Showing 12001 words to 15000 words out of 26465 words

Chapter 5 - Auren Kaddara Ko Biyayya Book Compelet By Biilyn Abdull

BIYAYYA🌷

09093044460
Na billkisa ibrahim ��

31 «*****» tunda yadoso b'angaren nata yakejin k'amshi yana bugosa, ya tura kofar falon ya
shiga, yashak'i dadda d'an k'amshin ya lumshe idanu, tare da fad'in ya SALAM, yabi palon da
kallo yay murmushi yana nufar kofar bedroom d'inta.

Tana tsaye ga ban madubi tana saka lip stick abaki, jin anturo kofa yasata saurin juyowa tana
kallon kofar, shima tsaye yake k'yam yadasa mata fararen idanunsa yana mata kallon sama da
k'asa, sanye take cikin farin material da d'igon d'igon ja tayi kyau sosai.
" ta zame kasa ta durkusa, yaya ina kwana??
"Cinkin sark'ewar murya yace kin tashi lafiya??
"Tace k'alau"
Ya k'araso cikin d'akin yana tanbayar jakkar aikinsa💼 ??
Taje ta d'akko masa saida ta russina sannan ta bashi.
"Yace to ni bari nawuce aiki ya fad'a yana kallon agogon hannunsa"
Har ya juya zai tafi, tace yaya !!!

"Ya juyo yana kallonta ba tare dayayi maganaba"
Dama.......sai kuma tayi shiru batare data k'arasa fad'a ba
"Yace ina saurarenki"
Cikin rawan murya tace dama cazanyi bakayi break ba zaka fita, gashi kuma har na had'a tun
d'azu.
"Cikin mamaki da al ajabi yake kallonta sukaima juna kallon tsakkiyar ido, tai saurin janye
nata dan bazata juri kallonsaba"
"Ya b'oye mamakinsa, yace to muje kibani, dan ina saurine, inada tiyata karfe 11: 30am ya
kalli agogon hannunsa gashi har 10: 38am tayi.

Yay gaba tana binsa abaya, taji dad'i da zaici, dan ita atunaninta zaice bazaici abincintaba tayi
k'arama, kamar yanda yakebfad'a
Suka k'arasa wajan tebirin cin abincin yaja kujera ya zauna, ita kuma tafara zuba masa abincin,
k'amshin ya daki hancinsa ya lumshe idanu,tare da had'iyar yawu.

Ta gama ta tura masa kofin shayin☕ da filet d'in� gabansa, ta mike zata bar wajan
Yace, "k" zonan !!!
"Wani haushi ya turnik'e ta ta tsani ace mata "k" amma ta kula shi wannan d'an latsin rainin
wayon yana neman maida mata suna haka"
"Wai ko bakijini bane?
"Ta dawo da tace gani"
Ya nuna mata kujera, sannan ya d'auki kofi ya had'a shayi, tana zaune tana kallonsa �.
Yak'are had'awa ya mik'o mata ☕, tasa hannu ta karb'a, ya d'auki cokali yasaka cikin filet d'in
data zuba masa abincin, oya bismillah, dole taci dan tana tsoron wannan d'an hayak'in.

Bayan sun kammala ya mik'e, itama ta mik'e ta d'auki jakkar aikinsa.

Har wajan motarsa tara koshi, ya bud'e ya shiga ita kuma tazagaya d'ayan b'arin tasaka masa
jakkar, ya tada motar, tad'an lek'a tace ALLAH ya tsare ya bada sa'a"
Yay d'an murmushi batare da yayi maganaba yaja motar ya fice bayan sun gaisa da mai gadi...

�billy�
{�Mrs Abdus'salam�}
{MrsMrs Abdus'salam🀠Mrs

[1/14, 4:10 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳
🌷ko BIYAYYA🌷

Na billkisa ibrahim ��

32 «******»saida ya fice ta koma cikin gida, ta d'auki waya ta kira 'yan biyu wai dan ALLAH suzo
su tayata hira,

Shikam gogan naku koda yafita gidansu ya nufa, zuciyar sa fal tunanin wannan 'yar shilar
yarinyar da ya raina, dukkanin abinda tai masa yau ya d'aure masa kai da kwanya, idan ya tuna
su husna da ayyukansu,a tsawon shekara d'aya d'auka tare dasu amma ko maka mancin
abinda yarin yarnan tai masa yau, basu tab'a yimasa ba, dai dai da d'akinsa sai dai shiya gyara,
to bare girki, koda yake nasu d'akunan ma bagyarawa sukeyiba saidai masu aiki su gyara
musu, yay hon mai gadi ya bud'e masa get, saida suka gaisa ya k'arasa cikin gidan.

