Showing 12001 words to 15000 words out of 31162 words

Chapter 5 - Darajar Yayana 1 Complete By Halima Abdullahi K Mashi .pdf

bayan sun fita suka tafi banki in da ya
ciro kudi suka dinga yi masa lissafi yana ba su,
nan fa suka ce jibi za su yi hutu, suka amince a

haka. Ni kam ko da suka dawo bai fada min ba
gurin Anty Abida na samu labarid Usman ke fada
mata, na ce shi dai ya sani can da yawarsa.
Idanu na zuba ina kallonsa yau da na ga yanzun
yana dan zakewa tare da rawar kai, sam ban zata
ba, ya sa a yi gyaran gida. An yi fenti na kwashe
kayan yarana daga dakin da ta zauna tunda nan
za'a sa ta, ya ce da ya so canza min gado,amma
in yi hakuri ko daga baya ne. Yaba ni dubu
talatin,na yara ashirin na karba na aje tare da
cewa mun gode. Na dauki waya ta ina dannawa
ya ce, Wai Sadiya akwai wani laifi da nayi
makine?na kalleshi' Me ka gani? Ya ce, Na ga tun
jiya da na zo ba wata fuska a gurinki?Na maida
kaina ga kallon wayata,sannan na ce, Akwai abin
da ban makaba daga cikin wanda na saba
yimaka?Yace, A'a,kin min komai MY CHOICE, sai
dai ni na gane kamar ba ki da walwala. Na ce, Ba
ka yi min komai ba. Ya ce, To anjima zan tafi, Na
ce, Allah ya kai mu. Har ya kai bakin kofa na ce,
Au! Na manta in fada maka an dauke ni amma
ba aprimary ta nan unguqar Ma'azu ba, ta can
Tudun wada. Ya tsaya yana kallona, nima shi
nake kallo don son jin ta bakin shi,a zuciyata ina
cewa yanzun dai a ce ya hana ni, tabdijan! Da sai
ya ji magana. Tamkar ya sani sai ya ce na san
kina zaton zan hana kineko? Ai ba ni da yanda
zan yi tunda na rigana yi miki alkawari,amma ki
sani raina baya so. Ban ce kala ba na ci gaba da
danna wayata shi kuma ya fita.
Ban tabbatar da cewa ina da kishi ba sai da
lokacin auran ya gabato,wallahi ko abinci kasa ci
nayi duk datausar da Aisha ke min da kuma Anty
Abida dan ganin na kwantar da hankalina, amma
na kasa, bana bacci sosai duk da cewa bana
nunawa Yaya damuwata sai dai shi duk lokacin
da muka yi waya sai ya yi min korafin in daina
damuwa in kwantar da hankali,To kurum nake ce
masa, amma zahirin gaskiya zantukansa ma soya
min rai suke yi.
Ana gobe daurin aure zasu tafi can Lagos din ina
kallo shi yana ta shige da fice yana shiri,an zuba
sababbin dinkuna an sai Huluna da Takalma sai

