Showing 1 words to 3000 words out of 3054 words

Chapter 1 - Bakar Sarauta Compelet By Maman Sharifa

30 Jul 2026

30

BAƘAR SARAUTA
Complete Book 1
Page 1

By
Nana Deejah ce (mrs sharif)

Ban yarda a juya mn lttfi ba

JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI

مسب الله نمحرلا ميحرلا

Birnin Bahar usuƙ birni ne da ya yayi shura a arewacin kasar sin, birnin ya shahara da manyan
mayaƙa sadaukai masu kifar da gari guda a lokaci daya, sannan birnin ya shahara ta ɓangaren
manyan bokaye masana ilimin sihirin tsafi.

manyan sadaukan sarakuna sun mulki birnin Bahar usuƙ na tsahon shekaru masu yawa,
saidai dukan su suna rasa rayukan su ne a hanyar cimma wani buri nasu guda ɗaya wanda ya
gagari
kowannen su cikawa,

ganin yadda manyan
sarakunan dake mulkin nahiyar ke rasa rayukan su yasa sarakunan baya hakuri da wannan
buri .


Sarki Urwat bin Shamraz shine sarki na ashirin da biyar cikin sarakunan birnin Bahar usuƙ.

Sarki Urwat ya kasance basamuden sarki ne gabjeje mai matsanancin ƙarfin damtse tare da
sani akan sihirin tsafi, sarki Urwat ya gagari manya manyan sarautun dake gefe da fefen
nahiyar sakamakon tara manyan sadauki dangin mutane da aljanu da dabbobi.

birnin Bahar usuƙ ya samu babbar kariya ta yadda koda dan tsako bashida ikon shigowa cikin
birnin ba tare da izinin sarki Urwat ba, ƙasashe da dama sun kawo hari birnin Bahar usuƙ amma
koda mutum ƙaya baya samun damar barin birnin da ƙafarsa.

angina manyan katangun birnin da jinin manyan mayakan da suka kawo hari suka rasa
rayukan su.

Dan madaidaicin ɗaki ne wanda aka ƙawata shi da zallar jauhari babu komai cikin sa kujeru
guda uku ta tsakiya itace babba wacce aka sana'anta ta da ɗanyan dinare sai guda biyun dake
gefe da fefen wanda basu kaita girma ba.

A kan kujerar tsakiya sarki Urwat ne sanye da ƴar shara fuskar sa a buɗe kansa babu rawani
fuskar sa cike da kwariji yayin da damatsan hannun sa ke a murɗe kallo ɗaya zakayi masa
kaga zallar jarumta da sadaukantaka irin na manyan sarakai.

gefe da gefen sa wasu matasa ne masu tsananin kama da juna .

A gaban kujerun wani
yamutsatstsen tsoho ne ma'abocin farin gashi mai tsaho wanda ya haɗe da dogon gemun sa,
kansa a ƙasa ya fara jawabi kmar haka.

""Ya shugaba kayi sani cewa wannan tsohon burin tin daga kakan ka na biyar aka ajiye shi
domin kuwa daga shekara dubu uku da dari uku da sittin zuwa lokacin da aka ajiye burin babu
wanda ya taɓa tinkarar cikar wannan buri ya dawo a raye.

Kafin tsohon ya rufe baki sarki Urwat ya daka masa wata gigitacciyar tsawa wacce tasa tsohon
hantsilawa ya dago daƙyar jikin sa na rawa ya ce "" ka gafarceni ya shugaba na wannan buri
bakomai bane face mulkin birnin kangiwa, wanda kaf nahiyoyin mu babu wata ƙasa data kaita
arziki da kuma iko, kujerar wannan birni ba kmar kowacce kujera bace, ya shugaba na kabarin
sarkin aljanu ne da sarkin bokayen duniya tareda sarakan yaki guda goma shabiyu aka gina shi
sannan aka sana'an ta karagar akan su, ya shugaba dalilin burin mallakar wannan birni shine
duk sarkin daya mallaki wannan birni to tabbas duk wasu burane dake cikin wannan duniyar
zasu kasance a ƙarƙashin ikon sa sai abnda yaso za'a zartar.

