Showing 3001 words to 6000 words out of 17405 words
Chapter 2 - Auren Wata Bakwai Book Compelet By Aisha Muhd
Haka ta tuɓeta da kyar tana sa mata ruwan zafi a jiki ta kara sulle mata tana ihu, "Zaki karni ne
Baba, na shiga ukuna ni Gaaji zata ƙona ni."
Haka sukata fama tana gudu tana binta har aka rage daudar dan ba ace ta fita duka ba,kanta
kuwa kin yarda ma tayi a taɓasa sam bare a wanke.
Suna gamawa ta dauko sabon brush tasa mata toothpaste ta ce, "Yawwa ungo wanke bakinki."
Tana karba ta suɗe toothpaste din tas ta shanye ta fara tauna brush din.
Uwar Soro ta bude baki, "Subhanallahi wanke baki ake ba sha ba fa." Karba tayi ta kara zuba
mata wani sannan ta wanke mata bakin da kanta.
Ai kuwa datti kamar ruwan kasa jini ma bakin ya fara yi, tuni Gaaji ta rikice ta fara kuka tana
ganin jiki ta ce, "Dok Allah karki shanye mun jinina kadan ne dani ba yawa kuma bai da zaƙi ma
Don Allah."
Sai da dariya ta kusan subucewa Uwar soro ta danne tana, "shikenan yanzu ga ruwa kuskure
bakin,kar ki shafa,ki kuskurewa kawai."
Nan fa tana sa ruwa abaki ta shanye tana, "ita ba zata zubar da jininta a banza ba ta mutu."
★★★CIKIN GIDA
FULANI ce kishingiɗe a parlour hannunta dauke da tuffa tana ci a hankali, gabadaya yanayin
fuskarta sam babu walwala kallo ɗaya zaka mata ka tabbatar da cewa tana da damuwa cikin
ranta.
Jakadiyar ta dake gefe tana lure da hakan ta ce, "Ranki Ya Dade Fulani lafiya kuwa?"
Ta ce, "Jakadiya kira mun Hajiya Maimuna."
Tashi tayi ta je ta kirata cikin sauri.
Hajiya Maimuna wacce take Aminiyar Fulani kuma mata agun Kawun Mai martaba ce ta shigo
bangaren Fulani kamar yadda ta samu kira daga gun Jakadiya.
Zama tayi tana fadin, "Ranki Ya Dade na amsa kira, amman ya na tarar da fuskarki ba walwala
fatan dai muji Alkairi."
Jakadiya na fita ta laɓe abakin kofa tana sauraren abun da Fulani zata ce.
Numfasawa tayi tana gyara zama, "Maganar Yareema ne, kina ganin kullum mai martaba kara
girma yake,kwanaki na kara ja, lokacin murabus dinsa na ta kara tawowa, tsufa ya kamasa,
amman Yareema sam yaki mai da hankali kan batun aure kuma kin san ba makawa shi za a
daura, ba ma wannan ba ni kaina ina bukatar ganin wata wacce za ace sirika ce gareni ta haifa
mun jikoki, yanzu haka fa ya kusa cika Shekara talatin a duniya."
Murmushi Hajiya Maimuna tayi ta ce, "indai Don Wannan ne ki daina damuwa Uwar giyata,ina
tunanin kawai za a shirya yi masa auren ba zata ne kawai ba tare da saninsa ba kuma ba tare
sanin kowa cikin Masarautar nan ba, Mai martaba kawai zaki sanar a shirya bikin na Tabbatar
da cewa Yareema ba zai taɓa bijirewa zaɓinku ba amman kafin hakan a gwada tuntubarsa na
ƙarshe ko yana da wacce take zaɓinsa,in ya tabbatar da cewa babu kawai sai mu shiga
shirye-shiryen abubuwan da ya dace kuma a zaɓo matar data dace."
Gyara zama fulani tayi tana sakin Murmushi ita ma ta ce, "Maddallah da ke Hajiya Maimuna
babu shakka hakan za ayi domin kuwa shine mafita kawai, amman Babbar Matsalar ma ban
san ko yana gari ba, zan binciki Uwar Soro muji."
Jakadiya na jin motsin Hajiya Maimuna ta wuce da gudu ta nufi dakin Fulani Kilishi.
