Showing 9001 words to 11539 words out of 11539 words
Chapter 4 - Auren Dole Book Compelet Yar Mutan Dikkawa
madou yazo da hanzari hannunsa,dauke da langa,ya mikawa kakan Nsu,Ya ce
Gashi nan inji malam tankari,"ya ce,abata tasha awanke mata fuska,"
"Madallah Baba mallsm,yace tare da ba lami,taje takai rubutun taimakon haihuwa aba Asma'u
tasha."
"Amsa tayi ta shige dakin tare da sallama da su sahura da ke kokarin wucewa,Yusuf ko abinda
duniya ya dameshi fatan shi Asmau ta sauka lafiya."
[1/10, 11:05 AM] Nordin: SHAFI NA SHIDDA
****************
"Alh.kalle agadon Asibiti,sai dai Addu'a!Saboda ciwonsa ya tsananta,Komai baya iya yi sai
an masa!duk gefen jikinsa na dama ya mutu!!!"Iyalansa sun sha kuka har sun godewa
Allah,Gashi baya kula yan uwansa shiyasa suka juya masa baya!"Ba mai zuwa gidansa ko
yanzu asibitin ba Wanda ya zo!"
"Cikin hutuncin ubangiji bayan tsawon awowin da Asma u ta dauka tana nakuda,Tasha wuya da
azaba!A karshe ta haiho 'yartah qatuwa,wacce nauyinta da ya wuce misali,Bayan likitoci sun
gama gyara Asma'u da yartah,Dakin hutawa aka wuce da su."Su uwani sun zo sun duba
yarinyar cikin murna da godiyar Allah Asma u ta sauka lafiya."
"Bayan mintici gab da magariba qannan lami suka bayyana a asibitin da su Gwaggo husai da
Mariya suna farin ciki agefe suna tausayin Asma'u tare da zagin Alh.kalle,anan sukaji labarin
shima bayada lafiya."
"Mutuwar Kamilu,ta kasance abin cecekuce a cikin gari!Kowa da abinda yake
fad'a,Wanda a haqiqanin gaskiya,Maganin bera ya sayo a kanti,ya sha saboda ciwon so da
kaunar Asma'u wacce aka raba shi da ita akai mata *AUREN DOLE* da Alh.Kalle,"
"Innar Kamilu tayi kuka kamar ranta zai fita,yaro mai hankali kamar kamilu ace ya kashe kanshi
saboda macce,Abin ya kona mata rai!"Saboda ba halinsa bane!"Kowa ya sanyi da
nutsuwa!"Wannan kaddarar ta afka masa."Rarrashinta yayyensa da 'yan uwanta keyi!yan gulma
ko sunzo daukar rahoto!"Nan ne wata makociyar su Balki ta ce"Allah dai ya sauwaqa ya Baku
hakuri malkah,Abin nan shi kadai ake yi kuma duk fa wannan masifa akan *AUREN DOLE* Ku
duba nan shekaranjiya wata yarinya ta sanya hetur ajiki tasa ashana ta kone kanta akan
*AUREN DOLE* da iyayenta zasuyi mata shi kuma saurayin yana jin labari ya kashe Kansa!!!
"Ke balki yaushe wannan labarin ya faru wata mata ta tambaya cike da mamaki."
"Wacce ke kusa ga balki tace wallahi ko nan garin ga anyi shi kun mance yarinyar nan Asabe
yar gidan dillaliya...da tasha guba akan za'ayi mata *AUREN DOLE* tanada Wanda take
so,shima faah ance yanada sana'arsa da yasamu labari,duk kudaden dinkinsa gina yayi ya
turbudesu aqasa sannan shima ya sha guba ya mutu!sai lahira."
Kuka inna malka ta fasa tace kaicoh!yanxu shima kamilu za a fara jera shi acikin masu kisa
Kansu akan soyayyah Allah ka yafe mai ya Allah!!!!"
"Kiyi hakuri malkah,wannan kaddara ce!kowa da tashi!haka Allah ya nufa da shi!Domin kowa na
yabonsa, Allah dai ya yafe masa!"Inji qanwar ta."
