Showing 15001 words to 18000 words out of 35581 words

Chapter 6 - FIN KARFI 3 end Na Marubuciya halima Abdullahi Mashi .pdf

ba kaya na canza na ce ni gida zanje Momy ta ce na ƙwana,na ce

a'a dole Dady da wasu Abokanshi suka kaini. Sai da suka buga gida sannan aka buɗe musu ina
ji Affa ya ce "lafiya cikin daren nan?" Suka ce Ruƙayya muka rako. Affa ya ce "Shirmen banza
can ɗin baƙon guri ne da bata ƙwana?" Dady ya ce Momy tayi ta yi taƙi yarda.

Ita dai ta shige sai ɗaki ta cire kaya tasa rigar bacci doguwa ta kitse gashinta kitso ɗaya,ta faɗa
gado. Komai haka yake dawo mata tamkar yanzun yake faruwa,ita ce ƙwance a jikin Dady wai
mijinta? Ta mirgina ta rungume filo har Yanzun ƙamshin turaren Dady jikinta keyi,ƙamshin da shi
kaɗai ta sani dashi tana son Dady shima tasan yanzun yana can yana tunaninta.
Wata zuciyar ta ce kodai yana can tare da matarshi, gabanta ya faɗi haka nema,yana can tare
da matarshi yana gaya mata daɗaɗan kalamai,kishi ya turnuƙe ta, Dady yaci amanar son da
yake mata, can ta tashi ta ɗauko wayarta bari ta kira wani yaji yanda ake ciki.

Tayi ringing sau biyu yana yankewa ana uku ya ɗauka cikin yanayin bacci yake magana......
Prettyna lafiya na neme ki ban same ki ba? Ta ce kai dai bari wai kasan menene? Ya ce a'a, ta
ce aure.........bata ƙarasa ba taji ɗif ta gurin shi ashe shi da chaji ne,ta neme shi ta gaji.

Zuwa can wayar ta soma ringing a zaton ta Nuraddeen ne don haka ko number bata tsaya
dubawa ba ta ɗauka tace Nuri kana jina? Gaban Dady ya faɗi, ya ce Pretty wanene Nuri? Itama
gabanta ya faɗi ta ce kai mai maganar wanene? Ya ce ki dai yi hankali yanzu ke matar aure ce,
shiyasa nike ta neman number ɗin ki ana ce min Number busy ashe kina ta hira da wani ƙato
ko? Ta ce kaima kayi da matar ka kada ka dameni, ya ce ki iya da harshen ki kuma ni ina da
izinin hira da matata amma ke baki da wannan damar ki kiyaye ina da kishi bana wasa ba. Ya
kashe wayar ya jefar da ita can gefe yarinyar nan fa yaga kamar bata son shi da gaske,kai ko
bata son shi zai zauna da ita koda zata rinƙa yankar naman jikinshi kullum. Alwala ya yi ya
soma gayawa Allah.

Saɓanin ita data shiga kuka rurus wai ita Dady yake gaya ma yana da damar hira da wata
mata? To zata nuna mishi mata suna suka tara.

*** *** ***

Da safe sai ga Sabi'u niƙi-niƙi da kayan tea, Ruƙayya suna zaune ɗakin Umma har da Affa ta ce
Affa yau zan koma tunda yau Lahadi, gobe ina da aiki." Ya ce "wannan ke da mijinki,ni menene
nawa?,ni da zai zo ma yau ki tare gidan shi ai da yafi min." Na ce "Affa ai min agaji in ƙarasa."
Ya ce "To ai yarda da haƙuri yana gurin mijin naki ko? Ta ce"shikenan."
Misalin ƙarfe sha ɗaya ta gama kimtsawa ta ce bari inje gidan Amina. Umma ta ce kin sanar da
mijinki? Babu ruwa na fa. Ran Ruƙayya ya ɓaci ta koma ɗaki ita dai bazata kirashi ta tambaye
shi ba sai dai kar da taje.

