Showing 18001 words to 21000 words out of 22948 words

Chapter 7 - Nahuce Book 1 Complete Writing by Sumayya Abdulkadir Takori.doc

tareda Habibu ba zasu zargeta da raina musu hankali ba?
Da wani irin zafin nama ta bude murfin motar ta fice, Allah ya so ta ya saki lock din, ta leko ta window tace cikin muryar kuka.
"Allah ya isa taba ni da kayi, Allah ya saka min!".
Habib Nahuce. Bai san sanda dariya ta kwace masa ba duk da halin da yake ciki. Yace "Allah ya saka mana tare Rahinatu! Akwai mugu a duniya irin ki? Kin ci albarkacin Baby na, na rantse da sai kin kunshi wani sabon cikin a yau kin haifo su tare sun zama biyu.......". Bata tsaya sauraron mugayen kalamansa ba masu kama da sabon Allah a kunnuwan ta ta nufi titi da mugun sauri tana tare taxi.
Yohana sai ganin ta yayi taxi ta sauketa a gefen sa, ita da tace library zata shiga ta karbo littafi ta fito. In ya kirga daidai ta kwashe akwalla awanni biyu kenan. Ba wannan ne ya bashi mamaki ba sai yadda ta bude motar ta afko kamar wadda aka biyo.
"Are you okey Madame?"
Ya tambaya calmly.
"I'm okey Yohana let's go, kada ka tsaya a ko'ina sai mun isa Frankfurt".
"Is someone following us? So that i report to police?"
"A'a babu mai bin mu, kaidai ka tafi da sauri ka bar harabar wajen nan".
Ya ja motar suka bar wajen yana cewa "alright Madame, but kowanne karamin abu ki dinga gaggawar sanar da police".
Ita dai tace masa ta ji.
Sun yi nisa sosai wayar ta ta sake kara, tayi ajiyar zuciya sai yanzu ta fara samun nutsuwa data tabbatar sun fita daga shiyyar birnin Cologne. Sun kama hanyar da zata kai su Frankfurt.
Da ta duba sai ta ga 10 missed calls daga Nene.
A take ta kira ta jikin ta har rawa yake, ji take kamar Nene ta ga komai da ya faru, ita da Habibu a mota suna kissing. Wani hawayen bakin ciki ya zubo mata, ta ji ta tsani kan ta, ta tsani karatun da ya fiddo ta daga gidan Ambasada, in bata yi wasa ba Habibu na gab da sake rusa mata rayuwa.
"Nene wallahi ina cikin library ne wayar kuma na barta a mota"
"Meyasa kika je makaranta baki jira ni na dawo mun je tare ba idan zuwan ya zama dole? Kinsan Dr. Yace ki daina zirga-zirga" ta share wani uban gumi daga kan goshin ta, tace "Nene i'm sorry littafai na je amsow na clinical assignment dina, kinga ma ban samo su ba, bazan ma kara zuwa ba har sai na haihu. Zan gayawa Daddy a nemomin na saya kawai" Nane tace "better, me zan dafa miki kan ki iso?" Tayi murmushin samun relief tace "anything traditional""to shikenan zan miki tuwon alabo miyar ugu leaf da alayyahu da ganda da busashshen kifi, yayi miki?"
Wani hawaye ya bullo mata, ashe haka soyayyar UWA ke da dadi? Allah ya barta da danta itama ta bashi kauna irin wannan. Allah yasa kuma kada mutuwa ta raba su yana karami sai ya mallaki hankalin kansa ko da zata mutu. Ya zamo cewa ta gama bashi duk wata kulawa da tarbiyyar da ya kamata ya samu daga gareta.
