Showing 6001 words to 9000 words out of 31162 words

Chapter 3 - Darajar Yayana 1 Complete By Halima Abdullahi K Mashi .pdf

iyaye in wata matsala ta
gifto muku ku daina sa'insa gaban 'ya'yanku, don
gudun lalacewar tarbiyyarsu, tare da jefa rayuwar
su cikin rudani,Tun daga ranar dayace min yana
tafe nayi ta hada abubuwana ina sha , yanxun
ma zumata na samu na kada kwaina na hada na
shanye.Sabon wanka nayi na saka sabuwar rigar
baccin daya zaba in a fitar da mukayi, yanxun na
kama gashina shi kam yana falo yana kallon
labarai a tashar Aljazeera,Yara tuni sunyi bacci,
ban fito ba nima sai nabi kan gadona na fada
tsakiyar gadon nayi kwanciyata.Da zai yiwu in
bada labarin daran ranar kila da nan zan kare,
domin ya shiga sahun tarihin da ba zai gogu ba a
zukatanmu.A cewar yaya, daran ya dara na
farkonmu.Da safe mun tashi tamkar sabon aure,
cikin kwalliya muke aiki tare dashi a kicin.
kwanaki biyun da Yaya ya yi sai da na rubuta su
cikin dan kundin adana mahimman sirrikana. Da

zai tafi har kuka nayi. Allah sarki rayuwa,mun
koma tamkar da har mun fi da kyau,rayuwar
aure d zaman lafiya gami d soyayya akwai dadi.
Tuni Aliyu ya mantar da ni abinda ya faru a baya.
Kuma ko na tuna bana jin haushi,don na dauke
shi matsayin jarabta. Sai dai fa duk lokacin da na
tuna cewa wata tana can dauke d cikinsa ina
tsorata da abinda zai biyo baya. Kwatsam sai ga
shi anyo ma Yaya transfer zuwa Abuja.mun yi
murna don ganin Abuja ni ke tamkar kaduna,
tunda ya koma nan ba ya jimawa bai zo ba. Wata
rana har can Abujar ya kan tafi da mu muyi
hutun karshen mako. Rayuwa dai ta jin dadi
muna ciki. Kwatsam wani yammacin ranar Talata
ina tsakar gida ina kwashe shanyar kayan
makarantar yara da na wanke. A jikina ina sanye
da doguwar riga mai hade da hula blue da ratsin
fari,sai naji ana buga min gida, na nufi kofar ina
tambayr kaina ko wa ye?? Ina budewa muka
hada ido da ita, gabana yayi mummunar faduwa.
Ina zaton ko cikin duhu na ganta zan gane ta,
bare a haske,domin na sha ganin hotunanta cikin
facebook, tana sanye d doguwar riga ja hade d
mayafinta. Sannan tana janye d akwatinta, ga
wata ta rataya a kafada. Na dake na sake
dubanta. 'Malama daga ina? Kuma wa ki ke
nema? Ta ce, 'Nan ne gidan Aliyu Tukur jami'in
dan sanda? Na ce, eh nan ne. 'Sai naga ta turo
kai, na ce 'Ba ki minbayani ba kina kokarin shige
min gida. Tayi min wani kallo sama da kasa, 'Ni
bakuwarshi ce, Allah yasa yana gari? Na maida
kofar na rufe,tare d cewa 'Bayanan yana Abuja,
lafiya? Ta nufi ciki. Zo ki nuna min inda zan
zauna, a gajiye nike, don na wahala kafin na
gano gidan. Falo na sauketa duk da tafasar da
zuciyata ke yi, amma na danne har ruwa na
bata. Sannan na zauna na kalle ta. 'Baiwar Allah
daga ina ki ka zo neman Maigidana? Ta gyara
zama 'Ciki ya yimin,ta fada a gadarance ba tare
d jin wani nauyi ko shakka ba, ni kuwa duk da
cewa nasan batun sai da gabana ya fadi da jin
furucinta. nace, 'Ciki? Ta ce 'Eh, shi ne don
wulaqanci ya ci moriyar ganga zai yada

