Showing 12001 words to 15000 words out of 30109 words

Chapter 5 - Masarautarmu Book 1 Compelet By Sumayya Abdulkadir Takori


karshen kowanne zangon karatu, sai kuyi sallama yau, don gobe da sassafe za'a kai su ita da
Humaira".
Fuskar Fulani ta tattare cikin rashin jin dadi, bata son a alaqanta komai na Sa'ade da 'ya'yan
gidannan, ba don komai ba sai don gudarwa kanta gori. Balle 'ya'yan Hibbani sarakan surutu,
ita kuma Hibbanin uwar tsugudidi, in taji abu to tabbata Ya Gumsu ta ji ta gama. Amma ai da
kunya tace masa bata so ya hada 'yar ta da 'yar sa, shi da yayi wannan kara ta mutuntawa in
ba'a gode masa ba akalla baza'a kalubalance shi ba.
"Allah ya kaimu"
Kawai ta ce. Sa'ade ta dago cikin farin ciki ta ce "Alan....amma inna tafi sai bayan shekara
zan dawo ko?" Cikin mamaki yace "ba kya marmarin ganin Innar ki zaki yiwa kanki fatan yin
shekara a makaranta?" Ta sunkuyar da kai a ranta tana so ta gaya masa ita Innar ce bata son
gani kusa da ita da wadannan muzuran idanun nata masu karkada mata 'ya'yan hanji, sannan
kadaici yana damun ta, banda yanzu da aka jona mata talbiin take debe mata kewa.
"Wata uku zaku yi ku dawo hutu, na hada ki da 'yar uwarki Humairah don ki ji dadin zama
kina ganin na gida a kusa da ke. Ki maida hankali kiyi karatu, ki kawo min sakamakon da zan yi
alfahari da ke, kin ji Sa'adatu?"
Ta gyada masa kai "insha Allah zan yi kokari Alan....guburo, nagode, Allah yayi maka fin
abinda kayi min".
Shi da Fulanin duka suka kalle ta jin abinda ta ce, don basu yi zaton tana da hankalin sanin

an yi mata alkhairi ta bi da kyakkayawar addua irin haka ba.
Cikin daren Fulani ta kasa barci, ba kewar Sa'ade ta ke ba, damuwar ta na hada Humaira da
Sa'ade da za'ayi ne waje daya, ta san Humaira da shegen kinibibi kamar na uwar ta zata iya jan
Sa'ade a jiki ta ji sirrin su ta fesawa uwarta. Don haka ta mike daga kwanciyar ta ta sanya hijab
kan rigar barcin ta ta nufi dakin Sa'ade. Ta yi dai-dai sai sharar barci take abinta, santala-santalan fararen cinyoyin ta a waje, rigar
barcin ta yaye can sama, gashin kanta da Fanna ta wanke mata dazu da shampoo sai sheki
yake ga santsi, sai ta ganta exactly like herself when she was twelve years of age, a perfect
replica of Bilkisu! Bata taba yi mata cikakken kallo irin na yau ba, kauyancin duk ya fara barin
jikin ta, a maganarta kawai zaka ji shi.
Ta daddage ta daka mata duka a cinya, Sa'ade ta zabura ta tashi tana sosa wajen tana
mutstsikar ido. "Haka kike kwana tsakiyar kwan lantarki sabida baki da hankali ko? Me yasa
baki kashe ba?" Sa'ade ta zumburo baki "ni ban san ana kashewa ba" "daga yau duk sanda
zaki kwanta ki kashe fitila mai haske ki bar dim, na ga alama ke kidahuma ce" Sa'ade ta
kumburo kumatu bata amsa ba. Ta dora kafarta daya bisa gadon ta tsaya akan daya, sannan ta
kama kunnenta na dama da kyau ta murde, Sa'ade ta saki tsuwwa don zafi, Fulani tace "idan
kika gayawa wani a makarantar ku ko wadda zaku tafi tare ke 'ya ta ce sai na kabari ya fi ki jin
dadi a gidannan, kowa ya tambayeki wacece ni a wurin ki ki ce ke 'yar kanwata ce, babar ki ta
mutu, kin ji ni ko baki ji ni ba?"