Amarya ga Fulani Babba wacce take ita ma mata ce ga Mai Martaba ta biyu.
Tana ganinta ta daka mata tsawa, "Ke Lafiya zaki shigo mun daki haka? Kina da hankali kuwa?"
Ta ce, "Ranki Ya Dade labari na samo miki ina so Hajiya Maimuna ta wuce ne kada ta ganni."
Tsaki ta daka mata tana fadin, "Oya ni fadamun to ."
A hankali murya irin ta munafukai ta ce, "Za ayiwa Yareema auren bazata ance ba wanda zai
sani sai Mai Martaba da Fulani Babba."
Wani irin Murmushin takaice ..... Ta yi, "Aure? Wannan zance ne, hakan ba zai taɓa yiwuwa ba
ma kada ki damu ni na san matakin da zan dauka,bama wannan ba , shin wa za a aura masa?"
Jakadiya ta ce, "basu kai ga fada ba,sun dai ce za a duba."
Dariya ta fara wacce azahirine kadai take dariya a zuciyar ta kuwa ban da tsantsar mugunta
babu abun da ke ciki.
"In an fada yarinyar ki zo ki sanar mun, ba wanda ya isa aiwatar da komai cikin Masarautar nan
ba tare da sani ba, don ban haihu ba hakan baya nufin in zam saniyar ware ahir."
Jakadiya na fita ta kara nufan bangaren Hajiya Rabi wacce take kishiya agun Hajiya Maimuna
ta sanar da ita.
Tsaki Hajiya Rabi tayi tana fadin, "Lallai kuwa za a sha mamaki cikin Masarautar nan,
Mussaman in ya kasance ba ɗaya daga cikin 'Ya'yana za abaiwa Yarima ba saidai kowa ya rasa
ko ya mutu ko ya yi rai ba aure, ke ban ma ga ta zama ba,amman ina fatan dai baki sanarwa da
kowa hakan ba?"
Girgiza kai kawai Jakadiya ta yi alamar eh.
Hajiya Rabi bata kara bi ta kanta ba tuni kawai ta dauki mayafi ta fice.
Tana fita Jakadiya ta tuntsire da wata irin dariya ta wani wasu surutan da ita kadai ta san
fassaran su.
★★★kiran Uwar soro Fulani Babba tayi kan tana neman Yareema.
Uwar Soro ta sanar da shi kai tsaye ya nufi cikin Masarautar.
Yana zuwa zuwa daga kafar shi da zaiyi ya shiga ciki kafar ta kame kam.
[8/7, 9:47 AM] Xayyeesherthul-humaerathí ¾íµ€: *AUREN WATA BAKWAI*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*
© *Xayyeesherthul-humaerath*
Page-5&6
Duk kokarin da ya yi wajen ganin ya ja kafar kin motsawa tai sam sam.
Jakadiya na fitowa daga kitchen ta hangosa tsaye kafa a kame, rike baki tayi a zahiri tana fadin,
"Subhanallahi Yareema lafiya?"
Ko kallon inta take bai ba bare ya bata amsa ya ci gaba da kokarin daga kafa amman ina
tamkar ana kara danna kafar.
Bangaren Uwar Soro tayi tana kurma ihu, "Na Shiga ukuna,Yareema ya kame,kafar Yareema ta
kame ya kasa takawa."
Uwar Soro na jin hakan ta fito cikin sauri tana fadin, "Subhanallahi ya aka yi hakan? Ina
Yareeman."
Jakadiya ta ce, "Gashi can a kofar shiga bangaren Fulani Babba."
Aiko Yareema na tsaye ban da zufa ba abun da yake tun yana kokarin motsawa har ya hakura.
Uwar Soro na zuwa tayi kokarin jan kafar tasa amman ina sam hakan ya gagara.
Addu'a ta shiga tofa masa,cikin kankanin lokacin gabadaya matan cikin Masarautar sun cika
gun.
Fulani Kilishi ce ta fara karasowa garesa tana, "Subhanallahi Yareema meke faruwa haka?in
kafar nan taki motsawa ta karshenta sai dai a yanketa."
Tana fada suka hada ido da Magajiya tare da sakin wani ƙayataccen murmushi.
