Showing 3001 words to 6000 words out of 20855 words

Chapter 2 - Butulci ko So Book Compelet Eashat

Eashat   

16 Aug 2026

346

anbashi gado
ya........momy tai saurin fixge wayar takashe
kiran sannan tace kana hauka ne!?me kake shirin
fada mishi to ina me gargadinka karda kasace
naji wannan maganar abakin kowa hatta
yayanka Habibullah ban yarda yaji wannan
maganar ba nagaya maka!;cikin rashin faminta
Ahmad yadubeta tare da cewa to momy ai
wannan maganar bazata boyu ba dole ne kowa
yasan abinda afnan ya aikata kuma koma me
akai mishi ai shiyaja makanshi wannan maganar
ai tafi qarfin a boyeta momy:'cikin sanyin jiki
momy ta kama hannun d'an nata hawaye suka
zubo afuskarta sannan tace Ahmad kataimakeni
da wanne kakeso naji so kuke baqin ciki ya
kasheni Ahmad kasan halin yayanka habibu
yanxu idan yaji wannan maganar me kake
tunanin zai faru ko so kake a haifi danda ba
ido;yanxu ga salma rai ahannun Allah ga sadiya
kwance afnan kwance so kake kafada yayanka
yaxo yaita hauka yanemi hanyar salwantar da
rayuwar wannan yaron ko kamanta zai iyayin
komai akan duk Wanda ya cutar da salma?!
yanxu abinda
kakeso yafaru Keenan baqin ciki yakasheni-
taqarasa maganar tareda fashewa da
kuka,.shima Ahmad kukan yafarayi'nan yazaunar
da mahaifiyar tashi kan kujera sannan ya
durqusa aganta yana kuka'yace momy na yanxu
ya kikeso ayi!?dan allah karki tada hankalinki
walh momy duk abinda kikace zanyi,.gani sukayi
sadiya tatashi ta zauna itama hawaye ne keta
faman sintiri a fuskarta da alamun ta jima tana
sauraronsu,.momy tamaida dubanta garesu
sannan tace Ahmad yace na'am.sadiya tace
na'am momy!,inaso kuyimin wata alfarma.

===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 8
==>momy tace ina roqonku dan Allah karbu
fadama kowa abinda yafaru kar wannan maganar
taje bakin kowa kubarta anan dagamu sai
allah,dan Allah kuyimin wannan qoqarin idan ba

haka ba abinda zai biyo baya me girma ne kuma
kanku saikunce mema yasa kuka
bayyana,.Ahmad yai wata ajiyar zuciya..,sannan
yace yanxu momy kina ganin wannan maganar
zata boyu!? wannan fa ba qaramar magana bace
yanxu idan an boyeta ya salma zata kasance
wajen
mijinda zata aura yanxu idan aka boye wannan
maganar anyi mata adalci kenan momy?!momy
tace Ahmad ba shawararka nake nema ba umarni
nake baka abinda nakeso kuyimin kenan duk
wani abinda zai biyo baya me sauqi ne akan idan
aka bayyana maganar nan.,sannan ai dole ne ma
afnan ya aura salma domin ayanxu babu Wanda
yadace da auranta idan bashi ba'.dan haka kuyi
abinda nace kuma kubar komai a wajena ni
nasan mezan fada musu!!sadiya taja wani
numfashi ta dubi momy tace momy be kamata a
quntatawa rayuwar salma haka ba momy walh
gwara ma a qyaleshi da babib din yai masa duk
abinda yaga dama domin ya cutar masa da
abinda yake matuqar tattalinta da rashin son
bacin ranta.dan haka yadace ya fuskanta
hukunci momy walh bana goyon bayan a rufa
masa asiri.,ta qarasa maganar tana kuka!,momy
ta dubeta sadiya hannunka baya rubewa kayanke
kayar kome yaronnan yayi yakamata muyi masa
adalci idan muka duba
tsakaninshi da salma bedace mujuya masa baya
ba dan ya aikata kuskure irin wannan danni na
tabbata ba halinshi bane,.dan haka sadiya kuyi
haquri kawai kubi abinda nace.,sadiya dai shiru
tayi Ahmad ne yai qoqarin cewa insha allahu
zamuyi yadda kikeso momy kuma babu Wanda
zaiji wannan maganar abakinmu dayardar Allah
munyi miki alqawari;momy tadan saki fuska tace
yauwa Ahmad allah yaimuku albarka yanxu
kiramin habibu nagaya masa muna asibiti.,kuma
inaso idan zaka tafi kuwuce tareda sadiya domin
su kwana da yaran nan.yakarba wayan yakira
yamiqa mata.,bugu 3 yayi taga an danna busy
bata damu ba tinda daman tasan baya daukar
kiranta saidai yakashe yakirata.,jim kdan kuwa

