Showing 3001 words to 6000 words out of 35581 words
Chapter 2 - FIN KARFI 3 end Na Marubuciya halima Abdullahi Mashi .pdf
yaushe suna tare.
Yau sati ta fito sanye da baƙar doguwar riga gyalenta baƙi takalmi da kuma baƙar jaka. Ta yi
ƙyau sosai, Nuraddeen ya dube ta,sai ina Ruƙy, ta ce "Ina son naje saloon gashina ya yi datti
ina son na ɗan wanke, ya ce to bari muje, suna tafiya suna labari har saloon bayan an gyara
mata ya nemi ta rakashi kasuwa sun shiga gari sosai kafin su ga wani super market.
Gaban Ruƙayya ya yi mugun faɗuwa, ta tsaya, Nura ya ce "Kin gaji ne?" Ta ɗan wayance.
Sosai ma, ina son na huta" ya ce "To mu ƙarasa daga nan sai gida suna shiga idon ta ya sauka
akan Dady,yana tsaye yana waya ta ja gyalenta ta rufe gefen fuskanta ta kuma shige ɗaya
gefen.
Dady bai kula da ita ba sai dai gaban shi ya yi mugun faɗuwa, waige-waige ya shiga yi tamkar
mai neman wani. Lokaci guda kuma ya fita wajen. Sun jima sannan suka fito bata ganshi ba
tanata yi ma Allah godiya. Sai dai kuma taji sanyi ganin da tai mishi. Shi kam Dady tana ganin
kullum ƙara masa ƙyau ake yi,yaya zata yi da son Dady?.
*** *** *** ***
Hajja ta dubi Dady sannan ta dubi aƙwatunan gaban ta. Haƙiƙa kaya sunyi tuzuru, sai dai nace
Allah yasa kada itama muji shiru irin na wancan lokacin, don wannan karon in bai yiwu ba Allah
ƙauye zamu je ma samo maka mata,mun gaji da ganin ka haka,ko so kake sai na mutu? Ya ce
"Allah sarki Hajja insha Allahu sai kin goya min ƴaƴa da jikoki."
Ta ce "Allah ya tsare ni in samu ma inga auran naka,ai ko yanzu nagode ma Allah.
Ya ce "To Hajja zan wuce amma ranar juma'a zan zo nan Kaduna don haka zan iso da azumi
zan buɗe baki a nan, Please ai min waina da fankasu,in kuma samu Hollandia mai sanyi, ta ce
Allah shi kaimu, yanzu ai kayi hankali ba irin da ba, ya ce da me nake yi? Ta ce wancan auren
da kayi bai yiwu ba ai kayi rawar kai,nan fa kazo kasa ni gaba kana cewa ga waya in ma
Momyn ka magana su wuce da wuri kai kayan lefe,yayi murmushin yaƙe tare da girgiza kai don
Hajja ta tuno mishi wani abu mai motsa rai ya ce "Hajja bazaki gane ba ne wancan auren da
man aƙwai bambanci,na tabbata inda ace Pretty ce zan aura wannan auren tabbas cewa za kiyi
da,ban yi komai ba saboda rawar jiki ya tsura ma window ido tamkar a nan zai ga Pretty ɗin shi
a gurin. Wasu ƙananan hawaye suka taru a zagayen ƙwayar idonshi. Ya furta a hankali "Allah
ya rage ma aya zaƙi." Ya dubi Hajja har in mutu zan kasance ina son Pretty."
Hajja ta yi data sanin furta mai maganar auran shi na da,
A fili ta ce "Nasan kana son ta Yusufa, ta dalilin ta ka samu hawan jini,baka dangana da
yarinyar nan ba sai da aka haɗa da roƙon Allah sannan ka lafa kayi haƙuri,matar mutum kabarin
sa, ya ce "Hajja sam ban so ni aka haɗa da roƙon Allah ba wai don na dangana da son Pretty
naso a ce son ta ya kashe ni,." Hajja ta ce "Ashsha! Ashsha kul na kuma ji koda bai kashe ka ba
ai ya saka rayuwarka cikin wahala tunda in ciwon nan ya tashi duk hankalinmu tashi yake. Ya ce
ai Dad shine ya ja min dan da basu cuci Affa sun zalunce shi ba wallahi na san ba zai hana min
Pretty ba,kuma banga laifin Affa ba domin an yi mishi FIN ƘARFI, kafin Hajja ta ce wani abu
wayar Dady ta shiga ƙara ya duba Hussain ne ya tuna suna can suna jiranshi game da
programs ɗin bikin shi. Ya ce "Hello, Hussain sorry kuna jirana ko, ina zuwa. Ya kashe wayar
sannan ya kira layin direban shi ya ce ka sameni gidan Hajja a Kabala ka hawo achaɓa kazo ka
jani.
