Showing 3001 words to 6000 words out of 6373 words

Chapter 2 - Akwatin Mutuwa Hausa Book By Maryam H

Maryam H   

10 Jul 2026

64

wanda haka na nufin
hajara ta mutu shi ne kuma suka dauke gawar.lallai ya zama dole mu tashi tsaye da addu'a
sannan wannan jaririyar gobe za'a yanka mata rago asa mata sunan mahaifiyarta"" da to kawai
ummah ta amsa sai sharar kwalla take...

××××××××××××××××××××××××××
Wani saurayi ne zaune cikin dakinshi da yasha mai da yaji na kayan alatun duniya idan kaga
dakin zaka rantse baza'a mutu ba,kwalaben giya ne gaban shi sai kwalbewa yake abunshi daya
shanye wannan sai ya ture kwalbar gefe yaja wata. Yana cikin wannan yanayin ne yaga kamar
mace na mashi gizo tun yana tunanin ko giyar da yasha ne ta fara aikinta yaga dai ba haka
bane


Kallo ya kare mata iya haduwa ta hadu kamar ita tayi kanta don kyau kusa dashi tazo ta zaune
sannan ta fara magana kamar mai rada cikin wata iriyar murya mai saka mutum fara jin baccin
dole "haba salim me yasa kullum baka gajiya da shan giya ne eyen to nidai yanzu ka tashi muje
ka rakani shan ice cream" kamar wanda aka dorawa wani magana disu haka yaji gashi shi dai
baya son zuwa tunda bai san ko wacece ita ba kawai cikin dakinshi ta bayyana sannan tana
wani ya kaita tasha ice cream shida ya riga ya dawo gida sai gobe zai fita kuma,amma kuma
baya iya musa mata. Haka nan ya mike suka fita daga dakinshi na bacci zuwa falo kamar
rakumi da akala.

Falon ya hadu karshe kamar ba duniya ba, haka suka fito suka shiga mota mai gadi ya wangale
masu gate yana ranka ya dade sai ina baiko kalli inda yake ba yasa Kai ya bar gidan; tabe baki
mai gadin yayi yana Allah dai ya shirya ace yaro kamar dangin maguzawa yanzu kullum sai yayi
tatil zai dawo ma gida kuma iyayenshi babu Wanda ya damu da halin da kake ciki su ganinsu
burgewa ce,yanzu ko Ina yayi shi kadai haka cikin daren nan oho(ido na zare shin mai gadi
baka ga su biyu suka fita kake Kiran shi kadai,to ina bakuwar tashi ta labe da har mai gadin ya
kasa ganin ta)surutan shi ya gama sannan ya kulle gate din ya koma dakinshi ya kwanta.


*Waye Salim*

Salim shazali shi ne sunanshi da ga Alh shazili Muhammad hamshakin mai kudi dake garin
kano,sana'ar saida gwala gwalai yake yana da shaguna kusan uku a garin kano sannan da
wasu dake kasar amurika duk na gwala gwalai, Yana da mata hajiya falmata kanwar abonkin
shi ce dake maiduguri ya aura. Salim shi kadai Allah Ya basu Wanda dalilin haka suka nuna
mashi gata na kazanta,tun daga secondary har University a amurika yayi wanda sanadiyar haka
ya kara samun lasisin lalacewa.Ba abinda Salim baya yi na assha shi ne shan giya,neman mata
da dai sauran miyagun dabi'u sannan duk abinda yayi wajen iyayenshi dai² ne basu taba yi
mashi fada ba,aya guda wannan ta qur'ani bai sani ba amma waka ko wani tsami yayi ta to
yasan da zaman wannan waka..

*Ci gaban labari*
Koda suka fito gida tambayar ta yayi inda zasu je ce mashi tayi su ci gaba da tafiya idan sun
kawo wajen zata mishi magana,haka ya dinga sharara gudu saman titi kamar wani dan tseren
mota. Sunyi nisa sosai dan har sun fara fita cikin gari wani daji tace ya tsaya; tsayawa yayi dan

ji yake kamar *konturolin* dinshi take.


