Showing 9001 words to 12000 words out of 39004 words
yake
wajan ambatar sunanshi,
"Rayhan!!!"
Murmushi yayi gami da samun guri suka zauna,yace"surprise ko?"
A hankali doctor ta koma ta zauna bakin ta bud'e tana kallonsu kamar a mafarki.
"Doctor ya ayki,ya kuma akaji da jama'a,kin ganmu se yau"cewar Rayhan fuskarshi d'auke da
murmushi.
.baki na rawa doctor tace"Alhamdulillahi Rayhan, na kusa haukacewa gurin neman ka"ta
'karasa maganar cikin damuwa.
Maida hankali shi yayi gunta sosai ya gyara zama sannan yace"da akayi ya ya doctor kike
nemana?banganeba"
Glass d'in fuskarta ta cire sannan ta share hawayen da suka zubo mata,tace"matsala aka samu
yayin gudanar da aykin dashen da aka yiwa safna"
A razane Rayhan da Safna suka d'ago ido suna kallonta,bakin safna har rawa yake tace"doctor
wacce irin matsala kuma,?don Allah kimana bayani"
File d'in komai ta d'auko,sannan ta mikawa Rayhan da sauri ya fara dubawa,ita kuma taci gaba
da masa bayani.
"Yayin gudanar da aykin aka samu matsalar sakamakon kamanceceniya ta suna da kuke dashi
kai da Farhan, cikin dake jikin safna Rayhan ba naka bane na Farhan ne,kai kuma kwayoyinka
da a kasa ma matarsa basu sa tayi cikin ba"daga haka de ta kwashe komai ta sanar
dashi,gamida had'a hannayenta guri d'aya alamar Neman afuwar kuskuren da aka samun.
D'ago ido yayi yana kallon likitar cikin alamar rashin yadda da abinda tace, ganin hakane yasa
doctor d'aukar Qur'anin dake gefenta,kasancewar tana da alwala tace cikin kuka"na rantse da
duk wata gaskiya dake cikin wannan littafi me tsarki gaskiya na sanar daku"
Yanke jiki da safna tayi ta fad'ine yasa su waigowa gareta a razane sukai kanta suna kiran
sunanta.
Da sauri doctor ta kira ma'aikata aka shigo da gadon d'aukar marasa lafiya aka d'auketa zuwa
wani d'akin inda doctor tashiga k'ok'arin ceto rayuwarta.
Rayhan samun Kansa yayi da kasa bin bayansu ya zube a office d'in doctor Aminar yana
danasanin amincewa da yin dashen da yayi tun lokacin da aka bashi shawarar yin
hakan,wannan wacce irin mummunar k'addara ce tabbas a matsayinsa na musulmi dole ya
yarda da hakan.
Runtse idonsa yayi wasu zafafan hawaye suka shiga zubo masa,da ya rasa ta ya ze tsaidasu.
Yana nan zaune doctor ta shigo,tace"ta farfad'o,kai take son gani yanzu"
D'ago ido yayi ya kalli doctor d'in yace a sanyaye,"zanje gida in dawo ki ci gaba da kulawa da
ita,"daga haka yasa hannu a aljihu ya d'auko kudi ya ajiyewa doctor d'in,sannan ya juya ya fice
daga office d'in.
Cikin rashin fahimta doctor tabi bayansa da kallo har ya fice.
Muje zuwa
Surbajo for life.
11/14/21, 12:44 PM - MY MTN 2: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������
*Zahra Surbajo*
*Page 12*
"Amma ay kasan ba zina nayi nasameshi ba,hasalima Kaine ka kaini inda na sameshin,ni meye
laifina anan"cewar Safna tana share hawayen dake bin fuskarta.
"Eh to marabar kadan ce, kuma laifinki daya anan, taya kika kasa gane sperm dina,tunda ay ba
yau nake muamala dake ba,yakamata ace tun farko ke kin gano cewa ba nawa bane"cewar
Rayhan cikin nuna halin ko in kula.
Safna sabida tsananin mamakin Rayhan din wani zazzabi ne ya kamata nan take,bakin ta na
rawa tace"Rayhan don Allah mubar maganarnan,banida lafiya, nan gaba mayi"
"Ay wlh in kinga nabar maganarnan tashi kikai mukaje asibiti aka zubar da cikin nan Dan bazan
taba barinsa ajikin matata ba wlh"ya fadi maganar cikin fushi.
