Showing 12001 words to 15000 words out of 29267 words
Chapter 5 - Masarautarmu Book 3 Hausa Novels By Takori Kabara
bai
bata cikakkiyar amsa ba akan hakan in zata iya tunawa cewa yayi zai duba.
Ta yi ajiyar zuciya cike da tausayin Saade, ta san duk ranar data shiga hannun Yareema sai
Allah. Tunda dan Askirama ne.
Ranar talata, wato ana i-gobe sakun lalle Saade ta fito wanka tana busar da lallausar gashin
kanta da dryer don ta cire wa kanta damuwar Yareema ko aurensa yanzu, ta hada su su duka ta
zuba a kwandon shara, ta sa a ranta ba inda za ta yarda a kai ta, ko dai a barta nan a gaban
uwarta ya koma gidan sa shi kadai yayi ta auren, ko ta bi su Innar Hanne su koma Tsanyawa ta
yi zamanta a gidan su Hanne. Karatun ta hakura ta yafe in dai sai ta amsa sunan matar
Yareema Sageer. Ina ita ina zama da yar giya matsayin kishiya? Ta je bar din ta ta dawo ta
rotsa mata kai? A hakan ma kowa yana zaman kan shi ya suka kare balle suna zaman auren sa
su duka? Wannan shine tunanin Saade.
Wata siririyar muryar budurwa ta yi sallama daga bakin kofa, da yakeSaade ta bada baya ne
tana fuskantar mudubi, amma jin wannan murya ba ta san lokacin da ta yi azamar juyowa ba,
muryar sounds so familiar a kunnenta.
Murya ce da ko mutuwa ta yi ta dawo ba za ta manta mai ita ba. Tana tsaye jikin kofa, harde
da hannayenta a kirji, yar gaye da ita kyakkyawa sai murmushi ta ke. Ta kara tsayi da haske, ta
murje sumul fiye da sanin da Saade ta yi mata.
Idanun Saade suka bubbude gabadaya, ta saki dryer din hannunta kasa, kafin ta tafi da
mugun gudu ta rungume RAHEEMAH.
Fulani ta shigo, a bayanta wata mata ce da akalla za ta girme ta. Kyakkyawa da ita, da
ganinsu ka ga mazauna kasar sanyi, sai kannen Rahima su biyu Sarina da Jamila. Kallo daya
Saade ta yi wa matar ta gane mahaifiyar Rahima ce sabida tsabar kamannin su, wadda Rahima
kullum ke kira da “Mama”. Ta saki Raheema ta tafi ga Mama za ta tsugunna, Mama ta yi saurin riko ta a jikinta, sannan
ta rungume ta. Cewa ta ke,
Masha Allahu, yau ga ni ga Saar Raheema, Saadatu Saar Mata!
Ta kama su ita da Raheema ta rike a jikinta, Sarina da Jamila sai murmushi suke mata. Ta tafi
gare su suka rungume juna don dai ita duk wani ahalin Raheema tana sonsa a kan dalilin da
zuciyarta har yau ba ta sani ba.
Raheema shi ne ki ka gudu daga El-Kanemi babu ko sallama, babu notice? Na shiga
damuwa Raheema, zaman makarantar ya fice min a ka saboda rashinki. Na dade kafin na saba
da rashinki Raheema, nayi kewar ki yadda harshe na ba zai iya bayyanawa ba, don Allah kada
ki sake tafiya ki barni Raheemah. Sai kuka. Raheema tana share mata hawaye da tafukanta, ta ce, har yanzu kina nan da kukan wofin
kin nan ko? Is o.k Saadatu. Im here now, da ni za a sha shagalin biki, ba zan tafi ba sai na raka
ki dakinki.
Ni ma ba da son raina muka koma Italy ba, kuma ban samu damar dawowa El-Kanemi don in
miki sallama ba. Ki yi hakuri.
Sannan ne suka zazzauna a kasa, iyayen na daga gefen gado suna kallon su withaffection.
Nan Fulani ta gaya wa Saade labarin da ya girgiza zuciyarta, cewa ita da Raheema yan uwa
ne na jini, da mahaifinta da mahaifin Raheema uwarsu daya ubansu daya.
na dade da gane hakan ban dai gaya miki bane tuntuni, don in Baban Rahimah ya san ke ce
ba zai bar ki hannu na ba.
Saade sai ta ji duk wata damuwar duniya ta yaye mata. Feeling din da mutum ke ji idan ya
san cewa yana da dangi na jini kuma na halali. Lallai da ake cewa wani farin cikin ya fi gaban
kuka, sai dariya.
