Showing 27001 words to 30000 words out of 31587 words
Chapter 10 - DUBAI BOOK 2 HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN.pdf
Ko giyar wake tasha
bazata taba kawowa uwa zata nakasa dantaba saboda mace girgiza kanta tayi tare da fadin
"astagfurullah" saboda batason ta dora rayuwarta akan zato kasancewarsa shima zunubi ne me
girma maganar Abbanta tana mata yawo a kwanyarta “kada ki dorawa kowa laifin gindayowar
wata kawalwainiyar qaddara cikin rayuwar aurenku babu wanda ya Isa ya cutar da wani bawa
saida sahalewar ubangiji kuma koda zakiji ance wane yayiwa wane abu kaza yayi tasiri tofa
bashine yayi ba shidai sanadi ne Amma asalin abun daga Allah ne"
Rungume qur'anin dake hannunta tayi tana kuka me ban tausayi tana furta “Mijina ya Allah
mijina! Hmmm Uhmmm!! Allah kabarni da mijina Allah kada kabawa wani bawanka abin halitta
ikon cutarmin dashi Allah kasa kowacce jarabawa ta tsaya iyakar ni inada tabbacin tunda baiqini
a baya ba babu tsananin da zaisa yaqini a gaba...." Ji tayi ya dagota cak ya hade bakinsa da nata cikin wani irin yanayi na tsananin qaunarta da
tausayinta ya janye bakinsa daga nata yace “ki daina kuka Habeeytah komai yayi farko zaiyi
qarshe insha Allahu zamu samu mafita gobe zanje asibiti ina tunanin ciwon marar dana yini
dashi shine yaja mana wannan matsalar" Dago idonta tayi dayake cike da hawaye tace “badon ni ba saidon don ita lfyr kowacce gaba
alfahari ce wa dan adam Ya Taheer koda ace haka zamuci gaba da zama na yarda Kuma na
amince zan rayu dakai rayuwa me tsafta rayuwar farin ciki rayuwar da tafi wacce mukayi a baya
ingancin" # *UMMUH HAIRAN*
[8/12, 9:52 AM] OPEN EYES MULTIMEDIA: *_HABEEYTAH_*
*_DUBAI PART 2_*
_Littafina na kudine ki biya kafin ki karanta bazance Allah ya isa ba amma nasan zai isarmin
tunda shi isasshene just 200 VIP 600 ta account number 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar
GTB ko kati MTN ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment dinki ta
wannan number dake sama Idan VTU ne ta wannan layin Zaki tura dari biyunki ko dari 600 ki/ka
09013307566 idan fah kika tura a wancan layin na sama to ki qaddara sadaka kika bani shi
evidence of payment kawai zaa tura_
*25* Sake matseta yayi a jikinsa yana sunsunar wuyanta ya dorata a gado ya zauna a gefenta
yana shafa cikinta tare da kwantowa jikinta da haka har bacci ya dauketa shima ya kwanta.
Washegari da safe ko karyawa bai tsaya yayi ba ya nufi asibiti iyakar binkicensu sunce qalau
yake babu wata matsala a tare dashi, hakanan ya dawo gda a kasalance wanna rana sunga
ikon Allah shi naci dole sai yayi sex abu Kuma yace baisan zance ba.
Days gaji saiya kwanta kawai zuciyarsa nayi masa zafi tunda yake bai taba shiga tashin hankali
irin na yau ba ita kuma sai rarrashinsa takeyi tana fada masa yayi hqr zai samu sauqi.
Wasa wasa abu sai qara gaba yakeyi itadai Habeey bata wani daga hankalinta ba tanayi masa
addu'a kullum sannan taqi barinsa ya fadawa kowa tace suyi addu'a kawai, suna addu'a yana
zagaya duk wani asibiti amma babu wani sauqi sai kamar qara gabama da abin yakeyi.
Lkc sai qara turawa yakeyi lamura suna qara tsamari tsakanin ma'auratan musamman Taheer
da yabi ya tsangwami kansa ya hana kansa sukuni kullum cikin damuwa yake.
Mafi yawan lokuta zuwa zatayi ta tarar dashi a dakinsa ya hade kai da gwiwa yana kuka
hakanan zata zauna tayita rarrashinsa idan yaqi yin shiru itama saita sanya masa kuka dole
ganin tanayi shidin ya haqura yayi shiru.
