Showing 3001 words to 6000 words out of 11539 words
Chapter 2 - Auren Dole Book Compelet Yar Mutan Dikkawa
"Abu na biyu,Ya kyautata sunan sa,
Sai Abu,na uku Ya aurar da shi idan ya balaga."
"Yaseera mu baki ilimin addini da na zamani,kinsan yadda zaki iya bautar Allah kuma kinsan
yadda zaki kare kanki daga wuta.. "Domin Allah (SWT) ya ce "Acikin Alqur ani mai girma,"Yaku
wad'anda kukayi imani,ku kame kanku da iyalanku daga wuta,wadda take makamashinta
mutane da duwatsu ne!"Allah ya karemu."
"Ameen Abbu yace"cikin jin dadin kalaman matarsa,azuciyarsa yana alfahari da samun mace
mai ilimi amatsayin uwar yayansa..."Muryarta ta katse masa tunani.."
"Inda ta ce"sannan kinga Abbunki ya sanyawa maki suna mai ma'ana irin na addinin
musulunci,"Kina ganin sunaye,da yawa agari maras ma'ana wasu iyayen ko da za'a kashe su
baza su iya fad'in ma'anar sunan da suke kiran yaransu da shi ba,To ki godewa Allah yaseera
saboda ke da kanki kinsan meye ma'anar sunanki!kuma kinsha karanta alqur'ani,Kina ganin
yaseerah aciki."
"Kinga anan kowanne daga ciki munyi iya kokarin mu wurin yi maki biyun na ukun ne mukeson
mu cika da yardar Allah."
"Ni da Abbu saida mukayi shawara da juna kafin mu sanarda ke, Saboda haka ba wata
shawara da zakiyi daman dai nice babbar qawarki kuma abokiyar shawararki,Sai ki fad'a mana
ra'ayinki muna saurare..."Umma ta qarashe zancenta tana kallon 'yartah da sadda kai tana
sauraren jawabinsu."
"Duk da ba hakan taso aranta ba,Amma ahankali tunani ya fad'ou mata arai!"Cikin sanyin
murya ta motsa labban bakinta da sukayi mata nauyi,domin wata kunya da nauyin iyayenta taji
ya kama jikinta.."
"Numfashi tayi sannan tace ahankali"Abbu!"Umma"Ba abinda zance da Ku sai dai godiya!"Ina
rok'on Ku da kada kusake tambaya ta abu,idan zakuyi min,Ku iyaye na ne bai kamata Ku nemi
wata alfarma awurina ba,domin yi maku biyayya wajibi,Nasan Baku kaini inda zan nakasa
ba!kuna sona!Hakika kunyi min komai rayuwa,fatana Allah yaqara maku rai da lafiya,yasa ayi
karshe mai kyau."
"D'ago fuskarta tayi ta kalli,iyayenta Wanda hasken annuri da farinciki ya bayyana afuskokin
su,itama murmushi tayi tace,Ina alfahari da Ku,A kullum ina rokon Allah yasa inyi rayuwa irin
taku,Wadda dole sai nasamu miji,nagari hakan zata kasance Alhamdulilah Abbu ya zaba min
Alaramma najibullah,mai addi,mai ilimi,mahaddacin Alqur ani,Nagode Abbu,na yadda na
amince koda za'a iya kiran aurena da *AUREN DOLE* na tabbata agurina aure ne Wanda
iyayena sukaga yadace da ni dan haka agefena babu *AUREN DOLE!*."
"Umma,Tabbas ina da hakki akanku,Amma naku yafi yawa akaina,saboda duk abinda
yakamata kuyi mana kunyi mana shi.."Bazan manta Acikin suratul Isra'i,Allah (SWT)Ya
ce"Kuma ubangiji ya zartar da hukunci kar abautawa kowa sai shi,kuma dangane da iyaye biyu
Ku kyautata musu,ko da dayansa yakai ga tsufa to karkace dasu tir!"Kuma karka tsawace
su,sannan kuma ka gaya musu magana mai karamci."
