Showing 12001 words to 15000 words out of 22014 words

Chapter 5 - Sanadin Boko 4 by Halima Abdullahi k Mashi .pdf

Ya
ce, "To." Na sake alwala na zo ina Nafila dan wannan
sallar tana da Muhimmanci gurinmu, in har zaki yarfe
bacci ki tashi daidai wannan lokacin ki fadama Allah, to
kuwa duk wata matsala taki zata yaye. Ubangiji da
kanshi yake cewa da mai bukata ya tambaye shi Shi
kuma ya biya mana, wannan kadai na tsare, ba boka ba
mallam ga matsalolina a hankali duk sun warware.
Allah ka yaye mana dukkan matsalolinmu Ameen.
Ranar Lahadi kuwa ranar da zai zo cewa yayi in masa
tuwon semo, sai kuma in masa jus din Shinkafa din
nan. Miyar danyar kubewa na yi masa, ta ji
bushashshen kifi da nama, na masa jus din shinkafa,
sai irin kunun ayan da nike sha mai dabino da kwakwa
da zuma. Wando da riga na ci sabbi ne na siyo su, da
ina zaton ba zan iya saka wando ba amma daga baya
sai na ce kiji kana cewa baka iya kukan mutuwa ba
Uwarka ce mata mutu ba. Da kadan ya wuce gwiwata,
rigar ma ta dame ni. Kallona yayi ta yi tunda ya shigo
na masa oyoyo, da kyar na bambare daga jikinsa don yi
masa shimfida, ya ce, "Ya ya aka yi kika san ina son
shigar English wears?"
Na ce, "Duk abinda ka ke so a kwayar idonka nake
karanta, ai ba kallon kawai nake maka ba." Ranar dai
mun ciyar da juna abinci, sannan muka shiga wani
shafin, daga baya muka yi wanka muka dunguma gidan
su Rahma. Shadad kuwa sai tsalle da ya ganmu, da
zamu tafi ya so binmu, har zan ce mu tafi da shi sai
Abubakar ya ce, "Shadad unguwa zamu, amma gobe
zaku taho da Uncle dinka na nan gidan." Ya ce, "To."
Muka dawo nan gidan muka kwana.

Gaskiya duk macen da ta samu miji kwatankwacin
Abubakar, to ta gode ma Allah, mamaki na daya, yanda
ya iya kula da mace ta kowanne fanni......


Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100


Sanadin Boko 4-05
Posted by ANaM Dorayi on 05:17 AM, 29-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Asubanci muka yi tare da su Sagir, Sagir ke tuki shi da
Abubakar, ni da Rahma da Shadad muna baya. Sagir na
zuba mana hira don shi Abubakar mutum ne bame
yawan surutu ba, sai dai mun ta hada ido da shi ta
madubi sai ya kashe min ido daya mu yi murmushi, har
Rahma ta gane mu ta ce, "Kai ku dai wanna soyayya ko
ina sai kun nuna ta?" Na ce, "Kuma ku nuna mana."
Kotu ta cika lokacin hankalina na tashe, gani nake shi
kenan za'a kwace min da. Bayan gabatarwa Alkali ya
bukace mu muka fito ya ce, "Ina yaro?" Aka fito da shi
ya ce, "To a musulunce za'a yanke hukunci tunda mu
Musulmi ne." Duk muka amince. Alkali ya yanke cewa,
"Duk da cewa fyade aka yi mata ta samu ciki, to dan ba
dan Sunna ba ne, ma'ana ba ta hanyar aure aka haife shi
ba. Don haka in ma ace tayi cikin shege dan nata ne ba
a danganta shi da namijin saboda sai da yardarta, don
haka wannan ma nata ne, sai dai shawarar da zamu iya
bata ita ce ta bawa wannan mutum dan saboda zata fi
mutunci, haka nan shi dan ko kuma a ba yaron zabi zai
bi Uban nasa shikenan. Sannan hukuncin fyade tunda an
ce bai taba aure ba, to za a yi masa bulala dari." Nan fa
suka soma kuka, Mom ta zo tana kuka tana rokona wai
in basu shi, na ce "Gaskiya ba zan iya bada dana ba."
Shi kuma Dad dinsu ya samu alkalin suka kiramu suna ta
rokonmu wai tunda gashi shi za'a dake shi, gashi bashi
da koshin lafiya. Abubakar ya ce, "In dai yayi hutu za'a
ringa kawo shi saboda ya san Ubanshi da danginshi."
Suka yi ta godiya muka kame kanmu. Kano muka wuce
bayan mun je gidanmu kowa na taya ni murnar cin
nasara, daga nan muka koma Kano. Na gama jarabawata
ta fita, murna ba a magana yanzun saura service

