Showing 1 words to 3000 words out of 6373 words
頎巾被頎巾被 AKWATIN MUTUWA頎巾被頎巾被
鈽 FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION鈽
FCWA
鈽home of qualities and trusted writers of the nation鈽
~Assalamu Alaikum~
~Gani na dawo maku da wani sabon littafi ina fatar yanda na fara lafiya Allah Ya bani ikon
gamawa lafiya~
*Wannan shafin sadaukarwa ne gareku masoyana duk inda kuke*
*Ina sonku sosai*鉂も潳
*Page 1_5*
Wata mata ce zaune cikin daki wacce baza ta wuce shekara 35 a duniya ba,kana ganinta kaga
mai ciki saboda yanayin zaman da tayi. Tabarma ce ta shimfida take zaune sama
Cikin yayi girman haihuwar yau ko gobe,tagumi ta buga kuma da ka kalli fuskarta kasan tana
cikin damuwa. Numfashi ta saukar mai sauti sannan ta fara magana "oh ni hajara tunda na
samu cikin nan kullum cikin faduwar gaba da zullumi nake na rasa gane menene,duk da ban
taba haihuwa ba nasan dai ba haka masu ciki suke ji ba gashi ina ji kamar wani mummunan
abu zai faru da zuri'arta amma koma menene zan barwa zuciyata in dage da addu'a dan nasan
kona fada ma yaya umar ba yadda zai yi ba"
Tana cikin zancen sai ga wani mutum ya shigo shekarunsa zasuyi 41,fari ne sannan yana da
tsawo. Ko sallama baiyi ba haka nan ya fado cikin dakin kamar wani bijimin sa Wanda inda
sabo hajaru ta saba da wannan dabi'a ta mijinta. "Yaya sannu da zuwa" yauwa kanwata ya
jikinki da zaman kadaici? To yaya jiki kam Alhamdulillah sannan zaman kadaici ai har na saba
shekara kusan goma fa kenan muke nan to wane kadaici zanji'' hakane kanwata wlh naga
nawar inga kin haihu lafiya sannan abunda zaki haifa ma haka kinsa ina son yara yanzu tunda
da bana zubar miki da ciki yanzu kila diyanmu sunkai biyar ko ya kare zancen da dariya
Hmm yaya kenan Allah dai Ya saukeni lafiya ; bai amsa mata ba wanda dama tasan hakan zata
faru duk wata addu'a da zata yi indai kusa da yaya umar ne bazai taba amsawa ba shi kullum
burinshi yaci ya kwanta ibadar ma ba wani damunshi tayi ba sai idan hajara ta matsa sannan
yayi wani lokacin ma ba yayi.
Maganarshi ta dawo da ita tunanin da takeyi " kinyi abinci yau da a'a ta amsa yaya kafa San
yanda nake fama da jikina yau lafiya gobe ciwo kuma duk nayi maka magana muje asibiti baka
taba yadda bansan me yasa ka kawoni wannan mugun dajin ka ajiyeni ba ka rabani da kowa
daga Kai saini sannan Kai dinma fita kakeyi ka barni kamar wata mayya.........dallah rufe mani
baki wannan maganar da tana tsiro da tayi ga jikinki wai me yasa kin cika mitar tsiya ne sau
nawa zan fada maki ba wanda ya isa ya sakani fita dajin nan idan ba nine naso ba amma
kullum sai kin dameni da zance to wlh ki kiyayeni ko dan kinga cikin ki ya girma na daina
dukanki ne kawai Dan yanzu ina son ganin kwai na duniyar nan amma da ba haka ba wlh yau
na lahira sai ya fiki jin dadi wawuya kawai" Yana gama fadar haka ya mike yayi hanyar dakin shi
ya bar hajara zaune tana sharar hawaye. Itama da taga kukan bazai tsinana mata komai ba
face ciwon zuciya Wanda take sa ran tana ma dashi tunda wani lokacin idan zuciyar ta na
bugawa sai taji kila da akwai wani kusa da yaji sautin,mikewa tayi da kyar dan cikin yayi nauyi
sosai ta wuce daki dan ta kwanta itama.
脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳
Wasu mashaya ne guda biyu keta tambele cikin wani daji da ganinsu kasan mugun sha
sukayi,surutu sukeyi maras kan gado. Dayan ne yace yaa baaba ni wlh talaucin nan ya isheni fa
kullum idan zan kwalbe sai nayi sata sannan nake samu ; Wanda aka kira da baaba yace "kana
ji ba gaye wlh gwanda kai tunda saika samo sannan kake bani nima fatana kawai Allah Ya
kawo wani naman daga sama sai mun mashi eyane wlh" dariya suka kwashe da ita sannan
wanda aka kira da gaye yace bari in dan matsa daga cikin wurin cen inyi fitsari Dan nan mutane
sunyi yawa kallo na zasuyi ni kuma bana son ana kallon tsiraicina'' dariya suka saka sannan
gaye ya fara tafiya yana kara shiga cikin daji Yana yan surutan shi na mashayi.
Tafiya yake tayi har yanzu ya kasa samun wurin da zai yi fitsarin. Iska ne ya taso yana daga
ganyen dake nan kasa shidai gaye bai tsaya ba da tafiyarshi ba cen yaji yayi tuntube da wani
abu kamar dutse; tsayawa yayi sannan yace "kaga tsinannun mutane wato duk da nazo nan inyi
fitsarin Saida kuka biyoni ko to zan maka eyane wlh.
Har zai wuce sai yaga kamar akwati ne wajen dukawa yayi ya taba yaji dai shi ne dariya yayi
yace sai ni tanimu gaye ashe dai labaran da nake karantawa da gaske ne wadan dake shiga
daji suna samun akwatin kudi da gaske ne, ihu ya sakeyi sai ni tanimu gaye mai sa'a yau dole in
kwana ina kwalbewa. Kokarin bude akwatin yayi amma ya kasa sabida wani kwado da akasa
aka kulle; wani dutse ya gani kusa ya dauka ya fara bugun kwadon tun yana na marmari har ya
fara gajiya da kyar dai ya samu ya balle akwatin budewa yayi yaga babu komai sai 茩warangwal
ja ba baya yayi Wanda yayi dai虏 da wata irin walkiya tare da wani iska mai firgitarwa da suka
taso lokaci guda. Wata irin kara akayi mai firgitarwa sannan aka fashe da wani kuka Wanda
amon shi ba dadin sauraro;wata irin halitta ce wadda idan ka kalla sau daya to baza kayi
marmarin kara kallawa ba, tanimu gaye naga iska ta dauke ta maka shi da bishiyar dake nan
sannan aka jawo shi kamar kayan wanki aka dinga makawa kasa ihu yake yana kiran dan Allah
kuyi hakuri ku kuke ganinmu bamu ke ganinku ba wlh na fasa son kudin ko giyar ma na daina
sha sannan zan dinga gaida iya kullum kuyi hakuriii... shiru yayi sanadiyar wuyanshi da aka
karya kum. Dariya ta kwashe dashi sannan ta fara magana "daga yau na fara farauta kuma
babu Wanda ya isa ya dakatar dani shekarata dari cikin akwati yau gashi wani ya fitar dani
hhhhhhhhhh,bat ta bace.
Wanda yayi dai虏 da wani faduwar gaba daya tsinkayi hajara dan tunda ta shiga daki ta kasa
bacci sai tunani takeyi; iska taga yana kadawa tare da jin wani sautin kuka daga nesa.
Baaba ne tsaye sai zage虏 yake irin na yan shaye虏 yana wannan banzan daga fitsarin ne har
yanzu bai dawo ba gashi dare yayi sosai har mutane sun fara watsewa (dariya nayi nace lallai
kam baaba kana ruwa ko ina mutanen suke nan oho) tafiya ya fara yana idan ka dawo ka
sameni gida nikam na gaji. Wani kare ya gani yana nufar inda yake da gudu gashi kana ganin
idanunshi jajir dasu kamar an barbada mashi barkono ciki, baaba na ganin dai kare wajen shi
yake zuwa ya fara tafiya da sauri yana hadawa da gudu ai kamar wucewar iska yaga kare
gabanshi.