"Ameen sauran jama"ar wurin sukace."Nan dai suka cigaba da hirar su da yan gulmace
gulmace da yake yanzu an mayarda gidan ta'aziyya kamar gidan buki,Yanzu zaman ba yada
wani amfani,ba asamu lada ba akwashe zunubi,Hattara mata!!!!"
"Baba mallam ne,Ahanyarsa ta dawowa daga asibiti Wanda da kyar dansa Yusuf ya
rarrashe shi,akan yadawo gida ya huta,tunda ma'u tana bacci,kuma tasamu sauki har zuwa
gobe, ganin dare yayi."yana shigowa unguwarsu wato Allugu,majalisin su ya biya cikin sa'a
yasamu su mallsm Iro,da dauda suna fira!"Da Sallama Malam Buba,Ya isa tare da musayar
gaisuwa da su malam Iro."
Mallam Iro,Ya ce lafiya yau duk bamu ganka ba!?"
"Ina lafiya!Ma'u ce kwance a asibiti!"
"Ma'u ko mijinta Alh.Kalle!?Shi mukaji labarin ya fadi rai a hannun Allah!"inji malam iro.
"Mallam Buba,Ya ce"Haihuwa ce ma'u tayi shi kuma ance ya hado da mutuwar barin jiki!"
"Malam Dauda dake gefe zaune ya ce "Allah ya sauwaqa."
''Ameen,Dauda inji Baba mallam."
"Mallam iro ya kalli amininsa cike da damuwa yace "Ashe yaron nan kamilu ya rasu,kanada
labarin maganin bera yasha akan jikar ka ma'u da kace har abada shi da ita!"
"Haka naji ana fadi agari shi ya mutu kafiri ba wani ba!Allah ya qaddaro Ma'u ba matarsa bace
haukar banza ce sukeyi,kuma duk Wanda yace ni ko jikata ne sanadi Allah ya isa!"Mallam Buba
yace ahasale!!!"
"Allah ya bamu hakuri Buba kasan ita duniya daman budurwar wawace!"Inji Dauda.
"Kaga ni daman tahowa niyyi na ganku mu gaisa daga asibiti nake,zan wuce gida na kwanta
duk jikina ciwo yake!!"sai gobe idan Allah ya kaimu
"To Buba agaida gida Allah ya huce gajiya ya basu lafiya!"Inji Iro
"Ameen,Buba yace kana ya nufi gidansa."
**************
"Najibullah da amaryarsa Yaseera ne,suka kawowa iyayen su ziyara,Amarya an sha kyau cikin
shiga ta alfarma,fuskarta sai haske da sheki take cike da annuri,kyaunta ya qara fita tayi jiki
gwanin Sha'Awa,Da zarar kayi tozali da yaseera da najibullah zaka fahimci akwai zaman lafiya
fahimtar juna da kwanciyar hankali arayuwarsu,Shi kanshi Najibullah,ya qara cika,kwarjini ya
wadace shi,Hankalinsu akwance."
"Bayan sun gaisa da iyayen su sun sanya masu albarka cike da farin ciki,cike da murna suka
nufi gidansu yaseera nan ma sukayi sa'a kowa na gidan,A babban falon suka same su har
yaseer da matarsa Raudhat tana cin Dan wake batada lafiya ta kamu sai kwadayi da sangarta
take ma su Umma,suka ma sai rarrashinta ake komai takeso shi ake mata."
"Bayan sun gaisa umma ta kira Abbu shima ya fito,Gaisawa sukayi sunyi farin cikin ganin
yaseera a kamile,batada wata damuwa,nan fa najibullah da yaseer suka samu wurin fira,Umma
madafa ta nufa domin shirya musu abinci,Abbu ma kanti ya wuce domin sayo masu kayan
masarufi azuciyarsa yana godewa Allah akan zabin da yayiwa yarsa,Yaseera tuni yawunta ya
tsinke ganin qawarta bata sammata Dan waken ba,yasa ta dauke kwanon duka tayi hanyar
madafa tana ci tana dariya."