Watanninsu takwas lkcn cikinta yanada watanni biyar, a ranar da ya gama abinda yakeyi yace
ta fara package na kayanta jibi zasu tafi cikin murna tace “wlh dama duk na gaji My life" kallonta
kawai yayi ya girgiza kai ya fice.
Jikinta ne yayi sanyi ta dafe qirji a ranta tace “yanzu fah sai yayi tunanin da wata manufa nayi
maganar nan ko?" Ilai kuwa yana dawowa taga idanunsa ya kada yayi jajir ya kalleta yace “kin
gaji da zama dani saboda bani da amfani a gurinki ko Habeeytah?"
Idonta ne ya kawo ruwa ta matsa gabansa ta ruqo hannunsa yayi saurin janyewa tare da
komawa jikin bango ya dora kansa a bangon yace “nasan ba kowacce mace takeda qarfin
imanin zama da namijin da yake da matsala irin tawa ba"
Juyowa yayi suna fuskantar juna tana girgiza masa kai ya matso gabanta yace “hakanma kinyi
qoqari Habeeytah ko iya haka kika barni kinyimin halacci ki fadi duk abinda kikeso kafin muje
zanyi miki shi Koda kuwa Zaki zabi rabuwa danine...."
Dagowa tayi da sauri ta fada qirjinsa ta rushe da kuka tace “meye yasane Taheer me yasa
kullum kake dangantani da abinda bantaba dangantaka dashi ba meye yasa kakemin kallon
butulu Taheer meye yasa ka kasa gane matsayinka a gurina? Kullum nayi magana saika
fassarata da wani abu daban, ta yaya Taheer tayaya zan zabi nesanta kaina dakai, aa ka
dainamin haka don Allah kana saremin qwarin gwiwata ne please kada ka kuma inasonka a duk
inda kake zan rayu dakai ko bakada wani abin amfanawa rayuwata...."
Ajiyar zuciya ya sauke me qarfi ya dora bakinsa saman kuncinta yana lasar hawayenta nasa
suna zubowa yace “inaji kamar Ina cutar dake Habeey inajin kamar Ina zalumtarki ne kunyata
da soyayyarki gareni tasa kin kasa gane hakan wlh Habeey banajin ruhina zaici gaba da zaga
gangar jikina matsawar baki tare dani" Sake narkewa tayi a jikinsa tace “ni takace har abada My life" da wannan suka mantar da
junansu damuwarsu suka shiga bathroom sukayi wanka sukazo suka shirya suka fita wani
shopping mall sukaje duk wata siyayyarsu ta Safnah ce da babyn dake cikin Habeey itakam
kallonsa kawai takeyi. Koda suka gama suka juya gida sunata shagalinsu a parlourn yanata qissima mata irin dadin da
zaiji idan yaga Safnansa, wayarsa ce tayi ring ya dauka yana murmushi ya kara a kunnensa
yace “hello Dad..." Zabura yayi ya miqe yace “what innanillahi wa innah ilaihirraji'un yaushe?"
Jifa yayi da wayar ya zube a gurin jikinsa na rawa.
Nufoshi tayi da sauri ta zauna a gabansa da rawar murya tace “waye ya mut..." Dago kananun
idanunsa yayi da suka canza launi yace “Mom ce tayi accident ta hadu da matsalar spinal cord"
Dafe kanta tayi tana fadin “innanillahi wa innah ilaihirraji'un garin yaya" share hawayensa yayi
yace “bansani ba nima" Shiru ce ta ratsa babu abinda kakeji sai shassheqar kukan Habeey
kawai akeji dagota yayi yace “meye kikeyiwa kuka?" Cikin kuka tace “ina tuna halin da mutum
yake kasancewa idan ya rasa gabar da zatayi motsi a jikinsa" Kwantar da ita yayi yana murmushi yace “karki damu kowanne bawa baya wucce qaddararsa
gobe zamu tafi Dad yace akwai jirgin da zai tashi da kayansa gobe sai mu bisa" jinjina kai tayi
suka tashi suka shiga daki suka kwanta kowa da abinda yake saqawa a ransa har bacci ya
daukesu.
