Showing 18001 words to 21000 words out of 22014 words
Chapter 7 - Sanadin Boko 4 by Halima Abdullahi k Mashi .pdf
dafa kafadar Abubakar "kada ka damu, ka yiwa 'yarka
addu'a Allah yasa mai albarka ce."
Duka suka ce "Ameen" Masu habaici da rawar kai kowa
dai baki tsuu, shiru kake ji. Kullum nake zuwa gidan mai
jego har ana jibi suna.
Ranar da ya kawo mata zannuwan fitar suna ta ce basu
yi mata ba, ranar ce ya amayar mata da takaicinshi a
gaban 'yan koran nata.
Ya ce "ki bini a sannu, banza makaryaciya, zan
maganinki, kuma in na dawo baki dauki kayan nan ba sun
zama ba rabonki ba.
Ki sani ko bari kika yi zan so shi, bare dan mutum. To
meye ribar karyar da kika yi kika sa muma muka yi?
Mutuncin ki ya zube a gurina da sauran mutane. Sannan
baki isa ki juya ni ba, kinfi kowa sanina.
Zata yi magana ta rike kugu, ya ce yi min shiru, in kin
furta wata magana zan bata maki yanzun nan.
Ta yi tsit, ya fice. Nan ta shiga kuka suna bata hakuri,
Rukayya tana cewa sai ta fadawa Dada da Abba.
Yarinya taci suna Nana Fiddausi, in da ni kuma na
shiryawa Abubakar kalolin girki kusan bakwai da kayan
drinks.
Suka yi walima, Ummi da kanwata Ummi sune yan taya
aiki.
Bayan suna da sati daya muka je Kaduna don maida
Ummi tare da dauko Shadad daga gurin babanshi.
Har da Umminsu ta mana rakiya don sun kulla kawance
da Umminmu,saboda xaman mota sai kafafuna suka
kumbura,sannan nayi ta shar amai,duk Abubakr ya rude
hankalinsa ya tashi.kafin kace haka na kwana
shrkaf.muna isa kaduna asibitin Garkuwa ya wuce dani,
da gudu-gudu aka kawo gadon tura mara lafiya aka yi
ciki dani,likitan yana duba ni yana mishi tambayoyi,tana
da ciki ne?ya ce kai bana xatao, sai dai ko in yanxun.
likitan ya maida allurar da yayi niyar yi min ya aje,yasa
aka tura ni xuwa dakin scanning, kusan min 30 aka fito
dani yaxo ya dauko ruwa aka yi wasu allurai a ciki,
sannan aka dora ni ,ana da nan bacci yayi gaba
dani,likitan ya kalle shi"matarka tana da ciki kusan
wata 5 ko ma fi,sai in ta farka nayi mata wasu
tambayoyi tukunna. Abubakr ya tsura mishi ido,kace
tana da ciki wata 5? likitan ya ce kila ma ya fi.
Abubakar dai yayi shiru,amma ba don ya yarda ba, ya
kira Umar ya fada masa kusan minti 30 suka iso dasu
Baabah.Sannan ban tashi ba, ya ce don Allah yaya
umar ya kai su Ummi gida don suna ta kuka,kujera
Abubakr yaja ya xauna ya rike min hannu su Baabah
sai waje suka fita don kunyar yanda ya tasa ni gaba
kamr xai cinye ni.ya kira su Hashim ya fada mishi su
Daada ma ya sanar da su,kusan wa daya na farka.Da
sauri ya tashi yasa hannunshi a kuskata, yana cewa
"Sannu Hafsat sannu.Na ce yauwa Na yunkura xan
tashi ya kama ni na xauna ya xauna gefen gado. Ina ne
ke miki ciwo yanxun?nace "Ba ko ina yunwa nike ji,
bakina ya cika da miyau,na ce xan xubar "ya miko min
wata yar tasa sannan yace bari in kira likitan.Da sauri
ya fita ya ce ma su Baabah na farka, suk shigo suna
min sannu, na amsa na ce ni babu gurin da ke min
ciwo,yunwa kawai nake ji (dama cin abinci a gurina tun
dana samu cikin nan kmr gara)suka shigo da likitan aka
ce su fita Abubakar kuwa xama yayi kusa dani likitan