Yanzu haka shekara dubu biyu kenan ba'a ƙara samun wani sarki ko sarauniya ko wani
hamshaƙin aljani ko babban bokan da ya sake hawa karagar Birnin kagiwa ba.

Bakomai yasa hakan ba kuwa face sarkin daya mallaki wanna birni na ƙarshe wani sadaukin
aljani ne wato sarki Darbuza, wanda ya mallaki mutane aljanu da manyan dabbobi ya shahara a
faɗin duniya yayi ƙarfin da koda tsuntsu sai yaso zai samu abinda zaici.

A lokacin sa ne duk wani boka da wani isashshen aljani saida ya kashe su ya maida sihirin
tsafin kan wani kwalkwali na baar azurfa wanda yake kasancewa akan sa koda a yaushe.
Lokacin da sarki Darbuza ya tabbtar wa kansa cewa rayuwar sa ta kusa ƙarewa sai ya shirya
dakaru suka ƙauki hanyar kogon Maɗaful Azab, shidai kogon Maɗaful Azab kogo ne da ta tara
manyan dabbobi da aljanu, birnin yana nesa da nahiyar mu tsafiyar tsawon wata uku a
ingarman doki wata shida a ƙananun dawakai, kasancewar sarki Darbuza sarkin aljanu da
mutane yasa sadaukan aljanu suka kaishi cikin kwana uku,

Koda sarki Darbuza ya tsinci kansa a gaban kogon Maɗaful Azab sai ya ciro kwalkwalin dake
kansa ya yanka wuyan sa da shi jinin jikin sa yayi tsartuwa ya jiƙa kwalkwalin, take jikin sa ya

fara karkarwa ransa na shirin bari jikin sa, cike baƙin zafin nama ya jefa wannan kwalkwalin
cikin kogon Maɗaful Azab, daga nan jikin sa ya sandare babu alamar rai a tare da shi, tin daga
wannan lokaci birnin kangiwa ya kasance babu mahaluƙin da ya sake mulkar sa, badon komai
ba sai don babu wanda zai iya zama akan karagar face ya je kogon Maɗaful Azab ya ɗakko
kwalkwalin sarki Darbuza ya dora akan sa, kamar yadda na faɗa maka ya shugaba na tafiyar
wata uku ce a ingarman doki sannan tafiya ce wacce a tarihi babu wasu hanyoyi da suke cike
da azabu masifu da tashin hankali kmar wannan hanyar, sannan ya shugaba na tin daga
wannan lokacin babu wani aljani dake iya tashi sama yabi hanyar saidai ya tafi da kafa ko akan
dabba kaga kenan babu damar aljanu su rage tafiyar.


Sa'adda tsohon yazo nan a zancen sa sai yaja baki yayi shiru kansa a ƙasa .


Tsananin baƙin ciki da ɓacin rai ne ya ziyar ci sarki Urwat sa'adda ya gama jin labari birnin
kangiwa nan take fuskar sa tayi ja iduwan sa suka furfuto kumatukan sa suka fara rawa har
wani ɗaci ɗaci yake ji a bakin sa, ba tare da yace komai ba ya miƙe a fusace ya fice daga ɗakin,
yayin da matasan dake tare da shi suka rufa masa baya.
COMMENT AND SHARE PLX


BAKAR SARAUTA


P 2

NANA DEEJAH CE

JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI ALKAIRI


مسب الله نمحرلا ميحرلا
Cikin wani dan loko sarki Urwat ya nufa ya shigo cikin wani katafaren parlor mai girman gaske,
wanda aka kawata shi da jeren silbobi a kusurwa hudun dake parlorn.
an zagaye shi da labulaye jajaye masu ratsin golden, hagu da dama na cikin parlon an jera
kujeru masu zaman mutun daya, ko wane bangare guda goma sha biyu ne.

daga tsakiya dogon lallausan kilishi ne ja, a saman sa katon taburi ne na glashi wanda aka
cikashi da kayan marmari tareda tambulan na lemuka kala kala.