Sabi'u ya ce "To ƴallaɓai." Komawa ya yi ya jingina da kujera. Hajja ta dube shi ta ce "Ina ce
kace tafiya zaka yi." Ya maida numfashi bazan iya jan motar bane shine na kira direba ya jani.
Gaban Hajja ya faɗi ta ce,ba dai jikin ba ne? Ya ƙaƙaro murmushi ya ce "a'a ba jikin bane
Hajja,kin san jiki da jini gashi muna yawan zirga-zirga aikin ba hutu,ta ce To bari in baka wani
magani na gajiya ne shima na hawan jinin ne, ta miƙe ta shiga bedroom ɗin ta ta ɗauko garin
magani ta miƙa mishi.
Gashi kuma kai ba gwanin shan koko ba sai kasha da Yoghurt ko Hollandia naka,ya yi,sai
sannan direban ya yi mishi waya ya iso, ya ce to,gami da faɗin Hajja ni zan tafi." Ya ciro kuɗi,ba
dai ki buƙatar komai ko? Ta ce a'a ba komai, ya miƙa mata kuɗin da shima bai san iyakar su
ba............
️️️
[7/31, 16:44] Ummi Tandama: *FIN ƘARFI BOOK 3*
*LITTAFIN*
*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
Page 2
Baisan yawan su ba, ya ce "gashi na cin goro, wannan kuma ki ba ma Saude." Ta ce mungode
Allah shi albarka ya biya buƙatu. Ya ce amin Hajja nagode, ta ce a'a nice da godiya Yusufa aini
sai hamdala da Ubangiji ya barni da raina, da ubanka ne me min komai gashi har mun kai
matsayin da ya haifeka gashi kaima kana kula dani, ya ce duk albarkarki muke nema Hajja.
Har waje ta rakashi inda ya shiga mota direba yaja shi suka tafi.
*** *** *** ***
Yau kam a gajiye Ruƙayya ta taso daga kotun da aka tura ta game da wata shari'a. Bakin gate
suka yi kiciɓis da Nuraddeen Kano. Ya ce a'a Ruƙy yana ganin ki haka hula a hannu jaka hannu
gari yai sanyi? Ta ce kai dai bari kawai Nuri,yau ɗin nan na gaji sosai fa ta nufi ɗakin su ta shiga
sai da ta huta tayi wanka taci abinci sannan ta yi sallah.
Washegari tana ɗauraye after dress ɗin ta da T shirt ɗin ta,Nura ya sameta Ruƙy ina tunanin
duk ma yanda za'ayi gobe Friday koda yamma ne zan je Kano, ta ce ka dawo yaushe? Ya ce
Sunday ko Monday." Ta ce Kash, nima da ina da issasun kuɗi da mun je sai nima na sauka
Kaduna,in yaso in kana dawowa sai na baka adireshin gidan mu sai mu dawo.
Ya ce "Oh muje in kuɗin naki sun kasa sai na cika miki dan nima sai a hankali,allwasce ɗina ne
na wancan watan ta ce aini nawa tuni sun sha aiki.
Ranar juma'a tunda safe suka soma shiri,tasowar asuba suka yi,dan haka huɗu tai musu a
Kaduna. Sun tsaya a garejin Mando nan Ruƙayya ta sauka,Nura ya rako ta inda yake cewa
gashi ba waya a hannunki bare in na shigo unguwarku na kira ki. Ya kamata ace kina da waya
fa ba girmanki ba ne. Ta yi dariya sannan ta ce Nuri kenan,Ni nan daka ganni ban so na riƙe
waya ba ne, Amma ko ada,na riƙe waya a lokacin da sai wanda ya isa ne yake riƙewa, kuma
ma yanzun ban ga dama bane, amma ka bari insha Allahu sai dai kaji calling ɗina. Alƙawari zan
kiraka da layina, ya ce shikenan.