ya ce "Madam cikinki wata nawa ne?Da sauri na kalli
Abubakar sannan na sunkuyar da kai.Ya ce "Fada min
mana "Na ce na zaton cewa xai kai shidaa."Abubakrya
dago idona ina da yaro dan wata shida a gurinki, ina me
ban sani ba?likitan yayi daria,'kila tana son ta baka
mamaki ne ko?na ce"Ina son in ci abincin. Da sauri
likitan ya ce me xa ki ci?na ce "Tea xan sha.Nan da
nan yayi waya a kawo min tea.Abubakr kuwa cikin
rigata ya xura hannu yana shafa cikina yana min
magana a kunne."d only me yasa kika rufe min?na ce
To kana fama da mara lfy sai nima in kwanta mu taru
mu daga maka hnkl?Ni ba xan iya ba, bana son in
ganka ckn damuwa,shi yasa na daure. ya ce "Allah yi
miki albarka, dama nasan kece mai son kwanciyar
hankalina. bayanna huta ya sallame mu muka nufi gida
sai yau naga gidan da aka sai masu Baba a nan dai
Abuja Road din ne amma can kasa gurin sabon guri ne
kuma gida mai kyau flat.
.. Abubakar kam da ya fita sai ya je ya kama masauki,
sai dare ya dawo. Ya ce na zo muje, bansan ko ina
bane na cewa su Baba ina zuwa.
Sai kurum ya kaini masauki, wai nan zamu kwana, na
ce "Haba Mr Cool, ka maida ni gida mana su Baba zasu
ga rashin kunyata."
Ya ce, "Bazan iya barinki ba, bakiji Likita ya ce na kula
dake sosai ba?" Sai waya nayi wa su Baba na ce munje
gidan wani abokinsa can zamu kwana.
Suka ce to, kwanan mu uku, kullum da safe zai kawo ni
amma da dare zai zo ya tafi dani.
Wata sabuwar soyayya da tarairaya Abubakar ya soma
yi min, da zamu koma gida jirgi muka bi.
Muna isa ya fara yadawa ina da ciki, dama Likita yace
in mun dawo na soma yin awo.
Shine ya kaini asibitin ya yankar min kati, a dakin
scanning Likita ya ce "Madam kin san cewa 'yan biyu
ne?" Na zaro ido "'yam biyu?" Ya ce "kwarai kuma kin
gansu duk maza"
Na ce ba a fi sati daya ba da akayi min scanning a
Kaduna ba a fada min haka ba."
Ya ce to yanzun dai gashi nan" na ce to don Allah ka
taimake ni kada ka rubuta a cikin sakamakon"
Ya ce "don me?" Na ce "Don haka ta faru ga kishiyata,
a karshe sai ta haifi mace guda daya."............
Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100
Sabadin BOKO 4-07
Posted by ANaM Dorayi on 05:21 AM, 29-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Ya ce to shike nan, ya rubuta komai lafiya amma bai
rubuta mace ko namiji ba, bare ya saka 'yan biyu.haka
naci gaba da samun kula, yanzun da asiri ya tonu sai
cikin ya fito yayi rum.
Da da ba a sani ba kuwa lakwam, har cikina ya kai wata
takwas ban taba yi masa batun kayan haihuwa ba.
Shi ne da kashi ya ce "wai the only baza mu sayo kayan
haihuwa ba? Na ce to, sannan muka je ni da shi da
Ummi.
Wata safiya na tashi da matsanancin ciwon ciki da mara,
gashi ya je Lagos amma ranar zai dawo.
Da ya kira duk da koakrin da na ke na nuna masa bani da
wata matsala sai da ya gane.
Ya kira Dada ya ce a zo a duba ni lafiya? Ummi ce ta zo
har ta tafi ban bari ta fahimci wani abu ba, tunda ciwon
yana yi ne yana lafawa.
Kafin dare na jigata, lokacin da ya shigo fayata ta fashe
haka suka kwashe ni zuwa asibiti.
Da Lamido na fadan me ya sa naki fadin banda lafiya,
sai su Gwogwal suka ce ai kunya ce.