ina mamakin mutumin da na dinga shan kan shi
da kyar shi ne yake zumudi. A fili na ce Allah
yasa abin ya tsaya nan. Ya fito cikin shiri ina
kwance kan gadon yara ya ce 'My Choice mun
shirya,na dago na kalle shi, yayi matuqar kyau
cikin Shadda Wagambari Blue shar kaladaya da
hularsa mu hadu a banki, kamshinsa ya cika
gidan, kishi ya kama ni mai tsanani,na kau da kai
gefe. Ya ce, 'My choice yaya ne? Ban tanka masa
ba sai zuciyata ta ce gwada shi ki gani da yake
cewa in na ce ya fasa zai fasa,in ya so duk ma
abin da zai faru to ya faru. Ya tallabo fuskata.
'My Choice, yaya ne? Na ce, 'Ni fa gsky na sake
tunani a kan wannan auran, gaskiay ina tsoron
abin da zai biyo baya. Zai fi kyau a barshi.
Zumbur ya mike tsaye daga russunawar da ya yi,
na kalle shi ga mamakina fuskarshi daure, ya ce,
'Me ki ke nufin maidani? Karamin mutum? Kin sa
mun yi magana yanzun kuma kizo ki ce ke kina
jin tsoro, ya kamata ki fadi haka ne tun kafin
yau, sai dai ki yi hakuri,mamakida tsoro suka sa
na kasa daina kallonsa sannnan ga hawaye yana
ta zuba tamkar an bude famfo, na girgiza kai
tare da sauke ajiyar zuciya,sai kuma ya zauna
kusa da ni tare da dafa kafadata. My choice bana
nufin cutar da ke kece kika karfafani kika nuna
min yin auran nan shine mafita, to me zai sa
yanzun ki bijiro min da wani sabon batu bayan
aski ya zo gaban goshi? Kuka ya kwace min na
shiga rera shi, tsam ya makaleni jikinsa yana
lallashina. Sadiya in kin ce baki so wallahi abar
shi. Ya ciro wayar shi yasoma dannawa. Bari na
fadawa Usman ya kira Yaya Sulaiman ya fada
masa cewa nafasa.ina jiyo shigar wayar ta soma
ringing a can,da sauri na dago na amshi wayar
da sauri na katse. Ya ce, yaya kuma za ki katseki
bani in dakatar dasu su daina shiri. Na cecikin
shagwabar kuka, Ni fa ban ce ka fasa ba.yasa
hannunsa ya dago fuskata,To me kika ce?Na kalli
cikin idon shi 'In ka aure ta zaka daina sona? Sai
kurum naji bakin shi cikin nawa, minti1muka
dauka, sai wayarshi ta shiga ruri,ya sakeni tare
da daukar Wayar. Usman ina zuwa. Ya katse ya

kalleni. My Choice in na yi rantsuwa bazan yi
kaffaraba Ke ce 1 tak nake so, kum na soma son
ki ne tun lkcn da kika soma zama mace. Da farko
ban fahimci ina sonki bane sai da Usman ya
kwadaita mini da nazo iya ta ki sai na samu kaina
da kasa hakura, wannan ya tabbatar min cewa
ina mutukar sonki,Ke ce zabina, kada ki damu da
Mujidat sam ba na son ki hada son ta da naki, Ke
ba ita ba in miki ta mahaukaci duk duniya ba
wata mace da nake so ko kuma zan sota sama da
ke, ki rike wannan a cikin zuciyarki,so 1 tak Ke na
ke yiwa shi.,lumshe ido na yi inma karya Yayaya
fada min to na yarda don gaskiya maza da ace
zasu gane furta son ka ga matar ka komai
dadewar aurenku yana susutar da mace komai
shekarunta ta ji ta tamkar sabuwa,amma
matsalar maza musamman irin na yankinmu ba
sa iya cewa matar su suna sonta, ko wasu
kalamai na soyayya irin wanda suke yi mata yayin
yakin neman aurenta da zarar sunga cewa sun
aurenta shi Kenan ta tsufa Nima haka na ji
tamkar farkon aurenmu duk damuwar dake cikin
zuciyata sai ta gushe, sabida ina son a so ni,ina
son a nuna min soyayya, ina son a fada min
kalaman so. Nasa hannu a kumatun shi na shafa
ina kallon cikin idon shi, Yaya na gamsu da
kalamanka, Allah ya tsare hanya gobe zaku
dawo? Ya ce, insha Allah ko jibi, tunda da nisa in
mun taso da yamma ko da dare sai safe zamu
iso. Na ce shi Kenan. Ya mike tsaye, me zan sayo
miki a can? Na ce, gdnsu lesuka, in ka siya min
zanyi murna. Ya ce insha Allah zan zabo miki
masu kyau. Na ce to nagode. Har waje na raka
shi. Sai dai duk da haka kasa bacci nayi daren
ranar sai damuwa da sake saken zuci.
Washe gari kuwa data kasance ranar daurin aure
ba zan iya lissafa tashin hanklin da na shiga ba.
Da safe kasa zama na yi a gidan na tafi gidan Iya
wai don in manta da batun auren amma duk da
haka na kasa sukuni, har Iya ta fahimta, sai
kurum naji ta ce. Sadiya, hakika kishi wani abu ne
mai rai, amma yana da sauki in kin saukakashi,
ina son ki nutsu ki rike girmanki. Shawarar da zan

