Showing 6001 words to 9000 words out of 23680 words
Chapter 3 - Bakin Shafi Complete Book Oum Yasmeen
Dada suka bada amanarta sannan suka kaita gidan ta gaba da su sosai..
sai satin gidan nata suka ahaka taro ya watsai sai rufaida da ƙawayenta sai washe baki take
amma ƙasan ranta , ta kasa nutsuwa da kwanciyar hankali zare jikinta tayi daga na cikin
kawayenta ta shiga wani daki ta murza key dauko wayar ta tayi bugu ɗaya aka ɗaga ƙasa ƙasa
tayi da muryar ta, tace
'' wallahi anty tsoro nake karfa ya gane..,
saurarwa tayi domin jin me aunty nata zata ce ajiyar zuciya ta sauke tace
'' duk abin da kika ce insha Allahu zan kiyaye amma wallahi duk randa ya gane a kwai matsala
aunty..,
da hallacan rufewa mutane baki ke da kanki kikewa kanki mugun fata kinga sai an jima sauran
kuma ki ƙiyin abinda na saka ki wallahi ke ta dama ba ni ba kinsan irin kudin da na ɓatar akan
auren nan ita kanta babar tasa, zata shiga uku mudai gama da shi ita duk me sauki ce
Insha Allahu aunty zan kiyaye
karma ki kiyaye tana gama faɗar haka ta kashe wayar ta mai da wayar ta tayi inda ta ciro ta ta
gyara kanta ta fito yauwa tun ɗazu nake neman ki sara ta faɗa tana kunna turaren wuta a
bonner
dafa kanta tayi tace '' na dan shiga can daƙin..nayi waya hayaniyar ku ba zata bari naji
komai..ba,
dariya suka saka sara tace
'' amarya bakya laifi ko kin kashe dan masu gida kedai faɗi gaskiya ko kin matsu muyi gaba
ango ya shigo..?,
tura ɗauro gaban goshi tayi tace
'' ku kwana mana ni me ce damuwata...,
wallahi karya kike kina da damuwa ke ɗin ni wallahi nayi mamaki ma da har aka fara bakin nan
cikin sauri rufaida ta tari numfashin Maryam tace
'' haba dan Allah ku dinga sanin zancen da zaku yi yanzu me ne abin yin maganar nan anan
salon wani yaji kamar baki san komai ba..,
dariya sarah tayi tace
'' kura da fatar akuya wahainiya me canza siffa an zaton wuta a maƙera sai a ka ganta a
masaƙa...,
ke yi shiru kamar knocking naji ana yi ko
gaskiya kamar shi ake yi koma ɗaki wata kila yan uwansa ne mu zamu tare su da sauri ta koma
har tana tuntuɓe buɗe kofa sara tayi aunty lubna da aunty Aisha su suka shigo suna ɗaga kai
sama..
kusan halin su ɗaya da umman yaya wato mahaifiyar altab a kwai jin kai da isa da sauri Sara
tace
'' bayin Allah ku suwa ye kun shigo mana kai tsaye kamar baku ga mutane a parlour ba ba
gaisuwa balle sallama...?,
wani kallo aunty lubna tayi wa sara na sama da ƙasa sannan ta ja ɗan ƙaramin tsaki tace
'' da hallacan matsai ko na bige ki ke kinsan mu suwa ye to Kannan ango ne..,
Maryam ce ta, ta tashi tace
'' Allah ya saka uwar sa ce taya za ku shigo mana ba sallama ko wayanne irin gidadawa ne..?,
chingum ɗin bakin ta , A'isha ta tofar tace
'' ke har awa kike wannan maganar to wallahi idan yau muka ga dama sai kun yi kwanan cell
kinga ko abin da nake umma ta fahimta ta toshe kunnen ta dangin matsiyata ga kayan ɗakin
nata zo mu tafi..,
ta ina zata gane aminci ya rufe mata ido cewar aunty lubna
jan hannunta A'isha tayi suka fita sai jin karar tashin motar su sukai fitowa rufaida tayi tace
'' gwara da kukai musu haka yan iskan karya wallahi sai na gyarawa kowa zaman ta..,
dariya suka saka da shewa
POV ALTAB....
Dan rainin hankali ko ka gama zumu ɗin ne kamar baka son barin gidan nan tun ɗazu nake ce
maka an kawo ta ka haɗa kayan ka zuwa sallar isha sai mu kai ka amma kayi buruss
Cewar RUFA'I
dan murmushi yayi shi kaɗai yasan me yake ji a jikin sa ba daban biyayyar mahaifiya ba da son
kaucewa zaɓen tumin daren da yake neman ya yiwa kansa ba zai iya auren rufaida ba duk da
ba abin da ta rasa ilimin addini aiki da shi tsoron Allah ya khalil ne ya shigo a birkice zama yayi
ya na sauke gauran numfashi..
