Showing 12001 words to 15000 words out of 20855 words
yafaru da
salma! To amma nayi tunanin halinda inna zata
qara saka kanta aciki shiyasa nace bari dai
ngaya miki yanxu mene ne mafita!?
Hjy tai ajiyar zuciya daga bisani ta dubi Abba
tareda cewa.
Toh nidai alhj dazakaji shawarata anawa tunanin
wannan ai abin farin ciki ne kuma rufama juna
asirine.
Yanxu idan akace salma wani bare zata Aura
kaga dole ne sai an fada mishi abunda yafaru da
ita kuma wannan kamar cin zarafine da kuma
tonan silili.
Idan ba tayi dace da miji me sonta bane yadinga
mata gori kenan., akan abinda itama bada
sonranta bane tsautsayine kawai ya hau kanta.
To Amma yanxu kaga afnan shi yasan abinda
yafaru da ita kuma har yanxu yana sonta
ahakan.
To alhj kaga zaifi mana rufin asiri sai ayi tuwo
na maina kenan.
Ammapa ni anawa tunanin kenan.
Wani irin kallon rashin fahimta alhj yake mata.
Yace wato ke har yanxu kina nan akan bakanki
kenan.
Yaci gaba da cewa
Daman nasan abinda zakice kenan.sbd daman
cen abinda kikeso kenan.
To Amma idan da kinson wannan hadin yanxu
yakamata ki cenja ra'ayi sbd bakisan qatonda
yai mata fyade ba.
Yanada cutar qanjamau ko bayidashi.
Wannan duk be dameki ba. Ke baruwanki da
lafiyar danki.
To idanke kina ganin wannan hadin me yiwuwane
gwara ma ki cenja tunani.
Ke ko tunanin yadda aka wulaqanta miki yarinya
ba kyayi.
To kisani bazan taba bari a kashemin yaro ba.
Shi kadai Allah ya bani na miji kuma nabari azo
a goga mishi cuta.
Towai shiyace miki ma har yanxu yana sonta.
Ai shidinma ba mahaukaci bane.
Juya kanshi yayi yai wani dan gajeran tsaki...
Mtsw...tare da cewa keda akace kibada shawara
kinxo kina wani fadin abinda bazai yiwuba.
Sadda kanta tayi qasa tace Allah ya huci
zuciyarka..Amma alhj ai shawaran na bada
bawai nace ayi dole bane.
Kuma kace kayima inna alqawari akan zaka aura
mishi salma.
Sannan na tabbata afnan shiyasamu inna yace
tai maka magana domin Jiya bayan fitanka
shima yafita.
Na tabbata hakanan inna bazata taso da wannan
maganarba saida izinin afnan.
Kaga kenan har yanxu yanason salma!.
Taci gaba da cewa.
Ni nasan daman soyayyarsu da salma bazai iya
gudunta akan wannan abun daya sameta
ba.
Kuma ya burgeni.
Sannan Wannan shine lokacinda yakamata ya
nuna mata shi masoyin gaskiya ne.
Kuma zai iya kasancewa tare da ita a kowani
hali.
Yanxu sai kayi tunani.
Danka dai yanason salma!
Kai kuma kayima Inna alqawarin hadasu aure!
Sannan wannan abun alfaharine agaremu.
Kuma rufin asirin zuri'armu ne.
Sai kaje kayi tunani ni iyakan abunda zan iya
fada kenan.
Amma ka gafarceni idan na bata maka rai.
Gaba daya jikin Abba yai sanyi da irin
maganganun umma.
Saidai har yanxu yanajin bazai iya bari Afnan ya
auri salma ba"
To amma ya zaiyi da inna!?yakasa samun
wannan amsar.dan haka ya dubi umma yace
shikenan na gode! Ni yanxu zanshiga wanka ayi
qoqari agama hada break kafin na fito.
Umma tamiqe tace to alhj saika fito.
