Showing 21001 words to 24000 words out of 30109 words

Chapter 8 - Masarautarmu Book 1 Compelet By Sumayya Abdulkadir Takori

Bilkisu ta fada a zuciyar
ta. Tana son comparing soyayyar data ke ji akan Sa'ade da Zarah. Sai ta ga cewa ratar dake a
tsakani mai tsananin fadi da girma ce, ta haifi Sa'ade ne kawai amma babu ko digon soyayyar
ta a zuciyar ta, sai tausayi da kyautayi irin na zuciyar musulunci. Yanzu ne ta san kaunar uwa akan dan ta, da ta haifi 'ya da wanda take so. Can wani lungu
na zuciyarta kuwa kururuwa yake yana objecting: idan soyayyar Sa'ade da ta Zarah, bata zo
daidai da juna ba, sai dai ace ta Zarah ta rinjayi ta Sa'ade, amma ba wai ace babu burbushin ta
ko kankani a zuciyar ta ba. Bata ankara ba sai ganin 'yar ta tayi a bayan Sa'ade, tasa tawul din da aka nannade ta a ciki
tagoye ta tsam ajikin ta, ta soma dan jijjigata sabida dan rikici data ke yi irin na jarirai. Sai
tasamu kanta da kasa cewa ta sauko mata 'yar ta, ta mike ta shige turakarta ba tare da ta ce da
ita komai ba. Dama kuma tana so ta huta din, gashi ta sallami kowa tace bata son ganin
kowacce baiwa a bangaren ta sai gobe da safe in Allah ya kai mu. Sai ganin tsayuwar Sa'ade ta
yi a gaban ta ba zaton ta ba tsammani.
Sa'ade saboda jin dadin Fulani ta bar mata Zarah sai ta nufi dakin ta goye da ita, roba ta
samu ta hada ruwan dumi ta saukota ta soma yi mata wanka, ta gama ta nade ta cikin shawul
ta fito kan gadon ta ta dauki basilin din ta tana shafa mata.
A lokacin Fulani ta shigo, ta bude baki da zummar yin fadan don me ta yi mata wanka bayan
ba'a jima da yi mata wanka ba? Amma sai ta ga yarinyar na ta bangala dariya Sa'ade kuma ta
himmatu wajen yi mata wasa a cute kumatunta. Sai suka bata sha'awa, ta juya silently ta fita. Ta
dauko set din kayan baby na sanyi ta dawo ta watsawa Sa'aden ta sake juyawa ta koma. Shikenan daga wannan ranar Sa'ade ta kwace rainon Zarah daga hannun Fulani da masu
rainon ta, kayan yarinyar ma saida ta san yadda tayi suka dawo dakin ta. Tsakanin ta da Fulani
shine kawai idan ta bukaci nono.
Hausawa suka ce wai "Mai Da wawa ne", wannan kyautatawa da kauna ta Sa'ade ga Zarah a
hankali yake hakurkurtar da zuciyar Fulani Bilkisu, daga mummunan kullacin Mal. Hashimu
dake cikin ta, wanda ya hanata ganin farin Sa'ade har ta kaunace ta matsayin 'ya 100%.
A hankali ta soma rage fada, da tsawa da hantarar da take yawan yi mata, ta soma yi mata
magana jefe-jefi cikin sanyin rai.
Satin ta uku a gida sai ga Raheema Kyari, wannan karon ba'a hanata shigowa ba, Kuyangar
data rako ta sai ta hada ta da Fanna, ita kuma Fanna tace ta jira daga waje, ta nemo izni
tukunna.
"Kawa kuma daga Maiduguri?"
Fulani ta fada cikin mamaki.
"Haka ne ranki ya dade, sannan ta tabbatar min ita aminiya ce ga Sa'adatu sannan ta san da
zuwan ta".