Sallamarshi ce ta katse tunani. Umma ta amsa,ta jiyo shi yana gaisawa da Umma, ya ce Affa ya
fita ne? Ta ce eh,ya fita. Ai Ruƙayya tana nan cikin ɗakin ta, ya ce to, tana zaune bakin gado ya

shigo message take tura ma Nuraddeen tana sanar dashi abin ya faru gareta. Ya shigo da
sallama ciki-ciki ta amsa, kamar ta share shi ta dai ce ina ƙwana? Ba tare da ta dubeshi ba, ya
ce ban ganshi ba,ta ɗan ɗago ido ta dube shi sanye yake cikin jeans blue da farar t.shirt,ta ɗan
kama shi ya yi ƙyau sosai ya fito a Son Guy ɗin shi. Ta ce waye baka gani ba? Ya ce ƙwanan da
kike tambaya, ta ɗan taɓe baki ya ce bana son taɓa bakinnan in kika ƙara zanyi maganin ki.

Umma ta zo daidai ƙofar ɗakin ta ce Ruƙayya bari in shiga nan gidan mai ɗanwake." Ta ce
Umma kada ki daɗe zan fita ne." Dady ya ce "ina zaki ne." Ta ce sai kaji? Ya yi ɗan murmushi
mai sauti ya ce to ai dai sai na yarda sannan za'a ko? Ta yi shiru ya taso ya dawo bakin gadon,
ta matsa ya ce Pretty ni kike gudu? Kar dai ki manta ni mijinki ne, ta ɗan taɓe baki, bata ankara
ba taji ya kamo leɓunanta ya manna mata kiss, tayi saurin duƙar da kanta yana ta dariya tayi
banza dashi.

Wayarta ta soma ringing ta sa hannu ta ɗauka Nuraddeen ne cikin fara'a ta ce "Nuri kaga text
ɗina? Ya ce eh, Mustapha yazo yana ce min yaga amarya." Na ce wallahi auren dole akai min,
ban san mutumin ba ai kaga kiran da aka yi min ko? Ya ce eh, ta ce To ina isowa har an ɗaura."
Ya ce Allah ya yi shine mijinki sai kiyi biyayya." Ta ce nagode, ya ce yaushe zaki shigo Legos?
Ta ce nan da anjima ma zan taso, ya ce to sai kin shigo. Dady dake zaune yana jinsu ya ce "mu
ga wayar?" Ta ce ina ruwanka da waya ta, ya ce ki bani ko na ƙwata. Ta tura cikin bireziya, ya
ce ciro ki bani tayi banza dashi, ya haɗa hannuwanta guri ɗaya, ta ce zan maka ihu ya ce Kiyi
mana ya tura hannu cikin rigar ta ya ciro wayar ya tura cikin aljihun shi. Sannan ya ce ba batun
tafiya yau sai gobe,in ma mutum ya yi mini gardama in hana komawar. Jin haka sai tayi shiru.

Sallama ta ji kamar muryar M Bash, da gudu ta fito tana oyoyo M Bash ɗina." Munira ta ce kada
ki taɓa ni shegiya ina Kaduna ina Abuja har sai dai naga ana nuna bikin ki a T.V ai Mom ma
tace tana fushi dake. Ta ce wayyo nima fa auran nan yanda ku kaji shi haka naji shi,zo dai mu
shiga. Suna shiga Munira taga abokin mijinta ta ce ashe ma angon yana ciki,ai ban san kaine
angon namu ba,sai da na gani ana nuna dinner a ɗin newline, Ruƙayya ta ce zauna ƙawata kina
ta zuba, ta ce Armaya'u ta iso?

