Showing 186001 words to 189000 words out of 206906 words

Chapter 63 - Kanwar Maza Book 2 Complete By Aishacool .docx

12 Dec 2025

32841

/>
Yayi murmushi ya ce "Shikenan, but i already fall for you, ni ina son ki sosai rumaisa i love you, and i will surely keep loving you, to my last breath. Ina son ki rumaisa".

Ji ta yi tsigar jikinta na tashi, kalamansa na ratsa ko ina na jikinta, har wani lumshe ido take yi saboda daɗin kalamansa.

Ta yi ajiyar zuciya ta sake cewa "Papa, jaridar da suke wallafa ci maka mutunci, lokacin da anty aisha ta rasu, Yasir ya bi diddigin gidan jaridar, daddyna ya gano wakili ne suke ɗaukar nauyinsa, dan ya ce mini sun taɓa kiransa har aka nemi ya bayar da haɗin kan cutar da kai, ya ce ba ruwansa. Kaga dole a cikin family ba za a rasa wanda suka haɗa kai da shi ba, ake cutar da kai"

Ya lumshe idanunsa ya ce "Mimi kaina ya daina ɗaukar wannan abubuwan ma, bari na samu nutsuwa"

"Idan ka samu nutsuwar, ka yi bincike sosai a cikin gida. Sannan ka sani tun a yanzu ka sanya wa ranka cewar, zaka iya gano su waye, amma samun hukunci da adalci sai a wurin Allah, amma ba a wannan ƙasar ba"

Ya numfasa ya ce "Ina sauraren Bashir ne, na ji me za su ce mini, nayi magana da su barrister ma, waɗan da ki ka ce mini kin yarda da su, muna kan faɗaɗa bincike"

"Nima ni da ƴan team ɗina muna ta ƙoƙari, Allah ya yi mana jagora" ya jinjina kai ba tare da iya yin magana ba.

Abu kamar wasa mai sunan baba yake ta ƙoƙari akan kayan Alhaji Aminu ɗan fulani, kuma kasancewar an samu sauye-sauye a wurin, cikin ikon Allah komai ya zo masa da sauƙi, dan ana daf da releasing ɗin kayan.

Alhaji Aminu yana yawan kiran sa, su gaisa, shi kuma mai sunan baba, sai ya tambaye shi ina Ade, ya ce masa tana nan tana rigima.

Alhaji Aminu ya matsawa mai sunan baba, a kan lallai ya zo gidansa su gaisa, dan yana bawa Ade labarin sa, ita kuma ta ce tana son ganin sa.

Mai sunan baba ya ji a ransa yana son sanin ahalin Alhaji Aminu, ko zai samu abun da yake son tabattarwa, ko Alhaji Aminu yana da alaƙa da Iman.

***

Tamkar za su kacame da dambe, haka suke musayar yawu, tamkar ba aminan da suka kwashi shekaru suna cin mushe ba, tamkar ba tare suke ƙullawa da kitsa duk wani hatsabibanci ba.

Mummy tamkar za ta ari baki, saboda haƙilo da bala'i.

Hajiya Lubabatu a fusace ta kira Jabir a waya, a kan lallai ya zo tana son ganinsa, ta ajiye wayar ta kalli hajiya jamila ta ce "Kar ki sake kiran ɗa na da mazinaci ɗan iska, idan ma hakan ne, sai ki ce mazinata ƴan iska".

"Na faɗa ɗin, koda yake barewa ba ta gudu ɗan ta yayi rarrafe ba, tun da sai da ki ka yi yawon tazubar ki ka gama ki ka tuba aka yi auren. Kin yi wa mijinki asiri, kin ya da shi a Germany, kin cigaba da watsewa a gefe, ke ki yi ɗan ki yayi".

"Jamila kina nufin ni ce nake biye² ni zaki yi wa sharri? Ko kin manta kema irin abubuwan da ki ka shuka, yayan giwa da ki ka din ga sadaukarwa, da ƴaƴan Adam, ai ni ban kai ga aikata kisan kai kamar ke ba"

Jabir ne yayi sallama, suka yi shiru suka waiwaya.

"Sannu munafukin Allah ta'ala"

Jabir ya ce "Mummy lafiya kuwa?"