Zuciyar ta kasa aminta da abin da idanuwansa suka gani zancen ta yake so ya gaskata amma
me ya ga fa takai bakin ta innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Allah ya yaye mai wannan baƙin shafin
da ya lulluɓe kwakwalwar sa wannan wacce irin ƙaddara ce
kallon sa altab yayi ya taɓe baki wani irin haushi sa yake ji tashi yayi yace
'' malam lafiya ka shigo min ba ko sallama..?,
idanuwansa ne suka ƙada sukai ja haka idanuwan altab akwai abin da yake hangowa a
idanuwan altab amma tunanin da hangen nesan sa sun kasa hasaso mai mene wanne abu ne
kamar yadda idon altab yayi ja haka na Khalil kallon ido cikin ido sukewa junan su cikin jin zafin
abin da altab ya aikata khalil yace
'' Wallahi Allah altab ka bani mamaki yan zu da ka nuna musu wacce riba ka samu ni nasan
wace ce nasreen na Fika sanin ta..,
Cikin ƙaraji altab yace '' wallahi karya kake yarinyar da na raina da hannuna yarinyar da tun
tana cikin jini aka danƙa min ita a hannu na..,
tashi khalil yayi tamkar zai shiga jikin altab yace
'' wannan duk abanza tunda baƙa kokarin sakata farin ciki baka kokarin gushe mata damuwa ni
nayi rawar gani akan nasreen dan nayi mata maganin damuwar ta na haɗa wata mata da Allah
akan ta zama mahaifiyar nasreen ta nuna mata so tamkar mahaifiyar ta ta jawota a jiki sai dai
kash tun kafin a je ko ina matar ta gajiya...nasreen bata cancanci tsana daga gurin ka ba har da
zaka tun zura baffa yanzu dan an hanani aurenta sai me idan har nasreen mata ta ce zan aure
ta...,
Karya kake idan har ina numfashi a doron duniya baza ka taɓa auren ta ba
da sauri RUFA'I ya shiga tsakaninsu yace
'' haba khalil me kuke yi haka kun tashi tare komai naku tare kuna yara ba kuyi faɗa ba sai
yanzu yau fa ranar farin ciki ce a gare ku..,
Ni wallahi ba ranar farin ciki bace rana mafi muni a guri na kasan irin halin da ya jefa baiwar
Allah nan kasan a halin da na barta shi ya zo yana rayuwa kamar ba shi ya saka ta ba bara kaji
RUFA'I idan aka bawa ALTAB bindiga ya harbe nasreen tsab zai iya harɓe ta domin baya
kaunar ganin ta a doron duniya
A'uzubilla me kake faɗa ne haka..?,
Cewar rufa'i yana riƙe altab da yake kokarin kai wa khalil duka
Ja da baya khalil yayi yace
''sake shi RUFA'I ce mai akai shi ka dai ne me zuciya...,
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un wai me ya shiga kan ku ne ina raba ku , kuna ƙoƙarin yin faɗa da
hankalin ku da tunanin ku me maƙon ku kuyi wa wani faɗa kune yau da kan ku kuke yi kar ku
manta fa lokacin muna makaranta mahaifiyata Allah ya jikanta da rahama har kwatance take
mun da ku amma yanzu kune kuke neman illata junan ku
Rufa'i ya faɗa ya share hawaye jikin su ne yayi sanyi musamman Khalil juyawa yayi zai fita sai
kuma wayar sa tayi ringing ashe akan kujera ya ajiye ta komawa yayi ya ɗauka ganin baƙuwar
number ya ɗaga tare da akarawa a kunne sallama yayi ba tare da wanda ya bugo ba ya amsa
sallamar sa ya zarce da cewa kai ne khalil...?,
Cikin sauri yace '' eh nine me ta faru..,
zan turo maka address kazo asibiti yar uwarka tayi hatsari ana buƙatar ku
ehyi me kace kit ya kashe wayar kallon sa rufa'i yayi yace
'' me ya faru..?,
nima wallahi na rasa gane wa me ke faruwa wai zai turo min address yar uwata tayi hatsari
ko nasreen ce
nima haka nake tunani domin na barta a wani hali sai da na tawo nayi dana sanin tawowa
amma bara na ƙara kiran shi danna kira yayi message ya shigo wayar sa da sauri ya bude a fili
ya shiga karanta wa yace
Unique Care Al-Haramain Hospital
Plot 297 Jido Layout, Danladi Nasidi Housing Estate Mariri
da sauri rufa'i ya karɓi wayar karantawa yayi ka be ƙarasa ba ya karɓi wayarsa ya daka a aljihu
