Showing 1 words to 3000 words out of 35581 words

Chapter 1 - FIN KARFI 3 end Na Marubuciya halima Abdullahi Mashi .pdf

 *FIN ƘARFI BOOK 3*



*LITTAFIN*
*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*



Page 1


Shiri sosai tayi dama Sarkin gayu ce tayi ƙyau ƙwarai dan tana da irin jikin nan da ake ce ma
karuwan jiki,ko wane kaya tasa sai ya yi mata ƙyau an ɗebe su sai hotel ɗin da aka tsara
haɗaɗɗiyar dinner, wacce abokan Ango suka shirya guri ya yi guri sanda suka isa,jin gaban ta
bai faɗi ba yasa ta shiga cikin ƙwanciyar hankali suna zaune an soma ciye-ciye . Can sai taji
gabanta ya yi mugun faɗuwa take ta ji komai ya ginshe ta duk da waƙar da mawaƙin keyi da
farko ta shiga ranta, amma yanzu sai taji komai ya tsaya mata cak. Da sauri ta miƙe Sadiya da
Munira suka dube ta, ina zaki? Ta ce ina zuwa,can bayan wasu ƴan labulaye taje daga inda
take tana duban ƙofa. Haka kawai taji cewa yanzun zai shigo.


*** **** **** ****
Dady ya fito wanka ya kuma gajiye yake jin shi ba dan bai samu halartar ko ɗaya daga cikin
programs ɗin bikin ba da zaya huta ne don yayi azumi yau kuma a wahale yake ya ɗan ja tsaki
shima yana tunanin haka nan zaya haƙura asa bikinshi da Zainab ya gaji da azumin nan shi
kanshi yasan yana buƙatar mace kuma yana ganin kamar yana da ƙarfin sha'awa shiyasa gara
ya yi auren tunda wadda yake so bazai samu ko ganinta ba bare har ya aura.

Shadda kalar blue hularshi da duk kayan da yasa blue ne,rafar ƴan ɗari biyar ya zuba cikin
aljihu ya fesa turare ya ɗauki key ɗin Hummer ya fito. A falo ya samu Sunday yana zuba
Hollandia cikin firji, ya ce "Sunday kai min ɗaya cikin motar daka goge min", ya ce "Ok sir." Ya
ɗauka ya fita yana matuƙar mamakin irin son da ubangidan nashi kema wannan Hollandia ya
kamata campanyn ta suyi mishi ƙyauta ta musamman,ko dan tsananin ƙaunar da yake mata."

Gidan su Zainab Dady ya wuce a phone ya kirata ta fito bayan tayi sallama da mahaifiyarta,
Hajiyarta tana tsananin son ƴarta Zainab ta auri Dady ba dan komai ba sai don iyayenshi sun
tara, haka kuma shima ya tara sai godiya.

Yana daga cikin mota yana kallonta ta nufoshi cikin wani leshi ɗan gaske mai kalar green yasha
ado da zare silba haka sarƙa da ƴankunne suma silba jaka da takalmi sai wani ɗan mayafi
ƙarami duk farare ta yi ƙyau sosai sha'awarta ta ƙaru a zuciyarshi, ta shiga motar bayan ya
buɗe mata ƙamshin jikinsu ya buɗe su,ta dube shi My dear har na zaci ka fasa zuwa dani, ya ce

"saboda me?" Ta ce naga goma ta wuce sannan baka kira phone ɗina ba, ya ce ina can ina
tunanin yakamata mu ma azo mana dinner fa dan na gaji da rungume filo yakamata nima nasan
halin da nake ciki, daɗi ya kamata ta ce ba na ce maka ba tuni, amma ka ƙi wai na jira ka,Ƙila
kafi son ƙwana da filon shiyasa." Ya shafi fuskarshi ranar asabar za'a kawo lefe da komai tunda
Allah yasa sun san komai dama nine matsalar kuma yanzu nima ina buƙatar auran,sati Uku
zamu sa fa.?"

Cikin zumuɗi Zainab ta ce "Ya yi nima na matuƙar ƙosawa."