"Bayanta Raudhat tabi tana mitar ta bata kayanta ba dandane."
"Yaseera tace "nasan ke kade ce mai cikin,to nima ina da lalurar kwadayi."
"Umma suka samu tana daura sanwa,Kallon su tayi tana murmushi tace"toupha kun fara
ko!?"Shin ke yaseera bakisan batada lafiya ba!?"Dan Allah ki daina wahaladda ita, ki bata Dan
wakenta duk kin kusa cinye mata abu,naga dai yanxu yayarki ce ba qawa ba,to raini na meye!?"
"Raudat tayi dariya tace yawwa ummana gaya mata"
"Dariya yaseera tayi tace''Yanzu Umma,akan dan waken yaya babba ake min hakan!"Nima fa
ina son sa,kuma ta ci fa,Amma ba komai nima zance surukar tawa tayi min,sai ma yafi naku
dadi!"
"Munji Raudat,tace tana yiwa yaseera gwalou,
"Nan suka hada hannu suna taya Umma girkin faten tsakin masara da kayan lambu."A lokacin
ne ma umma ta fahimci ko yaseerarta ta kamu saboda yawan rufe hanci ba qamshin komai
takeso ba da zubarda yawo,Ta ce yaseera kenan kema sai ahankali!?"Sunkuyar da kanta tayi
cike da jin kunya."
"Umma tace lalle zan qara yiwa Abbu albishir na biyu kenan,Allah ya saukeku lafiya yabaku
zuriya dayyaba ya qarou arziki da farin ciki arayuwar ku,Tabbas muna alfahari da samun Ku
amatsayin yaranmu,Allah yayi muku Albarka."
"Ameen,Umma sukace dukkan cike da jin dadin kalamanta,sannan suka cigaba da ayyukan su."
_Allah Sarki,Hakan rayuwar Duniya,take yadda duk ka dauketa da sauki,ko wuya,sai tazo
maka ahakan,Zabin iyaye ba aibu ba ne,idan har kayi dace da zabi nagari,Hadisi ne
ingantacce,Annabi Muh'd (S.A.W) yana cewa "yardar Allah tana tare da yardar iyaye,haka
fushin Allah yana tare da na iyaye"Shiyasa aduk lokacin da iyaye suka baka umurni,to ka
umurnin matsawar ba sabon ubangiji ba ne,Domin babu d'a 'a ga abokin halitta wurin sabawa
Allah."Saboda hakan mummunan umurni kawai iyayenka zasu saka aikatawa,ka girgiza,musu
koshi acikin sigar rarrashi da nasiha,Babu auren Dole,Domin Hakkin iyaye ne su zabawa yaran
su maza nagari masu ilimi,mazan da suka yadda da addinin su,da kuma nasabar su tsakani da
Allah.Ba domin kwadayi ko buri ba,Saboda wajibi ne suyiwa yaransu Adalci."_
_Abin lura anan duk lokacin da D'a ya bi umurnin iyayensa sai yaga haske arayuwarsa sannan
aduk lokacin D'a yake baqantawa iyayensa sai duk al'amuransa su jagule!"Ita Tarbiyya abu ne
mai Kyau,arayuwa muyi kokari mu kasance yara nagari wadan da duniya zata yaba!"Kuma
iyaye suyi alfahari su,Duk abinda kayi khairan ko sharran kada ka manta yana bibiyar
rayuwarka da zuriyarka,Auren zumunchi,Auren Abota,Auren Hadi da sauran su duk sune aka
rikede aka mayar *AUREN DOLE!* Saboda da wuya asamu dukkan yaran nason junan
su,Daman karshen wuya sai dadi,kuma dogaro ga Allah jari ne,Kunga yadda Yaseera da
mijinta najibullah suka kasance abin alfahari ga iyayen su,suka samu jarin rayuwa da haske mai
daurewa arayuwarsu dalilin biyayya,Allah yasa mudace Ameen._
*********Tunda Asma'u ta dawo hayyacin ta,take kuka har yanxu takasa hakura da mutuwar
kamilu!"'yan uwa da dangi sai hakuri suke bata."
