Showing 3001 words to 4267 words out of 4267 words

Chapter 2 - Rana Daya Book 3 Hausa Novels By Halima Abdullahi Mashi


Salma ta yi mata banza. Tsaki ta ja ta fita tana mitar, yana fadin ba ya sonta amma ga shi nan
da cikinsa a jikinta.

Salma ta shiga kunci da bakin ciki sakamakon kalaman Shatima. Duk da wautarta da Kuruciya
ta san

Shatima ya ba da ita badawa ta karshe, ya kunyatata gami da tozartata. Ta yanke ma kanta
dakatar da son


Shatima, sannan za ta ja baya da shi. Za ta ci gaba da kallonshi a matsayin Yaya kurum

***

Kwanci tashi asarar mai rai inji masu iya
magana. Amna da Nafisa ciki na ta girma. Domin

Amna tana da shidda, Nafisa tana da wata biyar.

Shatima ya samu Amna da batun zuwa awon

ciki, ta ce masa ita sai sun dawo daga umara. Ya dube ta cikin al'ajabi,

"Za ku je ummara yaushe?"

Tace

"Jibi insha Allahu za mu tafi da su Momy

Yace, "Ikon Allah, shine ban isa ki fada min ba bare ki nemi izinina?

Ta ce,

"Jiya Mom ke fada min ni ma'

Shatima ya yi shiru cikin bacin rai. Ya sauke ajiyar zuciya, abu daya zai sa ba zan hana ki ba,
amma gaskiya a guji shigar min hakki"

Ta dube shi.

"Ban gane ba? Kana nufin da saika hana?"Yace

"Kwarai kuwa Ta yi *yar dariya irin ta rainin wayo, ta ce,

"Kai kana da son rigima"

Ya kauda zancen don ba ya son su fara sa'insa,

don haka sai ya ce, "Ke nan ba ki nan za a yi bikin su Hannatu, yaran Yayan Alhaji marigayi na
Kaduna?"

Ta dan yatsina baki,

"Ko ina nan ka san bai zama lallai inje ba don bana son hayaniyar mutane

Shiru ya yi yana kallonta, don tuni ya lura ba ta son duk wani al'amari da ya shafi danginsa,
domin ko

kwanan baya da Hajiya Kaka ta yi rashin lafiya babu yanda bai yi ba a kan su je a duba ta ba,
amma ta ki, kuma sauran duk sun je. Amma bari ya yi mata uzuri ta haihu.

Bikin "ya'ya biyu za a yi, babban dan Kaka wanda ya rasu, bikin a Zaria za a yi shi. Haka kuma

bikin zai kama ana saura sati daya azumi. Da Amna ta

Page 4

shirya za ta tafi Kano don yin tatiyarsu, Shatima ya yita maza ya ce,

"Allah ya tsare hanya". Ya kuma kawo dubu goma ya ba ta.

Kanwar su Alhaji Hajiya Sauda ita ce ta fito da

anko, ta kira Shatima tana sanar da shi cewa, ga na" matanshi kala bibbiyu, kudinsa naira dubu
arba" in.

Ya ce, "Anty na mutum uku za a cire, Amna bata nan anty tace To zan barsu gurin Kaka"

Ya ce, "*Shi kenan, ki turo account in tura miki

kudin Da ya sanar da su batun anko, Nafisa ta ce za tasa Hamida ta je ta amshi nata a gurin
Kaka din. Aliya ma cewa ta yi za a zo daga gidansu a karba mata.



' Salma kuwa cewa ta yi, nata a bai wa Anty Badi 'atu ta bai wa mai mata dinki.

Ya ce, "To telan ya sanki ne?"

Ta ce, "Ta yi masa kwatance na kawai

Salma Bash shine sunan da *yan makarantar su Salma ke kiranta da shi. Kawarta Salma Sadik
Dankasa

ita ce ta rada mata shi. Zuwa wannan lokacin Salma ta waye, ta goge, ga turanci tana gane
karatu sosai.

Haka nan in ka ganta tana tsalle-tsallenta sam ba za ka ce tana da aure ba. Salma da ma
yarinya ce, sannan ga ta da son wasa, shi ya sa kawancensu ya dace da Salma Sadik. Suna
cikin group din Kwallon tebur da kuma rawa irin ta makaranta. Wani lokacin ma wayarta ta

kan kunna a gida tana cashe rawarta.

