Showing 12001 words to 15000 words out of 22948 words

Chapter 5 - Nahuce Book 1 Complete Writing by Sumayya Abdulkadir Takori.doc

a motar gidan sa zuwa makaranta, in an sauke su Safwan itama a kaita har Cologne, karfe 6 azo a dauketa.
Zaman ta da iyalin Ambasada Shehu kadaran-kadahan, rayuwa ce ta ba ruwan kowa da kowa kuma kowa yana da abin yi da zarar gari ya waye, daga nan kowa zai kama gabansa wajen neman ilmi masu aiki su tafi aiki, wato Nene da Daddy, yaran duk a kai su makaranta kuma sai yamma suke dawowa a tare, idan direba ya fara dauko Raheenah sai ya zo ya dauki wadanda ke cikin gari, Frankfurt.
Akwai mahaifiyar Ambasada a gidan da suke kira Yafendo, kusan da ita jinin Raheenah ya fi haduwa duka gidan, sabida tana da halaye da dabi'u irin na Dadar ta. Su murza goro a magogi, kadin auduga, yawan girki, sannan bata cin girkin kowa ita take dafa abun ta na gargajiya, kullum in ta dawo makaranta tana son hira dakin Yafendo take tafiya, in kuma tana da karatu ko assignment to tana dakin ta. Safeenah jinin su bai hadu ba sam, saboda ta faya kishi, yadda take ita kadai mace a gaban iyayenta rana daya Daddy ya kawo wata tsarar ta ya ajiye musu a gida don kawai yana uban 'yan Najeriya a Jamus.
Gaisuwa kadai ke shiga tsakanin su da Safeenah, dakunansu na kallon na juna amma ba mai shiga harkar kowa, ita kam Nene akwai faram-faram kamar mijin ta, tana aiki a Frankfurt Airport. Amma bata jan baki a jiki, sama-sama dai, kowa yayi zaman kansa.
Babban abokin ta a gidan kam auta Ahlan ne, da suke yawan haduwa a dakin Yafendo. Abinci ba matsala bane a gidan, duk abinda kake so akwai a kicin in bazaka ci wanda kuku ya girka ba. You are free to cook. Wannan sune sabon family din da Rahinah Omar ta tsinci kanta cikin su. Tana kuma jin dadin zama dasu da dukkan zuciyar ta, musanman halayen su na rashin sa ido. Kowa a gidan goal-oriented ne.
****
Tayi sallama a dakin Yafendo, ta sameta tana kadin auduga, Yafendo tayi mata murmushi ta ce "har an dawo? To ga kwadon rama nan na ajiye miki, duk sanda muka je gida nake yo guzurin abuta busashshiya mai yawa in aje, in naji kwadayi in jika abata ta sha kuli kuli shikenan".
Ji tayi wani mugun yawu ya tsinke mata, tsabar how eager ta zama ga cin ramar, ta ja kwanon da sauri ta soma aikawa cikin ta.
Yafendo tace "bani labarin ki mana jikata? Iyayen ki 'yan wane gari ne?"
"Iyayena 'yan Girei ne Yafendo, amma ban taba ganin su ba sai a hoto, sunan Babana Malam Omar Modibbo, mahaifiyata Bingel ake ce mata bansan sunan ta na gaskiya ba, duk sun rasu ina karama a hannun kakata na girma, a sani na ita zan iya kira iyaye na saboda ban san dadin kowa ba sai nata".
Yafendo tace cikin mamaki "Girei ta Adamawa?" Tace "nan fa""mun taba zama ci rani a garin nida miji na kasancewar sana'ar kiwon shanu yayi, gari ne mai dadin zama, yaya sunan Kakar ki? Don akwai Umaru Modibbo dana sani a garin mai mukamin Sarkin Fulanin Girei aboki ne ga Baban Ambasada domin yana sayen shanu wajen sa".
