Showing 15001 words to 18000 words out of 19933 words

Chapter 6 - Sanadin Boko 3 Complete by Halima k Mashi .pdf

umar yace "Ehh don shigarsu dakin ne yAya
umar ya fita shi da shadad sai yanzu suka dawo. ya
shiga da sallama jikin sagr ya nufa yana me fadin Uncle
ina antyna? sagr yace tana gda. munir ya tsurama
yaron ido,gabanshi yana wata irn faduwa ya bi yaron da
ido lkcn da yaron ya fita a guje. tamkar ya cafko yaron
yakeji don ya sake kallonshi da kyau,ko kuma duk cikn
firgicin ganin hafsa din ne? ya mike cikin tashin
hnkali,yace to Hashim Allah yasanya alkhairi, nizan tafi.
Hashim yace da sauri? munir yace em inada dan wani
uzurine, suna fita yi masa rakiya sai waiwaye2 yake,ya
shiga motarsa ya tada tafe yake yana zantuka shi
kadai, tmbayr kansa yake" shon wannan yaron mai
matukar kama da shi dan hafsa ne? cikin sane kenan
ta haifa?a fili yace lallai zan amshi dana dubi yanda
kaunarsa ta zirga ckin jinina,amma kuma.... ya doki kan
styarin motar tare da cwa tab nasan za'ayi
rigima,yanxun wama zan tunkara da wannan magnar?
tunda iyayena ba wanda yasan zancen? ko gdansa
yakasa zaune da tsaye,duk ya damu gashi badama ya
fadawa matarsa. sai dai ya yanke shawarar dadynsu da
zancen, Nikam ban da tursasawar Rahma bazan yi wani
lalle ba,amma haka tasa sakinarmu da ummi suka
nemo mai zanen fulawa ta yarfa min a hannuwa. tasiyo
man shamfo sbd anwuce da akwatunana (lefa) dama
kayan dangi daban suka kawo wai suddaje. don haka
ba'a taba nawa ba,tayi min don tayi tayi nace bazani
saloon ba, na manta da wani abn takaicin da rahma
tamini tarkacen mata ne wai sai nasha.
Nace matama gwara takwashe tarkacenta inba hakaba
zatayi asarar kudinta, don zubarwa zayi, tace gashinan
cikin jakata in naso naje nazubar, inkuma na shirya sha
to inkirata taimin bayani yadda ake amfani dasu, nace
kanki akeji, gdan yaya umar mukaje kwana, sam na
kasa bacci, gaskia bansoba naga munnir sai naji nakara
tsanar maza, Allah ya sani indai dan'uwan abkr ne toba
zan zauna cikin zuri'arsuba, ke amarya tashin manta
doguwar tafia ke garemu? Wanka kawai nayi don ina
fashin sallah, na kintsa jikina sosai muka fita tare dasu
ya umar, ummi da matar ya umar duk tare zamu tafi
dasu, dangin inna duk tare muka tafi dasu, nida
sakeena da rahma a motar hashim da sagir, harda
shadad aka tafi, lallai yola akwai nisa, tun muna tafia

ina hira har nai bacci dan bantaba doguwar tafia irin
hakaba, bamu isaba sai gaf da magrib, tunda karfe 6 na
safe, kuma wai haka dinma sai naji ana cewa munyi
sauri, dankareren gate ne muka dosa, sai kace na gdan
yari, muna shiga gdan dam da mutane haske ko'ina,
mayafi naja na rufe fuskata, lkcn naji gdan yadauki
guda anata fadin gasu nan sun iso, rahma ce take
rungume dani, har zuwa kofar shiga tace, kishiga da
kafar dama kiyi addu'a, hakan nayi, sannan aka zarce
dani can dakin, nan da nan zugar dangin suka cika
falon, har dakin da nake, sai fillanci ke tashi,
daidaikune suke mgn da hausa irin wadda bata goge
din nanba. wata ta duko kaina, amarya bude fuskarki
muganki, ke kam wane irin kyaune dake har hamma
yafita hayyacinsa danke? Na sake sunne kaina cikin
cinyoyina, wata tace, nana ke kam baki ganta acikin
hotunan kalanda ba? Tace nagani, sonake inganta afili,
rahma tace, sai kingaji da ganinta, tunda nan zamu bar
muku ita, ankawo kulolin abinci, shinkafa da miya da
nama, sai kunun gyada da sauran drinks, suka dan rage
nan muka shiga cin abinci, nikam wanka na mike zanyi,
bayina acikin dakina yamin kyau, nafito na zura kayan
bacci, sukuma suka shiga sallah, rahma tace, shine
zakisa kayan bacci? Nace ina naga sabon dinki,
tsofaffinma banzo dasuba, na saka katon hijabi, sukuma
cikin daren nan suka hau yin jeren dakina, sun saka
kujeru a falo ina juyosu suna tababa, anan za'asa, anan
zaifi kyau, suka dawo daki suka hada gado, suka dibi
na kicin sukaje suka jera wanda shima kenan falon,
matsayina na yar talaka amma iyayena sunyi kokaro,
suka hau gado suka kwanta nikuma nakwanta kan kafet
dan nasaba da kwanan kasa, rahma tazo kusa dani
takwanta, sai wayarta tashiga ruri, nace to masoya ga
angonki nan, ta fito da wayar tana cewa, yanzun nanfa
muka gama dashi, kurum sai naji tana cewa,
ango_ango, munyi fushima, baka kira ba muna hanya,
mun iso tuni ka sharemu, ina jiyo muryarshi .......


