Showing 1 words to 3000 words out of 153326 words

Chapter 1 - Ba Kowanne So Bane Book Compelet By Ouummey

Ummey   

22 Jul 2026

751

 Ouummey 001 [ 6/12/2024 1:42 PM ]

BA KOWANE SO BANE...
(yake zama samu)
✍️ Ouummey
Free book!!!


page 1️⃣

_____________________Da ƙarfi aka buga ƙofar ɗakin tare da shigowa, a dan firgice na dago
kai na daga sunkuyar da shi ɗin da nayi, sedai Kafin nayi wani yunkuri tuni naji an rufe ni da
duka

"A'a a'a, kai Safiyya, me yasa bakya jin magana ne".

Fadin yaya tana kokarin hana  Mama dake amsa sunan Safiyya dukana.

"Ki bar ni yaya, ki bar ni in sabauta yarinyar nan ko zan ji sanyi a raina, wannan wace irin
ƙaddara ce, ka haifi da a cikin ka ya zame maka musiba, wallahi ina nadamar haihuwar yarinyar
nan, da na sani da tun a ciki na zubar da ita na huta da bakin ciki".

Yayah  ta janye Mama tana fita da ita daga ɗakin

"Ki dena fadin irin wannan mugayen kalaman kan yar da kika haifa da cikin ki dan kin san bakin
uwa, ki kuma yi hakuri ki daina wannan kukan dan ba abinda ze kara face musiba ga rayuwar ta
yau ace mahaifiyar ta na zubda hawaye akan ta".

"Banni Yayah, banni nayi kuka, tun fara girman NU'AIMAH take kunsa min takaici kala kala, ban
da bakin ciki babu abinda na amfana da shi a rayuwar yarinyar nan, wace irin soyayya ce ban
nuna mata ba, wane irin kauna ne ban gwada mata ba, a duk cikin ya'yan da na haifa wa na so
na kauna kamar ta, wa nai wa gatan da nayi wa AIMAH?, amma kaf cikin su ita ce kadai me
bakan ta min rai, ki fa duba irin tashin hankali da gwagwarmayar da ta saka ni shekara biyar
zuwa uku baya, shine kuma duk be ishe ta ba se ta sake wani yanzu? Kashe ni take son yi ko
me, wai Allah ni Safiyya na shiga uku".

Ta kai karshe tana sake rushewa da kuka,

"Koma dai ya faru a baya fa har da laifin ki Safiyya, ko da laifin AIMAH amma zan iya cewa
naku ya fi yawa dan kuka bata dama ku ka sakar mata kuka kuma sangarta ta shiyasa ta taso a
haka, se kuma daga baya kuce zaku gyara ta, bayan shi ice tun yana danye ake tankwara shi,
in kuwa ya girma aka ce za'a tankwara sedai ya balle".

Ajiyar zuciya Yayah tayi tare da riko hannun Mama

"Kiyi hakuri da yanayin ƙaddarar ta Safiyyah, ki kuma koyi yin kyakkyawan kalami a kan ta, ina ji
a jikina komai yazo karshe a wannan lokacin Insha Allah".

Zare hannun ta tayi daga na Yayahn

"Na dade da zare Aimah daga cikin addu'a ta dan ba lafiyar ƙwaƙwalwa ce bata da ita ba balle
ace ai bata san daidai ba, haka kuma ba aljanu gare ta balle ace she's possessed, kawai tsabar
iskanci da jin ita ta tsaga ne dan haka na bar bata lokaci na wajen mata addu'a tunda Allah ai ya
azurta ni da wasu ya'yan bayan ita, taje tayi rayuwar ta duk yadda taga zata iya sedai ɓacin ran
da take sani da damuwa da sannu itama zata haifa kuma zata gani, Abu daya na sani shine
wallahi se na raba wannan kaddararren auren tsakanin ta da MASDOOQ, dan shi ɗin ya fi
karfin ta, ba sa'an auren ta bane dan haka se ya sake ta taje ta naimo daidai ita".

"Ashe baki da hankali Safiyya, auren da aka ɗaura ɗazu ɗazu kike maganar rabawa?".

"Shi dai Yayah, ashe ma in na bar auren taci riba kenan, bayan duk abinda tayi a baya kina
tunanin ta dace da samun irin wannan damar ne?, Sam wallahi dan haka kar ki ma fara ce min
in dakata Yayah dan a wannan karon ba zan ji ki ba".

"Nima kuma ba zan saurari haukan ki ba dan haka auren Aimah da Masdooq ban ga wanda ze
raba shi ba ko da kuwa shi ɗin da kan shi ne".

A mamakan ce Safiyya ta kalli yayar tata

"Kar ki yi haka Yayah, kar ki fara fadar haka, kar ki sa zuciya ta ta fara saka min tunanin dan
Masdooq yana dan ki ne yasa kika fadi haka Yayah".