kwauronta? Bai isa ba. Sai yasan ya taba annoba.
Raina ya soma daukan zafi a gurin,na daga waya
na kira shi,ringing din farko ya daga tamkar yana
zaman jiran kirana ne. Ya ce,'Ya ya dai my
choice? Don in nuna ma Mujidat ban damu ba,
na ce 'Sweety kayi baquwane,da sauri ya ce,
Daga ina? Na kalleta tamkar ban san ds batunta
da shiba, na ce ya ce daga ina? Ta miqo hannu
'Ba ni wayar. 'Nayi 'Yar dariya. Ke ba ki d wayar
ne? Fadi kawai daga inda kike in sanar dashi.
Cikin son ta tura min haushi ta ce, fada masa
wadda yayi ma ciki ce. Kalmar tana dukan kirjina
in ta furta, amma na dake na ce 'Wai wadda ka
yi ma ciki ce. Na karasa zance da dariyar bakin
ciki. Da sauri ya ce, 'Mujidat? Subhnllhi! Lallai
wannan 'yar iskar tana son jaza min bala'i ne. Ta
ya ya ta gano gidana? Na tabe baki tare da cewa,
'Oho' ya ce, 'Kai wannan akwai 'Yar iskar yarinya.
Sadiya don Allah kiyi hakuri kinji? Zan taho yau
din nan kmai dare, amma yanzun ya ya za'a yi?
Na ce, kaika san yanda za ka yi da ita. 'Ya dan yi
shiru yana nazari, duk a rude yake,ya ce, 'Sadiya.
Na ce, 'Na'am, 'Ya ce, 'Kuna tare ne yanzun
haka? Na ce,'Eh. Ya ce, shiga daki muyi magana.
Na ce, To. Na miqe na nufi daki. Na shige Toilet
na rufe, sannan na ce 'Ina jin ka. Ya ce, 'Sadiya
don Allah kiyi hakuri kwakwalwata ta toshe, ki
buda min ita ya ya za a yi yanzun? Raina bace
yake matuka, na ce 'Lokacin da za ka yi sabonka
ka nemi shawarata? Don haka sai ka nemi
shedanin daya hure maka kunne ya sa ka a
hanyar da za ka warware matsalar. Ya ce, Sadiya
duk ba wannan zancen ba, yara na gida tayi
magana? Na ce, 'A'a suna islamiyya. Ya ce, 'Ok,
yanzu yaya za ayi? Na ce, 'Wallahi ban sani ba, ni
dai bani da dakin da zata kwana sai dai in
dakinka. Ya ce, 'Zan taho yanzun nan zansa
jami'an tsaro su kulle min ita. Na ce, 'Kana ganin
wannan mafita ce? Yarinyar nan irin 'yan iskan
nan ne ma su tutiya da iskancinsu. A shirye take
d ta shelanta ma duniya ita farkarka ce, kuma
tana da cikinka.ka shirya zubewar mutuncinka? In
ka shirya ka zo ka bi ta d zafii in ko kana son

tsira d dan ragowar mutuncinka,to koka tabbata
za ka bi ta ne da lalama ka kuma yi mata adalci
tunda lokacin daza ku yi shedanar ba ka
juyamata baya ba. Na kashe wayar tamkar in yi
kuka, amma sai na fasa don bana son wannan
Mujidat din ta fahimci abinda ta zo dashi ya daga
hankalina. Ko kuwa ya dadani da kasa,don na
lura 'Yar bariki ce.nasame ta inda na barta sai
dai yanzun ta dan kwanta akan kujerar. Na dube
ta 'ya ce ki jira shi yanzun zai baro Abuja,kina
buqatar wani abu yanzun? Ta ce, 'A'a bana jin
yunwa na ci abinci a gidan cin abinci. Na wuce na
ci gabad aikina sai dai kunci da takaici a zuciyata
ba a magana.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Shida daidai yara suka dawo Islamiya kallonta
suka dinga yi sannan suka gaishe ta. Ta ce yara
masu kyau,ina kausar?Ta ce, 'Gani. Mujidat ta
ce, Yar lelen Babanta duk ya fi ambatar ta cikin
yaran. Kai ne Al'ameen? Ya ce, 'Eh. Ta ce, 'Ka yi
min kyau, kana kama da babanka sai ka shiga
raina. Ta dubi Mama ta yatsina fuska, 'Ke ce mai
kama d mamnki ko? Sunfi ki kyau, Allah yasa
babyna ya yi kama da..............'' Da karfi na
daka mata tsawa 'Ke! Mahaukaciyace? 'Na kalli
su kausar, ku je dakin ku ku cire kaya ina zuwa.
Na dubeta bayan shigarsu daki,mekike shirin
fadawa yarana? Kina so ki fada musu kina da ciki
da babansu? Ta 'Eh ai dole su sani ko da ban
fada musuba, domin a gidan nan zan haife shi.
Na runtse ido don baqin ciki na bude tare da
furzar da takaicina ta baki, na ce ba zan hanaki
ki haihu a gidan nan b, sai dai zan gargade ki kar
ki sake ki fadawa yarana maganar data fi karfin
tunaninsu, kin gane? Ta yi 'Yar dariya,sannan ta
ce, Bani da magana dake bare ki sa min doka,
mijinki nake jira. Haushi ya turnikeni har na kasa
tsaida shi na ce, 'Mijina fa nawa ne kar ki ga na