saiga kiran Habib tadau ka yagaisheta cikin
ladabi.ta amsa muryarta babu
annashuwa.,sannan tace habibu muna nan fa a
asibity salma ba lapia yanxu haka dai gatanan
sai abinda allah yaso,.what?momy meya sameta
wani asibity ne momy ina fatan dai tana nan da
ranta momy bani ita dan allah ko bata magana
ne gaba daya Habib yarikice momy tama rasa
amsar dazata bashi ajiyar zuciya kawai tayi
sannan tace muna horeb hospital ne saikazo
kawai takashe wayarta.,afurgice Habib ya nufi
daki fadeela tamiqe a tsorace tana fadin
sweetheart lapia kuwa?waye ba lapia.ko
sauraronta beyiba yaje yasaka farar jallabiyyarsa
yafito da sauri yana fadin asibity zanje yanxu
momy takirani take fadamun salma ba lapia
yanafadi yana qoqarin ficewa,.batayi mamaki ba
dan tasan yadda yakeson qanwar tashi aranta
taji haushi amma afili cewa tayi subhanallah
allah yabata lapia saika dawo kafin tarufe baki
shiyariga ma yayi waje,aranta kuwacewa tayi
allah yasa ta mutu inga qaryar iskanci.,taja
tsaki ciki ciki tajuyo ta rufe qofarta ta wuce
dyning ta zquna cike da haushi.,shiko gogan
naka tuni yafigi motarsa sai asibity,.a bangaren
su abban afnan kuwa Abba yakira yakira wayan
sadiya amma anqi dagawa tuni yafadama hjy
abinda ke faruwa sannan yace tai maza ta dauko
hijjabinta dan basuga tazama ba dan yaji ance
afnan dinshi ba lapia kome yasameshi
oho.,hankulansu duk atashe suka kama hanyan
asibity mu samman ma Abba da ko kadan
bayason yaji abinda zai cutar masa da
dansa.,suna isa saiga Habib ya iso nan suka
hadu a harabar asibityn daidai nan kuma Ahmad
da sadiya sun fito da nufin tafiya gida.,nan suka
hadu babu Wanda yatsaya wata gaisuwa Habib
yadubi Ahmad yace ina ne word din?!Ahmad yace
kuxo muje suka dunguma gaba daya suka nufi
inda salma take.,nan suka tadda doctor a tsaye
kan salma yana mata allura sannan ya cire ledan
ruwan daya qare yasa mata wani.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 9