Tashin asuba jirginsu yayi suka lula 9ja abbanta ne yazo ya taresu tsoro ya kamashi ganin
yanda yar tasa ta rame sosai shima Taheer din duk ya zabge sai dogon hanci.
Bai iya tambayarsu ba har sukaje gdan gwomnatin yana riqe da hannunta suka fara ratsa
parlourn gabanta sai faduwa yakeyi da Bushirah sukayi kicibis da tsohon cikinta tana ganinta ta
saki wani ihu ta rungume Habeey tana cewa.
“Allah dai ya biya yayana sunqi Allah yaso kace mun kusa cika Fam da yara" kunya ce tasa
Habeey yin qasa shikuma yayi yaqe yace “ya jikin Mom din?" Tabe baki tayi tace “au Wai dama
saboda matarnan ka dauko baiwar Allah ka wahalar mana da baby? Hmmmm tana ciki tana
girbar abinda ta shuka"
Kallonta sukayi da rashin fahimta ta nuna masa dakin tace ka shiga ka ganta tana ciki ke kuma
zona rakaki bangaren yar'uwarki kiga mugun abinda son zuciyar uwarta yaja Mata Habeey ki
godewa Allah dakansa yake baki kariya"
# *UMMUH HAIRAN*
[8/12, 5:22 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: *26* Bin bayan Bushirah tayi gabanta na faduwa
suka shiga bangaren Saudat din tana kwance saman kujera lullube da wani mayafi suka
qarasa, a razane Habeey take kallonta tace “Subhanallahi meye haka" tsugunnawa tayi wani
wari da qarni ya daki hancinta zuciyarta ta hautsina ta toshe hancinta da sauri tana duban jikin
Saudat da da yake cike da wasu munanan manyan quraje sai zubar da mugunya sukeyi ta
zabura ta miqe tace “Innanillahi wa innah ilaihirraji'un meye haka Bushirah meye ya sameta
haka me yasa baa kaita asibiti ba?"
Numfashi Bushirah ta sauke cikin kuka tace “Anyi maganin har an gaji watanni takwas kenan
take fama da wannan ciwon satinku daya da tafiya su Mom da Aunty Zahrah da Hajja Ummah
suka tafi wani qauye a Zuru kwanansu uku sannan suka dawo cikin dare Aunty Zahrah ta tashi
ta dora ruwa a saman gas ta dauki barjajjiyar maiwa ta zuba a ciki ta kawo wani ruwan asiri ta
zuba taje ta bawa shanu suka shanye ta koma ta kwanta, tsakiyar talatainin dare gefin asuba
Saudat ta tashi ta rinqa ihu jikinta yana qaiqayi ana haskawa akaga wasu manyan quraje ne
suka feso a jikinta"
Rungume Habeey Bushirah tayi tace “da gari ya waye lbr yajewa Aunty Zahrah ta rinqa ihu tana
kururuwa wai ta manta ashe cewa akayi ta kiraki ta tabbatar da darene a U.S.A sannan tayi ita
Kuma ta manta tayi amfani da darenmu na 9ja Habeey ke akaso a dorawa wannan mugun
ciwon bakiji ba baki gani ba kawai saboda jahilci da zalumci bansan me kika tarewa bayin Allan
nan ba"
Hawaye ne ya rinqa sintiri a fuskarta ta sunkuya ta riqe hannun Saudat ta bude idonta a hankali
tana kallonta itama wasu hawaye na zuba a idonta ta buda bakinta da yake cike da quraje tace
“kin...kinga yanda Allah yayi dani ko Aunty Habbatullah Aunty ta jamin saboda Allah ba
azzalumin sarki bane gashi Mahfuz yace bazai iya zama dani Ina wari ba harma ya qara aure
sun tsallake sun barni shida matarsa sun tafi yawon cin amarci...."