"In har haka zuciyar ta ki ta saka miki to ki dauke shi as hakan, dan na gama magana, Aimah ta
zama matar Masdooq and ba zan yadda da duk wani matsala da zata shigo tsakani ba".

Yayah na fadar haka ta tashi ta fita daga ɗakin leaving Safiyya wadda ake kira da MAMA na
rushewa da kukan karin takaicin kalaman dake fitowa daga bakin yayar ta ta da bata da wadda
ta fita, wadda take ganin ko kowa yaki goyan bayan ta ita zata yi sedai gashi tun kan aje ko ina
ita ta fara kwaye mata baya, sedai wallahi baza ta bari ba, aure ne se ta raba shi sedai duk
abinda ze faru ya faru, ai itama NU'AIMAH yar ta ce, itace ta haifi abar ta dan haka zata yi iko
da ita.

*********

A can ɗakin kuwa ni Aimah ce zaune na hade kai da gwiwa cikin wani irin tashin hankali , a
kallon farko me kallo na ze shaida n din amarya ce dan kuwa kayan jiki na masu matukar kyau

da tsada dake ta daukar ido sun fallasa hakan, ban da kuma tsararren kunshin dake kan
kyakkyawar fair chocolate skin dina.

Shigowar da naji anyi dakin yasa na ɗago a firgice dan nayi tunanin Ummi ce ta dawo, a boye
na sauke ajiyar zuciya tare da lumshe idanuna da suka yi jajajaja na tashin hankalin da nake
ciki.

"Aunty Aimah an daura auren tun dazu, guess what, da yayanmu aka daura fa, bari kiji
recording din da Walid ya turo min".

Bata tsaya kallo na ba balle ta kalli reaction di na ta shiga danna wayar hannun ta cikin rawar
jikin farin ciki, recording din ta kunna tare da matsowa dab da ni

"An daura auren NU'AIMAH BASHIR da angon ta MASDOOQ MUHAMMAD kan sadaki dubu
ɗari biyar lakadan ba ajalan ba".

Kalaman suka shiga kutsawa cikin kunnuwa na tare da kurdawa cikin kwakwalwa ta suna ratsa
dukkan wata jijiya ta jikin na, a sannu na fara jin wani irin sanyi na ratsa gabban jiki na, jijiyoyi
na na sakewa haka kuma wani yanayi na ratsa zuciya ta.

Ban san lokacin da ba dauka a haka ba se buɗe ido nayi naga babu sumaiyya, cousin di ta ta
bangaren baban mu da ta kawo min labarin.

Sake maida idanuna nayi na kulle cikin zurfin tunani, gaba daya kwakwalwa ta ta cushe, tunani
na ya gushe kamar yadda lissafi na ya ba ce, se yanzu na gane dalilin dukan da Mama ta rufe
ni dashi dazu, se yanzu na gano kukan da Mama ke yi dazu.

Mahaifiya ta ce da zan iya dafa Kur'ani na rantse cewa ita ta dauki ciki na tsawon watanni tara,
tayi nakuda ta ta haife ni, ta kuma raine ni cikin tsananin soyayya da gata amma tashi daya
yanzu bata da makiyya kama ta, ta tsane ni kamar ta manta ita ta haife ni, ban taɓa ganin tsana
daga wajen wani mahaluki ba kamar wadda Mama ke gwada min yanzu.
Na sani na cancanci hakan, na kuma kama ci hakan daga kowa amma ban da Mama da duk
wani ahalin gidan nan domin kuwa ko me na zama yanzu SU NE SANADI, ko me nayi a baya
SU NE SUKA JA MIN, amma kuma yanzu se suce zasu juya min baya?.

Yayye na daidai har biyar duka maza, acikin su ba wanda be gwada min kauna da gata mara
algus ba, amma yanzu ba wadda suka tsani su buda ido su gani kamar ni, shin laifi na har ya
kai su min haka? Ko kuwa dama ba su taba kauna ta bane, ko kuwa.......!.

Tunanina ya katse sanadin bude kofar da aka kuma yi, wannan karan ban iya nako ɗago kai ba
balle na kalli me shigowar dan zuciya ta tayi wani irin rauni, tarin damuwoyin da nake dannewa
wata da watanni sune suka bijiro min tare da rauna ta duk wani kuzari na.

Daga bakin kofar itama ta tsaya cikin hade rai dan karfin hali ne kawai take yi dan hakan ne ya
kamata,

"Ki tashi ki yafa mayafin ki muje na kai ki gidan mijin ki".