Zaharaddeen shomar
whatsapp 08168575100

Sanadin Boko 3-06
Posted by ANaM Dorayi on 05:57 PM, 28-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
yana cewa, ai munata yin waya dasu sagir, sun tabbar
min kuna lfy, na tabe baki yace, to yaya kuke? Tace lfy,
mungama shirya muku komai, gobe asubanci zamuyi gda,
yace au, kuna nufin baxaku tsaya ayi budan kaiba? Tace
ai mun gama budan kai tunda munkawoma ita.
yace to nawa zan fansheta? Rahma tace mekenan? Nima
na tashi zaune tare da kara matsowa, sannan na kara
kanga kunnena, yace, toni kam bansan yadda zan muku
bayaniba, amma zaifi kyau ku tsaya dan kar kubar mata
abin gori, kunsan halinku dai mata, rahma tace, to zamu
tsaya, sai daifa mu bamusan yanda kuke gabatar da
al'adunkuba, sannan amarya bata da dinkakken kaya,
yace meya hanata dinkawa? Kodai bata shirya aurenaba?
Tunda tun asali bani takesoba? Rahma tace, wannan
batun aiya wuce, don dama bata da wanda takeso,
zuwankane kakoya mata soyyaya, yace rahma kenan! Ai
ina zaton soyyayar da kawarki ta iya niban kai gurinba,
amma dai ya wuce ta bakin naki, sannan kuma za'a
kawo mata kayan sawa, mu nan garin dama haka ake kai
kaya, don amare basa amfani da kayan akwatin sai dai
ayi musu a gidajensu, rahma tace, hali keyin haka,
mukam talakawa irinmu kuwa lefen muke amfani dashi,
ta canza batun da cewa, ina angona? Yace mun saidashi,
tace tabdi! Ba'a kake, da kunga gayyar kanawa, don
Allah yana kusa banishi inji muryarsa kona samu nai
bacci, ya saki daria, na lura kin shagwaba sagir dayawa,
shiyasa yadamemu da tadinki, na sulale a hankali na
kwanta, da alama bata fahimci abinda yake nufiba, suka
gama surutunsu da mijinta sannan sukai sallama da hirar
soyyayarsu, dare ya tsala, kowa na kwasar baccin gajia,
amma niban dani sbd hakikanin gaskia kalaman abkr sun
soki zuciyata, mutsu mutsu nane yatashi rahma, tace a
hankali lfy? Nace rahma mekika fahimta da mgnr abkr?
tace namefa? Na juyo da cewa, yace damacan bashi
nake soba, sannan yace soyayyar dana sani shi baikai
gurinba? Lkcn dakikace zuwanshine ya koyamin soyy,
rahma tace, kinsan nifa bakoda yaushe nake zama
nazarin mgn irin hakaba, amma ke mekika fahimta? Tace
wlh rahma koyaya mutum yai zance nasan meyake nufi,

