Showing 99001 words to 102000 words out of 206906 words
Chapter 34 - Kanwar Maza Book 2 Complete By Aishacool .docx
ya gano wanda suka saceta".
Rumaisa ta ce "Kamar ka na son takawa? Tun da har ka san abubuwa a kan sa, amma meyasa ba kwa shiri?"
Jiki a sanyaye ya ce "Kar ki damu, lambar wayata na nan, na rubuta miki, a bayan sashin su mijinki, duk lokacin da ki ke buƙata ki kirani, idan har ina Nigeria" yana gama faɗa ya juya zai tafi ta ce "Idan kuma na gane ka zaɓi uwar riƙon ka, ka yaudareni, zan yi maka abun da ba ka zata ba, zan iya yin komai a kan uban ɗa na"
Cak ya tsaya, ya waiwaya ya kalleta, kawai ta kwashe da dariya, ta ce "Kamar a film ko? Zan iya acting ashe, ai na san ba zaka yi mini haka ba"
Tun da ya dawo ƙasar nan, suka haɗu da rumaisa, suka yi magana, yake jin kamar wani abu ya sauya a tare da shi, sosai yake jin tausayin Adam, kuma a jikinsa yake jin, lokaci ya yi, da yakamata Mummy ta tuba, shekaru sun fara ja, ko ba komai ta mutu ta samu rahamar Allah, sarautar da take yi masa ƙuzu kuma, shi ba a gabansa take ba ma.
A ɗakin Iman rumaisa ta yi salla, iman ta baya doguwar rigarta ta saka, suka zauna su na ɗan taɓa hira, iman ta ɗan bata labarin, irin wahalar da yake sha, idan yana ciwon nan, da kuma wahalar neman magani da ammi take yi, ba yau ba gobe".
Iman ta ɗora da cewa "Anty rumaisa, da kin sani ba ki faɗi maganar nan ta ɗazu a gaban mutane ba, ba zan musa miki mummy ba ta asiri ba, amma idan maganar ta koma kunnenta fa? Zai iya haddasa wata rigimar".
"Ai na ga duk wanda yake wurin, amintacce ne. Waye zai je ya faɗa? Ammi ce za ta gaya mata, ko kuma ke? Ko kuma baba uwani, da dama dan ita na faɗa"
Iman ta kalli rumaisa da mamaki, rumaisa ta yi dariya, ta ce "Iman, ina da wayo fa, kawai dai ba na ji ne, amma dan Allah Meyasa papa suke gaba da daddyna? Ko da ba ammi ce ta haifesu duka ba, amma ai ƴan uwa ne"
Iman ta ce "Duk ƴaƴan ammi ne"
Rumaisa ta ce "Ai na zata kema zaki raina mini hankali ne, ai na sani, na san duk ammi ce ta haifesu, amma daddy ya dage wai waccan matar ce babarsa, amma dan Allah meyasa gaba ɗaya gidan nan naku, a hargitse yake? Kowa ba shi da gaskiya".
Iman ta rausayar da kai ta ce "Ai ba abun da ki ka gani, family ne mai cike da rikici da ƙulla-ƙulla".
"Ai shi ne wannan yayan anty aishan, zai raina mini hankali, ni kuma wallahi yadda mutum ya mu'amalance ni a farko, haka nake tafiya da shi, kin ga rashin mutuncin da suka yi mini ranar da muka je gidan su, da shi, da wannan masifaffiyar mai jan kaya ta ɗazu, da wannan jabir ɗin, shi ma jabir ɗin da babarsa, wadda ta riga Mummy tafiya ɗazu.
Wai takawa ya turo shi ya ɗauke ni daga makaranta, na ce ba zan hau motarsa ya kashe ni ba, dan na san haushina yake ji, saboda takawa bai auri ƙanwarsa ba, wai ni zai yi wa dabara, a gabana fa ya yi wa papan wulaƙanci, wai an sace ƙanwarsa bai gaya masa ba, shi a wa? Sai ka ce son anty aishar suke yi".