Bam san a ina na samo karfin da na ɗago a zabure ba jin kalaman Hajiya Yayah kamar yadda
mu yara ke kiran ta

"Eh haka nace, ba dai mamaki kike ba ko, ke da me kike zato, a tara mutane a tafi kai ki gidan
aure kwana kadan ki ɓallo ki dawo da abin kunyar da ze sake barar mana da dan ragowar
mutuncin da ya rage mana? To in haka kike tunanin maza ki aje shi gefe ki mike, kafin kuwa
Uwar ki ta zo nan dan ban da na janye ta a kan ki kin san se ta kusa kashe ki, ja'ira mara jin
magana".

Cikin wani irin kunar zuciya na mike dan kuwa kalaman Hajiya Yayah gare ni jin su nayi kamar
rushin wuta a rai na, amma kuma ai kome suka fada ni na jawa kai na, komai aka ce a kai na na
cancanta ne, da na kasance yarinya ta gari da duk ba za'a fada min ba, da naji maganar iyaye
na a lokacin da suke fada min da duk komai be faru ba, da tuni na ina cigaba da rayuwa da
kaunar ahali na gare ni, amma a lokacin se na kasa yi musu biyayya, na kasa duban darajar su,
na zabi farin ciki na saman na su, na zabi saɓa musu dan wani cikar buri na da Allah ya jarabce
ni da shi, dan haka dole nayi hakuri na shanye koma me za'a ce ko za'a yi mon, watarana se
labari.

A hankali nake takawa zuwa wajen motar Hajiya Yayah da take Parke a compound din gidan,
duk inda na wuce haka jama'a ke bi na da kallo suna kus kus abinka da gidan biki.

Har wata ajiyar zuciya ce ta kwace min lokacin da na zauna a seat din gaba da Hajiya Yayah ta
buɗe mim dan idanun jama'a da suka min yawa kamar sa kada ni.

Tada mota Hajiya Yayah tayi tare da ficewa daga gidan bayan me gadi ya buɗe mata gate, wani
irin yanayi na rashin jin dadi ya darsu a zuciya ta ni Aimah, gidan aure ne fa na tafi batare da sa
albarkar iyaye na ba, se ma tarin bakin ciki da ɓacin rai tare da fushi me tsanani da mahaifiya ta
ke yi da ni, anya kuwa zan ga daidai a rayuwa ta?, Anya zan ga alkhairi a gidan aure na, anya
kuwa aminci, salama tare da kwanciyar hankali zasu ziyarci rayuwa ta?!.

Bana tunanin hakan, dan ko ba wannan situation din daga iyaye na shi mijin fa?, Shine dai
Masdooq da na ki shekarun baya, shine dai Masdooq da ma guda a baya, shine dai na zaga,
na wulakanta na kuma guda a baya, anya ze yafe min kuwa?, Anya ze dube ni da idanun
rahma balle har ya karbe ni a matar aure?, Anya ze iya sake dubana kuwa?, To in ma ya dube
nin shin ni da wane idon zan daga ta kalle shi?, Lallai akwai sauran rina a kaba.

Kallo na Hajiya Yayah tayi ganin yadda na rakube kan seat kamar wata marainiya, kallo daya

za'a min a ga tashin hankali da damuwar dake shimfide kan kyakkyawar fuska ta wadda a baya
walwala da farin ciki ne mamaye da wannan fuskar.

Mai da kan ta tayi kan titi tare da cigaba da tukin ta,

"Duk wanda yace ze yi wa rayuwa garaje tabbas yana tare da nadama da dana sani. A baya ke
din halitta ce mafi soyuwa gamu iyayen ki, yan uwan ki har ma da abokan arzika, a cikin ya'ya
ba kowane ya samu gatan da kika samu ba, ba kowane ya samu soyayya da kaunar da aka
gwada miki ba, amma duk kika sa hannu kika tankwabar da wannan, kika sa kafa kika shure,
kika zabi namiji kan mu, kika fifita damuwar ki kan mutuncin iyayen ki, kika daukaki san zuciyar
ki kan umarnin ubangiji, taya ya?, Nace taya ya zaki ga daidai Aimah?.

Su iyaye daraja ne da su, iya haifar ki kawai da aka yi an gama da ke ko da kuwa ace ba ayi
kowace wahala dake ba bayan haka, amma ke se kika nuna naki iyayen ba wasu bane, banza
ma tafi su daraja a wajen ki, Manzon Allah ya jaddada mana darajar iyaye gare mu musamman
kuma uwa mace da seda ya ambace ta matsayin wacce za'a a kyautatawa har so uku kafin ya
ambaci mahaifi, Aimah ka bauta wa Allah ka kiyaye dokokin sa ka bi uwa ka bi uba a wannan
duniyar ya ake karewa balle ke da kika zabi tozarta su madadin biyayya?.

