Showing 1 words to 3000 words out of 39004 words
*AURE DA HAIHUWA*
*Zahra Surbajo*
*Ina mai Baku hakurin jina shuru da kukayi,da sauyi da kuka samu game da yadda nasaba
gudanar da lamurana,hakan ta farune sakamakon kaddarori da suka fadawa rayuwata Wanda
banyi tsammaninsu ba,Wanda Alhamdulillahi da taimakon Allah na cinye su,ina godiya ga
masoyana wainda basu yada ni ba,Allah saka da alkhairi,*
*Littafina na Hakki ne danake rubutawa watanni hudu kenan da yaci kasuwa,inda nasaida
labarin ga wani marubuci Dan kasuwa ze wallafashi akasuwa,ayi hakuri don Allah hatimin
nasara kowa ke nema shiyasa daya bukata na sallama ban sanar dakubane nabari se nadawo
rubutun se in sanar da fatan zakui min uzuri,sabida tsawon watanni hudun nayisune ahali na
rashin lafiya*
_wannan littafi nawa sabo ne me dauke da darussa masu maana,banyishi Dan cin zarafin wani
ko wata ba,nayi ne domin fad'akarwa da nishad'antarwa,ga soyayayya me tab'a zuciyar me
karatu,kuma kyauta ne bana kud'iba_
_Ku bishi ze k'ayatar daku_
*page 1*
I'd card d'in dake gaban rigarta ta gyara sannan ta gyara farin glass d'in dake fuskarta,cikin
murmushi takai dubanta gareshi,tace cikin harshen turanci.
"Ranka ya Dad'e,bawai baze yiwu bane,ina de so ka gane ne wannan shine kwayoyin
haihuwarka,da gwajin mu ke nuna mana na k'arshe ne, dole se anbi komai cikin kulawa da
takatsantsan,inba haka ba,za'a iya rasa komai"cewar doctor Amina Galadima kamar yadda aka
rubuta agaban rigarta.
Gyara zama yayi sannan yakai dubansa gefen matarsa dake ta cika tana batsewa, yayi
murmushin k'arfin hali sannan yace,
"Doctor badamuwa na mik'a lamuran ga Allah, ko adace ko akasin hakan,Dan haka kiyi me
yiwuwa kawai,kinsan yarda da nai dake ne kesawa in baro k'asata in zo gareki "be gama fad'in
abinda yakeson fad'i ba,matar tashi ta katseshi da cewa cikin fad'a da harshen larabci.
"Farhan wannan shine karo na biyar da za'ai dashen kwayoyin halittarnan,wallahi matuk'ar ba'a
daceba,to ni kuma zamanmu yazo k'arshe,taya in banda toshewar basira,kana zaune a k'asar
Dubai, zaka wani taho Nigeria Neman haihuwa,shekara biyar kenan muna zuwa kullum ba
sauyi,to Nide na fad'a maka"ta k'arasa maganar tana huci.
Jingina yayi da kujerar da yake zaune ya lumshe kyawawan idanuwanshi,yana sauraronta,harta
gama,sannan ya budesu a hankali,ya zubesu akan matar tashi wacce yake ji inba ita baze iya
rayuwaba.
Dubansa ya kai gun doctor Amina sannan yace cikin sark'akk'iyar murya,"doctor please do
something meaningful to save my marriage"
Cike da tausayawa doctor Amina tace "insha Allah"
Sallama sukai mata suka wuce masaukinsu,bayan an amshi seamen sample d'inshi,ko a hanya
matar tashi me suna shehnaz in banda masifa ba abinda take masa shide kallonta kawai
yakeyi,Dan besan yaze mata ta fahimceshi ba.
Bayan wasu kwanaki doctor Amina ta buk'aci daya kawo matarsa Dan adasa mata D'an tayin
acikinta.
Koda suka iso asibitin doctor ta shiga tiyatar gaggawa Dan haka d'aki na musamman aka basu
su zauna domin jiran fitowarta.