Mashin ta samu ɗari uku tun daga Mando gareji zuwa Kabala su kenan kuɗin ta dan haka ta ce
muje ai gida nazo kuma bana son shiga mota ga hadari yana ta harhaɗowa gara na isa gida
akan kari,bana son ruwa ya taɓa lafiya ta. Sun iso daf da shiga Kabala suna kan titin
independence aka soma tsula ruwa nan kuma mashin tayi faci. Ruƙayya ta ce "Oh ni Ruƙy ya
zanyi kenan? Ta sauka ta bashi ɗari ukun ya ce "Yaya zaki bani duka gashi bamu kai ba? Ta ce
ba komai kaje kawai bari na taka, ya ce ga ruwa? Ta ce kar ka damu,tana tafiya duk ta jiƙe.
Tun daga nesa Sabi'u ya dubi ubangidansa "Ƴallaɓai ga wata can tana buƙatar taimako." Dady
ya amsa ba tare da ya ɗago ba, ya ce "A taimaka mata." Ya rufe baki tare da faɗuwar gaba irin
wacce bai taɓa ji ba, ya kai hange ga yarinyar da Sabi'u ya ce su taimaka mata,da tazara
tsakanin su kuma shekaru baƙwai masu ƙyau bai ganta ba, amma sai da ya gane ta. Ko shakka
ba zaya yi ba waccan Pretty ɗin shi ce, domin duk da basa tare kuma idanunshi sun daina
ganin ta wannan ba zai hana zuciyarshi kullum karanta surar ta ba, haka yake tsarata kullum.
Sanye take da jallabiya doguwa baƙa haɗe da gyalenta,jaka da takalmin ta ma duk baƙaƙe
ne,sai dai ta jiƙe sharkaf har ɗiga take yi.
Jijiyoyin jikin Dady suka tsaya cak, komai ya daina kai saƙo a jikinshi lokacin da ya tsinkayi
muryar Ruƙayya suna magana da direba yana cewa baiwar Allah shigo mu taimaka miki ta ce
"a'a, nagode Malam na kusa gida gashi kuma duk na jiƙe,ka na jiƙa muku kujera." Ya ce,
bakomai shigo taimako ne ai."
Sam Ruƙayya bata ga Dady ba kasancewar motar na waje baya ganin na ciki, amma shi Dady
yana ganin ta, tana shaga gaban motar gabanta ya faɗi sai dai har ga Allah bata zata da wani
cikin motar ba, don haka sai tayi addu'a a ranta dan kar ta faɗa mugun hannu.
Ta ɓalle maɓallan gaban abayar ta cire sai ga riga T.Shirt mai ɗauka da rubutun N.Y.S.C ta
bayyana da wandon ta, ta zage jakar hannunta ta ciro rigar sanyin N.Y.S.C tasa ta ɗaura gyale
kamar ɗan ƙwali sannan ta ciro hijabi ƙarami tasa ta maida abaya cikin jaka. Ƙamshin da take
shaƙa da faɗuwar gabanta da yaa tsananta sune suka tuna mata da wani abu, tabbas duk inda
turaren nan ya fito daga gurin Dady ne, domin tun da suka rabu da Dady bata kuma jin ƙamshin
nan ba sai yau.
Ya Allah! Ta faɗa cikin wata muguwar faɗuwar gaba, lokacin da ta dubi madubi ta ga Dady
zaune a bayanta. Daga nan bata kuma motsi ba sai ƙwatancen da ta dinga ma direba har
lungunsu. Ta ce da direba nagode fa, ya ce bakomai." Ta buɗe mota ta fita.sannan ta saci kallon
Dady ta rufe ta tafi, zuciyarta cike da mamakin Dady. Lallai duniya wai kamar Dady ya ganta ya
share ta, hawaye ya zubo mata tayi nadamar zuwan ta Kaduna a yau.