Hmmm, bana miki baki, bana kuma yi miki fatan wahala amma kina da sauran aiki a gaban ki,
kin ga wannan auren kan sa gare ki sabon kalubale ne, haka kuma dalilin da yasa zan tsaya kai
da fata wajen ganin ba'a kashe shi ba shine dan ki samu experience na rayuwa, dan ki kara
hankali a rayuwa, dan kuma ki fahimci ba koyaushe kake rasa abu ka kuma samun damar sake
mallakar sa ba, haka ko ka samu damar akwai tarin kalubale, Masdooq da kika sani a baya
bana tunanin shi zaki tadda a yanzu, haka kuma rayuwar sa ba irin ta baya bace dan kuwa
yanzu shi ɗin magidanci ne me mata da ƴa daya, wani karin kalubalen gare ki kenan wato matar
sa.

Na sani, kin sani, kowa ya shaida SA'ADAH ba fitinanniya bace, yarinyar kirki ce me hakuri da
biyayya, wannan halayen su suka siya mata soyayya wajen mijin ta kuma mijin ki a yanzu, dan
haka bana tunanin samun gurbi a wajen shi gare ki yanzu abu ne me sauki domin ya saba da
bari na bari, yi nayi da dukkan nau'i na biyayya da girmamawa, kar kiga a baya yayi tolerating
tsayayyar ki yanzu ma kiyi tsammanin haka ne, sam sam dan haka se ki shirya tunkarar
sabuwar jarabawar ki.

Abu daya nake so ki sani, shi hakuri magani ne na dukkan kowace matsala, addu'a makami ce
na yakar kowace damuwa, kamar yadda ba zan iya bayyana miki tasirin biyayya ba, dole kuma
se kin koyi kau da kai.

Sedai fa kar in ji kuma kar in gani, na san SA'ADAH kamar yadda na san ki, duk naji fitina da
wata matsala na san daga gare ki ne, ba kuma ina fadin hakan dan wai Na tsane ki ko na fi son
ta ba, a'a sedan dukkan ku na san ku, haka kuma kauna ce tasa nake miki wannan karatun.

Eh ina jin haushin ki me girma Aimah, amma iyaye basu taba kin dan su ba sedai kokarin yi
masa gyara, in kika dage kika jure da sannu komai ze wuce rayuwar ki ta dawo kamar da ke har
ma ta iya fin da wajen daidaito, farin ciki da kuma kwanciyar hankali".

Hajiya Yayah na rufe bakin ta ta shiga yin horn gaban madaidaicin gate din gidan, haka kuma
na kwashe komai a kai na na daga nasihar ta ina yi wa kowace kalma fashin baki da har ban
san mun shiga compound din ba.

"Fito ko".

Ɗagowa nayi na kalli Hajiya Yayah da fuskar ta take nan ba yabo ba fallasa kana na fito da kyar
kamar wadda bata da laka a jiki, ko kafin na karasa fitowa tuni Hajiya yaya tayi gaba abinta.

Da sallama na shiga cikin falon a rai na kai na na sarawa, rayuwa ta ta baya a gidan na dawo
min daki daki

"Wai wane irin shashanci ne wannan ina miki magana kina ji na, ko kin fara kurman cewa ne
ban sani ba".

Da sauri nayi gaba jin fadan Hajiya Yayahn da ta ja tsaki tana min pointing wani daki

"Gashi nan ki shiga nan ki zauna kafin ya zo ya san yadda ze yi dake wajen gurin zama, in
kuma duk a nan din zaku zauna se kuyi magana, me gidan bata nan dan haka ni ba ni da abin
yanke wa, dakin baki ne kuma ciki da falo ne".

Ta faɗa bayan mun shiga cikin falon da me aiki ta buɗe mana, ba musu murya can ƙasa kamar
ba Aimah ba nace

"Angode Allah ya saka da alkhairi".

Batare da ta amsa mim ba ta juya ta fita dan sauri take taje ta sami SA'ADAH ta taushe ta sanin
sam ba'a kyauta mata ba, sedai ya zata yi WATA KUSAN TAFI WATA.................✍️.






Assalamu alaikum jama'a, barkan mu dai, fatan duk muna lafiya, kamar yadda Allah ya tsara
gamu mun sake hadewa cikin wata sabuwar tafiyar da ku, fatan zamu ilmantu, mu nishadantu
mu kuma wa'azantu, kuma ku kwantar da hankalin ku, BA KOWANE SO BANE..free book ne
domin jin dadin masoya na.

Fatan kawai ku faranta min ta hanyar sambado like, Comment tare da taya ni sharing, yawan
comments din ku ne ze yi determining wether to proceed or to stop!!!.

Ga masu neman litattafai na na baya, su tuntubi wannan number 👇
09013101854, heart you all ❤️.

Ouummey 📚✍️.





Ouummey 002 [ 6/13/2024 8:59 PM ]

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0