Showing 6001 words to 8992 words out of 8992 words

Chapter 3 - Dan Alhaji Book Compelet His excellency

26 Aug 2026

128

alhaji
ba karamin mai kudi bane amma hakan bai sa zuciyarsa ta karaya yaji tsoron fadin abin da
yake tafe dashi ba suka gaisa yace na zone na sanar da kai cewa dan ka safuwan ya yiwa ya ta
fade saboda haka har ciki ya shiga zirbir Alhaji ya mike yace au ta haka kuma ka bullo? kana
ganin hakan zai sa na yarda ya aure ta? to tsaya na gaya maka har yanzu ina nan kan bakata
ka nemi wannda ya yiwa yarka ciki tun da wuri kuna sakin yayan ku kamar awaki sai sun dauko
muku abin kunya ku rasa yadda zakuyi ku ringa kame kame idan kun sami warsali sai ku lika
masa kawai in so kake a taimaka maka a baka kudin dazaka zubar sa a baki ba sai kazo kana
soki burutsu ba duk wannan maganganun nasu kamar da almara da yake malam nasiru yana
tsaye jikinsa sai tsuma yake dan tsananin bacin zuciya tashi yayi ya dauko kudi masu yawan
gaske dan a kalla za suyi dubu dari biyar ya mika wa malam nasiru ya fisge ya yayyaga su ya
watsa wa Alhaji yace karya kake kace zaka siyi mutuncin yata baka da kudin da zaka girgizani.
.
"hmmm toh mata masu kwadayi a kiyaye,cikin zafin nama yayi kan malam nasiru ya ce kan har
ka isa ka zo har gidana kaci min mutunci hajiya bilki data shigo taga Allah yayi kan mallam

nasiru ta shiga tsakanin su da sauri shi ko nasiru ko zagesu Alhaji yaci gaba da fada sai naga
wanda ya tsaya maka a garin nan ko wayene wallahi baka isa ka jada niba kawai talauchi yana
damunka zaka zo kayiwa mutane hauka ga kanan babban mahaukaci kana ganin yata ko ta
rasa wanda zata aura zata auri dan kane? zan bari ta saurareshi ne kaine baka isa da danka ba
amma nina isa da yata banza shashasha banZa, ya ringafizgewa yana ki bar nina nuna masa
matsayina ta juya tace da mallam nasiru dan Allhah fita kayi tafiyarka kayi hakuri ya fita yana
cwa da kin bar shi ya dau raina tunda bani da galihu ta zaunar da shi tace kaga abinda nake
gaya maka ka barshi ya auri wacce yake so kaga yanzu ya jawowa mutane abim kunya yace au
ke kin yarda shi yayi mata?
.
kunya kuma su suka ji tunda ba a jikin sa cikin yake ba duk abinda namiji yayi adone kuma sai
na dau mataki a kansa zai sa yazo har gida yaci mutunci na sai na sa an daure shi ya raina
kansa hajiya bilki tace haba yallabai a cuce shi a hana shi kuka kasan fa duk abinda ya fada
gaskiya ne kawai dan bashi da kudi a danne masa hakki, a fussace yace ke tunda kina da kudi
basai ki tsaya masa ba wannan ai maganar banza ce kina ganin abinda mutum nan yayi min ya
nuna kudi a kaaa an yaya gasu gutsi gutsi baza su taba moruwaba tace ai bai rama ba na riga
na cuceshu ya harzuka yace walllahi ran ki zai baci saboda tashi ki ban waje ya sake daka mata
tsawa ta mike ta fice ya zauna yana ta kunfar baki yana hada gumi yana ganin tunda yake
bawanda ya taba ci masa mutunci irin wannan zaune suke a majalisa suna ta shewa duniya tayi
musu dadi mallam nasiru ya hango dan marakin zuciyarsa ta kuma yi masa zafi tafiya yake
kamar zai fadi har ya karaso kusa da inda suke ya tsaya jikin wata bishiya da aka sare cikin
daga murya yace kai safuwan wainwayo yayi da sauri kiran da yaji kamar daga sama ganin
malam nasiru yayi a tsaye yana ganinsa ya taso cikin faduwar gaba haka kawai yaji bugun
zuciyarsa yana karuwa.