Bata zame ko inaba sai kicking nan taga aunty
sadiya tanata hada abincin break.
Ta gaisheda momyn nata sannan tace umma ai
nashiga dakinki zan gisheki ban ganki ba.nace
ko kina dakin Abba ne shine kawai nataho
kicking nakama aiki dan yau inaso ne naje
gidansu salma.
Umma tace eyya aiko yakamata kije kidubata
kam,
Nima yau naso tambayan Abbanku zuwan .to
amma banga fuska bane dan yau ranshi abace
yake kuma hankalinshi a tashe yake.
Jiya inna tatayar masa da hankali.
Aunty sadiya ta ware ido tace topa wani abun yai
mata ne!?
Umma ta yamutsa Fuska tace kinsan dai halin
abban naku.
Wai tataso mishi da maganar auren salma da
afnan ne wai dole saiya hadasu Aure.
Shine ya nuna mata beyarda ba. Shine ta dinga
mishi kuka hankalinshi yatashi har saida yai
mata alqawarin hadasu aure.
Shine yau yatashi da bacin rai wai yaza'ai ya
aura mishi yarinyarda aikaima fyade be sani ba
kota kamu da wata cutar.
To shiyasama nakasa tambayarshi nabari saiya
huce.
Gaban anty sadiya saida yai wani mugun
bugawa.
Amma ta wani bngaren kuma taji dadin wannan
maganar.
Dan kuwa shiyafi kowa dacewa da aurenta. Bai
cuceta a banza ba.
Dan haka tace tohpa yanxu momy yaza'ayi
kenan"
Tace oho nidai nabashi shawara idan yaji
shikenan.
Aunty sadiya tace to umma Alllah yazaba abinda
yafi alkairi!
Tace Ameen dai.
Yi Sauri kigama kimtsawa dan yanxu zai fito
yayi break ya fita.
Umma ta fito tazo palo tadan kashin gid'a akan
kujera.
Abba kam yana gama kimtsawa beyi wani
jinkiriba ya nufo palo anty sadiya tana tsaye
tana shirya abinci akan dining ta duqa ta
gaisheshi ciki ciki ya amsa da ganinsa kasan
yana cikin damuwa.
Yace sadiya maza kije ki kirawomin afnan yataso
yanxu inason magana dashi.
Tace to abba.
Ta nufi sashen Afnan tafara buga qofa. Shima
lokacin ne yasamu dan bacci ya kwasheshi,
kamar a mafarki yaji ana buga qofa. Ahankali ya
bude ido yana sauraron ko Zaiji an qara.
Yaji anci gaba da bugawa.
Daqyar ya iya tashi jikinsa ko ina ciwo yake
haka yaqaraso bakin qofar ya bude.
Aunty sadiya yagani ta jefo mai wani harara
shiko yace ina kwana.
Bata amsa ba tace Abba na nemanka yanxu
kuma.
Ta juya abinta bata saurari me zaice ba.
Tana zuwa tace Abba yana zuwa.
Abba na zaune akan dining umma ta zuba mishi
abinci Amma ba abinda ya iya ci.
Saiga Afnan ya fito jiki a sanyaye yaxo ya zauna
akan Capet
Ya dubesu yace umma ina kwana.
Tace lapia lau ya jiki.?
Yace da sauqi.
Sannan yace abba ina kwana.
Wani irin kallo yajefo masa me cike da alamun
tambayoyi!.ba tare da ya amsa gaisuwanba.
Cikin zafin murya yace AFNAN..!
Firgicinda yayi saida qwaqwalwarshi da ruwan
jikinshi duk suka dena aiki.
Tsoro da fargaba suka ziyarci zuciyarsa.!
Muryarshi na kyarma yace Na'am Abba.
Abba yasake jefo masa wani hararan daga bisani
yace.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 25
==>Afnan kabani kunya. Ban taba tunanin zaka
watsamin qasa a ido ba.
