Showing 15001 words to 18000 words out of 34670 words

Chapter 6 - Allah Gatan Bawa Book Compelet By Zahra Surbajo

yiba sukaji kukan yazama biyu haa ay da sauri dady yabar gurin innace takarasa kusa da ita tadagata daga durkushen da tayi ikon Allah ilham tahaifi yara biyu duka maza Anwar yakai dubansa kan yaran wani farin cikine yalullubeshi dakyar momy ta turashi waje suka shiga aykin gyara mejego dayaranta kafin goman dare komai yayi normal kamar ba ayi haihuwa agidanba momyce tadauki yaran tana kallo hawaye nazuba a idonta tabbas base anfadamataba wainnan yaran jinin anwarne domin Bata inda suka rabu dashi kamarsu daya mamaki takeyi tayaya har Anwar yasamu damar kusantar ilham har tasamu ciki tahaihu kai dubanta tayi kan ilham wacce gabadaya tasace dama kumburin na cikine tausayintane yakama momy ajiye yaran tayi tarungume ilham tana hawaye dady ne yayi sallama yashigo dan yayi jiran akaimishi yaran yaji shuru shikuma yakosa shiyasa yazo dakansa kan kujera yazauna aka miko masa yaran seda kwalla tazuboma dady tafarinciki yayi mamakin yadda yaran suka dauko Anwar sak addua yayi musu sannan yamike dasu a hannunsa yatafi dakinshi danba karamin so yakewa jikokinnasa

shiko Anwar yana bakin kofa yanaso yashigo amma yanajin kunyar haduwa da dady =??gabahaba ay abun da kunya Anwar.


*to fans dun Anwar ga ranarku kuzo kuraka Anwar yaga yaransa*


maman yusuf
[2/6, 16:54] Zahra muhd mahmud=???: *ALLAH GATAN BAWA*('('('('('('('('('('


Zahra Muhammad mahmud



*page 45-46*



Anwar nanan tsaye ihsan tafito taganshi yana leke dariya tasoma yimishi kiranta yayi yatambayeta dady nacikin dakin aa tabashi amsa dan haka with confidence yashiga dakin guri yasamu yazauna yana sosa keya momy takalleshi tana murmushi tace Anwar kenan angon karni ko shekara ilham batayiba Sega yara amatsayinta nawacce bakaso keyarshi yaci gaba dasosawa yana. Murmushi kalle kalle yafara yanason gamin yaransa danshi bata ilham yakeyiba shide burinsa yaga yaransa tare da fatan Allah yasa shi suka biyo
Momy ce talura da yanayinshi tace babies din kake nemako kai yagyada mata suna gurun dadynka kaje dakinshi kagansu
Jiki asanyaye yamike yafuta dakin dady yashiga da sallama dan harga Allah yakosa yaga yaranshi sallamarsa dady yaamsa sannan yamasa izinin shigowa yaran n'a hannun dady har yanzu kuma dukansu suntashi amma basa kuka se wasa da kafafunsu sukeyi annadesu acikin tawul dan babu kayansu dan baasan da cikinsuba bare atanaji kayan samusu
Gaida dady yayi cike da Jin kunya dady yaamsa masa fuska asake sannan yace Anwar kaga tashin hankalin daya samemu ko ashe ilham da ciki tashigo gidannan kai amma Wanda yamata wannan abu be kyautaba ninarasa yadda zan bullowa lamarin dady yafadi yana kallonsa dan yanaso ne yaji me Anwar zece shiyasa yace haka
Kan Anwar ne yadaure ganin daranshi dady nashirin shegantamasa yara dasauri yakalli dady sannan yafara da cewa dady wlh yaranane nine mahaifinsu dady yace banganeba kana nufin kasan da cikin kenan amma baka fadawa kowaba nibansan tana da cikiba amma tabbas yaran nawane dariya dady yayi sannan yace taya bakasan da cikiba sannan daga ganin yara kace nakane kace kowama ze iya kama dan wani yace nasane
Anwar ganin dady da gaske yakeyi yasa shima yakara zage damtse wlh dady dagaske nakeyi nine mahaifinsu sabida ninafara sanin ilham yafada batare da shayin komaiba salati dady yayi sannan yace anya Anwar baka fara shayeshaye ba kuwa taya zakacemin haka bayan baku taba kwana guri dayaba. Habawa Anwar kamar jira yake yafara rantse rants??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????e yana shifa yaranshine kuma bawanda ya Isa yahanashi yaranshi shi wlh yaransane zuwa lokacin har yamike tsaye kamar meshirin yin dambe bakaranin dariya dady yayiba sannan daga karshe yayarda da Anwar din dama kuma gwadashi yayi danko mahaukaci yaga yarannan zece Anwar ne ubansu
mika masa yaran dady yayi yace yamusu huduba bayan yagama musu huduba yaci gaba da kallonsu yana hawayen farincikin yanajin son yaransa naratsa zuciyarsa
Wayarshi yadauka da niyar daukarsu hoto seyaga ba kaya ajikinsu betsaya tambayar komaiba yamikawa dady su yajuya da sauri yafita excode dinshi namaramasa baya mota sukaga yanufa danhaka suka gane fita zeyi kankace me kowa yashige mota cikin shirin kota kwana suka fice daga gidan