A d'akin suka tarad da wasu mata da miji zaune suma daga dukkan alamu ita suke jira.
Sosai ma'auratan suka tafi da hankalin Farhan,kasancewar manne suke da junansu cikin so da
k'auna,ya tsinkayo hirar da sukeyi cikin harshen turanci,inda mijin ke cewa.
"Baby ina fata da addu'ar Allah yasa in anyi dashennan mu dace da samun haihuwa"
murmushi matar tayi sannan ta shafi gefen fuskarshi tace"insha Allahu dear za'a dace jikina
yabani hakan"ta fad'i cike da murna a fuskarta.
Sosai suka burgeshi duba da ganin yadda suka damu da junansu kowa k'ok'arin kwantar da
hankalin d'an uwansa yake,sab'anin shi da tashi matar wacce keji kamar ta shak'eshi ya mutu ta
huta.
Suna nan zaune doctor Amina ta shigo d'akin ita da wasu ma'aikata guda hud'u,daga kallon
shigowar tata kai ba se an fad'a maka ba tana cikin tashin hankali,
Duk a firgice take,hakan yasa dukan su maida hankali kanta,cikin sauri sauri tace cikin harshen
turanci."don Allah Ku gafarceni,Mahaifina ne Allah yayiwa rasuwa yanzu sakamakon hatsarin
mota, zani gida yanzu,amma nayi musu bayanin komai,kuma zasu gudanar dashi cikin
nasara"ta k'arasa maganar tana nuna ma'aikatan data shigo tare dasu.
A hankali Farhan yace"badamuwa doctor, Allah yajik'an mahaifinki,yasa ya huta"
Suma wa'incan ma'auratan ta'aziyyar su kai mata,amma banda shehnaz,wacce gaba d'aya ta
d'auki tsanar duniya ta d'orawa doctor Amina sakamakon yarda da ita da mijinta yayi.
Cikin hanzari ta juya ta fice daga d'akin,ma'aikatan data shigo dasune suka buk'aci dasu taso su
bisu.
Cikin nasara,kowacce an dasa mata sperm d'in a mahaifarta,se fatan Allah yasa adace.
Haka suka baro asibitin kowa na fatan dacewa gurin Allah.
Muje zuwa.
Surbajo for life.
11/14/21, 12:43 PM - MY MTN 2: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������
*Zahra Surbajo*
*page 2*
Tsawon sati biyu kenan da yin dashen,kuma tsawon kwanakin da doctor ta d'ibar musu kenan
su dawo ay musu gwajin ciki Dan aga ko andace.
Misalin k'arfe takwas su Farhan suka shigo asibitin, zuciyarshi cike da zullumin abin da ze
tarar.a waiting room suka zauna zaman jiran iso daga doctor Amina.
Ita ko doctor Amina nacan cikin office d'inta cikin matsanancin tashin hankalin da ta ma rasa ta
yadda zata fuskanci matsalar.
Cikin tsananin bak'in ciki da tashin hankali ta kai duban ta gun ma'aikatan da ta sa su gudanar
da dashen,tace,
"Me kuka yi kenan?,innalillahiwainnailaihirrajiun,da wanne bakin kuke son in yiwa mutanen nan
bayani,?hankalin ku na ina lokacin Dana ware muku na kowa?,wannan wanne irin ganganci
ne?,fisabilillahi ta ina Sunan Rayhan yazo d'aya da Farhan,ta Ina?"ta k'arasa maganar cikin
zubowar wasu hawaye masu zafi data kasa tsaidasu.
Suko ma'aikatan motsin kirki cikinsu ba Wanda ya iya yi,Dan sunsan ba k'aramar b'arna suka
aykata ba,Dan haka sun rasa ma kalma a bakunansu bare su furta,.