A wannan daren, daga Habibu Nahuche har Rahina Omar, babu wanda ya iya ya runtsa. Dare ne mai matsanancin hazo, cikin watan Nuwamba, Habibu na nannade cikin bargo sanyin kasar Jamus na shigar sa, ba abinda yake so yake bukata a lokacin sai dumin matar sa Rahinah. Amma ta wace hanya zai bi ya dawo da damar da ya samu a baya? Masu iya magana dama sun ce opportunity comes only once in life! Ya bata komai, ya dade da bata komai, ya riga ya bata rawar sa da tsalle. Haduwar su a yau ta maida masa komai sabo in itsown special unique way..... girman Rahinah da soyayyar ta sun karu sun ninku sun hauhawa a zuciyar sa, ya fahimci abubuwa da dama wadanda a baya bai sani ba; Rahinah na daga cikin kasaitattun mata da samun kamar su sai an tona. Irin matan nan ne one in million wadanda duk namijin da Allah yayiwa baiwar mallakar su ya gama bashi rabin addini sa, ya gama bashi farin cikin rayuwa, da duk wani jin dadi dake cikin ta.
A yau ya amince da abinda a baya ya ki believing da gangan. Cewa zai iya rayuwa babu Rahinah, zai iya hakuri da rayuwar sa single ba tare da Rahinah cikin ta ba. A yau ya yarda ya amince rayuwar sa bazata taba zama straight ba ba tareda Rahinah a gefen sa ba. Ko zata yarda ta saurareshi idan ta haihun kamar yadda ta yi alkawari? Shi kuma zai yi komai don dawo da ita cikin rayuwar sa cikin martaba da mutuntawa, dadin dadawa soyayya mara yankewa har fiye da wadda bata tsammani. Daga wannan ranar yake bincike, wani irin bincike na yadda ake tafiyar da soyayyar mata. A rubuce-rubuce na masana ilmin psychology (self-help books and self-reflection). Ya samo wasu tips guda goma wadanda suka ce (How to keep your woman and make her love you forever). Marubucin ya ce; cikin abubuwanda zasu rike maka soyayyar matar ka sun hada da;
-work on yourself ; ka yiwa kanka self-evaluation; ka cancanci ta so ka ko a'ah?
-listen to her (and i mean really-really listen); ka saurareta akan duk abinda ta zo da shi da cikakken attention ka bata hankalin ka a lokacin da take bukatar hakan.
-learn how she prefers to be loved; ka duba abinda tafi so ka nuna mata soyayyar ka da shi.
-give her gifts (ka kasance mai yawan yi mata kyauta, kyauta tana kara dankon kauna).
-be honest with her (ka zamo mai gaskiya da kyakkyawar manufa akan ta).
-respect her (ka girmamata) and treat her with this respect.
-find creative ways to tell her that you love her (ka zama mai iya kirkirar hanyoyin gaya mata yadda kake son ta in your own special way).
-allow yourself to be vulnerable; wato ka dinga nuna mata raunin ka. (Allow yourself to make mistakes and admit to them. Allow yourself to be real and true and not hide any of yourself from her.
Don't be afraid to cry in front of her. And don't be afraid to let her cry, too.?Vulnerability allows for deep connection and bonding?in a relationship. If you can't be yourselves?in your most raw forms, how are you supposed to feel safe building a whole life together?"

Habeeb Nahuche sai ya ga cewa duka wadannan tips din da wannan masanin ya zano duk zurfin ilmin sa shi bai mallaki ko daya ba! Bai taba nuna wa Rahinah dayan su ba, yet yana blaming din ta da kasa son shi duk cancantar sa.
Ita soyayya ta gaskiya ba ta ta'allaka da appearance din mutum, but the way he demonstrates himself.
Ya yarda duk ilmin ka ilmi baya taba karewa a duniya, saidai ka dauki iya wanda zaka iya ka bar ragowar.
Inama! Inama! Inama Rahinah ta yarda ta sake bashi dama koda sau daya ne a rayuwar su???
****
A nata bangaren, Rahinah Omar, kwana tayi tunanin abinda ya faru a yau, tana mai tariyo komai dalla-dalla. Idan zuciyar jin tausayi ta kutso, sai zuciyar neman kwatar 'yanci ta hambare ta. Mutumin da bai ji tausayinta ba, ita akan me zata ji tausayin sa? Yana son ta koma ne don bukatun kansa amma bai taba tunanin ya tambayeta asalin ta ko na iyayen ta ba. Wanda ke kara tabbatar da cewa ba damuwar sa bace personal life din ta, abinda yake yimawa kawai shine a gaban sa.