** DAN ALHAJI 8**
.
Yana karasowa inda yake ya sunkuya zai gaishe shi yace dakata daga wajen ubanka nake naje
dan mu sami masahaal akan abinda kayiwa rufaida har ciki ya samu shine ya nuna min bashi
da mutunci kafin ya sake wata magana safuwan yace ya za'ayi kaje wajen sa o shi yayi mata
cikin?? malam nasiru yace rashin kunya zakayi min har kana da bakin fadamin wannan
maganar yace an fada maka kai kake niyyar zagin ubana to wallahi kar ka yarda ka zagar min
uba yace idan na zage shi me zakayi? yace rama masa zanyi uba bai fi U.
.
kafin ya karasa mallam nasiru ya kai masa mari fau!! yan majalisan ganin haka suka taso da
sauri shi ko safuwan ganin haka yana juyowa shima ya kai masa wani wawan mari anan da nan
mallam nasiru yayi sauri ya kauce kaucewar da zaiyi yaci tuntube ya fada kan wata reshen
bishiya yana fadowa kansa ya fashe kafin wani lokaci mutane sun taru kowa na fadin albarkacin
bakinsa,wasu nace wa shi ya tura shi wasu nacewa tuntube duk yabi ya rude ganin halin da
malam nasiru yake ciki nunfashin sa sama sama wasu na cewa ya mutu wasu na cewa da
ransa aka dauke shi akayi asibiti duk wanan abinda yake faruwa akan idon iyatu a kusa da
gidan su rufaida take aiki gidan wani wai Alhaji kabiru tana gani malam nasiru ta dauka fa da