Mummy ta ce "Saboda kai watsatstse ne, mara mutunci, na amince maka na amincewa uwarka, amma ku ka zalince ni, wace irin alaƙa ce tsakanin da ruƙayya har ka ke iƙirarin yaɗa hotunanta?"

Yayi shiru yana kallon Mummy.

"Wallahi lubabatu sai kun yi dana sanin abun da ku ka aikata mini, kai ba da ni ka ke zancen, dabba ɗan akuya".

"Kar ki sake kiransa ɗan akuya, ruƙayya ce babbar akuyar da ba ta san ciwon kanta ba"

Mummy kawai ta fice, zuciyarta na wani irin zafi, kuka take son yi amma ba ta son bayyana karayarta a fili.

***

Mai sunan baba ya amsawa Alhaji Aminu cewar zai kai masa ziyara ya gaida Ade, sai dai yana fargabar kar ya ga abun da bai yi tsammanni ba, zai fi kowa farin ciki, idan aka ce a sanadinsa Iman ta samu ko wani ne a danginta, duk da rashin hakan ba ya nufin zai juya mata baya ne.

Kiran Iman yake yi yana zancen zuci, ta ɗaga video call ɗin ta ce "Hi dear"

"My yellow, how are you?"

"Fine Alhamdilillah, ya aiki?"

"Ai akwai shi, yanzu salary ya shigo, na ce let me call the person close to my heart"

Tayi murmushi ta ce "Alhamdilillah ala kulli halin, mun godewa Allah" kallonta yake sake yi, hatta yanayin gashin girar iman, irin na Alhaji Aminu ne.

"Ya naga kana kallona ne, na canza ne?"

"Bakomai, yanzu ya za ayi da salaryn nan ne?"

Iman ta ce "Ai zaka shigo kano ko? Ka ce fa ƙarshen wata zaka zo".

Ya ce "Eh, ranar Alhamis zan shigo"

Ta ce "To Allah ya kaimu, idan ka zo sai ayi shawara, ka turawa mama dubu ɗari a sai mata abun da take so kan ka zo na neman albarka".

Ya ce "To ƴar mama, za ayi in sha Allah, zan cigaba da waya, zamu yi magana anjima"

Ya ajiye wayar yayi shiru, yana cigaba da fatan Allah ya sa Alhaji Aminu yana da alaƙa da Iman.

Har gida Alhaji Aminu ya aika da direba, aka ɗaukko mai sunan baba, yana da matuƙar karamci da son mutane, kamar ya goya mai sunan baba da ya ganshi a gidansa.

Aljannar duniya, an kashe dukiya an zuba kayan alatu a gidan nan, kamar ba za a mutu ba, karen da yake gadin gidan kuwa bayan mai gadi, shi kansa ba na Nigeria bane ba.

Ga iyayen motoci a parking space.

Ya ce wa mai sunan baba "Mu je ka fara ganin Ade, ka gaya mata ta haƙura da tafiya ƙauye ko Allah ya sa ta yarda".

Tsohuwa ce, a ƙalla zata shekara tamanin da biyar, tana zaune a ƙasan carfet, tana shan fura, sai mita take da fulatanci ita da jikokinta.

Ta ɗaga kai ta ƙure mai sunan baba da ido, har ya ƙarasa gabanta ya zauna.

"Ade, ga wanda yake ta yi mini ƙoƙari a kan kayana, shi ya ce a baki haƙuri, dan Allah kar ki koma ƙauye".

"Au jibo gulmata ka ke yi kana yamaɗiɗi da ni kenan, yaro na bar shanu da dabbobina a ƙauye, an zo nan ƙwam an ajiyeni, sanyi na neman yi mini illa, ga wannan yaran da suka addabe ni, ai zaman ƙauye yafi daɗi".

Mai sunan baba ko rantsuwa yayi ba zai yi kaffara ba, wannan matar na da alaƙa da matarsa, duk da tsufanta, tsananin kammaninta da iman ba su ɓuya ba, sai a yanzu ma ya ga Iman ba kama take da Alhaji Aminu ba.

Ade ba ruwanta, ta din ga zuba tana bashi labarin yadda take son shanunta, tun da a cikinsu aka haifeta.

Kayan marmarin da ya zo da su, ya din ga ɗauka yana ɓarewa yana bata, tana karɓa tana ci.