Shi kam Dady be ma san anzo har Ruƙayya ta fita ba,haƙiƙa jikinshi ya mutu, zuciyarshi ba ta
tare dashi,yana tunanin dama Pretty bata yi aure ba,ko ko tayi ta cigaba da karatun a gidan
mijinta? Auren ya mutu ne? Ko ko mijinne ya mutu? Ko ko da auren ta? Wanene zai bashi
wannan amsar. Ganin Ruƙayya ya tsorata Dady gami da firgita shi, ta taɗo mishi da wata
sabuwar muhimmiyar soyayyar ta.
A fili ya ce "Wannan karon ko Pretty tana da aure ko batada shi, koma wanene mijinta sai ya bai
mishi Pretty ɗin shi,kai koma ta halin yaya ne shi bazaya barta ba,bai san sun iso gidan Hajja
ba sai dai ya ji Sabi'u na cewa.
"Ƴallaɓai mun iso." Ga zaton shi gidan su Ruƙayyan, sai yaga gidan Hajja nan ya soma tunanin
kodai mafarki ne? Kai ba mafarki bane. Ya dubi Sabi'u ya ce "ina Pretty ɗin fa? Kan Sabi'u ya
ɗaure ya ce,wace Pretty kuma ko wacce muka ɗauko? Dady ya ce "Eh," Sabi'u ya ce ai mun
sauke gida Ƴallaɓai baka kula bane." Nan Dady ya wayance ya ce "Ok." Ya shiga gidan Hajja
ya bar Sabi'u da mamakin halin da Ƴallaɓai ya shiga kan yarinyar nan,a ranshi ya ce koda yake
fa yarinyar ta haɗu dole Oga ya ruɗe har magana yake shi kaɗai ina jin shi.
*** *** *** ***
Yaraf ya zube a kujerar falon Hajja,Saude da ke jira abinci akan centre table tana faɗin "Uban
masu gida kasha hanya,in fatan dai baka sha dukan ruwa ba?" Da ƙyar ya ce sannu Saude ina
Hajja? Ta ce gata nan zuwa tana ɗauro alwala ne, sama-sama suka gaisa da Hajja don haka ta
tasa shi da tambayoyi jikinne Yusufa ko ko gajiya ce?.
Numfashinsa yana sama-sama ya ce "Duk aƙwai." Ta ce "To ai gara ka je asibiti ko? Ya ce
"wannan bana asibiti bane ku barni na huta bana son magana." Duk shiru suka yi,yana ƙwance
har aka kira magriba, ya yunƙura da ƙyar ya tafi sallah. Hollandia kawai ya ɗaɗɗaka baici komai
ba ya kira direba a waya ya zo ya ɗauke shi. Hajja ta yi tayi ya ci abinci kasancewar ya yi azumi
ya ce "Kiyi haƙuri Hajja ba zan iya cin komai ba, ina cikin damuwa ki min addu'a." Ido ta bishi da
shi har ya shiga cikin mota sam baya tare da tunanin shi, tunanin shi kawai ta ina zaya fara da
wannan lamarin.?
A hankali ya ce "Sabi'u kaini gida gurin Momy."
Yana zube gabanta kan kafet ya yin da take zaune kan kujera, gabanta sai faɗuwa yake yi
saboda bata san dame ya zo ba. Kallonsa tayi yana bata tausayi dan tuni Dady ya mance da
ake dariya,ko yanayi su dai ya daina musu.
Sannan ya zama miskilin gaske ga zafin rai da ya koya waɗannan halayen sama taka ya same
su tun bayan da ya gama jinyar rashin Ruƙayya, sai dai har Yanzun yana basu girman su tare
da musu biyayya.
Ganin bashi da niyyar magana yasa ta ce "Dady menene damuwarka? Ya dubeta idanunshi sun
kada sunyi ja ya ce "Momy naga Pretty, Momy Ruƙayya na gani. Shin da gaske ne tayi aure
kamar yanda kuka sanar da ni?.
Gaban Momy ya yi mummunan faɗuwa cikin tsoro ta ce "Haka magabatanta suka sanar damu."
