Showing 9001 words to 12000 words out of 31105 words

Chapter 4 - Canjin Rayuwa Book 3 Complete Hausa Novels Na Halima Abdullahi K Mashi

ki ne? To kazo momy na tana jiran ka a falo, ya ta6e baki, wacece kuma
momy? Tace, don wulaqanci, mahaifiyata dince baka sani ba? Ya kalli danqareren agogon
bangon falon, me kuma tazo yi da wannan safiyar? Ya kalli computer dake gabansa. Ta jirani,
aiki nakeyi, in zata iya, in kuma ba tada lokaci, taje ta dawo wani lokacin, in abinda tazo dashi
ya dame ta. Na'ima tace, wadda ta haifeni ce fa? Yayi mata wani kallon banza, cike da izgili
yace, don ta haifeki, ni ta haifa? Kuka ta fasa, sannan ta juya ta tafi ranta a 6ace, hankalinta
kuma a tashe. Cikin kuka ta sami momy nafisa
zaune a falo, tana zaune tana jiranta. Momy kinji abinda na sameshi yanayi? "me? " inji momy.
Na'ima ta fada jikinta, tana kuka, na sameshi yana waya. Don nayi masa magana, kai tsaye
yace min waishi yana neman mata. Kuma wai yana shan giya da wiwi. Momy nafisa ta zaro
idanu, cikin faduwar gaba tace, da gske? Kai inajin wasa yakeyi, zalayarki kawai yake. Kin ta6a
ganin mai aikata irin wadannan qazaman laifukan sannan ya fada ma matarsa kai tsaye? Dole
zaiji shakka. Ki barshi bari yazo.

Inna👬 Habiba Sa'ad:na ce Kwadayi madudin wahala na'im da mom Nafisa bakuga
komaibama ai😂😂😂
Canjin rayuwa

3�1⃣Na'ima tace, ai yace, ba zaizo ba, shi yana aiki. Momy ta yi shiru tana ta kallon Na'ima
cikin matuqar mamaki, sannan ta miqe. Muje gurin nasa, mara mutunci kawai. Na'ima ta kalleta.
Da kin barshi kawai momy, tace muje kawai, bazan dauki raini ba, gara in taka masa birki. Ta
tasa Na'ima suka nufi saman. Yana latse latsensa a computer, yaji shugowarsu, amma sai ya
dauke kai, yayi kamar baiji shugowarsu ba. Saida momy tace, bakaji Sallamar mu bane?
Sannan ya waiwayo, fuskarsa babu annuri, yace, naji. Ina jinku, aiki nikeyi, ina kwana? Duk da
baice su zauna ba saida momy Nafisa ta zauna, sannan tace "lfy" shine wato Abbas nace kazo,
amma kacemin kana aiki ko? Ya nuna computer da hannuwansa guda biyu, ba gashi ba kina
gani? Ya juya yaci gaba da aikinsa. Tace, to zaka iya bani 'yan mintuna muyi magana? Ya hada
tafukan hannuwansa wuri daya ya murza tamkar mai jin sanyi, sannan yace, kamar minti nawa?
Ta zaro ido cikin mamaki. Abbas ni kk tambaya? Ashe baka da mutunci har haka? Da sauri ya