Ta ce "Kaga yadda ka ke yi mini ɗin nan, shi ba ya yi mini, kullum cikin rubutu yake da lissafin kuɗi, Euro ya leƙo mun gaisa, sai ya kama hanya ya tafi yawonsa"

Alhaji Aminu ya ce "Sai ka ce a ƙauyen hakan suke yi miki"

"Eh amma dai idan na ga nagge, zuciyana na sanyi sosai"

"Yallaɓai kai baka da ƴan uwana ne?"

Alhaji Aminu ya ce "Kowa ya kama gabansa, ka san ainihi daman mu fulanin tashi ne. To ƴan uwan nawa galibi wasu suna wasu garuruwan, wasu ma wasu ƙasashen. Ni ne ɗan autan ta, ƙauyen fa a gidan wani ƙaninta take, wai an rabata da ɗan uwanta, kamar ɗan uwanta ya fimu"

"Ya fika mana, shi yana zama mu yi hira, kai sai shegen son kuɗin tsiya".

"Ni zaki tozarta a gaban baƙo ko, saboda ya baki ayaba, da lemo, to yasin a daina yin ƙosai a gidan nan, tun da ba kya so na"

Alhaji Aminu kamar kakarsa ya ɗauki Ade, su yi ta faɗa wasu lokutan, saboda shi ne ƙaramin ɗan ta.

Mai sunan baba ya ɗan jima a gidan, sannan baba ya ce zai tafi, Ade ta din ga tambayarsa yaushe zai dawo, idan bai dawo ba, za ta ƙulle takalmanta a zaninta, ko ta katanga ta bi, ta gudu ta koma ƙauye.

Mai sunan baba ya ce "Ai ba za ayi haka ba"

"Ka rabu da ita, karen nan zan kawo ɗakinta na ɗaure, na ga ta wurin fita"

Ta galla masa harara ta ce "Tashi ke je ɗakina, ka samo masa ɗan biskit ɗin nan"

Alhaji Aminu ya ce "Biskit kuma? Ade kyautar nagge zaki bashi, me zai yi da wani biskit"

Mai sunan baba ya ga ƙoƙarin ta ma, rikicin taufan na ta ba na zage² bane ba.

Mai sunan baba har ya koma gidan da yake, yana al'ajabi, kuma ya yanke shawarar zai yi wa Mahmud zancen, koma ya zo lagos ɗin, ya je su ganewa idonsu, su san ta in da za a ɓullowa lamarin.

Dan baya son yayi gaggawa, a zo a gane cewar ba su da wata alaƙa.

***

Ammi ta kasa mantawa da matsananciyar cin amanar da babu uwani ta yi mata, har ta kai ba ta iya sakin jiki tayi magana a gaban kowa yanzu, saboda tsoro da tunanin kowa ma ba son ta yake yi tsakani da Allah ba.

Ranar da mai sunan baba zai koma, Iman gyara kala-kala, aka ƙalƙale ko ina, ta shirya girke² ta sha kwalliya.

Dama har kirari yake yi mata da ɗawisu sarkin ado, Iman akwai ado da kwalliya.

Sosai suka yi missing ɗin juna ita da shi, sai dai da ya kalleta, Alhaji Aminu yake tunawa da mahaifiyar sa.

Ya din ga jin tamkar yayi mata zancen, amma ya kasa.

Washegarin dawowarsa, da yamma ya shirya su ka yi wa mama siyayya, suka je gida gaisheta.

Mama tayi ta yi masa faɗa a kan yanzu yana da iyali, yakamata ya mayar da hankali a kan gidansa, ƴan samarinta sun ɗauke mata komai, kuma dubu ɗarin ma da ya turo tayi yawa, jiransa take yi ya dawo dama.

Ya ce "Ni fa ba ruwana, ƴar ki ce ta ce ayi haka"

Mama ta ce "Kuma sai ka biye mata?"

Iman ta ce "Mama idan bamu yi muku ba, wa muke da shi? Ayi ta saka mana albarka kawai".

Mama ta ce "Albarka da addu'a kullum cikin su muke, amma dan mun haifeku ba ya nufin, mu takura rayuwarku, ina fatan dai kun je wurin hajiyar?"

Iman ta ce "Gobe in Allah ya kaimu za mu je ammi, a can zan wuni, shekaranjiya na koma gida, idan na kuma zuwa faɗa za ta yi mini".