Sannan Manzon Allah (SAW) yana cewa yardar Allah tana tare da yardar iyaye,kuma fushin
Allah yana tare da Fushin iyaye,"
"Dan haka umma
...Abbu nabi Allah da manzonsa,kuma na biku,kuma in shaa Allah zan cigaba da bin umurninku
tare da yimuku biyayyah har karshen rayuwata..."Yaseera tace cikin ladabi.."
"Ajiyar zuciya Abbu ya sauke yace Alhamdulillahi Alaa kulli haliin..Tabbas nasamu mata,kuma
uwa tagari wacce tayima yarana tarbiya tagari,Juwariyya nagode abisa namijin kokarinki akan
yaran nan,Domin kece mai kula da su tare da sanya ido akansu da duk wasu lafuzza dazAsu
fito daga bakinsu..."
"Umma tayi murmushi tace"Mallam kenan, ai Kaine ka karantar da ni har nike sanarda su,karfa
ka manta Kaine jigon gidannan...daga ni har su muna bisa turbar inda ka ajiye mu,wannan
tsarinka ne,kuma kokarinka ne,Domin ko kana gida ko baka gida,ka tsara yadda za a tafiyarda
rayuwa da kuma mu'amulat agidanka."Sai dai mu godewa Allah nida yarana da yabamu
garkuwa mai kyau,mai kuma inganchi amatsayin jagoran mu."
"Dariya Abbu, yayi yace Masha Allah, Ya kalli yaseera da ke wasa da zoben azurfa dake
yatsanta,Ya ce Yaseera....."
"TaceNa'am,Abbu tare da dagou kanta.."
"Ya ce,Allah yayi miki,Albarka kinji,Kuma yadda kikayi mAna biyayya Allah ya ba ki wadanda
zasuyi miki,Hakika akullum ina alfahari da Samun 'ya macce irinki!"Allah ya sanya alkhairansa
da albarka a lamarin nan."
"Ameen,Ameen."umma tace tana murmushi.."
"Yaseera murmushi tayi cike da kunya,sai Abbu yace zaki iya tafiya abinki.."Aykuwa da gudu
yaseera tabar falon."
"D'akinta ta fad'a,da yake cikin dakin falon umma yake,A falon,akwai dakuna uku, biyu da falo
na umma,dayan nata,Shi kuma Yaya yaseer nashi na daga waje,Abdul kuma nashi na daga
cikin falon Abbu,na shi daga gabas na Abbu daga yamma."Haka suke rayuwarsu kowa da
dakinsa daban agidan,mazan ba ruwansu da harkokinta itama bata shiga lamarin su,wannan
tsarin yasamo asaline daga iyayen su,Kuma wannan bai hanasu so da kaunar junansu ba,tare
da sanin girma da kimar kansu Sam babu raini atsakaninsu."
"Yaseera saman gadonta da ke dakin tafada wasu hawaye masu zafi da ta kasa bambance ko
na meye, ke zuba afuskarta!"Abincin da bataci ba!kenan adaren, duk da kasancewar tanajin
yunwa,Tashi tayi,bayi ta fada domin dauro alwala,sallah ta tada bayan ta fito,sai da tayi
Nafilfili,tare da azkharul naumy,sannan tayi shafa'i da wutiri,Akarshe addur ar istihara, ta
karanto tare da fatan wannan zabi yazamo mata nagari,sannan ta tashi, kwantawa"Har kasan
zuciyarta taji sanyi da nutsuwa yana yatsa dukkanin jikinta..."
*WANENE ALH.KALLE*
"Alh.Kalle babban dan kasuwa ne,da yayi suna agarin Argungu,Yana kantina da dama na kayan
masarufi."Yana da arziki kwarai da gaske amma kuma kowa yasan jahili ne,ba boko babu
mahammadiya,yana da mata uku a halin yanzu,wad'anda yake aure yana saki basu kirguwa,
saboda haihuwa yake rabuwa da su,Da zarar macce tayi ciki yagama da ita matsawar bazata
zubar da shi ba!"kuma da ya gama yayin macce shikenan,Duk da hakan yana da tsabar yara
goma sha bakwai,cikin daga wasu na hannunsa wasun kuma suna ga iyayensu mata."