Daga karshen dakin wata hadaddiyar kujera ce ja wacce akayi mata ado da zallar gold.

hannun sa ya goya a bayan sa ya fara zagaye a cikin daki daidai tsakiyar dakin ya tsaya ya
bude tafin hannun sa ya kura masa Ido kamar mai nazarin wani abu yace "" na rantse da
girman kujerar birnin kangiwa saina mallaki birnin nan koda za'a rasa rayuwan da ba zasu kirgu
ba, koda dukkan nahiyar nan zata jike da jini, saina binne gawarwaki wajan gina katafariyar
masarauta ta.


Zaka iya ya kai baban mu muma mun yanke shawara akan yadda zaka mulki birnin kangiwa
cike izza ya juyo a nutse ya sauke idon sa akan kyawawan yaran sa guda biyu ya fadada
murmushin ba tare da yace komai ba

Daya daga cikin mai suna Rukkas ya dubi sarki Urwat yace yakai abban mu kayi sani cewa
zuciyoyin mu cike suke da takaicin tare da bakin cikin kasancewar mu anan bayan manyan
sadaukai sun shude wanda har yanzu tarihin sadaukantakar su bai gushe ba wanda suka amsa
sunan su maza ba mata ba nida dan uwa na Rakkus mun yanke shawara tafiya kogon Madaful
Azab domin neman kwalkwalin sarki Darbuza ya baban mu kayi sani cewa Koda bamu dawowa
zamu wanzu cikin tarihin jaruman da suka rasa rayukan su a hanyar kogon Madaful Azab
wanda ba kowanne jarumai ke ita tinkarar sa ba.

Koda jin wannan batu daga bakin Rakkas sai ran sarki Urwat ya cika da alfahari da farin ciki
bakin ciki dake zuciyar sa ya yaye kishin mazajen dake ransa ya kauce karfin zuciya da fatan
zama sarkin kangiwa ya kara mamaye zuciyar sa.


A hankali ya fara takowa gare su ya shiga tsakiyar su ya dafa kowannen su day hannun sa ya
ce "" yaku ababen alfahari ne hakika yau kun cika zuciya ta da farin cikin kun sawa zuciya ta
yakini dakuma yadda da irin jarumtar da baya na ke da shi na tabbata koda bayan raina mulki
na bazai gushe a wannan birnin ba saboda haka inason sanar daku cewa na shirya tsaf domin
tinkarar kogon Madaful Azab a sanar da sarkin yaki ya shirya mayaka nan da kwana uku zamu
kama hanya.



Lokacin da sakon sarki Urwat ya isa wa Ramwal kafafun sa ne suka fara rawa zuciyar sa ta
fara tsinkewa domin shi ya jima da sanin labarin kogon Madaful Azab nan take marar sa ta fara
kullewa fitsari ya fara jika masa wando, a tarihin sarkin yaki Ramwal bai taba girgiza don ganin
tawagar abokan gaba ba Koda kuwa jinsun aljanu ne a tarihin birnin Bahar usuk shine sarkin
yakin dake jagorantar tawagar mayakan aljanu zuwa kowane irin fafatawa shine sarkin yakin
dake dakawa aljanu gumba a hannu kaf mutane da aljanun dake zagaye da birnin Bahar usuk
suna tsoron gabza yaki da birnin ne saboda sarkin yaki Ramwal shine jarumin da yake saka
kansa gaba cikin mayaka saidai kaga kawuna suna zuba a kasa kamar ana sassabe a gona ba
tare da an samu wanda ke iya lakutar koda jikin sa ba zafin nama garshi tamkar wanda aka
cudanya naman sa da zaki duk sadaukantaka irin ta sarki Urwat bai kai sarkin yaki Ramwal ba
saidai ya fishi kwarijini da dabarun sarrafa makiyi.

Jiki a sanyaye sarkin yaki Ramwal ya koma gidan sa cikin zuciyar sa yana lissafa adadin
kwanakin da suka rage wa rayuwar sa idanun sa ne suka furfuto sukayi ja tamkar ruwan
hawaye zasu zuba daga gare su saidai wannan ba halin jaruma Ramwal bane .