inada wata baiwa tadaban akan karantar mutum, ko
zolaya yayi ina gane manufarsa, nufin abkr damacan
munnir nakeso bashiba, sannan na iya soyyayar da baikai
gurinba, to sbd soyyaya nasakarwa munnir kaina har na
samu ciki shiko bai taba hakanba, rahma tayi shiru itama
ta fahimta, amma don kada na tashi hankalina agane
inada damuwa sai tace, kada kiyi masa wani zato, ta
yiwu ba nufinsa kenanba, (kai abkr na gasawa hafsa
mgn gaskia, yan'uwa kuja mai kunne mana) nace hum!
Rahma tuni na hararo irin zaman da zamuyi da abkr
shiyasa nake gudun aurena, yanda na fahimci halinsa, shi
mutum ne mai tausayi dason kyauta, sannan mai
jajircewa ne akan abinda yakeso, wanda bai kaucema
addini, sai dai kash! Yanada naci tare da mita idan an
masa laifi, sannan baya bincike bare saurare, kinga
kozansha wuyar zama dashi in nayi la'akari da irin
halayen nan, sannan zai dinga jefamin mgn, hwy suka
soma zubomin tare da sintiri afuskata, Rahma tace, duk
wannan hasashen nakine, don haka kibar mummunan
zato a kanku, kiyi fatan alheri, nace to Allah yaxaba
mana mafi alheri, sai kusan assalatu sannan nasamu
bacci ya daukeni, da safe karin kumallo mai kyau mukayi,
kunun gyadane da lafiyayyen kosai, da kuma kayan tea
gamai muradi.natashi nashiga wanka bayan mungama,
kayan rahma nasaka cikin sabbabin kayanta, rahma tace
bari tadan fita cikin gdan tagani, jim kadan tadawo tace,
wai gaskia babban gdane, gasu da tarin zuri'a, nace
hum! Allah yasa mudace, rahma tace amin, can saiga
wasu yanmata 3, 2 manya, 1 karama, ina zaune bakin
gado suka shigo har ciki, biyun sunyi kama da abkr, duk
yanda akayi kannensane, duk suka tsuramin ido, bayan
mun gaisa, su kuma sai mgn suke cikin fillanci harda
daria, (nidai nagane gulma suke) karamar cikinsu ta
matso kusa dani tana cewa cikin harshen turanci, aunty
sunana ummi, wannan kuma sunanta rukayya, yayatace,
wannan kuma sunanta husna, abokiyar wasanmuce,
dukkanmu kannen hamma ne, nace to sannunku da
zuwa, ta dubi sauran tana sauraron abinda suke cewa,
sai naga tahade rai, sanna itama taci gaba dayi musu
mgn cikin fillancin, abinda nake zargi ni suke kushewa
ita kuma bahaka tasoba, saina samu kaina da tsarguwa,
su 2 suka tashi suka fita suna daria, nace musu sai
anjimanku, sukace to, ita kuma ummy tadawo kusa dani

tazauna, tacemin hammansu yana sona da yawa, dan
Allah na kula dashi, nayi yar daria nace to ngd ummy,
kuma zanbi shawararki, sai naji yarinyar tashiga raina
mai hankalin manya, tace kinyi kyaufa, anjima za'ayi
budan kai nace, ya akeyi? Tace kubakwayine? Nace a'a,
tace yanada kyau, zaku zaunane sai a bude fuskanki
inkin rufe, anayi ana gada, daga nan sai dangi suyi fansa,
nace mekenan? Tace kudine za'ayi ta zuba muku, sai
kuma a kawo faute daga gidan amare, nace shikuma
mene faute? Tace ba ankai muku suddajeba? Na tsura
mata ido, mene suddaje? Tace kayan dangi mana, ba
ankai mukuba? Nace eh, tace toshine suddaje din ai,
nace to menene faute? Ina nufin me akeyi dashi? Tace
kayane su kuloli dasu. Kaya dangin amarya suke badawa
wasuma harda gado sukeyi, nace to, rahma tace in kuma
mutum bai sanibafa? Tace ai duk zuri'armu sun sani,
rahma nace abinda mukeyi acan zamuyi sai mubasu hkr
muce bamusan sunayin hakaba, tace, ai baza'a damuba,
tunda an sani cewa baku saniba, karfe 4 daidai lkcn gdan
yacika dam kidan sarauta ke tashi, kai zuri'ar abkr akwai
kyau, sunata shigowa kallona, ummi taje kiran da abkr
yamata, don tuni sunyi waya yasan cewa tana gdan, ta
shigo dauke da katuwar leda, tace anty canza kaya
donga adda fadi nan sun iso, kuma nasan hamma da
abokanshi ma sunata shiri, shine yace in baki kayan nan,
muka bude nida rahma nace, kila dai a dinken yasiyo,
rahma tace, daga gani don gasunan a ledarsu, nace Allah
yasama to sumin daidai, daya leshine da aka hada da
swis, dayan kuma leshine zalla, sai shadda doguwar riga
taji aiki, sai atamfa, nace toni wanne zan saka? Rahma
tace kisa leshin nan, ummi tace aunty kisa shaddar nan
mana gata ja tunda keba fara bace, zakiyi kyau, nace
rahma duba akwatii akwai takalmi ja cikin kayan can?
Saiga ja takalmi gami da mayafi, ummi tace kiyi amfani
da bakake, kuma hamma yanason jan abu ga mata, don
in zai saya mana zani dole saikaga ja aciki, na sake yo
wanka na zauna gaban madubi nadauki kwalliya, harsu
ummi suna cewa gaskia nai kyau, na saka sarka da
sauran tarkacen karau, suk su rahma da sakina kowa
yayi kwalliya, zuwacan abokan wasansa suka shigo
sunamin tsiya wai in fito, yan'uwana suka takamin baya
muka nufi gurin. Katuwar darduma ce shimfide, tun kafin
mu karaso na hangi hamma sanye da shadda blue mai