Ruƙayya ta ce "a'a itama tana hanya ne?" M Bash ta ce eh tana hanya jiya muka shiryo tafiyar
ta kira ni da dare ta ce nasan ana bikin ki? Na ce mata na dai gani a Talabijin shine muka ce
bari muji laifin me mukayi?" Dady ya ce Gaskiya bata ƙyauta ba kuma babu inda bata kai kati ba
sai ku.
Ruƙayya ta harareshi sannan ta ce "ni fa ina Legos, Affa ya yi min waya wai inzo, hankali tashe
nazo garin nan,jiya kamar yanzun muna hanya,wai ina zuwa na samu an ɗaura min aure da
wanda ban ce ina so ba." Ta soma hawaye,M Bash ta ce "Ni fa nasha mamakin ace kinyi aure
bamu ji ba." Dady ya ce "Munira ina angon naki wato shine bai zo min ɗaurin aure jiya ba?" Ta
ce to ai yazo maka na wancan satin, ya ce to ni wannan na gayyace shi wancan ai a garin yake.
Ruƙayya ta tsani ta tuna Dady yana da aure,duk sai taji ta tsane shi. Ta dubi Munira ta ce M
Bash bari in kawo miki ruwa, Munira ta ce ina Umma? Umma ta shiga maƙota, ta fita dan kawo
ma M Bash ɗin ruwa.

Dady ya ce "Munira nayi mamaki da Pretty ƙawarki ce." Munira ta ce "wai Ruƙayya Aminiya ta
ce ta wuce ƙawa,B.U.K muka haɗu baka ganta gurin bikina ba?" Ya ce sam amma ta taɓa baki
labari na? Ta ce kasan Ruƙayya da shegen zurfin ciki, koda wasa ko sunan ka bata taɓa kira
ba." Ya ce labari na da ita aƙwai tsawo wata rana zata gaya miki." Ta ce shikenan ina kuma
Zainab? Ya ce tana Abuja kin san halin ku na mata wai bazata tsaya ba ta tafi.

Ta ce abinne sati ɗaya fa? Ya ce ke da kinsan son da nake ma Pretty a rashin ta ne fa na auri
Zee wallahi."

Ruƙayya ta shigo da sallama ta ajiye goran ruwan swan water da lakaseera. Umma da
Armaya'u suka shigo tara Ruƙayya ta fito da murna ta ce lah Umma a ina kika samo mini
Sadiya? M Bash ga Armaya'u, Armaya'u ta ce ashe ta riga ni,ɗakin ta shiga itama ta ce ashe
angon namu yana ciki? Ruƙayya ta taɓa baki, ya ce bakinki baya jin horo ko zan gyara mishi
zama. Suka yi dariya ban da Ruƙayya.

Sun gaisa da Armaya'u take tambayar shi Zainab, ya ce tana Abuja Armaya'u ta ce lallai kaji
daɗi mai mata biyu cikin sati ɗaya. Ruƙayya ta yi waje, ya ce ku daina fada naga kamar Pretty
batason ana labarin Zee. Suka sa mishi dariya, ya miƙe daidai sanda Ruƙayya ta dawo ɗakin.
Pretty zan tafi na barki da baƙin ki,bata tanka ba ta wuce ta zauna Armaya'u ta ce "Ruƙy ana
miki magana." Ta ce me zan ce mishi na riƙe shi ne? M Bash ta ce ke dai Allah ya yi ƴar iska."
Ya ce kuna nan ne? Suka ce gobe zamu tafi, ya ce Ok,zan shigo zuwa dare. Ruƙayya ta ce
baka bani wayata ba, ya tafi yana faɗin da kin ƙwata ai.

Yana tafiya suka hauta da masifa ta ce ba fa sonshi nike yi ba don ma na barshi ya zauna ne
shi ne harda ce min zai tafi, Armaya'u ta ce munafuka daga ganin yanda kike mai wannan
kallon ƙasa-ƙasan kin sonshi,ai wannan gayen baya cikin mazan da za'a gani ace ba'a so. M
Bash ta ce ƴar iska tana sonshi Ruƙy munafuka ce kin santa sumumi sumumi da ita. Ruƙayya ta
ce "ko yana burge wasu banda ni yana da fa mata gaskiya bana son kishiya,auren dole ga
kishiya? Ba zan iya ba." Har suna haɗa baki "Kada ki iya." M Bash ta ce dama yanzun ya ce mu
daina maganar Zainab ba ƙya so." Ta ce mukayi dashi? Armaya'u ta ce ke kishiya ce zata baki
tsoro? Gara ma ki tashi ki riƙe mijinki" M Bash ta ce ballantana Zainab,ni ranar da su Mom da
ƙawatar suke labarinta da Mamanta duk saina raina mata wayo. Ruƙayya ta ce wacece Zainab
ki bani labarin ta mana?" M Bash ta ce "Zainab Adam mahaifinta ministane haifaffen Sokoto,
uwar ta ƴar Gombe ce ni ko bafullatana ce a Yoben Oho,bata da mutunci matanshi uku ance
duk sai da ta koresu, harda matarshi ta farko wacce sukayi auren saurayi da budurwa, ƴaƴan ta
biyu duk mata Zainab sai ƙanwar ta Jamila, sauran kishiyoyin data kora sune masu yara maza.