Hawaye na fitowa daga idon Sa'ade ta ce "na ji!".
Fulani ta sakar mata kunnen, ta juya zata bar dakin. Sai ta tsinkayo muryar Sa'ade cikin rishin
kuka.
"Amma me yasa kika tsaneni haka? Da har ba kya so a ce ni 'yar ki ce? Kawai saboda ni
Babana talakane ba sarki bane?"
Wuta ta daukewa Fulani Bilkisu, ta kasa gaba, ta kasa baya. Bata taba zaton yarinyar zata
iya yi mata wannan tambayar ba. Sa'ade tayi murmushi mai ciwo ta share hawayen ta da bayan
hannun ta.....
"Ki nemo min dan uwan mahaifina na Damaturu, tunda kinsan inda ya ke, insha Allahu zan
nesanta kaina dake kamar yadda kike so, zan koma wajen sa".
Bata bata amsa ba ta fita daga dakin, jikin ta yai matukar sanyi, bata zaci yarinyar nada
hankalin gane abubuwa har haka ba, a shekarun ta goma sha biyu, ko ta yi mata bayani bazata
gane ba, bata kin mahaifin ta don talaucinsa sai don rashin SO da zafin AUREN DOLE. Tunda
itama 'yar talakawa ce futuk! Gaba da baya, inda halacci ashe kuwa bazata manta talauci
sabida arzikin gidan aure ba.
Da maganganun da Sa'ade ta gasa mata ta kwana a ranar suna gasa mata zuciya. Shi yasa
da safe ta ki fitowa balle ta ga tafiyar ta, bata so ta karasa karya mata zuciya, bata shirya karbar
ta matsayin 'ya anan kusa ba kuma har abada bata jin zata iya idan ta tuna Hashimu ne Baban
ta. Fanna ce ta zo ta tashi Sa'ade ta taimaka mata tayi wanka, ta bata kayan makarantarta ta
sanya, tuni an fidda kayan ta zuwa mota. Tun shigar ta gidan kwana ashirin da daya sai yau ta
fito ta shaqi fresh air, daga iskar fanka sai ta A/C. Ta na ta wurga ido ko zata ga Fulani, amma
ko motsin ta bata ji ba, ta san kuma bata isa ta shigar mata daki ba bisa umarni ba. Duk ta ji ba
dadi da abinda bacin rai ya kwashe ta ta gaya mata jiya. Ta san a matsayin ta na uwa, ko me

zata yi mata bata cancanci wadannan kalaman daga gare ta ba.
Kawai sai ta kama kuka. Jikin ta a sanyaye ta bi bayan Fanna suka fita daga shiyyar Fulani,
kuyangin Fulani na ta kallon ta don su har sun manta tana cikin gidan. Da yake safiya ce basu
hadu da mutane sosai a hanya ba sai bayi jefi-jefi amma matan gidan da 'ya'yan su ko jikokin su
babu ko daya, kowa yana sashen sa. Har suka shiga dalleliyar motar da direba da dogarai biyu ke ciki, daya na tuki, daya na gefen
sa. Sa'ade bata bar kuka ba. A jikin motar an rubuta da ruwan gwal "ASKIRA EMIRATE". Gefen
hagu dogarawa suka bude mata ta shiga, kafin su rufe kofar ta kamo hannun Fanna, idanunta
narai-narai da hawaye tace. "ki ce ma Fulani don Allah don Annabi ta yi hakuri".