Wai harkayi girmanda zakaje kahadani da inna
akan salma ko?.to kasamu yadda kakeso. Domin
kuwa tayi abinda kasakata.
Kuma zan Aura maka salma!
Amma kasani duk abinda yafaru dakai kai kaja
ma kanka tinda kai bakasan ciwon kanka ba.
Baka kishin abinda akaima yar uwanka .
Dan haka zan Aura maka salma!kuma babu saki
atsakaninku har abada.
Sannan nacire hannuna akanka kaje kai duk
abinda kaga dama.
Afnan kansa na qasa ya dago kannshi ahankali
idonsa sunyi jawur ya kalli Abba kabinsa na
karkarwa yace Abba..walh..ni...kafin yaqarasa
tuni Abba ya daka mishi tsawa..get out
kabacemin da gani. Banason ganika agabana.
Agigice ya miqe kamar zai kifa sbd Sauri.
Umma ne ta kira sunan Afnan"tsayawa yayi cak!
batare da ya waygo ba. Sannan taci gaba da
cewa haba alhj dan Allah ka sassauta mishi
mana., baka ganin shima ba lapia ne dashi ba.
Abba bece mata komai ba ya miqe yadauki
jakarsa da keys din mota yai waje fuuuu!
Batareda yaci komai da aka Zuba mishi ba.
Ganin Abba ya fice afnan ya juyo ahankali ya iso
dining din yadda umma ke zaune yaja kujera ya
zauna idanuwanshi cike fam da qwalla.
Umma ta dubeshi tace Haba afnan kakwantar da
hankalinka kariga kasan halin babanku.
Fushi yayi kuma zai huce nan bana jimawa ba.
Kuma ni ina bayanka 100 bisa 100. Naji dadin
abinda ka yanke na taimakon yar uwanka.
Kuma karka sake kace zaka kalli abinda akaima
naka yar uwan domin kasamu hanyan
musgunama salma.
Dan kuwa ita babu laifinta aciki.
Inamai farin ciki da wannan lamari domin rufin
aairinmu ne gaba daya.
Dan haka ka kwantar da hankalinka ka qyale
alhj.
Yanxu dai kaci Abinci kasha magani kaga sai
rama kakeyi duk kabi ka lalace.
Nan dai taita lallashinsa har saida yaci ya qoshi.
Daman shi babban damuwarshi shine abba yaqi
amincewa.
Amma tunda sai ya amince komai zai faru me
sauqi ne.
Suna cikin firansu. Saiga aunty sadiya tafito ta
fesa kwalliya tayi masifar kyau.
Doguwar riga tasa na atanfa ya zauna daram
ajikinta taqaraso gunsu cikin takunta irin na
qasaita. Sannan taja kujera ta zauna gamida
janyo kulan Abinci tana qoqarin zubawa tace
umma Abba harya fita ne.
Ta gefen ido kuwa wata irin harara ta dinga
aikawa afnan din.umma tace eh yanxu yafita ko
break dinma beyi ba.
tace to umma nima na shirya yanzu zanci abinci
ne na wuce.
Umma tace to idan kinje dai kice ina gaisheda
me jiki kuma insha Allahu nima gobe ina nan
zuwa dubata. Afnan zai kawoni shima daganan
ya dubata.
Saida suka kalli juna aunty sadiya da afnan.
Sannan yai qasa da kanshi cike da kunya da
fargaban abinda Umma tafada. Sadiya taci gaba
da cewa toh umma zasuji insha allahu,.
Afnan ya miqe yace to aunty ki gaisheta.
Tai kamar batajishi ba. Yakama hanya yai
dakinsa. Aunty sadiya ma tatashi taje daki ta
dakko jakarta da takalminta Wanda sukai
macing da kayan gamida sa hijjab dinta taima
momy sallama ta fice.