miki tarbar mutunci ki za ta shakka ce, in na ga
dama ba ki ganin mijinnawa, sannan dole ki bar
min gidana. Ta saka dariya, sannan ta debi
kafafunta ta zuba kan kujerata kuma kallona
sama d kasa,sannan ta ce.........zandakata anan,
zakuji zarar Allah yanufa..
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347


Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100


Darajar Yayana3-03
Posted by ANaM Dorayi on 12:12 AM, 04-Apr-16
Under: DARAJAR 'YA'YANA
__________________NA
___________HALIMA K/MASHI
Assalamu'alaikum,akaro na barkatai gani na dawo
domin kawo muku cigaban labarinmu ,fatan kuna
sane da inda muka tsaya.
Yayi shiru. Na ce Hello, kana jina? Eh, kin fadawa
Iya ne? Na ce, nanmuka amshi haihuwar tare,
Kasan cewa taso ta gano cewa danka ne? Dan
yaron yayi kama da kai fiye da duk yaran gidan
nan.Da karfi yace Haba dai! Wlh, yaushe zaka zo?
Yayi dan tsaki, gaskiya bani da ranar zuwa, zan
turo miki kudi kiyi duk abinda ya dace. Nace,
zuwan ka yana da muhimmanci, sabida Mujidat
zata iya tana komaifa, inbata gankaba. Ya ce, to
zan zo kafin suna inkuma dawo
Gurin aikina. Nace to saikazo. Na kira auntyAbida
na fada mata, haka ma Aisha kawata.Makota duk
suna ta shigowa Barka. Su kausar ma nasa sunje
sunga baby,na fada musu cewa kaninsune, suna
ta murna har da kausar. Aisha ranar datazo
barka tana daukan yaron tace, kai Sadiya yaron
nan yana kama da Abban kausar. Nace, haka ake

ta cewa, dama kin san mutane sun ce in mai ciki
tana yawan kallon mutum ta kan haifi mai kama
da shi. Ta yi Yar dariyar yake,tare da cewa,
hakane kawata.Mai jego kam ina kallon ta sai
harara take watso mana. Muna shiga dakina
tace, Sadiya anya kuwa ba kanshin gaskiya a cikin
lamarin matar nan? Kin san halin mazannan ko
dai Dan sa ne? Ki yi hakuri kamarce naga tayi
yawa. Nace, hum! Ke dai bari kawata, tsakanina
dake nasan amanace, wlh dansane ciki yayo
mata, yanzun data haihu zasuyi aure. Aisha
amana na fada maki ko iya bata San wannan ba.
Aisha ta zabura tare da fadin, kan uba! Lallai
Sadiya ban taba sanin cewa Ke sakarya bace sai
yau, yayowa wata ciki sannan ki yarda ta zauna
maki a gida? Wallahi da ace nasan haka ne in
nazo barka shegiya nake,kin ma daure masa gindi
kenan gobe ya kara.Na ce, Aisha ki fahimta, uban
'ya'yanane,mijina kuma yaya zanyi? Nawa ganin
rufin asirinshi Nawa ne, kuma na yara nane. Ta yi
tsaki bana Jin zan fahimceki, in tazo gidan ta
koreki kin ga ai sai kiji dadin rufa masa asirin. Na
ce, nasan dama bazaki fahimceniba, shi yasa tun
farko ban sanar da Ke ba, dan na sanki. Ta dauki
yarta tasa a baya,ta suri jakarta da hijabinta, Ni
kin ga tafiyata. Na bita ina fadin, "Dan Allah
Aisha ki saurareni. Ki tayi ta tafi abinta. Na ce to
shi Kenan in kin huce za muyi waya ta ce ni kar
ki kira ni. Na dawo daki na kwanta kan gado ina
hawaye, in na tuno Yaya zasuyi aure da Mujidat
Abin na daga hankalina ya kuma sani kuka.
Ranarr da suka cika kwana 5, sai ga Yayakusan 10
na dare, Ni ce ma na bude masa kofa, ya janyo
ni jikinsa,ni kaina bansan me yasa jikina yayi
sanyi ba kuma banyi wani farinciki da ganinsa ba.
Ya dago fuskata, sannan yahaskani da wayarsa,
lafiya my choice? Na sa hannu na tare
hasken,lafuya mana Yaya mai ka gani? Na karbi
jakar hnnunsa tare da cewa sannu da zuwa,bai
amsa ba sai dai ya ce, na ganki cool ne, kamar
ba kiyi farin ciki da gani na ba. Na ce, bacci na
fara. Sannan nayi gaba na bude masa daki ya
shiga. Ya zauna bakin gado tare da fadin, na gaji