Da sallama ya shiga falon, suna zaune a darning table, suna break, ya gaida iyayensa su kairat
suka gaisheshi,
"Babana taso kayi break mana !!
Dady yay dariya dad nida abinci kuma ai sai na rana, yanzu kam akoshe nake.
Shima yay dariyar, babana ina kasamu abinci??
yanzufa naji mom d'inku tanacewa su kairat suzo sukai muku break.

A'a wlh mun hutash sheki mom ba sai an rik'a kaiwaba.
"Matata ta iya girki"
Dad a tanbayi mai mata a ina yaci abinci, ya fad'a yana dariya�
Suma gaba d'aya suka tun tsire da dariya, ya mike shima yana dariyar kunga sai anjiman ku ni
zan makara.

Dad yarage dariyarsa to kayi k'ok'ari idan aiki yayimaka sauk'i ko zuwa yamma ne kasa meni a
office.
"Yace to sai nazo"
"Mom sai anjima"
"To babana adawo lafiya"
Su kairat sukace yaya yanzufa zamu gidanka
To sai kunje, kuna can har dare ko??
"Eh har sai kadawo ma"
To shikenan ya fad'a yana fita

Yana isa asibitin ya fara shirin shiga tiyata bayan ya gama zagaya marasa lafiyar yana musu
sannu da tanbayar su ya jiki, wanna kyawawan halayen nasa ya sashi yin fice asibitin, koya
kake dady baya wulak'antaka ya iya tattalin mara lafiya da kwantar masa da hankali, in har baka
da k'arfi, zai taimaka maka da aljihunsa da basirar sa, duk sanda ya iso asibiti sai ya zagaya
marasa lafiya, yay musu sannu, mai buk'ar wani abu yay masa sannan ya dawo office yacigaba
da duba marasa lafiya
Shidai barahi da shegen miskilanci kuma abun ajininsa yake.

To yauma bayan yagama zaga yensa ya shiga tiyata bakin sa da addu'oin neman nasara.......

�billy�
{�Mrs Abdus'salam�}
[1/14, 4:10 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳

🌷ko BIYAYYA🌷

Na billkisa ibrahim ��

33 «*****» miye labari su husnane ??
Su husna suna gida abinsu umma anata lek'e lek'en gidajan malamai da bokaye, acewar ta
sai dady yazo dakansa yana kuka abashi su ikileema.
To suma sunanan sunata fankama akan sai yazo, iyayensu mata ma suna nemomusu agefe
kowa tana shirya d'iyarta acewar su, amma gashi yau har tsawon sati uku ba labarin dady bare
zuwansa.

Su har ma abin basu tsoro yakeyi dan sunsan halin dady sarai da,miskilancinsa,
Ikileema tana kwance bisa doguwar kujerar dake falonsu, sauran k'annenta sunata hirarsu.

Maman ta ta fito tazauna kusa da ita ikileema lafiya dai ko naganki akwance?
ga kuma sauran 'yan uwanki sunata hirarsu.
"Ta turo baki gaba gaskiya nifa mama nagaji da zamannan hakanan, nifa gidan mijina zan
koma, yakama ta ku daina biyema waccan tsohu war hakanan, dan wallahi nasan dady bazaizo
bikonmuba, garama tun wuri kubarmu mu koma, dan gaskiya nidai inason mijina, tafad'a tana
juyama uwar tata baya.
Mamarta tace ikileema kefa shashaahace duk wannan k'ok'arin da akeyi dansu ubanwa akeyi
badan kuba, shine har kike fad'a mini kefa kina son mijinki.

ALLAH mama ba haka bane ba gara ku bari mukoma ba, dukma abinda za'ayi ayishi muna can,
agidan amma azo ahanamu komawa gidan mijinmu, ita kuma waccan she giyar tana can tan
shan shagalinta awannan had'ad'd'en gidan.