Gaba data dakarun dake birnin Bahar usuk mutane da aljanu idan ka cire dabbobi wanda basu
san komai ba face kai hari hankalin kowa a tashe yake zuciyoyin mazaje sun raunana mataye
na kukan rabuwa da mazajen su domin kuwa suna da yakinin wannan ita ce ranar bankwaba.


Birnin yayi tsit bakajin sautin komai sai haniniyar dawakai da sautin tsintsaye tareda kukan
dabbobi yayin da jarumai na gida tare da iyalan su suna nasu kukan.





Gudu da haniniyar dawakai ke tashi cikin wani karamin daji dake nesa da birnin Bahar usuk
kura ta turnuke baka ganin koda gaban ka daga can wasu fararen dawakai guda biyu suka tawo
a sukwane da alama tsere suke yi daga saman kowane doki mutum daye ne sanye da riga da
wando na fatar damusa takalmin kafarsu ma haka fuskokin su a rufe baka ganun komai face
idanun bayan su rataye da kibiyoyi yayin da hannayen su ke dauke da kwari da baka wanda
suka saita wani zomo dashi daya daga ciki ne ya samu nasarar Harbin zomon yayin da zomon
ya tsaya can babu rai a jikin a hankali kuma dawakan suka rage gudu har suka karaso inda
zomon yake wanda ya harba ne yayi saurin sauka daga kan dokin ya dauki zomon yana
murmushi tare da kwance nadin dake kan su gaba daya kyawawan fuskoki ne suka bayyana
tare da kwantaccen gashi har kugu dole mutum yayi mamakin yammatan da suka iya sarrafa
dawakai kamar haka, gujr guje suka.farayi wacce tayi nasara tana yuwa yar uwar ta dariya suna
zagaye jejijn, sun dan jima suna gudun cike da shaawa kafin suka ajiye zomon suka karasa
wajan wata korama dake guda na a wajan tsugunawa sukayi suka daura alwala suka karasa
cikin wata karamar bukka suka fito da karamin kilishi suka shimfida tare da maida lullubin su
suka tada sallah.

*BAKAR SARAUTA*

P 3

NANA DEEJAH CE

JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI

مسب الله نمحرلا ميحرلا

Kashe gari mutanen birnin Bahar usuk sun cika makil a fada domin kuwa gobe ne ake saka ran
tafiya zuwa birnin Bahar usuk.

Fadar ta cika makil ba masaka tainke sai kawunan biladama.kake gani birjik tamkar taron
kiyasai, karan bugun tambura da busa sarewa da ke tasowa daga wani bangare dake cikin
fadar ya tabbatar wa mutanen isowar sarki Urwat, ha tare da bata lokaci ba manyan fadawan
sarki Urwat suka mike tare da baza manyan rigunan su , saida sarki Urwat ya zauna bisa
karaga tareda Rakkus da Rukkas sannan suka koma mazaunan su dattijan fada ne suka fara
tasowa daya bayan daya suna kai goshin su kasa suna gaisuwa ga sarki Urwat yayin da sarkin
ke daga kansa shi kuma zagi yana amsawa.

Bayan gama yan gaishe gaishe sarki Urwat ya dubi jamaar dake gaban sa yace "" yaku jamaar
birnin Bahar usuk kuyi sani cewa gobe itace ranar da zamu dauki hanyar kogon Madaful Azab a
bisa aladar masarautar Bahar usuk baa barin karaga babu sarki a dalilin haka ni Urwat na
yanke hukuncin barin waziri akan karaga ta dajin wannan batu daga bakin sarki Urwat sai
mutanen da zasu zauna a garin suka cika da murma da farin cikin domin kuwa sun san waziri
Larbus yafi sarki Urwat sauki da tausayin talakwa.

Suna cikin wannan farin ciki ne wata guguwa mai matukar yawa da kara tamkara zata rusa
garin ta taso saida tazo kofar fadar sannan ta rikide ta koma bakin hayaki wanda ya gigita gaba
daya jamaar dake fada.