Kuka sosai Habeey takeyi na tausayin yar uwartata da bataji ba bata ganiba laifin uwarta ya
shafeta, Saudat ta qara bude bakinta da yake buga wani uban wari tace “ashe dama Mom da
Aunty sune suka mantar da ruhin Abba dake da tunaninki tsayin shekaru saboda kawai
basason ki bayyana a matsayin yar Abbanmu ya kwanta ya mutu kici gadon" Miqewa Habeey tayi tace “Allah ya baki lfy Saudat bari naje naga jikin Mom" fita sukayi zuciyar
Habeey a karye sukaci karo da Taheer ya finciki hannunta a fusace yace “muje kawai basai
kinje ba"
Taso tambayarsa ba'asi amma yanda taji yana huci yasata jan bakinta tayi shiru suka fita ya kira
drive yazo yajasu zuwa gdansu da Addah tasa aka gyara musu suna tafe tana kwance a jikinsa
yana share hawaye zuciyarsa na quna ya gama tsinkewa da lamarin Mom dinsa Mom tayi nisa
ashe duk wahalar da yakesha da kudin da yake kashewa ita ta qullah komai itace ta lalata masa
gabansa saboda kawai ta hanasa farin ciki da iyalinsa shikam me yayi mata haka me Habeey
tayi mata da suke burin nakasta ta?.
Bashi da amsar tambayoyinsa saboda haka suna shiga ya zube a parlourn yana wuci jikinsa da
bakinsa na wani turirin zafi saboda ran maza ya baci, itakam lura da yanayinsa yasata haurawa
sama ta shiga tayi wanka ta canja kayanta zuwa wasu marasa nauyi cikinta ya fito sosai da
yake bana fari bane ta sauko qasan ta zauna a kusa dashi ta shafo kansa tace “kayi hqr don
Allah koma menene kaji" kwantowa yayi a jikinta ya fashe da kuka yace “ashe Mom tasan
komai itace ummul aba'isin faruwar komai da yake faruwa damu sune suka dora miki wannan
faduwar gaban data qararmin dake ta hanamu kwanciyar hankali, ashe sune suka kwantarmin
da gabana ya daina aiki Habeey ashe ciwon da aka cemin Saudat tana fama dashi tsayin
watanni ke akaso a dorawa shi Allah ya dawo musu da mugun nufinsu ashe a nufinta na ta
sake dora miki ciwon da kika tashi dashine taje sukayi hatsari Munafukar yayar tasu Ummah ta
mutu Mom ta samu wannan matsalar ita Kuma aunty Zahrah ta karairaye"
Sake shigar da ita yayi jikinsa yace wlh Mom ta cucemu hatta zargin da nakeyi miki ashe duk sa
sa hannunta nayi danasanin sanin Mom dama ba ita ta haifem..."
Rufe masa baki tayi tace “aa kar ka fadi haka don Allah komai yayi farko fa yanada qarshe
yamazo qarshen insha Allahu abinda akayi a baya bazaayishi gababa"
Lumshe idonsa yayi ya shafa cikinta yace “zan samu sauqi insha Allahu zakaran da Allah ya
nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi amma dai yanzu zaki barni na fadawa su Abba
matsalarmu ko?" Rufe idonta tayi tace “nidai kunya nakeji gsky..." Bakinsa ya dora saman nata
tace “nikam banajin kunyar neman lfy so nake da kin haihu na qara dura miki wani babyn"
harararsa tayi shima ya harareta sukayi dariya ya miqe yace “kina wanka Addah ta aiko mana
da abinci muci ki huta sai jibi zakije ku gaisa da su"
Abincin ya dauko ya ajiye musu a gabansu tuwon shinkafa ne miyar agusi ta dago ta kalleshi
tayi murmushi tace “Allah sarki Addah na ashe tana riqe da abinda nace mata inaso" qasa yayi
da idonsa yanajin dama mahaifiyarsa ce haka.
Sunci abincin sosai sunata zuba santi sauran yace ta ajiye ta dumama masa ya fice saboda ya
matsu yaga Abba su zauna ya zayyane masa matsalarsa sannan ga shauqin son ganin
Safnansa.
Yana shiga gdan ita ya gani tanata wasanta a saman lilo a harabar gdan ya qarasa inda take ta
dago ta kallesa ita a zatonta Mahfuz ne ta rungumeshi tana dariya shima dariyar yayi yanata
juyawa da ita yana cillata yana cafewa.
A haka Abba ya fito ya tarar dasu ya tsaya yanata kallonsa yanda ya ke wasa da yar tasa
soyayyarsa da yarinyar dabance dama ashe gaskene irin wadannan yaran shiga raine garesu,
duba da yanda shima yakejin yarinyar a cikin ransa.