Ita wannan soyayya ta Habibu ta kasa ganeta, domin ta hada biyu da uku bata bata ma'ana ba. Tana burin auren mijin da ke matukar son ta, wanda zai rungumi maraicin ta kada yayi amfani da shi ya cutar da ita, wanda zai so ta da dukkan zuciyar sa. Amma Habibu fa? Ta tabbata ba don cikin nan ba da daga ranar da ya sake ta bazai kara waiwayota ba tunda duk abinda yake so daga gareta ya riga ya same shi.
Tsaki tayi ta juya a hankali don taji dadin kwanciyar ta, sai taji gefen wuyan ta na kamshin Carolina Herrera (men) har zuwa lokacin. Abinda ya tuna mata da incidence din. Is what happened Haraam? Bata sani ba, in haramun ne tana neman gafarar Allah, domin kuwa bata da laifi, laifin ta shine kasa yi masa gardama wajen binsa tamkar rakumi da akala. "Ya salamu sallim". Ta fada a fili. Amma wani sako na zuciyar ta na gaya mata it's not haram din, tunda har yanzu cikin iddah take. Kuma abinda addini ke so a wannan tsakanin shine su yi sulhu. Sulhun da bata jin har abada zata yarda da shi.
Washegari Nene ta rakata anti-natal da suke zuwa duk sati, likita ta dubata sosai ta kuma ce baby is breach sai an gyara masa kwanciya. Haka ta daure aka gyara sannan ta karasa duba ta, tace tanaso tayi mata alfarmar zuwa dakin haihuwa tare da mijin ta, sabida suna so mata su dinga haihuwa akan idanun mazajen su, domin neman karin kauna da soyayya, jin kai da tausayi a garesu. Gashi bata taba ganin ta ta zo tare da shi ba.
Rahina dai bata ce komai ba, sai Nene ce ta ce baya kasar ne, amma in ya dawo kafin ta haihu da shi za'a shigo labour room.
Rahinah ta daga 'yan idanun ta taba kallon Nene kamar tace da ita akan me za ki mata karya! Mun rabu, short and simple. Sai ta tuna abinda Ambasada ya taba gaya musu cewa saki ba karamin abu bane a kasar jamus, and it should be abiding by German law. Don haka rufe zancen da Nene tayi kawai shine daidai.
Watanni biyu a gaba, ta shiga watan haihuwa, ta kuma gama shekarar farko ta karatun ta. Wato tsayin semester biyu. A haka take zuwa zana jarrabawa da tsohon ciki har ta kammala da kyakkyawan sakamako. Ambasada ya baiwa Nene kudi yace ta saya mata duk abinda zata bukata na haihuwa ba ruwansa da abinda Habibu zai bayar.
A daren ranar ne kuma sai ga tarin akwatuna shaqe da sitturun jarirai unisex daga Habibu Nahuche. Hatta pampas da feeding bottle sai da ya sayawa dan sa, amma ita ko tsinke bai saka da sunan ta ba. Wannan ya sosa mata rai ba don tana son abin hannun sa ba, a'a yadda ya nuna yafi son abinda zata haifa yanzu akan ta shine abinda ya sosa zuciyar ta.
"To a kan me?"
Zuciyar ta tambaya.
"A kan dalilin da nima ban sani ba!" Ta amsawa kanta a fili.
****
EDD dinta saura kwana biyar rannan da daddare suna zaune a dakin Yafendo suna cin tuwo taji damshi-damshi daga kasan jikin ta. Bata kawo komai ba sabida sabida bata ji ciwon komai ba. An ce mata kuma ciwo ake ji mai tsanani.
Amma ba'a dauki wani dogon lokaci ba ta soma 'yan mutsu-mutsun da ya ja hankalin Yafendo kanta.