Washegari da gaggawa Abubakar ya zo ya tafi dani Yola.
Shadad kuma dama Sagir ya kai shi Kaduna gidan
Babanshi suna ta murna. Shi kam da kyar ya lallasu daga
kukan da yake sai da Sagir din ya kira ni ya ce in mishi
magana. Na ce, "Shadad." Ya ce, "An'am Aunty, ni zan
dawo ne ki fada ma Uncle ya dawo da ni." Tausayinshi
ya kama ni na ce, "Gidanku ne ai, gidan Babanka da kake
ta damuna da zancenshi." Ya ce, "Aunty ban san su ba."
Na ce, "Zaka san su kayi hakuri kaji ko?" Ya ce, "To."
Munir ya ce ma Mom ta amshi lambata in ya so sai su
dinga kira mishi ni. Sagir ya bada lambar sannan ya tafi.
Ikon Allah Shadad na ganin gata, tamkar a cinye shi don
tarairaya, har an sai mishi waya don ya dinga kirana, ni
kam cewa na yi kada su bata min tarbiyyar yaro, saboda
su ba su da tarbiyya. Mahaifin Munir ya yiwa Shadad
kyautar gidanshi da ke Kabalar road, tunda wai an ce
bashi da gadon Ubanshi. Suka bude mishi account ni kam
ina can Yola gidan mijina mai sona da gaske.
Yau gidan Fadima yake, amma ya kira ni wai zaya zo
cin abinci da rana. Na ce, "A'a, sai dai na yarda ka aiko
a karba maka, don kada mu shiga hakkinta, Don nima
ba zan so amin ba." Ya ce, "To naji." Na yi masa
french dish rice serve with grill chicken, sai kuma na
masa dan waken rogo da dawa, dama ina da garin,
sannan na masa jus din karas, duk san da zanyi girki na
kan yi da dan dama saboda mutan gidanmu suna son
abinci na.
Hakan nan na kan kirkira girki inyi ma Abba da Lamido
da kalokin Jus na kan zauna ina kallon tashar girke-
girke ina rubutawa na Chanis ko Italia ko Senegal da
dai sauransu. Saboda kawai in samo girki wanda ba a
saba da shi ba.
Fadima ta dube shi, "Ban gane nufinka da amsa abinci
gidan Hafsa ba?" Ya dube ta bayan ya dire kofin
hannunsa ya cea, "Ta iya girki ga kokarin yi, bata da
kuiyar dafa abincin ko kala nawa ne." Ta hade rai, "Ni
ban iya ba kenan?" Ya ce, "To ke ko kin iya din ma
yaushe kyuya zata bar ki? Ballantana kure girkinki shi
ne shinkafa da miya ko taliya. Da zaki daure da kin je
kin koyo kafin ta tafi CAMP." Ta harare shi sannan ta
ce, "God Forbid in je gurinta koyon girki ka cuce ni,
kuma wallahi ba zan yarda ba. A ranar girkina ace
abincin ta zaka ci? In an sake kawo min nan zan zubar