jin karar jiniya ne yasa dady yagane Anwar fita yayi ko ina zashi oho momy ce tashigo dakin tsiya tasoma yiwa dady tana cewa kode shine angon karnin dariya yayi sannan yakwashe yadda sukayi da Anwar yafadamata momy dariya harda kwalla
daukar yaran momy tasake yi tana kallonsu sannan tace alhaji kaga ikon Allah ko. Wlh son yarannan nakeyi kamarni na haifesu rungumeta dady yayi gaba daya ita da yaran yana fadin mugodewa Allah shiyabamu hakane inji momy



shiko Anwar yawo yadunga yi ? garin abuja har yasamu wani baby care suka shiga dakanshi yadunga zabarma yaranshi kaya kowanne iri daya motoci guda biyar yafita dasu amma bawacce boot dinta becika da kayaba yabiya kudin suka nufi gida sukansu masu shagon se mamaki sukeyi zuwan Anwar shagonsu dan ba boyayye bane kowa yasanshi


misalin shadaya darabi su momy suka ga se shigo da kaya security sukeyi kamar hauka basuyi musu mgnb
har suka gama sannan Anwar yashigo
tambayarshi momy tayi wannan kayanfa na yaranane yabata amsa mamaki sukayi daga momy har dady ihsan ce tafara bude kayan wow kawai take fadi daga karshe yashiga tayata suna shigar da ayan dakin ilham tunkafin sugama tuni inna tadauki wasu kaysn sanyi farare tashirya yaran aciki bayan ansamusu Pampers
koda Anwar yashigo yagansu bakinshi yaki rufuwa daukarsu hoto yadunga yi awayarsa gashi yaran sunbude ido gwanin shaawa gasu identical twins ko ganesu bazakayi ba sekalura dazaran da inna tadaura musu itama tabanbancesune yayinda ta daga ilham bayab ta haihu anan taga daya akasa daya asaman dayan to nan tagane nakasan shine yafara fitowa

har yanzu Anwar kotakan ilham bebiba wacce ke kwance tana sharar baccin gajiya tayaransa kawai yakeyi
kan gari yawaye gaba daya hotunan twins yagama zagaya social media waya ko kama daga Anwar dady momy ihsan Sun fara amsata tun cikin dare duk yan taya murnane

dasafe inna tayiwa ilham wankan jego dan haka ta lura ilham na yoyon fitsari duba da tayi shinfidarta tajike hankalin innane yatashi
[2/7, 17:05] Zahra muhd mahmud=???: *ALLAH GATAN BAWA*('('('('('('('('('('

