miki?"

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login