Cikin tsananin faduwar gaba Rahinah ta ce "har yanzu 'yan uwan sa suna Girei?""Eh toh bana ce ba, tunda mu zaman dan lokaci muka yi a garin, mun san shi a matsayin sarkin Fulanin Girei, amma yaya sunan Kakar taki?""Sunan mu daya, Rahinatu, sunanta aka sanya min. Ana kiranta Dada""ai ko dai sune wadanda na sani, ita Dada tana sayar da daudawa da man shanu kuma na kan saya a wajenta, kuma a lokacin da na santa ba Umaru ne kawai dan ta ba, tana da wasu yayan biyu, ta taba gaya mun Daya yana Kaduna da iyalin sa tunda ya tai karatu birni ta rasa shi, daya ta mutu wajen haihuwar Farko, amma dai na san in aka je Girei zaa samu cikakken bayani a kan su tunda sarkin Fulani ba boyayye bane, to amma kin ce a garin Adamawa kika girma, su kuwa a Girei na san su" da sauri Rahina ta mike tana fadin bari in nemo miki hoton Dada ki tabbatar min idan ita ce don Allah Yafendo""wannan abu mai sauki? Idanun nan nawa duk yawan shekaru da tsufa ras suke. Ba abinda bana ganewa" kafin ta rufe baki Raheenah ta fita a dakin.
Ta jima tana bincike a cikin kayan ta, ta hargitsa komai na dakin ta, kafin ta samo hoton su ita da Dada tun tana karama, tsabar dadewar hoton ma na farar kala ne. Ta dawo ta kawowa Yafendo, gabanta na wani irin faduwa da fargabar abinda Yafendo zata ce.
Tsohuwar ta kura ma hoton ido, kafin tace.
"Wannan Rahin ce, tabbas Rahin ce babar Ummaru,,,," Rahina ta saka kuka tace "don Allah ki kai ni garin in nemi dangina, Dada bata taba gaya min komai a kan su ba, banda cewa da tayi iyaye ne sun mutu, itama daga baya ta rasu. Nikadai ce bani da kowa a duniya.....".
Yafendo ta kamata ta rike tace "daina kuka 'yar nan, insha Allahu da kaina zan kai ki har garin Girei, kuma zan sa Ambasada yayi bincike mai yawa idan mun je gida, duk shekara muke zuwa ganin gida, yanzu bamu jima da dawowa ba amma da zarar zamu je har da ke zamu tafi, ki kwantar da hankalin ki, kinsan 'yan bokon nan ba abinda basa iya bincikowa".
Da haka ta samu ta lallashi Rahinah, suka yi sallama ta koma daki cike da zullumi.
A daren bata yi wani isashshen barci ba sabida taraddadi da ya cika ranta, ashe tana da rabon ganin wanda zai ce ya san wani nata ma bayan Dada? Excitement ya cika zuciyar ta, ta dokantu shekara ta zagayo ta bi iyalin gidannan Najeriya.
Washegari da safe ta yi shirin makaranta, ta hada tea a dining din kitchen zata sha, kawai sai taji zuciyarta na tashi kuma ba abinda take so sai ramar Yafendo.
Da sauri ta suri jakar ta ta nufi dakin Yafendo. Ta idar da sallahr walha kenan, ta shigo dakin kamar an jefo ta, "Yafendo don Allah don annabi ki sammin rama da kuli, in ban ci ba yanzun nan mutuwa zan yi".
Yafendo ta katse lazimin ta jin abinda Rahinah ke cewa, kafin kuma ta bata amsa ta hau daddaga shirgin Yafendo tana neman Ramar, Yafendo tace "Rama da safiyar nan 'yar nan? Ki tafi makaranta kafin ki dawo zan kwada miki, yanzu ki nemi ruwan dumi ki zuba a cikin ki""na hada na kasa sha, tashin zuciya bambita yake sa ni, don Allah ki taimakeni".
Da sauri Yafendo ta dauko ramar, tace "jona ruwan dumi a butar can" cikin minti biyar tayi mata kwadon ta bata.
Nan ta hau ci ba kakkkautawa hannu baka hannu kwarya. Yafendo tana ta mamaki a ranta, anya lafiyar ta?
Data dawo daga makaranta ma kai tsaye dakin Yafendo ta zarto. "Na kwaso yunwa Yafendo, zan samu kwadin ramar ki?' Kawai sai ta ga Yafendo ta zaro kwano a rufe ta mika mata, already ta kwada tun kafin ta dawo".