"Alh.kalle Sam baida addini ko sallah da kyar yake cika biyar ayuni,Katon gaske ne ga girma ga
tsayi bakine wulik Wanda akalla zai kai shekara sittin adunia."Yanada yara yammata biyar da
sukayi aure har sun hayayyafa,harda ,maza uku,yayiwa aure,ko yanzu tare da diyan sa uku
mata za'ayi auransa,rana daya.zasuyi sa'annin Asmau"Bai da mutunci ko kadan,duk matansa
suna tsoronsa da shakkun masifarsa,Sakin mace da aurenta awurinsa yafi sanya hula da
sauketa akai sauki."Gashi da sakewa mata kudi awaje,amma da zarar sun shigo wayam,sai
wuya da wahala,yaransa kullum kamar almajirai saboda baya kula da suturunsu acewarsa
sunyi yawa,cishesu kawai aikine,Idan Alh.kalle yaga macce ya hadiye mata miyau to saidai
wani ikon Allah,Domin kudi zaisa ko da so ko da *AUREN DOLE* sai ta shigo gidansa."Hakan
ce tafaru domin tunda yaga Asma'u fara kyakkyawa yar kimanin shekaru sha takwas,ya liqe
mata tayi masa wankin babban bargo!"Tana tare da kamalu,shima ya ci mutuncin Alh.kalle,suka
wuce abinsu,shine yaji zafy!"Yayi alwashin rabata da kamilu,sai kawai ya mannewa kakanta
malam Buba akan sai ya aura masa ita,kudade masu yawa yake damkawa mallam Buba,Dan
kawai ya samu Asma'u wacce suke kira da (Ma'u)"
"Daman Hausawa sunce rana bata qarya, sai dai uwarda bata shirya ba,taji kunya."Domin yau
takama Assabar tun safe ake kid'e kid'e da wasannin Al'ada da kuma gadon gida wato na
mak'era,Kofar gidan mallam Buba mak'eri cike take timjin da yara matasa,da mutan gari,Mallam
Buba ansha babbar riga sai washe baki yake yana d'aga robar fanta sama,yana sha,shi da
abokinsa mallam iro ."Zaune suke akan kujerun roba da aka dazAwa mutanen da ke
zaune,kofar gidan suna kallon jikokin gidan dake wasa da wuta.."
"Hatta yara qanana yan kimanin shekaru bakwai,Da mazan gidan an zuba musu kalanzir ajiki,
an kunna wuta ajikkin kayan nasu,wasu a zaune cikin wutar,wasu ko suna tura makamashin
wuta abakinsu,Amma sam wutar bata cin jikinsu,kuwwa sukeyi da shewa suna fad'in gado sai
dan gad0,saimu diyan mak'era ba dai wuta ta ci mu ba,sai wani ikon jallah,Mune jikokin mallam
Buba mak'eri ikon Allah,Ina Wanda wuta taci taki warkewa,ina Wanda wuta kema
gaddama!"Kuzo ga yayan guduma,....."Masu kida ko sai kara kaimi sukeyi...can farinciki ya
kama Baba Malaam."
"Baisan lokacin da yafada filin wasan baa,domin tuni yace yabarwa diya da jikoki,Cikin kwarewa
Jikinsa sai mazari yakeyi galan din fetur yatada yana zubawa ajikinsa, wutar kara ya dauko tana
ci ya goga ajikin kayan sa,amma Sam wuta taki kamasu....shewa aka dinga yi, mallam buba
kudinsaya kwakulo duka ya zube aqasa yasa wuta ajikinsu, taki cinsu...sake kuwa akayi"daga
yan kallo har jikokinsa kowa tsaye suna kallon Baba malam sunajin dadi,tofi yayi awuta sai
kawai takama ajikinsa da kudin harda tururin hayaki amma ko alamun cinsu batayi
ba....Yace,ina mai ja da Buba dan gambo jikan ila makerin manya!kowa yabar gida,"gida ya
barshi,Cigaba yayi aikin gadou mai kidi naqara kashe kid'a...."Mallam iro ne dai yazo da Sauri
ya janye malam Buba hakan nan."Nan wasa ta cigaba da kyau kowa na nuna tashi gwaninta."