Yau Shatima dakin Salma yake. Dafadukan taliya ta yi, ta zubo masa don ta lura yanzun yana
cin abincinta, tunda aka yi wannan hayaniyar.

Ta aje a gefensa yana zaune kan kujera yana aiki da laptop. Ta

koma ciki tana atisayen rawar da za su yi gobe in sun je makaranta. Ya kwalla kiranta.

Ta fito ta durkusawa a gabanshi, ya ce,

"Wai ke duk lokacin da zan shigo sai in ji kina jin wannan sautin, ina ki ka samo shi?"

Ta ce, "Muna amfani da shine a club dinmu na rawa"

Ya kware da abincin da ke bakinshi, nan ya shiga tari.

Salma ta ce, "Ya salam!"

Ta tsiyaya ruwa a kofi ta mika masa. Ya amsa

ya shanye, ya ajiye kofin sannan ta dube ta murya a shake ya ce, "Rawa? A wane club
kuma?"Ta ce,

"Yaya na makaranta ne, an ce mutum ya zaba ko rawa ko waka Ya ce,

"Kina manta cewa kina da aure ko?"

Ta ce,

"Ban manta ba". Ta sunkuyar da kai.

Ya ce,Gaban maza ku ke rawa ko?" Ta ce,

'A'a Ya ce,

"To kar dai ki sake in ji an ce kin shiga gasar rawa, balle a zo ana yinta a gaban mutane

Ta ce, "Ba zan yi ba, jibi ma za a yi mana hutu' Ya ce,Shi kenan.

. Yauwa Badi'atu ke ta damuna wai dinkin anko wane kala za a yi miki? Na ce in na dawo zan
neme ta. Bari in kira miki ita"

Salma ta ce,

"Mun yi waya dazun Yaya, da ma wai ba ta same ni ba ne ta kira ka. Nida zaka barni inje Zaria
din da na kai wadansu kayan

Ya ce,

"A'a sai biki za ki je gaskiya

Ta ce,Allah sarki Yaya, kayana sun sha ruwa wadanda aka dinka min"

Ya ce,Yau saura kwana goma sha daya bikin,zan je ranar asabar sai ki ba ni sako Ta ce,

*Badi'atu za a bai wa, zan amshi wasu style a hannun Salma Sadik"

Ya dago ya dube ta,

"To wa zai biya kudin dinkin?"

Ta yi murmushi,

"Ni zan biya kayana

Ya tattara hankalinsa a kanta,

"Ina ki ka samu kudi?"Ta ce,

"Wanda nike tarawa.Ya yi murmushi, "Kawo su mu gani, sun kai) dubu goma?"

Ta yi dariya tare da nufar daki. Ledar da ake

saka zanin gado ta dauko ta zo gabanshi, ta juye kudin a Kasa. Mamaki ya kama shi, ya ce,
"Wannan duk sune?"Ta ce, "Sune mana"

Ya ce,Lallai kudi wawaye ne, sun, kai nawa Yanzu tace

, "Sai dai a kirga a gani".

Ya dauki yan dari biyar, bari in hada wadannan, ke kuma ki hada sauran

"Bari in hada

Ta soma hadawa tana cewa,

Kila su kai irin dubu talatin din nan

Sun gama lissafi abin da yaba su mamaki, sai ga kudi dubu dari da biyar har da naira sittin.
Salma tace, "Kudina ne kadai kuwa?"

Ya ce, "Ana ba ki ajiya ne?"

Ta ce, "A'a, ni dai to ko aljanu suna saka by Mistake?

Ya yi dariya, "Kin dauki watanni kina tara su'

Ya dube ta, "Ni ma za ki ba ni aron dubu hamsin

Ta ce, "a,a dai a raba zan dai ba ka kyauta.

Toni ban ma san ya zan yi da su ba. Ka amsa duka

mana?"Ya ce, "A'a ba zan amsa ba, ai kudinki ne"Ya Kirgi hamsin, "Wannan ma na ara ne,

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0