Zahra Muhammad mahmud


*page 47-48*


Tunkafin inna tagama shirya yaran dady ya ayko adauko masa su bata bata lokaciba tagama tabadasu sannan tashirya ilham
Tagama kenan momy tashigo dakin kamar hadin baki Sega Anwar shima yazo ganin babies dinsa bayan Sun zauna inna tamusu jawabin matsalar data sami ilham momy gigicewa tayi shiko Anwar ko ajikinshi hasalima barin dakin yayi tunda abinda yakawoshi basanan
Dakim dady yanufa dan yasan sunacan sallama yayi yashiga bayan ya gaida dady sannan yadauki yaransa yana musu wasa harda yimusu selfie video shida dasu suna ta wuntsila kafafuwansu sama shikuma yanata musu wasa

Yananan zaune adakin dady momy tashigo afirgice ko sallama babu jikin dady tafada tasa kuka tana munshiga uku alhaji kar garin neman lada mukai kanmu wuta rudewa dady yayi yashiga tambayarta meke faruwa dakyar momy tamishi bayani


Shuru dady yayi yana girgiza kai sabanin Anwar Wanda bazaka ce yana dakinba. Se wasanshi yake da yaransa

Dady ne yamasa mgn dacewa Anwar bakaji lalurar data samu matarkabane.kallon dady yayi cikin sakin fuska yace naji dady allah yasauwake iya abinda zakace kenan inji momy wacce zuwa yanxu tafara fusata without care yace tomezance bayan hakan begama fadin abinda yayi niyyaba momy tadaukeshi dawani gigitaccen mari tace kana da hankali kuwa Anwar anya akwai imani a zuciyarka kuwa yarinya tasamu matsala tasanadiyyarka amma baka damuba

momy gaskiya kunfara takuramun akan lankwasasshiyarnan haba dawanne zanji da auramin miskiniyar dakukayi koko da abin kunyar daya sameni nazamantowarta uwar twins dina ni gaskiya kusauraramin haka haba yafadi batare dayajira mezasu ceba yasa kai yafice abinsa bayan yasauke yaran
momyce tamike da niyyar rukoshi dady ne yayi saurin kamota shikuma Anwar yakarasa ficewa
Kuka tasawa dady behanataba seda tayi shuru dankanta sannan dady yasharemata hawaye sannan yace banason matsalar Anwar tadameki zangasamiki Anwar dayardar Allah se yazo gabanmu yana kuka akan ilham kuma dama ban fadamiki bane jiya nayi waya dawani aminina nake fadamasa matsalar ilham shine yake cemin yanada yaro babban likita akasar indiya acan yayi karatu kwarewarsa tasa suka daukeshi ayki ababban asibitin kasar dake Mumbai kuma yakaranci fannin lalura irinta ilham danhaka gobe insha Allahu ilham da yaranta da inna ladi zasu wuce indiya zan gama musu komai ayau dinnan ko ihsan banason tasan da tafiyar bare Anwar kinjiko
Farincikine yalullube momy takara rungume dady tana mishi godiya dady ne yaci gaba kuma wannan matsalar yoyon fitsari data sameta duk acan akwai likitocin cutar dan haka ba matsala insha Allahu Inde kudi da mulki na rana zasuyi akan ilham murnace tasake kama momy


Kamin rana gidan yafara cika da yan barka yaran kawai momy tabada umarnin afito dasu in ance ina mejegon sede tace doctor yahanata zama cikin hayaniya suyi hakuri
haka aka ci gaba dazuwa barka har dare

shiko Anwar tun fitarsa office yawuce yana shiga yafara tura video din dayayi shida twince a social media habawa jamaa sunkara gigicewa da kyan twince se fatan alkhairi ake musu