Fulani ta hadiye fushin ta wanda tayi aniyar saukewa akan Sa'ade bayan tafiyar bakuwar, ta
ce Fanna ta shigo mata da yarinyar.
Cikin sallama da shiga ta mutunci da kamala Raheemah ta shigo, tunda ta shigo Fulani ta
kura mata ido. She looks so much like her father wanda ta yi wa farin sani. Mikewa tsaye tayi ba
tareda ta san lokacin da ta yi hakan ba, hatta tsagin fuskarsa biyu-biyu dogaye gasu nan
kwance a fuskar Raheema. Da ta gaisheta da kyar tayi controlling razanar ta ta amsa,
"yaya sunanki?"
"Raheema Kyari Babagana"
"Kyari?!"
Ta fada da amon muryar da ya baiwa Raheema mamaki, "eh, sunan Babana kenan" "daga
wane gari kike?" "Daga Maiduguri na zo, acan muke zaune, amma mu 'yan asalin Damaturu
ne".
"Shikenan dangin ubanta sun biyo ta, a lokacin da na fara sanyata a raina".
Fulani ta ayyana a zuciyar ta, ta kuma kudiri aniyar kin gayawa Sa'ade kowacece Raheema a
gareta.
"Shiga nan dakin, tana ciki"
Ta fada tare da nuna mata dakin, ta kuma tashi ta bar musu area din gabadaya zuwa turakar
ta.
Sa'ade sai ganin Raheema ta yi ta shigo da sallama, zo ki ga gudu da murna wajen Sa'ade,
saura kadan ta kada Raheema. Ita kuwa sai dariya take. Ta dauki Zarah dake tsakiyar gadon ta
tana fadin "masha Allah, beautiful baby". Hira kamar ta kashe su. Fanna ta shigo wa da
Raheema abinci na musamman suka ci tare cike da farin ciki. Can da yamma Raheema ta ce "Sa'adatu ki zagaya da ni mana in ga masarautar taku in
samu abun baiwa su Sarina labari". Sa'ade tayi dan jimm! Kafin tace "ni bana zuwa ko'ina, daga
daki sai daki, Fulani bata bari na". "Amma meyasa?" Inji Raheema. Ta dan kyabe baki "i don't
know. May be sabida kishiyoyin ta". Daga haka suka bar hirar. Washegari Fulani ta sa aka yiwa Raheema sallama ta girma, aka maida ita har Maiduguri.
****
Ya Gumsu ta shiga turakar mai Askira cikin kwalliya ta kasaita a matsayin ta na mai girki
ranar, abinci yake ci tana gefen sa tana masa firfita, cikin hila irin ta matan da suka san kan
mazan su ta yi durkuso a gaban sarki, ta ce "Alanguburo (Allah ya kara yawan rai) Yarima na
rokon alfarmar a bar shi ya zo gida, ko da na sati daya ne, shekaru goma kenan rabon sa da
gida, yayi digiri yayi masta ya jima yana aiki har ya fara digiri na uku, yana cikin damuwar rashin
sanin halin da 'yan uwan sa ke ciki, yayi alkawarin baza'a sake samun sa da laifi makamancin
na baya ba".
Nan da nan wani kwantaccen bacin rai ya bayyana a fuskar sarki, ya dago idanun sa da suka
kada ya dube ta, sai da hantar cikin ta ta kada. Ta yi azamar sunkuyar da kai amma a ranta zata
jure komai in har zai bar dan ta ya zo gare ta, haka kawai ai ba shikadai ne fitinannen Da ba,
fitinannun nawa ya haifa? Amma bai daukewa Ya Kirjinoma nata ba sai shi kadai bayan ba fin
su fitinar yayi ba. Yana kusa da su ma suna masa fada ai zai fi gyarawa fiye da hannun aminin
nasa.