Ya dubeta "dame kika ƙosa?" Ta ce "Da abin da yake hana ka bacci." Kai ya girgiza yana
mamakin Zainab, Sam batada irin kunyar nan ta mata, ya tuna Pretty ɗin shi, ita kam kowane
lokaci ya yi mata wata magana mai ɗan nauyi takan rufe fuskarta da tafukan hannayenta ta
ce,kai ko? Ita kam Zainab sai dai ta biyeshi suyi,hakan baya birgeshi yana son mace mai kunya
da jan aji.

Suna shiga gurin dinner yaji gabanshi ya faɗi inda sabo ya saba,ba wata Pretty ɗin shi a nan
gurin, zuciyarshi ce dai kullum tana ayyana mishi sai gabanshi ya dinga faɗuwa, haka ya raya a
ranshi don haka sai kawai, ya shige, sun samu an daɗe da soma dinner, amma duk da haka sai
da aka sanar da zuwanshi a matsayin babban abokin ango akan idon Ruƙayya suka shigo, tana
dubansu san da suka zarce kusa da ango suka zauna yayin da Zainab ta maida ɗuwawunta
gurin da Ruƙayya ta tashi, gaban Ruƙayya ya faɗi ta tsorata da ganin Zainab domin ta gane
wacce suka haɗu a saloon ce, ta gode Allah da yasa ta tashi don haka can ta fita duk da tsoron
dake cike fal a ranta haka ta zauna a harabar Hotel ɗin tunda ga haske tamkar rana.

Sadiya ta dubi Munira "M Bash har yanzu kusan awa Ruky M bata dawo ba fa." Munira ta ce
"Kai gaskiya ki je ki duba ta, tunda ba phone a hannunta bare ma mu kira."

Son Guy (kamar yadda suke kiran Dady) ya dubi Al-Mustapha.

"Ina neman afuwa Musty bamu samu isowa akan kari ba." Zainab ta ce "Ya hidimomi ango?"

Al-Mustapha ya ce da godiya.

Zainab ta dubi Munira "Amarya ya jama'a?" Munira bata gane Zainab ba, har suka gaisa suka
gaisa da Sadiya basu gane ta ba, Zainab ta ce "Naga baku gane ni ba ko?" Sadiya ta ce "Ni dai
ina son tuna inda muka haɗu." Zainab ta ce "A saloon." Nan take suka tuna ta, amarya sun
gaisa da Son Guy inda ya yi mata ƴar tsokana. Zainab ta ce "ina ɗayar nan kuma mai gashi?."
Sadiya ta ce "kina nufin Ruƙy M ko?" Ta ce "Yes ita kam bata zo ba?" Ta ce yanzun nan ta tashi
ko ina ta shiga Oho, Zainab ta ce "Ashe zamu gaisa." Munira ta ce "Armaya'u ki je ki duba ta kin
san fa Ruƙy ƴar daru ce zata iya tafiya gida."

Al-Mustapha ya ce "Kai Ruƙy ɗin nan tana da shagwaɓa,da ƙyar dama ta zo.

Shiru Dady ya yi yana ƴan dube-dube tamkar baisan mai suke cewa ba, amma kunnen shi yana
gurin su,a ranshi kuma sai yaji yana mai tsananin son yaga Ruƙy M ɗin nan, wancan karan ya
kuskure ganinta sakamakon wanka da tashi ga, yanzu kan shi sai fa yaga kalarta, shi kam
dama yana matuƙar girmama mai sunan ta,yasha alwashin in har ya haifi ƴa mace sunan ta
Ruƙayya. Nan ya tuno ma kanshi son Ruƙayya take hankalinshi ya tashi kanshi ya shiga
sarawa nan ya ji zuciyarshi ta tsani duk wata mace, duk hirar da Al-Mustapha yake yi mishi sam
bai ji ba,sai da Zainab ta ce My dear ya kamata ka duba masu waƙar nan tuntuni sai waƙa suke
yi. Nan ya tashi cikin sanyin jiki yana musu liƙi, Zainab ta zuba mishi ido tana tsananin son shi
ita ma nan take ta tashi taje tana mishi liƙi, Ango da amarya suma suka taso suna ma su Dady
liƙi nan fa guri ya kaure mai waƙa sai rerawa yake yi.