sauri ta nufi gidan sa tana shiga ta tarar da habiba zaune tana bawa kamal nono ta labarta mata
batasan lokacin da ta ajiye kamal din ba ta dauki mayafi bata tsaya daukarsa ba tayi waje da
gudu ba takalmi rufaida ta rufo mata baya suka bat iyatu a tsaye yaro an dagwar dashi yaga
fitar yan gidan su ya daga ido yaga baisan iyatu ba ya barke da kuka tasa hannu ta dauke shi ta
ringa rarrashin sa yaro yaki bi sutayi da shi suna isa wajen da abin ya faru suna kokarin tsallaka
titi lokaci da ake kokarin sa shi a mota jini yana tsituwa habiba ba tare data duba titi ba ta
tsallaka mai mota yana tayi mata horn rufaida tace wa ummi ga wata katuwar mota nan tsaya ta
wuce ina motar nan tazo tabi ta kanta take ko shurawa batayi ba.tab!
.
Ana wata ga wata ga kuma wata Allah ya sawwaka dai,ana barin wajen da aka sa mallam
nasiru a mota kallo ya koma titi gawar habiba kwance ita ko rufaida tunda ta kwallara wata uwar
kara ta nufi wata hanya (abinda likita ya fadi ya tabbata) mutane suna ta habiba ba wanda ya
kula da ita iyatu na karasawa da kamal a hannunta taga abinda ya faru jikinta ma rawa yake
tana ta kuka tana cewa itace matar mutumin nan dya fada kan bishiya mutane sunyi jugun
jugum sai ga motar data dauki malam nasiru ta nufi gidansa dashi kafin su karasa asibiti ya cika
a ranar mutane unguwar da dukkan wanda abin ya faru a idonsu koya jiyo labari ba wanda bayi
kuka ba alhaji kabiru ne komai ke hannunsa banda kukkan ba abinda yake shi da matarsa sun
shaku sosai anyi zaman mutunci aka sitirtasu aka sallace su aka kai su makwancinsu bayan
dowowarsu ne kowa ya nutsu aka tuna ba'a ga rufaida ba mutane da yawa sunce tare suke
lokacinda abin ya faru iyatu ce ta bada shaidan hakan kmal sai kuka ya ke yana dube dube
mutane yana neman uwarsa gashi ba'a ga yayarsa ba karamin tada hankali mutane yake ba
alhaji kabiru ne ya dauke shinyayi waje dashi yana rarrashinsa har bacci ya daukesa jikinsa yayi
zafi sosai saboda kukan daya dade yanayi Allahu Akbar! Alllah ya jikan malam nasiru da
malama habiba
.
Gashi ba wanda inda yan uwasa suke ba irin bakin cikin dasu alhaji kabiru da abokan aikin sa
ba suyi ba rufaida ko jin wanda ya ga mai kama da ita ba'ayi ba mutane unguwa sunce sai sun
dauki mataki akan safuwan wasu nace wa abar shi da Allah tunda yanzu ina mallam nasiru da
mai dakinsu da yar tasu da abin ya faru saboda ita wannan kawa ibtila'i ne daga Allah yan
sanda ko tunda abin ya faru suka tsar keyar safuwan Alhaji duk ya rame yayi baki hajiya bilki ko
tunda taji abin daya faru da iyayen rufaida bata cikin hayyacinta tana kwance a asibiti jininta ya
hau sosai safuwan ko in ba kyakyawan sani kaya masa ba baza ka gane shi ba yan sanda sun
hana ganin shi ko Alhaji ma sau daya ya ganshi.kamal har ya fara sabawa da mutanen gidan
alhaji kabiru ba irin sabon da basu yi da Alhaji ba barcine kawai yake rabasu kullum zai tafi
kasuwa sai da dabara suke rabuwa wani lokacin ma boye shi akeyi sai nono ko dama ba'a kara
bashi ba tunda dama ya isa yaye gashi Allah ya jarrabi Alhaji kabiru da hajiya naja son sa Allah
ne ya basu dama basu taba haifuwaba kusan shekara ashirin da aure Allah bai basu haifuwa ba
yaro yasake wani girma da wayo Allahji muazzamu duk wa babba wanda yasan mai fada ajine
ba wanda bai gani ba akan a bashi safuwan hakan ta gagara saboda duk wani abin da yake
makama da shi gaba da gabanta Alhaji kabiru yafi shi idon ko batun kudi ne yayi masa fintinkau
ba yadda baiyi ba akan suyi masahalaha da alhaji kabiru abin yagagara yaune ranar zuwa kotu
duk wani wanda abin ya shafa ba wanda bai halattaba yan kallo ko kamar kasa ba wanda ke jin
tausayin safuwan ko mahifinsa kusan mutane unguwar su murna suke suna cewa ai dama gaba