dashi." Ya ce, "To shi kenan, zan so ki zubar din." Cikin
fushi ta shige daki. Duk ranar da yake gidana akwai
wasu jus na kankana, Apple, ayaba, madarar ruwa,
zuma da kuma garin ridi, in sa kayan itacen a blender
in nika in zuba madarar da zumar da kuma garin ridin in
sha, in kuma zuba masa ya sha, har dai wata rana ya
tambayeni me nake sawa cikin wannan jus din? Don shi
kan shi yana jin shi kullum yana kara lafiya da kuzari,
yakan kuma ji yanayi daban da in bai sha ba. Na ce
'ya'yan itace ne. Har ma watarana a gabanshi nake
hadawa. Wataran kuma in hada rake, zuma, madara
peak, garin ridi. Kafin wani lokaci sai gashi na zama
Malama ta hada kayan gyaran jiki, in mun yi waya da
Rahma in na fada mata wasu sai tayi ta mamaki, na ce,
"Dama na fada miki."
Abin da yafi bani mamaki, da zan tafi CAMP a Kaduna
aka tura ni har da kukan shi da hawaye don damuwa.
Shi ya kai ni sannan ya biya ya taho da Shadad ya kai
shi gidan Rahma a Kano. zaman sati 2 a camp ko ni na
san na yi missing din gwarzon masoya, Abubakar
Sadiq.
Fadima ta dubi Rukayya, "Kin san Allah ni zan kai karar
Hamma gurin Abba, sam baya cin abincina sai na
Hafsa. Don gulma har nan zaki ga ta yo ta aiko mishi
da shi, kenan ya fada mata cewa ban iya girki ba."
Rukayya ta ce, "Ai Hamma ta riga ta gama da shi, ke
har su Daada ma in kinji yanda suke yabonta? In ta yo
abinci ta kawo ma Abba kiga su Ummi har ma Daada
din sai suyi ta yabonta." Ta ce, "To gurin Lamido
zanje." Rukayya ta ce, "Kin ji ma inda zaki fi jin dadin
kai karanki, kuma zaya ci musu daga shi har ita. Dama
ai ba son auren yake ba, kila ma yana kushe auren."
Cikin zumudi Fadima ta ce, "Anjuma zan je."
Ta shigo gidan da sallamarta suka gaisa da mutan
gidan, tsoffin suna mata tsiyar cewa sun kwace miji. Ta
shiga gurin Lamido, bayan sun gaisa ta ce dama ta
kawo karan Hamma ne. Lamido ya gyara zama ya ce,
"Tun kafin aje ko'ina har an soma matsala? To me ya
faru?" Ta ce, "Baya cin abincina, ranar da yake gidana
sai ya aika nan a karba mishi abinci fa, kuma in nayi
magana sai ya ce ta fini iya girki. Shi ne ni na gaji da
wannan maganar." Can ya ce, "Shikenan?" Ta ce, "Eh."
Ya ce, "To yanzun ina Baban nawa?" Ta ce, "Yana cikin