juyar da kansa gefe yana kuma dannar zuciyarsa, don kar ya nuna mata ainihin kalarsa. Taci
gaba da cewa, to zuwa nayi inji laifin da Na'ima tayi maka da har zaka soma wulaqanta ta daga
kawo ta. Har na qaryata ta, sai kuma gashi nima ka gwadamin. Ya kalli Na'ima, me nayi miki
harda zaki kai qara ta? Tace, ko Yanxun dana shigo ba na sameka kanayin magana da wata
bane? Ya daga murya cikin zafin rai yace, me ya dameki don kin sameni ina waya da wata?
Meye naki a ciki? Ya kalli momi, tunda taxo gidannan ban ta6a shiga harkarta ba sbd banason
matsala. Tayi harkarta inyi tawa.
[8/19, 11:16 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 3�2⃣Momy tace wannan kuwa ba zai yiwu ba
kana mijinta. Sannan kace, kowa yayi harkarsa? Ko kuwa dama baka amince da auren bane?
Ya miqe tsaye yana kallon momy tare da cewa, "au dama baku sani ba? Ya girgiza kai, ni gsky
mimi na gani nace inaso. Momy tayi shiru tana kallon sa, gabanta ke faduwa, damuwa ta
bayyana qarara akan fuskar ta. Ta sauke ajiyar zuciya, ta rasa me zata ce, sai ta kalleshi tare
da aje fushinta, to ynxun me kace? ko ince me kk nufi? Ya kalleta, ban gane ba. Momy tace,
matsayinta. Yayi murmushi, sannan ya koma ya zauna kan kujerar computer tare da yin juyi.
Ban sani ba gsky. Momy ta miqe tsaye ta sake daga murya, to me ya hana ka cewa iyayenku
baka sonta tun kafin a daura auren? Yace, momy karki kiji haushi na. Ko na fada musu ba zasu
fahimceni ba a wannan lokacin tunda suna da burin kansu. Ya nuna Na'ima, ke kuma ki bani
lokaci, in burikan iyayen mu sun cika, sai in sauwaqa miki. Da sauri momy ta katse shi da cewa,
ha Abbas, ai ko mutuwa tana kunyar idon mahaifi, inji masu magana. A gabana kk fadin
bakason 'yata? Yayi guntun murmushi, momy kenan. Don dai ni ba danki bane, saiki takura
min? Ya kamata kusan cewa, shi so ba'a masa dole. Ni mimi na gani nace inaso. A tsari na
farar mace nake so. Kinsan kowa da ra'ayinsa. Qila da fara ce da nayi manage. Momy ta miqe,
shikenan na fahimce ka. Yace, Yauwa nagode da kk fahimceni, kuma naji dadin haka, don ni
mutum ne mara son takura. Ta kalli Na'ima, tashi muje.
[8/19, 11:16 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 3�3⃣Na'ima wadda ke ta faman kukan takaici, ta
miqe tana cewa, nidai kawai momy ki tafi dani, bazan iya zama ba. Yace, kin kawo shawara, ku
tafi tare kawai momy, ta dube shi a qufule. Babu inda zanje da ita, zan kuma sanar da
mahaifiyar ka, daka-duka auren yau kwana biyu, sannan ace tana gida? Yace, umm, yadda
kuka za6a haka zakuyi. Amma in da zakiji shawara ta, da sai ince kar ki kai qara ta gurin momy
na, sbd itama irinki ce, tafi son 'ya'yanta akan na kowa. Ni dai kunji ra'ayina. Sannan don Allah a
daina takura min, a kuma guji shiga harkata. Basu sake cewa komai ba suka fice. Shi kuma yaci
gaba da aikinsa. Dakin Na'ima suka koma sukayi jugum-jugum. Na'ima tana ta faman kuka.
Mommy ta kalleta cikin damuwa, sannan tace, share Hawayenki. Badai farar mace yakeso ba?
Na'ima tabi ta da kallo. zamu duba mayukan cikin akwatinki, in babu wanda zaisa kiyi fari,
saimu shiga kanti. Kafin da wata guda, sai kin koma tamkar baturiya. Daga nan sai ki dinga yin
duk wani abu da zaki ja ra'ayinsa. Na'ima ta dan ta6e baki tallafe kanta sbd tsabar ciwon da
yake yi, tace, hmm mu gwada mu gani, haka suka sauke kafatanin kayan shafan dake cikin
lefen, amma basu fahimci komai ba, ma'ana basu gane ko mayukan zasu iya yi mata bilicin din
ba. Momy ta dafa Na'ima, cikin sigar lallashi, karki damu Na'ima, zan nemi Shawarar Aminiyata
hajiya nana, domin na ta6a jin suna zancen qwayoyin da suke saka fari. Na'ima tace, to kafin ta
wuce saida ta tabbatar hankalin 'yar tata ya kwanta, ta nuna mata cewa ta zauna tayi haquri, ta
zauna kada ta sake maganar tafiya. Ta kwantar da hankalinta, wata rana sai abin da tace masa
zaiyi.