kyau da tsada sai sheki take, gefenshi fadima ce wato
kishiyata, tana sanye cikin wani yadi, tsananin kyan
yadin ne yake bayyana tsadarsa, taci gwargwaro, ga
gwala gwalai, gabana ya fadi don kyawunta ya wuce
misali, ina isowa kanshinsu yadaki hancina, duk sai na
jini na zama wata ga daini nan, donko nasan ko a kyau
baxan kama kafa da itaba, muka kalli juna nida ita ido
cikin ido sannan na dauke kaina na zauna, guda ta soma
tashi, sai aka umarcemu da mu rufe fuskokinmu da kyau,
duk muka rufe sai aka kira kannenshi wai su fara bude
uwargda, rukayya ta bude fadi, mai guda tafarayi sannan
danginta suka shiga zuba kudi, daganan saini, ummi ce
ta bude fuskata nima, nima dai dangina sukadan
watsamin abinda ke garesu, bandamu da kudin da aketa
zuba musuba, musamman abkr don al'adace da addiniba,
(inama ni suka bawa kudin nan) can kuma saiga iyayen
fadi sun kawo faute wajen dangin abkr, kayan gado dan
italy na kwali, da kuloli da sauransu, aka shiga sanarwa,
rahma ta duko kusa dani tace ya za'ayi? Nafito musu da
garar nace suma abasu, buhunan shinkafa talia, dasu
dubulan da alkaki da yan samirun damukazo dasu, haka
kuwa sukayi, basuce komaiba da aka basu, rahma tace
suyi hkr bamusan yadda suke abubuwansuba shiyasa,
nan naga anata raba kalandu zuwa jakunkuna da memo
da jota, dadi sauransu, hotuna nake mamakin inda
akasamu nawa, kamar tare muka dauka? To suna nufin
tare muka dauka? Yana tsakiyarmu ya kwanta bayan
fadima, nikuma na kwanta a bayanshi, dukkanmu muna
daria.
ina sanye da jallabiya, al'ajabi ya cikani, sai daf da
magrib aka tashi, muka koma dakina, dama na kosa mu
koma, na janyo daya daga ciki jakunkunan da akaba
dangina nace, yaushe ne har mukai wannan hotunan ni
hafsa? Rahma tai daria tace lkcn daxamuje gdan
kwamishina, idan nace kizo muje baxuwa zakiyiba,
shiyasa nahada baki da mai hotan yamiki baki saniba,
computer kuma tatsara abubuwa, daman fuskarki kawai
muke bukata kuma gashi munsamu, rahma tabude
jakarta tace ga hotunan yanzu kigani, tabani na kalla,
amma nace Allah ya isana amma, nace dubi yanda nayi
acikinsu kamar wata yar aikinsu, badai shine yaji kuma
ya ganiba inji rahma? Nace ga yanmatan nan kannenshi
zasuyi rainin wayo, rahma tace, kedai tsakaninki da kowa

