Showing 237001 words to 240000 words out of 299763 words

Chapter 80 - SARAUTAR MATA BOOK COMPLETED BY ZAINAB MAKAWA

nace tayi barci ita ce, ma tasani kwantawa,
Mun gaisa da Zarah a cijin raha take ce min uwar buki yanzu nashigo nake tambayan ki akace min kin kwanta ai,
Nake ce mata dama ita nake jiran ta shigo muyi zancen zuwa gurin jeren da za,ayi,
Sai take ce min abinda ya kawo ta ke nan don ta kira shi angon yace mata an gama aikin dakin nasu,
Nan muka tsayar da ranan da zamu tafi gyara dakin Asmau take cewa na fadawa wanda ya dace ita zata tafi can family house din su tafada masu don kada suce ba,a fada masu ba nace ai dole mu tafi da,wasun su don shine daidai,
Wai Aisha kin san ashe mama Sa,a ce ta tafi har gidan su Abdul da,zancen Asmau na banz shine suka so su walwale auren da farko ,
Murmushi nayi nake cewa ai mun sani, shiyasa muma muka biyo mata tabaya muka gyara zancen yanzu ai ta dai ji kunya mutum idan bai hada aure to kada yayi kokarin bata shi don aure kamar rayuwa yake,
Yanzu ba zasu kara ganin ta da mutunci ba ai tun da ba dattijuwar arziki bane,
Shiyasa nake son yaya ya kashewa Asmau kunya,wallahi duk mai bakin ciki yaji kunya da haushi,
Umma tace cikkin jin dadin zance bari kedai Aisha wallahi naji dadin yadda yaron nan yai wa Asmau kayan mutunci,
Nace Umma idan bai ma dan uwanshi haka ba maye amfanin samun mutum ya na dashi bai fitar da dan uwan shi a kunya ba ,
Shiyasa ma nai ta lurar dashi akan ya taimakawa Abudul ya samu ya karasa ginan shi don asamu ayi bukin a lokacin da aka tsayar don duk abin da zai farautawa yan uwan shi rai shine yanzu ya kamata yayi tunda Allah ya bashi,
Shiru Umma tayi don duk wanan zancen bata san dashi ba sai yanzu take jin shi a bakina,
Sai da ya dawo take tuntuban shi a kan zancen cikin basarwa yake ce mata eh hakane ai Abdull din ya,zama dan gida a vurin mu don yaron yayi kokari wallahi,
Allah ya kyauta kawai Umma tace tare da nisaw tana tunanen gidan da Asmau zata shiga gashi ba,shiri a tsakanin ta da yan uwan shi tun ba,a shiga ba,

****** ********* ******
Sha,anin bukin mu muketayi wanda hakan bai hanani kula da, al,amarin mijina na ina ta faman kafa kafa dashi kamar yadda na saba,
Zancen abin da,aka jerawa Asmau yakai ko ina acikin uguwar mu sai yabawa mutane keyi ana ma Hamza adduan fatan alheri wanda Umma take jin dadin haka a ran ta,
Wasu yan mata suka shigo sukace a kaisu gurin Umma sunzo harda ledan su dake dauke da cooler a ciki,
Sun gaisa da Umma su ke cewa sun zo ne Hamza ya fada masu zancen buki shine suka zo gaida Umma,
Nan Umma ta shiga washe baki tana jin dadi da,farin cikin sarakuwar ta tazo,
Ina dakina da yan gidan mu da,wasu daga cikin yan uwan su Hamza Umma ta aika akirani,
Nashigo dakin cikin kwaliyana na wani rantsatsen lace da na,fara sawa a ranan nayi matukar kyau a cikin shigar sai kamshi nakeyi ,
Tun shigowa dakin wata tobashiyan su Hamza ta tare ni da ba,a irin na tobasai ke wanan shigar haka zaki bari wanan matsalon mijin naki ya kara aure,
Nace may zai hana anty duk wacce zata shigo ta,shigo mana ai ga kofa a bude, Aisha dai ce mutu karaba da shi takalmin kaza,
Ai nasani inji matar don duk kin bi kin kalalamay min kani kin hana shi hangen wata kina mashi wanan kwalliyan haka ina zai iya daga ido ya kalli wata, kon koma kamar karamar yarinya dake kullun baki tsufa,
Nace bai dai tashi ba anty idan ya tashi ai ko bashiri sai kuzo buki muci yar gwate mu watse,
Umma ta,tare zancen mu da cewa kawo wa bakin mijin ki abinci gasu nan,
Sai a lokacin na juya inda,suke na san dasu a cikin dakin nai masu wani kallo na son sanin ko su waye su kuma,
Ban san su ba don haka gaisawa kawai mukayi najuta zuwa kawo masu abincin,
Komai na,aje a gaban su yadda ya,dace na juya nabar dakin sai dai a cikin raina ina tunanen ko su suwaye da suka zo mai buki,
Ina shiga dakina na samu Kubura tashigo da yarta wani irin kallo tai min wanda sai da na tsargu don banji dadin kallon ba har cikin raina,
Amma sai na,washe ina cewa Anty nayi fushi sai yanzu kika shigo har ana batun watsewa,
Tace yanzu nagama abinda nakeyi kuma maigidan bai dawo da guri ba balle ya bani umurnin fitowa,
Na kawo mata abinci da kayan shaye shaye na girke a gaban ta sai wani yatsune fuska take tana bina da,satan kallo,
Wa wanan ranan nasan na samu canji rayuwa a auren gidan Hamza yadda mutane sai faman bina da kallo sukeyi,
Ina ga,su Anty Kubura basu san da ina daga cikin kuryan dakina ba sai naji suna gulmana,
Anty Luba ce tafara magana tana fadin ikon Allah ni tun dazun sai mamaki nakeyi wai yar Agwai ce ta samu wanan irin daulan haka ?