A raunane ta danna k'ararrawar kiran su,ba'a jima ba Farhan suka shigo shida shehnaz dake ta
faman cika tana batsewa,doctor na had'a ido dasu wasu zafafan hawayen tausayinsu ya zubo
mata ta runtse idon ta, Farhan na ganin hakan yasan ba'a dace ba,Dan haka addu'oi yay ta
karantawa a zuciyarshi da zasu sanyaya zuciyarshi.
Bayan sun zauna doctor tayi k'ok'arin dedeta natsuwarta,sannan ta fara magana cikin rashin
tabbas,tace"da farko de Farhan inaso ka yarda da k'addarar Allah, mekyau ko Mara kyau"
Murmushin k'arfin hali yayi sannan yace"karki damu Amina, nasan ba'a dace ba na bar komai a
hannun Allah"
A raunane tace"Farhan wannan karon ba dacewa bane ba'a yiba,an dace sede an samu
matsala daga ma'aikatanmu,akwai wani bawan Allah me suna Rayhan,shima ya zo nan da
matarsa Safna, suma haihuwa suke nema,to rana d'aya muka amshi sample d'inku, ranar da
za'ayi dashen ni kuma akamin rasuwa,nabar komai a hannun abokan aykina,sabida wajibine ayi
dashen a wannan Rana, to matsalar da aka samu,se suka d'auki sample d'inka suka sama
Safna,shikuma na Rayhan aka sawa shehnaz"ta k'arasa maganar cikin zubar da hawaye,
Runtse ido Farhan yayi yana karanto duk wata addu'a da tazo bakinsa,tashin hankalin daya
shiga baze iya misaltuwa ba,sei da ya d'auki mintuna a haka sannan ya bud'e idanun nasa a
hankali,yace,
"To yanzu ya akayi,shi Rayhan d'in ya san da wannan batun?"
Cikin dauriya doctor tace"be sani ba Farhan, sabida shekaran jiya ya kirani,yace yana son ya
kawo Safna ay mata gwajin cikin Dan jiya da asuba zasu bar k'asar,tafiyar gaggawa ta taso
masa,sun zo nan an mata gwajin kuma sakamakon ya tabbatar da tasamu cikin,ban duba
b'arnar da suka yi ba se yau nay ta kiran number Rayhan d'in domin in sanar dashi bata
zuwa"ta k'arasa maganar tana zubar da hawaye.
Kife kanshi yayi akan tebur d'in dake gabansu ya fara zubar da wasu hawaye masu zafi,duk
yadda yaso ya jure amma ya kasa dole ya koka,wannan wacce irin mummunar kaddarace D'an
wani a cikin matar wani,?ina zesa rayuwarsa,yana tsaka da wannan tunani ne ya tsinkayo
muryar shehnaz na fad'in.
"Wannan ni ba matsalata bace kai ta shafa,Ni de fatana a gwadani yanzu Allah yasa bana
d'auke da cikin wani gardi da ban sani ba"
Ba su da ta cewa dole doctor ta auna ta,abun mamaki,bata samu cikin ba,ita
ayko ana sanar da sakamakon ta mik'e,ta suri Jakarta,ta kai duban ta gun Farhan dake cikin
tashin hankali tace a wulak'ance,"zuwa yanzu kasan aure ni da kai ya k'are,Dan bazan k'arar da
rayuwata a gidan auren da ba albarkar aure ba,wato Haihuwa,Dan haka na tafi ka san inda
zaka ayko min da takardata"tana kaiwa nan ta bud'e k'ofar ta fice a fusace.
Sake runtse ido Farhan yayi yana karanta duk addu'ar data zo bakinsa.