Canjin rayuwa

3�4⃣V Momy dai ta tafi cikin takaici, ta bar Na'ima cikin damuwa. Ta jima sannan ta tashi
ta shiga cikin kicin dinsu masu aikinta ssuna ciki. Dattijuwar tana zaune tana firar dankali.
Yarinyar kuwa tana wanke-wanke. Daqyar ta amsa gaisuwar da suke mata, wai ita dole ga
matar gida, ta kalli tsohuwar, me za'ayi da wannan dankalin? 'Yalla6ai ne yace ayi masa cips da
shayi. Na'ima tayi sororo, cikin muzanta, domin itace ya dace tayi masa, ko kuma tazo tasa ayi
masa, amma sai ta wayance da cewa, dama har ynxun baku kai masa ba? Dattijuwar tace,
hajiya zuwansa kenan yazo yai magana. Na'ima tace, ni bance sai kinyi min lissafi ba. Inason ki
gasa min bread da kifi, Na'ima kenan. Wannan kuma ai cimar mimi ce. Yinin ranar, Na'ima ta
kasa sukuni. Domin ita gsky tana matuqar son Abbas. Tana jin lokacin da zai fita wuraren daya
saura na rana, ta fita taje gurin window tana leqensa har ya dau motarsa ya fice. Qarfe goma da
mintuna na dare, taji tsayuwar motarsa. Cikin sauri ta fito falonta wanda tasan nan ce kadai
hanyar binsa don hawa samansa. Ta dau gayu cikin riga da wando matsattsu, kanta babu dan
kwali, tayi wankan turaruka har maqaqi suke mata a wuya. Sai dai kash! Tayi dana sanin fitowa
daga dakinta, don burge angonta, domin kuwa da wata budurwa ya shigo, bayan ya buga alarm
ta bude, sororo tayi cikin tsananin kishi, ba tada wata power da zata iya ce musu wani abu.
Kuka ta saka sannan ta juya ta nufi dakinta. Abbas ya kalli Jenifer, kin gani ko? Har ynxun babu
kamarki, tayi murmushi suka nufi samansa bayan ta saqalo hannuwanta a qugunsa. Tana fadin,
na yarda honey.
[8/20, 10:57 AM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 3�5⃣Cikin matsanancin kuka, Na'ima ta kira layin
momy, wadda shugowarsu kenan daga asibiti, ita da daddy. Jikinsa da dan sauqi, shine ya
matsawa likitan ya sallamesu, don ya tsani zaman asibitin. Momy Nafisa bata son daddy yaji
wannan matsalar, don haka taqi dagawa, saida ta shiga dakinta. Tana dagawa ta fara da cewa,
meyasa bakida haquri ne? Na'ima ba nace zanyi shawara bane? Zan kiraki da kaina. Tsaya kiji
momy, da karuwa fa ya shigomin gida. Karuwa?? Momy ta tambayi Na'ima. Ta rantse, sannan
ta ci gaba da cewa, ni bansan yaya zanyi ba ynxun, Momy tace, ki barshi zuwa gobe zanje
gurin uwarsa. Na'ima ta shiga daki, ta zauna bakin gado cike da nadamar auren Abbas. Kuka
take sosai, amma babu mai lallashi. Qarfe shida na yamma, innar su Zainabu ta shigo tare da
Aminiyata, inna yalwa, suka sake dawowa gidan Zainabu, ta danji dama, tana zaune kofar
dakinta. Jin muryar innar tata yasa gabanta faduwa. Rai a dagule ta kallesu, sannan ta shiga
dakin, suka bi ta ciki, Aminiyar inna ta kalli Zainabu, meye kika dagule rai? Zainabu ta sunkuyar
da kai. Ni wallahi da baku dawo ba, za'a ce iyaye na suna ta sintiri. Da ma aikowa kawai kuka
yi. Ni bana son abin gorin nan gidan. Inna tace a daura miki goruba, mu dai in burinmu ya cika
ina ruwan mu dasu? Inna yalwa tace, anqi a turo wani din, basha zakiyi ba. Ta daga hijabinta, ta
ciro wata gora mai dauke da maganin da suka hado. Tace, zauna kisha shi maza-maza.
Zainabu ta soma kuka tana shan maganin. Tasha kusan rabi suka ce, ki ajiye Anjima sai ki
shaki shanye sauran. Karki sake baki shashi ba. Tun fitarmu daga gidannan, muna can muna
qoqarin hadoshi. Don haka ki maida hankali ki shanye.
Canjin rayuwa


3�8⃣Alhaji lawal ya dawo gurin su Maman bushira yanata zage-zage, wai shi za'a kawo wa