Uwar Soro ta umarce su da duka kowa ya bar gurin abarta daga ita sai Yareema,ba yadda suka
iya ba don sun so ba haka suka tafi, Fulani Babba kuwa daman bata fito ba.
Hajiya Maimuna ta ce, "Uwar soro ko zan iya tsayawa ni in taimaka?"
Girgiza mata kai tayi alamar aa haka ita ma ta bar wajen.
Addua ta ci gaba da tofa masa Kasancewar hakan ba sabon abu bane gareta tun yana karami
lokuta zuwa lokuta kafarsa ta kan rike sai ta sha faman yi masa addu'o'i kafin ta sake.
Yau yafi na kullum domin kuwa da kyar kafar ta sake, tana sakewa tare suka shiga bangaren
Fulani Babba.
Bayan sun shiga saida aka ɗauki kusan Second biyar kafin Fulani Babba ta fara magana.
"Yareema!."
Ta yi shiru kafin ta ci gaba da fadin, "ka san dai a yanzu ban da damuwa da burin da ya zarce
ace yau ka yi aure."
Tana fada tsigar jikinsa ta fara tashi kansa na yi masa wani irin tsiro.
"Ban san mene ne dalilinka na rashin son aure ba kasancewar ka haka a yanzu baka da abun
da ya kamaceka fiye da aure, na san cewa kana da nauyi akanka na juya dukkanin abubuwan
da ke tafiya a masarautar nan, zuwan mata kila tana tallafa maka ta wani bangaren ka samu
sauki ban sani ba ko akwai wacce kake so,indai akwaita zan so ace kayi gaggawar bayyanar da
ita domin ayi komai kan lokacin da ya dace."
Shiru ya yi bai ce komai ba kansa na kasa.
FULANI babba ta kalli Uwar soro ta ce, "ko ya sanar da ke wata wacce yake muradin Aure?"
Uwar soro ta ce, "Aa Ranki Ya Dade."
"Hmm to ina jinka Adeel yanzu kai ba yaro bane kasan abun da ya ce da kai fiye da kowa."
Cewar Fulani Babba.
Yareema ya ce, "Babu Ranki Ya Dade amun hakuri tukun zuwa gaba."
Fulani ta girgiza kai tana, "Shikenan Allah yasa mu dace."
Tare suka fice da Uwar soro sai ta tabbatar ya shiga bangarensa kafin ita ma ta koma nata.
Tana shiga ta samu Gaaji na surfa uban kuka ita akaita gun Baffanta tana so ta ganshi kar a
kashe mata shi.
Dakyar Uwar Soro ta lallabata har ta samu ta yi barci.
Cikin dare ta farka wai tana jin kashi.
Uwar Soro ta kaita toilet ta ce ta hau tayi.
"Wallahi na Rantse da Ubangiji na ba jan hau wannan abun a wawushe mun duwawuna
ba,haka kawai in rasa mazaune ni kam ba zan hau ba, kawai mu fita anuna mun kasa inyi
yadda muke yi a ruga."
Duk Yadda Uwar Soro tayi da Gaaji tayi kashi a toilet dinnan ki tayi fur daga karshe sai leda ta
dauko mata,ta bata,ta tsuguna tayi, ga shegen yawa da uban wari tsabar da nannagi abinci
harda na hauka.
Tana gamawa tasa hannu ta kulle abunta a ledar ta ajiye a gefe tana, "kuma Aradun Allah karki
samun kashina cikin abunnan a ajiyemun da safe zan dauke abuna da kaina inje in binne."
Sai da ta koma barci kafin Uwar Soro ta samu ta je ta yi floshin din kashin.
Prince Adeel Muhammad Rohaan
Tun da ya koma kansa ke sara masa gabadaya wani gitaccen ciwon kai yake ji, zuciyarsa kuma
ban da muradin kasancewa da wata ba abun da take.
Wayarsa ta fara ringing, yana dubawa ya ga number Safina, a jiyar zuciya ya yi aransa yana
raya tamkar tasan yana da bukatar ta a yanzu.
Kara Wayar ya yi a kunne ya yi shiru.
A bangarenta ta ce"Prince inzo mu kwana? Na kasa barci Please."
Da "alright." Kawai ya amsa mata yana ajiye wayar.