A razane ta dubeshi tace"kyautace Allah yazabeni yayimin,Dan ya gwada imanina,wallahi
Rayhan matukar ina numfashi babu wani mahaluki daya isa ya zubar min da cikin jikina,har se
na haifeshi,"ta fadi cikin dakewa.
Sosai ta ba Rayhan mamaki,Dan ko a mafarki be taba tunanin ze sa doka ta tsallake
ba,hakanne ya kara fusatashi yace,"Amma ay kinsan cewa ba gudan jini na bane ko"
Tun kan ya gama rufe bakin tace cikin karaji "Ni gudan jinina ne Rayhan, ni Dana ne,kuma ina
son Abuna"tana kaiwa nan ta mike tayi hanyar ficewa daga dakin.
Cikin zafin nama ya fincikota ta dawo gabanshi ta tsaya,ya fara magana cikin izza.
"Ke matata ce, dole ne kibi abinda nake so,ciki se an zubar dashi wallahi,matukar kina matata"
Kwace hannunta tayi daga rukon da yay mata sannan ta dubeshi ido cikin ido tace cikin rashin
tsoro "idan kuma na tashi daga matar taka fa?"
A atsorace Rayhan yakai dubansa kanta,Dan jin maganar yayi kamar saukar aradu,sosai ta
firgitashi,bakinsa har hardewa yake yace"Ina sonki Safna sede bazan zauna dake da cikin
jikinki ba,ban kuma shirya rabuwa dake ba,pls ki amince azubar da cikin nan mu zauna
lafiya"yafadi cikin sigar rarrashi.
"Ciki bazan zubar dashi ba,zama dani ban tilasta maka ba,haka shima zaman lafiya dani ban
rokeka ba,duka iko ne da Allah ya damka a hannunka"tana kaiwa nan,ta rabe ta gefensa ta fice
daga dakin,ta nufi dayan dakin Nata, ta shige ta kullo kofar.
Kuka take me tsuma zuciya,yau Rayhan ya sa ta aykata abinda Allah ya hana sainsa da miji.
Wani kukan ne ya kubce mata sanda ta tuna,bata da wata madafa a rayuwarta,sai Rayhan
din,tana sonshi so na hakika,amma bazata yarda ta sabawa Allah sabida shi ba.
Har gari ya waye be nemeta ba,itama haka,tana jin karar motarshi alamun ya fice,fitowa tayi ta
nufi kitchen, Dan samawa kanta abin da zata karya.
Ga mamakin ta kitchen din arufe yake se wata takarda da ya manna ajikin kofar,dauke da
rubutu kamar haka,
"Bazan iya ciyar da Dan da ba nawa ba,ki nemi ubansa ya baku abinci"
Zubewa tayi agurin tana kuka,bata taba tsammanin Rayhan ze mata haka ba ko a wasa.
Muje zuwa
Surbajo for life.
11/14/21, 12:45 PM - MY MTN 2: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������
*Zahra Surbajo*
*Page 13*
Mikewa tayi ta koma dakin ta, kudi ta dauko tasa hijabi,ta nufi gun megadi,yana hango ta nufo
shi yataso da sauri yadan risina yace "barka da safiya hajiya,me kike da bukata?"amsawa tayi
cikin sakin fuska tace"baba don Allah cefane nakeso kayomin,a wuse market,"
"To badamuwa ranki ya Dade kawo aje ayo miki"
Lissafa masa komai tayi sannan ta bashi kudin kimanin dubu tamanin,yatafi .
Kulle gidan tayi ta ciki sannan ta koma cikin gida,wanka ta shiga sannan ta shirya ta dawo falo
zaman jiran akawo mata cefanen.
Baa jima sosai ba megadi yashigo mata da sakonta bayan ta bude masa gidan,sosai tai masa
godiya sannan ta kwashe komai takai dakinta.
Dan karamin gas din datasa ya siyo mata ta kunna ta daurayo tukunyar daya siyo mata tazo ta
hada komai ta Dora indomie acikin dakin Nata.
Dan duk abinda zata bukata seda tasa ya siyo mata.
Haka taci gaba da gudanar da rayuwarta a kulle acikin daki,koda wasa batason ganin Rayhan,
shiyasa ta kulle kanta aciki,sabida akwai toilet acikin dakin Nata,
A nashi bangaren Rayhan ko tunda ya fice yabar gidan,kotu yaje ya shigar da karar doctor
Amina sakamakon abinda sukawa matarsa,inda alkali yabada sati biyu su hallara agabansa.
Lokacin da sakon ya riski doctor Amina,tashin hankalin data shiga,bashida adadi.Neman
Farhan take a waya tun lokacin data ga su Rayhan din amma bata shiga,wannan shine yakara
daga hankalinta.