Ance tana ji da Zainab sai dai babu tarbiyya, tamkar karuwa haka Zainab ta rinƙa bin maza,
Uban dama an gama dashi, shegen son kuɗi ne da uwar harma ƴar in gaya miki shine aka yi
rufa-rufa aka bawa mijinki.

Ruƙayya ta ce "na shiga uku banason kishi da mace mai shige-shige aje a sabauta ni a banza."

Armaya'u ta ce ba sai ki nemi tsari gurin Allah ba,ga addu'o'i nan na tsari. Ruƙayya ta ce nidai
an haɗani da aiki ina da kishi mai tsanani musamman akan Dady wallahi da ace be aure ba
bazan damu ba.

M Bash ta ce "kamar ya ya?" Nan Ruƙayya ta basu labarin farkon haɗuwarta da Dady har zuwa
yanda abubuwa suka kasance ta ɗaga yatsun hannunta,kunga zobunan alƙawuran da muka yi
ma juna har sau biyu. Armaya'u ku kanku shaidu ne cewa bana kula kowa, amma ba tashi
ganin Dady ba sai in ganshi da budurwa, M Bash in bazaku manta ba lokacin da muka je bikin
Uncle ɗin ku ban dawo Kaduna da lafiya ba." M Bash ta ce ƙwarai har Mom tasa Dakta ya duba
ki." Ta ce kin tuna to lokacin ne na ganshi da wannan Zainab ɗin haka ganina na biyu,dan na
uku ma tsabar wulaƙanci ban ganshi ba sune suka ganni suka rage min hanya amma ƙala bai
ce min ba har na sauka, shi ne don iko aka ɗaura min aure dashi.


*** *** ***
Sun jinjina labarin data basu, sannan suka bata shawarar yanda zata zauna da mijinta. M Bash
ta ce kada ki damu kin san kana naka tsarin Allah na nashi, Allah ya tsara ku biyun ne
matanshi.

Armaya'u ta ce ban ma ga abin damuwa ba tun da tasan irin son da yake miki." Ruƙy ta ce ke
rabamu da mazan nan munafukai ne yazo ya ce min I love You yaje ya ce mata I miss You." M
Bash ta ce koma menene yanzu dai ki dage da shan kankana da aya da dabino,da ƴan kayan
marmarin nan muna rainasu, aƙwai aiki zaki gane in kin kama su, kuma akwai wasu sinadarai
da Mom ta bani na Arabic ne, Armaya'u ta ce nifa? M Bash ta ce a'a sai anyi bikinki zan baki, ta
ce One month fa ya rage, ta ce to zan baki sai kin zo Abuja, Armaya'u ta ce zan zo amma kafin
nan zan je in fara amfani dasu kankana ɗin, Ruƙayya ta ce kai ku rabu dani ya ma samu in tare
gidan shi bare ma har na tsaya shan wani abu aje a ƙwararraɓa ni, dariya suka saka mata, M
Bash ta ce yanzu duk kishi ne matsalar ki,kina shiga hannunshi shiru za'a ji ki tunda kina
sonshi. Ruƙayya ta ce zaku sha mamaki aini bana son cin amana, kuma zan nuna mishi mu
mata dabanne. M Bash ta ce ina son fita anjima mu ɗan shiga kasuwa.