Fanna bata san akan me ake aiken ta bada hakurin ba, ta dai lura akwai wani babban
al'amari tsakanin uwargijiyarta da wannan bakauyiyar yarinyar. An raineta ne kawai a bisa bin
umarni, babu tambaya, don haka tace "insha Allahu zan gayawa Fulani sakon ki".
Fanna na barin wajen ba da jimawa ba Sa'ade ta hango wata kyakkyawar budurwa na
tahowa karkashin rakiyar bayi 'yammata tsararrakin ta, tafiyar ta kawai data banbanta da tasu
ya sa ta gane itace Humaira da Alanguburo yace zasu tafi tare wato 'yar autar sarki. Duk da
kayan makaranta ne a jikin ta irin wadanda ke jikin ta amma an dora farar alkyabba wadda ta
sha aiki da zare ruwan gold mai matukar walwali akai.
Tun kafin ta karaso dogarawan nan suka bude kofar da azama suna yi mata kirari irin wanda
'ya'yan gidan kawai ake yi wa. Ta shiga barin dama, yayin da Sa'ade ke barin hagu. Da ta zo
bakin motar sai kuyangar dake bayanta ta zare mata alkyabbar ta shiga daga ita sai kayan
makaranta. Daga haka aka ja sullubebiyar motar a hankali suka soma tafiya, kuyangin nata
basu bar wajen ba har motar su Sa'ade ta hau kwalta.
Tunda suka mika hanya sosai yarinyar take ma Sa'ade kallo na kurilla, ita kuwa tun gaisuwar
farko data yi mata bata kara ce mata komai ba. Ta maida hankalin ta ga kallon hanya suna
wuce bishiyu da dazuzzuka kamar walkiya. Sanda suka cimma garin Chibok ta ce da Sa'ade
cikin ginshira. "Me ye hadin ki da Fulani?"
Sa'ade ta tuna gargadin Fulani don haka nan da nan tace "ni 'yar kanwar ta ce, mahaifiyata ta
mutu". Gimbiya Humaira ta yi mata kallon shakka don ita dai bata taba ganin irin wannan kamar
ta kwabo da kwabo ba irin wadda ke tsakanin Fulani Bilkisu da yarinyar da ke gefen ta. Kamar
kamannin sun zarta na matsayin data ambata din na kasancewar ta 'yar kanwa a gareta. To
amma wace hujja gareta na karyatawa? Tunda ta san bata haifi 'yar a gidan su ba?
Sai ta dauke kai itama ta koma kallon gefen titi. A ranta tana fadin ita sam bazata yi mu'amala
da 'yar kalen dangi ba mai maganar kauyawa.
****

EL-KANEMI COLLEGE OF ISLAMIC
THEOLOGY
Makarantar kwalejin kimiyya ce ta addinin muslunci wadda Larabawan Yemen dana Sudan suka
bude a Maiduguri da hadin gwiwar manyan masu kudin jihar Borno. Itace makarantar da sarki
Yusufu ke kai 'ya'yan sa maza da mata, tun daga kan babbar 'yar sa (Ya Maira) sunan sarautar
ta kenan a matsayin ta na babbar 'ya, har zuwa kan auta Humairah. A tsarin makarantar daga Lahadi zuwa Alhamis sune renakun karatu, Juma'ah da Asabar
renakun hutu.
Malamin maths na fita na Qur'an na shiga, na English na fita na Nahawu ko Fiqh zai shiga,
na chemistry na fita na Adab ko Tarikh ko Mutala'a zai shiga haka dai tsarin karantarwar su
yake. Wato kimiyya cakude da ilmin addini tsantsa.
Sannan ana gama lessons karfe uku ake fara Islamiyya ga mai son haddan Qur'an zalla ake
yi har zuwa biyar na yamma.
Malaman makarantar kuma yawanci larabawan Sudan da Yemen ne, sai kuma Yarabawa
Maza da mata basa haduwa sam, dan katanga ce makekiya a tsakanin su sannan kowane
bangare da gate din shi.