Sarki Yusufu AbdulHakimu mai Askira, ya dubi uwargidan sa Ya Gumsu da idanun bacin rai
kamar koyaushe ta sako zancen YARIMA SAGEER a gaban sa, idan da abunda ya ke bata
masa rai a rayuwar sa to al'amarin Yarima Sageer ne, babban Da, kuma zakka a cikin 'ya'ya
mazan da Allah ya bashi, yet mafi madaukakiyar soyayya a zuciyar sa. Dama an ce wai fitinannun 'ya'ya sun fi shiga zuciyar iyaye. Kusan wannan magana haka
take. Duk cikin 'ya'yan sa maza da mata ba wanda yake so irin Muhammad Sageer, sai kuma
ya zamo mafi munin jarraba da Allah ya taba yi masa. Ubangiji yayi gaskiya da ya ce "ya'ya da
dukiya fitina ne......". "A takaice dai kina rokawa dan ki alfarmar ya dawo cikin gidan nan ya cigaba da turmushe
'ya'yan mutane, ya cigaba da wulakantani tare da tozartani a idanun Bayi na da hadimai na
dake tsananin ganin girma na, ta hanyar turmushe musu 'ya'ya dake hidimta masa?".
Fulani ta runtse ido cikin jin zafin kalaman sa, "Alanguburo, wannan abu ne na kuruciya, kai
kan ka da ka ga Yarima ka ga nutsuwa da hankali a tattare da shi, abinda yayi yana yaro ba zai
taba maimaitashi cikin hankalin sa ba, balle da 'ya'yan bayi makaskanta a gare shi. Wallahi don
an ki yarda da nine, amma Yarima makiya ne suke jifan sa a baya, ba yin kansa bane. Kai shaida ne akan tsantsani da tsafta irin na Yarima, amma a ce ya rasa matan da zai bi sai
'ya'yan bayi, ai daga nan zaka gane akwai lauje cikin nadi a al'amarin sa.
Bayan haka kuma na dukufa da yi masa addu'a tun tafiyar sa, Allah kuma baya juya addu'ar
Uwa, inada kyakkyawan yaqinin cewa ya daina, mu taru mu kyautata masa zato, mu bashi
dama ya rayu cikin gidan su kamar kowanne Da cikin gidannan, idan aka sake samun sa da
wani laifi makamancin wannan, na amince ayi masa duk hukuncin da ya kamata da shi". Maganganunta ga dukkan alamu sun dan shigi Askirama. Ya dade cikin halin shiru, ya kasa
cigaba da cin abincin sa. A karshe yace da Ya Gumsu wadda ke jiran amsar sa kamar ta shiga
zuciyarsa taga abinda yake yankewa.
"Zan yi shawara da Waziri".
"Alanguburo (Allah ya kara maka yawan rai nagode matuka, kuma insha Allahu Waziri zai
amince da abinda na zo da shi, don shima na tabbata yana son ganin Awaisu)".
"Ina bukatar kadaicewa". Ya ce da ita.
Ta mike cikin azama ta soma tattare akusan abincin dake gaban sa. "In ma kwana zaka yi
kai kadai ka yi, ni dai a bar Da na ya dawo gida". Ya Gumsu ta fada cikin ranta, a fili kuwa
dukawa ta yi a gaban sa tana fadin.
"Na bar ku lafiya gatan Askira".

Fitar ta ke da wuya ya kishingida ya lula cikin tunani. Tunani mai zurfi na shekarun da suka
gabata.
****