"A cikin gida kowa sai hidima akeyi anci an sha masu farinciki da murna nayi masu bakinciki
kuma sunayi."
"Asma'u kuka takeyi kwarai tun alokacin da taji labarin an dawo daurin aurenta da Alh.kalle."Ko
wanka da kyar su Gwaggo husai suka tilasta ta,babu abinda takeji sai haushin kanta da batayi
tunanin guduwa tun wuri ba,Kamalunta ya dade da cewa su gudu wani,wurin daban har ayi
aurensu,sai su dawo!Amma tsoronta ya hanata binsa gashi yanzu ya Shiga dunia sanadin
soyayyarta!,Kuma Batasan a ina yatafi ba, domin ahalin yanzu tafi son ta fada uwa duniya,da
akaita gidan Alh.Kalle,kazami mai Faso da warin baki,kuma tsoho..."Kukanta ta cigaba da yi har
lokacin da aka zo daukarta bayan tasamu horo awurin iyayenta,Baba mallam ko kashedi mai
kyau yayi mata akan ta zauna da mijinta,kishiyoyinta,da tawagar yaransa lafiya."A lokacin
hankalin Asma'u ba ya tare da su, ko A bata kama ba, acikin horonsu zuciyarta na ta shirya
mata yadda zatayi,jin takeyi arantà!zata iya yin komai harta kisa! matukar kalle bai saketa ba!!!"
[1/10, 11:05 AM] Nordin: *SHAFI NA HUD'U*
*ALKALAMIN NABEELA DIKKI*
"Yaseera da qawarta Raudhat a hanyarsu two dawowa Islamiyya,Fira sukeyi sosai,Nan ne
Yaseera ta labartawa Raudhat Mas'ud duk abinda ke faruwa."
"Dan tsakaita tafiyar sukayi,Raudhat ta dafa qawarta cikin nutsuwa,Ta ce,Yaseera nasanki
kuma nasan dukkanin halaye,Ba sai na baki shawara ba,A kan cewa ki amshi zabin su Abbu."
"Na tabbata wannan aure naki da Najibullah alheri agareki!Ina miki fatan Alheri,Allah ya nuna
mana lokaci,wallahi nayi farin ciki matuka domin kin samu miji na idon duniya,Ga ilimi,mutunci
tarbiya da asali mai kyau,"Kinsani sarai wadannan su ne halayen miji nagari,Ina son ki
kwantarda hankalin ki,Kada ki sanya musu acikin lamarinki sai karshen sa yayi kyau."Raudhat
ta qarashen zancen tana murmushi tare da zubawa aminiyarta ido."
"Hannayenta yaseera ta hade da nata,Ta ce tabbas kice kawa tagari mai sona,nagode Raudhat
hakika shawararki mai kyau ce,Daga yanzun nan zan dauki najibullah da zuciya daya,
amatsayin mijin da nake fatan yazamo uban yaranah.."
"Haba tawan ba godia haka atsakanin mu, Raudhat..Ta ce tana dariya."
"Saleem da Abdul suka zo,Inda suke tsaye."
"Abdul ya ce kagan su ko sale,daman nagaya maka sai mun cimma su,suna nan suna surutu..."
''saleem qanen Raudhat yake,yayi yace tabbas abokina naga zahiri kamar kullum wato su
yayah basa gajia da fira,Dariya suka sa dukkan su."
"Sallama da juna sukayi da zummar gobe zasu hadou Islamiyya,Tunda qannan su sun saka
masu ido,Kowacce hanyar gidan su tabi itada qananta da yake layin gidajen su ya bambanta
sai dai duk a unguwa d'aya ne."