Bayan sun ci sun sha girkin da Umma tai musu can gurin la'asar suka shirya zuwa kasuwa,
Ruƙayya ta ce Umma zamu kasuwa, Umma ta ce ki ma mijinki waya ki sanar dashi, takaici ya
cika Ruƙayya su Sadiya suka ce ki kirashi, ta ce ya tafi da wayar ai, Armaya'u ta kirashi da
tawa, ta ce ai ban ma riƙe number ɗin shi ba,ke ni ban ma san me zance mishi ba." M Bash ta
ce bari na kira number Al-Mustapha ya yi min text ɗin number Dadyn.

A wayar Armaya'u suka kira M Bash ta ce Ruƙy M gashi tana ringing ta amsa tana cewa me zan
ce mishi? Ya ɗauka ya ce "Hello," ta yi shiru ya ce "who is speaking?" Ta ce Ni ce, duk da
ciki-ciki ta yi maganar hakan be hanashi gane muryarta ba, ya ce Pretty ya ya ne? Ta ce
kasuwa zamu je, tana wani ɗaure fuska tamkar tana ganinshi, ya ce to bari na turo muku direba,
ta ce daka barshi zamu hau mashin.

Da sauri ya ce kada ki yarda ki hau mashin ki jira ni, ta kashe wayar ranta ɓace ta ce kunji ko ya
samu na kira shi har da cewa kar na yarda na hau mashin wai mu jira shi. Armaya'u ta ce yana
da gaskiya aje a yadda mishi mata, M Bash ta ce ƙyale ta da Allah da kanta zakiga ta ƙanƙame
mijinta. Ruƙayya ta ce sai kuma kuyi,wayar Armaya'u ya kuma kira ya ce su fito, baya suka
shiga.

Ruƙayya na ƙoƙarin shigowa bayan suka tura ta ta zauna gurin mijinta, dole ta zauna gaba tana
wani zumɓura baki, ta ɗan saci kallon shi a ranta ta ce ya ci sunanshi Son Guy ko yaushe cikin
gayu yake, yanzun ma jeans ne baƙi da baƙar riga mai dogon hannu ta ɗameshi, fuskarshi fes
sai ƙyakƙyawan sajen da ya kewaye bakinshi zuwa gefen fuskarshi, idanunshi masu hasken
nan suna birgeta.

Ya tada mota yana cewa "Wai ke kallon fa?" Gabanta ya faɗi ashe ya gane, ta dake ta ce "Me
zan kalla a nan?" Ya yi murmushi sannan ya ɗan ɗaga murya ya ce wace kasuwar zamu? M
Bash ta ce Ruƙy wace zamu je? Ta ce ka kaimu Abubakar Gumi, ya ce me zaki siya? Ta ce
sune zasu yi siyayya, ya ce baki da kuɗi ne,in ga jakarki,ta ce a'a ni ba'a ganar min jaka,kai ka
cika tsokana kayi abin da ke gabanka..........



️️️
[8/16, 08:44] Ummi Tandama: *FIN ƘARFI BOOK 3*



*LITTAFIN*
*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*


Page 6


Ya ce "ai ni kece a gabana komai na Prettyna." Ta kuma shan mur.

Haka ya yi ta janta da magana tayi mai shiru har suka je kasuwa. Shagon wasu masu leshi da
materials suka yada zango,ƴanmatane keta siyayya a shagon Dady yana daga ƙofar shagon
yana duban Pretty ɗin shi suna taya M Bash zaɓe, duk abinda take yi baya gajiya da kallon ta,
komai nata birgeshi yake yi.
Wasu ƴanmata da tun zuwansu gurin suka maida hankali kan Dady ya tafi da imaninsu,ɗayar ta
ɗebi wasu lesuka guda biyu tazo gabanshi don Allah Malam muna musu ne wanne yafi ƙyau?
Ya ce a'a ni ban san kayan mata ba, ga mata can ƴan uwanku. Sai cewa tayi to kai wanne yafi
maka ƙyau? Nan take yasha kunu ya ce ban sani ba. Ya maida dubanshi ga Pretty ɗin shi suka

haɗa ido ranta a ɓace a zatonta shi ya soma yi musu magana. Ya shiga falon kun gama? Yana
magana yana kallonta ta juya mai kai.

M Bash

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login