Ji dan Allah yadda gaba daya ta canza ta koma kamar matar wani minister can tai kyau har da kiban ta,
Ba dole ba inji Anty hasiya yar Kubura ta,samu Hamza ya rike mata kan maciji tana wasa da bindi,
Ko Uwar ta baki ta canza ba tai kiba ga kuncen kayan da,diyar ke kai mata sai shiga take tana cirewa,
Kubura tace aikin banza tunda ba sabo take iya bata ba may tayi ke nan,
Yanzu fa da kece nan haka Kubura rabon wanan yarinyar ya kaiki guri wanan dan iskan mijin ki da,baisan mutuncin mutane ba,
Kubura tace ai duk wanan uwar tashi ce mai shegen tsegumi tasa mama jin haushin ta raba abin amma nima daga baya ai yadda naga Hamza din yana da kokari da kwazo gashi gaba daya ya canza kamar wani hamshaki
Sai nake dana sani dama ahi na aura na huta da wanan auren ukubar ta gidan wanan mara mutucin da nakeyi,
In banda wahala da bacin rai mai wanan bakin auren ya tsinana min a,rayuwana,
Kawai dai mutum na zama ne dan kar ace ya gaza ko wani abu ni wallahi da tuni nafito daga gidan shi,
Yanzu du bi zanin da mutum ya,daura wai yazo buki dashi kamar wata yar aikin gida,
Kedai kiyi hakkuri ki zauna dakin ki kowa ma hakkurin yakeyi dama abinda ka raina watarana sai ya baka tsoro shiyasa tun farko ban so ki ki auren hamda ba shi baba yasan abin d,yahango kikaga ya nace a lokacin,
Ai kin ga,wanan mai shegen wayau ta bayar da yar ta har muna mata dariya a lokaci ashe mu takewa kallon, wawaye bamu sani ba,
Yanzu ga hakkurin su ya haifa masu alheri a rayuwan su don Allah kadai yasan abinda,suke samu a gurin shi,
Shigowar wata mata tana nema na yasa su tuhumar ko ina daga ciki ina ji abinda su ke fadi sai da,matar ta,daga labulen dakina take cewa aiko bata ciki,
To ina ta shiga ne muna son karban kudi ne a gurin ta da za,a sayo labulen da za,a,sawa dayan dakin Umma tace muzo gurin ta ,
Daga ciki nai magana zakace fitowa na kenan daga bayi na saka wani dogon rigan shadda mai ruwa maron,
Ina kokarin daurin dan kwali gaba daya sun sha jinin jikin su don gani ina daga cikin dakin kila naji su ga kuma wanan rantsatsen shadda da na,saka a jikina sai maiko da,sheki yakeyi yana daukwn ido,
Nake cewa wai na dan shiga,ban daki ne na kewaya sai na tsaya na saka kaya a ciki,
Sai lokacin suka sauke ajiyan zuciya don sun san banji su ba ke nan tunda ina can bandaki daga ciki,
Na juya gurin su ina cewa dan Allah anty kuyi hakkuri na dan kewaya,ne,
Ina fitowa tsakar gida idanuwa caaaa a,kaina kowa da abinda yake nasawa a zuciyar shi,
Wasu na fadin na samu guri wasu kuma,sai cewa sukr na tare ko ina sai abinda nace wasu kuma suna fadin hakkurina ne yakai ni ga,samun riba, haka ,
Mutum baka da gadon shi amma,shi yana da gadon maganan ka don bai gani bai nasa ba, a kan ka ,
Fitana dakin yasa yan gidan mu samu daman ci gaba da zancen su suna mai cigaba da gulmana ni da mijina da uwarshi, da,ta hana rayuwana,shakat,
Ina shiga dakin Umma,na,samu wa yan nan yan matan suna shirin fita,daga dakin Umma sai faman godiya,take zabga masu godiya take ta faman yi,,
Gani tafe kai tsaye dakin fuska na,sai sheki yaki yi yasa suka, dan kauce min don ba,alamar zan kauce masu,
Nake cewa Umma ance wai na bada kudin da,za,a sayo wasu labulaiyya Umma suna jin murya sai suka dan kara tsuke fuskan su,
Suna fita daga gidan dayan tace tirka shi ashe akwai aiki a gaban ki ja Biba wanan matar ta Hamza ban taba zaton haka take ba wallahi,