Tuni ta tashi ta feshi jiki da turare ta sa wasu irin kananun kaya da zai iya gigita kowanni Ɗa
namiju daga kallo ɗaya, Mussaman ma ita da take da diri bayyananne mai daukan hankali.
Tana zuwa ta kira wayarsa tashi ya yi ya bude mata kofar bayan ta shigo sannan ta rufe ta bi
bayansa.
Zama ya yi a gefen gadon yana danna wayar dake hannunsa, tana shiga ta wular da Doguwar
rigar da ta rufe jikinta da shi tana wata irin tafiya ta karasa garesa tana shafasa, harshenta tasa
a wuyansa tana bi tana leshewa, da hannunta tana bin jikinsa a hankali, tuni ta gama sakar
masa da jiki, murya a sanyaye ta ce, "Please Prince, yau kada ka ƙi, ka yarda muyi abun da ya
dace,ina da bukata kuma kai ma na Tabbatar da cewa zaka ji dadin hakan kaji."
Ba tare da yace kamai ba ya kara janyota yana sa harshen sa cikin bakinta yana kankameta,
ganin hakan ta fara kokawar rabasa da kayan jikinsa, subulewa tayi daga jikinsa tana binsa da
wani munafikin kallo mai kara kashe jiki ta ce, "Wait taya hakan zai yiwu da kaya jikinka bara in
cire ma ko."
Shi ko tsayawa kallonta ya yi kawai tamkar hoto ta rabasa da kayan jikinta tana kokarin janye
masa gajeran wando da ke ciki kenan ya dakatar da ita da hannu alamar aa.
Wani guntin tsaki tayi azahiri cikin zuciyarta tana fadin, "duk abun ka dai Wallahi yau sai na
samu abun da nake so nayi galaba akanka."
Murmushi ta masa ta dawo jikinsa tana shafa girjinsa.
Shi kuwa sakewa ya kara yi,yana bin dukkan ilahirin jikinta yana kai mata wasu irin saƙonni, ban
da kokarin ta hake masa ita kuwa ba abun da take, da ta kai hannunta zai rike.
Ya gama duk wasannin da yake da bukata janye jiki ya yi yana numfasawa ya ce, "Safina Is Ok
Please ya isa haka barci nake ji."
Kukan karya ta fara yi tana yi masa magiya.
"Prince Wallahi baka ji yadda nake ji ba, zan iya rasa rayuwata muddin baka biyamun bukata ta
ba, ka tausayamun Please, ko na yaune kadai just once."
Jiki a mace idanun sa na rufewa ya ce, "Ki bari Gobe."
Yana fada ya kifa da kansa tuni barci ya yi awon gaba da shi.
Dafa kai Safina tayi tana, "wai wannan wani irin Bala'i ne kullum sai anzo gabar da zan aiwatar
da aikina sai kace barci ko kuma wani abu ya faru? Baka da aiki sai romance? This wil be last
time da zan bata lokaci na ba zan dawo gidannan ba sai da maganin da dole zai sanyaka
aiwatar da abun da ake da bukata ko na huta."
Tashi ta yi tasa rigarta ta fice,tana fita cikin duhu wani Mutumi ya karaso gareta yana, "Ya na
ganki haka? Ina so inji labari mai daɗi kar ki fada mun akasin hakan."
Tsaki ta yi ta ce, "ni fa na gaji wallahi kullum sai ya kaini makura sai ya juya mun baya, Gobe ko
jibi ina da bukatar anemo mun magani mai karfi da zai rikitashi duk yadda za ayi asa masa cikin
abun da zai sha inaga wannan shine shawarar karshe da zata iya aiki in ba hakan ba akwai
Matsala,har na gaji da binsa Wallahi."
"Shikenan kada ki damu zamuyi magana a waya." Mutumin ya fada yana waige-waige ya tafi.
WASHEGARI.
Tun da akayi sallar asuba ma'aikata da dogarai ke kai kawo cikin masautar kowa na aikinsa.
MASARAUTAR BENONI babbar masarautace wacce ta amsa sunan masarauta a kasar hausa,
ta tsaru iya tsaruwa daga wajenta har ciki,inda kudi da kayan masarufi na magana Tabbas na
wannan masarautar in suka fara nasu ba sauki, Aljannar duniya ga wanda ya taba shiga cikinta
domin babu mai tunanin fita koda kuwa cikin mafarki ne.
