Showing 21001 words to 24000 words out of 31162 words

Chapter 8 - Darajar Yayana 1 Complete By Halima Abdullahi K Mashi .pdf

karatun Alkur'ani mai
girma, ki zauna da ita zuciya1, sannan ga aikin ki
ma, ai ni naji dadin barin ki da yayi wannan
koyarwar, na ce, nima naji dadi iya, don ina da
yara gara dai yanzu da muke mu 2 aikin ya dauke
masa matsalolina in ina samu ba sai na jira shi
ba, kudin da ya bani ma nawa da yara wai muyi
siyayya su dai na Dan sai musu wani abu, so
nake in hada jari in dinga saye da siyarwa. Iya
tayi dariya tare da cewa, da kyau Sadiyayyena.
Haka nayini Iya tana kwantar min da hankali tare
da bani shawarwari sai kusan 10 na dare na debi

ya'yana ta raka mu har gida, nima na sake rako
ta hanya.ina sa hakarkarina a kan gado na dauko
wayata nakunna dama yinin ranar kashe ta na yi.
Nan fa sakonni suka soma shigowa na yaya sai
na Aisha da Anty Abida, na su na soma dubawa.
Tanbayata suke ina naje sun zo ba nanan? Na yi
dan murmushi, a fili na ce da kun zo gidan Iya ni
kam ba zan yi wani taro ba, sai na soma duba
nashi,duk kusan yana nuna damuwane akan ya
kira bai sameni ba. Sai na karshe da yake cewa
sun taso 9 suna hanya, akwai yiwuwar su iso
kafin 9 na safe, kuma suna tare da wasu daga
danginta dan Allah ta tanadar musu abinci. Kiran
Abida ya katse karatun sakon da na keyi, na daga
muka gaisa, ta ce min, ina na shige yau? Na ce
ina gidan Iya,tace to, ki yi sammakon tashi don
mijinki zasuyi shigowar safe ne, nace Anty me
zanyimusu?tace karin kumallo mana kiyi zuciya1
kada ki sa kishi ciki, bakin kine, kin kuma san
darajar baki a musulunci. Na ce to Aunty zanyi.
Tin 4 na tashi na fara firar dankali da nayi sallah
kuma na hau suya, har kaji biyu nayi musu
farfesu, kwai ma isasshena yi musu kwai da kwai
na dafa ruwan tea mai yawa, sannan na gyara
gidana nayi wa yara wanka na zabo musu
sababbin kaya nima na sheka nawa adon.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Takwas daida na ji tsayawar motoci,gabana ya
yanke ya yi wata muguwar faduwa,sai na hau
karanta Hasbunallahu wa ni'imal wakil. Na mike
na je na bude musu kofa gabana yana ta
faduwa,zuciyata tana maimaita addu'a.suka shigo
suna yi min sannu, wasun su suna kallona wani
iri,amma duk da haka na saki raina ina yi musu
sannu da harshen Turanci.Najee na bude musu
dakin suka yi sororo a tsakar daki don ga
al'adarsu miji ke shiryawa mace daki ya zuba
komai, ita kuma iyayenta su yi mata kayan sawa,