Matsawa yayi suka gaisa yace “ta riqeka ko sarkin surutu ba baki sai gwaranci" murmushi yayi
yace “ai bakin ya kusa idan tayi qani zata ware ne" shiga sukayi ciki sun jima suna tattaunawa
sosai yasha fada yake cewa “akanme zakuyi Shiru da matsala banda shirmenku"
Qasa yayi da kansa yace “wlh Abba My life ce ta hanani fada wai kunya takeji" haushi ya cika
Abba yace “shine kuma kai dake juyin mace ne ka biye mata ko?" Wayarsa ya dauka yace dare
yayi yanzu amma gobe ka fito da wuri sai muje Billire gurin Mal Zaa dace insha Allahu" da
wannan suka fita ko Addah basu gaisaba tana sama tanata girki. Da yarsa ya tafi Habeey ta gama aikinta ta haye sama ta kwanta ta rinqa jiyo hayaniyarsa a
parlour bata fito ba har ya gama abinda zaiyi ya hauro saman ya taddata a kwance ta miqe da
sauri tana murmushi tace “Safnah ta" karbarta tayi da sauri ta rungumeta tace “inata kewarki ke
bakiyi tamu ba ko?" Daga Kai yarinyar tayi suka kalli juna sukayi dariya yace “dama ai abinda
akaso kenan kada ki shaqu damu to kinzo kenan yarinya"
Sosai suka shagala da yiwa yarsu wasa sai dare yayi mata wanka suka kwanta bacci.
Washegari da asuba ya tashi yayi wanka ya fice itama tayi sallah suka koma suka kwanta goma
ta gama komai sukayi wanka suka karya tanason zuwa ta gano jikin Mom amma data kirashi
wayarsa busy dole ta hqr ta zauna da yarta wajen qarfe tara na dare ya shigo baije inda take ba
Saida ya shiga dakinsa yayi wanka ya canza kaya yayi duk abinda Mal Kakan Habeey ya bashi
tun a Billire ya farajin sauyi a jikinsa ya shiga dakin Habeey suna kwance itada Safnah ya janye
Safnan a hankali ya kwantar da ita a gefe ya shige jikin matarsa yanajin wani yanayi daya dade
baiji a jikinsa ba,
Yanda taji yana shafeta dinne yasata saurin bude idonta ta saukeshi akansa ya daga mata gira
tana binsa da kallo shi Kuma yana lasheta tuni ya mantar da ita komai suka lula duniyar da
suka dade basu shigaba ranar sun gurzu sun qwaquli juna kamar ba gobe ta dandana Habeey
saboda ta dade bataji mazan ba. Qarfe biyu daidai wayarsa ta buga ya dauka ya kashe batare daya duba me kiranba, sake
shigowar kiran ne yasashi dagata ya dauki wayar tare da janye jikinsa daga na Habeey ya kara
a kunnensa Kubrah ce cikin kuka tace “ta mutu Yaya Mom ta mutu tana kiran sunan matarka
kaqi barinta tazo su gana"
# *UMMUH HAIRAN*
[8/14, 7:22 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: *27* Miqewa yayi a sanyaye yace “da gaske ta
mutu? Innanillahi wa Innah ilaihirraji'un" itama tashi tayi tace “waye ya rasu Life?" Kamota yayi
ya rungumeta ya fashe da kuka yace “mom Habeey Mom dinace ta rasu"
Kuka ta fashe dashi jikinta na rawa tace “ya Allah Allah ya jiqan Mom wayyoh Allah Taheer
shikenan Mom ta tafi ta barmu" hakanan suka qarasa kwanan nan da asussuba suka dunguma
suka tafi gidan government suna shiga suka tarar da gdan a cike da yan'uwa Kubrah ce ta
kama hannunta suka shiga dakin da Mom take kwance.
Suna shiga ta matsa da sauri ta bude fuskar Mom ta fada jikinta ta fashe da kuka abubuwa da
dama suka rinqa dawo mata tace “Allah ya jiqanki Mom Allah ya gafarta miki" shigowar su Dad
ne yasa Taheer ya janyeta daga jikin Mom din suka dauketa suka sanyata a makara aka fito da
ita suka fice da ita zuwa harabar gdan akayi mata sallah aka fice da ita gabadaya, Haka suka yini a gidan suna karbar gaisuwa itadai sulalewa tayi ta tafi bangaren Saudat yau sai
taga jikin da