Tunda aka kai Sa'ade da Humairah dormitory dalibai 'yan uwan su ke kallon su, ba don komai
ba sai don irin tsadaddun kayan abincin da ake shigo dasu katan-katan ana loda musu a lokokin
su, a karshe lokokin nasu ma sun yi kadan su kwashe kayan, sai Humaira ta ce da metron da
masu jerawar su je da sauran ta bar musu. Ko kallon Sa'ade bata yi kada a ce tare suke, amma
kayan abincin su ba banbanci haka takalmi da jakar makarantar su, wanda ya tabbatarwa 'yan
dakin cewa tare suke din.
Gadon Humaira na gefen na Sa'ade, don haka ta yi amfani da wannan damar ta maida ita
baiwar ta, komai tana daga kwance take sa ta ta yi mata, dauko wannan miko wancan, ko kofi
zata yi amfani da shi sai ta sa Sa'ade ta wanke mata shi, kuma da yake Sa'aden ta iya kitso ita
ke yi mata duk sati, basa yin wanki iyayensu ke biya a wanke musu shiyasa Sa'ade ta samu
sauki, da har wanki da guga ita zata ce ta yi mata.
Girman kai irin na Humaira ya hanata alaqa da mutanen dakin, ita kadai take rayuwar ta ko a
class don bata ga wanda ya isa tayi mu'amala da shi ba duk da cewa duk 'ya'yan masu kudi ne
a makarantar amma a wurin Humaira in ba ka da jinin sarauta cikin jikin ka to baka isa mutum
ba. Kuma duk makarantar ita kadai ce 'yar Sarki. Sabanin Sa'ade wadda ta maida kanta abokiyar kowa a dakin nasu, in har bata hidimar
Humaira to zaka sameta cikin jama'ar dakin suna hira da harkar arziki, ga ta da kyauta, haka
take ta rabar da kayan abincin nata musamman ga wanda ta lura yana da bukata, cakuduwar ta
da dalibai 'yan uwan ta wadanda suka fita experience da exposure ya sa ta fara samun
wayewar kai. A aji kuwa duk ita ce koma baya a kowane darasi daga na boko har na addini,
amma bata barin hakan ya kashe mata gwiwa, ya cire mata hope na cewa da sannu zata iya
idan ta sanya jajircewa da bada himma.

Haka monitar ajin nasu Raheema Kyari ke yawan gaya mata, wadda tasu ta zo daya,
sakamakon yawan tambayar ta abubuwa da Sa'ade ke yi idan bata gane ba ba tareda nuna jin
kunya ko girman kai ba. Ba ajin su daya da Humairah ba ita 'yar JSS 3 ce yayin da Sa'ade ke
JS 1. Don haka tafi jin dadin rayuwa a class fiye da a dormitory (dakin barcin dalibai) sabida
babu Humaira mai takura mata, a nitse take karatun ta tare da likewa monita Raheema tana
daukar ilmi daga wajen ta.
Malaman ko sun so yin korafi akan rashin kokarin Sa'ade sai su fahimci abin nata daga tushe
ne wato bata samu foundation a makaranta mai kyau ba kamar sauran daliban makarantar, don
in sun tambayeta wace makaranta tayi tana gaya musu a kauyen Tsanyawa ne, makarantar da
maigari yasa aka bude, don a koyawa yara A BA CA DA sai su daga mata kafa musamman in
suka lura da yadda take da kishin abun a zuciyarta, in aka koya abu bata gane ba har kuka take
yi. Duk kokarin Raheemah na koyar da ita ba komai take ganewa din ba musamman darasin
lissafi, da yawa a makarantar sun dauka Sa'ade baiwar Humairah ce, irin 'ya'yan bayi da ake
hado 'ya'yan sarakai dasu su zo makaranta tare don su dinga hidimta musu, sabida haka
Humairan ke nunawa.