Iman ta ce "Ke dai kawai ki ce, an taɓa miki miji kin ji haushi. In dai yaya jamil ne sun saba, faɗa da takawa kuma daga baya su zo su shirya. Amma duk da haka na yi mamakin yadda ki ka iya kawo, yaya Mahmud sashen nan, ba ya son ammi da abun da ya shafe ta, balle adam. Lokaci na ƙarshe da ya zo, shi ne lokacin da aka fasa aurena, saboda rashin asali, ammi ta roƙe shi ya aureni, har da kukanta, ya ce ba ya so na, ba zai aureni ba". Ta yi maganar hawaye fal idonta.
Rumaisa ta yi shiru, ta ce "Wane irin abu ne wannan kuma? To duk saboda me? Ban gane ba ki da asali ba"
Iman ta share hawayen da ya zubo mata, ta ce "Zan yi miki bayani, yanzu mu cigaba da addu'a papan mimi ya warke" ta yi maganar cikin ƙarfin hali tana murmushi.
"Shikenan, ara mini wayarki, na kira gida na gaya musu papa ba lafiya".
Iman ta ce "Amma idan mai sunan baba zaki kira, ki yi masa magana ta what's app, ya hana ni kiransa a waya".
Ruma ta ce "Au kuna waya ne dama?" Ta yi maganar tana dariya.
Da sauri Iman ta ce "A'a, ba waya muke yi ba, ke ce da ki ka kira rannan bai ɗaga ba".
Ruma ta yi dariya ta ce "Buɗe mini data mu yi magana da shi".
Iman ta karɓa ta kunna mata data, ta ba ta, yaya umar ta ga iman ta yi saving number.
Ruma ba ta ce komai ba, ta yi masa voice message "Mai sunan baba, ni ce, ka gaya wa mama mijina ba shi da lafiya, mu na gidan ammi, idan ka ga message ɗin dan Allah ka yi mini magana, rumaisa ce".
Iman ta zare ido ta ce "Ba kya jin kunya, ki ke cewa ace da ammi mijinki babu lafiya"
Rumaisa ta miƙe tsaye ta ce "To me zan ce? Ai maman ma mijina take ce masa, bari na je na gani ko ya tashi, idan mai sunan baba ya yi magana, sai ki kira ni" ta fita daga ɗakin, ta tafi na ammi.
Ammi ba ta ɗakin, ta tarar da adam a zaune, sai dai ta ga samha a zaune a gefen sa, da flask ɗin abinci.
Wani abu ne mai nauyi, ya daki zuciyar rumaisa, da ba za ta iya tantance ko menene ba.
Iman kuwa ta cigaba da chatting ɗin ta, sai ga video call na mai sunan baba.
Gudun kar ta yi laifi, kan ta kai wa ruma wayar ta katse, ya sanya ta ɗaga, gabanta ya na faɗuwa.
Maimakon ya ga rumaisa, ya ga kyakywar fuskar iman, ta bayyana a kan screen ɗin wayarsa.
Ta ɗan sunkuyar da kai ta ce "Barka da yamma yaya umar"
Sunkuyar da kanta da ta yi ne, ya bashi damar ƙare mata kallo, ya na jin releif na abun da yake damun ruhinsa.
Ayshercool
08081012143
What's app only please, ban da kira please 🙏.
₦500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank.
Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Susbcribe my YouTube channel please 🙏
Jin shirun ya yi yawa, sai da ta yi zaton, ko wayar ya katse, ta sake ɗaga kanta, ta ce "Ina wuni yaya umar?".
Wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke, ya ce "Lafiya ƙalau, ya mutan gidan?".
Cikin jin daɗi ta ce "Suna nan lafiya, ya mama da su Yaya Aliyu"
"Lafiya ƙalau, na ga message ɗin wannan Yarinyar ne, na mijinta ba shi da lafiya". Yayi maganar yana sake fatan iman ta ɗago kanta ya kalleta, ko ya cigaba da jin nutsuwa a zuciyarsa.
Ba tare da ta ɗago ɗin ba ta ce "Eh, ba shi da lafiya, su na gida ita da shi".