gari." Lamido ya kira shi a waya ya ce ya zo yana
nemanshi. Kusan minti 30 sannan ya iso Lamido ya ce
masa, "Daga ina?" Bai ji mamakin ganin Fadi ba.
Lamido ya karanta mishi laifukan da ta fada, sannan ya
tambaye shi ko haka ne? Abubakar ya ce, "Haka ne."
Lamido ya ce, "Don me to baka son cin abincin nata?"
Abubakar ya ce, "Don bata iya ba, kuma don na amso a
gurin Hafsat wadda ta iya bana zaton na yi laifi.
Saboda Manzon Rahma (S.A.W) yana amso abinci a
gurin Nana Safiyya ya ci in yana dakin kowacce daga
cikin matanshi. Don haka ni Sunna na yi." Ta ce,
"Amma shi bai yi wulakanci ba." Lamido ya ce, "To naji
yanzun dai sai kiyi kokari ki gyara." Abubakar ya ce,
"Abin da in riga ta dawo wa kullum sai na fa jira ta ta
dawo sannan ta min abincin. Ita kuma Hafsah ko ina
zata sai tayi min abincin ta bari in dai tana gari, amma
ita wannan sai son jiki." Lamido ya ce, "Ka yi hakuri
tashi ka je abinka.Bayan fitar Abubakar Lamido ya ce,
"Ke Fadima abin da zan fada miki, kin ga bakuwar
yarinyar nan? To ta fiki hankali. Tun yaushe rabonki da
gidan nan da sunan ki zo gaishe mu? Ita kuwa ko bata
garin nan ta kira mu ta gaishe mu a waya. Girkinmu
daban ga girmama mutane, don haka ki nutsu ki zauna
lafiya. Ba zan 'kita ba don tana bare, dama ai mugun iri
ake tsoro." Fadima dai ta tashi jiki babu kwari ta tafi
gida, zuciyarta cike da haushin Hafsah, wato ta zo zata
siye dangi? Ta ja wani Uban tsaki.
Allah cikin ikonsa mun gama CAMP sai dai Abubakar
ya ce zai yi duk yanda zai yi a barni a Yola, ba zan
kara nisa da shi ba. Daga baya ma ya ce in na gama
bazan yi aiki ba, ni dai ina jin shi ban ce komai ba.
Allah ya taimaka da ya shiga ya fita sai ko aka barni a
Yola, ni kaina nayi murna don bana son inyi nisa da
mijina, Shadad ya dawo Yola shima Abubakar ya canza
masa Makaranta mai kyau, duk da cewa Iyayenshi suna
ta turo kudi wai na karatunshi. Dad har Yola ya zo
kuma ya sanar da abokinshi Mai Martaba Baban su
Hashim cewa Shadad jikan shi ne, don haka yaron bai
da matsala ko cikin gida, gashi da farin jini.
Cikin haka ne FADIMA TA SOMA LAULAYIN NAN, naga
rawar kai wurin Abubakar da 'yan uwansa, ganin haka
nima na soma zuwa kullum ina dubata, sai ta tsiri cewa
wai turarena na sata amai, in daina zuwa. Abubakar ya

ce, "Fadima ta ce bata son turarenki ki daina zuwa
kawai." Allah yasan na ji haushi, amma sai na share
saboda sanin halin Abubakar shi mutum ne sak babu
kwane-kwane a tsarin shi, baya rufa-rufa ko kara
zance, yanda aka fade ta haka yake daukenta, shi yasa
na sha wahala lokacin da na ce mishi ni karuwa ce, har
sai da ya zo ya ji komai da kunnanshi na samu sukuni.
To yanda Fadima ta ce haka zai fada gaskiya
tsagwaronta yake yi ba ruwanshi, don haka na ce, "Shi
kenan, na ringa kiranta a waya muna gaisawa." Ya ce,
"Hakan zai fi." Daga baya sai ta tsiro cewa ita ba zata
iya bacci ba sai in yana gurinta, Ya ce to bari ya same
ni. Ina kwance na dawo daga gurin aiki wata makaranta
aka turani ta 'yan mata nake koyarwa. Na yi abinci na
gama nayi wanka na kwanta, ya zauna na tashi na
mishi sannu da zuwa, na dire mishi abinci. Yana ci ya
ce, "The only, ina son ki yiwa Fadima taimako daya."
Na ce, "Na me?" Ya ce, "Bata samun bacci don
Rukayya ta fada min cewa zaune suke kwana. To tana
son in dinga kwana gurinta har ta dan
murmure."Zancen ya bani mamaki, sannan na fahimci
cewa makirci ne, amma sai na ce, "Ba komai." Ya ce,
"Dama na san ki baki da matsala." Da dare kuwa ya
tafi, haka-haka har sati uku. Sai dai fa in yana da
matsala ya yi min sammako ko kuma in ina gurin aiki
ya zo ya dauko ni daga baya ya dawo da ni. Ban taba
nuna mishi damuwata ba.
Lamido ya kira shi ya ce, "Ubana an fada min baka
kwana a gidan nan ko?" Ya ce, "Eh, saboda bata samun
bacci ne in bana na." Lamido ya yi murmushi sannan
ya ce, "An fada min kuma tana zuwa hurin aiki ko?"
Abubakar ya ce, "Eh, ai matsalar tata da dare ne."
Lamido ya ce, "To, daga yau na hana, kowacce ka
dinga kwana gidanta a ranar kwananta, kanta aka soma
ciki? An ce ta samu sauki ba shike nan ba?" Abubakar
ya ce, "Shi kenan." Har na soma bacci na ji kwankwasa
kofa, na zo na ce, "Wane ne?" Ya ce, "Ki bude." Na
bude na ganshi na ce, "A'a baka tafi ba?" Ya ce, "Ke ce
kika fada ma Lamido cewa Fadima ta ji sauki amma
ban daina zuwa ba ko?" Na ce, "A'a bani ba ce." Ya ce,
"To wanene?" Na ce, "Ka tambaye shi." Ya ce, "To ni
bana son kai kara, don ban soma zuwa ba sai da
izininki." Na ce, "To gaskiya ba ni bace." Ya ce, "In ma