Ranar shiga kotun da safe Rayhan yaje kofar dakin na safna yace cikin dakewar murya.
"Ki bude kofa ki fito mu tafi kotu Dan yau alkali yabada mu hallara agabanshi ina jiranki a
mota"yana kaiwa nan yayi fucewarsa abunsa
Safna jin maganar tayi kamar saukar Aradu,yau itace Rayhan yakai kara kotu?wannan wacce
irin masiface.
Tunda ya fada tasan dagaske yakeyi,Dan karya bata daya daga cikin halayensa.
Jiki asanyaye ta janyo hijab tasaka,ta zura takalmi ta fito.bayan ta kulle dakinta.
A motar ta sameshi yana cika yana batsewa,ba me cewa shine Rayhan din ta me yawan
murmushi.
A harabar kotun suka samu doctor Amina ma ta iso ita da maaikatan da suka gudanar da aykin.
Karasawa gunta Safna tayi suka gaisa,inda doctor Amina tace"Safna kinga kaddara ko?"
Hawaye ne suka gangaro daga idon Safna masu zafi sannan tace"doctor ina cikin tashin
hankali"
Karasowar Rayhan gurin ne ya katse musu hirar,inda ya dakawa Safna tsawa da cewa "wuce
mutafi".ba musu tabishi abaya suka shiga cikin kotun.
Bayan kowa ya hallara ne me gabatar da kara yatashi ya gabatar da karar da Rayhan Hashim
ya shigar agabanta,yana me kalubalantar doctor Amina,da sauya kwayoyin halittarsa Dana
wani ta sawa matarsa,Wanda hakan ya janyo matarsa ta dauki ciki,yana me rokon kotu datasa
matarsa ta zubar da cikin,kuma yanaso kotu me adalci da ta bi masa hakkinsa.
Bayan an gabatar da kara ne alkali ya bukaci ganin doctor Amina,jiki asanyaye ta karasa inda
aka tanada domun tsayuwar Wanda ake tuhuma taje ta tsaya.
"Munaso ki gabatar mana da kanki"cewar alkali,
"Sunana Amina Galadima,likita,kuma mamallakiyar Asibitin Galadima special hospital"
"Kinji korafin da aka shigar akanki shin haka akayi koko kina da ja game da hakan?"alkali
yasake jefo mata tambayar.
"Duk abinda aka fadi ranka ya Dade haka ne,sede ba nice da kaina na gudanar da aykinba,
kuma kuskuren suna aka samu ta hanyar kamanceceniyar suna,ina me rokon kotu datai mana
sassauci".ta kwashe komai ta sanar da kotu gamida mika takaddu na bincike da kuma duk wani
Abu daya shafi dashen tun kan ayi har zuwa bayan anyi,
Alkali ya bukaci maaikatan da suka gudanar da aykin dasu gabato gabansa,suma suka amsa
sune suka yi,
Bayan dogon rubutu alkali yafara magana,"Bayan nazari da bincike,wainda ake tuhuma basu
wahalar da sharia ba kotu ta gamsu da duk bayanan kowanne bangare,kuskurene babba suka
aykata,Wanda dole ay musu hukunci,Na farko,kotu ta yankewa doctor Amina hukuncin biyan
Tara ta dubu Dari,bisa laifin daukar maaikatan da suke sakaci da aykinsu,su kuma wainda suka
aykata laifin,kotu na umartar da akaisu gidan gyaran hali na tsawon wata guda,ko zabin Tara,ta
dubu goma goma"kotunce ta hargitse da surutu,kamin alkali ya tsawatar akai shuru, sannan
yaci gaba
"Kotu na kira ga Rayhan da yayi hakuri bisa faruwar wannan Lamari,sabida kotu bazata sa
Safna ta zubar da cikiba, Wanda aykata hakan zunubine,kuma shi wannan Abu daya faru,shima
kuskuren ne babba, duba da tabbaci da aka samu daga bakunan maaikatan na cewa cikin an
sameshi bada kwayoyin halittarka ba,kuma kamin ayi an tabbatar da bata da ciki,bayan anyi
kuma baka kusanceta ba seda aka tabbatar da ta samu cikin,hakan ya tabbatar da cewa cikin
jikinta ba naka bane,Dan haka kotu ta sallami wannan karar"
Gaba daya kotun ta kaure da hayaniya,Safna kuka take kamar ranta ze fita, wannan kaddara
dame tai kama.