Koda suka tsaya cewa tayi ya fito ya biyota; fitowa yayi yana binta da baya har suka zo wajen
wani tafki , shiga tayi shima Salim ya shiga tafiya suke yi har sukazo tsakiyar ruwan hannu tasa
ta jawoshi ta tura kanshi cikin ruwan

Wutsil² ya fara yi da hannunshi tun yana yi da karfi har jikinshi ya saki alamar dai rai yayi
halinsa( mudai sai muce Allah Ya jikan rai su salim anyi zuwan zomo kasuwa yazo da gudu ya
fita da gudu. Tunda aka haifeka baka taba tsinana komai mai kyau ba sannan aikinka na karshe
ma marar kyau gashi ka tafi inda ba'a dawowa. Mudai fatar mu Allah Yasa mu cika da imani
sannan mu mutu muna aikata alkhairi. Amin)



Tana ganin ya mutu tayo wata sufa ta fito daga ruwan girgiza tayi sai gata ta koma sak
Salim,dariya tayi sannan tace saura iyayenka. Mota ta tayar tayi hanyar gidansu Salim ,Koda
taje mai gadi harya fara bacci odar da ta dinga yine ya tadashi da sauri ya fito ya bude gate din
Yana Allah wadai da halin Salim Dana iyayenshi.
Saida ta shigar da motar sannan tayi sashen iyayen su kuma lokacin har sun lula duniyar sama
jannatin bacci .tana shiga ta girgiza sai gashi ta dawo wata halitta mai tsoron kallo

Kwalamniyarta tayi kawai saiga gida ya fara kamawa da wuta ,Saida tayi dariyar muguntar ta
sannan ta bace

Su Alh shazali da Hajiya falmata an bude saleba sai kwasar bacci ake ana minshari kamar
wasu shanu da suka ci dussa suka kasa tashi. Cikn bacci hajiya falmata ta fara jin hayaki kamar
ana shakar wuyanta da sauri ta tashi ta fara bubbuga mijinta tana Alh tashi kamar wuta fa keci.
Magagin bacci ya fara Yana "dan Allah falmata ki kyaleni inyi bacci na gaj.....bai karasa zancen
ba yaji wani duka da takai mashi aiba shiri ya mike hanyar fita dakin sukayi suka kama jan kofa
amma taki budewa wajen wayar tarho ya koma ya danna lambofin *faya sabis* suna dauka
yace "nine shazali mai gwala gwalai kuzo gidana wuta ta kama... Bai karashe zancen ba aka
jeho wani harshen wuta Wanda yayi sanadin shi nan take itama falmata tashin hankalin abunda
ta gani yasa zuciya ta buga nan take ta zube kasa mace.

Mai gadi ne yaji kuwwar motar yan *faya sabis* da gudu ya tashi ya bude kofa sai sannan ya
hango yanda wuta ke ci,bude kofar yayi suka shigo binsu yayi da gudu har suka Kai wajen kofar
shiga gidan. Ruwan aka fara watsawa amma kamar ba'a watsa komai Saida kusan mota uku
tazo sannan wutar ta tsaya, da kyar aka gano gawarsu su Alh shazali.
Lokacin gari yayi haske mutane har sun fara taruwa . gawar ba kyan gani sabida soyewar da
tayi

Danginsu aka kira sukazo aka basu gawar su sukai masu sutura akai kaisu gidan gaskiya inda
babu Wanda bazai je ba.


Anyi bincike an rasa gano mai ya jawo gobarar aka watsar da *kes* din aka raba gado dingi
suka dinga bushasha.......


AKWATIN MUTUWA


☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION ☀️

FCWA

☀️home of qualities and trusted writers of the nation ☀️



*Page 26_30*


Sai kusan shida na safe ta tashi wanka tayo tare da alwala tayi sallah,shiryawa tayi cikin kayan
makaranta yadin riga da siket kalan kwai sai hijabi karami kalan anta. Falo tazo lokacin bakwai
da rabi ta kusa abinci taci agurguje sannan ta fito wajen gate dan ko ummah basu hadu ba
dama ta saba sai ta dawo daga makaranta suke haduwa ita ummah'r na cen tana gag gabar
bacci.