"Yar nan lafiya kike yanka gumi haka?" Tayi yake tace "bakomai fa Yafendo, zafi kawai nake ji" Yafendo ta gyada kai ba don ta harda ba suka cigaba da hira. Safeenah ta shigo ta gaida Yakumbo, sannan ta dubi Rahinah tace "Nene ta ce kina da bako a falon Daddy........" amma kafin ta kai karshen maganar ta sai gani suka yi tana shure-shure. Yafendo tace "Aha! Ni na san abun ne ya zo, kika yi mirsisi ke ga jaruma. Ke Safeentu kira Nenen ku ki gaya mata haihuwa ta zo a kawomin reza". Safeenah ta zaro ido sannan ta fita a guje, kada taje ayi haihuwar a gabanta.
Nene ta fado dakin da gudunta, tace "Yafendo wace irin Reza? Ki rufa min asiri in mutu maza su kai ni, ba'a kasar mu muke ba inda ake haihuwar gida. Maza kwarara jikin ki Rahinah mu gangara asibiti, ga Habib nan yana nan ya zo sai ya kaimu tunda direba bai dawo ba har yanzu."
Tsananin halin da take ciki, shi ya hanata yin musun tafiya asibiti tare da Habibu kuma a cikin motarsa. Daga ita sai Nene a baya tana shafa mata kanta da bayan ta tana yi mata addu'a yayin da shi yake tuki cikin wani mawuyacin hali. Ji yake da zai iya da ya karba mata nakudar, kanar yadda ya zamo silar wahalar ta daga zuwa karatu.
Sun samu ganin Dr. Saliha Widad wato likitar data ke gani itace on duty, nan da nan ta karbeta akan gadon tura marasa lafiya daga hannun Habibu da ya sunkotota gabadaya daga cikin mota zuwa cikin reception. Dr. Saliha ta duba ta tabbatar haihuwa ce gadan-gadan sai ta fito tana kiran sa. Ta tambayi Nene shine mijin Rahinah? Nene ta gyada kai ba tareda ta ce komai ba, yayin da likitar tace "kazo ka tsaya tare da ita, ka ga yadda dan ka/'yar ka zai iso duniya".
Habibu ya hada kai da bango yana ce mata "a'ah..." tayi murmushi tace "ashe raggo ne baban baby, Rahinah ta fika juriya. C'mmon ka biyo ni nace". Ya juya yana kallon Nene sai ta gyada mai kai, don bata so a tsaya ana tone-tone. Ai har yanzu tana cikin zummar auren sa.
Tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki, haka ya daga kafa ya bi bayan Saliha Widad.
****

"Dada!"
Kawai take kira hadi da sunan Allah,ta yi gumi kashirban, kanta na bisa cinyoyin Habibu gashin kanta ya bazu jikin sa. Ya rike hannayen ta cikin nasa, ita take nakudar amma ya fi ta hada gumi, jikin sa har kyarma yake. Dr. Saliha na fadi tayi nishi baby ya kusan isowa. Da ta daddage ta saki nishin kuwa sai gashi ya fado tare da mabiyar sa. Ya kuma canyara kuka a hannun Dr. Saliha wadda bakin ta ya kasa rufo, shekarar ta kusan goma tana karbar haihuwa amma bata taba ganin haihuwar katon baby black beauty irin na Rahinah ba. Saidai bai dauko komai nata ba har duhun fatar sa na mahaifin sa ne.
Aka gyarata, aka gyara wajen haihuwar, aka dau baby ana gogewa da man zaitoon aka shirya shi tsaf cikin kayan sanyi, aka nannadeshi a shawul sannan aka kawo mata shi saitin kanta. Sai a lokacin ta soma dawowa hayyacin ta ta kuma ji kamar a jikin mutum take kwance. Tana so ta kalli fuskar babyn amma tana son ganin wanda ya baje mata jiki ta kanannade akai ta haihu haka. A hankali ta daga kanta, sai idanun ta cikin na Habibu, wanda hakan ya haifar mata da matsananciyar faduwar gaba. Kafin ta soma yunkurin tashi ta kuma fashe da kuka.
