Showing 6001 words to 6373 words out of 6373 words

Chapter 3 - Akwatin Mutuwa Hausa Book By Maryam H

Maryam H   

10 Jul 2026

65

jikinsa, saida yacire duk
wani kaya dake jikinsa, kafun ya ɗaura towel a ƙugunsa kaitsaye ya shige bathroom,, a ƙalla
ya kwashi kusan 1 hour a cikin bathroom ɗin kafun yafito, sanye da rigar wanka a jikinsa,
gaban mirror ɗinsa yaje ya ɗanyi shafa, combat jeans black ya sanya haɗe da black t-shirt,
sosai kyawun Zaid ya bayyana acikin wannan kayan, wayarsa kawai ya ɗauka yafice daga cikin
ɗakin, makeken friedge glass ɗin dake cikin katafaren falon nasa yanufa, zuƙeƙiyar kwalbar

wine mai tsadar gaske yaɗauko a cikin friedge ɗin haɗe da glass cup zama yayi akan ɗaya
daga cikin kujerun falon, yayinda ya buɗe kwalbar wine ɗin ya tsiyaya a cup, kana yakai
bakinsa, a hankali yake shan wine ɗin, yayinda idanunsa ke alumshe, bakomai yake hasa
sowa ba sai kyakkyawar surar Zahrah wacce ke tafiya da imaninsa ako da yaushe, haƙiƙa ya
kamu da tsananin sha'awar Zahrah, kuma alƙawari yaɗaukar mawa kansa idan dai har yacika
*SHU'UMIN NAMIJI* kamar yadda abokansa ke ƙiransa, to sai ya keta mawa Zahrah rigar
mutumcinta kota wani hali kuwa,, wayarsa yaɗauka haɗe da laluɓo numbern sim ɗin dake cikin
wayar Zahrah, yana dialing aka sanar dashi cewa wayar a kashe take, wani irin munafukin
murmushi Zaid yayi haɗe da sanya hanu ya shafi sajen dake kwance akan fuskarsa, kashe
idanunsa ɗaya yayi haɗe da cewa "My Sugar Baby bakijin magana ko ?" yayi maganar tamkar
wanda yake gabanta,, sosai Zaid ya sha wine a wannan dare, da ƙƴar ma yasamu bacci ya
ɗaukesa bayan yagama kwarara aman giyan da yasha .......



*21/October/2019*


*MRS SARDAUNA*




Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels Group
Hausa novels and fashion Group
Cool novel, makeup and kitchen1 Group
And
WOMEN24 TV Group

WHATSAPP NO:+2349030159301

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login