Ruƙy wacce abin duniya ya dama sai gizo Dady ke mata tana ganin san da suke shigowa da
Zainab fuskarshi wasai ƙyawun shi ya ƙaru fiye da da, wata kamala ta musamman ta sauka a
fuskar shi, ya zama namiji sosai ga wani ɗan tumbin kuɗi da ya fito ya yi mishi ƙyau,a da sam
bata son tumbi amma na Dady ya yi mishi ƙyau.
Hawaye suka zubo mata lallai Dady ya karya alƙawari. Ta tuna da yanda suka so juna ashe duk
na baki ne,sai yanzu ma tayi wani tunani, gaskiya ya kamata ma ta gane tuntuni dan me ya
hana ya neme ta tuntuni bayan rabuwar su? Kuma phone ɗin da ya bata me ya hana shi kiranta
akan layin. Har ta tafi makarantar ƙwana? Duk ma shekarun nan da yana sonta daya neme ta,
don haka taba kanta baki tare alƙawari sauraron duk wani wanda ya zo da sunan sonta. Kuma
daga yau tayi banƙwana da garin Abuja gobe tana tafiya shikenan,in ba kuma M Bash bace ta
haihu bata ƙara zuwa bare ta ganshi. Kai tana ganin ma gara ta je ta auri talaka ɗan'uwanta ya
fiye mata ƙwanciyar hankali. Ga Nasir tela duk da ya yi aure har da yara uku,yana nan yana
nacin ta har tayi degree ita kam yanzu zata daina biyewa ƴaƴan masu dashi ɗin nan,gara
Armaya'u da M Bash suna da halin shiga law school ita kam zata je service ɗin ta ya fiye mata
tana gamawa ta nemi aiki koma a ina ne kafin Allah ya bata miji, tunani bar katai sun cika ta har
san da aka tashi.

Tana ganin mutane sun soma fitowa, sai ta koma can gurin motar da suka zo cikinta. Ta ganin
su Armaya'u da sauran ƙawayen suna sallama da Zainab, yayin da Dady dasu Al-Mustapha
suka nufo gurin da take. Tsoro ya kamata da sauri ta zaga bayan motocin ta ɓoye bayan wata.

Jikin wadda ta ɓoye ya shiga tana jin san da yake cewa Musty "Musty Allah ya bada zuriya
ɗayyiba, kayi ƙoƙarin samun Baby a yau dare na farko." dariya suka saki sauran abokan suna
cewa "Gaskiya ne Son Guy." Ya ce Zee zo muje dare nayi fa." Ta na barwa su Sadiya saƙon
gaisuwa zuwa ga Ruƙayya, ta zo tana cewa,My dear mu tafi ko? Ya ce shiga, ta tsugunna tana
jin su a bayan motar da bata zata tashi bace sai da taji ya tashi motar ta koma bayan wata da
sauri.

Yana bari gurin ta miƙe tana maida numfashi taje gurinsu Munira dake ta shishshiga mota.
Sadiya har tsoro ta ji ta ce daga ina? Ruƙy ta ce ku muje kawai basu jima a gidan Munira ba
Abokan ango suka ƙwashe su sai gidan Mom. Sun cika su uku Munira M Bash, Sadiya

Armaya'u, Ruƙayya M Sani, tayi ta yi da safe su biyo kafin su wuce, sun ce to dan ta ƙwantar da
hankalinta, amma ba zasu dawo ba saboda Armaya'u Kano ta nufa, Mom ta haɗa su da kayan
biki da kuma godiya tare da cewa suyi ma iyayen su ban gajiya. Dan Umma ta zo Hajiyan su
Sadiya ma tazo.
Tunda suka dawo bikin Munira kullum maganar aure Umma da Affa suke mata,ita kam ta ƙosa
a tura su service. Takardun na fitowa sai taga ita Legos aka tura ta, bata damu ba dan ita
burinta shi ne ta matsa daga gidan.