"Allah ya kara nisan kwana Yafendo nagode" ta soma ci a urunce. Yayin da Yafendo ta tsura mata ido.
Ta koma dakin ta ta sunce zata yi wanka, amma sai ta bige da kallon kan ta a mudubi, a take ta hango wasu bakin sauyuka a halittar jikin ta. Abinda ya fi daukar hankalin ta shine karuwar girman kirjinta sosai, sannan tayi wani irin fari dau! Kamar babu jini a jikin ta.
Rahinah bata damu ba ta cigaba da wankanta tana fadin mutum na kara girma ai dole kirjin sa ma ya kara girma.
Tana fitowa Ahlan ya shigo da gudu, "Aunty Rahina Nene tace wai yau baki ci abinci ba ko lafiya?" Ta ce "Ahlan ka gayawa Nene wallahi kwanan nan ban iya cin komai sai RAMA".
Ba jimawa sai ga Nenen da kanta, tayi sallama ta shigo, tace "Rahinah me kika ce a gaya min? Ban gane hausar Ahlan ba, Jamusanci ya masa yawa" nan ta maimaita mata. Tace "ke a ina kika ga Ramar?""Wajen Yafendo, tana da ita mai yawa" Mami ta tsura mata ido, a take ta hango sauyukan data ke son gani. Tace "Rahinah kina yin period kuwa?" Kanta tsaye ta amsa "ai ni rabo na da shi har na manta, amma kin san i'm too busy to notice that ba don kin fada ba".
Nene tayi mata kallon tausayi, sannan ta ce yanzu idan ramar ta kare ya za'ayi?"
"Nima ban sani ba Mami,na dai san in ina so ban samu ba mutuwa zan yi, yanzu kam na koshi sai kuma gobe in Allah ya kaimu".
Mami ta juya ta fita tana fadin "on weekends zaki raka ni asibiti, mutum baya period ai gara a duba shi a san dalili".
Cikin damuwa tace "Nene, is there any problen with that?" Nene ta dafa kafadarta tace "don't worry". Sannan ta fita.
Nene ta ce kar ta damu, amma sai ta ji ta damun, ko wata cuta ce rashin yin period din?
Nene na fita dakin Yafendo ta nufa, ta samu kujera ta zauna, tace "Yafendo ko kin lura da abinda na lura da shi game da yarinyar nan?"
Yafendo ta ce "kwarai kuwa, kallon ta kawai nake, in kuma jira in ga ko zaki kula da kiwon da Allah ya baki. Shi aure dama in Allah bai nufi karewar sa ba wa ya isa ya karar da shi? Da zata ji shawara ta gara mata ta koma gidan mijin ta ta cigaba da hakuri irin wanda kowacce mace ke yi a gidan auren ta, ba namijin da yake cikakke a komai dukkan su suna da gibi, amma yadda na lura tafi jin dadin rayuwar ta da mu a haka bata ko so a dago mata zancen sa". "Kwarai wannan haka ne, bari in je in samu Daddy muyi magana a kan ta".
Yana sauraron radio Jamus a 'yar karamar rediyon sa lokacin da Nene tayi sallama ta shiga. Ya amsa mata, sannan ta samu gefensa ta zauna.
"Ranka ya dade magana ce ta kawo ni, akan yarinyar nan Rahinah".
Ya rage sautin rediyon sa ya bata hankalin sa. "Ina zargin ciki ke gareta". Radeyon hannun Ambasada ce ta subuce kasa, tace "wallahi alamu sun gama nunawa, amma duk da haka ban tabbatar ba""kuje asibiti a tabbatar pls" Mami tace "insha Allahu, amma in ya tabbata cikin ne yaya zamu yi da ita ga karatun ta mai tsayi?" Ambasada ya nisa yace "yadda zamu yi da Safeenah, idan irin haka ta same ta".
****
Rahinah bata san me ta rako Nene yi a asibiti ba, amma tunda suka zauna a gaban likita ya kuma ce ta bashi fitsarin ta komai ya fara kwance mata.
As a medical student ta san awon fitsari na nufin abubuwa da yawa.....awon cuta ko awon ciki! Don haka kafin sakamako ya taddasu, ta yi ligib cikin tashin hankali da tararradi.