raini da rashin mutunci? To, shifa ba zai bada jininsa ba bare kuma kudinsa. Duka-Duka yaushe
ne akayi auren ma? Ko wata daya ba'a yi ba za'a ce har tanada wani ciki? Uwar gidan tace,
haba Alhaji yaya kake irin wannan maganar? Sbd Allah, dubi yadda mutane suke kallonka. In
jiya kuka yi aure, ai ba abin Mamaki bane ku wayi gari da ciki. Kai dai kayi fatan samun
sauqinta, ka kuma bada duk abinda ake nema. Ya kalleta a fusace, sisi na bazai ciwon kai ba.
Zanje in fadawa uwarta, wadda ta kawo mata maganin zubar da ciki. Sai su zo suyi jinyar ta, da
kuma kudin sun, tace haba Alhaji don Allah ka duba wannan al'amarin. Cikin tsawa yace, in
zakije gida, kizo muje! In ba zakije ba, in tafi. Tace, abarta da wa? Tsaki yaja, sannan ya wuce
abinsa. Nurse tazo ta kira maman bushira zuwa dakin da aka ajiye Zainabu. Sannan taba ta
wata takarda, ta nuna mata wata qofa, ki shiga zakiga wasu nurses, anan ne zaku biya kudin
gadon, sannan zasu rubuta muku takardar shaidar biya. Likita zai shigo ya rubuta magungunan
daya kamata tasha. Maman bushira dai, to, kurum tace, tana tsaye da takarda bayan tafiyar
nurse. Gashi ba tada ko sisi tunda fitar bana shiri bane.
[8/20, 9:17 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 3�9⃣Shi kam Alhaji lawal, kamar yadda ya fada,
gidan su Zainabun kuwa ya zarce. Kafin ya kai saida ya kira direbansa, dan korensa. Bayan ya
daga, sannan yace, iroro kana ina ne ynxun? Yace, Alhaji naje gidan, ance kunje asibiti da
amarya ba lfy. Alhaji yace, mu hadu gidan iyayenta ynxun nan. Ka hau aca6a. Yana isowa qofar
gidan, ya hangi iroro har ya iso, suna tsaye da dan acha6an, iroro ya nufo Alhaji yana cewa,
sannu da qarasowa Alhaji. Alhaji yace, har ka rigani, to me kuma dan acha6a ke jira? Iroro
yace, banida ko kwabo Alhaji, daman kai nake jira in sallameshi. Tsaki Alhaji yaja, sannan ya
ciro naira dari biyu ya miqa masa, iroro ya amsa tare da cewa, Yauwa. Ya biya dan acha6a,
sannan ya zuba sauran aljihunsa. Ya kalli. Alhaji, "lafiya dai kazo nan? Alhaji yace, zuwa nayi in
sanar da iyayen Yarinyar nan Zainabu suje suyi hidimarta a asibiti. Kaji ma wai har tanada ciki,
Duka-Duka yaushe akayi bikin? Iroro yace, tafdijam! Ba don ma baka mori kudinka ba ai da
sakinta kayi kawai, ka kawo wata. To, jinyar cikin takeyi a asibitin? Alhaji yace, sun dirka mata
maganin zubar da ciki, jini ya 6alle mata. Ai shiyasa nace, suzo suyi jigilar, iroro yace, kayi gsky
Alhaji. Kuma zan soma duba maka madadinta tun daga ynxun. Alhaji yace, shiyasa nake
matuqar sonka iroro. Sau da yawa in kayi magana, kamar ka shiga raina. Da ace ta kwana biyu,
zuwan nan da nayi, yadda take asibitin nan, da takardar ta zanba iyayen ta. Amma su gama
jinyarsu, zan dawo da ita, ba zanyi asara ba, kuma ba zamuyi dogon Zango da ita ba, don daga
gani ita irin masu jarabar haihuwarnan ce, sai kace 6era.

Canjin rayuwa

4�2⃣Cikin fada likitan ya shigo, ya kalli Ismail, "kai kanaso ne sai zuciyar ta ta buga
tukunna? Me zaisa ku fada mata mutuwarsa? Don Allah ku fita waje, banason ganin kowa anan
sam. Bai saurari kowa ba, bare yasan ba laifin Ismail bane. Gaba dayansu sukayi waje,, Ismail
yana cewa, kun gani ko? Nasan dama laifina zai gani. Cikin kuka mai tsanani, mahaifiyar khalil
take cewa, kuyi haquri, nima ban sani bane, Mahmud yace, karki damu hajiya, babu komai,
shidai Allah ya jiqansa. Tace Ameen, bari mu tafi, Allah ya bata lfy. Ameen ya rabbi, ina fata 'yan
sandan sun baku jakarsa da wayarsa ko? Sai dai ban sani ba, tunda tare da mahaifinsa muka
zo, qila sun bashi, Mahmud yace, 'yan sandan sunzo lokacin da mukazo. Tace bari zanyi musu
magana in munje. Mahmoud yabi su da kallo, suka tafi cikin damuwa. Ismail kam tamkar zuciyar