Salma kuwa yau tatashi ta qarfinta domin
tanajin qarfi ajikinta sosai. Sauqi dai yasamu da
izinin Allah. Kwalliya kuma yadawo sabo!!.Tsaye
take gaban mirror tana taje gashinta yadda ta
sakeshi abaya, gamida dakko wani siririn hula
Wanda macing color ne da kayan datasa
tsakiyarshi a bude yake. Ta gaban hulan kuma
an rubuta (love is life!) Riga da sket ne ajikinta
Wanda yaya Habib yayo mata tsaraba daga
Dubai. Sunyi matukar amsar jikinta.
Tayi masifar kyau Wanda ba'a magana.
Ta sanya wannan hular gamida fito da gashin ta
tsakiyar hulan.
Ta qara duba mirror sannan tasaki wani
murmushi Wanda yasake bayyana tsantsar
kyawunta gamida lumshe ido domin it a kanta ta
burge kanta.
Palo tayo tana tafiyarta a nutse tana isowa palo
kafin takaga zama tajiyo sallamar aunty sadiya
nan tatsaya cak! Aunty sadiya tana shigowa ta
aika mata da wani irin qayataccen murmushi tuni
Anty sadiya ta ware idanu gamida fadin. Woww!!!
Sister irin wannan kyau haka ai saikisa inyi
rangaji in fadi aqasa. Taqara sakin mata
murmushi sannan ta ruga ta rungumeta tana
fadin kai aunty ai kinfini hadewa.
Taqara dubanta tace kai!!waneni da had a kaina
da matar manya. Wannan ai dole kidinga furgita
maza irin wannan kyau haka"Ammapa kar karki
ya fashe kidauka wai kinfini kyaune. Kin wani
zabga jan baki kamar yar hayin kogi. Gaba daya
suka kwashe da dariya.
Salma tace to aunty ni duk ba wannan ba ina
wayana!toce kwantarda hankalinki gata a jaka.
Ta karbi jakar tana kokuwan budewa. Saiga
momy tafito tana dariya tace kudai bakwa rabo
da barkwanci Indai kuka hadu.
Dariya kawai sukayi salma ta ciro wayarta tayo
daki tafada kan gado aunty sadiya kuwa nanta
baje suna gaisawa da momy. Tin kafi tacire
wayar a key take ganin saqonni daban daban
messages miss call WhatsApp.!dan haka tarasa
ina zata fara dubawa. Saita yanke shawarar bari
tafara shiga whatsapp tana shiga saqonwa zata
fara gani..uhmn..saida gabanta yafadi dan jitayi
kamar yana kusa da itane zai kamata. Afnan ne
yai mata sqo har gashi biyu..hannunta na rawa
ta danna ta shiga ga abinda saqon farko ke
dauke dashi...Amincin
Allah shi tabbata agareki yake yar uwata kuma
abar begena a kullum. Na kirawayarki baki
pecking ba bansani ba ko kina bacci ne.
Daman ba komai bane inaso na fada miki ne
daman zanxo anjima in kawo muku ziyara
kigaya momy kuma ki shiryamun kayan dadi
kinji my dear sister!! Lallai fa afnan an shirya
maka kayan dadi irin Wanda baka zata ba kuma
kaci ka qoshi..!! x
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 26
==>Da wani dogon tsuka. Mtswwwwwww!!!.gami
da cewa...!Allah shi kyauta in Auri mugu! Ai ko
maza zasu qare aduniya bazan taba aurenka ba
sbd na tsaneka tsana mafi girma.!mugu kawai"!
Tana turawa tai blocking dinsa.
Amma mezai biyo baya!?
Tunanin baya ne ya fado mata! Kalmomin da
tafada masa abaya suka dinga dawo mata kamar
anyi recording dinsu. Tabbas ta fada masa wasu
kalmomi.
a gurin da take zaune. Kuma a irin wannan
yanayin na baqin ciki,.
Lokacinda take zubarda hawaye.