"She's two months pregnant". Likita ta fadawa Nene ita kadai, bayan ta ce Raheenah ta je reception ta jira ta. Sannan ya bata shaidar hakan a rubuce.
Nene ta yi masa godiya, sannan ta fito ta tadda ita suka tafi, a hanya take gaya mata an ga shawara (jaundice) cikin fitsarin ta.
Raheenah tayi wani ajiyar zuciya, feeling relieved. Har suka zo gida zancen rama take wa Nene, wai yanzu idan ranar Yafendo ta kare ina zata sa kanta? Nene tace "sai ki ci salad, ai shima ganye ne""amma bai da dan tsami-tsaminnan kamar na rama" murmushi Nene tayi, tace "sai a masa vineger".
Suna sauka a mota kuwa ta tafi dakin Nene cin rama.
Kwana bakwai kenan bata iya cin komai banda ramar, har yau gashi rama ta kare, babu kuma inda za'a sameta a Jamus.
Don haka tun safe take cikin kunci, haushin kowa ta ke ji, da Ahlan ya shigo yana mata surutu sai ta shige toilet ta rufe kanta don bazata iya korar sa ba.
Nene ta shigo dauke da plate a rufe ta sameta, "Rahinah yau bazaki makaranta bane? Yara duk sun fita sun barki, ga wannan ko a mota sai ki ci kada ki tsaya ci ki makara, kin dai san kina da nisa".
"Nene yau ban iya zuwa makaranta" ta fada hawaye na ciko idon ta. "Sabida me?""I'm not feeling well, sabida tun jiya ban ci rama ba, Yafendo ta ce ta kare""try this" ta fada tana mika mata plate din hannun ta.
Bata yi musu ba ta karba ta bude, salad ne Nenen ta hada mata da kanta, yaji kuli da vinegar da tumatur, cocumbrr da albasa. Wani mugun yawu ya gudana a bakin ta, ta karba tun daga tsayen ta soma ci kafin ta zauna. Amma ko loma hudu bata yi ba ta dinga kwaro amai kamar zata amayar da hanjin ta.
Tun daga ranar komai ta ci sai ya dawo, ta galabaita matuka, karfin jikin ta ya yi kasa sosai. Ambasada yace da Nene ta kaita asibiti, koda taimakon da zasu yi mata abinci ya dinga zama a cikin ta.
Suna asibitin likita ya riketa, domin yace she's 60% dehydrated. Aka sa mata drip nan take. A ranar ne Ambasada ya kira Habib a waya.
"In ka samu lokaci kazo 'Sachsenhausen Hospital' da daddare ina son ganin ka". "Insha Allah i will". Ya fada cike da girmamawa.
Karfe takwas na dare a Sachsenhausen ta yi wa Habibu Nahuche. Yana sanye da Native Hausa Attire dinsa na shadda sharaton ruwan makuba, ya kafa hula a gaban goshin sa ruwan toka mai turuwa sosai (deep grey), yayi kyau kamar koyaushe amma kallo daya Ambasada yayi masa ya gane muguwar ramar da yayi cikin watanni biyu da yayi bai ganshi ba.
A wajen parking motoci suka hadu, direba ya sauke ambasada, shikuma taxi ta sauke shi. Ambasada ya bashi hannu sannan tare suka taka zuwa dakin da aka kwantar da Rahinah. Daga ita sai Nene a dakin. Kamshin turaren sa ne ya fara shiga hancin Raheenah, wani kamshi mai tasirin da bazata taba mantawa ba....da sauri ta juya kai zuwa bakin kofar shigowa. Idanun su suka hadu, wanda hakan ya haifar da wani irin shock ga Rahinah dake kwance, domin ta ganshi ne ba zato ba tsammani.
Yayin da Habibu Nahuche ya tsura mata ido, gabadaya ta zabge ta lalace, maimakon ya zo ya ganta very healthy and jovial tunda ta samu rayuwa yadda take so? Ta karbi 'yancin ta da take ikirarin ya danne mata? Banda girman idanun ambasada da yake gani babu abinda zai sa shi amsa wannan kiran, don bai ga dalilin sa ba. Tunda komai ya kare a tsakanin su.