Ta zama kamar wata karamar zararriya don murna. Ta rungume Raheema, ta saki ta
rungume Sarina, ta saki ta kamo Jamila ta rasa inda za ta sa su don kauna, su kuma sai dariya
suke mata, don sun riga ta jin labarin tun suna Italy.
Maimartaba ya kira Fulani a waya ya gaya mata ta sa a rako Saade da Rahima falon saukar
bakinsa ta gaisa da Babanta, wato Alhaji Kyari Babagana. Tare da Fulani suka tafi har falon
ganawa ta musamman da bakin Maimartaba Sarkin Askira.
Kallo daya ta yi mishi ta hango kamanninshi da mahaifin ta Malam Hashimu, saboda jini ba
ya buya. Har kasan kafafunshi ta je ta zauna ta gaishe shi a ladabce. Shi kuma ban da kallonta
da tasbihi ba abin da yake a fili, tamkar Bilkisu ta yi kaki ta tofar, ko kadan ba ta debo dan
uwansa Hashimu ba ko da da kalar fata ne. Sai yanzu ya tuna kallon sanin da yayi mata a ganin
sa na farko da ita a El-kanemi. Ashe fuskar Bilkisu ya hango cikin idanun ta.
Alhaji Kyari ya ce, Madallah da yata mai albarka, Allah ya sanya alkhairi da albarka cikin
aurenki. Allah ya hada hankulanku, Ya bada zaman lafiya.
Ba ta iya ta amsa wannan adduar ba, saboda nauyin da ta yi mata a zuciya da kwakwalwa.
Idan ta ce, ameen, Allah ya amsa adduar fa? Aurenta da Yarima ya zama tabbatacce ba
mafarki ba kamar yadda ta ke kallonsa? Duk da Yareema Sageer ya tabbatar mata cewa, reality
ne, ta hanyar da bata taba zato ba, kuma ba shi da alamun ja da baya daga hukuncin
iyayensu?
Don haka ya rage nata ta cigaba da yaudarar kanta da kanta, da cewa mafarki ne.
Sun dade yana mata tambayoyi tana ba shi amsa a kan marigayi da rayuwarsu a Tsanyawa,
karatun da ta ke yi a yanzu a NTNU da kuma burin ta na yanzu wato barin karatun ta zauna a
gida.
Daga shi har Askirama suka hada baki wajen tambayarta,
Saboda mene za ki bar karatunki Saadatu?
Ko shi Yareeman ne ya ce ba ya so?
In ji Maimartaba, sounding worried da hukuncin Saaden, duk da ya san hakan mawuyaci ne a
matsayin Yareema Sageer na malamin jamia cikakke ya ce ya hana matar sa karatu.
Saade ta bude baki a hankali kamar mai ciwon makogaro, ta ce,
Saboda na fi son in ci gaba da zama a Askira, bana son komawa Abuja Alanguburo.
Fulani ta ce, Babbar magana, mijinki yana wani gari ke kina wani gari, a dalilin me?
Maimartaba ya yi saurin cewa, Ya isa Fulani, Saadatu za ki zauna a gidan Yarima na Askira
har ki kare hutunki? Inyaso daga baya sai mu raka ki Abuja da kanmu ni da Fulani ki koma
makaranta, kin amince?
Askirama ya yi maganar cikin lallashina uba mai tsananin kulawa.
Kaunar da Mai Askira ke nuna mata da yawan alkhairinsa gare ta ya fi gaban ya yi hukunci ta
ce, aah. Sauran zai kasance ne tsakaninta da Yarima, tunda shine bai ce shima baya son auren
ba, yayi uwa ya yi makarbiya ya amshe auren, ita ta fada a ce ta yi rashin biyayya, da kyar in
Fulani bata bubbuge mata baki in ta fada hakan a gaban Askirama ba, amma tsakaninta da
Askirama babu jayayya.
A hankali ta gyada kai alamar ta amince, idonta kuma ya cicciko da kwalla. Amma ta yi
kokarin maida su sabida Askirama. Ko yayan da ya haifa ba ta taba jin ya raka gidan miji ba ko
ya je gidajen auren su. Amma ita ya ce shi da kansa zai kaita. What an honour! Wannan ba
karamin girma ne da kulawa ya ba ta ba.
A wannan daren daga Raheema har Saade sai goshin asubahi suka kwanta. Labarin juna
suke bai wa juna. Inda Raheema ita ma ta sanar da ita ta samu miji a Damaturu suna karatu
tare a jamiar Heartfordshire, U.K. sunansa Usman Bello Jajere. (Jajere garin fulanin Damaturu
ne suna da kyau farare ne kuma suna karatu sosai yan garuruwan Jajere da Kollere. Yan Jajere
kan yiwa kan su kirari da Jajere garin jajaye in ka ga baki to bako ne), amma aure sai ta gama
karatu, shi kuma ya dawo gida ya yi service.