da gabanta duk iskancin da yaron kayi ubansa baya kwabarsa.
** DAN ALHAJI 9**
== == == karshe == == ==
.
Komai yayi daidai dan tunda abin ya faru ko kare a cikin unguwar ba wanda yaje masa jaje
hakan yan uwansa wannan abin ba karamin tayarwa da alhaji muaZzam hankali yayi ba duk sai
yaji ya tsanni halayensa yasan shi ya jawa kansa halinsa na wulakanta talakawa ga irinta nan
tun daga yanzu hatta yan uwansa sun tsane shi lokaci daya ya gane kuskuransa ga kuma dana
sani da yake tayi akan malam nasiru ga shi cikin lokaci kankani ya bar masa duniya gashi ya
rataya akan dansa kai! duniya abin tsoro ce daga wannan lokacin yasan lallai ya yarda kaki
naka duniya taso shi kaso shi duniya taki shi gashi dai ta faru akan Alhaji muaZzamu ya gani
tun kafin aje ko ina duk kowa ya natsu ana sauraron fitowar mai shari'ah waje ya cika makil can
tsayin wasu yan mintuna sai ga shi mai shari'a ya fito kowa ya tashi ana fadin kotu ya zauna
sannan kowa ya zauna waje yayi tsit ba wanda ya sake ko tari sai can ga wani mai sayar da
doya ya doso get din kotun ganin mai gadin baya wajen ya zagaya ya hango mutane da yake
babbar kotu ce wajen kotun biyar ce ya fito yana a sayi doya wani mai tsaron kotu number 2
yace ka bar wajen nan ba wajen talla bane mai shari'a ya shigo banza yayi masa yaci gaba da
fadin a sayi doya mai shari'a ya daka tsawa yace waye mai mana tallan doya anan wai?
.
yan sanda sukayi kansa da yake mai taurin kai ne sai ya zagaya yaci gaba da tallansa mai
shari'a yace aje a shigo da mai doyar nan b bata lokaci suka cika aikin su kafin su shigo dashi
ya tsaya zai yimusu taurin kai ya sha kulki kotu mao shari'a yace kai na ce maka nan wajen talla
ne kuma ba anje an yi maka magana ba? saboda kai dan taurin kai ne kaki maza ku ajeshi sata
daya ya durkusa yace dan Allah yallabai kayi hakuri yace an kara maka sati biyu ya sake cewa
wallahi talla na fito ban barwa iyalina na komai ba yace sati uku shigo ku tafi dashi ya tsaya ya
sake cewa dan Allah ayi hakuri alkali yasake cewa idan baka shige ka tafi ba in ka sake
magana sati hudu ya sake cewa in kun kulleni yayana da matata zasu shiga damuwa alkali ya
sake cewa kar ka kara magana sai ko cewa yayi tunda ka dauke ni ta karkarewa yai ya ringa
cewa asai doya! asai doya! asai doya! ba wanda abun bai bawa dariya ba amma ba hali mai
shari a ya mike yana cewa ya shiga cember aka yi gaba da mai doya a na ganin mai shari a ya
tashi mutane suka shiga dariya har da tsuntsire wa shi kansa alkalin da ya shiga camber
fadawa yayi kan kujera yana dariyar mai doya yace lallai wannan dan iskan kauyene bayan
komai ya lafa an bar kowa yayi dariyarsa ya gyatsr mai shari a ya sake dawowa yaje yasa akayi
tsit aka kira wata shari a sannan sai tasu safuwan lauyan malam nasiru mai suna mustafa
dauda sai mai kare safuwan shine ya mike mai suna bala ali aka shigo da safuwan alhaji
muazzam rudewa yayi ganin muguwar ramar da dansa yayi bashi ba har sauran mutane da
suka san shi sun san yana cikin damuwa mai tsanani mai sharia yace ina safuwan?
.
yace gani yace kotu tana tuhumar ka akan silar mutuwar mallam nasiru da batan yarsa wacce
kayiwa fyade kayi mata ciki" yayi shuru mai sharia yace kotu tana sauraron ka yace a gaskiya
nasan ni nayiwa rufaida fyade a sakamon yaudararata da abokina sulainman yayi yaje gidansu
yace bani da lafiya duk dai yasan maganganun daya gaya mata ta yarda da hakan ta amince
akan inta sami lokaci zata neme shi a waya ya dauketa ya kai ta ta dubani muna zaune ta bugo