"To zauna mana kun tsaya kuna kallon-kallo kamar zakaru" Ambasada ya furta masa sounding fatherly. Ya nemi guri can nesa da gadon da take kwance ya zauna. Wani irin abu na hankoro a zuciyar sa, ta shiga bugawa fat-fat-fat, bai san idanunsa sun yi kewar ta ba, sai yanzu da suka ganta kwance a gaban su, hatta zuciyar sa neman fitowa take daga tsakiyar kirjin sa....shikadai ya san halin ragaitar da ya samu kansa cikin wadannan watannin biyu masu kama da jiran tashin alkiyama a gare shi.
Rahinah ta dauke kai daga kallon sa, ta mayar wani gefen daban, tunda suka rabu ko sau daya bata ji kewar sa ba. Bai bar mata wani abun tunawa a zaman da tayi da shi ba na kwanaki bakwai, banda kyakkyawar fuskarsa ta Rumawa data zauna a zuciyarta ta ki fita.
"Na kira ka ne Habib, don in sanar da kai Raheenah na da ciki na watanni biyu".
Daga Habib har Raheenah, a tare zuciyarsu tayi wani irin dokawa, ta doka ta sake dokawa ta ci karo da bango. Idanuwan Rahinah kamar zasu fado kasa.....jin maganar tayi tamkar saukar aradu a kunnuwan ta, zata rantse ko mutuwar Dada da aka gaya mata a waya bata firgitata ta ruda ta kamar abinda Ambasada Shehu ya fada yanzu ba...

Yayin da Habib, Mustapha Nahuche ya wani irin lumshe idanunsa.
Wani albishir ne zai ce ko bushara da ba'a taba yi masa kwatankwacin sa ba.
Wani irin maganadisu ya ji yana fizgar zuciyar sa akan Raheenah da abinda ke cikin ta..
The feeling is so sweet da bai taba jin mai dadi a zuciyar sa kamar sa ba...nitsatstsen SO!
A hankali ya bude idanun sa akan Raheenah, wadda ta tamke nata idanun tamau, hawaye na zirara ta gefe da gefen su.
Which means she's not happy at all, she's mourning kaddar da ta afka mata rana daya.......ta tabbata ta rasa farin cikin ta daga yau, bata ga amfanin sauran rayuwar ta ba..
Ashe dai ta yi gudun gara ne ta tadda zago..... Habib Nahuche bai shigo rayuwarta don ya fita a lokacin da take so ko yake so ba.
Kaddara bata kare tsakanin su ba, mai hada eternal dangantaka ya riga ya hada wato gamayyar jiki, wadda a yau ta maida ita matar Habib a karo na biyu har sai ta haife masa dan sa ko 'yar sa wanda take jin ba abinda ta tsana a duniya sama da kawo shi duniya...
A fili ta fada ".......bai yi sa'ar mahaifi ba, he's but selfish by nature wato mutum ne mai son kan sa da yawa (tana nufin Habib din).
Muryar Ambasada Shehu ta cigaba da ratsa mugun shirun da ya ratsa kamar daukewar ruwan sama. "My dear Son and Daughter isn't it high time you reconcile? Tunda kun ga yadda kaddara tayi daku, kowanne Da yana burin ya tashi tsakanin iyayensa biyu, broken home shine babbar matsala ga tarbiyya da rayuwar kowanne yaro, rayuwa duka 'yar afuwa ce, in kuka afuwantawa juna kuka kuma zauna kuka gano matsalolin ku i'm sure zakuji dadin zama da juna tunda har ga rabo a tsakani...".
Habibu yasa hanky dinsa ya goge gumin fuskarsa da hawayen da suka cika masa ido, wadanda yake da tabbacin na farin ciki ne. Ya dubi Raheenah wadda ta kautar da kai gefe tana jin tamkar Daddy na diga mata narkakkiyar dalma a kirjin ta da ya ce wai ta komawa auren Habibu. Ya ce "ranka ya dade ni bani da matsala da hakan in har ta amince, abinda ba zanyi ba shine sake zaman aure da ita ba tare da amincewar ta 100% ba".
Rahinah ta juyo a hankali zuwa side din da yake, a hankali ta ce "to in dai ko amincewata kake bukata to har abada bazamu koma ba, once beaten twice

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login