Hmm bari kedai Amina wallahi narasa gano wani abin makusa a jikin yar iskan yarinyar nan,
Ashe ma karamar yarinya ce haka sharaf wanan ai kin,gimay mata nisa ba kusa ba,
Ashe shiyasa yake min wani gani gani yasan abinda ya aje a gidan shi amma dai komai tsiyar ta sai na shiga gidan nan wallahi ko,
Zaki ko sha kallo don wanan yarinyar da nake gani akwai shegen wayo gare ta, ba karami ba jifa tun bata masan ko mu suwaye ba irin maganan da takeyi,
Ni ko sai nake gani kamar ta gane komu su waye don kin da zamu fita ko kallo bamu ishe ta ba fa,
Wanan dole na,sake shiri a kan ta don akwai aiki gaskiya sosai saboda naga kamar ta dan waye,
Mu dai yi bincike a kan ta don mu san ko wacece ita ,
Wai wanan ce ake cewa matar hadi ce ba wai soyayya sukayi da ita ba ya aure ta,
Haka dai suna tafiya suna zance a kaina dakuma gidan namu har suka kai gida suke shedawa Uwar su cewa sun ga matar hamza a gidan da suka tafi,
Nikan ranan na jigarartu sosai don mun sha fama da jama,a anyi taro lafiya an kuma watse lafiya,
Sai dare Hamza ya samu ya shigo gidan don jama,a sun watse sai yan garin su Umma da suka zo mata buki ne a gidan,
Tun shigowan shi gidan yake kokarin kallon fuskana sai dai ya kasa fahin ta na ,
Ban tsaya ta kan shi ba kamar yadda na saba na gama kimtsawa na haye gado abina tare da yar diyata wace tayi wayo ko sosai yanzu,
Jin motsin shi danayi a,bayana yasani kara lafewa saman gadon wai make faru dake ne yau nagan ki haka Rangida ?
Ran gida ai suna can maka a waje nikan ai yar gadin gida ce ko ince yar aikin gida,
Kuma dai duk may yakawo wanan zancen kuma haka yau,
Nace matan banzan ka da ka turo buki don ai min dariya mana,
Katuro sune dama don su zo su ganin ko kuwa ni fa ban hanaka sha,aninka ba yaya amma cin fuska ne ban so,
Su tsaya a matsayin su kada su shiga gonata bazata iya bari idan ka kwaso ta tazo ba, don bata da kunya shine za su muna har gida wai sunzo ma buki,
Kuma don a,wullakantani kamar yadda kake son nuna masu shine Umma zatace wai sai ni zanyi services din su,
Murmushi naji yayi yace akan zuwan su Biba ne kike wanan cika kina batsewa Humaira,
Yaushe kika fara kishi hakane wai ban sani ba nace kasan ni, ba mace bace ko ince ba mutum nake ba,
Tau idan kin yarda wallahi ni ban ma,san da zuwan su ba asali ma har sai da sukazo suka koma ne tai min text cewa tazo taga beautiful wife dina da yara na,
Nace dama ai shi ya kawo ta kuma tagani tunda wanan ne kawai daman da take dashi na shigowa gidan nan,
Ni yanzu wanan zance bai gaba don haka ki sawa ranki sanyi don ni wata Biba can bata a gabana,
Daga haka ya mike ya,zagaya ta bayan mu ya kwanta ban bita kanshi don tukaki nake ji a cikin raina a lokacim ina ga ya fahinci hakane ya kyale ni,

****** ********* ******
Ina zaune a falona bayan bukin Asmau da kamar wata daya, Hamza dake fitowa daga kuryan daki a cikin shirin shi nafita,
Na,dago idona kalle shi nake cewa yaya dama yau iba son zuwa gidan Antu Hindatu ne na,dubo su,
A take ya tsuke fuskan shi yana cewa wai l loop yawan yi zuwa gidan Hindatune, kullun fitan ki ke zuwa gurin hindatu ne,
Nace kullun har da,yaushe yaya rabon da nafita fa tun bukin Asmau da akayi a gidan nan,
Ko wanan ma ai dalili ne zai kaini don nai mata ban gajiyan zuwa muna bukin da tayi