masa waya ta sanar da shi inda zasu hadu ni kuma naji haka ni da mubarshir muka sami lemon
kwalba muka sa kwayoyi muka bata shine nayi abinda zanyi da ita ba tare da sanin taba ban
sani ba ko a lokacin cikin ya shiga lauyan mallam nasiru ya mike ya roki ai maaa uzuri yayi wa
safuwan sasu tambayoyi aka basa lauya mustafa yace mallam safuwan ina ganin zaka fi kowa
sani ina ma ba naka bane kai kasan yadda ka same ta? yace a gaskiya a cikakkiyar budurwa
na same ta bata taba harka da wani ba mai sharia ya dakatar dasu yayi ya dan rubuce
rubucensa yace an gama da wannan yace sai tuhuma ta biyu maibya faru tsakanin ka da
mallam nasiru? yace tsakanina da mallam nasiru yazo ya same ni a majalisa mu muna zaune
muna hira law mustafa ya sake mikewa yace da kai da wada wa? lauyan safuwan ya mike yace
ai wannan tambayar bata cancanci wannan lokaci ba law mustafa yace ai ko dole ne ya lissafo
wadanda suke wajen dan dukkanin su muna bukatansu anna law bala ali yace ba lalle ne yasan
su gaba daya ba law mustafa yace akan me bazai san suba bayan kullum tare suke law bala
yace ina rokon kotu ta duba wannan tambayar bazai yiyu ya iya lissafo suba saboda yana cikin
rudani law mustafa yace ba wanda zai manta tunda tare suke shedancinsu da abokin tsiya dana
arziki ba'a nemansu mai shari'a ya buga abin hannunsa yace kotu tana san safuwan ya lissafo
abokansa dake wajen kuma kotu nasan su bayyana nan da mako biyu safuwan ya fara
lissafosu sulainman,auwal,musbahu,nura,ali,da mubarshir habib
nurandi,hashim,muhannai,auwal,musa da sunusi nasidi kai harta ni abba sanda ya kirani yace
suke wajen.
.
ci gaba da yadda ku kayi da mallam nasiru bayan ya kirawo ni na durkusa zan gaisheshi yace
bashi ne ya kawo shi ba daga wajen ubana yake ya sanar da shi abinda na yiwa yarsa amma
da yake bashi da mutunci sai ya ci mutuncinsa nace shi yayi maka? ai bashi yayi mata fyaden
ba gurina zakazo kuma wallahi har ka yarda ka zagan min uba shi ne ya kai min mariya mare ni
na juya zan rama........
safuwan yasa kuka mai karfi sannan yaci gaba da cewa ina kai masa mari ya kauce yaci da
baka ya fada kan bishiya kan sa ya fashe muka dauke shi mukayi asibiti da shi kafin mu karasa
ya mutu kukan da yake ya sake tsananta ta cikin shashshekar kuka yace wallahi bani na kashe
shi ba alkali yace ya isa sai kuma tuhuma ta uku ina rufaida? ya shiga yin kuka mai tsanani
marar misaltuwa yace wallahi bani da masaniyar batan ta kuma har ga Allah nima inaa bakin
cikin rashin ganinta kuma ina addu'ar Allah yasa a gan ta dan ni har yanzu son tada kaunar ta
suna nan a dashe a zuciyata duk wannan abu da ya faru Allah yayi shi ya faru kuma nine sila
mai shati'a yace na daga shari'a zuwa ashirin da uku 23 july a koma dashi gidan maza da sauri
ya dafe kansa da hannunu biyu lokaci guda ya ji wani bugun zuciya kafin yan sanda su karaso
inda yake har ya fadi kasa babu wata gaba da take motsi a jikinsa lokaci daya alhaji shima ya
kwalla wata kara shima ya fadi kasa tsawar ce ta gigitani biron dake hannuna ya fafi
kasa.ALHAMDULLILAH
shin za'a ga rufaida kuwa? idan an ganta a wani hali za'a sameta?, shin ya hukunci safuwan zai
kasance?
ku saurareni a littafi na biyu da kuma littafina mai fitowa nan gaba mai suna..........
,
GODIYA da yabo sun tabbata ga Allah subahanahu wata ala mai kowa mai komai tsira da
aminci su tabbata ga annabi muhammad (s.a.w) da alayen sa da sahabbansa sa masu girma

da daraja.
.
KARSHEM DAN ALHAJI LITTAFI NA 1 SAI KARASHEN ZUWA MASU MAKONNI IN MAI
DUKKA YA KAIMU
.
Jinjina ga marubucin wannan littafi M. A Gana, Allah yakara basira..
.

sai ni kuma jabeer rabi.u idris dana kawo muku ke cewa ku huta lafiya

whatsapp 07034488635..........

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0