Tunda ta shiga mota direba ya fara tafiya take jin wani iri ga jikinta gashi sai taji kamar ana mata
rada cikin kunne, sannan ita ba wani ma'abuciyar addu'a bace duk da tana zuwa islamiyya
karatun ba wani dagata yayi ba tafi bama boko mahimmanci gashi tana da kokarinta
gwargwado tunda ita ke yin na daya tun tana firamare har yanzu da ta shiga sakandare aji biyu
sannan su iyayen nata ba wani kwaba ta suke ba komai taga dama shi takeyi a ganinsu tunda
ta rasa uwa baza tayi maraici ba,Abba ma ne ke tsawatarwa wani sa'in idan yaga abin yayi
yawa.


Suna zuwa cikin makarantar direba ya tsaya ta sauka magana yake "masu gida Allah Ya bada
Sa'a" wani juyowa da tayi shidai direba gani yayi kamar ba ita ba dan rabin fuskar ta a daye
sannan rabin ba ido daya; da gudun ceton rai ya figi motar yayi gaba.

Koda ta shiga aji babu wanda tayiwa magana duk da tana da fara'a amma yau kam fuskar nan
kamar kunun dare, kujera ta zauna ba tare da ta kalli kowa ba


Wani yaro ne dan kasada mai suna Abbas dake gaban kujerar ta ya juwa yana " wai ke yau
meya sameki kikewa mutane kamar kina jin warinsu" har ya gama zancenshi bata ce komai
ba,koda malamai suka shiga sunga canji wajen ta sabida taki magana da kowa. Har saida aka
tashi sannan tacewa Abbas ya tsaya zata ganshi bai kawo komai ba yace to,saida kowa ya
watse sannan Hajara ta mike ta dawo gaban Abbas irin fuskar da tayiwa direba tayi mashi wani
wuntslawa yayi da baya daya fadi hannu ta mike sai gashi yayi dogo bata tsaya wata² ba ta
caka masa kumbar ta wuya tun yana ihun neman taimako har dai ya kasa gashi ajinsu shine
kusan karshe ba'a jin komai,zuwa cen jiki ya saki bacewa sukayi sai cikin wannan mugun
dajin,cikin akwatin nan ta jefashi sannan ta bace. Bakin gate din makarantar su ta bayyana bata
dade ba saiga daddy'nta yazo dan direba ya sheme yace alan baran baida lafiya don gudu yake
ya koma ya kara cin karo da wannan fuskar tata kamar fatalwa. Koda yazo shi kanshi yasha
mamakin ganin yanda ta hade girar sama data kasa sai harde fuska take,shiga motar tayi ba
tare da tace kala ba saida suka fara tafiya sannan ya fara magana"haba baby'n daddy meya
faru kika kyalleni ne? Ko inda yake bata kalla ba bare yasa ran samun amsa da yaga taki
magana ya kyalleta


Suna zuwa gida ta buda mota ta fita ciki ta shiga ba tare da tawa kowa magana ba tana shiga
dakin ta ta fada kan gado ta fashe da wani kuka mai sautin ganga cikin kukan take magana "
badai kun kashe mu ba to nima saina ga bayanku.



*Wacece wannan fatalwa*

A'ishatu ibrahima ne sunanta su yan asalin jamhuriyar Nijar ne cikin garin agadaz su uku suke
ga mahaifinsu itace babba sai Usmanu da kanensu Yusufu. Ahali ne masu burgewa,mahaifinsu
ibrahima Yusufu su goma ya haifa amma shi kadai yake ga mamarshi bayan haihuwar shi da
awanni tace ga garinku sanadiyyar tsafin da akayi mata na turo mata bakaken aljanu,shi ne
karami sai yayunshi Abubakar,jimirau,auwalu,fatsima,mulaika,Sulemani,zuwaira,halimatu da
Idirisa; sun taso cikin kiyayyar dan uwansu wanda ammah wato mahaifiyarsu ta dasa masu.

Amma wata irin mushrika ce wadda ko cikin jahilan farko sai an tono irinta tun farkon da Yusufu
zai yi aure taso hanawa amma tsafin bai ci ba saida zainaba ta shigo gidan wato uwar ibrahima
Sannan ta ci gaba da kulle kullenta har ta samu ciki wanda hankalin ta ya tashi taje wajen
bokanta aburu kukuma tace tana so akashe zainaba kafin ta haihu yace bazai yiyu ba sedai
idan ta haihu; shi ne bayan ta haihu aka turo mata aljanu suka shaketa ta mutu.