Ni dai ban son kina masu zariya a gida har aga kamar wani abu kike yawan zuwa yi,
Nace in ba dalili ba yaya may zai kaini ni gidan wa nake zuwa,a garin nan banda gidan mu sai ko nata,
Fusace yace min baki zuwa nace Aisha don ban son yawan fitan nan ni gaskiya, yafita a hasale ya barni nan cikin mamakin shi,
Ban daga a gurin ba,sai na fara tuhumar ko dsi da wani abune a kasa yasa ya hanani zuwa gurin ta,
Jin ya tayar da motar shi ya tafi baya gidan yasa na dauko wayana na kira Hindatun,
Mun gaisa da ita take ce min kwana biyu haka shiru Aisha ba ko waya,
Nace wallahi yanzun haka dashirin zuwa gidan ki a jikina amma kuma mai gidan ya hana ni fita ko ina wai ni ke nan kullun zuwa gurin ki,
Murmushi naji tayi tana cewa kyaleshi Aisha tsoron kada kizo guri na ki samu labarin shi shine ya hana,shi barin ki kizo,
Ashe bai isa ba tunda yana jin tsoron a fada maki abinda yake yi a gari,,
Wani irin damm naji kirji yaba da nace ke nan a kwai wata akasa ko anty tace kyaleshi ai nai mashi tas ranan da yazo gidan nan,
Anty may ke faruwa ne wai don ni wallahi har hankalina ya tashi sosai wallahi,
Tace ke ba wani zance bane zancen yar iskan nan ne da ta lake mashi da kaman sun rabu dashi amma yanzu sai gashi sun dawo sun kara dinkewa kuma har ranan nagashi da ita a mota,
Kin san bani bada bashine nadaga waya na kirashi shine yake ce min zai zo gida gurina ya samay ni,
Nashiga Ukku anty badai Biban nan ba tace wallahi ita kuwa Aisha
Ni banga abinda Hamza yagani ga wanan mace mai tsowa kamar hannun lema ba
Magana antu keyi amma ni hankali baya,a,gare ta,ina can ina tunanen cewa wacce nagani baka,doguwa daga cikin su itace ke nan Biba din,
Sai ji nayi tana cewa kai kibar namiji kawai Aisha sai kiga sun kwaso abinda ko kwatan na gida bai kama ba,
Wanda ke da mace kamar ki a gidan shine wai ya tafi kallon wata Biba can maikama da siffan samudawan dauri,
Anty ni na,rasa may wanan mutimin yake tayiwa aure haka don banga abinda na,ragashi dashi ta fannin rayuwa,
Amma kuma yake fita waje yana hangen wasu da ba,su kai ko kwatana,ba,
Tace ai garama ya,auro maki waccd bata kaiki ba din yafi ace tafiki da,wani abu, ke namiji sai kiga kamar idon shi a,rufe yake neman wata,macen,
Ni dai yanzu nasan cewa bawai kina,gazawa da bukatan shi bane kawai dai shi mutum ne mai ra,ayin wanan auren,
Wanda idan kin duba,mu diyan hausawa dama mun gaji irin wanan rayuwan tun kakan ni da iyayye,
Da,wuya kiga dan bahaushe ya tabbata,da mace daya a,rayuwan sai kin samay su da irin aure auren nan wanda zance maki a jinin mu hausawa abin yake,
Don kin ga da,ace ana gadon abin ne da Hamza bai yi ta,wanan halin aure auren ba da kurciyar shi don ance mahaifin shi bai taba auren wata ba bayan Umma,
Don haka don Allah dai kiyi hakkuri ki barshi da halin shi yaje yai ta,aure auren shi tunda ke bai rage ki da komai ba na rayuwa,
Ba dai komai akewa kishi ba sai jijiyar namiji ko tau ai ajikin shi yake ba,a jikin ki ba shi ya sani da bakin auren don shi zai fadi ai ance jiki magayi,
Halin mutum mai kosar dashi, shi da,ya jajibo shi ne zai gasu kina zaune zaki ji shi da ita in har kinyi hakkuri,
Ko murai kada ki wahalan tayar da hankalin ki a,banza don ba bari zaiyi ba idan yai niyya,
Ke da ki kula da kanki da tarbiyan diyan ki, sa mashi ido kawai don ko shiru magana ne Aisha,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login