Iya tashin hankali doctor Amina ta shigeshi,Dan haka rarrashin Farhan d'in ta shiga yi da duk
wata Kalmar rarrashi data zo bakinta,
A hankali ya d'ago ya kalli doctor sannan yace,"Amina inason abinda wannan mata zata
Haifa,da dukkan rayuwata,fatana ki tabbatar da kin samo inda suke kin kuma shaida musu
cewa d'ana ne a cikinta,hakan da zakiyi shine kawai yafiyata a gareki,Duk tsawon lokaci Amina
ina Dubai Ina kallon hanyar da zaki kawomun gudan jinina,"yana kaiwa nan yamik'e ya fice
daga office d'in,doctor Amina na binshi abaya,jiki asanyaye,har zuwa gun da ya ajiye
lafiyayyiyar motarshi,ya bud'e ya shige,a hankali doctor ta dafa window motar tace murya na
rawa.
"Farhan ka taimakeni lokuta da dama a rayuwata,Kaine silar matsayin da nake kai
yanzu,kayimin alfarma so shurin masak'i,nayi maka alk'awarin nemo Safna da mijinta aduk inda
suke afad'in k'asarnan,Dan tabbatar musu da cewa D'an dake cikinta ba nasu bane na
mune,kuma in dawo dashi zuwa gareka"
Murmushi yayi me taushi,sannan yaja motar ya fice daga asibitin,
Ko takan shehnaz be biba Dan yasan tuni ta jima da barin garin na abuja,ta nufi Lego's Dan
siyan ticket d'in daze sada ta da k'asarsu,
Dan haka gida ya wuce yayi wanka ya kintsa duk abinda ze bukata,sannan ya kira agent d'inshi
aka tanadar masa private jet daze kaishi k'asarsa ta haihuwa wato Dubai.
Ba'a jima ba ya kirashi ya shaida masa komai yayi ready k'arfe shida zasu tashi na yamma.
Wuni yayi kwance ya rasa meke masa dad'i a rayuwarsa yana son matarsa shehnaz amma ita
son da takewa haihuwa yafi son da take masa, gashi kuma ya samu haihuwar ta inda be tab'a
tsammani ba,runtse ido yayi yana wa Allah kirari.
K'arfe biyar ya isa airport zuwa shida jirginshi ya d'aga dashi k'asarsa ta haihuwa,cike da kewar
gudan jininsa.
Muje zuwa
Surbajo for life.
11/14/21, 12:43 PM - MY MTN 2: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������
*Zahra Surbajo*
*page 3*
*TUSHEN LABARIN*
Safna Habu Sara shine sunanta,d'iyace ga malam habu,dake zaune a k'auyen Sara dake
Zangon Daura ta Jihar Katsina,
Malam habu shine limamin garin sabida yana da tarin ilimin addini Dede gwargwado yasa
dagacin garin nad'ashi limamin garin
Matanshi uku,inna hansai itace uwargida,se inna fure,se Amaryarsu jamila amma suna kiranta
da Sabuwa.
Tunda malam habu ya auro jamila take fuskantar matsi da takura agurin sauran abokan
zamanta,sun had'e mata kai sun wareta Wanda hakan ko kad'an be mata dad'i biyayya Dede
gwargwado tana musu amma su Sam basa gani,acewa da ganin su duk na munafunci ne.
Inna hansai Nada Yara biyu,jummai,da Ladidi,se inna fure itama guda biyu gareta,akwai Abu se
Zabba'u,inna sabuwa ce me guda d'aya wacce malam ya sawa sunan mahaifiyarshi Safina,
Yaran malam habu biyar duka mata Allah be bashi haihuwar d'a namiji ba,shi yasa ya duk'ufa
wajen ganin ya basu tarbiya da ilimi ta yadda za ay alfahari da su.
Duk wani cin kashi na gidan akan jamila da 'yarta ake yinsa,an maidasu tamkar bayi,da ike
jamila irin mutanen nan ne masu hak'uri ko kad'an bata cewa komai akan abinda ake musu ita
da 'yarta.