mutunci, nace shima sai wani shareni yake, shiyasama
da ana hotunan nan da danginsu ban cusa kainaba ciki,
nayi zugum ina kallon fadima, kishinta nacin raina, nace
rahma, fadima tana da kyau, ina zaton abkr yafi sonta,
me kamar wannan mezai damu kansa dani kila ya
aurenine don wata manufa, rahma ta mike cewa, saikiyi
kuma, nikinga tafiyata zan sallah, gara ke hutu kike, saiki
zauna kiyi tayi ke kadai, bayan sallar isha'ine aka kawo
mana abinci cikin kuloli, nan aka shiga ci tare da lbrn
karamcin mutanen yola, dan bikin nasu ya burge dangina,
tabbas yola nima zance sunada karamci, ina kwance
tunanin yanzu abkr yanacan tare da matarsa, sai mukaji
sallama, rahma ta amsa, tace rufe fuskarki ga angonki
nan, nace mezaizo yayimin? Rahma tace inya shigo saiki
tambayeshi magulmaciya, koda baki fadaba nasan
tunaninshi kikeyi, nace kada kimin sharri, tunanin me zan
tsayayi? Kafin tace wani abun sun shigo, hashim yace sai
mun sayi bake kenan? Naga amaryar tasha lullubi, rahma
tace dame kake zato? Nan dai sukayi addu'oi tare dayi
mana nasiha, sannan suka mikawa rahma kudi da ledar
kaza, daya daga cikin wadanda bansaniba yace, to tunda
anbiya saiki bude mana fuskarki mugani, nayi musu
shiru, haka nan naki bude fuskar sugani, nayi shiru
sannan suka mike dukkansu, abkr ya dubi rahma, saiku
zama cikin shiri, kunayin sallar asubahi in Allah
yatashemu zaku dauki hanya, tace to, abokan suka fita,
rahma ma tafice, saini saishi, duk mukayi shiru, yana dai
tsaye, yace, inbaki da mgn nizan tafi gurin amaryata,
uwargidanki kenan saida safe, da sauri na dubeshi bayan
na janye mayafin kaina, shima ni yake duba, bansan me
yake zuciyarshiba, nidai tawa zuciyar kishine fal, na
kauda kai cikin takaici nace, to dama akwai wanda yace
ba amaryarka bace? Allah yabamu alheri, na mike tare
da tura kofar toilet na shige, banjin fitsari amma dole
nayishi, don banason tsayawa kusa dashi, dana fito
yatafi, ina jiyosu sunayiwa sauran yan'uwana sallama
afalo, Rahma tashigo, har kunyi sallamar? Nace na lura
bazaki rike mijinki da kyauba, kada dai kimanta cewa ku
2 ne, nace um! Niba shine agabanaba, kuma bazan
wulakanta kainaba, don na lura bana cikin yan kayanshi,
abinda nasani shine, duk zaman daya zaba shi zamuyi,
rahma tace shikenan, in kinyi tunanin yanda zaki kama
mijinki a hannu kya kirani a wayata, tajawo ledar

gabanta, bari mu tayaki cin kajin tunda ba ango, nace ke
ango ya dama, niko ajikina, tace, abakiba, nan tafito da
kaza daya, nace su dauka suka tace a'a, bansan meya
hanani bacci ba wannan dare, alwala na dauro nazo na
duka inata nafila, sai naji raina yayi sanyi harma bacci
yana dibana, kacaniyarsu rahmace ta farkar dani, sunata
shirin tafia, nima na tashi nahau shiri, rahma tace, waike
inazaki naga kina diban kaya cikin karamin akwati? Nace
kano mana, karatuna zanyi wasa dashine? Tace kun
shirya hakan keda mijinki? Nace um! Zancen kikeso.Sai
gasu sun shigo, waisu fito yan kd, nace ni yan kn zanbi,
damasu mama sun tafi da shadad sbd makarntashi, na
zura hijabina, yan gdan sun shigo sunata godia ga yan
kd, tare dayi musu alheri wai inji lamido, turaman
zannuwa ne da kudi na shan ruwa a hanya, har sun shiga
motoci saiga abkr akan mashin ya tuko, yana sanye da
farar jallabiy mai gajeran hannu, dama ina cikin tunanin
watonba zayazo yayi sallama da yan'uwanama, kallo
daya nayi mishi nakau dakai, duk sai naji haushi yake
bani, musamman da zuciyata take rayamin cewa daga
ganinshi yasha amarci, ina kallo shima yaciro kudi ya
mika musu, motarsu tatashi ta nufi gate, na juya nabarsu
nan tsaye dasu rahma, ko karyawa na kasa, duk tsananin
son masa (waina) danakeyi, sagir yana kiran rahma waita
shirya, nima na hau kintsi, rahma sai daria takemin. Can
suka shigo dasu abkr, sai kamshi tare da kyallin goshi
yake, daga ka ganshi ango dai sosai, yasha boyil mai
ruwan kasa, hula minista baka, takami ma haka, suna
gaisawa rahma tace, waida hafsa zamu wuce kn? Na
zabga mata harara, wai nema? Ya dubeni da mamaki,
mexakije yi kn? Nayi farin rashin kunya tare da murguda
baki, menakeyi da jarabawa na tahowa zaman me zanyi
anan? Rahma tace zaman aure, nace hum! Sai naga yayi
murmushi, sagir yace, kibari ai angon zai kawoki ida lkcn
zana jarabawar yayi, nace nidai gaskia tafia zanyi,
idanuna suka kawo kwalla, sagir yace to abkr amaryar
nan shagwaba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0