*washe gari*

koda safiya tayi Anwar shigowa yayi yagaida dady sannan yagaida momy ga mamakinsa duk Sun amsa masa cikin sakin fuska
dakin mejego yashiga yatarar inna narike da yaro daya ilham nabashi nono dayan kuma nakwance akan gadon
ran Anwar ne yabaci ganin ilham nashayar mishi dayara azuciyarsa ya yanke shawarar daukomusu me renonsu daga london =?D?danshi baya kaunar ilham tashayar mishi dayaranshi
ganin nonon ilham awaje shine yatada masa da shaawa kuji mara kunya dan haka yashiga kallonsu yana lashe baki inna ce talura dashi danhaka ta ajiye yaron tafice karasawa yayi kusa da ilham yakai hannunsa kan nononta yafara wasa dashi itade kallonshi kawai takeyi tana murmushi
jin motsin mutum yayi abayanshi dasauri yajuya momy ce atsaye tana kallonshi kunyace takamashi amma ga mamakinsa momy murmushi kawai tayi masa sannan tace baban twince yau ba zuwa office ne gashi har t'en tayi mikewa yayi yakarasa kusa da yaran yanata kallonsu haka kawai yadunga Jin jikinshi yamutu daukarsu hoto yayi sannan yamusu vid?o abin mamaki yau harda ilham akama video momy mamakine yakamata gabin Anwar yaruko hannun ilham yanacewa maman twince pls ki kulamin da yarana sannan yayiwa twince Kiss yafice yana waigensu yana fita office yawuce dama shi ake jira yafita dan tuni jirgi na airpot yana jiran su ilham =??
shiryata akasakeyi sannan inna tarukota momy kuma tarungumo twince security najan kayansu har mota
airpot sukaje harda dady arakiya yayinda security mutum ashrin dady yabasu sunanan tsaye har jirginsu ilham yatashi zuwa kasar india Wanda kosu su innan basu San ina zaakaisuba
acikin jirgi inna se wukiwuki take da ido acikin security akwai mata guda biyu sune ke rike da twince Wanda dady yarada musu suna sultan da sudeis
misalin karfe shida na yamma jirginsu yasauka akasar india inda suka tarar da cincirundon motoci guda goma suna jiransu kai tsaye wani kerar gida aka saukesu fadin abinda ke cikin gidan yayiwa page dinnan kadan gida de yahadu komai akwai harda masu ayki


Anwar yataso daga office dawuri yau dan yau tunda yafita yarasa sukuni bawacce yake son gani irin ilham dan wani mahaukacin kewarta yake ayau dinnan dan haka yakosa ya Isa gida yasata a idonshi=??
[2/8, 12:08] Zahra muhd mahmud=???: *ALLAH GATAN BAWA*('('('('('('('('('('

Zahra Muhammad mahmud


*Page 49-50*



Anwar na Isa gida part din sa yawuce wanka yayi yazura doguwar riga yanufi part din su momy
Dukansu suna zaune afalo yayi sallama yashiga gaishesu yayi kai tsaye yanufi dakin dasu ilham suke ga mamakinsa basa ciki kuma ba kayansu kanshine yadaure yashiga tambayar to ina suka shiga
Dasauri yadawo falon

Momy ina su ilham suka shigane naje dakinsu bangansuba

Dady ne yabashi amsa dacewa ay tunda na auramaka ilham nafahinci na zalinceka kuma zamanku tare tana cutar dakai shiyasa nazabi farincikin dana
Namaida ilham gaban iyayenta kaga kahuta ko my son

What!!!!!!
Inji Anwar haba dady ninacemaka tana zalintata dazaka kwasheta kamaidawa iyayenta kuma ma inmaidata zakayi seka hada da yarana gaskiya nibakamin adalciba kuma wlh bazan yardaba yafadi yana kumburo b?ki