Mai Martaba Sarki Muhammad Rohaan ya gaji sarauta tun daga gun Kakansa, kakansa na
rasuwa mahaifinsa ya hau karagar mulki shi ma bayan mahaifinsa ya rasu ya hau wanda yake a
yanzu shi ke jagorantar BENONI.
Matansa Biyu Fulani Babba (A'isha) da Fulani Kilishi (Hafsat) Yaro Ɗaya garesa Prince Adeel
Muhammad Rohaan wanda yake tamkar gado ga ahalinsu Basu cika haihuwa sosai ba,
Kakansa shi kadai ne, kamar yadda mahaifinsa yake shi kadai,haka kuma shi ma ya Kasance
shi kadai sannan ya haifi Ɗa shi kadai.
Mai Martaba sarki Muhammad Rohaan mutum ne mai karamci da sanin ya kamata cike da jin
kan talakawa,sannan baya taba fadin magana biyu, Indai ya ce abu to babu shakka,ba canji a
wannan batun, baya da yan uwa na kusa sai wa inda suka zam dangi garesa na nesa, yan
uwan mahaifiyarsa ,yayunta da kanenta, dukkaninsu suna rayuwa cikin Fada da matan su da
'Ya'Yansu Waziri, Sarkin Fada, da Sarkin Yaƙi.
Waziri shine Mijin Hajiya Maimuna Yaranta mata yan biyu Nasmah da Basmah.
Sarki Yaƙi mijin Hajiya Rabi suna da yara uku mace Ɗaya Khalesa da kuma Ameen da Noor,da
kuma sarki fada mijin Magajiya Da yarinyarsu Ɗaya Rumaisa.
Prince Adeel Muhammad Rohaan shike tafiya da shigar da fitar dukka wani kudi da ke wakana
a MASARAUTAR BENONI kasancewar ya kammala digirinsa a bangaren tattalin arziki.
Khalesa da Nasmah suna masifar sun Prince Adeel sanadiyar yadda kowa ke bayyana
soyayyarsa gareshi yasa basa shiru da juna ko kadan, wajen zama ma in daya na gun daya
bata taba zuwa.
Hajiya Maimuna da Magijiya suna matuƙar nuna soyayya tare da kauna ga Adeel cike da
gujewa dukkan abun da zai iya cutar da shi saɓanin sauran matan da ke bayyanar da kishinsu
da tsantsar tsana a zahiri.
Aranar da Yareema yazo duniya aranar sai da aka nemeshi aka rasa a Masarautar daga
karshe sai Uwar Soro ce ta tsinto shi cikin kwali a na kokarin fidda shi daga fadan.
Hakan yasa tun Adeel na karami Mai Martaba ya zaɓi kebantar da shi tun yana da shekara Uku
ya koma gun Uwar Soro har sai da ya fara girma ya kammala secondary zai shiga Jami'a kafin
aka fara bayyanar da shi Wanda tunanin wasu ma da yawa a garin gabadaya ya mutu fitowarsa
kuwa ya girgiza tunanin kowa da ke Masarautar da garin.
Wannan kenan.
Karfe Bakwai na safe
Uwar Soro ta ga barci Gaaji fa bana karewa bane tadata tayi ta ce mata tayi sallah.
Kallonta tayi ido duk kwantsa ta ce, "Sallah? Tab ni fa ban girma ba ai sai an girma ake sallah ki
barni inyi barcina ni."
Ta kara shigewa bargo.
Sai da taji tace mata ga abinci aiko zumbur ta tashi ta na kokarin kubcewa.
Uwar soro ta ce, "aa fa sai kinzo munje Kinyi wanka Kinyi brush kiyi alwala kiyi sallah kafin kici
abincin nan?"
"Boroshe? wannan abun na jiya da kwashe mun jini ko? Na rantse banyi haka kawai aje ata
kwashe mun jini saidai in wannan abun zaki sammun abaki inshanye shi kam da gardi aradun
Allah kums wanka nayi jiya ai banyi yau sai ranar sallah ehee."
Uwar Soro ta ce, "to tashi muje kiyi dai koma miye sai kici abincin."
Fashewa da kuka Gaaji tayi tana, "Ni yunwa nakeji hanjin cikina kuka suke,na shiga ukuna na
mutu na lalashe