Showing 21001 words to 24000 words out of 29267 words

Chapter 8 - Masarautarmu Book 3 Hausa Novels By Takori Kabara

har Yareema ya gama sallolinsa, ya sunce ya shiga wanka. Da ya fito ya
tambayi Saade,
Manyan kaya zan sa ko kanana?
Ta yi masa shiru.
Ya ce, Alright. Bari kawai in sa kanana, ban sani ba ko saboda tsufana ne ba kya so na.
Ta juya masa baya bata ba shi amsa ba. Ya gama sanya kayansa riga da wandon
BALANCIAGA ruwan goro masu ratsin black. Sai ya fito a Georgeous Prince dinsa. Kai bazaka
ce ya taba aure ba.
Ya hawo bisa gadon daidai inda ta juya fuskarta yau zaki sha tea irin wanda baki taba shan
irin sa ba.
Sai ta rufe idanun ta gabadaya daga barin kallon sa, don ji ta yi zuciyar ta na racing.
A cikin dakinsa akwai karamar butar dafa shayi, ya jona kettle din bayan ya yi hade-haden
shayinsa na naa-naa da girfa, yadda Saadatu ta juya masa baya ta ki juyowa yana taba ransa,
sabida shi dai ba haka matarshi ta sabar mishi ba. Da sun wayi gari da ta soma haba-haba da
shi har sai ya ce ta dame shi.

Ya zuba kakkamsan shayinsa a dan karamin farin kofin shayi na karau, ya zauna a gefen
gadon daga daidai kafafunta yana sipping a hankali.
Kamshin shayin da yake sha duk ya cika ta, ya kuma tayar mata da appetite na abinci, sai
lokacin ta tuna rabonta da abinci. Tun na safiyar jiya da Hanne ta matsa mata ta ci lomar sinasir
guda biyu. Akuyar cikinta har wani irin kugi ta ke yi cikinta na murdawa da yake tana da ulcer
kadan tun a El-Kanemi. Dole ta mike ta nufi toilet ta yi brush, ta yi wanka ta kuma nemi pad din
da za ta canza ta rasa.
Kayan jikinta ta maida, wato doguwar riga mai bin jiki ta roba wadda ake sa wa a kasan
laffaya (underwear), ba ta nada laffayar ba ta fito gashin kanta da ya sha kitson nan jelunan sun
kwanta lambam a wuyanta. Kai tsaye ta nufi kofa don ta tuna Raheema ta gaya mata ta sa
mata pad din a lokar jikin gadon dakinta da suka kai ta jiya. Amma me? Kofar a kulle gam, kuma ya zare mukullin jiki.
Ta juya a sanyaye ta dube shi suka hada ido yana kurbar shayi, ya ga damuwa karara a tare
da ita. Ya ajiye kofin hannunsa a kan lokar gadon ya taso a hankali ya iso gabanta.
Hannayensa duka biyu ya zuba a cikin aljihun wandonsa, ya dube ta keenly, murya raunane
ya ce,

Me ya sa ki ke guduna ne Saadatu?

Ta sadda kanta kasa.
Ya ce, Ki kwantar da hankalinki kin ji, za mu zauna mu yi magana ta fahimta kafin mu tafi
Abuja, yanzu nan da awa guda za ki ga gidan nan ya cika, don haka ki yi hakuri ki ba ni one
hour in yi ta tare da ke, kada ki bar ni ni kadai.
Murya can kasa kamar an shake ta ta ce,
Zan dawo, abu zan dauko.
Gaya min ko mene ne in dauko miki, amma ba za ki bar dakin nan ba sai na miki umarni.
Kamar ta fashe da kuka, ta ce, Ba ka san inda yake ba, besides abin na mata ne.
Yarima ya ce,
Okey. I can relate. To mu je tare, kada ki yi min wayo ki shige daki ki rufe.
Ta turo baki, ta ce,
Na yarda. Sannan ya bude kofar suka sauka zuwa downstairs.

Bayin da aka ba su suna ta hidimar tsaftace gidan suka wuce su bayan sun gurfana sun yi
gaisuwa, yana kallo ta bude lokar ta dauko ledar sanitary pad ya sa ta a gaba suka koma
upstairs dinsa.
Suna shiga dakin ta wuce toilet, kafin ta fito Yarima ya zuba mata shayin da ya sha yana
firfita mata between two cups. Ta fito tana taku a hankali kamar mara gaskiya ta zauna a kan
sofa bed can nesa da shi ta zuba uban tagumi da hannaye bibbiyu.
Yareema ya taso zuwa inda ta ke, ya rusuna ya mika mata shayin, sannan ya zauna daidai
kafafunta, kai ka ce ita ce Yariman ba shi ba. Ta sa hannu ta karbi shayin don ba ta yi wa yunwa
fulako.
Ganin yadda ta ke shan shayin da sauri duk da zafinsa ya sa shi tambayarta.
Tun yaushe rabonki da abinci?