==>Habib yai saurin qarasawa wajen jikinsa na
rawa yana fadin doctor ya jikin nata da sauqi
kuwa!?Dr yace yp zazzabine me zafi yanxu ya
rufeta nayi mata allurori yanxu yanada kyau
kubarta ta huta domin gaskiya taji jiki tana
buqatar Hutu bamason ana yawaita surutu
kubarta ta huta pls!Habib yace insha Allahu za a
kula amma Dr menene matsalar nata abinciken
da kukayi meyake damunta ne pls walh bata
saba ciwo irin wannan ba naga harda qarin jini
akai mata,.Dr yace eh abin ya danganta ne daga
irin mijin da kuka aura mata wata qila yafi
qarfinta kuma kaga qaramar yarinya CE gaskiya
kunyi mata auren wuri gashi kun
hadata da ba qauye marar tausayi yayi muku
kaca kaca da yarinya gsskia ina iya cewa harda
laifinku.,amma insha Allahu zata samu lapia
karku damu.yafada tare da bude qofa yai
ficewarsa inda yabar Habib atsaye yasaki baki
hannunsa na rawa bakinsa na motsi amma
yakasa magana gashi kuma yanada tambayoyi
domin shidai be fahimci zantuttukan likitannan
ba shin meyake nufi ne menene yasamu
salman!;momy kuwa da Ahmad da sadiya tinda
likira yafara zancen nan a furgice suke tsananin
tashin hankali yaqara ziyartar zukatansu kuttt.!!
hjy da Abba suma dai sun kasa fahimtar
maganganun Dr dan duk yasasu a duhu.,amma
shidai Abba hankalinsa be kwanta ba dan kuwa
bega afnan ba.,babban burinsa kawai a nuna
masa dan autan nashi,.Habib ne ya katse kowa
daga saqe saqen zuci jiki a sanyaye yace momy
nifa ban gane maganar Dr ba wai meya faru da
salma!?.momy ta maida numfashi sannan tace
Habibu wannan ba maganar nan bane.,yqnzudai
yakamata kuje kuduba afnan din ko ta maida
dubanta gun Abba tace alhj kuje kuduba afnan
din ko,. Habib yai saurin cewa haba momy
kifada mana abinda ya sameta mana mu fita
daga cikin rudaninda Dr yajefamu yanxu ga
salma a kwance afnan din shikuma meya
sameshi??!yaqara sa bakin gadon yataba jikin
salma agigice yajuyo yana fadin momy kinji

jikinta kuwa,.dan allah meya sameta ne idonsa
duk sun ciko da qwalla.,ta dubesu gaba daya
tace alhj muje wajen afnan din inyaso mayi
maganar a waje kaga Dr yace kar a yawaita
surutu!,alhj kan daman ya qosa yaga afnan dan
haka shiya fara bude qofa hjy tabi bayanshi
dukansu zuciyarsu cike da saqe saqe,.momy ta
kalla habib sanna tace kataso muje cen zakaji
qaddarar data afko mana yau.,amma inaso
kazamo me yadda da qaddara kuma karka tashi
hankalinka domin haka allah yaso sannan itama
ta fice sadiya da Ahmad sukabi bayanta.,da
sauri yamiqe shima yabisu yna nanata
maganarda momyn nashi tai masa yanxu a
zuciyarsa!yasan lallai akwai wani Abu me
girma,.suna shiga suka cimma afnan
kwance sai rawar sanyi yake hatta gadon dayake
kwance girgizawa yake.,Abba yaqarasa a furgice
yana fadin afnan mega sameka ne haka!,dan
allah kuyi mana bayanin abinda yasamu yaran
nan.nan danan masu saurin kuka suka fara
musamman ma wa Inda suka San abinda
yafaru,.momy tai ajiyar zuciya sannan tace
tabbas abin kuka ne yasamemu kuma dole muyi
kuka bazan hanaku kuka ba,.taqara da
cewa an tsutsemu an tsutsi salma yau anci
mutuncin mu anci mana zarafi anje har gida
anyima salma fyade na rashin tausayi.!!ta fashe
da kuka
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 10
==>Dukkansu saida suka razana da jin
maganarda momy tayi.,Habib ne yameqe hankali
tashe yace what momy fyade fa kikace salma din
akaiwa fyade!;momy tace tabbas kuwa anyi mata
fyade na rashin tausayi.dan dalilin dayasa
kukaga afnan anan wajen kenan domin kuwa
sanda abin yafaru da ita afnan yaje gidan da
nufin yagaisheni yanata sallama yaji shiru gashi
kuma yaga qofa abude sai yace bari ya leqa
falon ko muna bacci ne aiko gana shiga yaga
salma cikin wani hali juyowanda zaiyi saidai yaji
an buga mai qarfe akanshi nan take shima ya
fadi qasa sumamme,.yakai wani lokaci sannan