sa ta buga don damuwa. Ya qosa likitan ya fito don yasan halin da ake ciki. Ya kusan rabin sa'a
tare da taimakon nurses, sannan ya fito, ya kalli Ismail, fuskarsa a daure, ku biyoni office. Sun
sameshi a tsaye yana duba wani file. Suna shigowa bai zauna ba, kuma bai musu izinin su
zauna ba. Sai ma fada da ya hau yi musu, tare da cewa, kasan meye? Kaje ka samo wacce
zatayi jinyar ta, domin kaikam baza ka iya ba. Ismail yace, doctor ba laifina bane, nan ya sanar
dashi komai, likitan yace, shikenan, daga yau zuwa gobe bamason ganin koea gurin ta. Ina
nufin 'yan dubiya. Likitan ya sassauta murya, ka nutsu sosai, ka lallasheta, sbd kasan dole ne ta
zamo ta farka cikin damuwa da tashin hankali. "Ismail yace, Insha Allah. Na gode likita. Ynxun
ta farfado ne? Mun kuma yi mata allurar varci, bamu fito ba saida varcin ya dauke ta. Don haka
saiku kula sosai. Tashi kuje, za'a zo a dabi jinin naka ynxun. Ismail yace, to nagode likita.
[8/21, 4:10 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 4�3⃣Suna fitowa suka dawo gurin su Mahmud,
yace vari ya wuce, sai zuwa anjima. Ismail yace, Allah ya kaimu. Bayan tafiyar su, Ismail, a
hankali ya tura dakin ya shiga. Ya jima tsaye a kanta, yana kallon ta tana varci, ya juya ya koma
kan kujera, zamansa keda wuya, sai aka turo qofar dakin. Ya dago ya kalli mai shigowar, Namiji
ne da riga fara, irin wadda likita ke sawa, sai wasu kayan aiki dake hannunsa. Yace. Kaine
Ismail bin Abdurrahaman? Ismael yace, Na'am, Mutumin yace, nazo ne in debi jininka. Ismail
yace, to bismillah. Bayan an dauki jininsa ne, sai wata nurse ta kawo masa wani dan tea a kofi
da wasu 'yan qwayoyin magani, yasha ya dan kishingida, kafin lokacin sallah. Bayan la'sar, sai
ga babban wan su Ismail yazo, lokacin Ismail yana dawowa daga masallaci, suka shiga ya duba
ta. Har lokacin bata farka ba, bayan sun fito yace masa, ance zata gudu ne tayi hadari. Ismail
Yace, eh, yayan yace, in bata sonka dolene? In ta warke ka maida musu 'yarsu, Ismail bayason
doguwar magana, don haka yace wa, to, sai ya sake cewa, ka fadama iyayen ta? Yace eh, da
haka suka kai qofar asibitin, inda yayan ya hau mashin, shi kuma ya koma ciki. Duk fargaban
Ismail, in ta farka baisan dame zata tashi ba, bai san wane qalubale zai fuskanta ba. Kuma shi
gaba daya ma zaman asibitin ya gundure shi, sam ya qosa ya barshi. kiran hajiya sauda yake
shigowa, sai lokacin ya tuna da zancen account number da tace ya tura mata. Suka gaisa,
bayan ya daga, tace masa. Baka turo ba, gashi har yamma tayi. Yace, kiyi haquri hajiya, kaina
ne yadau zafi. Ban tuna ba, kuma banida account nawa na kaina, sai namu na makaranta.
Insha Allahu dana sanar da malam Aminu zan turo. Tace, zancen dorin fa? Yace, sai gobe.
Ynxun dai jini za'a qara mata. Tace, an samu jinin ne? Yace, eh, nawa ne za'a sa mata. Tace,
Allah ya bata lfy, sai naga number, yace, insha Allahu.
Canjin rayuwa
4�4⃣Ismael ya shanyo kwanar da zata kaishi matakalar da zai koma dakinsu, sai kurum
ya hango innarsu Zainabu, ita da aminiyarta hannunta riqe da wata takarda. Ya jira har saida
suka iso gurinsa, sai dai da alamu innar bata lura dashi ba. Yaji tana cewa, wannan maganin shi
kadai dubu daya da dari bakwai, su kuma sauran kudinsu ya zama nawa? Qawar tace dama
nice ke, tunda ta samu dan qwarin jiki daukarta zanyi mu gudu, mu bar asibitin. Baiji mai innar
tace ba, sbd lokacin sun dan gota shi, ya hau sama yana tunanin, to wa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login