nan fa suka soma yare, duk da bana ji amma
ganin yanda suke magana suna tabe baki na
fahimci zancen nasu bana dadi ba ne, naje
nasoma fito musu d kuloli. Sai gasu Yaya sun
shigo, na kirkiro fara'a ina yi musu sannu da
zuwa. Falo suka je suka zauna na gabatar musu
suma da abin kari, na kula yaya ya ji dadin
yanda na saki jikina na kuma yi musu abin
kari.Nan nabarsu nayi daki,bayan Mujidat da
danginta sun gama karyawa sai suka samu su
Aliyu da Usman suna yi musu korafin ba su ga
kmai a dakin ba.Usman ya ce, Mu a nan da kaya
amarya take zuwa. Suka ce su kam ba haka ba
ne, nan suka fito masa da akwatunan amarya
har da na mijin da na Maman shi da kuma na
danginsa. Aliyu ya ce shi kenan zai siya daga
baya, amma yanzun a kwaso na dakinsa a sa
mata,sukace bakomai. Ina dakin nashi ya shigo
wanda zuwa yanzun ya zama nawa,ya zauna.
Sadiya kin ji wata sabuwa. Na kalle shi, ya ce,
Wai ni zan sai mata gado. Na ce, ina zaton haka
al'adar su take don mun taba yin zancen da wata
'yar ajinmu da muka yi N.C.E take ba mu labarin
al'adunsu, miji ke yin kayan daki kuma sadakin
su yana da tsada, amma mace za ta ja jari da su
ita ce za ta rike gida,wasu kuma jarin daban miji
zaibada, wadanda ba Musulmi ba sun fiyi,
Musulminsu kamsai sunyi aure suke tarewa gidan
mazajensu,yace,nidai yanzun ya za'a yi? Na ce su
zo su dauki wannan gadon. Na tsura masa ido
cikin mamaki,sai ya ce, ko ya ki ka gani? Na mike
na nufi dakina bayan na ce, Me zan ce kai da
abinka. Na shiga dakina na soma kallon dakin ina
lissafa yanda zan gyara shi ni da yarana da na
bar musu gadona tunda dama katifu gare su. Sai
ga shi ya shigo.Haba Sadiya,me zai sa ki
yankemin wannan hukuncin? Nazo miki da
shawara amma sai ki yi watsi da ni kitaho abin
ki? Na ce, Yaya kainefa da abinka kuma ka ba
matarka, mene ne laifina dan na taho? Yace, Ok,
kije amma ki sani kada nan gaba ki ce na daina
kawo miki Shawara,kin sani dai ke ce kurum nake
tunkara da duk matsala ta. Shiru na yi dan nasan

in hakan ta faru lallai ba zan zama uwar gidaba.
Ya mike zai fita na ce, Yaya'' ya dawo,Mene ne?
Na ce, Shi kenan ka yi hakuri. Ya zauna tare da
kamo hannuna, Nagode da ki ka fahimce ni,
yanzun ya ki ke ganin za'ayi? Na ce, Ka ba ta,ni
kawai sai naringa kwana a nan da yarana. Ya
tsura min ido, To nifa? Na ce, Ba komai ka yi ta
kwana dakinta. Ya yi dan murmushi, Har yanzun
baki huce ba.Na yi 'yar dariyar yake, Bana fushi
da kai. Yace, Zan siyo katifu yau a sa can dakin in
komai ya warware zan canza gadajen gidan.Na ce
to maimakon ka ba ta tsohon gadon ba gara ka
sai mata katifar ba? Amma yanda ka gani, Ya ce
na riga na fada musu ne na ce to su dauka bari.
In zo in kwashe kayan na wardrobe din. Ya ce,
A'a, gado kawai da katifa za ta dauka. Na ce, Shi
kenan, Allah ya rufa asiri. Ashe tashin hankali
yana gaba,sai lokacin bacci, Mujidat ta kira shi a
waya wai tana jin bacci, ya kalle ni muna zaune
kan gado,sannan yaci gaba da magana. To ki
kwanta mana. Ta ce, Ba dakin ka zan kwana ba?
Ya ce, A'a yanzun bani da daki in danginki sun
tafi na kwana adakinki. Mamaki da haushi suka
cika ni, ga kishi kamar in hade raina, na ce, Kuje
dakin naka mana? Yaja tsaki tare da cewa, Don
Allah ki bar wannan maganar. Na kwanta tare da
juya bayana na rungume yarana bankara
sauraron shi ba, shi ma ya kwanta a daya gefen
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Washe gari tun Asbahi suka soma shiri,suna
karyawa suka tafi, wata daya ce daga cikinsu
kadai ta yi min sallama da godiya, suna kama ina
zaton yarta ce dake illorin din, domin nayi
dawainiya dasu sosai ta fannin abinci. Ya tsaya
da su sun shiga gurin Iya sun gaisa duk da cewa
ba sa jin yaren juna, sannan ya wuce dasu zuwa
gareji. Ranar ne matan Yaya Sulaiman da su Anty
Abida sukayi ta zuwa ganin Amarya. Anty Abida