Ta gama cin tuwon ta ƙwashe ƙwanukan har da na Umma ta nufo bakin rijiya tana wankewa,
Umma dake cikin ɗakin Affa tasa baki ta kira Ruƙayya, ta amsa tare da miƙewa ta nufi ɗakin.

Gabanta ne ya faɗi san da taga takardar ta a hannun Affa, bayan ta samu guri ta zauna sai Affa
ya ce "Ummanki ta sanar da ni zaki tafi Legos?" Gaban Ruƙayya yana faɗuwa ta ce "Eh, can
aka tura ni ɗazun naje na amso." Ya ce "A da dai kinje Kano, yanzu ma da Kanon ne ko irin su
Katsina jihohinmu na nan Arewa sai in yarda amma ba zan amince ki je gari kamar Legos ba,
a'a." Shiru Ruƙayya ta yi har sai da Affa ya gama sannan ta ce "Kayi haƙuri Affa wata tara ne
don Allah kayi haƙuri."

Ya ce "Ke ba ajin zancen aure a bakin ki sai dai na karatu,ki sani na matsu naga auren ki, Allah
yasan nayi miki yanda zan iya ita wannan ƙawar taki da ku ka je biki,ba gashi ba tayi auran in
ma bautar ƙasar ne ai tana ɗakinta zatayi yanzun ko?

Ruƙayya ta ce "Affa su fa karatu zasu cigaba law school zasu shiga dubu ɗari biyu da hamsin,
kuma suma wata tara ne zasuyi."

Ya ce koma menene ai yanzu a ɗakinta zatayi shi yi ko? Shiru Ruƙayya tayi Affa ya cigaba da
mata masifa kan aure don haka ba batun wani service.

*** *** ****
Goma daidai ta gama tsantsara ƙwalliyarta cikin Ankon bikin Munira da suka yi,ta fito ta shiga
ɗakin Umma.

Umma ta ce "To maimakon ki tuna min sannan in sanar da Affanku shine ki kayi shiru." Ta ce yi
haƙuri Affa zai ce a'a ne kinsan baya son yawan zuwa." Ta ce ki gaida su, Shagon kusa da
lungunsu ta tsaya tayi ma su Mama da su Muhsin tsarabar chizee da bisket. A hankali take
tafiya bakin shagon Nasir "Kai Oga gafa mutuniyarka." Inji wani yaron shagon shi "Wa kenan.?"
Yaron ya ce "Ruƙayya,kai Oga yarinyar nan aƙwai yanga,dubi tamkar mai tausayin ƙasa , koda
yake ai tana da abubuwan yangar."

Nasir ya miƙe daga aikin da yake ya fito ya tsaya suka gaisa ya ce zaya zo da dare. Bayan ta je
gidan Murja sun wuce gidan Fati a can ta ce don Allah su roƙar mata Affa ya yarda ta je service
suma sun mata ƙorafin aure ta yi musu ƙaryar cewa ai aƙwai wanda suka haɗu dashi bikin

Munira kuma shi zata aura.

Kafin ma ta gama service komai zai kammala kuma zaya yarda tayi aikin ta. Sun yanke
shawarar kan cewa Ruƙayya ta je ta samu Yaya Amina da Yaya Suwaiba da Yaya Sadiya ta
gaya musu su haɗu ranar juma'a kasancewar Affa in ya dawo sallar juma'a baya komawa
kasuwa shi ne suke son magana dashi.
*** *** *** ***
Yasha mamaki da ya samu gidan tamkar kasuwa, ƴan jikokinshi suka yi mishi oyoyo, ya ce biki
kuke yi ne a gidan?" Ummansu wacce ta fito dan taran shi, ta ce, sun zo gaida kaine affansu."
Ya ce "sai dai bayan masallaci don lokaci ya ƙore,in na dawo sai mu gaisa." Sun mishi sannu da
zuwa sannan suka koma suka ci gaba da hirarsu.
Ɗakin Umman shi ma ya shigo suka dinga gaishe shi ɗaya bayan ɗaya Sadiya ce ta soma
magana "Affa dama gurinka muka zo." Ya ce to ince dai lafiya? Ta ce lafiya lau dama kan
zancan Ruƙayya ne. Muka ce don Allah kayi haƙuri ka barta tayi bautar ƙasar tunda wata tara
ne. Suwaiba ta ce kuma Affa ai Auta tana da kamun kai munsan zata tsare kanta," Amina ta ce
"Kayi haƙuri Affa wata tara kamar yau ne." Su kuma su Murja da Fati suka ce "Haƙurin da aka yi
na shekaru kusan biyar ban dama na secondary ai wata tara bazaya ga gara ba.