Sannu-sannu bata hana zuwa, saidai a dade ba'a je ba, a hankali Kwakwalwar Sa'ade ta
soma budewa, musamman a haddar Al'qurani da Ingilishi. Raheema ta taka rawar gani akan
hakan don fisabilillah take kaunar Sa'ade sabida saukin kanta, baban Raheema babban dan
kasuwa ne a jihar Maiduguri wanda sunan sa yayi fice akan sana'arsa ta fata. Watarana Raheema ta kawo wa Sa'ade ziyara dakin su, sai ta same ta durkushe gaban
Humaira ta sunkuyar da kai tana hawaye, Humairan na ta zazzzaga mata fada har tana fadin
dama 'yan kalen dangi basu iya cin arziki ba, banda haka tun safe ta sa ta gyaran sittirunta
amma tasa kafa ta fice yawon neman suna bata gyara mata ba, su ko Fulani Bilkisu ba wata
tsiya bace a wurin su tunda sun san asalin ta balle su ya-ku-bayin data kawo musu gida suna
cinye arzikin Babansu.
Ba fadan data ke mata ne yasa ta kuka ba, domin in da sabo ta saba, ambaton sunan Fulani
data yi ta zaga ne ya tsaya mata a zucci. Ya kona mata zuciya. Fulanin da has never been nice
to her in any way amma zuciyar ta na mata wani irin so, da bata taba jin sa akan kowa ba
including Baban ta. Rahima ta kama hannun ta ta cira ta tsaye suka bar dakin, Humaira ta sakar musu tsaki tana
fadin "ya'yan mutsiyata, gayyar tsiya".
Can bayan dormitory suka zaga suka zauna akan duwarwatsun da ke wajen, Raheema ta ce
"wai don Allah Humaira ke baiwar ta ce? Ko iyayen ki bayi ne a gidan su?" Bata san me yasa ta
yarda da Raheema ba, tun sanda ta fahimci Raheemar na tausaya mata tsakani da Allah. Ta
girgiza kai tare da share hawayen idon ta "ni ba baiwar ta bace, ana riko na ne a gidan su,
kishiyar mamanta ce yar mahaifiyata a hannun ta nake".
Raheema tace "tabdi! Amma shine kike mata bauta tana miki wannan wulakancin? Ke ba
baiwar ta ba iyayenki ba bayin su ba? To wallahi ki kama kan ki, ki nuna mata zaman kan ki ke
yi ba zaman ta ba in ba haka ba watarana sai ta kai ga taba lafiyar jikin ki" da sauri Sa'ade ta
girgiza kai. "Zan yi mata komai saboda Baban ta!".
Raheema ta rasa abinda zata ce, sabida a amon muryar ta kadai ta fahimci akwai wani
girmamawa da kauna na musamman data ke yi wa Baban Humaira, abinda ta fada har zuciyar

ta ya ke. Wannan ya tabbatar mata Sa'adatu irin mutanen nan ne da basa manta alkhairin da
wani yayi musu komai kankantar sa.
****
An yi jarrabawar karshen zango, as expected Sa'ade ta dauko na biyun karshe, ta yi kuka har
ta gode Allah, amma a islamiyya ta yi dan kokari ba laifi musamman a hadda.
Damuwar ta yadda zata dauki wannan mummunan sakamako ta kaiwa Alanguburo, bayan ta
yi masa alkawarin yin kokari iyakar iyawar ta.
Raheema ta ce ta bata lambar wayar wani a gidan su zata kira ta in ta koma gida, Sa'ade
tace banda Fulani babu mai waya a sassan su, ita kuma bata san lambar ta ba, ko ta sani
bazata yi karambanin bayarwa ba Fulani ta tsinke mata kunne haka kawai.
A daren ta hada musu kayan su da zasu tafi dasu gida a kananan trollies din su, sauran
kayan abincin da suka rage Humaira tace ta fitar duka ta kaiwa metrons.
Ta yi sallama da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login