Zuciyarsu ke tsananin azabtuwa da son juna!.
take masa iqirarin cewa....Haba yayana walh
hannuwa na bazasu taba iya yin blocking dinka
ba.
Kayi hquri bazan iya aikatawa ba.
Kamar yadda bazan iya guje maka ba. Haka
baxan iya daina sauraronka ba. Idan kai zaka iya
yin blocking dina to ina me baka daman yin
hakan.
To amma kasani Kunnuwana bazasu taba gajiya
da sauraronka ba. Zuciyata bazata taba daina
azabtuwa da sonka ba.
Sannan a kullum zan kasance cikin baqin cikin
rabuwa dakai.
Idanuwana bazasu taba daina son ganinka ba
akoda yaushe. Alqawari ne na dauka bazan taba
auren wani namiji ba aduniya idan bakai ba.
Ashirye nake dana rayu dakai ako wani irin hali
ni bazan taba guje maka ba.
Ina qaunarka yayana qauna irinta har abada.!
Kayi haquri yayana walh bazan iyaba"hannuwana
bazasu iya blocking dinka ba.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 28
==>INNA..ki..taima..keni muryarta na rawa! Shi
kanshi afnan yai matuwar rudewa da furgita
tsoronshi daya karta fadi ta sume kamar yadda
tayi lokacinda yaje gidansu.
Dan haka yai miqe shima akidime yake fadin
SALMA!SALMA Dan Allah ki natsu ki natsu kinji
pls SALMA! Yana qara matsowa shima jikinshi
barin yakeyi,.
Haka take qara Ja da baya tana fadin INNA..kin
ganshin.. KO.. Daidai nan ta tokare da qofa tai
wani irin qara yayinda yaqaraso a guje ya ruqota
alokacinda take qoqarin kifawa. A daidai lokacin
daya ruqota taqara sakin wasu tagwayen ihu
gamida kuccewa ta fada cinyar inna ta
qanqameta sosai tana tsusa kanta a tsakankanin
Inna,!
Gaba daya mamaki ya hana inna cewa komai
ganin jikokin NATA sun afka wani irin yanayi na
rudu Wanda takasa fahimgarsu., batasan sanda
tafara fadin."LAPIA!LAPIA meyake faruwa ne!?
Salma kuwa qara qanqameta take tana fadin
Inna kaina ne kaina inna! Cikina..ke..inna ta
katseta da cewa meya samu kan naki?
Afnan yanajin haka be tsaya yayi wata wata ba
ya zari takalmarsa yabar gidan da saurinsa. Dan
yasan idan yazauna abin saiyafi haka.
Inna ta daqo tana qwala masa kira amma inaaa
dan talikin yayi nisa! Dawo wa tayi kan salma
taci gaba da cewa wai me kuke nufi ne
daganinsa kin fara kuka shi kuma ya gudu gudu.
Kin sakani cikin wasu wasi.
Wani irin sanyi salma taji aranta alokacinda ta
waigo ta tabbatar da cewa afnan baya palon.
Miqewa tayi batare da taceda inna komai ba ta
kwanta kan kujera domin har kanta ya fara ciki
ga wani zazzabi dayke niman kamata.
Inna tai juyin duniyar NaN akan salma tafada
mata gaskiya amma ta dake akan ita kanta ne
da cikinta kawai yake mata ciwo.! Haka ta gaji
ta rabu da ita tace ai idan tai tsami maji . idan
kuma Auren ne bakwaso ai
sai inji. Salma tai saurin tashi ta zauna gamida
cewa wani rin aure kuma.!
Inna ta galla mata harara tace irin na uwaki!