yau Sosai,8 ta wuce na baro Abuja, kuma da safe
zan wuce na zone Kawai sabida kin nuna zuwan
nawa yana da muhimmanci. Na ce, to Kayi wanka
zaka warware. Ya ce to. Kafin ya fito wanka na
kawo masa tuwo daman shi nayi a daren miyar
zogole. Sai da yaci na fitar da kwanukan, sannan
na shiga gurin Mujidat tana zaune da waya tana
chatting, na ce, ya kamata fa ki dinga bacci. Ta
ce, ba zan yi hira da kawayena ba? Na ce, kuyi
tayi, akawo yaro babanshi yazo. Ta kalli yaron
sannan ta kalleni, ya yi bacci. Na Isa gurin yaron
na dauko shi, ban tsaya jiranta ba na kai shi.
Aliyu ya mike tsaye zumbur likacin da ya kalli
yaron duk yadda Sadiya Ke bashi labarin
kamannin shi da dan bai zaci har hakaba. Ya kalli
yaron kusan minti 1, sannan ya miko mini tmkr
yana tsorace,na maida hannuwana baya. Kayi
masa addu'a kamar sauran yaran ka duk dadai
baka samar da shi ta hanyar da shari'a ta
amince ba, sannan ka yi masa hudu ba,ya daga
murya rikeshi mana Sadiya. Na juya na fita. Abin
mamaki sai ga Mujidat labe tana lekenmu, na
tsaya turus ina kallonta, ita ma ta yi tsuru-tsuru
na ce, a'a dama kina min labe? Ta soma Sosa kai,
sai kuma ta shiga borin kunya, kin zo kin
daukarmin yaro ba dole inbiba? Na ce, kina
zargin zan cutar miki da yaro ne? Yaya ya fito ya
mika mata yaron "ungo yaron ki kar ku tada min
da yara suna bacci. Ta amshi danta ta tafi, ni
kam a gurin na tsaya na ma rasa tunanin da
zanyi, tun yanzu kenan kafin a daura Auren? Shi
kam bai so yanda ya yi ba kada ma mu tada
masa yara suna bacci, maimakon ya gargadeta
kan cewa Kar tasake yi min labe, bai yi hakan ba
sai ya shige abinsa. Ni kam dakin yarana na nufa
amman ko zama ban yi ba sai ga kiranshi, sai da
wyrta kusa tsinkewa sannan na daga. Meyene?
Yace, zomana,sai da na dan bata lokaci, sannan
na je. Kai kawo na samu yana yi a cikin dakin,
ina shiga ya nufo ni ya kama hannuwana. Sadiya
asirin da muka rufa zai tonu sabida kamannina
da yaron nan ya dauko,ina ganin gara mu fadawa
Iya Kawai ita kuma Mujidat ta yi tafiyarta tunda