Haka ta mike tabi bayan Rayhan din daya fita afusace,
Sede kamin ta karaso tuni yaja motar sa yabar harabar gurin,Dan shi Sam ba haka yaso ba,so
yayi asa safna ta zubar da cikin, sannan adaure doctor Amina, amma gaba daya ba hakan
akayiba,
Hakanne yasa shi tunanin anya ma kuwa alkalin yasan aykinshi?
Muje zuwa
Surbajo for life.
11/14/21, 12:45 PM - MY MTN 2: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������
*Zahra Surbajo*
*Inna Ibrahim kime alkhairin Allah yakai miki, ina alfahari da haduwa dake arayuwata.*
*14*
Doctor Amina ce ta karaso inda take ta dafata, da sauri ta waiga taga waye,
Ganinta ne yasa ta rushe da kuka ta fada jikinta tana fadin,"doctor ki taimakeni banason rasa
aurena,Ina son mijina sosai"tayi shuru sakamakon kukan dayaci karfinta.
Jan ta zuwa mota doctor tayi sabida jamaa sun fara taruwa akansu,da gudu ta fice daga
harabar kotun.
Safna ko se aykin kuka take,har suka iso kofar gidan Rayhan din,bude mata kofa tayi ta
fito,sannan tace"gobe zan dawo in mijinki ya fita Dan musan yadda zaa bullowa da abun ki
kwantar da hankalin ki"
Jiki ba kwari ta tura kofar get din tashiga ita kuma doctor taja motarta ta bar gurin.
A harabar gidan tasameshi tsaye yana huci,kamar wani maciji,bata bi takanshi ba tayi hanyar
shiga ciki,wata tsawa ya daka mata sai da cikinta yayi juyi ta waigo a firgice,.
Tsayawa tayi cak a inda take,har ya karaso,cikin fushi yake magana "Safna koda wasa ban
dauka zaki ketare maganata ba,nadauka son da kikemin na gaskene,shiyasa na baki umarnin
zubar da ciki amma kika ki,to ni bazan iya zama dake ina kwasar bakin ciki ba,Dan haka zan
baki zabi wallahi sede ki zaba ni ko cikin jikin ki?"ya wurga mata tambayar batare da shayin
komai ba,
Cikin kuka Safna ta tsuguna agabanshi tafara bashi hakuri"don Allah Rayhan kayi hakuri, kasan
ina sonka, wlh nafi sonka akan cikin jikina,fushin Allah ne kawai banason na fada,sakamakon
zubar da cikin,don Allah ka fahimceni"ta karasa maganar cikin kuka.
"Zabi na baki malama ni ko cikin jikin ki?"yafadi batare daya tausaya mata ba.
Rokonshi take da duk iyawarta kan yayi hakuri amma fafur ya kafe,ganin bata da mafitane yasa
ta mike tsaye ta share hawayen ta tace asanyaye "na zabi cikin jikina Rayhan"
Kallon mamaki yay mata sannan yace "to kije na sauwake miki aurena dake kanki,na sakeki
saki daya"ya yi saurin barin gurin sakamakon kukan dakeson kubce masa,yana son
matarsa,yayi iya yinsa Dan yaso abinda ke cikinta amma yakasa,shiyasa ya sake ta gudun kar
zuciya takai shi halaka.
Safna ji tayi duniyar tai mata nauyi,rasa abun yi tayi kawai seta kife agurin tana kuka,ta jima
tana kukan kamin ta rarrashi kanta ta mike,ta shiga cikin gidan,dakinta ta shiga,ta hada kayanta
na sawa se Jakarta ta hannu,
Ta janyo akwatin ta fice,daga falon tana kuka.
Shima dake tsaye ta window yana kallonta kukan yake kamar yabita,sede hakan da yayi shine
masalaha agareshi.
Tana fita, taxi ta dauka drop zuwa jabi park, tana isa motar Daura ta hau,fasinga daya dama
suke jira Dan haka direba yaja motar suka nausa kan titi.
Muje zuwa
Surbajo for life
11/14/21, 12:46 PM - MY MTN 2: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������
*Zahra Surbajo*
*Page 15*
Da laasar ta sauka a kofar gidan su,sede dandazon mutanen da ta gani ne a kofar gidan ya
daure mata kai,tana kokarin Neman hanyar da zata sada ta ne da cikin gidan taci karo da
mutane na fitowa daga gidan dauke da makara da gawa aciki.