Saade ba ta ce komai ba, sai shan shayinta ta ke yi, kan ka ce me ye wannan ta zuke shi. Da
gaskiyar sa bata taba shan shayi mai dadin nasa ba da wartsake makoshi. Ya mike zuwa ga
bed side fridge dinsa, ya dauko danyar madarar oldenburger mara sanyi, ya zo ya bude ya
tsiyaya mata a tambulan ya zauna dab da ita ya kai kofin bakinta. Da farko kunya ta ji, amma kuma an ce mata suna son kulawa irin wannan daga mazajensu,
kulawar da ba duk maza ke iyawa ba sabida girman kan su. Sai ta ji ta kasa tankwabe wannan
kulawartasa, ta bude baki tana shan madarar sosai daga hannun Yareema, sai da ta shanye
madarar tas, zai kara mata ta ce a hankali, Ya isa.
Sai ya ajiye kofin ya juya ya kwantar da kai a cinyoyinta. Hannayensa zagaye da kugun ta.
Now, tell me Saadatu, why dont you love Sageer?
Ta rasa inda za ta sa kanta, sabida Uncle Sageer ya yi kwanciyarsa akan cinyoyinta, ya mike
kafafunsa bisa sofa din.
Uncle Ta fada a hankali very upset and unease. So take ta ce ya daga ta kada wani ya shigo,
amma kunya ta hana ta.
Kada ki kara ce min Uncle, ban san ta ina na zama Uncle dinki ba. Ni ba kanin Fulani ba, ni
ba kanin Baban ki ba...
Ni, (ya nuna kan sa) ni ne SAGEER kawai, Sageer Askira, ba ni da wani lakabi bayan
wannan.
Ya sa tafukan hannunsa a fuskarta.
Very smooth and supple. In ji dai ba shafe-shafen zamani ki ke ba? I love natural skin shi ya
sa nake son Sultana.
Ai ba ta san lokacin da ta ture kansa daga cinyarta ba ta mike. Allah ya so ta bai cire mukullin
daga jiki ba, ta bude kofar ta yi ficewarta.
An ce ko babu SOYAYYA kishin cikin AURE daban yake. Haka ta wuni ranta a bacea kan yar
maganar da Dr. Sageer ya fada akan Sultana, yayin da Dr. Sageer ya wuni cikin matsanancin
nishadi da bai taba tsintar kansa a ciki ba.
A yadda ya fahimta insha Allahu ba zai sha wahalar samun soyayyar Saadatu ba, tunda har
ta fara kishin matarsa. Dama ya fada ne don ya ga reaction din ta.
Ya canza kayan jikinsa zuwa Jabba da hular data dace da kalar kayan wato deep-brown, ya
fesa turarensa ya fito. Tuni bayi sun cika tebir da abinci naui-naui. wanda aka kawo daga
unguwar Fulani Bilkisu.
A cikin bayin da Maimartaba ya ba su akwai wata kuyanga Sadiya, burinta kawai Yarima ya yi
kwarkwara da ita ba tun yau ba, don haka ba karamin dadi ta ji ba da aka hado da ita cikin
hadiman gidansa.
Yanzun ma yana fitowa ta fadi gabansa,
Gyara kimtsi da kyau, lafiya dan zakin Duniya lafiya dan malafar duniya, lafiya dan mai fada
da cikawa lafiya dan mashasha lafiyarka dama da hauni mai nasara zauna daidai dan bawan
Allah zauna daidai dan masu alheri.
Yana zama bisa dining table ba tare da ya dago ido ya dube ta ba, ta hau yi masa firfita da
maficin gashin Dawisu tana ci gaba da zubo kirarin. Daidai lokacin da Saade ta bude kofar
dakin ta fito cikin wata irin sassaukar kwalliya ta riga da zane dark blue na yadin karen miski
wanda ba a samunshi koina sai gidan sarauta.