Ya ce "To duk naji jawabin ku yanzu, Amma ban ji wacce tayi zancan aure ba,ku ɗauki misali a
kanku aƙwai wacce ta wuce secondary dukkan ku? Suka ce a'a, ya ce na mata haƙuri ko ban
ba? Suka ce kayi, ya ce, to ta haƙura gara ma da da tsayayye ne da sai na amince.

Sadiya ta ce "Aƙwai wanda suka yi magana, haka suka yi tayi kafin daga baya Affa ya ce yana
da sharaɗin,sharaɗin sune zasu ɗauki nauyin yi mata siyayya, zuwa kuɗin mota dan bashi da
kuɗi. Ya ce karatun ta ne ya cinye komai harda kuɗin da bawan Allah ya aiko mishi da zakka,
suka ce mutumin nan ko wanene yana da mutunci, Allah yasaka mai da alkhairi. Umma ta ce
ƙwanakin nan ba'a yi sati uku buhun shinkafa huɗu da taliya ya aiko mana gashi nan har yanzu
ita muke ci Affa ya ce hakane gashi ya ƙi mu haɗu ina son in mai godiya ba hali. Yaran suka ce
Allah ya saka mai da gidan aljanna shima ya biya mishi buƙatunshi.

Sun gama yanke shawarar su kowacce zata bada daidai aljihun ta mata kenan sarakan
zumunci,Yaya Fati ta dubi Ruƙayya "Auta don Allah gidan mutumin nan na kusa da Bus stop
zan aike ki,mai saida litattafan Hausa, ina son wani littafi ne sabon fitowa ne,na je shagon shi ya
ce min suna gida.
Ruƙayya ta ce "To ki koma shagon mana tunda yanzun dai nasan baya gida ƙila ma ya kai
takardun shago, Fati ta ce "Ke dai baki son zuwa ne bari in zamu wuce zan biya da kaina."

Sadiya ta dubi Fati ta ce "har yanzu kina nan da shegen karance-karancenki ɗin nan."

Murja ta ce "Ai in gaya miki sai abin da ya yi gaba in dai Fati ce tunda mijinta ya ɗaure mata

gindi.

Fati ta ce "Dole ne ya ɗaure min tunda yana ganin amfanin shi, Allah ku kun jahilci karatun
Hausa ne kawai, amma yana da fa'ida sosai matsawar za kiyi amfani da abubuwan da ki ka
gani na ƙaruwa zaki koyi kula da mijinki yanda zaki zauna da kishiya da dangin miji,ban da
wannan ga kalolin soyayyar da zaki ma mijinki koda gurin ƙwanciya ne, sannan....." Dundu
Amina ta sakar mata tare da faɗin.

Lallai Fati Yaya Sadiya ki ke gaya ma maganar ƙwanciya da miji?.

Suwaiba ta na dariya ta ce "Allah ya ƙyauta miki Fati." Ita ko Ruƙayya sai tayi waje, Sadiya
kuma ta ce "Uhm ni dai ai kallon ta nake yi." Fati ta ce "Kun ji ku da wani abu, dukkanmu ba
mata ba ne.

Murja ta ce "kina da wani da yake bayani kan ƙwanciyar ki ara min." Ta ce bari in kinzo gidana
sai muyi maganar.

*** *** *** ***
Ruƙayya ƴar gata sun haɗa mata komai ta tafi garin Legos. Haka aikin nasu ya yi ta cigaba
ƙwanci tashi yau sati shida kenan Ruƙayya tana garin Legos, duk waɗanda suke tare tafi
shaƙuwa da Nuraddeen M Adam ɗan Kano ne ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login