Lallai ni yar mutunci ce, ni ba fulani ba amma ina da
kunya. A raina na ce kunya ai ta dan sunna ce bata
Fulani ba.
Don haka duk Musulmi mai Imani zai zama yana da
kunya.
Da kaina na haihu, dana kato zuwa can kuma sai
sabuwar nakuda, sai kuma ga wani dan.
'Yan biyu masu kama da juna, sannan duk wanda ya
kalle su yasan 'ya'yan Abubakar ne.
Tunda Nurse ta kawo na farko Abubakar ya ke ta murna
da su Hashim, sai ta ce zaka bani goron albishir ina
zuwa.
Da tazo da dayan sai suka kama murna, kafin ka ce
haka, dangi sun cika asibitin harda su Rukayya.
Ni dai na ga lele, Fadi ko leke don ko da ta sami labrin
ina da ciki bata zo ba.
Lamido har asibiti ya zo, kwanana daya aka sallamoni
zuwa gida. Tun a ranar Lamido yasa aka kada Sa aka
yanka, nima yan uwana washe gari suka zo tare da su
Rahma.
Abubakar tamkar ya goya ni don kauna. Ranar suna
kuwa fadar shagalin da akayi bata baki ne.
Kyauta dai mun samu Masha Allahu, nayi kyau mai zane
fulawa ta yarfa min nayi kyau har na gaji.
Mun sha hotuna, Abubakar kuwa da abokansa tare akayi
suna dasu.
Na cii gaba da shayar da yarana kuma ana basu madarar
M.S.A, suka yi tubarkallah.
Mijina kullum kara son mu yake. Fadi kuwa na sama
kanta damuwa, kullum ita kenan fada da miji ko a gaban
waye sai tayi ta karta masa rashin mutunci.
Yanzun ma sun raba jiha da Rukayya, dangin mijina
tamkar su cinye ni don so.
Tunda na gama service na samu aiki a gidan TV na Yola,
amma Abubakar ya ce sai yara sunyi kwari.
Ban ja musu ba, watansu shida na soma zuwa aiki na,
bayan ya mallaka mana mota ni da Fadi kowa da tashi.
Bani da matsalar rainon yarana don rubibinsu ake yi.
Account na bude ina zuba albashi na. Domin akwai burin
da naci dasu, tunda ba abindana nema na rasa.
Daidai da katin waya sai Abubakar ya zuba min dubu
biyar dubu goma, nayi kyau da ka ganni kaga matar so.
Gyaran jiki kuwa da sabbin girki ba a magana. Shi kanshi
mijina duk wanda ya kalle shi yasan matarsa tana son
shi.
Kusan in mutun yana cikin kwanciyar hankali daka kalle
shi zaka gane, musamman namiji.
In kaga namiji a hargitse a rame ton ba halittarsa kenan
ba to kila bai dace da mata ba.
Duk ranar da babu aiki na kan ce ya kawo min Nana
Fiddausi, ina son yarinyar don ina son mace.
Fadi bata son ya kawo mata 'yarta gurina. Amma
bayanda zata yi, tunda baza ta iya hana shi daukar
'yarshi ya fita da ita ba. Sannu a hankali rayuwa tana
tafiya kwanukan mu suna karewa, lamurra suna
canzawa.
A hankali na rika dora mijina kan hanyar taimako dukda
cewa yana yi dama.
Lokacin da ya gina sabongida Lamido yace ya saka ni a
ciki saboda ya yarda ni na zama daya daga cikin
zuri'arsu.
Na cancanci in sakata in wala a zuri'arsu, komai sabo ya
saka min, gado dan italiya, kujeru na alfarma, kayan kicin
na gani na fada.
Itama ya sa aka mata fenti ya canza mata kayan
daki.Nayi walima ta alfarma har su Rahma sai da suka
zo, gidan ya tsaru harda gurin wasan yarana.
A ranar farko da zamu kwana a gidan yana zaune yana
waya a bakin gadon dakinsa na alfarma.
Na shigo sanye da kayan bacci, da hannunshi ya nuna
min cinyarshi in zauna, ya ce "Alhamdulillahi, gida ya
dace dake."