ta yi ta yi min fada wai ya zan sa abu a cikin
raina ga shi nan duk na rame, na ce Anty dole in
sa a raina, ba za ki fahimci zafinkishi ba, duk irin
bayanin da zan yi miki, kuma bana fatan a yi miki
ki ji.Anty Abida tace, Ameen,don Allah ina son ki
saki ranki. Amarya dai tana daki bata fito ba, da
za su tafi na raka su ganin amarya ta ci rigarta
da wando na bakin Jeans, danta yana cikin gadon
shi ta yi ruf daciki kan gadon da suka kafa tana
chatting, a yatsine ta amsa sallamar,sannan aka
gaisa,suka yi fatan alkhairi suka fita.
Daran ranar ne ya hada mu a falo yana yi mana
nasihar zama lafiya, sam ban san me yake cewa
ba, ina can gurin tunani. Yau ga shi abin da nake
karantawa cikin littattafai ya zo kaina, ji nake
tamkar cikin mafarki, ashe dai nima za a min
kishiya. Girgiza nin da yayine ya sa na dawo cikin
hayyacina,cikin damuwa ya ce, Menebe? Na
girgiza kai ba komai. Ya ce, ina tambayar ki game
da kwana,na ce, Nawa nawa? Nayi hamma
kirkirarra, sannan duk yadda kace. Ya ce, To a
bar shi bibbiyu kamar yanda aka fi yi. Na ce shi
kenan. Ita dai tana ta jijjiga danta,na sake kirkiro
hamma, zanje in kwanta bacci. Ya kalli agogon
bango; Da wuri? Na ce, Na gaji ne. Na kalli
amarya wadda ta sha leshi kai ya ji gashin doki
ya zubo har kafada, na ce, Sai da safe,ta dube ni
da 'yar yatsina eh, dama ban jira amsar ta ba na
yi tafiyata. TABDI! Daran ranar kasa bacci na yi
har zuga ni zuciyata ta dinga yi wai inje in labe
inji me suke yi, amma sai na fi karfinta inda na
yo alwala na yi ta sallah in nagaji in dauki
Alkur'ani nayita karantawa,sai da na yi sallar
Asubahi sannan na kwanat. Allah ya taimake ni
yarana suna cikin hutun makaranta ne, don haka
da na tashesu muka yi sallah sai muka koma.
Ban farka basai tara, ina tashi Mama ta tashi, sai
da na yimusu wanka sannan muka
fito.....zandakata anan zuwa lokaci na gaba,fatan
zaku kasance tare dani
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347

Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100


Darajar Yayana3-04
Posted by ANaM Dorayi on 07:21 PM, 06-Apr-16
Under: DARAJAR 'YA'YANA
_________________NA
___________HALIMA K/MASHI
Tun a falo nasan cewa masu gidan sun jima da
tashi,domin ga gurin da aka karya nan ba a
kwashe kayanba,na shiga kicin na soyo wayara
dankali da kwai, dama ni ban damu in ci wani
abuba don bana jin yunwa, na hada musu Tea
sannan ni kuma na sha ruwan Lipton, na
kwanta ringine ina karanta wani post da Sheik
Daurawa yayo a facebook, sai ga shi ya shigo,
idanuna basa san kallonshi, ina jin su Kausar
suna gaida shi ya amsa tare da sumbatar su a
goshinsu su duka, sannan ya zauna bakin gado
kusa da ni. My choice,ina ta shigowa kuna bacci
da yaranki. Ban tanka masa ba ya ce, An tashi
lafiya?
A ciki na ce, Lafiya lau. Ya ce, ke kin ci abincin
ne? Na ce Um, ya yi shiru yana tunanin me zai
ce, ni ko da zai fita ma zan fi so. Sai ya ce,
yauwa am, Sadiya jiya namanta ba mu yi
magana ba. Ba tare da na dago ba na ce
inajinka. Ya ce yanzun wane hukunci zamu dora
Mujidat ko in ce ina za mu ajeta? Budurwa ko
bazawara? Yana cewa haka na fuskanci nufinshi
wato kwana nawa zaiyi, zuciyata ta soma
tafasa,amma sai na fara karanta addu'a, na
tashi na kalle shi. Mujidat budurwa ce, don
haka sati daya za ka yi a dakinta, garabasa ma
dazan yi maka ita ce ka gama hutunka kaf a
dakinta. Ya ce, a'a ban yarda ba. Na koma na
kwanta ba tare da na kara cewa komai ba. Ya
amshi wayar hannuna yana cewa. Me ki ke gani