Mama ta ce "Ai faɗan na gyara ne, mun kai ku ɗaki amma kullum ku ba kwa gajiya da zuwa gida"

Iman ta yi dariya ta ce "Mama kenan".

Kasancewar umar akwai kyauta, haka ya din ga bayar da kuɗi, ga bikin Abubakar saura wata ɗaya kacal ya rage.

Mai sunan baba suka yi waya da Mahmud, ya tabbatar masa da shima zai shigo kano, dan haka umar ya ce idan ya shigo yana son su haɗu za su yi magana.

Nusaiba har ta shirya tafiya makaranta, sun yi sallama da ammi, ammi tana ta fama Sabir, ya isheta da fitina, tana ta mita ta ce makaranta za a kai mata shi, ta huta.

Barira tana mata dariya ta ce "Anya ranki ya daɗe, kin hana mamansa shi ma balle kai shi makaranta, idan aka kai shi, sai kin fi kowa damuwa"

"A'a ba wata damuwa gara a kai shi, tun da yayi baki"

"Ammi, ammi" Nusaiba ta shigo tana ƙwalawa ammi kira.

"Lafiya baki tafi makarantar ba?"

"Ammi wai yaya Mahmud ne ya dawo shekranjiya, wai ya je har gida ya yi wa Jabir dukan tsiya, ta ƙarfin tsiya ya saka shi a mota a fita da shi, ya kai shi ofishin ƴan sanda an rufe shi. Yau shi kuma ya wayi gari da ciwon ciki, a asibiti ma ya kwana bai san waye a kansa ba".

Ayshercool

08081012143

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*

*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*

*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1.  Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2.   Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3.  Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4.  Supplements na karawa fata kyau da sheki  glowing skin*

*5.   Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6.   Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7.   Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8.  Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9.  Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10.  Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11.  Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12.  Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13.  Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*

*14.  Supplement na whitening/glowing skin*

*15.  Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please 🙏

*TALLA! TALLA!! TALLA!!!

*ƊANƊANO DAGA LITTAFIN NAZEEFA SABO NASHE, MAI SUNA ƘUDURAR ALLAH*

Ta Yaya zai zama jinina alhali ni na san bayan matana ban tab’a kusantar wata mace ba?” Ya furta kai tsaye yana kallon likitan da sakamakon gwajin yake hannunsa. Likitan yana jinjina kai ya sake furta “Tabbas Jaheed jininka don gwajin k’wayar halittarku da komai ya tabbatar kai ne mahaifinsa kafin a kai ga haka ma ko Kamanninku da suka zamo kwabo da kwabo sun tabbatar da Hakan koda Ba’a yi gwajin ba.”

Shiru na tsawon lokaci d’akin ya d’auka kowa da irin tunanin da yake a ransa ya kasa yarjewa zuciyarsa shine Mahaifin Jaheed duk da k’wararan shaidu. Abinda ya sani ko da wasa bayan matansa na aure na Sunna bai tab’a rik’ewa wata mace hannu ba, idan kuwa ya tabbata Jaheed d’ansa ne ta yaya ya samar da cikin nasa a jikin wacce aka kira mahaifiyarsa da ko a mafarki bai tab’a ganin mai kama da ita ba TABBAS AKWAI LAUJE CIKIN NAD’i. Mahaifiyar Jaheed ma Zata iya zama abar tuhuma da zargi.  Kai tsaye zai iya cewa hakan zai iya zama K’UDIRAR ALLAH….

(*Ina ma'abota karance-karancen litatafan hausa, na san kun santa, Nazeefa sabo nashe, tsohuwar marubuciya, da ta saba nishaɗantar da ku, da ɗaɗan litatafan hausa masu ma'ana da ilimantarwa, ya kuke tunanin wannan turka-turka, DNA ɗin sa ya kasance daidai da na yaron da bai taɓa ganin mahaifiyarsa ba, haka zalika a iya saninsa tun daga ƙuruciya har girmansa, bai taɓa aikata zina ba? Ku kasance da Nazeefa sabo nashe, dan jin yadda zata warware wannan turka-turka a cikin littafin ƙudurar Allah. Masu buƙata kai tsaye za su iya tuntuɓar ta a kan lambar wayarta 08033748387*)

*Littafin kuɗi ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143*

Miƙewa Ammi ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0