Lokacin da hayakin yazo kusa da karagar sarki Urwat sai ya jiya ya koma dan karamin mutum
wanda ke zaune kan wani karamin buzu baya sama baya kasa ya dubi sarki Urwat fusk dauke
da murmushi yace yakai dirkar burnin Bahar usuk hakika ka cika jarumi abin alfaharin mutanen
birnin Bahar usuk saidai inaso ka sani cewa baka da damar zuwa kogon Madaful Azab domin
kuwa akan hanyar ka ta zuwa Madaful Azab akwai wata babbar alkarya mamallakiyar wannan
alkarya wata Sarauniyar mayu ce mai suna Zamratul Ukub ita dai wannan mayya ta kasance
gagarumar matsafiya hatsabibiya mara Imani tana da dakaru wanda yawan su ya kai dubu dari
biyar gaba dayan su mayu ne Basu da abinci face naman biladama kowanne daya daga cikin
su yana iya cinye mutum goma ba tare da ya koshi ba su dai wadannan mayu sun kasance
gabza gabza sannan kaifin takobi ko tsinin mashi baya tasiri a jikin su balle Kuma sihirin tsafi
domin kuwa idan har kayi kuskuren yin amfani da sihirin tsafi a gare su to fa ni kaina bansan irin
bakar azabar da zaka fada ba, Zamratul Ukub ba zata taba bari ka wuce ta garin taba har sai
kazo mata da abu guda daya wannan abun ba komai bane face jaririn aljanin dan ahalin aljanin
Taranzat sudai wannan aljanu sun kai su dubu biyar suna zaune ne cikin wani kauye wanda ake
kira Bazzar a kullum aljana daya na haihuwa a kauyen Bazzar itakuma jaririn da aka Haifa ranar
da ka Isa kauyen Bazzar shine abinda Zamratul Ukub take son yin kalaci da shi.

Su dai wadannan aljanu sun kasance ahali guda ne sannan suna iya sadaukar da rayuwar su
wajan ceton yayan su sannan suna da hadin kai matuka ba zaka samu damat daukar jariri daga
gare su ba har sai kayi yaki dasu kayi nasara .

Abu na gaba shine shidai wannan kauyen akwai gidaje gufa dari a cikin sa sannan a cikin gida
daya ne wannnan aljanu suke dole saika nemo gidan da suke kafin nan sai ka fafata da halittun
dake kowane gida saannan Mayya Zamratul Ukub zata bukaci jaririn ne kafin cikar kwana
bakwai idan ya wuce kwana bakwai jaririn yayi sanyi ba taso duk wahalar da kasa idan kaje ba
zata karaba ba sannan kune zaku zama abincin ta itada dakarun ta.

Saadda mutumin yazo nan a zanjen sa sai tsuke bakin sa kmar ba shine ke magana ba sannan
ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa a wajan ba.

Bacewar mutumin keda wuya sarki Urwat ya dubi jamaar dake gaban sa ya ga alamun tsoro
karara a tare da su duk da shima a tsoracen yake amma haka ya bude baki yace yaku dakarun
birnin Bahar usuk kuyi sani cewa a tarihin masarautar mu idan muka dada bama canzawa koda
zamu rasa rayukan mudon haka gobe idan rana ta fito zamu dauki hanyar kauyen Bazzar aje a
fara shiri yana fadar haka ya mike samarin sa na binsa a baya suka koma ta inda suka fito.


Tin da daddre aka shirya guziri aka Dora su akan dabbobi komai an shirya lokaci kawai ake
jira, kashe dari da sassafe tawaga ta hadu mutane da aljanu wadan da zaayi tafiya dasu suka
shurya babu jimawa sarki Urwat tareda yaransa suka suka fito amintaccen aljanun sarki Urwat
ya baza fuka fukan sa suka hau shida yaran sa ya tashi sama ya lula yayin da ragowar aljanun
suka sauki mutanen da sauran dabbobin aka nufi kauyen Bazzar.

Sun dauki kwana goma sha biyar suna tafiya idan dare yayi su sauka su yada zango su kwana
da safe su tashi sun hadu abubuwa kala kala kananun dabbobi sun kashe sunyi kalaci yau ne

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login