Na ce yanzu saura ka gina dakin Allah (Masallacin
Juma'ar) ungwar nan ka sabunta shi. Sannan ka gina
wanda za a dinga kamsus-salawati, a wannan layin da
muka dawo.
Ya ce "an gama gimbiya, yanzun sai ki zabi wanda za a
ba kwangilar ginin."
Na ce duk wanda ranka ya kwanta dashi. Mai amana."
Ya ce "To zan duba." Hakan ce kuwa ta faru nan da nan
aka soma gini.
Taimako marasa lafiya, gajiyayyu da marayu duk na
kwadaita masa yasan zakinsu. Yana mutunta iyayena
tare da taimaka masu.
**********
Shekarar yarana daya da wata biyu, naji ban gane kaina
ba. Hankalina ya tashi matuka. Ranar Abubakar yana
gidan Fadima, na mashi text cewa zanje asibiti, ya ce
Hassan ne ko Hussaini ba lafiya?
Na ce "Ni ce" ya ce sai ga kiran shi, ya ce meke
damunki the only? Sai kawai na saka kuka na kashe
wayar.Minti ashirin sai gashi ya zo. Kayan bacci ne ma
a jikinsa, me aiki na ya samu tana kara goge kicin.
Ya ce "ina take?" Ta ce ina ciki sai gashi na tasa
'ya'yan idanuwana jajir, ya ce wai lafiya? Na soma
sabon kuka, ya zauna ya jawoni jikinsa yana lallashi na,
wai in fada masa meke damuna?
Na ce nifa banga al'adata ba, ya ce ban gane ba? Na
ce ina da ciki ne fa gashi kuma ban yaye su Hussaini
ba.
Sai naji ya hau fadin Alhamdulillah, Allah ya amshi
addu'ata, don Allah wannan karon ma don Allah twins,
na harare shi banfa yaye yarana ba.
Ya ce goben nan za a yaye su, na ce tab! Wata ashin
da uku fa zasu yi. Ya ce "in basu yi kani ba ba?"
Na ce ni dai zanje a bani magani." Ya fita ya ce "Me
kika ce?" Nan take ya hada girar sama da ta kasa.
"To shike nan kije ki cire" ya fita washe gari na tsi da
amai, na sheka shi har na gaji.
Nayi ta kuka karshe na kira Rahma na fada mata, ta ce
lallai Hafsat samun guri, ni yanzun dakyar na samu
Allah ya bani kinsan dai yawon asibitin da nayi. Amma
yanzun don Allah yayi maki kyauta shen zaki butulce?
To kiyi kokari ki batawa mijinki rai. Sai ta kashe
wayarta. Ina kwance jikina zazzabi yaran nata kuka ko
wanka ban masu ba.
Ranar shine yayi masu wanka ya shrya su, sannan ya
zuba su cikin mota da abincin su, sai gidan Dada ya ce
mamansu bata da lafiya ina ga ma yaye su za a yi, ta
ce me yake damunta?
Kai tsaye ya ce ciki ne, tana can tana tana ta kuka ma.
Ni dai na kawo su zan kawo kayansu. Dada ta ce to
Allah ya bata lafiya.
Gidana ya dawo yayi ta lallashi na.
"Haba Hafsat, ke da nike kallonki mai ilimi da sanin
yakamata? Bai dace kiyi irin wannan tunanin na jahilai
ba.
Kinsan matsayinki a gurina? Duk yanda kike tunanin
matsayinki ya wuce haka a gurina.
Kada ki zubar da kimar ki a idona, ina alfahari dake,
kuma yayin da kike haifa min 'ya'ya lokacin ne nake
kara so da kaunarki."
Kunya ta kamani, lallai naso nayi wauta. Yanda mijina
ke nuna min baikamata inyi masa haka ba.
Ni da na kasance mai bada shawara ba girmana bane
in yi haka, don haka sai nace kayi hakuri Mr Cool.
Tausayin yaran ne."
Ya ce "yanzun ma kayansu zaki hada suna gurin Daada,
mu kuma sai muyi rainon wannan ko?
