Showing 66001 words to 66982 words out of 66982 words

Chapter 23 - Fuska Biyu Book Complete By Halima K Mashi

05 Jun 2025

5446

cuce ni ka koya min yadda zan soka a
karshe ka tsunduma ni cikin kogin sanka sannan
ka sake ni, ban yafe ba. Yace haka kika min. Na
tafi na rasa inda zan nufa.
[7:59PM, 17/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: Fuska Biyu 2----15
Karshe
Gidansu naje a tsakar gida na saka ihu da gudu
su momy suka fito dasu anty cikin kuka nake
fadin ya umar ne ya sake ni. Saki? Inji momy.
Shiru abba yayi, anty tace me ya hadaku? Nace
ni ban mishi komai ba shine yace wai ba ya sona
yanzun ya samu wata. Momy tace anya bai samu
matsalar kwakwalwa ba hadarin nan? Abba yace
ku shiga daki bari na neme shi a waya. Muna
daki sai kuka nake ba ran ma da nonuwana suka
soma zuba wannan alamace ta junior ya tashi,
nace momy dan Allah ku bashi hakuri ban san me
nayi mishi ba yaace ya sake ni, in ma auren zaiyi
ai ban hana shi ba, momy tace to ya isa haka yi
shiru, abin da kara firgita ni shine duk wayoyinshi
a rufe. Ya kira aliyu ya kai shi gidan ya umar
amma maigadi yace musu ya dauki mota ya fita,
kwana nayi kuka damke da takarda a hannuna.
143-Da safe kam labari ya kai gidanmu. Abba da
alhaji a falo suna tattauna yadda za'ayi. Abba
yace anty amarya ta kira ni suji ko saki nawa ne.
Ta same ni momy tana ta min fadan kukan da
nake ta ce ai yazo ma sai ya kara raina miki
wayo. Gara ma ki daure ki nuna bai dame ki ba.
A raina nace momy ba zaki gane bane, samun
kamar ya umar zai min wuya. Anty tace su abba
suna kirana shima ya umar din sunci sa'a ya
kunnan wayarshi kuma sunce suna neman shi
yanzun nan. Kizo da sakin saki nawa ne? Fuskata
duk ta kumbura cikin kuka nace bansani ba. Na
dauko takardar kan madubi da zanyi sallah na aje
ta don hannuna ta kwana muka tafi har momy
tana cewa muje zai ga fushina yau. Muna shiga

yana shigowa, wani kyau naga ya kara min
shigar kananan kaya ta kara maida shi matashin
yaro ya zauna. Momy dake zaune kusa dani ta
zungureni ta baya alamar wai in daina kallonshi.
Na sunkuyar da kai can na kara kallonshi sai ya
min gwalo. Abba yace yanzu umar abin da kayi
yayi daidai kenan? Yace me nayi abba? Momy
cikin fada tace ina fa zaka sani, shiyasa nace a
caji kwakwalwarshi. Alhaji yace duk ba haka ba,
yanzu ta kawo takardar saki nawa ne? Na mika
musa. Abba ne ya fara dubawa, tsaki yayi sannan
ya ba alhaji. A raina nace shi kenan uku ya min.
Na kalle shi ina sabon kuka shi kam dariya yake
yi. Alhajin ya mike sun maida mu 'yan iska ne ma
yaran nan. Momy tace saki uku ne ko? Alhaji ya
bata gashi ki gani itama ta mika ma anty amarya
ta fita. Dariya naga anti tana yi ta fita duk sun
bar mu. Na dauki takardar a hannun kujera in da
anty ta ajemin na soma duba ko saki nawa ne?
Sai naga ya rubuta:
144 “Ni Umar faruk na kara nunka igiyoyin
aurenmu, ba saki ba yaji. Ina son matata shin
tana sona?� Na mike ina kallonshi yana min
dariya nima dariyar nakeyi fuskata ga hawaye. Ya
iso gurina ya rungume ni na dan mihsi dukan
shagwaba a kirji nace kai ko? Yace sorry kin son
umar ko? Nace ina sonka sosai. Ta kofar waje
muka fita ba tare da na koma cikin gidan ba
muka je muka bude sabon shafin soyayya da
rayuwa mai dadi.
145 Na fito daga cikin mr biggs ina tare da
yarana, sayyida da sayyid 'yan shekara biyar
suna dauke da kayan kwalama. Junior yana da
saurin girma don ya kamo 'yan uwansa, sai yaron
cikin da nake dauke dashi muka nufi gidan
rahma. A hanya ya umar ya min waya ina dauka
yace kin zama matar general gobe za'a tabbatar
damu, sai ku shiryo kuzo akwai shagulgula.
Murna ba'a magana. Ya umar yana da sa'a duk
cikin wadanda suka samu wannan mukamin ya
umar ne mai karancin shekaru. Gurin dinner ne
mata suka so su minkwace don haka na manne
mishi. Munsha dauka gurin 'yan jaridu da kuma

tambayoyi. Ranar muna kwance wata number sai
kiran min miji ake yaba dauka sai naga yana
kallona. Ana sake kira na dauka muryar mace naji
tana cewa don Allah ka taimaka min ciwon sonka
yana damuna, nace sai dai ya kashe ki, miji nawa
ne ni daya. Yace haba asmy yaya zaki kashe min
kasuwa? Na harare shi na tashi xan fita ya kamo
ni Allah ni naki ne ke daya, da ace ina kula mata
da nayi goma yanzu. Na dube shi bana son
kishiya fa kaji mijina? Zo muyi wata hira mai dadi
ki bar batun kishiya ke kina wadatani baki hanani
abin da zai sa inji sha'awar wata. Kina wadata
ni, zokiji wani story kanwata. Yau asibitoci muka
nufa don kai taimako ga marasa lafiya. Ya umar
kan ware kudi duk wata uku dan taimaka ma
al'ummar annabi. Yace yau zan rakaki asmy nima
ina son samun ladan ziyara. Kai fa ke bada kudin
gurin 'yan HIV, muka soma a bakin gdon wata
mata na tsaya jin tana cewa soja, baiji ba nace
ya umar, farida ta fita hayyacinta ta koma
kwarangwal. Duk wannan kyan babu shi ya gudu,
ta soma kuka tana neman gafara. Yace yau ga
sakamakona kuma kinga yadda Allah yayi dake,
dama kince da sannau zanga yadda Allah zaiyi
dake. Ya fita nima na bishi. Ina dukiyar da ta
tara? Ina iyaye da 'yan uwanta? Duk sunki ta da
ko itace ma shanawa a dangi. Mu kam soyayya
akalar rayuwa, dan iyaye sun miki zabi kada ki ki.
So da yawa yana zama alheri.
Tammat bihamdulillah.
THE END!!!

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0