Baya ya fara ja yana fadin kada ka matsoni dan wlh zan maka eyane inaa kare bai San meya
ke fada ba wata irin tsalle yayi sai gashi saman jikin malam baaba wata kara ya saki yana
jama'a ku kawo dauki zai cijeni,wlh kada ka fara nace zan maka eyane fa. Wata cafka da karen
yayi mashi kawai sai ga kan baaba cikin bakin kare,nan ya fadi ba kai jiki sai rawar disco yake
kasa,bacewa Karen yayi sannan wurin yayi tsit kamar wucewar mutuwa..
脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳
Koda safiya tayi da kyar hajara ta mike sabida ciwo da mararta keyi haka nan dai ta daure ta
sauko saman gado sannan ta shiga bayi tayo alwala fitowa tayi ta shinfida abun sallah ta tayar
da kyar take dukawa cen tana cikin sallar taji kamar an tureta faduwa tayi saman cikin wata
kara ta saki nan take jini ya balle mata saiga haihuwa kuma gadan虏 ta fara nakuda cikin ikon
mai sama ta haihu ihu ta sakeyi ko yaya umar zaiji tunda tasan bai kaida fita ba amma shiru
babu shi ga jini sai malala yake kasa kamar ruwan wani teku.
Yan dabaru tayi ta yanke cibi nan ne taga ashe mace ta haifa' kurawa yarinyar idanu tayi tana
jin tausayinta na shigar ta ga wani bakon al'amari da takeji ga jikinta,cikin minti biyar hajara tace
ga garinku tana rike da yarinyar ta ga hannu da sai kuka takeyi.....
*Maryam H*
[10/15, 8:04 AM] Hayat: 頎巾被頎巾被 AKWATIN MUTUWA頎巾被頎巾被
鈽 FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION鈽
FCWA
鈽home of qualities and trusted writers of the nation鈽
*~WANNAN PAGE DIN NA SADAUKAR DASHI GA DAUKAKIN MASOYAN WANNAN
LITTAFIN BANIDA BAKIN DA ZAN GODE MAKU AKAI SAI ADDU'AR ALLAH YA BAR
ZUMUNCI DA KAUNA~*頎卷蛋頎卷蛋
~*INA YINKU OVER*~頎巾睂頎巾睂
*Page 11_15*
Tafiya sukeyi har suka zo bakin kofar shiga gidan tura kofar yayi ya shiga itama ta shiga,kujera
ya nuna mata da ta zaune ya kawo mata ruwan da kai ta amsa mashi. Kicin yaje ya dauko kofi
sannan ya dawo ya bude firiji ya dauko goran ruwa,inda take ya kawo mata ruwan godiya tayi
sannan ta bude goran ruwa ta zuba tasha; Saida taji ta koshi sannan ta ajiye kofin magana ta
farayi "bawan Allah na gode da taimakona da kayi dan da ban samu ruwan nan na nasha ba da
bansan yanda zanyi ba" kai ya gyada mata sannan yace babu komai ai, ta buda baki da niyyar
magana sai sukaji kukan jaririya cikin daki umar ya mike yace ina zuwa da sauri yayi cikin dakin
dauko ta yayi yana jijjigawa alamar tayi shiru. Cen falo kuma bakuwa na gani ya bar wajen
itama saita bace tana dariya
Bacewar ta yayi dai虏 da shigowar umar falon turus yayi na ganin ba kowa falon; magana yayi to
ita wannan ko tafiyarta tayi taga ban fito ba. Zama yayi yana tunanin abun yi dan shifa yarinyar
nan yake tausayawa ba wanka balle akai ga maganar abinci.
Gaskiya ya kamata ya kirasu ummah asan abunyi yanzu gashi gawar hajara ma ta bace baisan
inda zai ganta ba sannan ga karin tashin hankalin abunda ya faru dashi lokacin da zai bar dajin
nan.
脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳
Wani irin daji ne wanda ko cikin mafarki ka ganshi kasan mugun mafarki ne kayi. Wani katon
akwati ne wajen duk ya tsufa alamun ya dade wajen gefe dashi kuma kawuna ne da gangar jiki
na matattu har sun zama kwarangwal. Wata irin iska ce ta kada mai tsoratarwa baka ganin
komai sai kura dake tashi sama dariya aka farayi sannan iskan ya fara ragewa,wata halitta ce ta
fara bayyana ;farin kayane jikinta amma duk ya farke sannan gashin kanta wani iri dashi duk ya
mike tsaye gashi kamar sayyun itatace,idanunta kalar ganye,bakinta kamar wani kofi sannan
bata da hanci dan wurin shafe yake kamar anyi filista.
Wajen akwatin nan ta matsa hannu kawai ta daga sama tayi wata kwalamniyar magana saiga
akwati ya bude, kwalamniyarta ta sakeyi saiga gawa ta fito ta fadi kasa,wata ta fito saida gawa
uku ta fito daga akwatin sannan ya rufe. Ashe gawar su hajara ne dasu tanimu gaye.
Wani irin ihu tayi sannan ta fara magana cikin karaji "bazan taba sanya ba saina kashe kowa
yanda kuka kashe ahalina sannan ni kuka sakani cikin wannan akwatin to dashi zan dinga
farauta duk wani ahali dake doran kasa saina batar dashi" tana gama fadin haka ta bace batt..
脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳
Umar ne zaune ya rafka uban tagumi abun duniya ya ishe shi yaje da niyyar daukar waya ya
kirasu ummah amma baiga wayar ba ashe tana cikin motarshi kuma gashi motar tayi batan
dabo,yanzu tunaninshi yanda zai bar wannan gidan ya koma gari ko suna a sakawa yarinyar
nan da itama daga zuwan ta duniya ta fara cin karo da bala'i. Tun dazu yake gwada fita cikin
gidan amma ya kasa da yaje buda gate sai yaji kamar an dora wani gingimemen dutse wajen
sannan sai ya dinga jin kamar muryar hajara na kiranshi
Yana cikin wannan tunanin ne yaji kamar silin dakin zai fado saboda wata irin jijjiga da yakeyi
mikewa yayi da sauri ya dauki diyarshi ya riketa sosai sannan ya dawo falo ya tsaya; kofar falon
aka bude cen saiga wani kwarangwal ya shigo falon wasu na biye dashi suna zuwa basu tsaya
wata虏 ba guda ya cafke wuyan umar ya daga shi sama tari ya fara saboda azaba sannan ga
yarinya hannunshi wanda idan yayi wasa tana fadowa. Suna cikin haka saiga wata halitta ta
bayyana inda suke wani yare tayi saiga umar ya fado da kadan ya haye diyarshi su kuma
kwarangwal suka koma baya.
*Bari mu koma wajen iyayensu umar*
脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳脳
Ummah ce kema Abba magana akan yayi sauri suje su dibo yaran nan ko lafiya tunda umar bai
zo ba kuma bai kira ba gashi wayarshi ko an kira kashe take, fitowa Abba yayi yana wlh Fatima
kin cika mitar tsiya yanzu dai gani sai mu tafi ko. Fitowa sukayi suka shiga mota direba yaja mai
gadi ya bude kofa suka fita. Tunda suka fito gaban ummah ke faduwa addu'a kawai takeyi har
suka fara nusar cikin daji shi kanshi Abba wani iri yake ji dauriya kawai yake tare da addu'ar.
Sunyi tafiya mai nisa sannan suka zo gidansu umar Abba ya fita ya budewa direba kofa ya
shigar da motar ciki, karasawa sukayi ummah ta fito aka bar direba cikin mota, ummah ke gaba
har sukazo dab da bude kofar falo wanda yayi dai虏 da ihun da umar yayi sakamakon fatalwa ta
caka mashi kumbarta ga wuya....