Da sauri taja baya, tana binsu da ido,kanin babansu ne karshen fitowa,suna hada ido yace
"Safina ya muka ji da hakuri,sabuwa kuma sai yayi,Allah yajikanta"
Safna daskarewa tayi a tsaye tanajin maganar kamar a mafarki,innarta ta rasu,.batasan sanda
ta yanke jiki ta fadi agurin sumammiya ba.
Matan dake cikin gidan ne suka hango faduwarta,da sauri sukazo suka dauketa zuwa dakin
mahaifiyarta, aka shiga yafa mata ruwa ana mata fifita,ta jima kamin ta farfado.
Wani kuka tasaki me tsuma zuciya, wannan wacce irin rayuwace,miji ya korota asanda take
tsaka da bukatarsa,mahaifiyarta ta rasu a lokacin data iso gareta domin Neman mafaka.
Rarrashinta makwabtansu ketayi,dan su kishiyoyin mahaifiyarta ko ajikinsu sabgar gabansu
kawai sukeyi.
To haka rayuwa taci gaba da garawa,har Safna ta dauki danganar mutuwar mahaifiyarta,
Matan babanta ne suka sata agaba da tambaya me yasa mijinta bezoba ita kuma bata koma ba
shine ta shaida musu komai bata boye ba,
Ayko kan kace kwabo garin ya dauka Safna cikin shege tayi agidan mijinta ya korota,duk inda
tabi zunde da munafuncinta akeyi.
Ta rasa ina zata sa ranta taji dadi, maimuna kawarta ce kawai ke tausarta,kasancewar
katangarsu daya da gidan da tai Aure.
Rayuwa tayiwa Safna tsada,ga matan babanta ba me bata abinci se ta wahalta masa shima
bame yawa ba zaa bata.
Maimuna ke ayko mata wani lokacin.
Tsawon watanni bakwai kenan da mutuwar Aurenta,Wanda tuni cikinta watan haihuwarsa ya
kama.
Kullum cikin fargaba take amma ta fawwala Allah,Dan ba me taimaka mata,se shi din.
Cikin dare yau ta tashi da ciwon nakuda,tayi kukan ta kira sunayen matan gidan Kansu zo su
taimaketa amma ina ba Wanda yabi takanta,
Cikin hukuncin Allah ta haifo danta santalele ita kadai adaki,gefe ta koma tana kallon shi
kwance akasa cikin jini yana ta rusa kuka,yana cilla kafa,
Ahankali ta matsa kusa da akwatin kayanta ta bude ta dauko zani,ta dauki jinjirin da mahaifar
duka tasaka aciki ta nannadeshi sabida rawar sanyin da yakeyi.
Jin dumin da yayi ne yasa ya dena kukan,ya koma yayi lub,jin shurun tayi yawane yasa Safna
saurin bude masa fuska,ta haska da fitila,ido cikin ido suka hada ita da jinjirin Nata, ko a wasa
bata taba ganin jinjiri me kyau irin nashi ba,hasalima tafi ganin irinshi a kasashen ketare.karewa
Dan kallo take sonshi na shiga zuciyarta,tana tunanin waye ubansa,
Mikewa tayi dakyar taja wani zanin ta daura,sannan ta bude kofar ta fice rungume da danta.
Gidan su maimuna ta nufa,batare da tsoron komai ba,taita bugawa,har mijin maimuna yaji yazo
ya bude mata ta shiga,
Tana shiga maimuna ta fito Dan taji muryarta,tana tambayar ta lafiya.
"Maimuna haihuwa nayi kuma baa yanke cibiya ba,su inna kuma sunki taimakamin"cewar Safna
a sanyaye.
Da sauri maimuna ta amshi jinjirin daga hannunta ta kamata suka shige daki.
Reza ta dauko sabuwa da zare, ta yanke jibiyar,sannan, ta kwantar da Dan koda ta fito tsakar
gida tuni mijinta yajima da hada wuta ya Dora ruwan wanka,tunda yaji duk hirar tasu.
Kamin asuba tuni maimuna ta kimtsa Safna da jinjirin ta,cikin kayan sanyin danta datake goyo.
Ita kuma ta bata kayanta tasaka.
Dumamen tuwo ta bata me zafi,tasa mata manshanu ta bata taci ta koshi.
Allah sarki bingirewa tayi agurin tana baccin gajiya.
Maimuna jinjirin tasa agaba take kallo,tana tasbihi ga Allah sabida irin kyau da kyautata surarsa
dayayi Wanda ko a mafarki bata taba ganin halitta me kyansa ba.
Muje zuwa
Surbajo for life.
11/14/21, 12:46 PM - MY MTN 2: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������
*Zahra Surbajo*
*Kwana biyu bani da