Maman tai ahiru tana kallonta, kai ikileema dafa gaskiyarki wlh, kumafa hakane mumu nanan
muna bad'oso goyon jirge, ita tana can tana shan lagwadar dad'i dak'ara mamaye gida, da mai
gidan, nasan hajiya salaha sarai da iya kissa, kuma tana koyar da 'ya'yanta.

FAD'AKARWA :- ni aganina dan mace ta koyar da yaranta kissa inhar bata cutar da wani bace,
tofa tayi dai dai, dan kissa nad'aya daga cikin halayyar dake jan ra'ayin miji ga matarsa, ba sai
ta hanyar boka da malam ake jan ra ayin mijiba, a'a kema malamar kankice, bari nabarku haka
ku biyoni kuji yanda Munneerah take damk'e dady ahannunta cikin ruwan sanyi da kissa irin
wadda ta halatta.......

�billy�
{�Mrs Abdus'salam�}


[1/14, 4:10 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳

🌷ko BIYAYYA🌷

09093044460
Na billkisa ibrahim ��

34 «*****» to kinjifa mama dama kinsan wannan amma kika barni agida ita waccan sarkin iyayin
husna uwarta tace ba yanzuba, to nidai duk ma yanda za'ayi kiyi nakoma d'akina awannan
satin,
Gaakiyarki ikileema in ALLAH ya yarda yau da abban ku ya dawo zan masa magana gara ki
koma d'akinki.
"Ta tashi cikin murna ta rungume uwar tata tana godiya.


To ab'angaren husnama haka abin yake ita babanta ma tasanar tanason komawa d'akinta, yace
karta damu zaije yasamu umma da yaya da maganar yau da daddare.
"Tace to"


Agidan dady kuwa zama akeyi irin na k'anwa mai girmama yayan ta, da yaya mai kula da
k'anwarsa amma babu wata shakuwa data wuce gaisuwa da safe, ta had'a masa break, ta
rakashi wajan motarsa in zai tafi aiki, tadawo ta gyara masa d'akinsa, ta wanke kayansa daya
cire, tayi girki da rana mai dad'i da gamsarwa akai masa asibiti,inya dawo ta taroshi tarakasa
har b'angarensa, ta basa ruwa yasha, dama ta had'a masa ruwan wanka, da dadare ta dafa
musu abinci mara nauyi suci, koda ba wata hira mai tsawo ke had'asuba sukan zauna apalo
d'aya suna kallo, koyana bincikensa akan aikinsa, ita kuma tana kallo, duk abinda yasakata
zatayi babu fushi bare canja fuska kota nuna gajiya warta.
Wannan ne yakansa kan dady girma dajinfa shima fa ya isa maigida, shima yana kyautata mata
indai yafita yaga wani abida ya birgeshi zai siyo mata,

TUNA TARWA :- 'yan uwana mata bamu cika san yiwa mai gida wankiba, bare idan ALLAH
yad'an bashi karfen nasara ahannu (kud'i) masu d'an k'ok'ari a cikinmu sune masu wanke
singlet da gajeren wando, kina zaune mai gida zai had'a wanki ya bayar, sai kiji muna fad'in
bazamu iyaba gana yara ganashi kai wallahi aiki yay mini yawa, a'a uwar gida tsarama kanki
yanda zaki zauna agidan miji kinji, kula dashi da dukiyarsa sutturarsa, tsara wani d'an lokaci
kina yima mai gida wanki yanasa farin ciki da kaunarki azuciyarsa, zaki k'ara samun fada a cikin
zuciyarsa,....kudai biyoni 'yan uwa........

�billy�
{�Mrs Abdus'salam�}
[1/14, 4:10 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳
🌷ko BIYAYYA🌷

09093044460

Na billkisa ibrahim ��

35 «*****» Munneerah tana zaune apalo tana kallo bayan tagama sallar isha'i, lokaci lokaci
takan d'an cije leb'enta da alama akwai wani guri dayake mata ciwo, ta zame ta kwanta saman
doguwar kujerar datake zaune.