ke ce din ai yana zuwa kanki, tunda an ce ai haka ciki
ke yi muku." Na yi masa shiru don haushi.
Abinda bai sani ba nima lokacin ina manne da nawa
cikin wata biyu, ina kuma laulayina sai dai bai yarda ni
ba, sai dai amai kuma nafi yin shi da rana, kuma ban
fasa komai ba.
Azumi ya kusanto ya zo ya same ni wai in zo muje
gidan Fadi, zai yi wata shawara, na ce to..........
Cikinta ya fito, amma yanda take tike kugu gami da
turo cikin ko watan haihuwarta ne sai haka, tana yi da
kyar take daga kafa, a dole ga mai ciki shi kuma
kallonta yake yana murmushi, ni sai suka ma bani
dariya. Ya kamata ta zauna yana yi mata sannu, ita ko
sai faman cije-cijen lebe take, na yi 'yar dariya nace,
"Maman twins an fito?" Ta ce, "Umm na fito." Muka
gaisa ya ce, "Dama saboda zuwan azumi ne ina son in
bada sadaka wa kuke ga ya dace in ba?" Fadima ta
dube shi, "Kawai honey ka bamu mana, ni ga ma
sayayyar da ke gabana na kayan baby." Ya dubeni, "Ke
fa?" Na ce, "Ka kai Masallaci ko ka samu mabukata ka
basu tunda Alhamdulillah mu muna cikin wadata." Ya yi
murmushi, "To dama nima tunanina kenan, don haka
zan bai wa masu bukata Zakka, sadaka kuma zan baku
ku bada, ko cikin family dinku ko nawa."ta zobaro baki,
"Kenan shawarata bata yi ba?" Ya ce, "Eh." Ta yunkura,
"To ai da ba'a kirani ba." Ya ce, "Hakkinki na baki da ba
sai na zo ba din, don nasan ita zata iya bani shawara
ta masu ilmi." Kudi ya zube min dubu dari uku da dari
biyar, wai in raba ma masu bukata. A zatonshi zan tafi
da shi gidanmu ne in raba ma dangina, sai na
tambayeshi zuwa kasuwa ya yarda. Ni da Ummi muka
je. Shinkafa kawai na lodo da taliya sai kuma zannuwa,
Ummi ta ce, "Aunty me zaki yi da shi?" Na ce,
"Sadaka." Ta ce, "Don Allah akwai wasu dangin su
Daada dake can wata ruga talakawa ne, jiya ma Abba
ya aika musu da gero da sugar na kunun azumin." Na
ce, "To." Daada din naje na samu na ce, "Sadaka zan
raba ta abinci saboda neman falalar wannan wata, to
ina so in cire na dangi na can Ruga shine nake so ki
cire musu nasu sai na ba makota sauran." Ta ji dadi
sosai, tayi ta shi min albarka, duk da ta san cewa shi
ne ya bamu kudin, ta ce min ya shawarceta, ita ce ma
tace yayi shawara da mu, ta ce ya ban kai dangina ba?

Na ce, "Da ku da dangina Daada ai duk daya ne ba
wani bambanci." Ta ce, "Allah ya shi min albarka. Ta
cire musu sannan na saka 'yan samarin gida mua yi ta
mika wa makotanmu wadanda ke da karamin karfi.
Dama kananan buhuna ne. Lamido har kofata ya zo
yayi min godiya tare da shi min albarka. Abubakar
kuwa da ya dawo ya ga makota na ta mai godiya tare
da addu'a sai kuwa kanshi ya daure, da yai zaton geron
da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0