"Za su koma gidansu yau ne, ko su na nan?"
"Wallahi yaya ban sani ba, amma dai ba na tunanin su koma yau, bari na kai mata wayar, yanzun nan ta tashi".
"No ƙyaleta, idan ta dawo ki ce mu na yi masa sannu, Allah ya bashi lafiya, a gaida sabir".
Murmushi ta yi ta ɗan ɗago ta ce "To in sha Allah zan gaya musu, mun gode sosai".
"Zan shigo zuwa an jima, sai na duba shi".
"To yaya umar, Allah ya kawo ka lafiya"
Ji yake tamkar kar ya katse wayar, wata irin narkewa zuciyarsa take yi, da jin iya muryarta kawai. Mussman idan ta kira shi da yaya umar, ji yake tamkar ta fi kowa iya faɗar sunan.
Kamar wanda aka yi wa dole, haka ya kaste kiran wayar, ya lumshe idonsa ya na haki, ya na gazgata zuciyarsa da babu tantama wannan shi ne so.
Girgiza kansa ya yi ya ce "Ya salam, why? Why? Abun da ban taɓa yi ba, ni ko shirin aure ba ni da shi, ina zaman zamana meya aikeni" ya tambayi kansa. Gashi Abubakar ne abokin hirar sa, Abubakar baya nan, kuma duk da haka ma, ya san idan ya gaya masa dariya zai ta yi masa, abun da ba ya so, dan haka yake jin, zai iya jure koma menene.
A ƙasan zuciyarsa ya ji kamar dama ce, da zai yi amfani da zuwa duba Adam, ko zai samu ya ga iman.
Rumaisa kuwa, takawa ya ga reaction ɗin ta, ta ƙarasa wurinsa ta ce masa "Wai dama ka tashi, ina ammin?".
"Ta fita ita da Nusaiba" ya bata amsa.
Ta je ta zauna a kusa da shi, ta ce "To meyasa baka ce a kirawo ni ka tashi ba?"
"To yanzu ba ga shi kin zo na tashi ba".
"Ammi zan mutu, ki zuba mini ruwan sanyi, idan mutuwa ce hutu a gareni Allah ya sa na mutu, to ba in da za ka mutu ka tafi, sai na gama makaranta mai lilo" ta yi maganar farko tana kwaikwayon sa.
Murmushi ya yi, da sai da haƙoransa suka bayyana, ya ce "Rashin lafiyar ta wa ce, ta zama abun tsokana kuma".
"Wane irin wulaƙanci ne, ina magana da ɗan uwana zaki zo ki zauna ki na wasu surutan banza?"
Rumaisa ta kalli Samha ta ce "Au dama ɗan uwanku ne? To ni kuma ƙarewar ƴan uwantaka gidansa a kai ni na zauna, ke meyasa ba a kai ki ba? Me ɗan uwa?"
"Shut up" yayi maganar yana matse mata baki.
"To ina ruwanta da ni, ba bu kyau wata ta kula mijin wata ba?" Kallonta kawai yake yi.
"To ina ruwana. ka ci abinci ne?"
Ya numfasa ya ce"Ammi ta bani, tun da tafiyarki ki ka yi, ki ka barni".
Ɗan shiru samha ta yi, abun da take gani yanzu, ya sha ban-ban da wanda baba uwani take gaya mata, ƙarya take yi mata kenan ko kuwa? Ta ce mata ba sa wani jituwa, amma alamu sun nuna mata, kamar shaƙuwa a tsakanin su, babban tashin hankalin ta da fatanta, Allah ya sa wani abu bai taɓa faruwa tsakanin su ba, ta kuma fuskanci rumaisan tantiriyar fitsararriya ce.
Ruma ta ce "To yanzu ya ka ke ji, da sauƙi jikin?"
"Eh, Alhamdilillah"
"To sannu, ka tashi mu tafi gida"
Adam ya ce "Mu je gida ki yi yaya da ni, ba iya jinyata za ki yi ba"
Miƙewa Samha ta yi, ta fice zuciyarta na zafi, a gabanta adam ya sakarwa wannan shegiyar yarinyar baki, wata banza da ita mara aji, balle mamora.