Wani kallo da ta sakar wa Sadiya ya sa ba shiri ta juya tana mata nata kirarin.
An fito lafiya uwar masu gida, zauna daidai uwar alheri taka lafiya matar Zakin duniya.
Saade ta kira sunanta a hankali kafin ta wuce ta ce,
Sadiya!
Kada ku kara zuwa nan in ba ni na kira ku ba. Lokacin aikinku daga karfe shidda ne zuwa
bakwai na safe, da kun gama jera abincin karin kumallo shi ke nan na sallame ku.
Sadiya ta amsa a matukar ladabce, sannan ta fice.
A ranta tana fadin, Ta Allah ba taki ba. Insha Allahu ni ce Sa-dakarsa ta farko duk boyon da
za ki yi masa, me ya kai ki auren Basarake in kin san kishi gare ki?
Yarima yana jinsu kansa a duke yana danna wayarsa, sai ya ji murmushi ya kwace masa. Ya
dauka zuba masa abincin ta fito ta yi, amma tunda ta kori Sadiya sai ta juya ta koma daki abinta
ta barshi a nan zaune.
Sai ya ji ya kasa ci. Ya zuba abincin daidai misali a kan plate, ya dauka ya bi bayanta.
Ta zauna kenan a bakin gado ta yi tagumi, wadannan yammata da aka cika mata gida da su
kullum suna sintiri a gaban Yareema yaya zata yi da su? Ta isa ta ce zata zauna babu kuyanga?
Ko cewa zata yi a kwashe su a kawo mata tsoffi? Kowa ya ji hakan a take zai fassara ta da
kishi. Ita kuma ta san ba kishi take ba tsoro ta ke ji, tunda ta san wa aka aura mata. Tana
wannan sake-saken sai gani ta yi tattausan hannun Yarima mai daure da agogon ‘Swatch
Blustery’ ya miko mata plate cike da soyayyen dankali da sauce din koda da hanta.
Saade ta dago ido a hankali ta dube shi. Ya daga mata gira, ya ce,
Karbi.
Sai ta kasa tankwabe wannan kulawar a karo na biyu. Ta sa hannu ta karba cike da jin nauyi,
ita ba ta ba shi ba shi ya dauko da kansa ya kawo mata, ta tuna wane ne Yareema Sageer a
masarautar Askira gabadaya da yadda kannensa da yayyensa duka ke sonshi da girmama shi.
In ta ce ba ta ji wani iri a ranta ba kan rashin kyautawar ta ta yi karya, sai ta ji somehowkamar
abin da ta ke yi ba daidai ba ne. Don haka ta motsa dan bakinta a hankali yana shirin ficewa
daga dakin tace.
Uncle kai ba za ka ci ba?
Ya juyo gabadaya ya fuskance ta sabida ya tsani wannan Uncle din da ta ke ce masa.
Ya ce, This will be the last time da za ki sake kirana Uncle tunda dai ni ba kanin Fulani ba ne,
idan ba za ki fadi sunana ba ki sa ma min wani. Amma ki ka sake ce min Uncle Allah zan cire
hijabin da ke tsakaninmu Saadatu, wanda ke sa ki yi min kallon kanin Babanki.
Maganar ta bata dariya amma bata yi ba.
Ya juya ya fice yana cewa, Mun tafi Ta-Sani ni da Awaisu.
Murmushi ya subuce wa Saade, kowanne irin hijabi ne tsakanin nasu? Oho! Ta maida hankali
ga cin abincinta, kunnenta har motsi yake sabida yunwa da dadin abincin wanda daga jin
kamshin sa ta san daga unguwar Fulani Bilkisu yake.

Yareema da Awaisu sun je sun gaida Alhaji Kyari, bayan sun gaida Maimartaba, sannan suka
wuce cikin gida, unguwar Ya Gumsu suka fara zuwa suka kwashi gaisuwa, ta amsa musu
kadaran-kadahan sai kallon Yareema ta ke da wutsiyar idanu kamar mai son gane cewa ya bi
umarnin ta ne ko aah? Ya maida Saadatu cikakkiyar matar sa? Tsoronta Allah tsoronta ranar da Sageer zai hada shimfida da Saadatu, don ta san daga