Dole takama bakinta tai cit! Tadan huta nawasu
yan daqiqu tatashi tace zata wuce. Domin ita
kam yau bataji dadin zuwanba ma. Daqyar
tasamu ta isa gida tana tangadi jiri take gani
sosai dan haka tana zuwa ta zube akan kujera
jikin nan NATA ya dafe yayi zafi rauu! wasu
zafafan hawaye ne keta sulalo mata. Momyce
tafito daga sashenta gaqaraso wajenta da Sauri
tana fadin salma lapia kuwa!meya sameki?!.
Tana kai hannu jikinta taji zafi rau!tace
subhanallah zazzabi kikeji haka kuma shine baki
gayamun ba"bari nakawo miki Abinci kici nakira
driver muje asibity.
Momy ta qwalama sumayya kira saigasu sun fito
dukkansu aguje suna dariya. Ganin salma a
kwance yasa sukai tsuru tsuru momy tace ma
sumayya maza kije ki zuboma auntynku abinci
batajin dadi ne. Ba musu ta wuce kicking sai
gata dauke da pleat din kuskus taxo ta dire ma
momy sannan taje firji ta dakko robar faro daya
ta kawo momy tace to tashi kici.!
Taqarayin wani narai narai da ido tace momy
cikina ciwo yake.
Momy tace kiyi haquri kici koda kadanne. Haka
tatashi momy tafara bta abaki. Bai wuce cokali
4 tayi ba kawai sai amai momy ta tallabota da
sauri haka ta dinga kwara amai duk jikinta yai
yaushi. Momy kam duk ta rude tasamu ta
kwantar da ita sannan tamiqe dasauri taje ta kira
habib tafada masa halinda suke ciki sannan taxo
tafara gyara wajen.!ba a dauki lokaci ba habib
ya turo da driver.
Aka kwashesu sai asibity. Suna zuwa aka
karbesu cikin kulawa kasancewar habib yayi
waya tun kafin su iso..Dr ya dubata sosai tareda
wasu yan tambayoyi itakam tadinga jera mashi
amsa. Tagaya mishi cewa takai 2weaks tana
fama da ciwon ciki kadan kadan. Sannan takanji
tashin zuciya lokaci lokaci ga yawan ciwan kai.
Dan hak Dr yasa aka debi jininta da fitsarinta
sannan yahada musu wasu yan magunguna dazai
taimaka mata yace suje gida tafara sha kafin su
dawo gobe a tabbatar da result din da aka
samu.! Momy bata kawo komai aranta
ba"sabanin ni da harna fara wani tunani! Kaji
iyayen katslandan
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 29
==>A dimauce momy ta miqe tana Innalillahi wa
inna ilaihirraju'un Dr karufamun Asiri jikinta ko
ina fari yake.
Yayinda ni da Dr muka saki baki da hanci da ido
duk muna kallonta.!
Mamakin Dr shine shin meyasa momy ta furgice
haka shin bata bataraba da qaruwanda suka
samu ne ko kuwa"
Mamakin salma kuwa shine.. Wani irin ciwo ne
juna biyu dahar momy ta furgice haka take
Neman faduwa.! A tsorace ta kalli Dr tana
qoqarin yimishi tambayar wani irin ciwo ne take
dauke dashi.!
Kafin ta kaiga cewa komai sai ganin momy
sukayi ta sulele aqasa sumammiya!.
A haukace salma tai kanta tana kwarma ihu tana
fadin Dr wani irin cutane nake dauke dashi har
baqin cikinshi yake Neman ya kashemin
mahaifiya"
Shima gaba daya yagama kidimewa yayo kan
momy yana fadin kawai nace mata ne kinada
ciki shine tashiga tashin hankali haka!? Ko
bakida Aure ne dai! Allah dai yasa
ba abun kunya kika daukoma iyayen naki ba.
Cikin wata irin murya salma ke cewa Dr cikin
baby nakedashi!? Yanxu baby ne acikina
taqarasa maganar tareda shafa cikin! Dr yace
qwarai kuwa kina dauke da juna biyu har na
tsawon wata uku babu yan kwanaki!" Ai kafin
yagama rufe bakinshi sai