SHEKARUN CAN BAYA
(A Masarautar Askira)
Lokacin da Ya Gumsu ta samu cikin babbar 'yar sa 'Yaa Maira' duk burin sa da dokin sa shine a
haife masa Da namiji domin ya samu magaji, kamar yadda kowanne sarki ke burin samu.
Amma sai aka haifi Ya Maira, ciki na biyu ma yayi ta fata da addu'ar samun da namiji, amma sai
ta kara haihuwar diya mace. Dalilin sa kenan na kara auren Ya Kirjinoma a daidai lokacin domin
yana ganin 'ya'ya mata kawai Ya Gumsu zata yi ta haifar masa.
Kamar Allah ya san cewa bai yi farin ciki da haihuwar Mairam Lubabatu ba, bata fi shekaru
uku ba Allah ya karbi abinsa.
Ya Kirjinoman ma da ta tashi haihuwar ta ta fari, sai ta haifo masa Mairam Murjanatu.
Wannan ya kara mayar da shi desperate ga son haihuwar da namiji. Ba ruwan sa da 'ya'yan sa
mata, duk kulawar su da hidimar su da tarbiyyar su tana wuyan iyayen su mata. A kullum ya
tuna wancan lokacin ya kan ce "wannan shine deadly mistake da ya taba yi a rayuwar sa". Ba
shikadai ba, masu sarauta da yawa hakane tunanin su akan haihuwar fari, idanunsu rufewa
yake ga son haihuwar da namiji ba tare da baiwa Allah zabi ba.

Ciki na uku da Ya Gumsu ta samu kusan a tare suka sameshi itada Ya Kirjinoma. Ita ta haifi
MUHAMMAD SAGHEER, Ya Kirjinoma ta haifi MUHAMMAD ASHGAR tsiran watanni biyu kacal
ne a tsakanin su.
Ashgar sai ya zo da rashin lafiya ta Autism wadda aka fi sani da (autism spectrum disorder).
Baya magana (in a meaningful way) tun yana karami saidai ya maimaita abinda aka fada masa
sannan kamar kwakwalwarsa ba daidai take ba.
Wannan yasa sarki Yusufu ya dauki soyayyar duniya da tattali da kulawa ta duniya bakidaya
ya dora akan lafiyayye Yarima Sageer, wanda hakan ya ruruta wutar mummunan kishi tsakanin
Ya Kirjinoma da Ya Gumsu, ya kuma sa Ya Gumsu daukar girman kan duniya ta dorawa kanta,
da jin tafi kowa, tunda kuwa ita ta haifarwa sarki Yarima. Koma waye zai biyo baya saidai ya zo
a matsayin kanin sa ba Yayansa ba.
Soyayyar data sa tun yana yaro daga uwar har uban suka sangarta shi, basa iya kwabar sa,
gata na duniya babu irin wanda basa gwada masa. Hakan bai hana shi yiwa Sageer addu'a ba
a duk sallahr farillar sa kan Allah ya kare masa shi a duk inda ya shiga. Musamman da ya
bayyana ga kowa cewa yaron fitinanne ne na kin karawa. Ya addabi 'ya'yan jama'ar gari da mugunta da tsokana, baya zama cikin masarauta saidai
cikin 'ya'yan talakawan gari, sune abokan sa abokan mu'amalar sa, don Sageer ya tare yaro a
lungu ya targadashi ya fasa masa hanci babu gaira babu dalili ba wani abu bane sabo a wajen
jama'ar gari, suna dauke ido ne sabida mutuncin mahaifin sa da farin jinin yaron. Yaro ne mai
shiga rai matuka, sabida kwarjini da kyawun suffar da Allah ya bashi.
Yana girma fitinar sa na karuwa a ciki da wajen masarauta.
Kullum Sageer ya fita makaranta da yaron da zai targada ko ya fasawa hanci ba'a kuma isa a
kawo kara ba sabida tsoron Ya Gumsu, saidai Awaisu ya gani ya zo ya fada a gida. Waziri ya
aika a bada hakuri. Don ba'a bari ma Sarki ya ji. (Awaisu dan Waziri ne kuma sa'an Sageer don