"Bayan kwana biyu aka sallameta suka dawo gida!"Sai dai sabon ciwon da ya bayyana agareta
bata iya riqe fitsari ko da aka koma asibitin ciwon yoyon fitsari ya kamata aiki akai mata tare da
bata magani!"A hakan ta cigaba da fama da lalurar,Bacin rai da suke ciki itada iyayenta baya
misaltuwa,
"Kishiyoyinta sunzo duba yarinya,Da diyan Alhaji da ke jin haushinta domin aganinsu itace
sanadin ciwon mahaifin su,Da kyar da rarrashi suka zo gidan su Asma'u,"
"Abokin Alh.kalle ya kawo ma yarinya kaya Asma'u zanen atamfa uku,da rago ayanka ma
yarinya."Duk acikin kudaden Alh.kalle da ke kwance asibiti babu bakin magana."Gashi yaran sa
uku maza suka sako yana kwancen ba lafiya yanzu hakan suna nan zaman gida,mutim dayan
ma nata na garaje!"Ga yammata biyu ba mazan aure!"Banda nadama tare da danasani ba
abinda ake hangowa acikin idanuwansa da ke zubar da hawaye ba dare ba rana."
_"Daman ance idan zaka gina ramin mugunta....."Duk abinda kayiwa Dan wani sai anyiwa
naka!"Kayi kokari ka Gina rayuwarka da ta iyalanka akan turbar gaskiya sai kaga sakamako mai
kyau,Idan zakayi kayi Dan Allah haka idan zaka aikata kayi Dan Allah,Kasance mai Sara kana
duban bakin gatari!"_
"Ranar suna yarinya ta ci sunan (Anna) wato Amina sunan kakar Asma'u Wanda mahaifinta
Yusuf yayiwa innarsa takwara!"Duk jama'ar gidan sunji labarin Alh.kalle ya saki Asma'u yanzu
kuma ta haihu ta gama iddah."
"Mallam Buba ya tausayawa rayuwar da ma'u ke ciki ga raino ga fama da cutar da ke
damunta,Yayi kuka da nadama aganinsa kamar shine sanadi!"Saidai ana cigaba da nema mata
maganin asibiti Dana gargajiya."
"Bayan wata daya abubuwa da dama sun faru,Wanda akarshe mallam buba yayi kokarin kashe
duk wata fitina da ta kunno kai agidan makera,da gulma tayi yawa acikinsa,ya hada kan
iyalansa duka komai ya zama tarihi,Kuma yace''Daga Asma'u ba zaya qara tilasta Iowa
*AUREN DOLE!* ba sai dai da kashedin duk Wanda za a kawowa to akawo mai kirki da
ilimi."Idan akasamu sabanin hakan bazai aminta ba!"
"watarana da safe mallam Buba ya fita majalisar su, malam Dauda ya samu shi kadai zaune a
teburi yana shan kunu,da kosai,da yake yanayin sanyi ne,hantsi na rasa jikinsa,Bayan sun
gaisa ne,Malam Buba,ya rokeshi akan ya yafe masa duk abinda yake masa,Dan Allah yayi
hskuri!saboda ada can baya ya kullace shi,kamar yana bakin cikinsa,sai yanzu ya gane!kuransa
na tilastawa Asma'u auren da bataso domin gashi akarshe abin baiyiwa kowa dadi
ba!"na tabbata kai mai sona ne,domin masoyinka kadai ke gayamaka gaskiya!"
"Murmushi malam Dauda yayi yace komai ya wuce malam Buba daman naso ace ka fahimce ni
amma giyar kudaden da Alh. Kalle ke baka,ta bugeka bakaji baka gani sai yanzu ta
sakeka,bayan wasa takarewa Dan kada!!"