"Kuma duk mai kula mijin wata, ɗan wuta ne, kuma sai ya daina magana" ta yi maganar cikin ɗaga murya.
Samha ba ta ko juyo ba, ta yi gaba tana ƙwafa, ba dan Adam ya auri rumaisa ba, da duk hakan ba ta faru ba, ta ɗora zargin komai a kan sa, kuma ya kasa tsawatar mata.
Samha na fita, ya rungumo rumaisa jikinsa, tare da kwantar da kansa a jikin na ta.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, meye haka kuma, dan Allah ka cikani"
Bai ce uffan ba, ya ƙara lafewa, yana sauke numfashi.
Shiru ta yi, ba ta kuma ko motsawa ba, ta na jin bugun zuciyarsa a jikinta.
"Ita ma haka ka yi mata ko?"
"Ita wa?"
"Wannan matar da ta fita yanzu".
"Eh, tun da ba kya jin magana, ba zaki saita bakinki ba, idan ta zaneki shikenan" ya sake rungumeta sosai.
Cikin tsoro ta ce "Ba kyau fa"
Yayi ƴar guntuwar dariya, yanzu abubuwanta sun daina bashi haushi, akwai wayo wasu lokutan, wasu lokutan kuwa kanta a kwano yake, gashi dai ta fara girma, amma kamar ba mutum ba, har mamaki take bashi".
Ya kalleta ya ce "Wani alƙawarin ki ka yi wa fulani?"
Ta numfasa ta ce "Ba yanzu zan faɗa ba. Kuma gaskiya ka ɗagani, ka yi mini nauyi, na ji da matsar hannun da ka din ga yi mini ɗazu, ƙasusuwana sai ciwo suke yi".
Bai ɗagata ba, ya kwanta sosai a kan cinyarta, ya lumshe idanunsa.
***
A fusace Jamil yake sosai, ya dubi Jabir ya ce "Jabir, har ni wannan Yarinyar za ta yi wa fitsara, wai ba son fulani muke ba, kenan adam zuwa ya yi yana ɓata mu a wurinta, abun da ya wuce ba ya riga ya wuce ba? Shikenan ba ni da zarafin bincike a kan ƴar uwata, ni da a tunanina, na lallaɓata na samu wani abun daga bakinta, yadda ka san na harbeta na huta, ka ga iskancin da ta din ga yi mini?"
Jabir ya ce "Wai kai da na gaya maka halinta baka yadda ba? Kai ka ga zaryar da jami'an tsaro suka din ga yi tana asibiti, amma ta ƙi magana, sai da aka kai ruwa rana, sannan ta yi".
"Ni anya ba fulanin ce ta gaya mata wani abun ba?"
Jabir ya ce "Ba tabbas, ka san halin Aisha bana tunanin ita ce, bari dai a yi sallar magariba, zan shiga na duba shi"
"Ka dai yi a hankali, ciwon nan nasa ne, ya tashi, ka san kuma shaƙe mutane yake yi".
Jabir yayi murmushi bai kuma cewa komai ba.
Tamkar mai comedy, haka rumaisa take ta zuba, tana yi wa Adam shirme samfur -samfur.
Can kuma ta ce "Tashi, in ɗauko maka filo, cimyata ta gaji, zan kuma je kitchen in yi girki".
Gyara kwanciyarsa ya yi ya ce "Ina jin releif a haka, ba zan tashi ba"
"Gaskiya cinyata ta gaji, duk jikina ya yi tsami".
"Mimi"
"Na'am basarake"
"Meyasa ki ka faɗi maganar ɗazu?"
Ta ɗan yi jimm, sannan ta ce "Wacce?".
"A kan Mummy, kar ki sake makamanciyar wannan maganar,Idan maganar ta koma kunnenta fa? Zaki iya haddasa rigima, babu ruwanki da irin wannan abubuwan kin ji ko?".