Dariyar momyce tamaida hankalinshi gareta azatonshi zatace wasa suke
Lalle Anwar baka da kunya tunda har kasamu kwarin guiwar tsayawa agabanmu kana neman ilham matar dabakaso katsaneta cewafa kayi zaka iya kasheta sabida tsananin kiyayyarka gareta kobaka fada bane momy ta tambayeshi

Zuwa yanzu Anwar yafahinci iyayensa yan rainin wayone=??danhaka dole yanunamusu shidan zamanine
Cewa yayi haba momy wacce kiyayya kuma bayan har haihuwa ilham tayi kinga ba zancan kiyayya anan danhaka dan allah kusanar dani inda yarana suke yafadi yana durkusawa agabansu cikin fuskar tausayi
shewa momy tayi sannan tace dadina da gobe saurin zuwa to mun cinyesu kashakemu muyi amansu
Dady yamike yawuce daki batare dayace komaiba momy tamike tabi bayansa suka barshi shida ihsan afalon

Ihsan dan Allah fadamini inda su twince suke da mamansu

wlh bross ban san inda sukeba nima zaman danayi anan tambayar danake musu kenan kuma desame answer suka bani dawacce suka baka inji ihsan

Iska ya fesar sannan yaruntse idonshi ranshi namishi kuna zuciyarshi kamar zata tsage. Azuciya yafara mgn haba dady meyasa zaku rusamin farincikina twince sune rayuwata amma kunrabani dasu ilham ninasan basonta nakeba amma zuwa yanzu inason ganinta. Wasu hawayene masu dumi suka gangaro akan fuskarsa tabbas yasan wannan shirin nadadyne dan yayi imani dady yafi kowa kinsa tashi yayi afusace yabar part din dakinshi yanufa yana shiga wayarsa yadauka yakira naseer awaya yana shaidamasa abinda ke faruwa
naseer seda yatausayamasa sabida twince kowaye mahaifinsu baze so suyi nisa dashiba hakuri yadunga bashi yanacewa horone su dady sukemishi abisa wulaancin dayayiwa ilham Wanda yasan nanda dan lokaci zasu hakura sudawo mishi da matarsa sallama sukayi

*Bayan wata biyu*

Zuwa yanzu Anwar yatabbatar da ilham tamishi nisa gaba daya yazauce akanta ita da yaranta kullum cikin kallon hoton daya musu yakeyi

kuma har yanzu iyayensa sunki suce masa komai gameda ilham da yaransa
harga Allah yanzu yasoma tausayin ilham amma basonta yakeba( nace kuji wawa )

*Ilham*

acikin watanni biyunnan anyi nasarar tsaida miyaun datake zubarwa haka shima lalurar yoyon fitsari andade da maganceta dayake akwai kudi domin baabinda dady betana darmusuba
haka suma su twince kullum kara wayo sukeyi abin gwanin shaawa kuma itama ilham yanzu tagane su amatsayin yaranta dan har wasa take musu

yaune aka saka ranar yima ilham ayki wajen ganin anmikar da kafarta dakuma hannunta wani injine zaa sata aciki na tsawon kwana uku ana kuma sa ran dazaran tafito dayardar Allah zata warke. Dan haka tun safe suke tawaya da inna da su dady tana fadamusu abinda ake ciki duk da shima doctor din yana waya da dadyn
tun zuwan dasuke asibitin doctor betaba kallon ilham ido cikin idoba sabida becika kallon mataba
yau anyi saa suna shigowa office dinshi idonshi ne yasauka anata afirgice yatashi yanakallonta badan komaiba sedan tsananin kamar datakeyi da mahaifinsa tirkashi wai waye doctor din ilham ne

Maman yusuf
[2/8, 17:49] Zahra muhd mahmud=???: *ALLAH GATAN BAWA*('('('('('('('('('('


Zahra Muhammad mahmud


*page 51-52*


Har suka karasa cikin office din doctor natsaye yakasa zama har seda inna tafara gaisheshi sannan yadawo da tunaninsa zama yayi yana cigaba da kallon ilham

Bayan yadauko file na ilham ne yakara lura da sunan dake rubuce ajiki ilham bukar shettima. Tabbas zatonshi yazama gaskiya amma zebar komai har zuwa ilham tasamu sauki rubuce rubuce yayi sannan yaba inna madarar dazata dunga ba twince nan da kwana ukun

Anshigar da ilham cikin machine dan haka inna direba yadawo da ita gida ita dasu twince zuciyarta cike da adduar Allah yasa adace.