"Shi *AUREN DOLE* Da kake gani mallam Buba akan gina shi ne abisa tilasta yaro auren
Wanda bayaso kamar yadda kayiwa Ma'u!"Sannan mafi yawan lokuta akan samu banbamcin
ra'ayi ko shekaru masu yawa tsakanin ita yarinyar da Wanda aka tilasta mata aure."kamar
Alh.kalle mai shekaru sittin da ma'u mai shekaru sha bakwai warin yarsa ta kusan biyar,Sannan
son abin duniya shine son dukiya gaba da soyayya,irin wannan aure ana yinsa domin
tsammanin asamu dukiya,ko hanyar samunta,Yanzu mallam Buba kaga duk abinda kasamu ka
Tara adalilin auren ma'u yanzu yaqare gurin nema mata magani!"Meye amfanin badi ba rai!!"
"A ganina *DALILIN da ke sa AUREN DOLE!*
*sune idan akayi la'akari da iyayen yaro ko mijin suna da nasaba.*
*Anayinsa domin kasancewar yaro jarumi.*
*Anayinsa Dan kara dankon zumunci ko abota.*
*Anayinsa domin kwadayi da son abin duniya!*
*Anayinsa domin rashin Sabin hakkin 'ya'ya.*
*A karshe anayinsa idan anga yarinya tafara lalacewa.*
"Mallam Buba anan ni nasan cewa kaima kasani Alh.kalle kowa yasan cewa ba'san asalin su
ba!Taho nataho ne!"Sannan baida mutunci,auri saki yake!Kuma kasan ya tsofewa ma'u
sosai,Ance hadda sallah bata dame shi ba!"Amma ka hadashi da yarinya kamila mai kirki wacce
dubban mutane sun yaba da hankalinta,ka rabata da Wanda takeso yake sonta!"
"Wallahi Dauda na tuba!"Yanzu meye mafita!?"Malam Buba ya tambaya cikin damuwa!"
"Malam Dauda yace *"MAFITA* daya ce shi ne Mallam Buba
*Adinga yin Aure domin Allah.*
*Asan Hukunce-Hukuncen Aure.*
*Ladabtar da mata kafin aure*
*Sannan Adaina tilastawa 'ya'ya Auren Dole!*
"Kaga yin hakan shine mafita!"Buba
"Tabbas haka ne nagode Dauda kuma daga yanzu nayi karatun ta nutsu!"Domin ga ma'u nan
da ciwon da bamusan raner warakarsa ba!"inji malam Buba yana share kwallah!!"
"Allah ya sauwaqa!zanje na karbo kekana wurin tanko mai faci!Iska nakai asaka min tun jiya da
dare,malam Dauda yace yana kokarin tafiya!"
"To nagode!Dauda sai ka dawo,malam Buba yace,nan ya cigaba da zama shi kadai yana
nazarin zantukan Dauda."
"Bayan wani lokaci Asma'u ta warke harda Ameena ta yaye tayi wayonta,wacce tuni mahaifinta
Alh.kalle ya amsa kiran Allah."Asma'u har tayi aurenta da wani Jamilu duk da auren soyayya ne
tayi da shi amma zaman hakuri takeyi agidansa!"Nan taga izina domin auren Marigayi
kalle,tace auren dole ne!"Gashi yanzu tayi na soyayya da Jamilu bawani dadi takeji ba!"Sai dai
hakuri,Tabbas kowane aure,"Aure ne addu'ar nagari shiyafi dacewa ga kowacce mace!"
_Hattara mata da maza masu kokarin hallaka kan su,kashe Kansu,shiga duniya duk akan
*AUREN DOLE!* ya kamata kuyi karatun ta nutsu kuji tsoron Allah Ku gujewa sabawa Allah,Ku
daina bijirewa umurnin iyaye,matukar kuna son ganin haske da cigaba arayuwar Ku."Wannan
shi ake kira da "JIRWAYE NE!MAI KAMAR WANKA,SAi naga Kuma ai gyara kayanka ba sauke
mu raba ba!"Amma fa tun rana gini ran zane! Haka komai Nisan jifa qasa zai dawo!ALLAH YAYI
MANA JAGORA AMIN._
*_TAMAT BII HAMDILLAH._*