dama dan Kar Iya su sani ne zan aure ta, ni
wallahi bana son ta, zata iya tarwatsa min iyali,na
zame hannuna daga nasa na zauna bakin gado
tare da rike kaina na ce, Yaya ba dan Kar asirin
ka ya tonu Kadai ba ne na ce ka aureta, don
gudun kada kuci gaba da haihuwa a titi babu
aure, don nasan bazaku rabuba. Shima ya zauna,
sai dai in itace baza ta rabu dani ba Sadiya,
amman wallahi ni tuni na barta,na girgiza kai,
Yaya yin Aurenku yafi a kan barin shi, don
Mujidat ta tabbatarmin da hakan kuma na San
zaku iya... hawaye suka soma zubomin cikin
rawar murya na ce. kuma duk laifin kane. Ya
kwanto ni jikinshi, wallahi Sadiya nayi nadama
matuka, kuma naji kunyarki Sosai ki yi hakuri
kidaina kuka, Kecefa kike Karfafa min gwiwa,kike
bani shawara. Ya dago fuska ta. Hankalina
yatashi da yawa ganin kamannin yaron
nan,nasan sai dai mutane su ji mu Kawai,
ammababu wanda zai yarda cewa ba yaro na
bane. Ya share min hawaye. Ki yafe min. Na ce,
Yaya ni dai alfarma Kawai zan roka a gurin ka
guda biyu. Da sauri ya ce, na miki alkawarin yi
miki su fadi inji.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Na ce, na farko duk rintsi kada ka juya min baya
ko ka wulakanta ni. Ya rike kafaduna muna kallon
juna, insha Allahu Sadiya ba zan miki ba ko bisa
kuskure insha Allahu. Nace sai na biyu, izini zaka
yi min in nemi koyarwa a makaranta, ko L.E.A ta
nan unguwar Mu'azu. Ya yi shiru yana nazari, can
ya ce, kin gane Sadiya ba wai ina son hanaki
bane, nafison ki nutsu a gida wallahi bana son
matata tana yawo. Na ce, akwai dalilina, ka ga
Kwanan nan zamu zama mu biyu a Kasan ka,
duk wata bukata da zan nema a wurinka dole ne
ka yi mana mu biyu, inko inada nawa zan yi
bukata ta ba tare da na takuraba. Ya ce, wannan

bai kai dalilin da zan bar ki ba sai dai in bar ki
sbd tun farko na amsa cewa nayi miki alfarmar
da kika nema,da dai tun farko na san wannance
alfarmar da bazan yardaba, sai dai kimarki ta
wuce in amince, sannan in dawo in ce a'a, kije
kiyi koyarwa ki, amma ki tsare mutuncinki da
nawa.Na sauke ajiyar zuciya 'nagode mijina, Allah
ya saka da Alheri. Ya lumshe ido sannan ya
bude. Yanzu wane suna za'a sa masa?
Na ce, a'a wannan shawarar tsakaninkane da
Mujidat, da safe ka sameta ku tattauna. Bai ce
kalaba sai ya kwanta rigingine.
Da safe falo ya zauna yace in kirata,ta fito tana
yatsina cikin Riga da wnd ta zauna, ya ce, wane
suna kika zaba? Ni kam mikewanayi. Ya ce,zo
mana My choice. Na ce, ina zuwa. Dakina nashiga
na bar su dan zancen na su ne.Ta mike daga
Inda take ta koma kujerar da Ke daf da shi ta
ce,Sweety kaine zaka bashi suna in dai nice nafi
son sunanka don yaron yafi kama da kai. Darling
kabiyani dakabani mai kama da kai. Ya waiwayo
ya daga mata hannu, tsaya!baki dacikakken
hankali ko? Ni ne nake bada haihuwa?Ki sawa
yaron ki duk sunan da kike so amma ban da
nawa kin gane ko? Ta ce, to ina son a samun
Abdul-kareem. Ya ce, ya yi Allah yaraya shi.tace
ameen. Sai maganar auranmu. Ya mike tace, na
zata tun ranar dana haihu zamuyi maganar shine
yanzu na kawo maganar za ka tashi? To bari kaji
daurin auren nan in ya wuce gobe za ka ji
mamakin abinda zai faru.Ya shigo daki, ina jiyo
duk yadda sukayi nace, Yaya ka amince nima ina
son a daura a wuce gurin kawai,ya ce, ba zanyi
yanda takeso ba, tana ganin itafa wata cikakkiyar
marakunyace. Bata San cewa ina daga mata kafa
bane sabida Ke,nace, dan Allah kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0