ranar ba za ta sake gane kansa ba,kamar yadda ba ta kara gane na ubansa ba tunda ya auri
uwarta, kai ba ita kadai mahaifiyarsa ba, har waccan baturiyar tata ta kare. Ita ta san sirrin
matan BAGGARA, ta san ta inda Fulani Bilkisu ta bi ta birkice musu kan miji kenan. Allah kadai
ya san iya abubuwan da ta koya wa yarta, da sirrin mallakar da ta dankara wa Saaden(Allah
Sarki ZATO. Mu kasance masu kyautata zato ga yan uwanmu musulmi, in ba haka ba za mu
kare ne da daukar nauyin zunubansu. TAKORI).
Daga wajen Ya Gumsu suka nufi unguwar Yaakirjiloma, Mairam Murjanatu na shirin tafiya
tare da yayanta, tana ganin Yarima faraarta ta fadada, ta ce,
Ka ga ango sha kamshi. Angon Saa da Aisha-Sultana. In ce ko an rago min kazar amarci?
Dariya Yareema Sageer ya yi, don yana son Yayarsa Murjanatu sosai, tana da son zumunci
da hadin kansu, shi sai yanzu ma ya tuna wai ana kai wa amarya kaza, shi haka ya tafi hannun
sa na dukan cinya, dan banzan Awaisun nan kuma bai tuna masa ba, amma babu komai bari
lokacin ya zo su koma Abuja, zai yi komai don Saadatu. Ko dawisu ne zai sa a gasa mata ba
kaza ba.
Ya ce, Mairam Murja, ba dai shirin tafiya ake ba? Na dauka za ku zauna har ku raka amarya
Abuja?
Murjanatu ta ce, Na so hakan, amma Ambassador ya yi waya maza-maza in koma sabida
yara sun koma makaranta, kada ka damu za mu zo suna next year in Allah ya yarda.
Yarima ya ji kamar ya nutse kasa don kunya, amma a zuciyarsa ya ji dadin wannan fatan
nata, fata na gari lamiri in ji masu iya magana, kuma babu wanda zai so ta haifa masa Da a
duniya irin Saadatu. Wani disappointment din is a blessing (Aisha Sultana da ta cire mahaifa)
don an ce yaya suna tsotso dabiu da halaye na mahaifan su. Ya ce, Wa zai kai ku Maiduguri (airport)?
Ta ce, Maimartaba ya bada mota da dogarai su kai mu, Humaira da Najaatu za su raka mu
har su ga tashinmu sai su dawo.
Ya fiddo wayarsa daga aljihun gabansa yana fadin, Bari in kira Suhail da Ahmad duk su raka
ku, tafiya da maza za ta fi dadi.
Ya yi magana da Ahmad da Suhail, sannan suka yi sallama da Murjanatu, suka karasa falon
Yakirjinoma suka yi gaisuwa ta sa musu albarka. Ta kawo turaruka ta ce a kai wa Saadatu.
Daga nan sai Unguwar Fulani Hibbani. Najaatu da Humaira suka gaida yayyun nasu, Sageer
da Awaisu. Humaira sai faman dauke kai ta ke don tsananin haushinsa da ta ke ji, ya rasa
wadda zai aura sai yar Fulani Bilkisu don kawai a wulakanta iyayensu? Ita tun filazal ta tsani
Saadatu sabida son da Askirama ke mata, balle yanzu da ta zama surukarsa kuma matar
Yarima dungurugum.
Shi bai kula Humaira na ciccin magani da shi ba, ya dube ta da kulawa, ya ce,
Auta, sai yaushe za a shigo mana?
Ta yi wani dan murmushi na dole, ta ce, Matarka Yaya Yareema Junior ta ce fa, ya za a yi ni
in je gaishe ta? Ai sai dai in ta zo nan mu gaisa.
Cikin mamaki ya ce, Junior? Don sam bai gane me ta ke nufi ba.
Ta ce, Kwarai, tare aka kai mu makaranta a El-Kanemi, ina aji uku tana aji daya, she has
been washing my pants and undies, kai har gugar kaushi ta ke min, everything.
Yareema ya kufula iya kufula saura kadan ya kai mata mari Awaisu ya rike shi.
Ya ce, Saadatun? Wa ya ce miki baiwar gidanku ce? To yadda ki ke ya a gidan nan haka ita

ma ta ke, idan watarana na ga kafarki a gidana sai na kakkarya ki, sakarai kawai.
Ya Hibbani ta fito daga dakinta tana daura dankwali, ta ce, Yareema mene ne? Ina barci na
ke jin tashin fadanka.
Nan ya gaya mata a gajarce. Hibbani ta kyabe baki, ta ce, Kada ka ga laifin kanwarka
Yareema, saboda da farko mu ba mu san yarta ba ce, boye mana ta yi. Cewa ta yi yar riko ce ta
karbo, so don Humaira ta sa ta aikatau a makaranta ba ta yi laifi ba.
Kada ka manta Humaira yar sarki ce, jikar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0