ne cikin wayar ki, wanda ya fi ni? Juyowa na yi
ina kallon shi,sai da ya gama karantawa,sannan
ya ce, Banace kirufe wannan account din ba?
Bana son kina hawa facebook fa. Yayi maganar
tare da dan hade rai. Nace, To ni menakeyima a
facebook din? Daga ganin abin da duniya ke ciki
sai post din malamai,sai ko gidajen da akabude
dan wayarwa da mata kai. Ya ce, Duk da haka
dai na ce ki rufe zan sai miki kasunan wa'azi in
namu sun miki kadan, sannan zan baki kudi ki
sai littattafai na wayrwa da mata kai din,
huldarki da internet din ne ba na so,ban
amsaba,shi kuma ya fice. A raina na ce ka zaci
abin da kakeyi a internet din haka kowama keyi?
Na ajiye wayar batare da na goge ba, sai dai
cikin zuciyata na dauki aniyar gogewa,amma ba
yanzu ba. Duk zatona da naganta kicin tana girki
duka gidan za ta yi, amma sai na ga ta juye
kula daya ta nufi dakinta, don haka sai na tashi
nayiwa yarana.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Bai shigo gidanba sai Magriba duk da dai ya
kirani ta waya da rana yace menadafa? Na ce
masa taliya, shi dabagwanin taliya ba ne don
haka sai ya ce to bari ya ci tuwon sa gurin Iya.
Ya sameni daki ina karanta littafin Hausa, su
Kausar suna ta wasa, nan suka tashi suna
yimasa oyoyo, na dube shi tare da yi masa
sannu da zuwa. Ya amsa,sannan ya zauna. Kin
ganni sai yanzun? Na ce, Eh, ina zaton wani aiki
ne ma ya taso maka. Ya ce, A'a, wallahi gidan
ne sam baya yi min dadin zama duk jina nake a
takure, shi yasa naso in sayi wancan gidan ga
shi duk na kashe rabin kudin.
Dariya ta subuce min cikin zuciya nace ai ba a
banza aka kashe ba,tunda aure kayi, ko ba nan
kudin suka wuce ba? Shiru ya yi tunda ya san