Ba abin da Saade ta tuna a lokacin sai Saidu, da yanzu ita ma yaro dan makaranta kamarta
za ta aura, ina ma ta bawa Saidu damar da yake nema tuntuni tana gwasale shi? Yanzu gashi
girman kanta ya sa an dauki mijin wata an ba ta wanda a haihuwar kauyensu Tsanyawa ya
haife ta. Allah kadai ya san irin farin cikin da Usman zai sa Raheema, ita kam yanzu sai dai ta je
ta yi ta fama da yar giya
Wannan tunanin ya fiddo hawaye daga idon Saade, wanda Raheema ta nace sai ta ji dalilin
saukarsu. Don bata ga dalili ba.
Saade ta tuna cewa, wannan Raheema ce, mai kaunarta da zuciya daya tun tana bakauyiyar
ta, kuma yar uwar da ba ta da kamarta a yanzu. Babu wanda ya dace da sanin halin da zuciyar
ta ke ciki a halin yanzu ya kuma fahimceta ya bata shawarar data dace kamar Rahimah.
Don haka Saade ta gyara zama, ta warwarewa Rahimah komai a kan rayuwarta gidan
Yareema Sageer, da halin da matarsa ke ciki, irin kyautatawar da yake mata, girmansa da ta ke
gani, har da labarin Said sai da ta bata. Amma ta rasa dalilin da ya sa ta kasa ce da Raheemah
Aunty Sultana na yawan cewa Sageer yana neman mata. Maganar ta yi nauyi sosai a bakinta
tunda ba ta taba gani da idonta ba, shaidar zina kuwa sai ka kwana a ciki in ba ka yi
taka-tsan-tsan ba.
Ta gaya wa Raheema damuwarta shi ne ba ta taba jin wani abu a zuciyar ta a kan Yareema
ba, bayan na kasancewarsa guardian dinta a Abuja. Ita a wurin ta Uncle Yarima Yayanta ne mai
kula da alamuran karatun ta.
Rana daya ta ji labarin aurensu daga bakin Fulani bagatatan kamar saukar aradu, ita ta fi son
in auren ne ma a aura mata Saidu ba za ta damu ba, shine tsaran auren ta daidai da rayuwar ta
ta yar talaka. Amma ina zata kai YARIMAN ASKIRA???
Raheemah Kyari, ta yi wani irin lallausar murmushi. Ta kama hannayen Saade ta rike cikin
nata.
“inda kowacce mace take kai mijin ta Saadatu! Ina ma ni ce ke Saade! Ki yarda ba tun yau ba
cewa you are among the luckiest. Auren matured men shi ne aure, wadanda suka san ciwon
kansu, ki rabu da samarin nan yan rawar kai ki kama mijinki da iyayen ki suka zaba miki kin ji?
What is your own business da rayuwar matar sa? Kuma tunda Fulani ta ce ya raba muku gida, kuma ya amince, ina ruwanki da matarsa?
Wannan rayuwar su ce shi da ita bai shafe ki ba.”
Saade ta zumburo baki, Raheemah ba za ki gane ba. I have no feelings a kan Yareema
Sageer, na dauka zaman auren sai da feelings din soyayya yake yiwuwa???
Raheema ta girgiza kai, ta ce, inji wa? Saadatu, ki gode wa Allah kawai, ki kuma hada da
addua, ki roki Allah ya sanya miki soyayyar mijinki, kuma zabin iyayenki. Soyayya da kike
ambato shirme ce, cike take da unbearable challenges, aure daban soyayya daban, sai kin yi
auren soyayyar in gishiri ya sauka daga kan kaza za ki gane shayi ruwa ne. Above all kin ce kina ganin girman Yareema, to magana ta kare. Along the way soyayyar za
ta zo, irinki in ku ka tashi soyayyar ma mahaukaciya ku ke yi, kuma makauniya, tunda kin ce ba
ki ga alamun shi yana kin auren ba.
Muryar Saade abin tausayi ta ce, Sai ma kin ji bakar maganar da ya gaya min da na ce ba
zan koma Abuja ba zan gudu kauyenmu he was like (in yi ta gudu, in fi ruwa gudu, giya in shirya
sha tare da matarsa) meaning bai dauki maganganun nawa da wani muhimmanci ba.
Raheema ta yi dariya sosai, ta ce.