Ta numfasa ta ce "Waye zai je ya gaya mata, ni fa ba ƙarya nake yi ba, wata mata na gani tare da ita, gaba ɗaya ba kalar mutane ba, kuma da za ta tafi ta tashi ta bita k....."
Ya katseta ta hanyar cewa "Wannan matar tun ina da shekara bakwai a duniya nake ganinta, take azabtar da ni, ko ta ɗaure ni tamau da sarƙa, ko ta din ga dukana da sarƙar, na yi mamaki da ka ce ki na ganinta, ban taɓa gaya wa kowa ina ganin ta ba. Rumaisa wannan shi ne ainihin adam, kin ga abun da na din ga yi jiya, kamar mahaukaci, dan ma na daina duka da cizo kamar maye, zaki iya cigaba da zama da ni a haka, abokiyar gaba?"
Ga tausayi ya bata, amma hakan bai hanata yin dariya ba, ta ce "I tuntuni na sani, baba uwani ce ta gaya mini, idan ranka ya ɓaci ka na komawa kamar mahaukaci, har yaya Abubakar aka gayawa, kan ka aureni, wai kai maye ne. Sanan ban manta ba, kuma ina nan a kan baka na. Ai sai yanzu na gane ka na da ɗan kirki kaɗan, kar ka mutu sai na gama makaranta mai lilo"
Shiru ya yi jikinsa a sanyaye "Ba ki damu da ni ba sai lilo ko?".
"Kai fa ka gama addu'a ka mutu, kana mutuwa zan koma gida, idan na ƙara girma na auri Yaya Mahmud" ƙuri ya yi mata da ido, sai kuma ya tashi daga kan cinyarta ya koma kan gado ya kwanta.
Ita kuwa madigar ko a jikinta ta yi nata wuri, dama ba ta son zaman wuri ɗaya.
Abun da ya tsaye masa a rai bai wuce, yadda rumaisa ta ce Baba uwani ce ta gaya mata, ya na komawa kamar mahaukaci ba, sai ya ji kimar dattijuwar ta ragu a idonsa, sai kuma abun da rumaisa ta faɗa na ƙarshe bai yi masa daɗi ba.
***
Tamkar ya janyo dare, haka yake ji, ƙasan zuciyarsa ya na fatan idan ya je gidan ya ga Iman.
Iman ma sai kaiwa take ta na komowa, ta na fatan Allah ya sa mai sunan baba ya zo.
Ammi kuwa da ta dawo, zuwa ta yi aka yi wa adam tofi, wurin malamin da take sawa ya na yi masa, ta karɓo masa, sai dai ta bar shi ya ɗan farfaɗo har da fara'a ta dawo ta tarar da shi sai a hankali.
Sai ta yi zaton kawai jikin ne.
Haka nan iman ta tsinci kanta da yin kwalliya cikin doguwar riga, har ammi ta na tsokanarta, ko siriki za ta kawo mata.
Ta na nan zaune a falo, ta na danna waya, Sabir sai wasan sa yake yi a tsakar falon, gefe rumaisa ta na cin abinci, dan ba ta kuma komawa wurin takawa ba.
Jabir ne ya yi sallama, duk suka amsa masa, ya shigo cikin fara'a, "Autar Ammi da sirikar Ammi, Barkanmu da wannan lokaci"
Ba yabo ba fallasa, Iman ta amsa masa, rumaisa kuwa ta share shi.
"Ina takawan yake ne?" Iman ta nuna masa sashin Ammi, ya ɗan tsaya ya kalli Iman ya ce "Bari in shiga in fito, zamu yi magana dear, kin yi kyau masha Allah"
Iman ta yi masa shiru, rumaisa kuwa ta kwaɓe baki.
Ya na shiga ciki, message ya shigo wayar iman "Na zo" message ɗin mai sunan baba.
Da sauri ta tashi ta yi waje, a harabar gidan ta tarar da mai sunan baba, a cikin ƙanan kaya yake, amma yayi kyau sosai da sosai.
Sai da ta furta Masha Allah, a hankali.
Unexpectedly ya ɗaga kai ya ga Iman, cikin zazzaƙar