bai fada min cewa kudinsa sun wuce a gurin
auran Mujidat ba, sai ma ya dauko wani batun.
Yauma baki cemin lesukan nan sunyi kyau ba?
Nace, Na fada maka mana, ka dai manta ne ko
dai anan kakashe kudin? Da sauri ya ce, A'a ni
ban ce ba. Wayar shi ta soma ruri ya dauka, sai
na ji ya ce, Ke ina zuwa nafa shigo gidan. Ina jin
haka na san cewa Mujidat ce, a raina naji zafi
mijina wata ke kira kuma tana da damar yin
hakan, jin hawaye na son zubo min sai na mike
na shige bandaki tare da cewa, Bari in yo
alwalar Isha'i.
A dakin Mujidat Aliyu ya zauna idanun shi yana
kallon Abdul wanda daga jiya zuwa yau ya soma
son dan shi, ita kuma tana kwance rufda ciki
tana chating ya sa hannu ya amshi wayar, ta
tashi zaune. Honey ban waya ta, muna hira a
group dinmune, don Allah.Ya soma danna
wayar yana dubawa,can ya dube ta, Har da
maza fa na ga kuna hirar? Ta ce, Eh, ba za mu
yi hira ba,'yan group din mu ne fa? Ya kashe
wayar, sannan ya sa ta cikin aljihunsa, ta ce,
Ban gane ba, amma kai ka sai min? Ya ce, Zan
sai miki wata da wani sim din yanzun karkashina
kike ba zan yarda ki yi hulda da kowa ba,tace
Kana nufin har da iyayena,da sauran dangina?
Aliyu ya ce, Bance zan hana ki hulda da
danginki ba, amma sai na tantancesu.taja
tsaki,sannan ta zauna cikin fushi, ya isa gabanta
yasa yatsunsa ya damki lebenta, Kar ki sake yi
min tsaki sabida yanzun ni mijinki ne yana da
kyau kisan darajata. Taji zafin yanda yayi mata,
har ta yi 'yar kara sannan ya saki ya kuma fita.
Na yi hakuri tare da cijewa gami da kau da
kaina game da Yaya da matarsa.Ranar da ya
cika sati dayama nace nakara masa wani
satin,amma ya ce sam ba ya so. Kafin hutun shi
ya kare wani aiki ya taso don haka ya shirya
komawa ya kira mu falo ya ce to ni zan tafi. Ya
kalli Mujidat. Kada ki sake in dawo inji wata
matsala ta faru, sbd in na ga sabon abu daga ke
ne. Na dade dasanin wace ce matata,sannan
duk abin da ki ke bukata ki tambayeta. Sai abu

na gaba bance kitafi ko'ina ba, don baki dakowa
a garin nan, kin fahimta ko? Ta turo baki gami
da bata rai,sannan ta ce yana yi mata gorin
dangi kenan? Ya ce in kin dauka haka to hakan
ne. Ya dube ni, Kici gaba da hakurin da nasan ki
da shi,sannan ki kama girmanki, kamar yanda
kikeyi, inda wata matsala ki sanar da ni,sannan
yau kwanana daya a dakin ki tafiyar nan ta
taso,ina dawowa zan sauka dakinki in yi kwana
dayan da ya rage,sannan in koma gurin ta,nace,
to Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya. Yara ma
ya sallame su, kamar yanda ya saba muka raka
shi har mota,har da Mujidat din sabe da danta
a kafada,duk da ba ta zo kusa da shi ba. Na
ce,baka sallami Abdul ba.nakalli Mujidat, Ki ba
Baban shi su yi sallama. Ya ce, A'a, bar shi
kawai. Ya tada mota, sam ban so yanda ya yi
ba,domin a gabanta ya rungumi sauran yara
tare da sumbatar su, fuu! Ta juya ciki, tun kafin
ya tada motar,nabita da kallo,sannan na
kalleshi. Yaya ka daina haka, yanzun mun zama
daya kuma wannan yaron ka ne kar ka gwada
bambanci ko ka ce za ka yi kara dan ganin
idona na san dai kana son danka,ya tada motar
tare da cewa, Na tafi.Na ce Allah ya tsare.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Gaskiya Mujidat ba ta bukatar muyi zaman
lafiya yadda take mu'amalarta da yarana amma
ni na sawa kaina alwashin sai dai tayi da wani
amma badaniba, duk da cewa na san ban girme
ta ba,amma a gurina zubar da aji ne in tsaya
cacar baki da kishiya,gurin cin abinci dama tun
yana nan bai hana kowa yin na shi ba.Da farko
na so in masa magana kan cewa ya za a ce
muna gida daya karkashin miji daya, amma mu
raba girki,sai kuma na ce bari dai in bar shi
tunda shi ke nemowa.sai kuma ta tsiri fita zuwa

gurin wasu 'yarbawa yarensu,sai ta kai dare.
Randa ta fita na uku na yi mata magana,tana
shiga dakinta na bita. Maman Abdul. Ta waigo
ta dube ni,sannan ta ci gaba da kwantar da dan
ta a kan gado. Na ce,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0