baki ki kara zage damtse gurin kyautatawa mijinki
kada ki dauki halayen wasu matan masu cewa in
miji ya kara aure zasu daina yi masa komai suce
ya je can matar da ya auro tayi masa, wannan
kuskure ne, don in aka samu wadda ta san
hannunta kafin ki samo mijinki sai wani ikon
Allah,ki zama a gidanki Ke ce uwar kowa. Ina
nufin duk abinda ya taso na kudi ko matsalar
lalacewar wani abu a gida Kar ki tsaya jiransa kiyi
da kudinki in yaso in yazo kya karba ko yaturo
miki, sannan ba'a fata in har sabani ya shiga
tsakaninki da ita tunda an ce zo mu zauna zo mu
saba, to kada ki sake ki fara kai kara Kinji ko? Na
ce, to. Yauwwa sabida in kinyi nazari cikin
ya'yanki mai yawan kawo kara duk gaskiyarshi sai
kinji haushinsa. Na ce, haka ne. To ki rike hakuri
da addu'a ki dinga yawaita karatun Alkur'ani mai
girma, ki zauna da ita zuciya1, sannan ga aikin ki
ma, ai ni naji dadin barin ki da yayi wannan
koyarwar, na ce, nima naji dadi iya, don ina da
yara gara dai yanzu da muke mu 2 aikin ya dauke
masa matsalolina in ina samu ba sai na jira shi
ba, kudin da ya bani ma nawa da yara wai muyi
siyayya su dai na Dan sai musu wani abu, so
nake in hada jari in dinga saye da siyarwa. Iya
tayi dariya tare da cewa, da kyau Sadiyayyena.
Haka nayini Iya tana kwantar min da hankali tare
da bani shawarwari sai kusan 10 na dare na debi
ya'yana ta raka mu har gida, nima na sake rako
ta hanya.ina sa hakarkarina a kan gado na dauko
wayata nakunna dama yinin ranar kashe ta na yi.
Nan fa sakonni suka soma shigowa na yaya sai
na Aisha da Anty Abida, na su na soma dubawa.
Tanbayata suke ina naje sun zo ba nanan? Na yi
dan murmushi, a fili na ce da kun zo gidan Iya ni
kam ba zan yi wani taro ba, sai na soma duba
nashi,duk kusan yana nuna damuwane akan ya
kira bai sameni ba. Sai na karshe da yake cewa
sun taso 9 suna hanya, akwai yiwuwar su iso
kafin 9 na safe, kuma suna tare da wasu daga
danginta dan Allah ta tanadar musu abinci. Kiran
Abida ya katse karatun sakon da na keyi, na daga
muka gaisa, ta ce min, ina na shige yau? Na ce