yafarka jini sai binshi yace domin anfasa mishi
kai daqyar ya iya qoqarin daukar wayanshi shine
yakira sadiya yafada mata ita kuma tai maza
taxo da mota aka kwasosu sai asibity nanne ma
aka gane Ashe fyade akai mata.,innalillahi wa
inna ilaihirraju'un gaba daya suka sa salati
sadiya kuwa da Ahmad suna mamakin abinda
momy ta shirya amma babu yadda suka iya dole
suyi shiru,.afnan dake kwance yana fama da
matsanancin zazzabi da ciwon kai.zuciyarsa ta
qara daukar zafi.tabbas shidai beji dadin yadda
momy ta rufa masa asiri ba,yazatai mishi
haka,wata qila data bayyana gaskiya hakan ze
iyasa ya mallaki salma amatsayin matarshi.ji
yayi kawai zuciyarsa tana qara masa quna da
zugi,shin kodai ya bayyana gaskia ne!?.,Habib
ne yataso jikinshi yana karkarwa yaqaraso
yazauna a bakin gadon da afnan yake.'ya dafa
qafarsa zuciyarsa kamar zata buga yana fadin
afnan ko kaga fuskar wanda yaima salma
wannan mugunta?pls idan kaganshi zaka iya
ganeshi!?nayi alqawari ko dan gidan uban waye
sainaga bayanshi tinda ya cutarmin da
salma!kuka ne ya kubuce masa tare da cewa na
shiga uku shikenan an lalatama sister na
rayuwa.innalillahi wa inna ilaihirraju'un",momy
ta dubi aljh tace dashi inaso sadiya taje ta taya
yara zama kafin mu koma gida yanxuma nace
tabi Ahmad su tafi,aljh yace ba matsala,ta dubi
Ahmad tace yakamata kutafi dan dare yayi sosai
anbar yara a gida,tashi kawai sukayi suka fice
ba tareda sun CE komai ba.,momy ta biyo
bayansu sukai sallama ta wuce wajen
salma,.Habib yasake maida dubansa kan afnan
yana qoqarin sake yimishi magana,.sai gani
sukayi yana wani miqewa yana nadewa jikinsa
yasake dafewa kamar wuta gaba daya sukayo
kanshi kar kuso kuga rudewa wajen Abba da
ummanshi.Habib ma yadan tsorata da ganin
yadda yakeyi.,dan haka da sauri ya miqe yace
Abba bari akira Dr.dasauri yafice sai gashi tare
da Dr umma dukta rude gani take kamar dan
nata mutuwa zeyi.harta fara kuka,Dr yayi masa