haka tare aka raine su), har ta kai ga Awaisu ya kwaso kayan sa duka ya dawo dakin Sageer
kwatakwata, sai dai hali kowa nasa daban. Don kuwa Awaisu babu ruwan shi yaron kirki ne,
amma duk inda Sageer yasa kafa nan zai mayar da tasa.
Darajar Sarki yasa jama'ar gari suka yi ta hakuri da Sageer tun yana yaro har ya shiga
sakandire anan Askira. Kafin ya gama sakandire ne kuma yayi dan hankali ya daina taba
'ya'yan kowa, sabida yawan addua'ar Alanguburo akan sa. Har yake dan shigowa fada a zauna
zaman fada tare da shi kamar yadda Sarki ke so ya dinga yi kullum amma ya ki. Lokacin da
Sageer ya soma balaga, sai abubuwan gabadaya suka canza, 'yar nutsuwar da yake da ita tabi
ruwa. Ya koma neman bayin sa mata.
Lokacin da wannan mummunan labari ya kai kunnnen sarki Yusufu mai Askira sai ya kira
Wazirin sa cikin sirri.


"Na yanke shawarar in aura masa mata hudu a rana daya, ina ganin hakan ne kawai mafita
ga al'amarin sa".
Waziri Ibrahim ya girgiza kai yana kallon maimartaba sarkin Askira cikin tausayi, ganin yadda
ya zabge ya birkice a kwanaki uku kacal da samun wannan labari da yayi. Lallai 'ya'ya da
dukiya fitina ne. Kamar yadda mulkin kansa fitina ne da rashin kwanciyar hankali ga bawa.
Yace. "Baza'a yi haka ba Askirama. Baza'a yi haka ba gatan Askira, aure ba laifi bane a shekaru
goma sha tara amma karatu za'a kai shi, zamani ya canza, auren mata hudu a rana daya ba zai
zamo solution ba, don kuwa zai hanashi maida kai ya yi karatu musamman idan ya soma tara
iyali. Ka manta da komai ka kwantar da hankalin ka ka barshi yayi karatun da zai amfane shi
muma watarana ya amfane mu. Zan hada shi da Awaisu zuwa duk inda zaka kai shi zan kuma
san yadda zan yi Awaisu ya zame masa jagora a komai nasa. Mafi a'ala shine mu bisu da
addua".
Ya sani duk duniya babu mai kaunarsa cikin 'yan uwan sa na jini irin Waziri Ibrahim, wanda
ya kasance Da ga wan mahaifin sa marigayi sarki AbdulHakimu mai Askira. Bai taba bashi
shawarar da in ya bi ta baya ganin mafita da yaqini a cikin ta.
Don haka yayi na'am da shawarar Waziri ba tareda shawara da Ya Gumsu ba.

Kafin ya zama sarki shi Ambasada ne na kasar Egypt, saida mahaifinsa Sarki Abdulhakim ya
rasu ne aka dawo dashi gida aka bashi sarauta, don haka yana da kyakkyawar alaqa da
ambasadan Egypt mai ci a lokacin kamar amini yake a gare shi, sannan yana da connections
mai yawa da kasar ta Misra domin yayi sama da shekaru goma yana aikin jakada a cikin ta. Don haka ya yanke shawarar kai shi kasar muslunci bai kai shi kasar turai ba don ya kara
hankali, a Egypt din ma hannun Aminin sa Amb. Hassan Labaran ya damka shi bai yarda ya
zauna a hostel ba. Amb. Hasan bai taba haihuwa ba shida matarsa Hajiya Laila, suka karbi
amanar Sageer da Awaisu a gidan su wadanda aka samarwa gurbi a jami'ar Al. Azhar. Saidai
ba fanni daya suke karanta ba.
Daga wannan lokacin ne kuma haihuwar 'ya'ya maza ta budewa Sarki Yusufu daga duka
matan nashi biyu, a lokacin ne ya hadu da Hibbani ya aure ta, daga baya ya auri Bilkisu,
haihuwar ta biyar suna mutuwa.

Amb. Hassan zazzafan da boko ne mai zafi da sanya ido akan iyalin sa, tashin farko ya gano
dabi'ar da Sageer

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login