Tun tasowar 'yanmatan na malam habu Allah yay musu farin jini, kasancewar dukan su da
mahaifinsu suke kama,kyau kamar su sukai Kansu,kasancewarshi bafulatani,Safna ce ta
kerewa kowa kyau acikinsu kasancewar ita ba iya kamannin malam d'in ta d'ebo ba harda na
mahaifiyarta.Wanda hakan yasa ta fice zakka acikinsu.
Duk da tafisu kyau,wani ikon Allah ko kad'an ita bata da farin jinin samarin, kamar wata me
bak'in jini,hakan ya sanya su inna fure yiwa sabuwa gorin 'yarta ba mashinshini.
Ita sabuwa abin be damunta Dan tasan aure lokacine,in yazo za ayi.
Wasa wasa har an kawo kud'in sauran 'ya'yan gidan amma Safna har yanzu ba me cewa yana
sonta.
Suna Aji biyar a secondary school aka sha bikin sauran 'yan uwanta,inda kowacce ta tare a
gidanta,aka bar Safna ita kad'ai a gida.
Zuwa lokacin lamarin yafara tab'a zuciyar sabuwa,amma ta duk'ufa da addu'a.
To bayan aurar da 'yanmatan gidan ne wahalhalu suka k'aru akan Safna, ita ce d'ebo ruwa,ba
dabbobi abinci,shara wanke_wanke,girki,yo itace ,acewar matan gidan in bata yiba Wa ze mata.
Duk ta fice hayyacinta kullum mahaifiyarta kwarin guiwa take bata da cewa watarana se labari.
Muje zuwa
Surbajo for life.
11/14/21, 12:43 PM - MY MTN 2: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������
*Zahra Surbajo*
*page 4*
Yau tun asuba ta mik'e tayi duk aykace aykacenta,sabida yau ake taron sunan 'yar gidan inna
hansai jummai ta haihu.
Ko da ta gama shiryawa,tuni su sabuwa da inna fure da sauran makwabtansu sun tafi gidan
sunan,da ike a zango tai auren, Dan haka fitowa tayi cikin kwalliyarta ta nufi gidan su k'awarta
Maimuna,dama tare zasu tafi gidan sunan.
Tana zuwa ta samu Maimunan ta shirya ita kawai take jira,Dan haka rankayawa sukai suka nufi
titi Dan samun abun hawa da ze kaisu garin na zango.
Tsaye suke a bakin titin amma babu abun hawa,cikin damuwa Maimuna tace"yau fa alamu sun
gwada 'yarfillo a k'afa zamuje zangon nan,kuma wallahi ga rana"
Murmushi Safna tayi daya k'ara fito da kyawun fuskarta,tace cikin siririyar muryarta,"da alama
kuwa,kawai mu fara takawa,tunda ba wani nisa bane sosai,watak'ila a gaba mu samu"bata
k'arasa maganar ba taji k'arar taka burki a gabansu,a tsorace dukan su suka dubi kan titin,wata
shirgegiyar mota suka gani tana k'ok'arin gyara parking a gaban su,
Tana gama tsayawa na cikin motar ya fito,matashine kyakkyawa ajin farko,Wanda Hutu da ilimi
suka samu masauki a jikinshi,sanye ike cikin farar shadda,tasha d'inkin zamani,kanshi ba hula
se sumar daya Tara data dace da tsarin kwalliyar tashi.
Cikin takun burgewa ya k'araso gabansu fuskarshi d'auke da murmushi,yace"Amincin Allah ya
tabbata a gareku,Ku gafarce ni firgitaku da nayi"ya k'arasa maganar yana had'e hannayensa
guri guda.
Safna sarkin kunya,sunkuyar da kai tayi tana murmushi,yayin da maimuna tace"amin,mungode
ba komai"
"In bazaki damuba Dan Allah kitaimaka min da sunan k'awar taki Dan naga kamar rowar
magana gareta "yayi tambayar yana kallon fuskar Safna wacce har yanzu murmushi kawai take
yi ba tace komai ba.