ya fita cikin sauri ya ke komai mantawa da yayi mukulli baya jikinsa tsaki ya ja ya koma part
dinsa ya dauko key ya fito bude mota yayi ya shiga
yayi mata key ya kusan buge me bawa shukoki ruwa sai kaucewa yayi ganin a yadda yake
Sahara gudu a cikin gidan ya bawa ma'aikatan gidan tsoro sudai sunsan baya shaye shaye
buɗe mai get me gadi yayi dai-dai sako hancin motar su lubna sai dai sune suka kauce mai
amma shi kamar ma be gansu ba
ko da ya hau titi sharara gudi ya dinga yi har ya isa asbitin parking yayi a waje domin ba zai
tsaya jira ba har a ba shi katin shiga da mita ayi checking ta ƙaramar kofa ya shiga wayar sa ya
fito da ita daga aljihu kiran mutumin ya shiga yi amma ba ɗauka ƙara kira yayi sai a na biyar
sannan ya ɗaga kai tsaye yace mai kana kina gani nan a cikin asibitin...?,
Faɗama masa yayi nan da nan ya mai da wayar aljihu ko tsayawa kashe wayar be ba ya shiga
reception hannun sa na dama ya shiga akwai hanya miƙe hanyar yayi har emergency room
wuru wuru ya fara can ya hango mutumin yana zurga zurga cikin sauri ya ƙarasa yace
'' tana wanne daki ne..?,
kai hakuri yanzu likitoci na kanta ta bugo ne akai nima wucewa na zo yi na ganta na kaita wasu
asiti saboda rashin dan sanda ba a karɓeta ba shi ne na kawo ta nan da ita saboda abin yayi
yawa zato suke ba hatsari bane
jingina da bango khalil yayi ko me ya faru da nasreen da sa hannun altab shi ne sanadin komai
da ya faru da ita kasa cewa yayi sallar magariba aka kirawo dole ta saka ya tafi yayi salla bayan
ya idar ya tsaya yayi mata addu'a sannan ya dawo lokacin wani likita ya fito yana share zufa da
sauri khalil ya ƙarasa gunsa yace
'' yaya take kun shawo kan matsalar...?,
dafa shi baturen yayi yace
''don't worry everything will be fine..,
kai khalil ya gyaɗa yace
''I can go in and see her..,
yanzu za a fito da ita a Kaita wani dakin zaka iya shiga amma kafin nan ina son ganin wanda ya
kawo ta
sai a lokacin khalil ya lura da mutumin nan baya nan yace
'' kawo ta yayi nine dan uwanta shi temaka mata yayi..,
Okay biyo ni office binsa yayi har office dinsa zama yayi sannan yace
'' a'a ga guri ka zauna mana...,
zama yayi zuciyarsa na tsananin bugu buɗe laptop likitan yayi sannan yace
'' yar uwar ka ta kamu da cutar ciwon zuciya me tsanani i am sorry to say
da sauri khalil ya ɗago yana hango baƙar fuskar altab duk shi ya sakata a cikin wannan hali ci
gaba da cewa likitan yayi idan ba ayi taka tsantsan ba ko wanne lokacin zuciyar ta zata iya
bugawa sannan ta kamu da cutar mental processing disorder amma wannan ba wata matsala
bace hankali ana tafiyar fa ita yadda take so zata war ware idan har kun lura za ku ga akwai abubuwan da take selecting idan kunyi kokarin da raba da shi
ciwon zai ci gaba har ya girma ya zame mata matsala
Rubutu yayi a takarda ya miƙo amsa yayi yayi mai godiya magani zai siyo sannan ya biya duk
wani kuɗi da aka ka she mata wayar sa ce ta fara ringing cirowa yayi sunan mamy ya gani raɗa
raɗa akan screen din wayar sa yasan yanzu za su iya samin labari wata kila saboda haka ta
kirawo shi ɗan haka be ɗauka ba...
A yanzu nasreen bata da wani gata da ya wuce nasa insha Allahu ba zai taɓa barin ta tayi kuka
ba fita yayi yaci ka ciɓis da mutumin da kawo ta hannu ya miƙa mai yace
'' bawan Allah kai hakuri a dazu bana cikin kwanciyar hankali nagode nagode Allah ya saka da
alkairi ya baka abin da kake nema duniya da lahira...,
Ba komai ai yiwa kaina wallahu nayi maka wannan uzurin kallo ɗaya za ai maka a san baka
cikin kwanciyar hankali ya me jiki
aa nine da godiya me jiki alhmdllh komai ya zo da sauki
kai masha Allah motar ta tana gurina zo muje na nuna maka inda take...