Dady ya turo k'ofar ya shigo da sallama, ta amsa cikin dauriya, da cije baki,
" Yad'an kalleta lafiya kuwa??
Ta daure tace bako mai, yanemi guri ya zauna kujerar dake gefenta,
Ta tashi zaune tana fad'in yaya abincifa??
"Yad'an tsura mata idanu dan son gano matsalarta, amma saita kauda kai tana laluben
wayarta,
Ta kuma maimaita tan bayar sa cin abinci?
"Ya girgiza kai saidai zuwa anjima, bani dai lipton na sha"
"Ta mik'e tana fad'in to"
Bayan kamar minti biyar ta dawo hannunta d'auke da tire k'arami, ta d'oro butar shayi da kofi sai
k'aramin cokali, ta ajiye saman tebirin dake gefen kujerar daya ke zaune, ta zuba tasaka shuga
ta motsa, sannan ta bashi, ya karb'a yana binta da kallo harta koma saman kujerar ta kwanta,
"Gaskiya yana buk'atar abokiyar jalittarsa, sai dai yana ganin Munneerah tayi k'ank'anta,
babu abinda zata iyayimasa, ab'angaren auratayya, kai idanma ya b'ullo mata da wannan
maganar saita rainasa, girma mawar data ke masa ta daina, to inma banda abinsa mai zai
samu wajan wannan 'yar shilar yarin yar, wadda ahaihuwar kaji ya haifeta, a gabansufa aka
haifeta susuka rainet.....
Wayarsa ta katse masa tunani, ya d'auka yana dariya, ango kasha k'amshi, kaima kazama
sojan sama ko ka kashe arna dubu??
Daga can b'an garen jafar yay dariya nida kai a tantance sojan sama, d'an rainin hankali, kai
mai mata uku ma ba ace dakai sojan samaba har zakace da wani.
"Dady yay dariya kaini nida gwauro babu maraba ai"
"Kai haba inji jafar, kodaya ke ance mini matanka sunyi yaji, to aikai gaba ta kaika malam
saika kwashi amarci abinka"
"Kai daina fad'a dan ALLAH ina abin yake bare romonsa ai da sauran lokaci,
Dariya sosai jafar yakeyi haba d'an uwa kardai nanda wata tara ace muzo suna
Kai d'an iska sai anjima kaji, ya yanke wayar yana dariya.

Da sauri ya mik'e ya nufi Munneerah dake kuka rik'e da ciki, yay saurin tarbo ta tafad'o jikinsa,
cikin rikicewa yace Munneerah mike damunki??
cikin kuka ta nuna masa k'asan cikin ta,
"Mararki ke ciwo tad'aga masa kai tana murku susu ajikinsa, ya kalli agogo 8:55 pm, ta
k'ank'a mesa cikin zafin ciwo yaya zan mutu wayyo yayan ka taimakeni,
Cikin sark'ewar murya yace bazaki mutuba Munneerah......


�billy�

{�Mrs Abdus'salam�}
[1/14, 4:10 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳
🌷ko BIYAYYA🌷

09093044460
Na billkisa ibrahim ��

36. «*****» duk ya rud'e gashi likita amma ya kasa yimata komai, k'arshe dai ya rarumo waya ya
kira wani abokinsa Dr Anuwar, bayan sun gaisa yace my friend ! Please in ban takuraka ba dan
ALLAH kazo gidana yanzu??
"Cikin sauri Dr Anuwar yace inazuwa"
Cikin minti 15 ya iso gidan kai tsaye ya shigo dan yasan gidan, har sannan Munneerah kuka
takeyi tana fad'in yaya ya taimaketa.
Dr Anwar ya shigo, ko gai suwa basuyiba ya fara tanbayarsa mike damunta ??
"Dady yace mararta ke ciwo""
Allura Dr Anuwar yay mata, cikin minti 3 sai komai ya lafa, barci ya d'auketa ajikinsa, yay ajiyar
zuciya my friend nagode fa"
"Dr Anuwar yay dariya karka damu my friend, dama haka tana faruwa akanmu likitoci sai kaga
wani naka bai da lafiya amma saboda tsabar rikita mukasa bashi kulawa,
Sai mun nemi taimakon wani.
Wallahi kuwa hakane kagama inada allurar amma tsabar rikicewa tasa na rud'e"
Dr Anuwar ya mik'e yana dariya aidama hakane,bara na wuce saimun had'u gobe a asibiti, to
my friend na gode, ya fad'a yana kwantar da Munneerah akan carpet, Dr Anuwar yace kaga yi
zamanka wallahi na gode ALLAH ya k'ara lafiya, sukai hannu ya tafi.