*Maryam H*
[10/16, 6:52 AM] Hayat: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/L3K7SmNat3v1GNB8AxWxdJ
頎巾被頎巾被 AKWATIN MUTUWA頎巾被頎巾被
鈽锔 FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION 鈽锔
FCWA
鈽锔廻ome of qualities and trusted writers of the nation 鈽锔
*Page 16_20*
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un me nake gani haka cewar ummah da sauri fatalwar ta sake
wuyanshi suka bace,fadowa yayi wanda jaririyar tayi gefe guda tare da tsallara wani kuka na
azaba. Da gudu su Abba suka karaso inda suke ummah ta dauko jaririyar shi kuma Abba yayi
wajen Umar daya sume tuni sabida azaba, kuka ummah ta fashe dashi tana fadin "wai menene
haka nake gani ina ita Hajara din tabar yarinyar hannunshi sannan wace irin halitta ce wannan
me kuka yi mata" ta karashe zancen tana kuka; Abba ne ya fita da sauri ya kira direba suka
kama Umar suka kaishi cikin mota, dawowa yayi yace ummah ta tashi ta dibo Hajara tazo su
bar gidan,koda ta duba bata ba dalilinta ko'ina an duba bata haka nan suka kama hanyar gida
ba Hajara amma kuma kowa da abunda yake sakawa cikin ransa.
Sun zo fita cikin dajin kawai suka ga mutum kamar an jeho shi daga sama,wani wawan burki
direba yaja wanda saida Umar ya kusa fadowa daga kujerar da yake kai. Tasowa mutum yayi
yana nufo su amma kuma baida kai gangar jiki kawai ne,ashe gawar baaba ce ai suna ganin
haka Abba yace ma direba yayi sauri ya tayar da mota su bar wajen
Haka ko akayi yana tayarwa baaba na kawowa kusa dasu ji kawai sukayi ana "tunda kuka zo
wajen nan yau saina maku eyane kun gane ai bazan bari ku bari wajen nan haka siddan ba tare
da na maku eyane ba",da wani matsiyacin gudu direba ya bar wajen su kam su ummah ba
abinda ake sai addu'a dan iya tsoro anji shi. Suna barin wajen baaba gaye ya kwashe da wata
irin muguwar dariya sannan wata iska ta tashi tayi sama.
Koda suka kai gida baki daya jikinsu yayi lakwas kamar wadan da suke je filin daga aka kayar
dasu,fitar da Umar sukayi aka shigar dashi gida ita kuma ummah daki taje ta dauko zani ta goye
jaririya sannan ta fada kicin ta dora ruwan zafi saida suka tafashe sannan ta samo roba ta zube
ruwan kadan ta surka sannan ta wanke jaririyar tas,Allah Sarki yarinya taji ruwan zafi har wani
kulle idanu take alamun dadi. Kaya aka canja mata lokacin Abba ya fita ya siyo madara aka
dama mata sannan aka sa mata a baki,tana kamawa kam ta dinga tsotsa ''saida tayi nak
sannan ta saki ta bingire da bacci.
Wasa虏 saida Umar ya kwashe kwana uku baisan duniyar daya dosa ba a kwana na ukun ne ya
farfado yana bude ido ya kafta wata irin ihu da ta kusan saka ummah sakin jaririya da take ba
madara, da gudun ceton rai ta fada dakin saiga Abba shima yaji ashe. Suna zuwa suka iske shi
sai fizge虏 yake yana "kada ku kasheni dan Allah kuma ku dawo mani da gawar matata wlh koda
ta mutu ina sonta" da sauri Abba ya matsa kusa dashi ya fara tofa mashi addu'a ita kuma
ummah har ta bare baki ta fara kuka tana "yanzu badai hajara ta mutu ba to kuma ina gawar
waya....." wani kallo da Abba yai mata yasa ta yin shiru ba tare da ta karashe maganar ba. Cikin
ikon *mai sama* Umar ya bar fizge虏n da yake sannan ya rage surutun ma haka nan bacci ya
dauke shi, saida suka ga haka sannan suka baro dakin falo suka dawo suka zauna sannan
Abba yace "na rasa gane wani irin tunani ne kuke dashi mata wlh ace kinga mutum ya farka
cikin yanayi amma wasu tambayoyin rashin kai kike mashi ai kya bari ya dawo hankalin shi
duka sannan mu tambayeshi meke faruwa,Ni tsoro na ma idan ba wajen daukar maganar shi ya
yaje ya jawo aljanu ba gashi kuma yace su dawo mashi da gawar mata