wata allura sannan yace su samu towel da ruwa
su dinga jiqawa suna goge mishi jikinshi
ahankali zazzabin ze sauka,.sannan akula kar
ana yawan surutu akanshi,.dan jininsa ya hau
saisun kula Dr ya fice,nanfa hankali yaqara
tashi!!,Habib ficewa yayi abinsa ya nufi gun
salma,yana zuwa yaga momy tana sallah
yazauna bakin gadon ya tallabo salma tanata
bacci saidai jikin nata har yanxu da zafi,.addu'a
yafarayi cikin ransa ya allah ka nunamin Wanda
ya keta haddin yar uwata.lallai an cutar mai da
yar lelenshi,umma ta idar race dashi yakamata
kaxo katafi gida ko,ya kalleta momy kije gida
kawai ki huta zan zauna da ita.,momy so nake
da zarar ta farka ta kwatantamun fuskar wannan
azzalumin;.momy ta girgiza kai tace habibullahi
abinda yafaru yariga yafaru,kaje gida abinka
nizan kwana da ita kuma Dr yace da wuya ida
zata farka yau,kuma kota farka ba lallai ne ta
iya wata
magana me tsawo ba.dan haka katashi kawai
kaje gida abinka.,,haka momy ta matsa masa
yatashi yatafi badon ransa yaso ba
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 11
==>Gari na wayewa sadiya ta kimtsa komai daya
kamata ta hada musu,.Ahmad yaxo yace idan
tashirya taxo suwuce shima zaije yaga yadda
suka kwana kafin ya wuce wajen aiki.sumayya
tasa kuka itama sai anje da ita taga
salma,.daqyar Ahmad ya lallabeta tareda
alqawarin anjima zai dawo ya kaisu idan anty
sadiya ta dawo sannan ta haqura,.suka kama
hanya sai asibity,suna shiga sukaga momy tsaye
akan salma suka qarasa da sauri,wai Ashe taga
tana motsi da qafarta ne shine duk ta rude wai
ko farkawa zatayi,.nan suka gaisa momy tace
suje su duba afnan rai abace sukaje badon sunso
ba,shima dai baccin yaketayi kamar
matacce,suka gaisa da umma sama sama Ahmed
yai sallama ya wuce abinsa,.sadiya taje ta
kawoma momynta abinci.sukaci sannan tatashi
taje ta duba salma ta dawo.,fitarta keda wuya
saiga Habib yaxo ya nufi qanwar tashi yna

tambayar momy ta farka kuwa,tace tadai dan
motsa yau da safennan,inaga da alamun
sauqi,likita yace babu wata damuwa zata tashi
cikin ikon Allah.yace ya afnan dinfa.tace shima
ba laipi kaje kadubashi mana.momy tayi tayi
yace shidai agaisheshi koyaje tinda ba magana
zai masa ba ai ba anfani,.ranar dai daqyar momy
tamatsa masa yatafi office yana maqale da
qanwarsa ko zaiga farkawanta amma shiru
hakadai yadaure ya wuce.,duk wannan abin da
ake inna bata sani ba.,aiko rufayda ta fakaici
idon sumayya ta salale sai gidan inna, tana zuwa
ta tadd inna a Palo taruga aguje ta fada jikin
inna tana haki,,inna tace yau naga arziki yannan
karyani zakiyi,daga ina kike haka kamar an
jefoki kodai kinyo tsokana ne aka biyoki.,tace a
a inna gudowa nayi sumayya bata sani ba nasan
zata iya biyoni shiyasa naketa gudu nasan
zataina nemana na barta ita kaidai.inna tace oh
kudai Baku rabo da shiririta.to ai yanxu zakiga
tabiyoki., ta dago kai a a inna ai bata isaba
tinda momy batanan kuma Khalid yana bacci
bazata fito tabarshi ba.,inna tace ina Maman
taku taje bayan jiya tabar nan!?rufy tace ai
tinjiya damuka koma gida bamuga anty salma
muna shiga dakinta mukaga jini a towel dinta
Ashe an yankata ne da bamanan shine momy ta
fita itama taqi dawowa aunty ne ma tatayamu
kwana shine....ai tuni inna ta hankadeta daga
jikinta takai mata duka ban gane an yankata ba
dan ubanki wani irin magana ne wannan ni zaki
kawoma shashanci.,rufy ta zumbura baki tace to
shine zaki dukeni ni gidama zan tafi abuna"inna
ta ruqota yanxu ina salman take?! Taqara turo
baki toba nace miki an yankata ba;,gaban inna
ya yanke ya fadi lallaima yarinyannan da gaske
take ko kuwa,.dan haka taqara jefo mata
tambaya! to ina mamanku tace ai tin jiya bata
dawo ba!,inna tasa salati innalillahi wa inna
ilaihirraju'un. Inna tayo waje tna qwalawa husna
kira!husna husna ta nufi sashensu,.momyn husna
ne tace ke bakyaji inna na kiranki husna tace ni
walh momy kinsan kiran inna yanzu haka ba