Dady yadawo yana kallon Munneerah da take barci, karki damu matata in sha ALLAH sai kin
rabu da ciwonnan tunda kina tare da gwarzon namiji, ya d'auketa gabad'a ya kai ta d'aki ya
kwantar, sannan ya dawo yana nazari akan ciwon nata abincikensa abu ukune ke kawoma
mace ciwon mara yayin al'adah, amma zaidai sake bincike akai.......

Washe gari abban ikilima ya isa gidan umma suka had'u da abban husna bayan sun gaida
tsohuwarsu suka gaya mata buk'atarsu ta maida yaransu d'akin mijinsu, abban husna ya d'ora
da fad'in umma kinsan taurin kai irin na yaronnan Abdul'aziz, ga shegen miskilanci kamar d'an
sarauta, to kawai tinda yaran sun buk'aci komawa d'akinsu a maidasu, duk abinda za'ayi
saimuyi suna cikin gidan, kina ganin Mansur tundaga ranar dayazo yabada hakuri sukoma
muka k'i baisake yin maganar amaida yarannanba, amma umma yakikagani.

Taja nummfashi to shikenan kuma kun kawo shawara sai su shirya gobe na maidasu d'akinsu in
ALLAH ya kaimu
"To shikenan umma ALLAH ya kaimu kowa ya mik'e yanufi gidansa dankai albishir.......

�billy�
{�Mrs Abdus'salam�}
[1/14, 4:10 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳
🌷ko BIYAYYA🌷

09093044460
Na billkisa ibrahim ��

37 «******» dady yakai tsawon awa biyu afalon yana sak'a da warwara, ya kalli agogon dake
palon, yata shi zaune da sauri danganin lokaci yaja, ya mik'e ya nufi b'anga ren sa.
Wanka yayi yay shirin barci, ya dawo b'angaren Munneerah, ya kashe komai ya rufe ko ina,
sannan ya shiga bedroom d'in ya kalleta tanata barcinta, ya kamata ya canza mata kayanta
zuwa na barci, bayan ya canza mata, yay musu addu'a yay kwan ciyarsa.

Da Asuba ya tashi yay alwala ya wuce masallaci batare da ya tasheta ba, bai dad'e da tafiyaba
tatashi, tabi jikinta da kallo cikin mamaki waye ya canza mata kaya, wakuma ya kawota kan
gado, tunda tasan afalo ta kwanta, zuciyarta tace mata mijinki, ta zaro idanu waje � ni
Munneerah kice yagama kalleni abanza, taja bargo tarufe jikinta da sauri danjin an turo k'ofa.
Ya tsaya cak yana kallonta danganin tanata faman cikukuye jikinta cikin bargo, ita kam tai k'asa
da kai ta kasa kallonsa, yay d'an murmushi ya k'arasa jikin gadon yana fad'in ya jikin naki??

"tad'an kalleshi kad'an taikasa da kai, dasauk'i ta fad'a asaman leb'enta"
"Yanzu dai ba inda yake miki ciwo ko??
Ta kad'a kai batare datayi maganaba.

Shima bai sake cewa komaiba ya juya ya fita abinsa.
"Ta mik'e ta shige bayi"

*************»«
Tunda labari yajema su husna akan zasu koma gidan mijinsu suketa farin ciki, dan suna son
dady da gaskiya, iyayensune kawai suka k'ulla auren nasu da wata manufa.
Tun adaren suka had'a kayansu, karfe goma na safe agidan umma tai musu,
Umma ta rik'e baki oh ni yaran yanzu bakuda ta ido, yanzunan danza ku koma gidan mijinku
shine kukayo irin wannan sammako haka.
Husna tace to umma bamuyi dai daiba kenan.
Ah bar tsohuwarnan kinji itama idan itace abinda zatayi kenan,ikilima tafad'a k'asa k'asa,
Umma ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0