ina gidan Iya,tace to, ki yi sammakon tashi don
mijinki zasuyi shigowar safe ne, nace Anty me
zanyimusu?tace karin kumallo mana kiyi zuciya1
kada ki sa kishi ciki, bakin kine, kin kuma san
darajar baki a musulunci. Na ce to Aunty zanyi.
Tin 4 na tashi na fara firar dankali da nayi sallah
kuma na hau suya, har kaji biyu nayi musu
farfesu, kwai ma isasshena yi musu kwai da kwai
na dafa ruwan tea mai yawa, sannan na gyara
gidana nayi wa yara wanka na zabo musu
sababbin kaya nima na sheka nawa adon.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Takwas daida na ji tsayawar motoci,gabana ya
yanke ya yi wata muguwar faduwa,sai na hau
karanta Hasbunallahu wa ni'imal wakil. Na mike
na je na bude musu kofa gabana yana ta
faduwa,zuciyata tana maimaita addu'a.suka shigo
suna yi min sannu, wasun su suna kallona wani
iri,amma duk da haka na saki raina ina yi musu
sannu da harshen Turanci.Najee na bude musu
dakin suka yi sororo a tsakar daki don ga
al'adarsu miji ke shiryawa mace daki ya zuba
komai, ita kuma iyayenta su yi mata kayan sawa,
nan fa suka soma yare, duk da bana ji amma
ganin yanda suke magana suna tabe baki na
fahimci zancen nasu bana dadi ba ne, naje
nasoma fito musu d kuloli. Sai gasu Yaya sun
shigo, na kirkiro fara'a ina yi musu sannu da
zuwa. Falo suka je suka zauna na gabatar musu
suma da abin kari, na kula yaya ya ji dadin
yanda na saki jikina na kuma yi musu abin
kari.Nan nabarsu nayi daki,bayan Mujidat da
danginta sun gama karyawa sai suka samu su
Aliyu da Usman suna yi musu korafin ba su ga
kmai a dakin ba.Usman ya ce, Mu a nan da kaya
amarya take zuwa. Suka ce su kam ba haka ba
ne, nan suka fito masa da akwatunan amarya
har da na mijin da na Maman shi da kuma na

danginsa. Aliyu ya ce shi kenan zai siya daga
baya, amma yanzun a kwaso na dakinsa a sa
mata,sukace bakomai. Ina dakin nashi ya shigo
wanda zuwa yanzun ya zama nawa,ya zauna.
Sadiya kin ji wata sabuwa. Na kalle shi, ya ce,
Wai ni zan sai mata gado. Na ce, ina zaton haka
al'adar su take don mun taba yin zancen da wata
'yar ajinmu da muka yi N.C.E take ba mu labarin
al'adunsu, miji ke yin kayan daki kuma sadakin
su yana da tsada, amma mace za ta ja jari da su
ita ce za ta rike gida,wasu kuma jarin daban miji
zaibada, wadanda ba Musulmi ba sun fiyi,
Musulminsu kamsai sunyi aure suke tarewa gidan
mazajensu,yace,nidai yanzun ya za'a yi? Na ce su
zo su dauki wannan gadon. Na tsura masa ido
cikin mamaki,sai ya ce, ko ya ki ka gani? Na mike
na nufi dakina bayan na ce, Me zan ce kai da
abinka. Na shiga dakina na soma kallon dakin ina
lissafa yanda zan gyara shi ni da yarana da na
bar musu gadona tunda dama katifu gare su. Sai
ga shi ya shigo.Haba Sadiya,me zai sa ki
yankemin wannan hukuncin? Nazo miki da
shawara amma sai ki yi watsi da ni kitaho abin
ki? Na ce, Yaya kainefa da abinka kuma ka ba
matarka, mene ne laifina dan na taho? Yace, Ok,
kije amma ki sani kada nan gaba ki ce na daina
kawo miki Shawara,kin sani dai ke ce kurum nake
tunkara da duk matsala ta. Shiru na yi dan nasan
in hakan ta faru lallai ba zan zama uwar gidaba.
Ya mike zai fita na ce, Yaya'' ya dawo,Mene ne?
Na ce, Shi kenan ka yi hakuri. Ya zauna tare da
kamo hannuna, Nagode da ki ka fahimce ni,
yanzun ya ki ke ganin za'ayi? Na ce, Ka ba ta,ni
kawai sai naringa kwana a nan da yarana. Ya
tsura min ido, To nifa? Na ce, Ba komai ka yi ta
kwana dakinta. Ya yi dan murmushi, Har yanzun
baki huce ba.Na yi 'yar dariyar yake, Bana fushi
da kai. Yace, Zan siyo katifu yau a sa can dakin in
komai ya warware zan canza gadajen gidan.Na ce
to maimakon ka ba ta tsohon gadon ba gara ka
sai mata katifar ba? Amma yanda ka gani, Ya ce
na riga na fada musu ne na ce to su dauka bari.
In zo in kwashe kayan na wardrobe din. Ya ce,