"Ko da su yaseera suka dawo gida sun sami yayansu yaseer ya dawo daga makaranta,Ai kuwa
murna aka shiga yi,Musamman Abdul da akayiwa tsaraba da yawa,Yaseera kayan kwalliya da
hijab aka saya mata."
"Nan take ta fada kichen umma ta samu tana sanwar rana,zage hannu tayi ta tayata,bayan sun
gama dan wake da zobou tayiwa yayanta domin shi yaya yaseer yafiso,dan kawai ta faranta
masa yadda yayi musu abin alheri."
********************
"Tunda aka kai amarya Asma'u agidan mallam kalle kullum cikin masifa da rashin mutunci
take,Allah ya jarabci Alh.kalle da ciwon son Asma'u Wanda ya haifar masa da jin tsoronta."
"Kusan kwanaki hud'u da auren su amma har yau Asma'u bata bashi dama ya dama ba kamar
kowane Ango."
"Gidan Babban gidane mai dauke da ciki da falo hud'u na matan gidan,Uwargidan sa uwani,sai
mai binta sahura,saina Asma'u,dayan arufe yake ba kowa,sannan dakin yammata biyu da filin
gida, sai turakar mai gidan,,shimaa babban falone,da daki da bayi."A harabar gidan akwai
dakunan yara maza uku,da wurin ajiye motoci,duk gidan tayal ne,an fenti shi da farin fenti,har
qatoun get din gidan."
"Dakin Asma'u an gyare shi tsaf,ansa mata gadon jan katako,kalar jinin kare,da madubi,da
wadirof,afalo ko kananan kujeru ne saiti daya,suma kalar kayan dakinta da labule."Alh.kalle shi
yayi gadara ya sanya mata talabijin da bidiyo duk gidan dakinta ake kallo,saboda ba mai kayan
sai ita,da sashen Alhajin kuma shi idan yasa ba mai shiga yayi kallon."
"Yadda Asma'u tayi tsammani agidan ba haka bane,domin kowa tsoronta yake ita kuma sai
rashin mutunci takeyi."
"Batasan cewa Alhaji yayiwa matansa da yaransa kashedin kwarai akanta ba!."Shiyasa kowa ya
zuba mata ido sai yadda taga dama."
"Tun a kasuwa Alh.Kalle ya kudurta aiwatar da kudirin sa ayau,shiyasa ana tashi kasuwa
yadawo gida tun wuri."Asma'u ko tun safe suke Abu daya wato kallo ita da larai da Jummai
yayan Alhaji da bazasu wuce sa arta ba,A yanzu sune manyan abokanta agidan,shiyasa ta
daina yiwa uwani da sahura rainin wayo daman can da mama take kiransu."Tana zaune lafiya
da su sai kurciya take zubawa agidan da hauka duk da Alhajin ya saketa dan har girki batayi sai
dai taci ta kwanta acewarta bata iya ba,kuma ko ta iya bazata yiwa katti da yawa abinci ba!''
"Da misalin 12 na dare Alh.Kalle ya fad'a dakin Asmau da yake yanada mukulayen
dakinta,shiyasa bai samu matsala awurin budesu ba!"Kwance ya sameta rashe-rashe akan
gado,Baccinta takeyi cikin nutsuwa,Tasbaha ce rike a hannunta ga alamu tana janta ne bacci
barawo ya saceta,Sam Asma'u bata bar addininta ba!Bata wasa da lokacin ibada,tarbiyarta
ce,kawai tayi watsi da ita,saboda *AUREN DOLE* shiyasa take rashin mutunci kamar ba ita ba!"
"Ba kunya bare tsoron Allah Alh.kalle ya farma Asma'u,Warin 'ya'yansa mai karamcin shekaru."
"Tashin hankali marar misaltuwa tasamu kanta aciki,kusan sati d'aya ana jinyarta!"Tayi kuka
harta godewa Allah,kishiyoyinta ke kula da ita tare da bata baki,akan tumasancin da mijinsu
yayi mata,Batayi mamaki ba!Saboda daman can jahili ne!shiyasa ya nuna mata karfi!"