I would like to see Yarima Sageer. Sister you are blessed for having him as a husband, ina
son brave men, wadanda suka yarda da kansu, cika baki ko rikicin mace ba ya razana su su ja
da baya a kan soyayyar su. Ni ma sai in ce,
Sai kin dawo, a gaida mutanen Tsanyawa.
Saade ta kai mata bugu ta goce tana mata dariya. Muryar ta abin tausayi tace.
Wato dai Raheema kema kina bayan in auri mai mata ko? Ta je bar ta dawo ta yi min dan
karen duka?
Dariya sosai Raheema ta sake yi, ta ce, Tunda ki ka ce ga inda ya auro ta kuma ga asalinta
me ye abun mamaki don ta sha giya? Su fa yadda muke shan soft drinks, haka suke shanta
don baki taba fita ketare bane, canjin addininta ba zai sa ta iya dainawa farat daya ba, tunda dai
ba shi yake sha ba shi kenan falillahil hamdu, ki yi mata addua Allah ya sa tana da rabon
dainawa.
Sai kiran sallar asuba suka ji a kunnuwan su, dole suka mike don bada farali. Daga nan kuma
suka kwanta, Hanne sai barcinta ta ke hankali kwance bisa katuwar katifa ita da danta Naziru.
*****
Washegari aka tashi da event na farko, wato sakun lalle. Masarautar ta cika ta batse da yan
uwa da abokan arziki da baki da aka gayyato daga masarautu daban-daban, ga kuma alummar
garin Askira wadanda ma ba a gayyata ba. Da ma in dai biki na gidan sarki ne ba sai an
gayyace su ba, kwansu da kwarkwatarsu suke tahowa daga gidajensu zuwa gidan Sarki. To balle auren Yareema Sageer kuma wanda Maimartaba da kanshi ya shelanta gayyatar ga
kowa da ke Askira, bayan saukowa sallar jumaa a babban masallacin jumaa. Don haka ba a
taba ganin taron bikin da ya hada jamaa irin na yau ba a masarautar gabadaya. Tun daga kan
auren su Yaa Maira har zuwa kan na yar sarki ta karshe da aka aurar Najaatu. An saka amarya a lalle lafiya, Raheema da Hanne da kanwar Raheema Sarina sune
kawayen amarya. Washegari alhamis aka yi NIYA wato ranar yin royal snacks su nakiya, alkali,
dubulan, bakilawa da sauransu daro-daro don raba wa mutane.
Ranar jumaa aka yi WUSHE-WUSHE. A babban filin dake cikin fada aka kira decorators suka
tsara shi yayi kyau sosai. Wushe-wushe shine wuri daya da Yareema da Sa'ade Zasu hadu a
duk tsawon bikin su, makada ne aka gaiyyato daban daban daga garuruwa daban-daban ciki
har da HajjaGumsu da yaran ta da suka zo daga Maiduguri. Sai da aka taru ana kade-kade
ango ya zo cikin manyan kaya da abokan shi karkashin rakiyar Awaisu Ibrahim Waziri da kuma
sisters din shi mata su Mairam Murjanatu, Yaa Maira and co.zagaye da shi cikin laffaya mai
hasken sararin samaniya suna rike da kaskon turaren wuta suna turara shi, makadan fada na
biye da su,suna kide-kide da bushe-bushe suna wake Yarima da amarya Saadatu har su ka kai
shi mazaunin da aka tanadar musu shi da Saadatun.
Abokanen shi kuma aka yi musu shimfidun kilishi na alfarma daga gefen sa, sannan su yan
uwan shi mata su kuma suna zaune inda aka tanadar musu.
Sai aka cigaba da wasa da kide-kiden cikin zakuwar fitowar amarya, wanda yawanci sai an
dan ja lokaci sosai kawai dan a ja wa ango rai, haka aladar bikin masarautar Askira ke gudana
a kowanne bikin dan sarki.
Saade an shirya ta cikin laffaya an rufe ta ruf har kai. Sannan kawayen ta su Rahimah da
Hanne sun saka ankon dongasho da su murjani sun rike kaskon turarukan wuta suka sako ta a
tsakiya kamar yadda aka koyar dasu.Maman Rahimah da Innar Hanne na rike da ita cikin
rakiyar kide-kide har aka kai ta aka zaunar a gefen Yarima Sageer, wanda a lokacin da Saade
ta zauna a gefen sa sai da ya dauke numfashin sa na wucin-gadi. Kawayen ta kuma by her side
akan shimfidundake kallon na abokan ango.
Daga nan sai aka cigaba da kide-kide da wasanni.Saade bata yarda sun hada ido da Yarima
ba duk kokarin sa ga son faruwar hakan, bata ma