"Amma Dr. Widad kin cuce ni......" ta fada cikin kuka sosai, kamar Dr. Na jin harshen nata, tayi Allah ya isa da fillanci, tayi da hausa, tayi da German, tayi davduk yaren data iya. Duk akan Dr. Widad data shigo mata da Habibu dakin haihuwa. Nene tana ta bata baki kan ta yi hakuri. Shikuwa ya harde hannuwa a kirji yana kallon ta da wani irin murmushin SO. In da a ce zai iya, zai iya ciro zuciyar dake kirjin sa ya bata a halin yanzu don kawai ya nuna mata dimbin godiyar sa da soyayyar sa gareta. Bisa bashi farin cikin da wani a duniya bai taba bashi ba. Bisa maida shi UBA, bisa bashi precious gem din da kudi ko mulki basu isa su bawa dan adam ba.
Dr. Ta mika mata Babyn bayan ta gama kukan bakin ciki ta share hawayen ta, da sauri ta karbe shi tana kallo. Ba shiri ta daga ido ta dubi Habibu. Yaro kamar Ubansa yayi khaki ya tofar. Ya lumshe mata lumsassun idanun sa ya kuma daga mata girar sa daya, "eh dani yake kama ba da ke ba, kamar ya san ba kya son uban sa". Ta gatsina baki ta cigaba da kallon babyn tana tazbihi a zuciyar ta. Wata irin kauna ta da da mahaifi na keta ruhin ta da zuciyar ta. Her only relative, her only blood! Ta yaya bazata so shi sama da komai a duniya ba?
Bata yi aune ba ta ji Habib ya kashe su da hoto da camerar wayar sa.
Hararar sa tayi, duk wani abu da zai bakan ta mata ya san shi, yanzun ma Nene na bada baya ya matso gabanta, "wai sabida kin haihu gabana kike wannan kukan? Yo wane dare ne jemage bai gani ba? Bani Da na nan in ji dumin sa, kin wani kama shi kin kankame kamar ke kadai kika yi nakudarsa". Ya mika hannu, ta yi maza ta janye dan ta.
"Ba zaka dauke shi ba!"
Ya saki baki yana kallon ta da mamaki, Nene ta shigo jin sautun kukan ta, tace "lafiya? Ki bashi yaron mana ya yi masa khutbah?""Nene bazan bashi ba, da na ne nikadai, ba ruwan shi da mu ba ruwan mu da shi" Nene tace "Rahinah kin san abinda kike fada kuwa? Mahaifin sa ne fa? Yau na ji karfin hali wai barawo da sallama. Ki bashi yaron nan kafin raina ya baci akan hakan". Rahinah ta saka kuka sannan ta mika masa yaron. Ya karbeshi da wata irin kulawa tamkar ya maida shi cikin sa. Yayi masa khutbah da sunan da ya zaba masa wato sunan mahaifin Manzo SAW. Ya tauna dabino (ajwa) ya sanya masa a baki, yaron ya hau motsa dan bakin sa gwanin sha'awa, Habib bai san lokacin da wasu irin zafafan hawaye suka zubo masa ba. Ya rungume yaron a kirjin sa. A haka Ambasada ya shigo ya same su. Safinah ta biyo bayan sa dauke da kwandon abinci. Ya yi wa Habib da Rahinah "congratulations" sannan ya karbi yaron yayi masa addu'a.
Washegari aka sallame su. Suka koma gida. Tun daga ranar Habib yake zarya, sayo banza sayo hopi, duk don ya farantawa Rahinah. Amma ina! Zuciyarta ta riga ta kekashe akan Habibu, babu wani repenting da zai yi ya burge ta.
Babban tashin haankalin sa shine Rahinah ta gama iddah, gashi yayi alkawarin bazai maida ita ba da amincewa da yardarta ba, shima Ambasada bazai taba amincewa ba yayi forcing din ta akan abinda ta nuna ta gama bashi baya.
Tsayin watanni uku tana shayar da Abdallah kasancewar suna cikin hutun summer. Ta saba da yaron sosai, bata barci sai yana kan kirjin ta, har fargabar komawa makaranta take, don ta san dole zai koma haunnun mai raino. Ita kam ba wanda take jin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login