wani abin azo aji bane.,saiga inna tashigo
agigice ta miqa mata waya tace kirawomin
abubakar yanxu rafida tazo take cemin wai an
yanka salma wai mamansu ma bata kwana a
gida ba.,safiya tace wani irin an ynkata
kuma.husna ta kwashe da dariya tace umma kinji
ko yanxu shirmen rufy zaki kama,.inna tace
atafaf sai ankira mata abubakar.,husna ta kira ta
miqa mata, yana dauka inna bata bari sun gaisa
ba tace bukar
meyafaru da salma ne?!shiru yayi yana tunanin
waye yafadama ina abindake faruwa.tace kayi
shiru ina sauraronka kafadamun abinda yafaru
da salma.kame kame yafara inna..walh..inna
wayace miki.tsawa taimasa taredacewa zaka
fadamun kosaika rainamin wayau kodai salman
ta mutu ne da gaske.,yace a a inna bata mutuba
walh suna asibity tamaji sauqi inna ki kwantar
da hankalinki. Kuka inna tasa da salati shikenan
Ashe gaskiyane an kashe salma ba ason
fadamunne magana yake mata amma kojinsa
batayi duk. ya birkice gashi akan hanya yake
zaitafi asibity ba shiri ya jiyo yayo gidan Inna.,
husna da mamanta sunyi tsarko tsarko suna
kallon inna cike da mamaki.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 12
==>Zama tayi dirshan tana tafa hannuwa tana
cewa kungani ko yrinyar nan nasan haka nan
kawai bazatazo ta fada wannan maganar a
banza ba. Nasan ba hakanan ba akwai wani
abinda ake boyemin.,husna tace inna wani Abu
yafaru da salman ne?!tace gashi kuwa abubakar
yacemin suna asibity to da wuya idan salma tana
Raye., hjy safiyya tahau salati tace inna barida
asake kiranshi aji!;sai sukaji sallama abubakar
ne yashigo da sauri yayogun inna yana fadin
inna bata mutu ba tashi muje nakaiki ki ganta
.,tamiqe da saurinta tayo waje yabiyota
abaya,.husna tafito a guje tana fadin Abba nima
zanje kujirani Abba wai salman batada lapia ne?!
yace wai waye yaxo yafadama inna ne,.husna
tace rufy CE taxo tace mata wai an yanka
salma., murmushi kawai yayi yace allah ya

shirya jeki dakko hijabinki mutafi.,dasauri taje
da dakko suka fice akabar hjy safiyya a gida.,ita
kuwa rufy tuni ta sulale tai gida abinta., basu
tsaya ko inaba sai asibity.,suna shiga momy
saida ta tsorata da ganin inna amma ta dake
tace inna waye fada miki muna nan?!tace ban
sani ba an bari saita mutu sannan agayamun
ko.tace yi haquri inna walh tin jiya hankalinmu
be natsu bane,. Inna taqarasa gun salma tana
fadin oh
ni zuwaira meya samarmin salma ne!alhj kam
juyawa yayi yanufi gun afnan yana shiga yaga
dakin ba kowa mamaki ya kamashi yawo waje
sai suka hadu da hjy tafito daga toilet tayo
alwala.,yace ina afnan din?!tace ai yana ciki
baka shiga bane yace yanxu nashiga banga
kowaba tace wani irin bakaga kowa ba muje
nabarshifa yana bacci,suka shiga tare hjy taga
wayem tasaka salati tace alhj ina yanufa ne?!
sukayo
waje arude tai hanyan word dinda salma take
yace dawo karkije tare mukaxo da inna yanxu
kinazuwa hankali zai qara tashi murasa yadda
zamuyi da ita,.tace saida nace
ma sadiya tazo tazauna dashi amma ashe bata
xoba,.yace yanxu taho muje inyaso daga baya
saimu kirasu awaya mugaya musu abinda ke
faruwa. Da sauri sukai mota suna tafe suna duba
hanya, nan bangaren salma kuwa motsawa
tafarayi gaba daya sukayo kanta suna
tsatstsaye.Salma kuwa jitake kamar awani
duniyar take jikinta duk inda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0