KU HANZARTA PAYMENT DIN KU BAZAN DADE INA FREE PAGE BA DOMIN SHIGA PAID
GROUP ZAKU BIYA
500
Amina Muhammad Alhasan opay 8141785374
Ku turo da sheda ta wannan number 09061890481
ƁAƘIN SHAFI
EPISODE 4
A'a bara na haɗa ka da bakanike ni a kwai inda zani tunda kacs motar ta samu matsala sai ya
tafi da ita ya gyara ta
gaskiya ta samu matsala ga ban motar duk ya lotsai ba damuwa kira shi sai na je da shi ya
dauki motar
waya ya khalil ya ciro a aljihunsa yace '' to sai dai ban san sunan ka ba..,
dariya yayi yace
'' nima ban san sunan ka ba ni dai sunana HAFIZ JIBRIL MAI DAWA...,
ƙara waya yayi a kunne yana cewa '' KHALIL HAMZA HUSSAIN MAI TANGARAN..,
to nayi saving number ka kai ma sai kayi tawa insha'Allah zan ƙara kawo muku ziyara na ga
jikin ta wallahi na tsorata da ganin halin da ta shiga a lokacin da na kawota jini jiƙa min rigata
yayi
Okay ba damuwa mun gode sosai wallahi sauke wayar yayi yana cewa kaga be ɗauki kiran ba
rana na ƙara yi mai ko Allah zai saka ya ɗaga kaga dare na ƙara yi
Haka ne wallahi
cikin sa'a ya ɗaga karawa yayi a kunne ya danna matsa gefe ci gaba da danna wayar sa Hafiz
ke yi har ya gama wayar ya dawo yace
'' ga shinan zuwa ni zan tafi phamarcy na siyo magani..,
okay Allah ya kawo shi lafiya sai ka dawo
amin ya Allah ya ce yana fita da ga gurin ba ƙaramin bill sukai mai ba haka ya dawo hannun sa
riƙe da ledar magani daidai karasowar makanike dan haka juyawa yayi yana cewa
ka ganshi ya kirawo ni yana waje zo muje sai ku tafi
wayar sa hafiz ya mayar aljihu suka fara tafiya har wajen musabaha sukai da me gyaran mota
sannan ya juyo ya barsu tare da man ya riga da ya gama yi mai bayani
kai tsaye dakin da aka kwantar da nasreen ya shiga tana kwance ban da na'urar da aka saka
mata ke motsi alamar tana da rai ba abin da ke motsi a jikinta kanta an nannade mata shi da
bandeji ga oxygen da aka saka mata limshe ido yayi ya jingina da bango a lokacin wayar sa ta
ƙara ringing wannan karon adda asma ce
ɗagawa yayi cikin tashin hankali tace mai har yanzu fa nasreen bata dawo gida ba ko zaka
bincika kaga inda take
kallo yabi gadon da take kwance yace
'' tayi hatsari yanzu haka ina asibitin da aka kwantar da ita amma da sauƙi...,
ajiye Sultan tayi da yake hannunta gaban ta ya yanke ya wadi tace
'' innalillahi ya akai haka ta faru...?,
adda asma ina zan sanu nima kirawo ni akai aka ce ga halin da take ci wallahi kin ganni nan
jikina duk ba dadi ga ta nan ko motsi ba tayi sai na'urar da aka saka mata ita ke motsi amma
baya ga haka ba abin da ke motsi a jikin ta
innalillahi wainna ilaihir raji'un Allah ya bata lafiya bara na sanar da su
cikin sauri ya dakatar da ita ta hanyar cewa adda asma kin manta dazu me ya faru...? Kinga
wanda ya damu da ya neme ta ko yasan halin da take ciki wallahi abar tausayi ce NASREEN
farin ciki muka kasa bata shi ya saka take tare da mutanen da take tare da su tafi jin dadin
zama da su fiye da kowa
wallahi tun ba yau ba ma fahimci haka ɗebe mata kewa suke shi ya saka take zama da su
amma Allah yaye wannan baƙin shafin da ya lulluɓe zuciyar mu da idanuwan mu Amin ya Allah
zan dai sanarwa da daddy Sultan idan zai faɗa musu ya faɗa muku
cewar adda asma
Okay hakan yayi sai an jima
turo min address din gobe zan zo Insha Allah
tu zan turo miki ya faɗa yana kashe wayar
zama adda asma tayi ta zuba ta gumi kasa motsi tayi har sai da uncle Yusuf ya shigo firgigit ta
ɗago kanta, ta kallesa tace
'' sannu da zuwa...,
zama yayi ya