Murmushi maimuna tayi sannan tace "Safna sunanta dafatan ba zuwa sace ta kayi ba?"
Murmushi yayi yace"ita ta fara satoni,so shine nima nake so da taimakon ki ki tallafamin in
saceta zuwa gidana na aure"
Da sauri Safna ta b'oye a bayan Maimuna,alamun taji kunya sosai,har zuwa lokacin murmushi
be bar fuskarta ba.
"Se mun bincika tukuna in nagartarka ta kai a baka se ayi hakan sabida komai nufin Allah ne"
"Sunana Rayhan Hashim Daura,mahaifina Dan daura ne amma muna zaune a Abuja sabida
yanayin Ayki,nazo bikin abokina ne nan yardaje,se kuma Allah ya had'ani da tawa amaryar a
hanya"
Haka yay ta jansu da hira amma Safna ta gaza furta komai,har suka samu abun hawa,fafur
suka k'i yarda su hau motarshi,gashi dukan su bame waya,Rayhan ganin zata kubce masa ne
yasa ya d'auko wayarshi dank'areriya a gaban motarshi ya mik'awa Safna, yace "ba Dan na isa
ba Dan Alfarmar Annabi ki amshi wayarnan,in muka rabu yanzu ban san ina zan sake ganinki
ba,sabida yau zamu wuce gida,amma inda wayar a hannunki zan kira kimin kwatance"
Jiki a sanyaye Safna tasa hannu ta amshi wayar,se alokacin tace a tsorace murya na rawa,"zan
zan...ajiyema in...muka had'u zaka amshi abunka"wani sanyine ya ratsa zuciyar Rayhan
sakamakon jin muryarta da yayi.
"Na amince beauty semun had'un,"
Daga haka sukai sallama suka shiga mota shima ya shiga tashi,da ike hanya dayace haka yay
ta bin su a baya har aka sauke su a zangon sannan yay musu hon yayi gaba.
Jikin Safna a sanyaye suka isa gidan sunan daya cika da jama'a.
Ko a gidan sunan seda aka mata habaicin ba mashinshini,ayko carab maimuna ta amshe
zancen da cewa,"mashinshini de kam Safna Allah ya nufa ya shinshino ta,kuma insha Allahu se
ya tsone idon mak'iyanta"
Ayko gaba d'aya gurin aka sa shewar zancen Nata.
Basu baro gidan sunan ba se isha'i sabida seda suka gyarawa mejego gida tukuna suka tafi.
A gajiye Safna take,Dan haka tana zuwa gida wanka tayi ta kintsa sannan ta Ciro wayar ta
samu innarta tai mata bayanin komai game da had'uwarta da Rayhan yau.
Farincikine ya mamaye zuciyar innar ta,gami da yiwa Allah godiya daya fara haska tauraruwar
'yarta a idon manema sabida itama ta samu tai aure ta huta.
Nasiha da Jan kunne tai mata kan tade kama kanta da mutuncinta banda giggiwa,daga k'arshe
tai fatan alkha'iri.
Muje zuwa
Surbajo for life
11/14/21, 12:43 PM - MY MTN 2: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������
*Zahra Surbajo*
*Page 5*
Safna shirin bacci tayi,tayi addu'a ta tofa tana kwanciya taji wani sauti me dad'i na tashi ak'asan
fulonta,da har ta firgita can kuma ta tuna da wayar da Rayhan ya bata,Dan haka a tsanake ta
d'auko wayar,bata wahalar gane kanta ba,sabida tana karatu,a hankali ta d'aga wayar ta kara a
kunnenta,wata sassanyar ajiyar zuciya Rayhan ya saki wacce ta haddasawa Safna wani bak'on
lamari ajikinta,sosai jikinta ya mutu,a hankali ta jiyo muryarshi yace a kasalance "beauty"sosai
sunan da muryar da yay amfani da ita gurin kiran sunan Nata sukai mata