"Lami mahaifiyar Asma'u da gwaggo usaina sun zo da kansu har gidan,sun duba yarsu,ran su
yabaci matuka!"sai dai hakuri suka ba Asmaun!!"Wacce banda kuka da cewa ita bazata zauna
ba!zata bisu ba abinda take fadi!"
"Amma kashedin Baba mallam, Gwaggo ta tuna mata!"Wanda yayi sanadiyar katse mata
hanzari!"Kuka ta cigaba da yi tamkar ranta zai fita!"A haka suka lallabata suka koma gida rai ba
dadi musamman mahaifiyarta lami!!"
"Zama ta cigaba da yi agidan Alh.kalle zaman bakin ciki da ganin azaba domin da girkinta da na
kishiyoyinta duk Alhaji farmata yakeyi ya mayarda ita kamar wata baiwarsa akullum cikin kuka
take!tare da dinbim da nasani akan zaman da tayi ta zuba ido har igiyoyin *AUREN DOLE* suka
rataya awuyanta!"
***************Najibullah,Ya dawo gida lafiya,kuma kwas din da yaje madina yayi nasara
domin yadawo gida Nigeria da sakamako mai kyau."
"Mahaifinsa malam Usman,Babban Alaramma ne,yanada ilimi sosai yanada mata biyu,Hajiya
Rabi'a da Hawwa suna zaune lafiya,sai yaran sa biyar Najibullah ne babba,sai Rahma,da
Sudais dukkansu yayan Hajiya Rabi ne,Sai Nabeela da Khadija yayan Hjia Hawwa."Suna zaune
lafiya cikin karamci da son junansu,haka kan yaran ahade yake suna da ilimi da tarbiya mai
kyau."
"Najibullah matashi ne kyakkyawa wanda mata keta kai kawo akansa,Allah yayi masa baiwar
kira'ah kamar sheik sudaisi idan yana karatu.Gashi da dimbin Ilimi bayada makosa ko daya
iyayensa na alfahari da shi kwarai da gaske."
"Da dadewa mahsifinsa ya sanarda shi zancen aurensa da yaseera,sai dai shi ya amsa masu
domin kawai bin umurnin iyaye,Amna aganinsa yafi son zabin sa, ba hadin iyaye
ba!"Kasancewar bai taba haduwa ita ba,akan tana makaranta har yayi tafiya,shiyasa Mallam
usman ya kirashi tare da bashi umurnin,ya tafi gidam malam Aminu ya ga yaseera wato matar
da zai aura nan da wata d'aya."
"A zuciyar Najibullah mamaki da tunanin wannan aure nasu yakeyi shin *AUREN SO NE!KO
KUWA AUREN DOLE* ne za'ayi musu."Amma afili da ladabi ya amsawa mahaifinsa da in shaa
Allah zai tafi bayan magrib,godiya yayi masa tare da sanya masa albarka."
"Murmushin jin dadi najib yayi kana yabar falon mahaifin nasa cike da zancen zuci,"Da tunani
wannan wace irin mata ce!?Shin tayi dai-dai da ra'ayinsa,irin kalar macen da yakeso ce!?"Oho
dai ido kannan kai..."Inji Nabeela Dikko
"Kofar gidan,Ya tsaya yana nazarin ta ina zai fara,Sai kawai ga Abdul Raheem riqe da
leda a hannu ga alama daga ake yafito,Fuskarsa a sake yace,Abdul ne ko?"
"Abdul da ya kada fadarsa daya a bakin get din gidan,ya waigo kasancewar bai lura da
Nabullah ba.."
"Da sauri ya karaso wurinsa ya gaida shi aladabce..."
"Amsa masa Najib yayi saboda daman sun san juna,Domin yaseer mutumensa ne."
"Abdul,"Ya ce "Yaya Najibullah ne!"Hannu ya bashi