Tunda ibrahima ya tashi yake cikin gararin rayuwar babanshi dai ke raga mashi kuma sai Allah
Ya albarkaci hannunshi komai ya rika sai yayi albarka,har dai yayi aure yana cikin ukuba wanda
wannan lokacin kuma babansu ya rasu yayi kukan rashi daga baya ya dangana


Ibrahima nada kudi sosai wanda shi ya kara tursasa hassada ga yan uwanshi kullum cikin
neman hanyar cutar shi sukeyi.

A'ishatu yarinya ce mai masifar tsiya idanunta tsaye suke bata da kunya ko kadan iyayenta
kawai take dagawa kafa sai kanninta.

Ranar babansu na zaune cikin gida yana hutawa saiga sulaimani yazo wai su hada aure
tsakanin diyansu wanda ko babu komai zumunci zai karu da jin haka ibrahima yace sam bazai
bama dan shaye² diyarshi ba kawai su nemi wata, wannan furici yayiwa sulaimani ciwo wanda
har yakai saida suka hada taro da yan dakinsu duka inda akace zasuje wajen boka aburu
kukuma sai asan abunyi; sunje ya basu wani magani da idan suka shiga gidan komai zasu iya
yi babu wanda zai hana su sannan da zarar sun hadu da ibrahima su barbada maganin ga
wuka su caka masa ga zuciya.

Saida dare yayi sannan sulaimani, Idirisa suka shirya tare da dan dan sulaimani mai suna
jibirila, gidan sukaje inda babu wanda ya gansu

Dakin baccinsu suka nufa suka tadosu suka taso keyarsu zuwa falon gidan sannan suka tado
da yaran koda sukazo, sulaimani bai tsaya wata² ba ya caka masa wukar saitin zuciya sannan
duk suka yanke sauran saura A'ishatu tana ganin haka ta fara ihu amma babu wanda zai ji wani
akwati ne da sukazo dashi suka jawota suka turata ciki tana ta ihu amma babu wanda ya kula ta
sannan suka saka kwado suka datse


Cikin daren nan suka kama hanyar wani daji mai abubuwan tsoro suka gefar dashi,wanda wasu
mutane suka shiga dajin suka ci karo dashi suka dauka a tunaninsu kudi ne sunyi tafiya mai
nisa har suka shigo najeriya sunyi bakin kokarin bude akwatin amma sun kasa shine suka
yadda shi inda tanimu gaye ya gani har ya samu sa'ar budewa...

*Ci gaban labari*




*Maryam H*

*Maryam H*




*SHU'UMIN NAMIJI !!*


*Written by*
phatymasardauna
*Mrs Sardauna*


*Dedicated To My Lovely Brother Khabeer*


*KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

*WATTPAD*
@fatymasardauna


*Editing is not allowed *

*Chapter 12*

*( INA MAI BAKU HAƘURI DOMIN KUWA KWANA BIYU, ZAKUJINI SHIRU BA NEW UPDATE,
WATA ƘILA NAYI 1 WEEK BANYI TYPING BA, WATAƘILA KUMA BAZAN KAI HAKANBA,
HAKAN YAFARU NE SABODA WANI DALILI NAWA, INSHA ALLAH AMMA ZAKUCI GABA DA
JINA IDAN KOMAI YA DAI DAI TA, NAGODE....)*
*Kuɗanyi manage da wannan *


Kasa ƙare maganar Baffa yayi sakamakon tozali da kuɗaɗen dake gaban Inna da yayi, cike da
tuhuma yake kallon Inna yamakasa ce da'ita komai, ganin haka yasa Inna ta washe baki, haɗe
da soma tattare maƙudan kuɗaɗen, cikin hanzari Baffa yasanya hannayensa duka biyu ya
wawashi kuɗin, haɗe da cusawa cikin aljihunsa, da sauri Inna tayo kansa tana muzurai, haɗe da
cewa "Haba Malam yazakayi haka, aidai katsaya nayi maka bayani kafun ka kwasa rabonka
ko" harara Baffa ya watsamawa Inna haɗe da taɓe baki yace " ba abun da bansani ba, nasan