*Doctor Adnan imam shetima*


Shine cikakken sunan doctor dake duba ilham dane ga alhaji imam shetima saurayine matashi Wanda shekarunsa bazasu gaza 35 ba shikadaine agurin iyayensa kallo daya zakama adnan kasashi acikin jerin kyawawan maza domin kyakkyawane na ajin farko bashida son hayaniya kwatakwata shiyasa beson zama ? Nigeria. Mahaifiyarsa sunanta hajiya hauwa macece me kirki haka shima mahaifinsa Wanda yanzu haka suke zaune agarin kaduna tunbayan barinsu garinsu na aynihi wato meduguri asakamakon yakin daake a yankin

Adnan yayi primary da secondry schools dinsa duk agarin meduguri kuma Allah yaba mahaifiyarsadamar dauko jakar takardunsa shida mahaifinsa lokacin dazasuyi hijira dan haka kobayan zuwansu kaduna basu sha wata wuyar rayuwaba mahaifinsa yasamu ayki a nnpc kuma ana bashi albashi me tsoka shiyasa yanemar masa Abu zaria inda acanne yayi degree dinsa nafarko
Lifes move on mahaifinsa yazama hamshakin mekudi dan haka yakaishi kasar india domin yakarasa karatunsa n'a doctor acan
Duk da yawan tarin dukiyar mahaifinsa kullum cikin damuwa yake da bacewar dan uwansa bukar Wanda yanemeshi har yafidda ran ganinshi suko dama iyayensa yasan Sun mutu dan haka yake musu addua amma rashin sanin labarin kaninsa nasashi acikin damuwa dan so tari ze kulle kanshi adaki yaci kuka
Halin da mahaifinsa keciki yana dagamasa hankali har yakejin da yanada ikon cirewa mahaifinsa damuwarsa dayayi

bayan wasu shekarune mahaifinsa yafada harkar siyasa inda ananne suka hadu da mr pr?sident wato dadyn Anwar
Mahaifin adnan shine yadauki nauyin campagne din dady har kuma Allah yasa akayi nasara dady yaso yabashi minister naman petur amma yaki tun farko hawan dady mukamin Abban adnan yace bashida raayin mukamin amma shi ya yarda yadunga basa kwangila haka ko akayi ko lokacin auren Anwar baya kasarne yana saudiyya shiyasa be hallaci bikinba kuma shi baya hawa social media bare yasan wacece amaryar Anwar shide kawai dady yacemishi tsuntota yayi kuma sunanta ilham danse akwanakinannema yake shaidamishi Bata da lafiya shine yahadashi da adnan dan fannin yakaranta
Tsakanin adnan da Anwar basu San junaba dan iyayensune suke burin su hadasu Abota.

har kudi masu tsoka Abban adnan yasa gaduk Wanda yaga dan uwansa ko yaji labarinsa amma har zuwa yanxu bawani bayani yahakura yabarwa Allah


*cigaban labari*

twince koda suka daina shan nono basu damuba domin tun asalinsu masu hakurine shiyasa inna bata samu matsala dasuba


*Nigeria*
Anwar yanzu ko aski bayayi zuwa yanzu ko office yadena fita se mataimakinsane ke gudanar da komai.
da yadauka iya su twince kawai yakeson gani se yanzu yatabbatar da basu yake soba mahaifiyarsu yake da bukatar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login