A'a, gado kawai da katifa za ta dauka. Na ce, Shi
kenan, Allah ya rufa asiri. Ashe tashin hankali
yana gaba,sai lokacin bacci, Mujidat ta kira shi a
waya wai tana jin bacci, ya kalle ni muna zaune
kan gado,sannan yaci gaba da magana. To ki
kwanta mana. Ta ce, Ba dakin ka zan kwana ba?
Ya ce, A'a yanzun bani da daki in danginki sun
tafi na kwana adakinki. Mamaki da haushi suka
cika ni, ga kishi kamar in hade raina, na ce, Kuje
dakin naka mana? Yaja tsaki tare da cewa, Don
Allah ki bar wannan maganar. Na kwanta tare da
juya bayana na rungume yarana bankara
sauraron shi ba, shi ma ya kwanta a daya gefen
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Washe gari tun Asbahi suka soma shiri,suna
karyawa suka tafi, wata daya ce daga cikinsu
kadai ta yi min sallama da godiya, suna kama ina
zaton yarta ce dake illorin din, domin nayi
dawainiya dasu sosai ta fannin abinci. Ya tsaya
da su sun shiga gurin Iya sun gaisa duk da cewa
ba sa jin yaren juna, sannan ya wuce dasu zuwa
gareji. Ranar ne matan Yaya Sulaiman da su Anty
Abida sukayi ta zuwa ganin Amarya. Anty Abida
ta yi ta yi min fada wai ya zan sa abu a cikin
raina ga shi nan duk na rame, na ce Anty dole in
sa a raina, ba za ki fahimci zafinkishi ba, duk irin
bayanin da zan yi miki, kuma bana fatan a yi miki
ki ji.Anty Abida tace, Ameen,don Allah ina son ki
saki ranki. Amarya dai tana daki bata fito ba, da
za su tafi na raka su ganin amarya ta ci rigarta
da wando na bakin Jeans, danta yana cikin gadon
shi ta yi ruf daciki kan gadon da suka kafa tana
chatting, a yatsine ta amsa sallamar,sannan aka
gaisa,suka yi fatan alkhairi suka fita.
Daran ranar ne ya hada mu a falo yana yi mana
nasihar zama lafiya, sam ban san me yake cewa
ba, ina can gurin tunani. Yau ga shi abin da nake
karantawa cikin littattafai ya zo kaina, ji nake

tamkar cikin mafarki, ashe dai nima za a min
kishiya. Girgiza nin da yayine ya sa na dawo cikin
hayyacina,cikin damuwa ya ce, Menebe? Na
girgiza kai ba komai. Ya ce, ina tambayar ki game
da kwana,na ce, Nawa nawa? Nayi hamma
kirkirarra, sannan duk yadda kace. Ya ce, To a
bar shi bibbiyu kamar yanda aka fi yi. Na ce shi
kenan. Ita dai tana ta jijjiga danta,na sake kirkiro
hamma, zanje in kwanta bacci. Ya kalli agogon
bango; Da wuri? Na ce, Na gaji ne. Na kalli
amarya wadda ta sha leshi kai ya ji gashin doki
ya zubo har kafada, na ce, Sai da safe,ta dube ni
da 'yar yatsina eh, dama ban jira amsar ta ba na
yi tafiyata. TABDI! Daran ranar kasa bacci na yi
har zuga ni zuciyata ta dinga yi wai inje in labe
inji me suke yi, amma sai na fi karfinta inda na
yo alwala na yi ta sallah in nagaji in dauki
Alkur'ani nayita karantawa,sai da na yi sallar
Asubahi sannan na kwanat. Allah ya taimake ni
yarana suna cikin hutun makaranta ne, don haka
da na tashesu muka yi sallah sai muka koma.
Ban farka basai tara, ina tashi Mama ta tashi, sai
da na yimusu wanka sannan muka
fito.....zandakata anan zuwa lokaci na gaba,fatan
zaku kasance tare dani
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347


Darajar Yayana3-03
Posted by ANaM Dorayi on 12:12

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0