Ta cigaba "Ka nutsu Dady kaida gobe kamar yanzu ka zama Ango." Dubi yanda gidan nan ya
cika da ƴan biki sannan ka zo min da labarin ka ga Ruƙayya me ganinta zaya amfana maka a
halin yanzu?"
Ya yi wani murmushi irin na ɓacin ran nan ya girgiza kai shi kam yana mamakin yanda kowa ya
kasa gane irin son da yake ma Pretty, ya furzar da wani huci mai zafi sannan ya ce.
"Momy aini nama manta da wani labarin zan yi aure, domin dama a rashin Pretty zan auri
Zainab, kuma yanzu na ganta don haka har ga Allah na manta da wani batun aure.
Gaban Momy ya faɗi,dan tasan zaya iya fasawa don haka sai ta soma lallashinsa.
"Haba Dady yanzu, wannan girmanmu ne,ace wancan karon mu tara mutane abu bai yiwu ba,
yanzu ma mu ƙara maimaita na da? Ka tuna burinmu muga ƴaƴanka shekarun mu sun tsawaita.
Haba Dady ko so kake sai mun mutu sannan zaka yi?"
Hawaye suka zubo ma Momy abin da ko cikin mafarkin shi baya son gani,wato kukan Momy.
Da sauri ya isa gabanta
"Kimin afuwa Momyna." Ya sa hannu yana share mata hawayen, "Kada ki min haka Momy, abin
zaya yi min yawa,ban sama kaina son Pretty ba daga Allah ne,nima na kasa control ɗin kai na
ne, Momy ki fahimce ni." Ido ta zuba mishi gami da tausaya mishi, don haka sai ta ce "Dady kai
namiji ne mijin mace huɗu,kana da izinin auran Zainab da Ruƙayya har ma da wasu biyu idan
kana da buƙata. Yayi shiru na wasu lokuta sannan ya ce "Shikenan ku ci gaba da bikin ku." Ta
ce "To amma nafi son ka ƙwantar da hankalinka kada ciwon ka ya tashi,ka bi komai a sannu har
a gama wannan ko.? To kawai ya ce mata, ya miƙe ya nufi shashin daya gina wani tsatsaran
plate mai ƙyau a cikin gidan nasu.
Kai tsaye bedroom ɗin shi ya nufa ya shige toilet duk da sanyin da garin ya ɗauka sakamakon
ruwan saman da ake yi tun yammacin na yau,bai hana shi sakarwa kanshi ruwan sanyi ba sai
da yaji sanyin yana ratsashi sannan ya fito mai ya shafa ya saka jeans baƙi da ƴar shirt sannan
ya ɗauko wata rigar sanyi jibgegiya mai laushi ya saka yasa hularta. Har lokacin sanyi yake ji,
zazzaɓi ne ya sani amma sai ya share ya tsani shan magani ya ɗauki key ɗin mota ya fito.
Yana ƙoƙarin shiga motar,motar Hussain tana shigowa, dole ya tsaya ya ƙaraso kasancewar har
Yanzun ana ɗan yayyafi sai ya shiga gaban motar Hussain ɗaya gefen, suka yi hannu, Hussain
ya ce Ango ya za'ayi ne? Ni ɗazun na kiraka muna ƙoƙarin tafiya sai kuma ka ce min kana
hanyar zuwa Kaduna. Shi ne abin ya bani mamaki tunda nasan yau aƙwai wani program shi ne
ka taho? Yanzun dai nace bari na zo naji goben sai mubi jirgi da wuri ko?"
Dady ya ɗan takure jikinshi saboda sanyi sannan ya ce "kune zaku tafi da su Saddiƙ saboda ni
bana jin daɗi zan zo daga bayan ku,ku tafi da su Dad tunda suma jirgi zasu bi, amma fa sha
biyu zasu tashi gidana zaku sauka Sunday yana nan munyi waya dashi zaku samu komai,
sannan aƙwai Abokaina nacan su Sagir matansu zasuyi ma matanku tarba sosai,ba wata
matsala ku cigaba da gabatar da komai kar ku damu da cewa sai nazo.
Hussain ya ce "Daka ɗaure munje kada ita Zainab ɗin ta zama cikin damuwa." Ya