duk wani abu dakike shiryawa, kuma wallahi daga yau idan aka sake kawo kuɗi cikin gidannan
ba ki jira dawowata munraba ba, ninasan matakin da zan ɗauka, yarinyace dai ƴar wa na ne,
don haka babu wanda ya'isa ya gwadamin iko da'ita, kuma shima saurayin zaizo yasameni
haka ake zuwa hira babu wani tambayar izini ba komai" Baffa yaƙare maganar yana mai nufar
ƙofar fita daga gidan, yana fita Inna ta buga tsuka haɗe da cewa " shikenan kuma ae tunda
yagano abun danake shiryawa, bazai taɓa barina naci arziki ni ɗaya ba, mcheeew !" taƙare
maganar tana mai tattare ƴan ragowan kuɗaɗen da Baffa ya bar mata, raba snacks ɗin biyu
tayi taɗauki rabi, yayinda tabarmawa Zahrah rabi, waya kuwa danƙamawa Zahrah abunta tayi,
domin ita keypad ma bawani iyata tayi ba, balle kuma shafa shafa (touching screen)... Jigum
haka Zahrah tayi zuciyarta cunkushe take da tarin tunani kala kala, da zaran ta kulle idanunta,
mood ɗinsu na ɗazu ne ke faɗo mata, wanda hakan yasanya takejin gaba ɗaya jikinta yayi
sanyi, batasan dame zata ƙira wannan yanayinba, saboda batasan ma da akwaishi acikin
duniyar nan ba, duk dacewa bawani abune yashiga tsakaninsu ba, amma kusancin da sukayi
da juna duk ya dagula mata lissafi, ga fitinannen ƙamshin turarensa daya kama jikinta, tamkar
wacce tayi wanka da turaren,daga wani ɓangare na zuci yarta kuwa kaico takeyi da mummunan
hali irin na Inna da Baffa, wato su baruwansu da koma waye zaizo wajenta, sudai kawai abasu
kuɗi suka sani, koda ma iskanci takeyi su baidame su ba kuɗi kawai suke so, haƙiƙa rashin
iyaye babban matsalane arayuwar ƴa mace musamman ma idan batayi dace da iyayen riƙo
nagari ba, sai kuga rayuwarta nashirin lalacewa, akan abun da bai kai yakawo ba, Allah ka
zama gatan mu aduk inda muke Ameen,,, a hanakali taciro wayar daga cikin kwalinta,
subahanAllah shine abun da tafurta lokacin da'idanunta suka sauƙa akan haɗaɗɗiyar wayar,
jikin wayar ma kaɗai abun kalloce balle kuma kakai ga shafata, tabbas idan baza ta mantaba,
wannan wayar itace wacce taji ƴan school ɗinsu na magana sabuwar fitowa ce, kuma burin
kowanni ɗan gata da ƴar gata, shine su mallaki wayar, domin kuwa aƙalla kuɗinta zaikai dubu
ɗari biyar da tamanin,, wani irin faɗuwar gaba taji ya shiga zuciyarta a lokaci guda, take kuma
mugun zargin Zaid ya ɗarsu acikin ranta, tabbas akwai abun daya ɓoye acikin zuciyarsa, amma
idan ba haka ba babu yanda za'ayi yasiya mata wayan dubu ɗaruruwa, batare da suna da wani
kyakkyawan alaƙa atsakaninsu ba, a maimakon ta kunna wayar kamar yadda ya umarce ta,
batayi hakan ba saima mai da wayar tayi cikin kwalinta haɗe da cusata cikin kayanta, taƙudura
acikin ranta cewa idan yasake da wowa zata mayar masa da wayarsa, domin ita bata kai
martaba da ƙimar da zata riƙe wannan zuƙeƙiyar wayarba,, sam bacci ya ƙaurace mawa
idanun Zahrah kalaman Zaid ne ketayi mata yawo acikin kunnu wanta, bama kamar kalmar
*INASONKI ZAHRAH* daya faɗa, gaba ɗaya zuciyar Zahrah kasa sukuni tayi a wannan dare,
da ƙyar bacci ɓarawo ya ɗauketa......


Zaid kuwa yana barin unguwar su Zahrah guest house ɗinsa ya nufa, sai dai yau ba ya tare da
kowacce karuwa, yana shiga cikin bedroom ɗinsa yasoma rage kayan

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login