Na ce ya zaka kaima Daada aiki, kasan fa barna suke
dashi." Ya rike tafin hannu na ya ce "ni suka biyo Dada
ta ce lokacin da ina yaro nayi barna, ai kin san kuma ga
Ummi ga Rukayya ina kaisu kowacce ta zabi nata, na
ce Allah ya raya su."
Fadi taji cewa an yaye twins sai ta zargo ko ciki ne
dani, don haka hankalinta ya tashi.
Har gida sai gata da yake bata taba zuwa ba, tayi ta
bin ko ina da kallo, sannan daga bisani muka gaisa.
Na ce "Maman Nana yaune kika taba zuwa gidana."
Ta ce "to bama zama ko nazo kina gurin aiki, nima
haka." Na ce "Amma koda dare?" Ta ce "da dare kowa
ya gaji, yanzun dai ba gashi nazo ba."
Na ce to na gode" ta ce "can naga su husaini a gidan
Daada, wai an yaye su, na ce me ya jawo maki yaye
yanzu?"
Na ce Abban su ne ya kwashe su ya kaisu. Ta tabe
baki lallai sweet heart shine lokacin da zan yaye Nana
ya hau yayi ta fada.
Na ce to ai kinga ita mace ce, dole ya tausaya mata, ta
ce kodai kin sake kunsar wani cikin ne?
Na ce to inma hakan ne meye aibu tunda mijina na so?
Ta ce kedai fadi gaskiya, kina son kiyi ki cika gida da
yara saboda kiyi gado."
Ta mike tsaye, "kiyi haihuwarki a sannu dan mu
mungaji kudi, so kinga banda matsalar su.
Na ce gaskiya ne baki da matsalar kudi, shi yasa na
ganki zaune a gida bakya zuwa aiki, sannan suna nan
cike da daki a gidanki sai dai ki bude ki diba.
Ta ce "inma kina yi min ba'a ne nasan dai na fiki." Ta
fita fuuu, na ce "sauka lafiya."
Tare muka je asibiti dashi, inda likita ya gwada ni ya
tabbatar cikina wata uku. Kuma lfy lau, sai murna gurin
mijina.
Munje Umara tare harda ita, haka nan aikin hajji lokacin
cikina ya tsufa.
Mun dawo bada jimawa ba ba haihu, 'yar budurwa mai
kyau, tamkar inyi tsalle don murna.
Ina son 'yar budurwa, itama anyi sha'ani, don lokacin
Abubakar ya kara zama (Don).
Yarinya taci sunan Daada, Abubakar yace ya yarda in
kana taimako Allah yana taimakonka.
Budi ta ko ina, sai yanzun na binciki kudin account
dina, lallai kudi wawaye ne, in da zaka tara su zasu
taru, don haka na kuduri niyar yin abinda zanyi dasu.
Kaduna naje yawon arba'in, na dauki babana na kaishi
aka yi masa hoton fita, wato international passport.
Lokacin aikin hajji kuma na biya masa. Abubakar ya
fara min fada wai yana cikin lissafinshi a bana zai biya
masu.
Na ce yayi hakuri alkawari na dauka, SANADIN BOKO
sai na kaishi makkah.
Ya ce "Allah ya biya ki" shi kuwa baba da na fada
masa na biya masa kujera da kudin aikina sai ya sa
kuka.
Ya ce gashi SANADIN BOKON nan da nayi ta tsana
zanje daki Allah, inda ban taba zaton zuwa ba.
Ki yafe ni Hafsa, tuni na gane boko ba dukka ta ba ce
illah, tana da amfani."
Ya ci gaba da cewa Hafsa na gane hakan ne ta hanyar
taimako da wata likita mace tayi ta mun lokacin da na
kwanta a asibiti.
In shaa Allah su Ummi zasu yi karatun boko, dama dai
na addini wajibi ne, zan bisu da addu'a Allah ya tsare
su yasa su sami ilimi mai amfani. Ya raba su da sharrin
ko hadarin da ke cikin boko, na ce ameen Baba. Ya ce
in da zaki yi adalci Innar ki ya dace da wannan kujerar,
don ita ce tasha wuyar iliminki."
Na ce "ita ma Abubakar ya bata kujerarta da Yayana
Umar, kai nidai na gode Allah da nasha